Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

qara taka wuta, namatsu inga Abbana."

Murmushi yayi had'e da d'an juyowa ya kalleta sannan yace.

"Wai! Agaidasu gimbiya, wato kema da kika sharqi baccinki kece kika gaji bani ba ko?, Bawani kin matsu kiga abbanki, kedai kice kin matsu kici abinci wannan uwar hamma da kika buga ai tsaf kan akuya zai shiga ta bakinki."

Hannuwa tasa tad'an duddukesa ga kafad'a yana dariya yace.

"Kai ko, wane kan akuya zai shiga awannan d'an mitsitsin bakin nawa?, ALLAH bana son sheri."

"Bakiga yanda kika bud'esa bane shiyasa, tsaf kan tinkiya ma zai shiga aciki."

Gano salon zolayar tasane ta motsa yasa tayi murmushi had'e da langab'ar da kanta gefe tana cewa.

"Naji d'in, ba dole ba ambar mutum da yunwa fiye da awa hud'u kuma duk ansan dole ajiyarsa zata dami mutum tace itama yunwa, to meye ma idan kan tinkiyar ya shige abakina tunda yunwa nakeji sai nakama abuna na kamtse na cinye."

"Aw abun sharri ne?"

"Eh man, ba yanzu kagama yimun ba nima, kaga narama mun zama 1-1"

"Ai shikenan! Kiyi haquri mun kusa isa saura kilometers biyar in Sha ALLAH"

"To kad'an qara gudu mana sai muyi saurin isa tunda mun kusa kace."

"Ehm.ehm..rufamun asiri, inyi maki ta bakin gwaggo tace uncle, to uncle yace kada muyi gudu, kiyi haquri muqarasa lafiya tunda munkusa isa, SANNU SANNU ai Bata hana zuwa saidai a dad'e ba'a kai ba ko kuwa?"

"Hakane in Sha ALLAH.."

Tana rufe baki sai ga wata babbar mota da alama burkinta ya katse ta nufosu aguje, da sauri little ya koma ta d'ayan hannun ALLAH yasa babu wata mota agabansu tafe ya sauka gefen titi yayi parking gabansa na fad'uwa, yafi mintuna uku aciki yana kallon yanda waccan motar ta fad'i tana qoqarin gangarawa cikin daji ta madubi kafin can ya kashe motar yafito ya nufi wajen yana kallon ikon ALLAH, nan fa sauran motocin dake tahowa wasu suma suka tsaitsaya ana jiran aga yanda sarautar ALLAH zatayi da motar, sai da babbar motar ta dad'e tana juyawa sannan aka samu ta tsaya mutane sukayi ruuu wajen ko za'a iya ceto rayukan wasu, sai gashi koda akaje mutum biyu ne kad'ai a motar daga driver sai na gefensa kuma duka ALLAH yayi masu rasuwa, Saida aka gamo jajantawa sann little yadawo ya shiga motar jikinsa asanyaye yana fad'in.

"Ubangiji ALLAH ya jiqansu da rahama."

Batool da suma kad'aice batayi ba tsabar yanda ta tsorata ta samu daqyar ta amsa masa da Amin, had'e da cewa.

"Duk sun mutu ko?"

"Eh, dayake mutum biyune kad'ai acikin motar sun d'auko kaya da alama legas zasuje."

Yabata amsa yana kallon yanda duk yanayinta ya sauya.

"Kar dai kice mun kin tsoratane?."

"Sosai wlh."

"Ki kwantar da hankalinki kinji ko, in sha ALLAH zamu Isa lafiya."

Sannan ya tada motarsu sukaci gaba da tafiya, har suka iso cikin kano batool bata sake cewa uffan ba gudun kar maganar da zatayi ta d'aukar masu hankali don ta matuqar tsorata fiye da tunani, shi kuma dayaga hakan sai bai cemata komaiba fata dai su isa lafiya.

Suna kawowa daidai wata roundabout motar data d'auko Dr Nuraddeen na wucewa zasuyi yuton ta d'ayan titi ta jami'an da suka biyota baya ta shigo aguje lokacin little shi kuma ya shigo sai batool ta saki wata irin qara wacce ita tasa little rud'ewa saidai yaji sun bugi motar jami'an tsaron,

Da sauri Dr Nuraddeen da har motar da yake cike ta juya ta d'ayan titin ya hango abunda yafaru ya tsaida drivernsa.

Nan take go slow ya cika wurin don gaba d'aya gaban motarsu little data buga data jami'an tsaron ya molaqe Amma su babu abunda ya samesu, don little qoqarin ma bud'o gambun motar yakeyi yafito, d'an ja da baya motocin suka shigayi sannan aka taimaka masa yafito had'e da d'an dafe goshinsa daya bugu ya da sauri ya zagaya inda batool take, ita kam da alama somewa tayi da sauri wani mai keke napep ya miqo ruwan leda aka yayyafa mata ta farfad'o tana fad'in.

"Innalillahi wa'inna ilaihirrajiuun, Abbana."

Murmushi little yayi sannan yariqota tafito daga cikin motar wanda daqyar ta iya takawa saboda qafafuwanta da suka kumbura, adaidai lokacin Dr Nuraddeen ya qaraso shida drivernsa yana fad'in.

"Subhanallahi, injin ba abunda ya sameku?,"

Juyowa little yayi da sauri don bazai manta muryar wannan mutumenba, sai da Dr Nuraddeen yakusa fad'uwa saboda wani irin jiri daya d'ebesa lokacin da idanuwansa suka sauka akan fuskar little dake fad'in.

"Ko kad'an Alhamdulillah, ALLAH ya tsare." Nan ma gabansa ne ya sake fad'uwa tuna wannan muryar wanda yarage masa hanya ne jiya da daddare a jahar borno, Abu mafi qololuwar ban mamaki dashi shine yanda sak fuskarsa irinta Rashidarsa, to wannan wane mutumne dake bibiyarsa tun jiya, yana wannan tunanin ne yaga suna qoqarin barin wajen da sauri batool tajuyo had'e da dawo wajen motar tana fad'in.

"Abu sumayya su hassana fa."

Sai alokacin shima yatuno dasu da sauri ya qarasa ta gaban motar ya bud'e lock d'in daya danna tin tasowarsu don kada suyi yunqurin bud'e gambun tunda basaji, sannan ya dawo ya bud'e bayan, ga mamakinsa sai yaga gaba d'ayansu sun fad'o qasan sit d'in d'aya ta taushe d'ayar kuma baccinsu sukeyi, hamdala yayi tare da d'auko ta saman wani ya karb'eta sannanya d'auko d'ayar yana duddubata, haka batool ta qaraso wajen batare da taji nauyin cikin dake jikinta ba takarb'i ta hannun mutumen Wanda gaba d'ayansu sun tashi baccin sai faman murza idanuwa sukeyi da hannu suna kallon mutanen da sukayi cincirindo wajen, kallo Dr Nuraddeen yabi yaran dashi, ahankali ya furta subhanallah, saboda tsantsar kamarsu daya gani da wannan mutumen daya taimakesa jiya, Kai ko baka tambaya ba kasan 'ya'yansa ne, banbancin kawai shine hasken fatar da yaran suka fishi Wanda da alamu na mahaifiyarsu ne dake d'auke da tsohon ciki.

Gaba d'aya rud'ewa Dr Nuraddeen yayi ya rasa tawa zaiyi cikinsu, ta jami'an tsaron da wasu daga cikinsu sun fad'o sun d'anji rauni kota wud'annan ahali dake da matuqar yanayi da habibty d'insa.

Baisan lokacin da yaba drivern umurni yaje yayi qoqarin fiddo motarsu little data shige cikin ta 'yan sandan ba shi kuma yabi su little dake qoqarin komawa gefen titi yana fad'in.

"Sannunku ko.?"

"Yawwa" little yafad'a yana qoqarin amsar hassana a hannun batool bayan ya ajiye hussaina qasa.

"Am don ALLAH nace daga jahar borno kuke ko?"

"Eh, Amma kamar jiya kaine muka ragewa hanya da daddare zaka sauka hotel ko."

"Exactly! 'yatah."

Dr Nuraddeen yafad'a cike da mamakin yanda tagano shi yana miqawa little hannu.

"Bawan ALLAH baka ganeni bane, nine fa wanda kuka taimakawa daren jiya da taxxi d'in data d'aukoni ta samu matsala, Katina.!"

"Eh maigida natuna.." little yafad'a yana d'an dafe goshinsa inda yabugu, da alama wajen zafi yake yimasa,

"To barka da arziqi, kuzo mana ga mota can kada kutsaya abakin titi ga rana sosai, ga motar mucan kushiga kafin afiddo waccan d'in ko don yarannan."

Yaqarasa maganar jikinsa har rawa yakeyi yawuce gaba yanayi yana waigowa yana kallon su, idan ya kalli little ya kalli yaran har suka isa jikin motar ya bud'e masu suka shiga, 'yan jarida kam ba magana ga labaran da zasu iya bugawa amma tsananin go slow da taron mutane yahana tunda motacinsu nacan baya.

Anyi anyi aciro motarsu little amma taqi tashi balle asa ran za'a cirota don haka sai Dr Nuraddeen yace suciro kayansu sai su ajiyesu gida idan yaso daga baya in ancire motocin ajikin wajen sai yadawo ya d'auka, duk da little baiso hakan ba haka yayi haquri sukaje shi da drivern daya d'auko Dr Nuraddeen suka kwaso kayan aka zuba a boot, sannan yaba wani jami'i cikin jami'an tsaron da baiji ciwoba maquddan kud'i yace, a d'auki mutun ukun da sukaji rauni akaisu asibiti, sauran kuma suraba in Sha ALLAH zai biyo bayansu.

Sannan suka d'auki hanyar zuwa anguwar su batool, shi dai Dr Nuraddeen baisan ko Ina ba acikin garin asalima sai kalle kallen yanda garin ya sauya gaba d'aya yakeyi don komai ya canza badon ana rubuta wasu abubuwa da wurairai ba zai iya rantsewa yace ba'a cikin kanon daya sani yake ba, drivern kawaine daya san waje ke tuqinsa cikin natsuwa da kwanciyar hankali har suka isa anguwar, ita kanta batool taga wasu canje canje da dama tunda shekara bakwai ba wasa bane, hatta gidan nasu data hango ancanza masa tsarin wajen qofar shiga da fenti sai wasu sabbin gine gine data gani acikin anguwar tasu, ana kaiwa bakin qofar gidan drivern yayi horn saboda abud'e gate a tsammaninsa zasu shiga ciki ne Dr Nuraddeen yace a'a ya tsaya waje tunda wucewa zasuyi basai an bud'e ba.

Abba dake tsaye yana faman safa da marwa lokacin angama saukar alqur'anin ana addu'a suna jin horn gaba d'ayansu sukace Alhamdulillah tamkar an sanar masu da cewa su d'inne, da sauri su uncle da Abba sukayo waje jikinsa har rawa yakeyi yana qoqarin fad'uwa amma haka yaci gaba da nufatar bakin gate d'in da sauri da sauri, daidai lokacin mai gadi ya hangame gate d'in batool tafito ita da little suna rirriqe da gambunan motar, wani irin farinciki ya lullub'eta lokacin data hango mahaifinta kyakkyawan dattijo da gaba d'aya gashin kansa izuwa na fuskarsa yayi fari saboda tsufa, Amma hakan bai hana ka hango kyawonsa da hasken fatar da ALLAH yayi masa wanda adalilinsa ake kiransa da alhaji umar fari, ahankali take takawa izuwa garesa don bazata iya rugawa ba idanuwanta na zubar da qwallan farinciki, yayin da shikuma yafad'i qasa had'e dayiwa ALLAH sujudushshukur, su uncle ma tsaye sukayi suna dariya had'e dasa hannuwa suna goge qwallan da suka zubo masu yara da manya kuwa sukayo ruu wajenta suna yimata oyoyo. daqyar ta iya samu suka barta taqaraso wajen mahaifinta da alokacin ya d'ago daga sujadar da yayi, wani irin kuka ta kucce dashi had'e da durqushewa agabansa ta dafa qafafuwansa tana fad'in.

"Kayafeni Abbana natuba, nayi nadamar duka abubuwan b'acin ran dana saka ka aciki, nayi tir da halina da nazamo bijirarriyar 'ya agareka bayan duka soyayyar daka nunamun, haqiqa inuwar iyaye da kuma alfarmarsu da 'ya'ya suke samu awajensu tafi qarfin wofantarwa da kuma fifita ra'ayin zukatansu akanta, Abbana..."

Bata qarasa ba da sauri Abba ya duqa ya d'agota shima yana hawayen sannan yasa yatsunsa akan fuskarta yana goge mata itama hawayen dake zubowa afuskarta.

"Ya Isa haka Batool, duk da laifin nakine amma kuskuren nawane, mezai Hana iyaye sudinga fahimtar 'ya'yansu da kuma kwatanta yimasu adalci, tabbas ni nahaifeki Amma banida ikon sarrafa rayuwarki da kuma zuciyarki tayanda zance lallai sai kinyi abunda nake so, ALLAH nagode maka, kaine maji roqon addu'ar bayinka ya ALLAH, Ina godiya agareka daka iso mani da 'ya 'yana lafiya."

Yaqare maganar tare da rungumota ajiki yana maijin wani irin farinciki,

Kallon little dake tsaye dasu uncle h ana gaggaisawa yayi bayan yayiwa Dr Nuraddeen godiya yara sunciro masu kayansu sun wuce, a hankali ya bud'e masa d'ayan hannunsa yana fad'in.

"Zo mana yarona, ko har yanzu baka haqura ba fushi kakeyi da abunda abban naku yayi maka?."

Da sauri little yaqarasa wajensa cike dajin kunya yad'an russuna yana gaishesa, cikin hawayen nadamar abunda yatab'a yimasa randa yadawo da batool gida ya saketa tayi wajensu uncle tana gaishesu shi kuma yasa duka hannuwansa biyu ya rungumo little sosai ajiki yana fad'in.

"Haba Nuraddeen, nifa abbanku ne, don me zaka nesanta kanka agareni? kai da batool matsayi d'aya kuke dashi yanzu agurina, don ALLAH kayafemun duka abunda nayi maka abaya ko da sau d'ayane ka amsheni amatsayin mahaifinka kaima."

Shidai little baice komai ba don yanzu shima hankalinsa na wajensu baffa, ya matsu yaje garesu da albishirin mahaifiyarsa tabashi damar zuwa garesu tare da zuwa qasar da mahaifinsa ya tafi ya nemosa, Wanda ya tabbata hakan zai yiwa su baffa dad'i sosai, muryar Abba daya ji yana fad'in ko sai naduqa qasa zaka yafemun laifina d'ana had'e da qoqarin duqawar tasashi sairin fitowa daga tunanin da yake shima ya rungume abban yana fad'in.

"Abba duk abunda zakuyi mana aduniya kunfi qarfin duqawa agabanmu domin soyayya takansa kuyi mana hakan, wancan abun daya faru Abba yariga daya wuce, ka yafemana bisa damuwar da muka saka ka aciki domin mun dad'e da fahimtar hakan kuskurene."

'Dan juyawa yayi tacan gefen gate ya hango su hassana sun b'uya suna leqo mutanen gidan, don kam yanda sukaga ana koke koke bazasu d'auka na farinciki bane dole suyi takansu tunda d'an banzan wayone dasu, Abba ga matanka can sun b'oye wataqil fushi suke baka tarbesu ba.

Daidai lokacin ya hango shurahbil ya nufi wajensu don tun d'azu batool ke nuno masu irin 'yar b'uyar da sukeyi suna leqowa su koma ana dariya shine yatafi wajensu shima yana dariyar.

Hannu ya miqa masu har hassana zataje, hussaina tajaye hannunta tana fad'in.

"Ke Hassan karkije kema asakaki kuka, bakiga wancan garin mutum mai farin gashin yasa ummanmu nildown tana kuka kuma shima wai kukan yakeyi, sai nafad'awa kaka wannan sunfimu iya muguntar ikram da take cewa munayi idan mun sakata kuka."

Bushewa da wata irin dariya shurahbil yayi har yana riqe ciki kafin daqyar ya samu ya tsaidata yace.

"Kunga, uncle bazai yimaku mugunta ba, ai kinga ni bana kuka sai dariya ko?,"

"Eh amma dariyarka tayi yawa kaima, bakyau inji kaka." Hassana tafad'a tana kallonsa, d'an d'aure fuska yayi had'e da durqusowa saiti tsawonsu y miqa masu hannu.

"To nadena kuzo muje ko?"

"Zakije hussaina?"

Ganin ta miqa masa hannu yasa itama bata tsaya wata wata ba tamiqa masa hannun yariqesu suka nufi wajen da har lokacin su uncle ake tsattsaye ana sake gaggaisawa sannan aka shiga cikin gida fuskokin kowanensu d'auke da farinciki, tana ganin mahaifiyarta hajia mama tarungumeta cike da farinciki,

Murmushi hajia mama tayi tare da d'ora hannunta agefen fuskar batool tace.

"A gaisheki d'iyar albarka sarkin kafiya, wato haka kika yimana tafiya batare da kin fad'a mana ba duk kika d'aga mana hankali ko, wannan wace irin rayuwace haka, ALLAH yasa ba haka kike bawa mijin naki da gwaggon yara ciwon kai da kafiyar nan taki."

'Dan cije baki Batool tayi tana dariya sannan yace.

"Ayi haquri hajia mama, kewarku tasa bazan iya jira ba, kuma nasan idan nafad'a kema zaki hanani kamar yanda abbana yahanani, gashi zuciyata nafad'amun kamar cikin nan bazai barni in sake had'uwa dashi ba shiyasa, ammafa munyi arziqi har sau biyu."

Nan fa tashiga Basu labarin abunda yafaru, Abba dasu uncle suka shiga jinjina al-amarin ubangi, tabbas addu'a gaskiyace kuma duk wanda yayita ALLAH na sauqaqa al-amurransa saidai kawai qaddararce baza'a guje mata ba, haka itama sadaka tana tunkud'e kowace irin fitina ce aduniya, mafarki kuwa baya tabbata gaskiya sai abunda ALLAH yaso acikinsa, kusan atare duk ahalin gidan dake waje d'aya aka shiga yiwa Allah hamdala kafin hajia mama tace.

"Wannan abun daya faru izinane ga rayuwarki data mahaifinki harma damu duka, amma alhamdulillah tunda ALLAH yakawo sauqi cikin al'amarin, duk mutumen dake tsananta addu'a arayuwarsa to haka ALLAH zai dinga sauqaqa masa al-amurransa, idan ALLAH yayi nufin silin sai fad'o maka inkana addu'a to sai kaga kana zaune qasar silin ta burbuso maka a fuska saboda addu'ar da kayi, to shi Kuma ALLAH idan ya rubutowa mutum qaddararsa to ba'a kankare masa ita, don haka sanadin addu'a sai a sauqaqa masa ita, sai kaga ta tabbata akanka amma cikin sauqi, don haka muriqe addu'a acikin kowane lamari basai munajin tsoron faruwar wata musiba akanmu ba, sai muga ALLAH na tafiyar da rayukanmu cikin sauqi, ya ALLAH ka sauqaqa mana dukkanin wani Abu daya tsananta."

Duk aka amsa da Amin, nan aka halarto da abincin kowane part kowa yaci yasha ya qoshi su hassana na laqe da shurahbil sunqi yarda da kowa saida sukaga anzage anata fira kowa yasaki jiki sannan suma suka saki nasu jikin,

Little nahutawa yayi sallama dasu ya nufi bebeji wajen su baffa yanajin wani nishad'i aransa.

••• ••• •••
Dr Nuraddeen kuwa nabarin anguwar suka nufi qauyensu, tun daga kan hanyar shiga qofar qauyen yafara ganin manya manyan sauye sauyen kala kala, haka ya dinga bin ko ina da kallo cike da mamaki, tabbas ako Ina ana samun cigaba don ko aqauyen nasu yagani ba laifi, ganin motocin 'yan jarida lokacin da suke shigowa cikin qauyen ya tabbatar masa da har yanzu suna kan dakon jiransa kenan!

Adai dai lokacin su kuma su baffa sunka fara miqewa suna qoqarin shiga cikin gida saboda yanda sukaga taron ya soma yawa, kawai sai sukaga d'aya daga cikin 'yan jaridar ya nufatosu had'e da yimasu sallama,

Suna juyo motar Dr Nuraddeen da 'yan jarida kebiye da ita tayi parking adaidai lokacin.....
















*ALLAH KAJIK'AN IYAYENMU*👏😭
[11/14, 22:52] Billy S Fari: 🚶‍♀️🚶🏻‍♂️ *SANNU SANNU*🚶🏻‍♂️🚶‍♀️
💎 _Bata hana zuwa..._💎


_WRITTING BY:_ *BILLY S FARI💎*

_DEDICATED TO:_ *BLOOD SISTER'S (AMZAHFAZ)*💋

_BESTOWED TO:_ *ZAINAB AL-AMIN (MOM NA'EEM)* AND *AMINA UBA AYUBA (OUM ASHFAQ)*💞

*DOMIN FARINCIKINKI SISTER SADIYA ZANGO (MIEMAH)*💖

*FATAN ALKHAIRI AGAREKU MOMMAH ME NANA HAFSAT (MISS XOXO) AND MAMANA HAFSAT RANO(OUM AFFAN)❤️

Page___104💎

Duk yanda little yaso yayi mata maganar mahaifin nasa daya dawo kuma ya sadasu awaya hakan gagara yayi don koda yasake gwada kiran wayar sai yaji ance masa kashe take, d'ago kai yayi ya kalli mahaifinsa da nan take yaji wani sauyi atattare don har hakan ta bayyana a fuskar, kenan habibty d'insa fushi take dashi sosai ya tambayi kansa, wato zuciyar ce ta amsa masa da cewa to ai ta cancanci tayi fushinma da yafi wannan domin al'amarin ne da quna sosai azuciya, murmushi little ya sakar masa tare da cewa. "Baba bara nakira maka gimbiya.!"

Saida yafad'a sannan yayi saurin toshe baki yana dariya, ya manta agaban mahaifinsa yake bai kamata yafad'i hakan ba yace cikin ransa, waskewa yayi tare da cewa.

"Aww Ina nufin batool baba."

Murmushi Dr Nuraddeen yayi had'e da cewa.

"Babu damuwa."

Yana rufe baki saiga aunty marwiyya ta iso wajen tana tafa hannuwa.

"Ikon ALLAH, yanzu Kai little shine zaka jaye mahaifinka anan ana son ganinsa, to kazo maigidanka nason ganinka mu zamu wuce."

Hakan yasa ya fasa kiran ya kad'a wayar aljihu sannan yabi bayanta, bayan ansake tab'a wata firar little yayi masu rakkiya har inda zasu hau mota suka wuce shikuma ya dawo,

Ataqaice dai ranar har kusan goma na dare suna karb'ar baqi masu zuwa yiwa Dr sannu da zuwa da masu taya baffa murnar dawowar d'ansa harma da masu zuwa tsogumi, Wanda hakan yasa little ya kasa komawa wajen batool saidai sukayi waya inda anan ya sanar da ita komai akan dawowar mahaifinsa wanda ya kasance shine mutumen daya taimakesu ayau, duk da tajima tana zargin mijin nata nada alaqa da mutumen aranta hakan bai hanata mamaki ba sosai, musamman da taji koshi waye, tayi farinciki sosai tare da jin dad'i, cikin daren ta iske mahaifinta tabashi labarin mahaifin little yadawo shima nana take yanuna farincikinsa, da kansa ya d'auki waya ya amshi lambar da tayi waya dashi yakirasa yana tayasa murna, nan little ya had'asa da mahaifinsa yayi masa barka da isowa tare da tabbatar masa da cewa gobe zasu biyo hanya suma in Sha ALLAH.

Baba nusaiba kam yau gari nasu, abinci na musamman ta shiryawa babban d'a tare da babban jika, sannan ta kwashikke kayan yaranta mata tamayar a d'akinta tasa aka sharesa tass akasa qatuwar katifar nan mai tuli irinta family ta feshesa da room freshner da sababbin labulayye yayi gwanin sha'awa, koda suka shigo gidan su uku saisu baffa da suka rakkosu acan tayi masu masauki wanda hakan ba qaramin dad'i yayiwa baffa ba ta kawo masu lafiyayyen abincin data shirya masu sukaci suka sha suka qoshi sannan su baffa Usman sukayi masu sallama don lokacin dare ya miqa har qarfe d'aya tayi, Dr Nuraddeen yaso yabi su baffa ya kwana acan wajen mahaifiyarsa amma shauqin soyayyar d'ansa tasa ya shafa'a har dare ya raba suna zaune su uku suna fira cike da soyayya, duk little ya kalli mahaifinsa sai yaji wani dad'i aransa ya rufesa marar misaltuwa, yayinda shi kuma Dr ji yake ya tsani kansa sosai idan yakalli yanda mahaifinsa yakoma, Wanda ya tabbatar wahalace da kuma damuwar rashinsa akusa dashi ta jefasa aciki, nanma kasa jurewa yayi saida yayita kuka yana roqon mahaifin nasa da d'ansa yafiya don yasamu nauyin da yakeji aransa ya ragar masa.

Har aka kira sallar asuba suna zaune suna fira Dr nabasu labarin halin daya tsinci kansa aciki awaccan qasar da irin rayuwar da yayi, sun matuqar tausaya masa sosai don kam ba rayuwace mai dad'i ko ingantacciya yayi ba daga qarshe duk suka taru suka yafi juna tare da addu'ar ALLAH yabawa kowanensu tsawon rayuwar da zasuji dad'in juna, shidai baffa murmushi kawai yayi tare da amsawa da Amin don yasan shikam ai tafiya tayi tafiya saidai fatan cikawa da Imani, Saida baffa yatada baba nusaiba sannan suka wuce masallaci bayan sunyi arwala, da aka gamo sallah Dr Nuraddeen ya kalli mahaifinsa bayan ya gaishesa sannan yace yayi can babban gida wajen mahaifiyarsa.

Baffa ya amsa masa da "To ALLAH yatsare hanya ka gaisheta."

Ba kunya ba tsoron ALLAH little yaja qafafuwa yanda kukasan zariya yabi mahaifinsa yana yiwa baffa sai yadawo.

Baffa ya amsa masa da "Adawo lafiya" yana murmushi.

Baffa nakomawa gida yanemi waje ya kwanta saboda akwai bacci sosai a idanuwansa, kan kuma kace me har yayi awon gaba dashi.

Su Dr kuwa Saida suka lelleqa d'akunan baffa Ali da baffa Usman suka gaishesu sannan suka wuce d'akin Yaya hawwa, tanaji anturo qofa tace.

"Bilki ce?, Wai Ina yaron nan nura yaje ko yamani wayau yasake tafiyarsa."

Dariya sukayi atare Dr. Nuraddeen yaje kusa da ita ya zauna tare da jawo hannunta yariqe yana d'an mammatsa mata sannan yace.

"Ina zanje kuma nabarki innarmu?, Barka da safiya, Ina kwana kin tashi lafiya?"

Saida ta zare hannunta tad'an shafa fuskarsa sannan tace.

"Lafiya klw, Ina katafi tunjiya baka dawo ba."

"Kiyi haquri innarmu, a gidan baffa na kwana kinga nan babu waje, amma yau anan zan kwana tare dake."

"A'a nura, kaje ka dawo da matarka, a wajenta yakamata ace ka kwana ba'a nan ba, Ina ance batayi wani auren ba ko?"

"Eh innarmu, Amma abune mai wahala tayarda nadawo da ita koda naje."

"Kaje zanyi maka addu'a, nasan zuciyarta mai kyauce zata biyoka kudawo tare, idan ba haka ba kuwa kada ka kuskura kadawo nan har saita amince kaji ko?."

Shiru yayi yana mamakin maganganun dake fitowa daga cikin bakin mahaifiyarsa, wai yau ita da kanta take bud'e baki tace yaje ya dawo da matarsa duk irin tarin tsanar da tayi mata ada, tabbas rayuwa na koyar da mutum darasi aduniya kuma duk abunda yasaka kuka to da SANNU SANNU wata rana zai saka dariya, yana wannan tunaninne yaji muryarta kamar zatayi kuka tace.

"Bakaji bane nura!, ko kana haufine da jin tsoron kada in aikata mata wani abunne makamancin waccan da nayi?"

"Ko kad'an innarmu, nasani bazaki yimata komai ba, wancan ma kuskurene kikayi da Babu wani mahaluqi aduniya d'aya wuce yinsa, zanyi yanda kikace, zan kuma yi iya qoqarina, saidai idan takasa amincewa to kiyi haquri zan dawo na Ida qarasa rayuwata hakan don ko kad'an bazan iya takurata ba."

"Karka damu, zata amince in sha ALLAH kaji ko?, Ina shi wannan yaron ko yatafiyarsa shima."

Kallon little Dr yayi alamun dashi take yace.

"Ganinan kakata mai kuka!, Ban tafi ko inaba nima ina nan tare da babana, wato so kike natafi na barki daga ke sai shi ko?, to Babu inda zani nazo kenan!"

"Shikenan, ai ni banida ja, kayi zaunenka kayita kallon mahaifinka kanajin sanyi, nima duk da bana gani ina matuqar jin dad'i azuciyata muryoyinku danakeji."

Haka yayita tsokanarta tana basarwa har ya gaji yabari ya shiga bawa mahaifinsa labari akan iyayensa na borno da kakanninsa wato Dr nura da fatima sai dady da umma da kuma ammie, sosai Dr Nuraddeen yashiga jinjina al'amarin ALLAH yanda ALLAH ya tsaro b'atan matarsa zuwa wancan garin sai kuma zuwan iyayenta acan don ya wanzar da qulluwr alaqar dady da umma mahaifiyar rashida da kuma alaqar d'ansa little da batool, tabbas al'amarin ALLAH da girma yake, tabbas zaiso yaga wud'annan irin mutane masu tsananin karamci da kuma halacci arayuwa dako atarihin mutanen da masu tsananin karamci bai tab'ajin irinsu ba.

Ana haka baffa Usman da baffa Ali suka shigo, gaida Yaya hawwa sukayi sannan suka bud'e sabon shafin fira, inda anan Dr Nuraddeen ke tambayar baffa Usman yanda akayi mahaifiyarsa tasamu lafiya wanda tun jiya yake son ya tambayi hakan.

Kuka yayi sosai tare da rungume mahaifiyarsa yana maijin tausayinta akan qalubale da wahalhalun da tasha aduniya, haqiqa duk wanda ke tare dasu yakasa d'aukar darasin yanda duniya ke tafiyar da rayuwar d'an adam to tabbas yayi nisa koda kuwa zuciyar qarfene

Please Login or Register in order to submit comment