Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

hawwa tafara magana.

"Kam buhun uban nan, Bilki me nake shirin gani anan?, So kikeyi shi kuma yaron nawa bayan halin da yake ciki ki hallaka mani shi ta hanyar asirce manishi sai yanda kikayi dashi don mugunta?, To wallahi jinina yafi qarfinki munafukar banza munafukar wofi, hadda wani d'auko abu kina bashi abaki, kai Kuma sakaran banza da bakasan inda duniya tayi ba kasaki baki kana sha."
Yaya hawwa taqarasa fad'a tare da jawo hannunsa zatabar falon dashi tana cika tana batsewa, cike da tausayin mugun halin da ALLAH yayi mata yajarab tawar rayuwa dashi Inna Bilkisu ke kallonta kafin tace. "Dakata Yaya hawwa, kiji tsoron ALLAH, kiji tsoron ALLAH kitausayawa yaron nan halin da yake ciki, a matsayinmu na iyaye bamu kad'aine ALLAH ke hukunta 'ya'yanmu akan haqqoqan muba idan suka danne, hatta mu kanmu ubangiji na kamamu da haqqoqansu kuma yayi mana hukunci mai tsauri idan muka taushe masusu, su amana ne agaremu kuma ALLAH zai tambayemu, Nuraddeen d'anane duniya da lahira tunda nake auren qanen mahaifinsa, don haka banga ribar da zan samu ba idan nacutar dashi, dama haka rayuwa take idan kana abu sai kayi tsammanin kowa ma yanayi, kitaka sannu haqqin d'anki kad'ai ya isheki aduniya balle na sauran rayukan da basuji basu gani ba, agidannan Banda darajar mijina da yayansa da kike ci saita haihuwa da kikayi badon haka ba da saina koya maki darasin rayuwa, amma ko yanzu muje zuwa da sannu duniya zata koya maki."

Rab'awa tagefensu tayi tawuce bayan ta d'auko kwanon abincin data kawo masa tare da furar da Yaya hawwa ta b'arara,

"Kagani ko shashashan banza da wofi, bakasan mai sonka ba, dubi yanda tayi tsaye ta cimun mutunci agabanka amma ka kasa cewa uffan saboda tariga data gama da kai, dallah wuce mutafi samna sakaran banza, biye yake da ita kamar hoto har suka fito sashen tana rafka uwar masifa da zagezage, daidai bakin qofa taci karo da fadeela Inna taturota tagyara inda furar tazube, hannu tasa ta bangajeta gefe da kad'an tafad'e da sauri Nuraddeen yariqe mata hannu.

"Gidan ubanwa zakijene" Yaya hawwa tafad'a tana watsa mata wani mugun kallo,

"Inna ce tace nazo nagoge inda fura ta zube.."

"To ahalin kicifaffi anyo gadon ashibilanci da iyayi maza kiwuce kibar nan kafin in makeki, shegu d'iyan bani na iya.."

Da sauri fadeela tabar wajen tun kafin tarufe baki ita kuma tajawo gambun qofar tarufe har lokacin tana riqe da hannunsa kamar wani qaramin yaro,

'Daki tashiga dashi ta zaunar saman gefen gado ta jawo wani kwano da dambu aciki sannan ta d'ebo ruwa ga kofi ta ajiye agabansa,

"Maza kaci kada yunwa ta illataka, yanzu haka duk inda ta tafi tana can hankalinta kwance tabarmu da tashin hankali anan." 'Doga kansa yayi yana kallon mahaifiyar tasa had'e da cewa.

"Kamarya duk inda tatafi innar mu, taya Rashida zata bar gidannan da tsohon cikinta haihuwa ko yau ko gobe?."

"Eh mana, ai haka na iya yuyuwa idan taji tagaji da zama dakai, to don ta tayar maka da hankali tunda taga kana sonta, ya kamata kiyi tunani anya ba guduwarta tayi ba tunda auren naku na had'ine?." Murmushin da yafi kuka ciwo yayi kafin yace.

"Innar mu kenan! Ai aurena da Rashida ba had'in iyaye bane balle tagudu tabarni, ni naganta da kaina nace Ina sonta kuma itama ba tilastata akayi sai ta aureni ba, ita da kanta taji tana sona kuma ta amsa mani, kinga batun guduwa anan ga masoyan da sukaji sun amince da juna ai bata taso ba, Rashida inada tabbaci akan d'auketa akayi amma su waye? Meyasa? Duka ban sani ba, tsorona d'aya aduniya kada ace mahaifiyata nada sa hannu aciki, Ina addu'a kar ALLAH yasa tsanar da kike yimata bata Kai mizanin da Zaki iya salwantar da rayuwarta ba."

Hannuwanta yariqo had'e da durqushewa agabanta sannan yaci gaba da cewa, "innar mu duk duniya banida maccen da takai matsayinki araina domin ke kika haifeni, kikayi d'awainiya dani tun Ina cikin cikinki har zuwa girmana amma duk da haka farincikina da kwanciyar hankali na suna tattarene a hannun matata Rashida, don ALLAH idan kinada masaniya akan inda take don ALLAH innar mu kisanar dani kafin nakoma marar amfani adoron duniya."

Wani banzan kallo tayi masa kafin a hasale tace. "Tashi fita kabani waje tunda naga kai bakasan abunda kakeyi ba." Tsom ya tashi ya miqe jikinsa ba k'wari ko kad'an ya koma sashensa, bai jima da shiga ba yafito sanye da wasu kaya yamiqi hanyar fita gidan.

"Ina zaka?" Yaji muryar Yaya hawwa tana fad'a cike da gadara, batare daya juyo ba yace.

"Zantafi nemo farincikina." Bai tsaya sauraron abunda zatace ba yaci gaba da tafiya, daidai bakin qofar fita gidan yaci karo muneera tashigo aguje da alama wani tajawo sauran k'iris ta bangajesa tawuce, jikinta na rawa tatsaya tana fad'in. "Don ALLAH ya nura kayi haquri" kota kanta baibi ba yawuce abunsa batare dama yasan da ita awajen ba, biyo bayansa tayi tana fad'in, "ya nura, ya nura."

Ko juyowa beyi ba balle ma yakalleta har tasa ran zai tanka mata, hakan yasa tafashewa da kuka had'e da rugawa cikin gida, da sauri Inna ruqayya tafito tana fad'in.

"Ya rasulu manzon ALLAH, muneera keda wa acikin gidannan, fad'amun inji waya tab'aki ne, qara tale baki tayi tana cigaba da rere kukanta wanda nan take yasa hankalin mutanen gida yadawo wajen saboda sanin halin da ake ciki,

"Ke muneera lafiya? Wata tsohuwa data dudduqo daga wancan b'angaren dake cikin gidan tafad'a tana tokare sandarta akusa da ita, "ke fad'amun waya tab'eki ko d'an gidan uban waye inje dashi har iyayen da suka haifesa inci masu mutunci tas, fad'i Ina jinki keda waye?"

Cikin kuka tace, "Inna koba ya nura neba inayi masa magana ya qyaleni ko kallona beyi ba yai tafiyarsa." Kallon dan dazon mutanen gidan dake wajen Inna ruqayya tayi had'e da had'a wasu yawu masu kabrin gaske saboda sanin halin 'yar tata, hannunta tariqo tana fad'in. "To zo muje d'aka kiji kinsan yau yana cikin yanayi marar dad'i."

"Wlh Babu inda zanje ai bani na b'atar masa da mata ba balle yadinga qyaleni yana fushi dani kuma Inna ai haka kukeso tunda kunce bakwa son ya aureni tana cikin gidan."

'Dago kai gaba d'aya mutanen gidan sukayi had'e da maido kallonsu ga inna ruqayya data fara kalle kallen gefenta, tsohuwar dake kusa garetace tace. "Ke muneera kirufa mana asiri gidannan, wannan sheri da kike neman qaqabawa uwarki har ina?"

"Ai wlh basheri bane itama innar tasan gaskiya nafad'a, har magani suka karb'o aka barbad'awa ya nura saboda akarkato zuciyarsa yafara sona muyi aure amma gashinan beyi amfanin komai ba, ni wlh ALLAH bazan yarda ba sai an auramun ya nura." Taqare maganar tana bubbuga qafafuwa tana kuka.

Ana haka saidai mutanen dake wajen suna tafa hannuwa suna sallallami sukaga Yaya hawwa da bawanda ya lura da lokacin data fito tayi tsaye wajen tana kallon sakarci irin na muneera tayo wani irin kukan kura ta damqi wuyan Inna ruqayya tana fad'in

"Buhun uba, d'an nawa zaku kai ayiwa asiri don kuna munafukai algungumai, to wallahi ALLAH baku isa ba yau nafison garin bebeji ya tarwatse ya watse akan wannan rashin mutunci da kuka tafka mani matsiyata da bakusan abun arziqi ba." Taqare maganar tana kaimata naushi a gefen fuska, kokuwa suka shigayi ita da ita cikin sanyin muryar qasaqasa ta yanda baza'a jiba Inna ruqayya ta dinga bata haquri gudun kada suyiwa kawunansu tonon asiri, Amma saboda yanda Yaya hawwa taji zafin abun aranta ko saurarenta batayi taci gaba da tsigarta tana jifarta da miyagun kalamai, cikin b'acin rai da hasala Inna ruqayya tasa hannu biyu biyu ta tureta tana fad'in. "Ke hawwa bari nafad'a maki shuru shurufa ba tsoro bane, sannan shi abun fad'i kowa yana dashi qulle agindinsa saidai idan bai fito bane, karkiga na qyaleki kinemi maidani sakarai agaban mutane Ina d'an naki ba damuwa da rayuwarsa kikayi ba balle har kinuna mani cewa ke uwar sace, naji munkai nura wajen mlamin tsibbu a karkato da zuciyarsa ga muneera, ai nayine don farincikin 'yata, amma kefa? d'an naki kike zuwa kikai wajen bokaye don farin cikin kanki dana wasu, ko kina tunanin ban san cewa ke kika b'atar da yarinyar nan ba da har zakizo kina yimani cin mutunci agaban mutane, to
anyi masa asirin duk abunda kika iya kije kiyi, in shed'anci kike taqama dashi na damaki na shanye Kuma wallahi da sannu zan koya maki hankali, banza ke atunaninki duk wannn walaqancin da kike yimani kinasa ran zan barshine yatafi abanza? Wlh kinsha qarya dama jira nake kigama yaqin ni kuma nakwashe ganimar, kuma tunda kika yimun wannan tozarcin wlh saina tabbatarwa da duniya cewa kece nan kika b'atar da surukarki kika sa ahallaka maki ita don bakya sonta." Inna ruqayya taqare maganar tana shed'a guda guda had'e da gyara d'aurin d'an kwalinta.

"Kan hatta kazak kaza..ni zakiyiwa sharri ruqayya don 'yarki ta tona maki asiri, to baki Isa ba wlh..." Nan suka shiga tonawa kansu asiri mutanen dake wajen nata la'antarsu da miyagun halayensu.
Inna Bilkisu kuwa fashewa tayi da kuka tashige d'aki tana mai tausayawa halin da Rashida keciki, baffa kuwa da tun d'azu suna bakin qofar shigowa tsakar gidan yanata ko kuwar shigowa ciki saboda abunda kunnuwansa suka jiyo masa lokacin da zasu shigo amma baffa Usman yariqesa yace yabari har sai sun gama fad'in komai da zai zamo masu hujja tukuna, kasa haquri yayi ya fizgikke daga riqon da yayi masa jikinsa narawa idanuwnsa na hawaye yashigo yana nuna yaya hawwa da hannu yace....






*ALLAH KAJIK'AN IYAYENMU*πŸ‘πŸ˜­
[8/17, 10:19] Billy S Fari: πŸšΆβ€β™€οΈπŸšΆπŸ»β€β™‚οΈ *SANNU SANNU*πŸšΆπŸ»β€β™‚οΈπŸšΆβ€β™€οΈ
πŸ’Ž _Bata hana zuwa..._πŸ’Ž


_WRITTING BY:_ *BILLY S FARIπŸ’Ž*

_DEDICATED TO:_ *BLOOD SISTER'S (AMZAHFAZ)*πŸ’‹

_BESTOWED TO:_ *ZAINAB AL-AMIN (MOM NA'EEM)* AND *AMINA UBA AYUBA (OUM ASHFAQ)*πŸ’ž

*DOMIN FARINCIKINKI SISTER SADIYA ZANGO (MIEMAH)*πŸ’–

*FATAN ALKHAIRI AGAREKU MOMMAH ME NANA HAFSAT (MISS XOXO) AND MAMANA HAFSAT RANO(OUM AFFAN)*❀️

Page___40πŸ’Ž

Kin cuceni hawwa kinci amanar zaman da mukayi dake, haqiqa ba qaramin kuskure natabka ba wajen zab'awa d'ana ke amatsayin uwa, gashi yanzu duk wani farincikin mu dani har shi kin rusa mana shi, naso nacigaba da haqurin zama dake ko don albarkacin d'anmu har lokacin da mutuwa zata rabamu, amma bazan iyaba, ko kad'an bazan iyaci gaba da zama da mushirikar mace da bata tsoron ALLAH ba kamarki, macen da batada imani da tausayi, son kanta yasa ta cilla mutane da yawa cikin wani hali, ALLAH yasani nayi iya qoqarin zaman da zan iya dake amma yanzu kitafi na sakeki, na sakeki hawwa saki biyu, keji duk abunda kika yimun nayafe maki duniya da lahira albarkacin yaronmu, Amma Ina so kisani bazan tab'a d'aga maki k'afa akan sauran haqqoqan bayinsa da kika zalunta ba, wlh ni da kaina zan tsaya na bimusu shi koda duka abunda ALLAH ya mallakamun aduniya zai qare musamman haqqin wannan qanqanuwar yarinyar da kika d'auka, yarinyar da zuciyarta bata san komai ba sai tarin qauna da soyayya agaremu, tayi mana halacci mai d'inbin yawa kama daga soyayyar da take yiwa d'anmu har zuwa kulawar data bani agidannan nasamu lafiya da haqurin cin kashin da kika tayi mata amma kikasa qafa kika shure duk wud'annan abubuwan keda marasa imanin da kuka had'a baki kuka cutar mana da ita, in sha ALLAH, ALLAH bazai barki ba har sai ya hukuntaki tun aduniya kafin kije lahira." Yana gama maganar yajuya yafice daga gidan ko gani bayayi saboda tsananin b'acin rai, tafiya mai nisa yayi baffa Usman na biye dashi kafin yasamu waje ya zauna, kuka ya shiga rerawa tamkar qaramin yaro cike da nadamar sanin Yaya hawwa da yayi aduniya, gaba d'aya ji yakeyi yatsani duk wani abu daya dangance ta balle ita kanta, Saida yayi kukansa mai isarsa sannan yamiqe suka nufi asibiti, akan hanyarsu suka gamu da baffa Ali sai faman sabbatu yakeyi wai Nuraddeen ya maisheshi d'an iska ya gudu daga asibiti yabarshi, gashi yasa agaban mutane likita yayi mashi wala qanci, har ya d'an gotasu zai wuce baffa Usman yajuyo don da alama duk kansu basuga juna ba sai yanzu.

"Ali Ina kanufa kuma haka?, Ko har Nuraddeen d'in yatashi an baku sallama ne.?"

"Af Yaya kun dawo? Injin an dace anga yarinyar?, "

"Kai ka amsamun tambayar da nayi maka, yarinya kam idan da rabon agata ko anqi ko anso ai ganinta za'ayi da yardar ALLAH." Baffa Usman yabashi amsa yana kafesa da idanuwa,

"Aw Nuraddeen kake magana?, ai kabarni da shashashan yaro, wai daga infita inyo sallah yaronnan ya gudu daga asibiti, sai dawowa nayi natarar da likaita na tambayarsa yarufeni da fad'a agaban mutane baka ganiba abunnan zak kunya."

Shiru baffa Usman yayi cike da mamaki yana kallonsa kafin yaji muryar baffa yace

"Ba komai Aliyu, Nuraddeen ai d'an kane duk abunda kayi masa ko kabari ya samesa kanka kayiwa, shidai zumunci yananan rataye aqasan al'arshi duk wanda ya gyara yaga da kyau wanda kuma ya munana yaga akasin haka, ni dai addu'a ta d'aya shine ubangijin dake tare da waccan yarinyar shima yakare mani shi aduk inda ya tafi, kuma Allah ya qaddara had'uwarsa da ita cikin amincinsa da yardarsa."
Yana gama fad'ar haka yanufi hanyar gidan daya d'aukarwa su Nuraddeen haya yana fad'in. "Usman zo mutafi."

Bayansa baffa Usman yabi shi kuma baffa Ali yawuce gida yana maijin d'acin maganganun da baffa yafad'a masa, "wato duk abunda nayi masa baiga qoqarina ba, amaimakon yaga laifin d'ansa laifina yake gani, ai shikenan gobema ranace" haka baffa Ali yaba hanya yana fad'a cike dajin haushin d'an uwan nasa har ya isa gida,

Yana isa kururuwar yaya hawwa yafara jiyowa tun daga zaure har ya iso cikin gidan, gaba d'aya ta zauce sai masifa takeyi tamkar wata tsohuwar mahaukaciya, kallo d'aya yayi mata ya kauda kai Inna ruqayya na gefe yace da ita, "yau mutuniyarki ko lafiya?, Ko duk cikin tsarin data tanada ne yau don kar agano ita ta halakarwa da mutane 'ya?"

"Ohommata! Saki daine data sha yake neman zautar da ita bayan asirinta ya tonu."

"Tab kice yau taga fushin maza, ai dama Yaya haurine dashi amma idan ransa yab'aci ba'a mai kyau, ni kaina d'agamun qafa yakeyi saboda wasiccin da baaba tabashi shiyasa kikaga Ina cin karena ba babbaka, badon haka nan ba wlh inya riqani sai buzuna, kawai tagodewa ALLAH da yasa sakin d'aine yayi mata bai had'a mata da duka ba."

"Ita dai tasani can taqare mata."
Kujera Baffa Ali ya jawo 'yar ta zaman tsakar gida ya zauna yan sauraren asharariyar da Yaya hawwa ke d'urowa daga shiyarsu yace.

"Ikon ALLAH! Shin waike rakkiya meya jawo wannan sakin da maganganun da naji tana yab'owa masu kama da gugar zana, ko dai Yaya yagano ita tayi tsiyar?"
Nan Inna ruqayya takwashe qarya da gaskiya tafad'a masa akan abunda yafaru, wata irin zabura baffa Ali yayi yna kallonta sannan yace, "Amma wannan muneera anyi d'ebabbiyar yarinya, yanzu duk wannan fitinar ita tajawo mana ita? to tsakanina da ALLAH tajawo mana abunda yafi qarfinmu, wannan matar mara imani da kike gani ba qyalemu zatayi ba, shi kuma yaya da kikaji yayi shiru baice maki komai ba akwai had'ari, don wlh shirunsa da kike gani ba alkhairi bane."

Nan take tsoro da fargabar abunda zai biyo bayansu ya mamaye masu zukata, aran baffa Ali kuwa tunanin yanda zasu tsere na kwanaki ya shigayi don ya tabbata baffa zai juyo garesu, babban takicinsa d'aya yaran dake gabansu, idan sun gudu to a hannun wa zasu barsu?.

β€’β€’β€’ β€’β€’β€’ β€’β€’β€’
A b'an garensu Dr nura kuwa saida yakai Fatima d'akin da aka kwantar da jaririn Rashida tukuna yaje yabiya bill d'in kud'in da wata nurse tabashi lokcin da suka dawo nan inda Rashida take sannan yayiwa Fatima sallama bayan ya tabbatar mata da ko nawa ake buqata idan wata matsala ta taso ta bud'e safe d'in da yake ajiye kud'i ta d'iba, wata nurse takira tace don ALLAH takula mata da patient d'in dake gado no15 zataje tadawo sannan taje tashiga motar da Dr keciki yana jiranta, Tasha yanufa yasamu motar da zata kaishi kano ita kuma tajuyo da motar zuwa asibiti,

Bayan kwana biyu Rashida tafara jin sauqi sosai bayan ta shanye tulunan oxygen har guda biyar haka yaronta shima saida yashanye oxygen uku sannan yadawo normal don gaba d'aya likitoci da nurses d'in dake d'akin har sun fitar masa darai sai gashi cikin ikon ALLAH da yardarshi yatashi, yana samun lafiya sosai shima don har an fara kawo matashi yau ta bashi nono, sosai take samun kulawa wajen Fatima da ita har babynta kullum tana tare dasu, musamman tasamu wata tsohuwa a asibiti irin masu shara da mopping d'innan tana biyanta kullum idan zataje gida tayo wanka tare da had'o abinci sai tasa ita kuma ta kula mata da ita, gaba d'aya Fatima ta sadaukar da lokacinta a asibitin don ganin tabasu cikakkiyar kulawa,

Zaune take agefen gado tana kallon yanda nurse d'in dake gyarawa Rashida yanda zataba jaririnta nono, cike da sha'awa take kallonsu tana murmushi kafin can taji 'yar qarar Rashida saboda zafin da taji lokacin da yaron yafara Kama nonon yanasha, da sauri tamiqe tazo kusa gareta tana shafa kanta.

"Sorry kiyi hak'uri ko! Haka kowace uwa keji lokacinda yaronta yafara kama nonon, amma idan kika jure ahankali zai dena zafin gaba d'aya."

Ita dai Rashida kasa amsa mata tayi sai faman b'ata rai takeyi tana cije baki saboda zafin da takeji, dariya nurse d'in tayi had'e da yimata sannu sannan tabar wajen, Saida yasha ya qoshi tana kallonsa kamarsa gaba d'aya babu inda yaron yabarota kamarshi sak da ita farin fatarta kad'aine be biyo don duk da take da duhu ga alama bazaiyi hasken taba, wasu zafafan hawayene suka zubo mata tanajin wata irin qauna yaron da soyayyarsa na mamaye mata zuciya, a hankali tashiga rera kukan tausayin kanta dana d'anta, ko kad'an bata tab'a tsammanin cewa tsanar da uwar mijinta keyi mata ba tayi zurfin da zata iya salwantar mata da rayuwa ba har tarabata da farincikinta, gashi yanzu tahanasu jin dad'in rayuwarsu, tahana d'anta yaji d'imi da soyayyar mahaifinsa, tajefata cikin wata rayuwar da batasan ko meye makomarta ba, ta nisantata da iyayenta ta cutar da ita, tun kukan nafita ba sauti har yafara bayyana, Fatima dake zaune tana kallonta ta karb'i yaron don har ya soma bacci had'e da cewa.

"Maman baby." Don da haka take kiranta sannan taci gaba da cewa. "Kiyi hak'uri, duk da dai nasan cewa awannan yanayi da kika tsinci kanki dolene kiyi kuka amma idan kinduba duk wata gata da ALLAH keyiwa bawa yayi maki, idan saboda ki cutu akayi maki wannan abun ALLAH yahana tunda gaki da ranki kuma da lafiyarki, idan kuma saboda a cutar da abunda ke cikinkine shima ALLAH ya karesa tunda gashi kin haifi abunki cikin qoshin lafiya kuma ya rayaki, idan kuma don asalwantar maki da rayuwane, ALLAH yadubeki da idanuwansa na rahama ya kad'oki a hannun da baza'a tab'a cutar dake ba, don ALLAH ko meye kiyi haquri, in sha ALLAH dakin samu sauqi zamu hannuntaki ga iyayenki, wannan kukan naki bana sonsa sai inga kamar nayi raggwancin baki kulawar daya kamata nabaki ne, keda yakamata kiyi farinciki ALLAH yabaki babynki kyakkyawa tubarkallah kamar ke, natabbata idan mahaifinsa ya ganesa baqaramin jin dad'i zaiyi ba, ko yanzu kika mutu kinbar magajinki mai kama dake da zai gani ya dinga jin sanyi, kiyi haquri kinji ko? In sha ALLAH komai zai daidaita."
A maimakon Rashida tayi shiru sai kukan nata ya sake tsananta, awannan karon ba abunda takewa kuka irin rashin sanin halin da habibynta ke ciki, meyasa duniya tayi masu haka? Me yasa za'a rabasu?, Meyasa za'a haramta masu renon d'ansu da bashi tarbiya atare?, wud'annan tambayoyin kad'aine keyi mata yawo a qwaqwalwa yayinda alokaci d'aya kuma suke sake tunzura zuciyarta wajen sata zubar da qwalla, yanda take kukan yasa nan take b.p d'inta ya sake hawa kasancewar har bayan ta haihun bai koma mata normal ba, da sauri Fatima taje ta kira likita tana d'auke da babyn, allurai akayi mata kafin alaqa mata gorar drip a hannu, nan take bacci yayi awon gaba da ita, ita kuma Fatima taje ta maida jaririn d'akin da ake kula dashi don dama kawoshi sukayi yasha nono.

β€’β€’β€’ β€’β€’β€’ β€’β€’β€’
Nuraddeen kuwa yana fita bai zame ko ina ba sai qauyen yarimawa gidansu Rashida don sanarwa da iyayenta halin da ake ciki, abunda bai sani ba tuni su baffa sun sanar masu har dalilin haka ya haifar masu da shiga wani halin, bakin qofar gidan ya tsaya ya ganesa arufe, waige waige yafarayi yana so yaga ko wani yarone ya tambayesa saiga makwabcinsu ALLAH yakawo masa, da sauri yaqarasa wajensa ya gaishesa had'e da tambayarsu ko Ina masu gidan, nan yake sanar dashi halin da suke ciki da abunda ya samesu, wani irin jirine ya d'ebesa da sauri ya dafe iccen dake kusa dashi yana fad'in. "Innalillahi wa'inna ilaihirrajiuun."
Anan maqwabcin nasu yatafi yabarsa anan tsaye don da alama bai san cewa shid'inne surikinsu da ake zancen matarsa ta b'ace. Da sauri yabi bayansa ya tambayesa awace asibiti suke ya fad'a masa yayi masa godiya sannan ya wuce asibitin cike da damuwa aransa.

Yana shiga cikin asibitin ya hango Baba balarabe yafito da ward d'in da aka kwantar da umma riqe da wasu takardu a hannunsa, d'aga qafarsa yayi don yasamu ya cimmasa kafin ya b'acewa ganins,

"Baba.." Nuraddeen yafad'a daidai lokacin daya isa inda yake, juyowa yayi yana ganinsa yad'anyi murmushi. "A'a Nuraddeen kaine tafe a wannan lokacin."

"Eh baba ina wuni.?"

"Lafiya klw. Zo muje musamu waje muzauna ko? Wai takardu ne na amso da zamuje scanning da ummanku gobe idan ALLAH yakai ranmu." Baba balarabe yafad'a yana tura tamardun ahannu, gaba d'aya Nuraddeen jinsa yayi kamar wani soko saboda sakacin da take ganin kamar yayi ya b'atar masu da 'yah Wanda har hakan ya jefa mata iyaye cikin matsala amma duk da haka babu wani sauyi d'aya gani atattare dashi da zai nuna yana jin haushinsa.

Tafe suke shi da baba balarabe yana jajanta masa abunda yafaru tare da yimasa 'yar nasiha akan haquri da kuma yarda da qaddara har suka iso ward d'in da aka kwantar da baba, Baqaramin tashin hankali Nuraddeen ya shigaba ganin halin da baba yake ciki, gaba d'aya b'aren jikinsa na hagu ya shanye bakinsa ya karkace baya iya magana, duqewa yayi bakin gadon ya fashe da kuka yana maijin gaba d'aya yatsani rayuwarsa ta duniya, a hankali baba ya d'ago hannunsa na dama ya aza saman kansa yana so yayi masa magana amma yakasa sai dai kawai ya dinga d'an shashshafa kansa hawaye shima nafito masa agefen idanuwa.
Ganin kukan nasa bazai qareba yasa baba balarabe d'agosa daga duqen da yake yariqo hannunsa suka fito tare,

"Baba meya kamata kirani dashi aduniya? Sakaran miji, ko shashasha ko kuma wanda baisan abunda yakeyi ba? nayi sakacin b'acewar matata gashi nacilla iyayenta cikin wani hali kuma nakasa gano wace mafita zan samu don gyara wud'annan kurakuran da nayi, baba bansan ya akayi ba, bansa ta ina aka shiga har cikin gidana ba aka rabani da matata, nashiga waqi'ar da banida mataimaki aciki sai ALLAH, damuwata d'aya shine me yasamu Rashidata, Ina take yanzu, meya faru da ita duka ban sani ba..."

Ganin yanda yake suruttai kamar wani zararre yasa baba balarabe yayi saurin katsesa tare da cewa.

"Nuraddeen rashin Rashida ba kaikad'ai ya shafa ba, hattamu iyayenta da muka haifeta muna cikin wannan damuwar amma dole zamuyi haquri mubarwa ALLAH komai har zuwa lokacin daya qaddari muganeta, baffan nan ka sunyi qoqari matuqa wajen zuwa dubota sannan shi baffanka Usman yakai cigiyarta a kafafen yad'a labarai, don haka kayi hak'uri ka koma gida kayita addu'a, natabbata ubangijinmu yana tare da ita aduk inda take ko don tausayin halin da take ciki."

Sosai yayita bashi magana kafin ya rakasa har bakin gate d'in asibitin bayan ya kaishi yagano umma da har zuwa lokacin kwance kawai take tana ambatar Rashida, Rashida. Nan ma d'in sai dai yayi kuka sosai tare da addu'ar ALLAH ya bayyana ta kodon iyayenta sufita cikin wannan yanayin rayuwa da aka jarabcesu da ita.
Kid'in daya

Please Login or Register in order to submit comment