Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kallon abunda ke shirin faruwa,

Ganin umma na neman sandarewa a inda take tasaki little yasa Fatima qarasawa da sauri takarb'esa tana kallon ikon ALLAH,

Rashida da tuni hawayen farinciki suka jiqa mata fuska tafara takowa cikin rashin kuzari jikinta har wata tsima yakeyi cikin rawar murya tana fad'in.

"Um..mata ni..ni..ce Rashida, nice Rashida 'yarki data b'a..b'a.ta."

Kafin taqaraso tuni qafafuwanta suka kasa imata tafad'i qasa tana kukan da babu shakka zata iya cewa na farinciki ne, haka umma gaba d'aya kasa motsawa tayi saboda qafafuwanta da suka yimata nauyi Saida taji su Yaya Maryam sunce.

"Aisha.." atare sannan tasamu wani irin qwarin guiwar qarasawa wajen 'yar tata dake jan qafafuwa tana neman isowa inda take ta rungumeta tana wani irin kuka mai cike da ma'anoni kala kala,

"Ina kika tafi Rashida kika barmu, munyi kuka mun shiga damuwa marar adadin duk ta dalilin rashinki, Ina kika tafi baki nememu ba kika sa gaba d'aya mukabar kowa namu Rashida saboda rad'ad'in rashinki akusa damu?."

Kasa amsawa Rashida tayi sai sake naniqe mahaifiyarta takeyi cikin jiki tanajikamar lumfashinta zai fita saboda tsabar farinciki, daqyar tasamu cikin wata irin murya mai ban tausayi tace.

"Kuyi haquri, kuyu haquri umma, son zuciya da biyan buqatar rayuwa tasa aka rabani daku, akanisantani da farinciki na aka nemi salwantar da rayuwata batare da andubi halin da nake ciki ba, saidai tsananin addu'arku agareni ya kubutar dani ga shiga duk wani irin gararin rayuwa, ya haskakamun dukkanin lamurrana, ya damqani a hannayen da babu son zuciya balle son kai acikin al'amurransu, d'ago kai umma tayi fuskarta jiqe da hawaye tariqe fuskarta tana goge mata hawaye da manyan 'yan yatsunta.

"Kidena kuka 'yata, muyi godiya ga ALLAH daya sake had'a fuskokinmu ba tare da yad'au rayukanmu ba, haqiqa dukkanin bawan da yayi Imani kuma yayi haquri ubangiji bazai tab'a bari ya tozarta ba."

"Hakane umma, nayarda da ALLAH shike jarabta rayuwar bawansa kuma yayi masa mafi qololuwar sakayya alokacin daya maida dukkanin al'amurransa agaresa, nayi kuka mai yawa lokacin dana koma agareku ban taradda kuba, saidai yau dukkanin kukana yaqare umma tunda gani gaku."

Tare suka juya suna fuskantar alqiblah had'e dayin sujudush shukur sannan suka juyo Rashida ta sake rungumeta tana fad'in.

"Ummahhh nayi kewarki"

Murya suka jiyo a bakin qofa ana fad'in,

"Ummanki kad'ai kikayi kewarta bada abbanki ba 'yata?."

juyowa Rashida tayi daqarfi jin muryar mahaifin nata dake tsaye fuskarsa jiqe da k'walla yana takowa izuwa garesu yana bin 'yan uwansa daya gani a tsaitsaye da kuma 'yar tasa tilo da tuni yagama fidda ran cewa zasu sake had'uwa,

"Babaaa..!"

Rashida tafad'a tare da rugowa da gudu tayi tsalle ta hayesa had'e da rungumesa, wani irin sanyi taji aranta da yasa ta runtse idanuwa tsabar jin dad'i hawaye naci gaba da kwaranyo daga cikin idanuwanta.

"Nayi kewarka baba.."

"Kika ce?"

"Nayi matuqar kewarka sosai babana."

Murmushi yayi cike da farinciki yasa hannu ya goge hawayen dake zubowa daga cikin idanuwansa, sake rungumeta yayi sosai tamkar wanda za'a k'wacewa itama tashige jikinsa tanajin wani farinciki marar misaltuwa atattare da ita.

Wannan al'amari da yafaru ba kad'an yasa dukkanin wud'anda ke cikin falon hawaye ba, musamman baba balarabe da Yaya Maryam da sukafi kowa jin dad'in faruwar haka idan aka cire Rashida aciki.

Ganin taqi saukowa daga jikin baba yasa baba balarabe da tuni duk suka hallara afalon jin abunda kefaruwa ya qaraso wajen yad'an tulli bayanta kad'an had'e da cewa.

"To cikamun d'an uwana haka kada kiqarasamun shi."

Lokaci guda duk sukasa dariya kowane nagoge qwallan da suka zubo masa, rungumesa baba balarabe yayi yana fad'in.

"Meyasa d'an uwa?."

Baba daya kasa tsaida hawayen farincikin dake yimasa zarya a fuska yace

"Tsarin alqalamin qaddara d'an uwana." D'agowa baba balarabe yayi had'e da cewa

"Baka kyauta ba ko kad'an kuma kada kasake yin hakan?, ko kamanta cewa mu muna buqatarku idan har ku bakwa buqatarmu da har zaku yanke hukuncin guduwa kubarmu batare dakun fad'a mana inda kuka jeba?"

Duk da shine Yaya akansa hakan bai hanashi bashi haquri ba, Yaya Maryam kuwa koda yanufi wajenta d'an marin fuskarsa tayi hawaye nazubo mata had'e da cewa.

"Zaka sake?" Kafin yabata amsa tasake kaimasa wani d'an marin agefe d'aya tana fad'in.

"Zaka sake guduwa kabarmu.?"

Cikin kukan farincikin irin son da suka nuna masa yace.

"Kiyi haquri Yaya Maryam bazan sake ba." Yasa hannu yagoge mata hawayen farincikin dake kwance a fuskarsa.

Nanfa dady yayi gyaran murya had'e da cewa.

πŸ˜… *HOPE YOUR MISSION IS ARCHIVED?*







*ALLAH KAJIK'AN IYAYENMU*πŸ‘πŸ˜­
[11/14, 22:52] Billy S Fari: πŸšΆβ€β™€οΈπŸšΆπŸ»β€β™‚οΈ *SANNU SANNU*πŸšΆπŸ»β€β™‚οΈπŸšΆβ€β™€οΈ
πŸ’Ž _Bata hana zuwa..._πŸ’Ž


_WRITTING BY:_ *BILLY S FARIπŸ’Ž*

_DEDICATED TO:_ *BLOOD SISTER'S (AMZAHFAZ)*πŸ’‹

_BESTOWED TO:_ *ZAINAB AL-AMIN (MOM NA'EEM)* AND *AMINA UBA AYUBA (OUM ASHFAQ)*πŸ’ž

*DOMIN FARINCIKINKI SISTER SADIYA ZANGO (MIEMAH)*πŸ’–

*FATAN ALKHAIRI AGAREKU MOMMAH ME NANA HAFSAT (MISS XOXO) AND MAMANA HAFSAT RANO(OUM AFFAN)*❀️

Page___66πŸ’Ž

Kasa bacci baba yayi, inbanda juye juye babu abunda yakeyi, da zaran yarufe idanuwansa babu wacce yake tsinkayowa sai Yaya hawwa da suka gani a cikin tv d'azu, tambayar kansa ya shigayi.

Shin meke faruwa da matar aminin nasa kuma surukar 'yarsa?, shin gaskiyane ita d'ince idanuwansu suka gane masu acikin tv ko kuwa?, Idan har gaskiya ne itace meye silar fad'awarta a cikin wannan mummunan halin da gaba d'aya duniya ta shaida shi,

Ganin yakasa samun amsoshin tambayoyinsa ya yanke shawarar isko aminin nashi da shikad'aine zai iya bashi amsarsu, miqewa yayi yafito daga cikin masallacin lokacin qarfe ukku saura kwata yanufi fanfunan dake jikin masallacin yayo arwala sannan yanufi sashensa saboda hasken wutar d'akin daya hango wanda shine ya tabbatar masa da cewa har yanzu su umma basu kwanta ba.

Knocking yayi abakin qofar d'akin Rashida tagwalo idanuwa waje tana kallon umma da gaba d'aya jikinta yayi sanyi akan labarinsu Dr da take bata na rashin haihuwarsu da soyayyar da suke nunawa little Nuraddeen, yanda tayi da idanuwa yaba umma dariya don kana gani kasan tsorone kwance fal a qasan zuciyarta, jin baba na sake bubbuga masu qofar ahankali muryarsa qasa qasa yana fad'in.

"Maman Rashida wace irin firace haka kukeyi har qarfe uku takusa kuna zaune, da haka kutashi kufuskanci ubangiji mana kufad'a masa buqatocinku inaga yafi wannan b'ata daren da kukeyi a banza" Yasa umma saurin cewa.

"To malan dama yanzu nake tunanin haka."

"Yawwa to ai yafi, kutashi."

Baba yafad'a tare da juyawarsa yakoma masallaci yana mai fuskantar ubangijinsa yana mai godiya tare da sake miqa d'imbin buqatunsa agaresa.

Haka ta b'angaren aunty marwiyya tsabar farinciki hadda sadaka tayi lokacin dasu Yaya maryam suka isa gida suka sanar da ita zancen had'uwarsa dasu umma da sukayi acan garin, rawa tadinga kwasa tanayiwa ALLAH godiya, duk da bata san taya had'uwar tasu ta kasance ba itama harda k'walla tayi.

A b'angaren baba balarabe ma bacci yayi yana tunanin ko meye gaskiyar abunda yafaru ga iyalin baffa?, Kenan maganar da d'an uwansa yafad'a masa ba gaskiya bace? Idanko haka ne yatabka babban kuskure abunda yayi masu,

Tsaki ya dingayi naba adadi yana ALLAH waddai da zuciyar data tunzurasa yakasa banbance qarya da gaskiya tsakanin maganganun da su baffa suka fad'a masa da kuma wud'anda d'an uwansu yafad'a masa.

Matsuwa baba yayi safiya tawaye don yad'au alwashin komawa garinsu saboda sanin halin da aminin nasa keciki, a iya saninsa yasan shi da kansa yace masu susa asako yaya hawwa da d'an uwan nasa da kuma matarsa, yana tsoron kada ace garin d'aukar matakine ya jefa iyalin tasa cikin wannan halin.

Tunda akayi sallar asuba baba yagama karanta azkar d'insa ya hau shirye shiryen tafiya, kasancewar dady part d'in ammie yake yasa bayan ya kammala shirinsa yace umma taje ta sanar da ammie yana son magana da dady idan yatashi bacci, yanda yace haka umma tayi sannan tadawo tana goye da little Nuraddeen tace.

"Wai malan lafiya naganeka kamar cikin damuwa? Ga alama ko bacci baka samu kayi ba jiya, Kuma yau tunda sassafe kahau shiri, meke faruwa da kaine kuma Ina zakaje?"

Taqare maganar damuwa kwance a fuskarta, ganin haka yasashi d'an murmusawa had'e da cewa.

"Babu komai maman Rashida, zancen bacci kuwa ai bani kad'aine banyi ba...."

"To naji basai ka qarasa ba, amma ina zakaje? Ko yau zamu koma."

"A'a bana tunanin haka domin idan nace zan koma banyiwa alhaji adalci ba don gaba d'aya amanar sabon shagonsa a hannuna ya damqata, zandai je kano ne Ina son in had'u da alhaji Idris akan abunda muka gani jiya dangane da iyalinsa? Kinga bai kamata ace nagani nayi shiru ba matuqar ita d'ince kamar yanda Rashida tafad'a."

"ALLAH ya kiyaye." Umma tad'an fad'a kamar cikin jin haushi zatabar wajen.

"Dakata mana, Ina Kuma zakije muna magana.?"

"Ai mungama magana tunda kafad'a mani inda zakaje."

"To meya b'ata maki rai aciki maman Rashida naga zakibar wajen rai a b'ace."

"Bakya son natafi ne?"

Shiru tayi batare data tanka saba tana d'an jijjiga little dake mutsu mutsu yana neman tashi, murmushi yayi don yasan dole hakan zata faru, mawuyacin abune ga uwa ta iya manta wanda ya cutar mata da d'a, musamman idan taga ana damuwa da al amarinsa alokacin da shima ya jarabtu sai taga kamar ita annuna rashin so akan nata ne da aka kasa nuna masa haka a lokacin da ake cutar dashi.

Lumfasawa baba yayi had'e da cewa, " kiyi haquri maman Rashida abunda zuciyarki ke tunani ba haka bane, iya sanina matuqar zamuyi koyi da mafificin halitta to bazamu rama cuta da cuta ba domin shi yakan rama cuta da alkhairi ne ga wanda yacutar dashi sannan karki manta da irin d'imbin alkhairin da d'an baiwar ALLAHn nan da mijinta suka yimani, koba komi tunda suka qaunaci 'yarmu sunngama mana komai arayuwa."

"Amma kuma meya biyo baya malan?, Cutarwa da kuma neman salwantar mata da rayuwa, yakamata kafahimci hakan kabarsu suma da tasu jarabawar suji idan akwai dad'i, 'yarmu aka cutar amma rad'ad'in da zafin akanmu yaqare muda muka haifeta, don haka dole suma suji irin wannan zafin alokacin da take cutuwa duk da kuwa basu ke cutuwar ba."

"Ashsha! Kada kibari 'yarki tafiki hankali da tunani, karki manta mu da muka shiga cikin tamu jarabawar ai ba qyalemu sukayi ba, qarfinsu, lokacinsu da kuma kud'insu harma da mutuncinsu duka sunyi amfani dasu wajen nuna mana damuwa akan halin da muke ciki, shine yanzu zakice mu muwofantar dasu saboda sun zamo silar cutuwarmu data 'yarmu?, Kiyi haquri mumanta da abunda yafaru tunda ALLAH ya maido mana da 'yarmu duk da nasan hakan abune mai wahala amma zamu iya matuqar mukaci gama da yawan tuna alkhairansu."

Sosai jikinta yayi sanyi kuma b'acin ran da takeji akansu yad'an rage sosai,

"Shikenan ALLAH yasawaqe yasa kaje lafiya kadawo lafiya."

"Amin ya rabbi, bari naje inaga kiran alhaji ne qilan yafito." yafad'a yana ciro wayarsa dake ruri a gaban aljihu.

Qarasa shiga cikin d'aki tayi shi kuma yanufi sashen ammie.

Sida suka gaisa cikin girmamawa sannan yasanar dashi zancen tafiyar da yake so yayi yau, duk da ko kad'an dady baya son yayi nesa dashi haka yadaure yabashi goyon bayan yin tafiyar tare da ciro dubu goma yamiqa masa yace yayi na mota.

"A'a alhaji da ka barsu wlh, akwai kud'i a hannuna sosai."

"Ai nasani, ka karb'a ni nabaka kaqara, kud'i ai basa yawa ga matafiyi." Karb'a yayi had'e da yimasa godiya sannan yami zaifita, har yakusa kai bakin qofa alhaji ya kirasa had'e da cewa.

"Am..malan bashar me zai hana kabari zuwa jibi sai mutafi tare don zanje sayo kaya, kasan duk kayan namu sunyi qasa.?"

Sosa kai baba yayi had'e da cewa.

"Ai da kabarshi alhaji, so nake yau ko gobe in juyo idan ALLAH ya yardar mana."

"To shikenan ALLAH yakiyaye hanya, dama nafi samun natsuwa idan kana kusa lokacin da zan tafi, don ALLAH ka gaishe mana dasu."

"In sha ALLAH zasuji mungode."

Abakin qofa sukaci karo da Dr nura yana qwalawa ammie da dady kira, kallo d'aya zakayi masa kasan cikin farinciki yake saboda wani annuri dake fita a fuskarsa, d'an sunkuyawa yayi yana sosa k'eya ya gaida baba, fad'ad'a murmushinsa yayi had'e da amsa gaisuwar daya yimasa yana fad'in.

"Agaida likita bokan turai kuna lafiya?.."

Bai qarasa magana ba yaga Fatima na qoqarin shigowa itama tajawo hijab d'in jikinta yarufe mata fuska, ganin yayi tarugo da gudu hango ammie nafitowa tafad'a jikinta tana kuka.

"Subhanallahi.. Dr lafiya?"

Baba yafad'a yana kallon Dr nura da shikam sai faman washe haqora yakeyi, gaba d'aya 34 d'insa sun kasa rufuwa, Saida ya d'an sinne kai qasa had'e da kallon Fatima ta wutsiyar ido sannan yace.

"Baba lafiya klw ku qyaleta kukan dad'i ne takeyi, addu'arku da kuka dad'e kunayi ne ALLAH yakarb'a mana shine fa tunda likita yafad'a take wannan kukan."

"Alhamdulillah, Alhamdulillah, Alhamdulillah..."

Gaba d'aya falon tundaga ammie dake faman rarrashinta har baba da dady suka fad'a atare, sai alokacin Dr yaji wata irin kunya tarufesa da sauri yajuya batare daya qaraso cikin falon ba.

Maida jiki gabas ammie tayi had'e dayin sujada hawayen farin ciki nazubo mata tace.

"Lakal hamdu ala maqadait, walakash shukru ala man a dait, tabarakta ya zaljali wal ikram." Sannan ta tofa tashafe a fuska. Dady kuwa Banda murmushi Babu abunda yakeyi, nan take yaqudurta aransa zai yiwa baba dake tsaye wata kyauta a matsayin godiyarsa ga ALLAH bisa wannan ni'imar daya yimasu duk dako ba itace ta farko ba,

Hajia fareeda wato ammie itace matar dady tafarko kuma uwar gidansa tanada yara uku dashi kuma sune manyan 'yayansa agidan, Dr nura shine babban d'ansa sai kuma qanensa faruq, saurayine Amma zaikai shekara ashirin da bakwai haka, sannan qanwarsu Khadija dake da shekaru ashirin da hud'u, tayi aure bayan shekaru uku da suka wuce bayan ta kammala karatunta a fannin lafiya wato (nursing), kuma ALLAH ya albarkaceta da samun yara biyu Shahid da Shahida idan kaganesu zaka d'auka tagwayene amma ba haka bane saboda haihuwar rurrutsa tayi, tana ilorin acan take aure saboda mijinta soja ne basu fiye zama waje d'aya ba, yau in suna wannan garin to gobe kuma suna waccan garin, wannan dalilin ne yasa dady cewa ba itace ni'ima tafarko da ALLAH yayi masu ba.

Tun daga nan ammie bata sake haihuwa ba kuma hakan bai tab'a damun dady ba, acewarsa sukad'ai idan ALLAH ya raya masa sun isheshi, amma da yake ammie macece mai tsananin alkunya da kuma son mijinta ta tirsasa masa cewa dole sai yaqara aure saboda yasamu qarin zuri'a ita kanta tana sha'awar yara qanana gashi ga dukkan alamu haihuwar ta tsaya mata, don haka tayita rarrashinsa har tasamu ya amince ya auro hajia nafeesa, 'ya ga amaninsa da suka tashi tare ya rasu yabarsu su takwas ga mahaifiyarsu, rashin wadatar da suke ciki don shi sana'ar noma yakeyi, sai gashi ALLAH yamasa rasuwa yasa dady ke tsananin tausaya masu kuma yake taimakonsu sosai, daga nan ammie tabashi shawarar ya auri nafeesar saboda hakan zai qara bashi damar taimakon 'yan uwanta sai gashi tazamo butulu ta hanyar walaqanta duk wani dake tare dashi matuqar bayada arziqi, musamman hajia fareeda data d'auka wata maqiyiyarta aduniya.

Dawowa cikin falon baba yayi fuskarsa d'auke da farinciki ya taya su hajia murna had'e da fatan ALLAH ya sauketa lafiya sannan yajuya yafita.

Miqewa dady yayi shima had'e da cewa.

"Dota congrat, ALLAH yakawo mana rayayyi masu albarka." Sannn shima yajuya yafice, ammie na dariya tasa hannu ta d'ago fuskar Fatima da tayi sharkaf da hawaye tana fad'in.

"Kai 'yata wannan duk kukan farincikine ko kuma na shagwab'a ne akeyiwa ammie ankusa zama mama." Kasa tanka mata tayi saima faman share qwallar da takeyi tana wasa da gefen hijab d'inta had'e da sissinne kai qasa, karo nafarko kenan arayuwarta data fara jin kunyar ammie irin haka, arayuwa babu abunda take b'oyewa ammie, ta d'auketa tamkar uwar data haifeta da cikinta, hatta wani abun cikin rayuwr aure idan Bata sani ba ita take tambaya tafad'a mata, haka ab'angaren kayan jiki na gyaran mata duka ammie nahad'a mata tabata kuma tayi mata bayani batare da taji kunyarta ba, sai gashi yau gaba d'aya takasa d'aga kai takalli ammie su had'a ido.

Murmushi irin na manya ammie tayi had'e da cewa, "ikon ALLAH, karmuyi haka dake 'yata, kisaki jikinki ni mahaifiyarkice don haka dena wani jin kunya akan wannan abun farinciki daya kamata muyi sharing happiness d'inmu atare, let celebrate together my dota bawani abubane, show me how much appy you feel about this, i will support you and make you enjoy it better kinji ko?."

Ahankali tad'ago kai tana kallon ammie hawaye nazubo mata afuska.

"I couldn't believe ammie, ammie ashe nima zan haihu ba juya bace ni kamar yanda ake fad'a, Ashe nima zan zama uwa am...?"

Kasa qarasawa tayi sakamakon kukan farinciki da yaci qarfinta, Bata tab'a kawowa kusa cewa zata haihuba, Bata tab'a sama ranta tana da ciki ba duka da dai Bata tab'a cire tsammani da rahamar ALLAH ba, ako yaushe cikin sa rai take komai daren dad'ewa zata haihu itama in ALLAH ya yarda.

Cike da tausayinta ammie tajawota ajiki ta rungume tana fad'in.

"Ya isa haka 'yatah, just blieve it, dama haka ALLAH yake, yakan lullub'e bayinsa da rahamarsa a lokacin da basu tab'a tsammani ba, kuma yakan dubi zukatan bayinsa da sukayi Imani dashi suka kyautata al'amurransu ya share masu hawayensu, wannan shine abunda nayita fad'a maki cewa idan lokaci yayi bazato ba tsammani zakiga abun kamar qyaftawar gira, Kuma nafad'a maki tunda dai har akece lafiyanki qalaw to kiyi haquri domin SANNU SANNU bata hana zuwa....gashi naki ALLAH yakawo ijaba har kin iso ko kuwa?"

Tafad'a tana d'an turo idanuwanta kad'an tana dariya alamar tana jiran amsa.

Jijjiga kai tashigayi alamar tabbatar mata da cewa hak ne ammie tace.

"To mugodewa ALLAH ba kuka zakiyi ba kinji ko?, Yanzu fad'amun me kike son ci?"

Rufe fuska tayi ammie nadariya tamiqe tana fad'in.

"Ko zakici wainar fulawa nayi maki?"

Ta girgiza kai had'e da cewa.

"A'a ammie eba dai zanci."

Turo idanuwa ammaie tayi had'e da cewa.

"Tofah, kice maigidan nawa d'an yarbawa ne?"

Duk sukasa dariya harda Dr nura da tun d'azu ke tsaye abakin qofa yace.

"Ai kuwa ammie da yaci sunan qudusu" yafad'a kamar yanda yarbawa ke kiran sunan suka sake sa dariya atare, can batare daya ankareba ammie takamo kunnensa had'e da murd'ewa tana fad'in.

"Son yanzu rashin kunyarka har yakai da kanka kake fad'an 'yata nada juna biyu kuma ka taso mani ita agaba, To Ida cikashe rashin kunyar taka ka fad'amun ko how many month ne?,"

Fatima na ganin haka ta tashi tashigewarta bedroom d'in mom tana murmushi, komai na surukar tata cike yake da burgewa da kuma ban sha'awa, ko kad'an batada wata matsala komai nata tanayinsa da cikakkiyar wayewar da babu qazanta acikinta.

"Awwwshhh..ammie da zafi fa."

"Nasani mana, bakai rashin kunya ba?"

"Kai mom, albishir nefa nayi maku, ALLAH badon baba ba sai kun cike mani check tukuna zan fad'a, Ashe laifine nayi bansani ba, amma ita data azawa mutane kuka Ina gani sai wani lallashinta akeyi ana murmushi." Yafad'a yana turo baki sai kace wani qaramin yaro.

Murmushi tayi had'e da sakinsa tace.

"Srry kaji ko son, tsantsar farincikinne har yayi mani over shiyasa nanemi regesa akanka, congrat soon zaka shiga next level arayuwa, wato mtakin zama uba bayan magidanci, ubangiji ALLAH yayi maku albarka yabamu rayayye."

"Amin ammien mu" yafad'a yana rungumeta.

Baba kuwa koda yakoma sashensa acan ya tarar da Dr nura suna gaisaw da umma da Rashida yana basu labarin jiya a asibiti suka kwana saboda zazzab'in daya tasowa Fatima har saida aka qara mata ruwa, baikai ga fad'a masu zancen cikin ba baba yashigo yamiqe zai fita baba ya tsayar dashi yake sanar dashi batun tafiyar da zaiyi kano, nan take Dr yaji tafiyar bata kwanta masa ba, yayi iya qoqarinsa naganin ya hana baba tafiyar har zuwa banda gobe idan zaije wajen aiki suwuce tare amma yakafe kai da fata shidai ya barshi ya tafi ai yau zai dawo, hakan yasa babu yanda ya iya dole sukayi sallama akan idan zai tafi ya aika Rashida yakirawosa zai koma wajen ammie sai ya ajiyeshi tasha sannan yabar sashen yanajin wani irin.

Baba kuwa zaunawa yayi suka sake d'an tab'a hira dasu umma yanata zolayarta wai yanzu idonta sun bud'e tadena kunyar Rashida amatsayinta na 'yarta tafari ashe b'oyewa takeyi tana sonta sosai sunata dariya.

Daga nan kuma yajuya akalar firar tasu izuwa yimasu nasiha akan rayuwar duniya sai kace wanda akace idan yatafi bazai dawo ba, bayan yagama umma tayi ajiyar zuciya had'e da cewa.

"Malan nifa duk jikina yamutu wlh, nidai don ALLAH kabar zancen tafiyarnan har zuwa wani lokacin."

Murmushi yayi had'e da cewa

"Karki manta sau da yawa bama son abu sai kiga ALLAH yasanya alkhairi sosai acikinsa, kika San alkhairan da wannan tafiyar zata jawo mana, qilama 'yar qanwa zan samomaki shiyasa duk kikabi kika tada hankalinki akanta." Yaqarasa maganar cikin sigar zolaya yana dariya had'e da miqewa yana d'auke da litte,

"Rana nayi bari na hanzarta yau nake son nadawo in sha ALLAH, Rashida jeki kikira Dr ni kam nad'au harma."

Gaban Rashida ne taji yafad'i da sauri tace.

"Baba kayi haquri kuwuce da uncle banda gobe."

"Ikon ALLAH, har dake Rashida? Bakyason sanin halin da mijinki da surukarki suke ciki halan?"

"A'a baba, ni kawai..."

Saurin dakatar da ita yayi tahanyar cewa "maza jeki kice Ina jiransa."

Har takusa fita yakira sunanta had'e da cewa.

"Dawo nayi maku albishir ni namanta, maman Rashida matar Dr fa tasamu qaruwa."

"Da gaske baba?" Rashida tafad'a cike da farinciki tare da ficewa da kad'an ma tafad'i garin sauri, umma kuwa Alhamdulillah tace tana fad'in "ALLAHU AKBAR, ALLAH maji roqon bayinsa, kai madalla bari naje nataya hajia murna."

Kusan tare da ita suka fita yana maijin wani sanyi aransa saboda yanayin farincikin da yaga ya bayyana a fuskarsu wanda hakn baqaramin tasiri yayi ba wajen qara masa natsuwa azuciya.....

_Godiya agareku masoya masu karamci da halacci bisa bibiyar lafiyata da kukayi, nagode sosai ALLAH yabar tare, maman ameera da ummu sauda ban manta daku ba, kunnuna kulawa agareni kuma jazakumullahu bikhair, fatan alkhairi aduk inda kukeπŸ‘πŸ»_




*ALLAH KAJIK'AN IYAYENMU*πŸ‘πŸ˜­
[11/14, 22:52] Billy S Fari: πŸšΆβ€β™€οΈπŸšΆπŸ»β€β™‚οΈ *SANNU SANNU*πŸšΆπŸ»β€β™‚οΈπŸšΆβ€β™€οΈ
πŸ’Ž _Bata hana zuwa..._πŸ’Ž


_WRITTING BY:_ *BILLY S FARIπŸ’Ž*

_DEDICATED TO:_ *BLOOD SISTER'S (AMZAHFAZ)*πŸ’‹

_BESTOWED TO:_ *ZAINAB AL-AMIN (MOM NA'EEM)* AND *AMINA UBA AYUBA (OUM ASHFAQ)*πŸ’ž

*DOMIN FARINCIKINKI SISTER SADIYA ZANGO (MIEMAH)*πŸ’–

*FATAN ALKHAIRI AGAREKU MOMMAH ME NANA HAFSAT (MISS XOXO) AND MAMANA HAFSAT RANO(OUM AFFAN)*❀️

Page___68πŸ’Ž

Saida 'yan uwan baba suka iso sannan akayimasa wanka aka sallaci gawarsa aka kaishi gidansa nagaskiya, a yanda mutane suka taru sukayi dandazo wajen sallar jana'izarsa kai ka dauka wani riqaqqen mai mulkine ko sarauta ko kuma wani hamshaqin malami, ALLAHU AKBAR, shiyasa akoda yaushe akeson mutum yazama mai sanyin hali da kyautata zamantakewa dtsakaninsa da mutane, duk da baba ba d'an asalin mazaunin cikin garin bane, kyakkyawan halayensa sun biyosa har zuwa qasarsa inda aka rufesa, bayada wani tarin arziqi kuma bai kasance wani sananne ba acikin garin da shekara d'aya kacal yayi acikinsa amma soyayyarsa ga ALLAH da kuma kyautata zaman takewarsa ga mutane yasa ubangijinsa ya soshi kuma yasa al'ummah ta soshi, babban abunda zaisa a kyautata masa zato shine yanda ruwa ke bulbulowa awajen haqar kabarinsa, har kusan sau biyu ana canza masa wani kabarin amma kowane aka haqo haka ake riskarsa, a dole aka d'aukesa akasashi hakanan acikinsu mutane namasu yabawa da ni'imarsa da ALLAH yayi masa tun akabari, duk inda kaduba cikin maqabartar cike yake da mutane ta ko ina da sukazo kawosa.

Bayan andawo su baba balarabe sukaje sukaa yimasu umma nasiha akan sud'au haquri da tsarin qaddarar da ALLAH yayi masu akan d'an uwan nasu domin yanda yasamu jama'a suna kyautata masa zato had'e da yima junansu gaisuwa.

Kwanan su baba balarabe uku sannan suka fara maganar komawarsu tunda anyi masa addu'ar uku, lokacin da sukaje wajen dady yimasa sallama akan zasu tafi kuma suna son suwuce da iyalan marigayin tunda dama shine jigonsu nazama garin kuma ALLAH yakarb'i abunsa sai dady yayi gyaran murya had'e da sake yimasu gaisuwar rashin d'an uwan nasu akaro na ba adadi sannan yace.

"Malan balarabe Ina son in roqeki wata alfarma awajenku idan zaku iya"

"Munaji alhaji ALLAH yasa batafi qarfinmu ba."

"Eh to! Banace haka ba amma Ina son ne idan har kun amince kubar iyalan marigayi anan har zuwa lokacin da zata gama takaba, nayi maku alqawarin cewa zan kula maku dasu bisa amana har zuwa lokacin idan ALLAH yabamu aron rayuwa."

Shiru baba balarabe yayi kafin yace to yabari sud'an shawarta tsakaninsa da sauran 'yan uwansa da suka zo tare, hakan yasa dady miqewa shida dr sukabar d'akin, bayan sun fita baba balarabe ya tambayi 'yan uwan nasa had'e da

Please Login or Register in order to submit comment