Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya kurb'i tea d'in yana sake motsasa da cokalin dake ciki saboda zafinsa sannan yace.

"Baffa kayi hak'uri bisa qin fahimtarka da nayi akan maganar tafiyata, a yanzu amince zanje saboda gujewa dana sanin rashin amfani da damar dake iya zowa mutum sau d'aya arayuwarsa, zanje nayi karatu, karatun da zansa kuyi alfahari dani har iya qarshen rayuwata, karka manta lokacin da kake jinya kaso ace d'aya daga cikin zuri'arku yayi karatu a fannin lafiya, to tabbas zan cika maka wannan burin da yardar ALLAH, al-amarin innar mu da Rashida kuwa, wa'ufawwidu amri ilallah, natabbata zai dafa maka wajen kula da komai, don haka shirin da nayi bazan warwaresa ba, da yardar ALLAH zantafi."

Kallo baffa Usman baffa yayi mumushi d'auke da fuskarsa yace.

"Kaji ko Usman, dama nafad'a maka bazan takura Nuraddeen ba, bazan tilasta saba amma ina da yaqinin bazai Bari wannan damar da ALLAH yabamu tawuce Saba."

"Alhamdulillah haqiqa naji dad'in sauya wannan hukuncin da kayiwa kanka da kayi, ubangiji ALLAH yayi maka albarka yasa kaje cikin sa'a, ALLAH yafaranta zuciyarka ybka kariya aduk inda kake kuma yayi maka jagora.."

Haka baffa yaci gaba da kwararo masa addu'o'i yana riqe da hannunsa baffa Usman na tayashi fuskokinsu d'auke da farinciki, murmushi Nuraddeen yayi ganin haka a fuskarsu had'e da cewa.

"Saidai baffa nakasa zuwa wajen baba balarabe inyi masa bankwana saboda rashin sanin da wace irin fuska zan kallesa in iya fad'a masa cewa zanje karatu waje a daidai lokacin da nine na zamo silar b'atan 'yarsa da kuma iyayenta.

"Karka damu Nuraddeen nasan bayada matsala zai fahimceka, Amma yanzu lokaci yaqure saboda qarfe bakwai naji ance zaku had'u a babbar ma'aikatar jahar nan don qarfe takwas jirginku zai tashi, don haka ni zani magantu dashi da yardar ALLAH kaji ko?"

"Shikenan baffa babu damu." Yafad'a tare da shanye sauran tea n ya ajiye cup d'in agefe, hannu yasa aljihu ya fiddo kud'i ya miqawa baffa.

"Ga wannan baffa, Inna Bilkisu ce da sauran mutanen gida da naje yimasu bankwana suka bani, banso karb'a ba Amma sun tilasta adole na karb'a."

"ALLAH sarki, angode ALLAH yabada ladar zumunci,"

"Amin baffa."

"Yawwa Usman ka tayamu godiya idan kaje, ALLAH yasaka da alkhairi."

"Amin Yaya Babu komai ai yiwa kaine." Baffa usman yafad'a yana murmushi.

Nan suka shiga fira tare dayi masa nasihohi kala kala akan yariqe addininsa da al'adunsu nad'an bahaushe idan yaje kafin baffa yaje ya d'auko kud'ad'en da yake ajiya saboda tafiyar. Saida yasake qidanyasu dubu d'ari biyu da ashirin don ya tab'a wasu ma sannan ya miqawa Nuraddeen yace.

"Ga wannan ka qara dasu, banida cikakken qarfi ko arziqi da na yimaka fiye da hakan, to kayi haquri dasu su kad'ai ALLAH ya horemun." Qin karb'a yayi had'e da cewa

"A'a baffa kabarsu ai su zasu bamu duk abubuwan da muke buqata idan munje, muradinsu kawai muyi karatu sosai mudawo mutaimakawa qasarmu, don haka kabarsu akula da lafiyar innar mu dasu."

Daqyar baffa suka tilastasa ykarb'i dubu d'ari suka ajiye d'ari da ishirin d'in kamar yanda ya buqata.

Shirune yabiyo bayan wasu lokuta kafin Nuraddeen yace "baffa kuroqamun sa albarkar baffa Ali koda bayan natafine a matsayinsa na mahaifi agareni, naje nayi masa magana nafad'a masa zancen tafiyata amma ko juyowa beyi ya kalleni ba."

Murmushin takaici baffa yayi zuciyarsa cike da damuwar halin da d'an uwansa ke nunawa, baffa Usman ne yace.

"Kayi haquri Nuraddeen, in sha ALLAH komai zai wuce kaji?"

"To baffa Usman ALLAH ya yarda."

Miqewa baffa Usman yayi yace zai wuce baffa ya rakkosa har qofar gida suka yiwa juna seda safe sannan yatafi.

Aranar kam zaune baffa suka kwana shida Nuraddeen suna firar bankwana cike da shauqin rabuwa da junan da zasuyi.

Tunda asubar fari Nuraddeen ya ida shirya kayansa lokacin shima baffa yagyara tsaf suka nufi can gidan saboda Nuraddeen naso yayi bankwana da mahaifiyarsa, a kan hanya suka had'u da baffa Usman yanata sauri zaije can suka sake juyawa suka nufi gidan tare, a bakin qofar d'aki suka tsaya Nuraddeen yabud'e ya shiga Yaya hawwa na kwance tana bacci bisa tabarmar data rage kad'ai a cikin d'akin don gaba d'aya Nuraddeen ya kwashe kayan dake ciki saboda gudun kada tajima kanta ya mayar dasu acan d'ayan d'akinsa nada.

A hankali ya qarasa ciki yaduqa saiti fuskarta yakai hannu zai shafa sai kuma ya fasa, wasu irin hawaye suka zubo masa a fuska yayi saurin gogege yana fad'in.

"Innar mu ALLAH yabaki lafiya, ALLAH ya yaye maki wannan lalurar albarkacin haihuwa da tarbiyar da kka bani, ALLAH yasa kaffarar kankarar zunubbanki ne wannan hlin da kike ciki, Ina maibaqincikin barin qasarnan babu addu'arki da sanyawar abarkarki atttare dani, fatan alkhairi uwata kafin nadawo agareki."

Yana gama fad'ar haka yamiqe da sauri yana hawaye yabar d'akin, kamar an tsinkili Yaya hawwa ta tashi da qarfi tanufo wajen qofar tana fad'in.

"Nura, nura, kana Ina d'ana, Ina kake nura"
Jawo qofar baffa Usman yayi da sauri ya rufe had'e da murd'a key.

Part d'insa ya bud'e har ya fara qura yana bin ko Ina da kallo, memory d'in da sukayi da Rashida tashiga dawo masa akai musamman daya kalli kitchen wanda ya zamomasu tamkar wani waje da suke d'ebewa juna kewa wajen aikawa da juna kalaman soyayya da kuma isar da saqon zuciya, bud'e cikin d'akin yayi ya shiga nan take yaji qafafuwansa na nema su gagaresa tsayi ya durqushe wajen yana kuka kamar ransa zai fita.

Yanajin qarar sautin ihu da bugun qofar da yaya hawwa keyi tana Kiran sunansa Amma rad'ad'in da yakeji azuciyarsa yanzu daya dawo masa fal ba zaisa ya iya sake waiwayarta ba,

Qarar wayarsa data fara ruri yasashi tsaida kukan nasa had'e da miqewa yashiga uwar d'akan ya jawo wata jikkar dake d'auke da pics d'in aurensu na ranar walima yaciro hotunanta inda take ita kad'ai tare da d'aukar wayarta data bari sannan yabar d'akin, Saida ya kulle part d'in yaba baffa makullan yana d'iba agogon hannunsa qarfe bakwai daidai ya d'auki butar dake gefe ya wanke fuskarsa su Inna Bilkisu na tsaitsaye suna kallonsa idanuwansa sunyi jawur saboda kukan da yayi har sun d'an kumburo.

"Inna Bilkisu mu zamu wuce asamu a addu'a." yafad'a yana kallon muneera data rakub'e gefe ya sakar mata murmushi, dashire hauru tayi tana fad'in.

"Ya nura ALLAH ya kiyaye hanya yabada ilimi Mai albarka, ALLAH yasa koda zaka dawo aunty rashidarka itama tadawo, akaro nafarko da yaji muneera tafara burgesa kenan yasake sakar mata wani murmushin had'e da cewa

"Amin muneera, ALLAH yazab'a maki kema miji nagari kafin nadawo In isko kin haifi mani d'a ko d'iya."

Washe haqoranta tayi gaba d'aya tana fad'in "amin ya nura amma d'an bunni irinka." Juyawa yayi yana kallon Inna ruqayya da tun d'azu ke zabga masu wata it muguwar harara had'e dayin tsaki yace. "Nawuce Inna ruqayya."

Ko kallonsa batayi ba balle yasa ran zata tanka masa daga qarshe saima tashi da tayi tabar wajen,

"Nuraddeen zo mutafi mana ga malan bello can a qofar gida da motarsa kai kad'ai muke jira." Baffa Usman yafad'a tare da bin bayan baffa daya fice daga gidan, rufa masu baya shima Nuraddeen yayi inna Bilkisu da sauran mutanen gida nabiye dashi suna yimasa addu'a,

Koda suka isa har motocin wud'anda zasuje sun soma tashi zuwa filin jirgin aminu kano da sauri yafita shima yaje ya gabatar da takardar shed'arsa da i.d card d'in da suka bashi sannan akace yashiga motar dake qoqarin tashi wacce itace ta qarshe.

Bayansu su baffa suka sake bi har suka isa filin jirgin, suna Isa aka fara kiran sunayen matafiyan kafin akai ga sunansa yaje ya duqa ya kwashi albarkar su baffa tare da rungumesu yana mai sake roqon dasu kula da mahaifiyarsa Wanda ananbaffa ya tabbatar masa da cewa kada yadamu suma dasun koma zasu wuce sokoto sufara amsar katin Kai mahaifiyar tasa asibitin ta mahaukata da sauran shire shire.

Yaji dad'i sosai kuma yasamu qwarin guiwar tsayawa ya jajirce akan karatunsa don ya tabbata mahaifin nasa zaikula da mahaifiyarsa duk da kuwa bata a qarqashin inuwar aurensa.

Basubar wajen ba har saida sukaga tashin jirginsu sannan suka juyo suka dawo gida cike da kewarsa....

_'yar uwa mekika fahimta acikin rayuwar littafin SANNU SANNU?, Nidai nafahimci girman uwa komai lalacewarta awajen nuraddin😍don haka bana wasa da mamana kaima karkai wasa da mamankaa,πŸ’ƒπŸΌπŸ’ƒπŸΌ domin itacee farincikinka duniya gabaa d'ayaaa (D.one voice)_






*ALLAH KAJIK'AN IYAYENMU*πŸ‘πŸ˜­
[11/14, 22:52] Billy S Fari: πŸšΆβ€β™€οΈπŸšΆπŸ»β€β™‚οΈ *SANNU SANNU*πŸšΆπŸ»β€β™‚οΈπŸšΆβ€β™€οΈ
πŸ’Ž _Bata hana zuwa..._πŸ’Ž


_WRITTING BY:_ *BILLY S FARIπŸ’Ž*

_DEDICATED TO:_ *BLOOD SISTER'S (AMZAHFAZ)*πŸ’‹

_BESTOWED TO:_ *ZAINAB AL-AMIN (MOM NA'EEM)* AND *AMINA UBA AYUBA (OUM ASHFAQ)*πŸ’ž

*DOMIN FARINCIKINKI SISTER SADIYA ZANGO (MIEMAH)*πŸ’–

*FATAN ALKHAIRI AGAREKU MOMMAH ME NANA HAFSAT (MISS XOXO) AND MAMANA HAFSAT RANO(OUM AFFAN)*❀️

Page___54πŸ’Ž

Kimanin awanni biyar da rabi suka shafe akan hanya kafin su isa garin kano, iya jigata Rashida tayita don ba kad'an ta tsargu da zaman na mota ba kasancewar bata tab'ayin koda makamancin irin sa bane, bini bini Fatima da Nuraddeen ke juyowa baya su kalleta har zuwa lokacin da suka iso.

Kai tsaye gidansu dake unguwar sharad'a phase2 suka nufa, da sauri mai gadi ya taso ya bud'e masu had'e da russunawa yana gaishesu dr.nura ya d'aga masa hannu yana fad'in "ahh...malan sule sannu da aiki, kana lafiya?."

"Lafiya klw ranka shidad'e barka da hanya an iso lafiya?"

"Lafiya klw malan sule" Dr .nura yafad'a daidai lokacin da yake karya starring motar had'e dayin parking, Fatima ce tafara fitowa tana fad'in.

"Ya ALLAH! Sweety wlh duk nagaji."

Daga can cikin motar taji yace, "To matar ke kenan, inata ga mmn baby ko ba haka ba?" Ya qare maganar had'e da juyawa yana kallon Rashida dake qoqarin sab'a Little Nuraddeen a kafad'a zata fita, dariya Fatima tayi ta zagaya tacan gefe tabud'e mata gambun motar had'e da karb'ar little tana fad'in.

"Sannu maman boy, ai ko da gani babu tambaya kinfini jigata, tafiya kam mai tsawo babu dad'i ko kad'an gaskiya in bata jirgi ba."

Ita dai Rashida Banda murmushi da takeyi tana shaqar yanayin iskan garin tare da bin tsarin gidan da kallo babu abunda takeyi har yafito cikin motar ya kulle tare da wucewa gaba sukabi bayansa,

Suna shiga duk suka zube tsakiyar falo a gajiya, Saida suka d'an huta sannan Dr nura yawuce part d'insa ita kuma Fatima tamiqe d'auke da little had'e da cewa Rashida tabiyo bayanta suka wuce part d'inta, har ga ALLAH Rashida ba hakan taso ba aranta, taso suna isowa sukaita wajen iyayenta duk da lokacin dare ya somayi don takwas na dare tawuce amma babu yanda ta iya dole tayi haquri idan talura da yanayin yanda kowanensu ya dawo agajiye,

"Maman boy kishiga toilet kifara watso ruwa kafin nan nima naje na watso nawa, sai in kawo maki little shima ayi masa." muryar Fatima ce taji tadaki kunnenta tana qoqarin ficewa daga d'akin, sai alokacin tayi yunqurin fita daga tunanin data shiga tare da d'aga mata kai sannan tafice sab'e da little dake faman baccinsa hankali kwance.

Rashida tajima zaune agefen gadon tana qarewa d'akin kallo kafin tamiqe tashiga toilet ta watso ruwan,

A b'angaren Dr.nura kuwa koda Fatima taje har yafito wankansa, "sweety shine baka jira nazo nataya kaba?"

Tafad'a cikin shagwab'e fuska. "Ina tuba matar kawo little maza kije kema kiyo naki musamu muranka sallolin dake kanmu mukai maman boy gida."

Shiru tayi na tsawon daqiqa d'aya dake nuna damuwarta akan maganar, har ga ALLAH tanajin rad'ad'i aranta idan ta tuna halin da Rashida zataje ta riska na rashin iyayenta, ba wani dogon shiri yayi ba face doguwar riga jalabiya daya zura ajikinsa sannan ya karb'i little a hannunta yana fad'in.

"Kidena bana son irin wannan dogon tunanin zai iya sakaki cikin damuwar da zata iya ankarar da ita halin da ake ciki."

"Shikenan Dr, Amma kana ganin bazamu bari sai gobe muje kaita ba? Ni sai nake ganin kamar dare yayi yanzu.

"Noo...hakan zaisa tayi kuka damu idan mukace mubari sai gobe, amma in mukaje yanzu mun kaucewa duk wani zargi daga gareta akan cewa rashin zuwanmu ne akan lokaci ya haifar da hakan kin gane?."

'Daga masa kai tayi sannan tashiga toilet, batafi mintuna biyar ba itama tafito tawuce falo tajawo akwatin kayanta dama tun d'azu Mai gadi ya shigo masu dasu ciki tawuce itama tashirya cikin doguwar rigar wani yadi marar nauyi, karb'arsa tayi takoma d'akin da Rashida ke ciki ta isko ita har tagama shiryawa tana ranka sallolin kanta tunda qasaru ne, tad'an jima zaune kafin taqarasa tamiqa matashi had'e da cewa.

"Ungoshi kiwatsa masa ruwa kifito falo muna jiranki."

Karb'arshi tayi tana fad'in "sannu aunty yaron nan nabaku wahala, shikenan shi baza'a ajiyesa shi kad'ai ba sai an tsaresa?"

"Ikon ALLAH! kin jiki da wata magana mmn boy, ai lalura ce takawo hakan, Amma badon haka ba mezaisa yana baccinsa ayita reto dashi hakan?"

Fatima taqarasa maganar tana murmushi sannan tamiqe tafice daga d'akin, a falo taci karo da Dr nura yadawo daga wajen ba maigadi saqo ya sawo masu abinci a wani restaurant dake kusa dasu a can bakin titi.

Hijab d'inta ta d'auko tadawo falon yana zaune ya miqe had'e da kabbarta sallah har suka gama ranka sallolin atare, suna zaune Rashida tafito d'auke da little ta gyarashi sai qamshi yake saye da hijab d'inta har qasa, duqawa tayi ta gaishesu suka amsa kowanensu fuskarsa d'auka da murmushi kafin Dr nura yamiqe had'e da karb'ar little d'in a hannunta ya zauna d'aya daga cikin kujerun dake falon, ita kuma ta zauna kusa da Fatima da har lokacin bata tashi daga inda sukayi sallar ba tana addu'a, sai da tagama suka shafa tare Rashida nafad'in. "Amin ya Allah masu albarka auntynah."

Zaro idanuwa wje Fatima tayi had'e da cewa.

"Nashiga uku ni batulu, yaushe kika fara shiga zuciyar mutane mmn boy kina gano sirrin addu'o'in da sukeyi."

Dariya Rashida tayi sannan tace. "Ba shiga zuciya bane auntyna, abunda ya tsaya mani araine har yakai yasa bana iya gama duk wata ibada tawa ba tare dana roqi ALLAH daya kawo mana qarshen saba, balle ke da nasan duk yanda nakai ga jin zafinsa kinfini shiyasa natabbatar idan ni ina yin addu'ar samun yayewar wannan abun toke zaki fini yin hakan sosai, ubangiji ALLAH yanda kuke bawa yaron nan kulawa kuma ALLAH yakula daku yabaku zuri'a masu albarka."

Tare duk suka had'a baki ita da Dr.nura suka amsa da Amin.

Maigadi ne yayi sallama Fatima taje ta karb'o saqon ta kawo falo ta ajiye sannan taje ta d'auko plates guda uku da cokulla da wani tray babba da yuqa ta ajiye bayan ta d'aurayosu, zuzzuba abincin tayi dake cikin robobin take away sannan taje ta wanko fruit d'in Rashida takarb'a ta gyara masu, miqewa tayi taje ta d'auko little a saman jikin Dr nura dae kwance saman kujera tana fad'in.

"Bisimillah yallab'ai."

Saida sukaci suka qoshi Dr ya d'auki makullin motarsa tare da d'aukar little dake saman kujera yana 'yan wasanninsa da hannuwa sannan ya fice yana fad'in.

"Ina jiranku a waje."

Kwashe kayan suka farayi suka wawwanke komai had'e da gyara wajen sannan suka bi bayansa, dama kayan Rashida nacikin mota ba'a fiddo komai ba inba 'yar jikkar baby bag d'in little dake sagale a hannunta ba, shiyasa shikad'ai ta gyara ta sauyawa kaya ita kuma tamaida wud'anda ta cire ajikinta.

Kasancewar akwai 'yar jayawa sosai tsakaninsu yasa koda suka isa anguwar tasu Rashida qarfe tara da rabi nadare har yayi, duk d'okin da Rashida keyi nason zuwa taga iyayen nata suna nufo anguwar taji gabanta yafara fad'uwa, a hankali tafara kirawo sunayen ALLAH tana mai neman tsarinsa daga dukkanin sharrin dake iya cutar da ita ko d'anta.

A daidai bakin qofar gidan ya tsaya da yake akwai wutar nepa da d'aid'aikun mutane dake kai da kawo cikin anguwar, ko gyara tsayuwar motar beyi ba ta b'alle marfinta ta ruga aguje tanufi qofar gidan tana kiran "umma, ummaa."

Turus ta tsaya ganin qofar rufe da kwad'o gabanta na tsananta fad'uwa, juyowa tayi jiki ba k'wari tace.

"Uncle ya naga gidan arufe?." Tana qarasowa inda suke a firgice.

Maqwabcinsu ne taga yazo wucewa zai shiga gidansa kafin dr yace wani abun tabi bayansa da sauri tana fad'in. "Baba, baba na kande!."

Da sauri ya juyo yana kallonta cike da mamaki yaja da baya, ya matuqar tsoratar ganinta awannan lokacin ba zato ba tsammani, matsawa ta sakeyi kusa dashi jikinta na rawa tace, "baba nakande nice fa Rashida, nice Rashidar umma fa, don ALLAH baba kada ka gujeni ka tsaya kafad'amun Ina su umma da baba sukaje, Ina son nagansu baba nakande, Ina matuqar kewarsu, kafad'amun ina ne suka tafi don ALLAH."

Wata irin ajiyar zuciya ya sauke cike da ta'ajibi yace. "Rashida!"

"Na'am baba nakande."

"Rashida ke ce?"

"Eh baba, Ina su ummata suka tafi?"

Jinjina kai baba nakande ya farayi kafin yafashe da kuka yana fad'in. "Wayyo ALLAH na Rashida sai dai kiyi haquri..."

Bata qarasa jin abunda zai fad'a ba tsabar fargaba da tsoron abunda take tunanin zai fad'a yasata fad'uwa wajen, da gudu su Dr. Suka qaraso wajen Fatima taduqa ta tallabota tana kiran sunanta, Dr nura dake riqe da little ya miqama baba nakande hannu dake kuka yace.

"Assalamu alaikum, baba meye kafad'a mata halama haka?."

"Yaro kaine?" Baba nakande yafad'a yana share hawaye don ya wayesa,

"Eh baba."

"Dama tana hannunka?"

"Eh baba,"

"To meyasa bak sanar da ita komai ba?, Gashi yanzu tun kafin infad'i abunda zan fad'a tasome."

Ganin halin da take ciki yasa Fatima takoma cikin mota ta d'auko gorar ruwan swan d'in dake ciki ta yayyafa mata had'e da shafa matasu ga fuska,

Ahankali Rashida tabud'e idanuwa tare da fashewa da kuka tana fad'in. "Nashiga uku aunty don ALLAH kada kucemun iyayena sun mutu sun barni.."

"Haba Rashida, waya fad'a maki cewa iyayenki sun mutu?, Iyayenki na raye amma bamusan inda suka dosa ba, sun bar garinnan kwata kwata saboda b'atanki.."

Kan baba nakande yarufe baki tuni sukaga Rashida tafara fizge fizge idanuwanta sun kakkafe."

Da sauri Dr yace Fatima takarb'i little da sai faman kuka yakeyi ya tallabi Rashida yasa cikin mota, "baba don ALLAH idan ka amince kazo muje asibiti dakai, nasan bazaka rasa sanin wasu daga cikin dangin taba."

Duk da baba nakande najin tsoron halin mutunen duniya tausayin Rashida yasa bai tsaya tunanin komai ba yashiga motar ya bisu, da gudu Dr nura ke taka motar har suka isa asibiti, cikin gaggawa aka karb'i Rashida kasancewar wajen aikinsa ne ba tare da antsaya wani b'ata lokaci ba, ba'a jima ba likitan daya shiga dubata yafito had'e da tambayar Dr nura cewa dama tanada hawan jini (hypertension)?.

Nan yabashi amsar cewa tana dashi lokacin data haihu amma yayi tsammanin cewa wannan is normal yariga ya wuce,

"Noo..gaskiya ba haka bane, yanzu hakan shine ya tsar mata, sai dai baiyi mata worst sosai ba za'a iya shawo kansa da yardar ALLAH, inaga ko yanzu saboda bata jima da haihuwa bane hakn tafaru, amma in sha ALLAH komai zai dai daita don Babu wata matsala bayan shi, yanzu haka anyi mata allur bacci ne saboda tasamu isashhen hutu"

"Alhamdulillah Dr. Ngd sosai."

"Ba damuwa dr.nura, ALLAH yabata lafiya."

"Amin Dr"

Nuraddeen yafad'a yana kallon baba nakande dake zaune yayi tagumi.....



















*ALLAH KAJIK'AN IYAYENMU*πŸ‘πŸ˜­
[11/14, 22:52] Billy S Fari: πŸšΆβ€β™€οΈπŸšΆπŸ»β€β™‚οΈ *SANNU SANNU*πŸšΆπŸ»β€β™‚οΈπŸšΆβ€β™€οΈ
πŸ’Ž _Bata hana zuwa..._πŸ’Ž


_WRITTING BY:_ *BILLY S FARIπŸ’Ž*

_DEDICATED TO:_ *BLOOD SISTER'S (AMZAHFAZ)*πŸ’‹

_BESTOWED TO:_ *ZAINAB AL-AMIN (MOM NA'EEM)* AND *AMINA UBA AYUBA (OUM ASHFAQ)*πŸ’ž

*DOMIN FARINCIKINKI SISTER SADIYA ZANGO (MIEMAH)*πŸ’–

*FATAN ALKHAIRI AGAREKU MOMMAH ME NANA HAFSAT (MISS XOXO) AND MAMANA HAFSAT RANO(OUM AFFAN)*❀️

_ASSALAMU ALAIKUM, GAISUWA DA FATAR ALKHAIRAN ALLAH AGAREKU MASIYANA, INA BAKU HAQURU AKAN RASHIN AMSA MAKU IDAN KUNYI COMMENTπŸ˜… KUYI HAQURI IN SHA ALLAH DAGA YAU ZAN GYARA, KUNA QORAFI AKAN HAKA ASHE ABUN SON KAINE WATO WANZAM BAKA SO GA KANKA,🀣 YO IDAN HAKAN NA BATA MAKU RAI ME KUKE TUNANI AGARENI NIDA NAZAUNA NAYIMAKU TYPING DON KU NISHA'DU SAI ACE ANWAYI GARI KO THANKS BAZAN SAMU AWAJENKU BA BALLE COMMENT, DUK DA DAI NI NASA KAINA AI KUNSAN BABU DADI DON NA TABBATA KUNA KARANTAWA, SHIYASA NIMA NA SHAREKU DON KUJI IDAN ABUN KWAI DA'DIπŸ˜‚ BUT TUNDA KUN QARA, TO ZAN GYARA KAMAR YANDA NAKEYI ADA, INA FATAR KUMA ZANGA CHANJI AWAJENKU TA HANYAR DA'DA'DAN COMMENT 'DINKUπŸ‘ NGD SSAI_

Page___55πŸ’Ž

Tuni baba balarabe da Yaya maryam dasu aunty marwiyya suka isa asibitin cikin daren sanadiyar wayar da baba nakande yayiwa baba balarabe ya sanar dashi zancen dawowar 'yar d'an uwan nasa shi kuma yakira Yaya maryam takira aunty marwiyya ta sanar da ita, kowanensu cike da farinciki yake a zuciyarsa naganin 'yar tasu duk da dai a yanayin da take ciki na nema ya gusar masu da farincikin,

Little kuwa yayi kuka har ya gaji saboda tsabar yunwar da yakeji, goyashi fatima tayi bacci ya d'aukesa shi kuma Dr nura ya koma gida don ya d'auko masu abunda zasu iya buqata kafin gobe don yasan bazasu wuce gobe ba shiyasa koda su baba balarabe suka iso asibitin Fatima kad'ai suka tarar sai baba nakande, ita tawuce dasu d'akin da Rashida take kwance tare da yimasu bayani ataqaice kafin Dr ya iso.

Jugum jugum ya tarar dasu kamar wud'anda k'wai ya fashewa cikin ciki ya wuce ciki ya ajiye kayan dayazo dasu yana kallon gefen da Rashida ke kwance hannunta laqe da drip sun kusa qarewa sannan yajuyo yanufi inda baba balarabe ke zaune shida mijin Yaya maryam,

"Assalamu alaikum." Yafad'a yana miqa masu hannu suka gaggaisa kafin baba nakande yayi masu bayanin cewa shine mutumen da yazo da Rashida, cike da girmamawa suka sake gaishesa kafin ya nemi waje yazauna yana fuskantarsu, matsowa su aunty marwiyya sukayi wajen suma suka gaisa sannan Dr nura yagabatar masu da kanshi ataqaice yaqare maganar yana nuna masu Fatima.

"Waccan kuma iyalina ce."

"Masha ALLAH." Baba balarabe yafad'a sannan yace.

"Ni sunana malan balarabe, qane ga mahaifin ita waccan yarinyar Rashida, ita Kuma wannan sunanta Maryam wato Yaya agaremu nida mahaifin Rashida, wannan qanwar mahaifiyar tace sunanta marwiyya sai kuma shi wannan mijine ga ita yayar tamu wato alhaji ubale."

"Dukkaninmu da kake gani abu d'aya muke babu banbanci, Kuma mukad'aine iyayen Rashida acikin wannan garin, munyi baqin ciki sosai alokacin da muka rasata wanda sanadiyar hakanne ya haifar mana da shiga matsanancin damuwa kala kala har yakai ga su iyayenta da suka haifeta sun kasa jurewa rashinta sunbar garin bayan doguwar jinyar da sukayi a asibiti."

A yanayin bayanin da baba balarabe keyi yasa Dr nura gamsuwa akan cewa su d'in shaiqanta ne na jini don haka yasaki jiki sosai dasu had'e da yimasu bayanin yanda suka tsinceta dalla dallah da irin wahalar da yaronta yasha wanda shine sanadiyar da yasa basu nemesu ba tun wuri, duk da dai yayi qoqarin ganin yasamu iyayenta alokacin Amma ALLAH bai yarda ba, gaba d'ayan su kuka da tausayin halin da Rashida tashiga ita da yaronta suka shigayi suna Mai godewa ALLAH daya miqata ga hannun mutane nagari masu d'imbin karamci da halacci, a daidai lokacin little dake goye a bayan Fatima ya tashi yafara mutsu mutsu yana neman yin kuka Nuraddeen yamiqa mata hannu ta sancikke masa shi, miqasa yayi hannun malan balarabe had'e da cewa.

"Wannan shine abunda ALLAH ya albarkaceta dashi wanda muka rad'a masa suna Nuraddeen bisa yardarta da kuma amincewarta."

Hannun baba balarabe na rawa ya karb'esa yana qare masa kallo don wajen d'auke yake da hasken wutar lantarki kamar rana, tabbas ko ba'a fad'a ba wannan yaron jinin sune don kamarsa sak da d'an uwansa wanda itama mahaifiyar tasa wato Rashida dashi take Kama, wasu zafafan hawayene suka zubo masa yana maijin inama d'an uwansa bai tafi ba yaga irin kyautar da ALLAH yayi masa ta hanyar dawo masa da 'yarsa da kuma jikansa a hannunsa.

Rungume yaron yayi yanaji tamkar d'an uwan nasa ne kafin yaji hannun Yaya maryam data kasa dangana tana qoqarin karb'arsa.

Murmushi tasaki alokaci d'aya hawaye nasake suko mata saman fuska itama lokacin data karb'i yaron tana fad'in.

"ALLAH mun gode maka daka dawo mana da Rashida lafiya daga hannun bayinka salihai masu kyakkyawar zuciya, ya ALLAH ka lullub'esu da tarin ni'imominka tare da yalwataccen farinciki marar yankewa acikin zukatansu da kuma fuskokinsu,"

Taqarsa maganar had'e da d'ago yaron tana sumbatarsa.

"ALLAH ka isarwa mahaifiyarka Nuraddeen ita da iyayenka, yayi maka sakayya kaida mahaifinka ga muguwar kakarka data nemi salwantar maku da rayuwa kida mahaifiyarka, ALLAH..."

Katseta mijin nata malan ubale yayi tahanyar cewa.

"Haba Maryam, menene haka? Keda yakamta kigodewa ALLAH sai ki koma kinayiwa bayinsa mummunar addu'ah? Shin ashe hakan ya kamatan ceki kiyi bayan

Please Login or Register in order to submit comment