Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kinsan ALLAH maiyin sakayyane ga bayinsa wud'anda aka zalunta?."

Shiru tayi had'e da miqawa aunty marwiyya little itama takarb'esa, shafa kansa ta shigayi cike da qaunarsa tana yaba kyawon da ALLAH yayi masa da yanayin jikinsa mai cike da ban sha'awa.

Ganin gaba d'ayansu sun shagala yasa Fatima komawa cikin d'akin da Rashida ke kwance, tana zuwa ta isko tafarka daga allurar baccin da akayi mata lokacin kusan qarfe d'aya saura mintota nadare, da sauri Fatima ta matsa kusa gareta tana jero mata sannu, qoqarin tashi zaune tayi ta dakatar da ita tana fad'in "a'a komawarki ki kwanta maman boy."

Tana dafa kafad'arta had'e da qoqarin maida ita kwance,

"Aunty da gaske su ummata sun tafiyarsu?, Da gaske ba'asan inda suka tafi ba?, Shikenan bazan sake ganinsu ba?" Rashida tafad'a had'e da riqe hannuwanta tana kuka, cikin dakewa Fatima da tuni zuciyarta tayi rauni hawaye sun soma kaida kawo a fuskarta tace.

"A'a maman boy, Zaki ga su ummanki komai daren dad'ewa, hakan bayana nufin kun rabu bane Rashida sai dai kawai ubangijinki na auna imaninkine ta hanyar yimaki jarabawa wata bayan wata Kuma dama haka rayuwar mumini take, idan anyi masa jarabawa ya canye ta sai asake yimasa wata jarabawar wacce tafi tafarkon da akayi masa don kawai a d'aukaka darajarsa da kuma imaninsa idan ya canyesu, kiyarda cewa zasu dawo agareki nan kusa bada jimawa ba in Sha ALLAH." Cikin kuka tace

"Yaushe? Awane lokaci kuma aunty? Bayan zukatansu sunriga sunyi imanin cewa sun rasani kenan har abada."

"Kisa aranki cewa kusa zasu dawo, haba maman boy karki manta ALLAH subhanahu wata'ala yana cewa."

_"Laa taqnad'u min rahmatllah (kada mu kuskura muyanke qauna ga rahamar ALLAH)_"

"Don haka kada kicire tsammanin cewa rahamar ALLAH zatasa iyayenki sudawo matuqar kika miqa dukanin al'amurranki agaresa kamar yanda kikayi abaya, haqiqa wawa, lusari, Wanda baisan kanshi kad'aine ke rabka hannuwa yana tsammanin cewa ALLAH bazai jarabcesa ba bayan kuma yace yayi Imani, walh Rashida ALLAH da kansa ke cewa matuqar kukace kunyi Imani to."

_"wala nabluwannakum bi shai'in minal haufi wal ju'i wa naqsin min amfusi wassamarat, wabasshirisubirin, allazina iza asabathum musibatun qalu innalillahi wa Inna ilaihirrajiuun, ma'ana idan kunyi Imani dani to (zamu jarabceku da abubuwan tsoro, da yunwa da rashin rayuka daga kawunanku da kuma tsirrai, muna yima masu haquri bushara wud'anda idan musiba tasamesu sai suce ga ALLAH mukazo Kuma agareshi zamu koma)"_

"Saboda haka ki daure ki zamo cikin bayinsa masu haquri da yake yiwa bushara kinji ko!"

Cikin kuka dake cike da sauti Rashida tafad'a jikinta tana fad'in.

"Innalillahi wa'inna ilaihirrajiuun, allahummah thabbit aqadami wa haqqiq Imani,.."

Qarar kukan nata yajanyo hankalin su baba balarabe dake waje da sauri suka shigo cikin d'akin har suna rige rigen qarasowa bakin gadonta, tana ganinsu taqara fashewa da wani kukan had'e da rungume aunty marwiyya tana fad'in.

"Wayyo ummana.."

Babu yanda suka iya domin rasa iyaye tako wace irin fuska ce yanada matuqar rad'ad'i arai wanda dole ko ana so ko ba'aso awannan gab'ar dole abarta tayi kukan domin ko anhanata yinsa rad'ad'in da takeji azuciyarta bazai barta tahanu ba, sai da tayi mai isarta tayi shiru sannan tajaye daga riqon da tayiwa aunty marwiyya takwanta akan gado tana ajiyar zuciya har lokacin hawayen basu dena fita daga idanuwanta ba, sannu suka dinga yimata d'aya bayan d'aya tana amsawa had'e da binsu da kallo hawayen naci gaba da zubo mata.

Rarrashinta suka taru sunayi had'e da ban magana da dad'ad'an kalamai Amma gaba d'aya ita ba abunda take gani sai hoton fuskokin iyayen nata da batasan ranar da zata koma had'uwa dasu ba.

Gaba d'aya takasa tsaida zubar hawayenta wanda hakan yasa Dr nura yaje yakira Dr daya dubata yazo ya sake yimata allurar bacci bayan aunty marwiyya ta aza mata little daya fara qananun kuka tabashi nono yasha,

Bacci mai nauyi sosai ya d'auketa sannan baba balarabe yace da aunty marwiyya taje gida tunda dare yayi sosai lokacin qarfe d'aya da rabi,

Atafau tabuga kai ga qasa akan babu inda zataje anan zata kwana, don gani take za'a iya sake d'auketa idan taje gida kafin tadawo gobe da safe. Adole aka qyaleta tunda ta nace akan haka, Kiran mijinta tayi tasanar dashi anan zata kwana Kuma cikin sa'a ya amince mata don mutumne da baida matsala kuma ko bayan hka su biyu suke ga mijin nata shiyasa Bata damu da sai takoma gida ba.

Yaya maryam ma daqyar baba balarabe ya samu tabi mijinta sannna yajuyo yana kallon Fatima dake riqe da little yace.

"Fatima dake da Dr. Yakamata ku koma gida saboda akwai gajiyar tafiyar da kukayo kuna buqatar hutawa sosai, inyaso nida qanwar mahaifiyar ta zamu kwana anan idan Babu damuwa koda za'a buqaci sawo wani abu kunga ni Ina nan babu matsala."

Ji Fatima tayi kamar ta k'walla ihu don har ga ALLAH bataso barin asibitin ba amma saboda dr.nura ya amsa yasa dole babu yanda zatayi ta haqura ta miqawa aunty marwiyya little kamar zatayi kuka ta karb'esa sannan sukayi saida safe suka tafi sai tunzurar baki takeyi, kallonta yayi yana tuqi yayi murmushi had'e da cewa.

"Fatima meye abun b'acin rai naga kina turar baki haka?" Saida ta kallesa sannan ta maida kanta gefe tace.

"Meyasa kaima bakace anan zamu kwana ba, ALLAH bana son rabuwa da maman boy ita da little hisby d'innan nawa, shine kai harda wani miqewa da sauri irin bakama damu ba." 'yar dariya yayi daidai lokacin suka iso inda 'yan sandan dake security akan titi suke yayi slow da motar had'e da ciro i.d card d'insa ya nuna masu suna yayyada bayan motar da wajen boot sannan suka basa izinin wucewa.

Bayan sun wuce wajen ya juyo ya kalleta tare da aza hannunsa saman nata yace.

"Kiyi haquri kinji matar?, Ba haka nake nufi ba amma yakamata kisn cewa yanzu bamuda wani sauran iko akanta, mu kawai masu taimako ne, munemi cikar ladar taimakon da mukayi, kada mu nemi shiga hurumin da iyayenta kad'ai suke da haqqi akansa, kada mutauye ladarmu tahanyar nuna ra'ayin zukatanmu bayan munsan ayanzu sunfimu tsananin buqatar kasantuwa da ita, koba haka bama ai dole murabu dasu ko bama so, don haka daga yanzu kifara koyawa zuciyarki yanda zata jurewa rashinsu akusa damu kinji ko?"

Batare data amsa masa ba ta d'ora kanta kawai saman kafad'arsa tana shafa hannunsa har suka iso gida.

Shima baba balarabe kiran iyalansa yayi yace surufe gida shi sai gobe zai dawo.

••• ••• •••
Su baffa nadawowa daga filin jirgi suka harhad'a kud'ad'en da zasuje kai yaya hawwa asibiti tare da wata 'yar qaramar jikka da kowanensu yasa kayansa kala d'aya da zasuyi amfani dasu don sai gobe zasu dawo kasancewar akwai nisa sosai tsakanin kano da kuma sokoto garin shehu, wanda koda sun isa dawuri bazasu kammala abunda ya kaisu ba har sai dare yayi, don haka dole suyi haqurin juyowa gobe idan ALLAH yakaimu bayan sun kammala abunda sukeyi.

Bankwana sukayi da Inna Bilkisu bayan baffa Usman ya jadda mata da kada abar Yaya hawwa da yunwa kafin sudawo, suyi qoqari kota tagane su dinga ajiye mata abinci har ALLAH yadawo dasu lafiya sannan suka tafi, akan hanya sukaci karo da Inna ruqayya ita da baffa Ali tafe suna magana qasa qasa, kallo d'aya baffa Ali yayi masu ya d'auke kai Inna ruqayya kuwa harara ta zabaga masu had'e dayin tsuki tawuce tana fad'in.

"Qarya dai fure take ba 'ya'ya, Kuma raminta qurarrene, sunyi abu yasha masu kai, gashinan garin neman gira anrasa ido, ba'a samu yabo ba ansamu wahala."

Kanta baffa Usman yanufo ransa ab'ace baffa yariqe hannunsa had'e da cewa.

"Haba Usman kada kataya mahaukaci hauka, ai kabarta tafad'i abunda ke ranta domin da kanta take, tafi muje ko nine a matsayinta zanfad'i abunda yafi hakan musamman idan akwai b'acewa atattare dani." Yaja hannunsa suka tafi.

Yanajin sadda suka kwashe da dariya baffa Ali nafad'in.

"ALLAH dai yaraka taki gona."

Inna Bilkisu kuwa da kanta taje tabud'e d'akin Yaya hawwa ta ajiye mata abinci had'e dayin tsaye abakin qofar d'akin tana kallonta, ganin tayi ana buga Yaya hawwa ajikin bangon d'akin kafin a d'agata sama ayar qasa batasha mamaki ba sai da taga anjuyar da kanta gefe yana kallon sama sannan an mammal qwashe mata hannuwa sun koma baya, qafafuwanta kuma anbud'esu kowace anjata gefe, ahaka taga tana jan ciki tazo inda abincin yake tasa kanta ta turesa ya zube qasa sannan tafaraci da baki kamar yanda dabbobobi keyi, kuka ne ya qwacewa Inna Bilkisu ganin yanda aka maida ita kamar wata muguwar dabba da sauri taja qofar d'akin tarufe tabar wajen tana kuka, kobata tambaya ba tasan wannan aikin shed'anun aljanune don haka taje ta d'auko redionta tasa karatun qur'ani tanufi d'akin, da sauri Yusuf yariqota had'e da cewa.

"Inna Bilkisu kada kiyi haka, bakisan wud'anne kala bane kada garin taimako kema su nemi cutar dake, kibari tunda su baffa sunje nemamata mafita anema mata."

Wata qara sukajiyo daga d'akin da tasa yusuf jawo hannun Inna Bilkisu yana fad'in "kinji ko inna Bilkisu, ALLAH kimaida kada kitafi, ALLAH zai baki ladar niyar da kikayi."

Inna ruqayya da baffa Ali nashigowa kuwa tsuki sukaja had'e da cewa.

"Bisimillah, 'yar mahaukatannan tafara, wlh mukam dai anzaluncemu da aka ajiye manaita anan tana neman kashe mana kunne da baqar qara sai kace dujjal."

Dariya baffa ya kwashe da ita had'e da zuwa ta tagar d'akin yana leqen Yaya hawwa yace.

"Ikon ALLAH, ke ruqayya zo kiga yanda matarnan mai shegen cin zarafi da iya walaqanci ta koma, wlh kyace wata qwaguwa ce," leqawa tayi tafashe da dariya tace.

"Ala gwai, wlh naji dad'i, dubi qafafuwan shegiya uwa na lala tacciyar mace, ke muneera.."

Ta kwalawa muneera kira dake d'aki kwance tana bacci. Cikin magagin bacci tafito tana susar kai tace,

"Matso nan kiga Yaya hawwa dake maki sherin gwalmammin qafafuwa kiga yanda ALLAH yamayar mata da nata."

Leqawa muneera tayi had'e da murza idanuwanta don ta tabbatar da abunda suka gane mata da sauri ta jid'o had'e da cewa.

"Tab.. ALLAH Inna hawwa takoma uwa banqararriyar kaza."

Suka kece da dariya, shidai Yusuf da Inna Bilkisu nagefe suna mamakin yanda baffa Ali da Inna ruqayya kefitar da munanna kalamansu ga Yaya hawwa cike da isgilanci, sai kace ada ba itace wacce suka d'auka shugaba kuma aminiyar duk wasu shawarwarinsu da al'amurransu na duniya ba.....

_"'yar uwa shin ko kinsan da wud'anne kalar mutane kike rayuwa dasu acikin duniya?, shin kina iya banbancewa wud'anda ke sonki da kuma maqiyanki acikin mutanen dake zagaye dake?,sanin hakan nabuqatar natsuwa da kuma nazari, tabbas ni nakoyi darasin sanin cewa mutum mugune kuma bayada tabbas awajensu baffa Ali haka kuma na d'auki darasin zaunawa nagano banbancin masoyin gaskiya da kuma naqarya awajen Inna Bilkisu, nayarda cewa mutum bayada alqibla wajen rashin gano ainahin kalarsa. Don haka kema yiqoqari ki tsinci naki darasin acikin wannan littafin mai suna SANNU SANNU Bata hana zuwa.._🥰






*ALLAH KAJIK'AN IYAYENMU*👏😭
[11/14, 22:52] Billy S Fari: 🚶‍♀️🚶🏻‍♂️ *SANNU SANNU*🚶🏻‍♂️🚶‍♀️
💎 _Bata hana zuwa..._💎


_WRITTING BY:_ *BILLY S FARI💎*

_DEDICATED TO:_ *BLOOD SISTER'S (AMZAHFAZ)*💋

_BESTOWED TO:_ *ZAINAB AL-AMIN (MOM NA'EEM)* AND *AMINA UBA AYUBA (OUM ASHFAQ)*💞

*DOMIN FARINCIKINKI SISTER SADIYA ZANGO (MIEMAH)*💖

*FATAN ALKHAIRI AGAREKU MOMMAH ME NANA HAFSAT (MISS XOXO) AND MAMANA HAFSAT RANO(OUM AFFAN)*❤️

Page___56💎

Saida suka gama shaqiyancin su day izgilanci tukuna suka baro wajen,

A hankali Inna Bilkisu ta tako zuwa bakin rumfar d'akinsu suna qoqarin shiga d'aki jikinta a sanyaye tace.

"Ruqayya, Ali kuji tsoron ALLAH, duniyar nan da kuke gani batada tabbas, shin ashe halin da Yaya hawwa take ciki bai isa yazame muna aya da kuma darasi ba?, Karku manta tare da muke zaune da ita acikin gidannan, itama mutumce kamarmu amma ALLAH yajarabci rayuwarta tahanyar komawa a cikin wannan yanayin da take ciki wanda muma bamufi qarfin ALLAH ya jarabcemu fiyema da yanda muke ganinta, I zuwa yanzu ya kamata ace mudukanmu munyi karatun ta natsu, mu zamo tsintsiya mad'aurinmu d'aya duk abunda yasamu d'ayanmu mu d'auka mu yasama kuma mu wa'aztu domin wannan halin da take ciki wlh iznane agaremu."

"To jikanyar limamai, Ina ruwanki meya shafeki da al'amarinmu?, Dama akace maki ke muke tsoro da zakizo kice muji tsoron ALLAH?, Ke nifa bilki bana son sa ido kiyi sha'aninki kibarmu muma muyi namu, yo Ina ruwanmu da halin da take ciki ai haukane ba'agareta farau ba kuma ta cancancesa, wlh Banda ALLAH ya isa tsakaninmu da ita bisa abunda taja akayi mana Babu abunda zamuyi mata, aikin banza in wa'azi kike son yi to jeki kiyi mata ita dake d'auke da haqqoqan mutane akanta take damunmu da kuwace kuwace tana hanamu bacci." Inna ruqayya tafad'a tana harararta, tsaki baffa Ali yaja had'e da juyowa yana kallonta cike da takaici yace.

"Ke Bilki, mufa yanzu babu ruwanmu da al-amarin kowa agidan nan don haka kifita harkarmu, baruwanki da duk abunda zamuyi koda kuwa kafirci ne, kabarinki daban namu daban kinajina ko!" Jinjina kai Inna Bilkisu tashigayi kafin tace

"Wal'iya zubillah, Ali meyakawo wannan zancen, ai _inni laku minnannaasihin (ni kawai agareku mai nasiha ce)_ ubangiji ALLAH kashiryemu kuma yabaku haquri."

Tana gama fad'an haka tajuyawarta tabar wajen tana maijin takaicin halin da suke ciki.

Muneera kam tutse baki tayi tana susar kai tace. "Inna wai meyasa kuke yima Inna Bilkisu haka?, ALLAH tanada kirki kawai don baku gane bane, amma lokacin da kuke rufe wajen 'yan sanda ALLAH duk ita take kula damu tana bamu abinci." A hasale Inna ruqayya tayo kanta tana fad'in

"Ke dallah rufemun baki, akace maki donku takeyi, duk wata maqarqashiyar rufemun da akayi ai da had'in bakinta ita da baffanninku, ai kinga kuwa dole su baku abinci ko don gudun duniya tazagesu."

"Kai Inna, ALLAH ba haka bane, ai mukad'ai ke zaune dasu ina duniyar take balle ta zagesu, kawai kice keda baffana bakwa son gaskiya kuma wlh sai anyi maku irin na inna hawwa idan baku dena ba, ni Babu ruwana, abunda ma nece mata (banqararriyar kaza) wlh da gaske ni haka naga takoma."

Kanta baffa Ali yayi da wani icce dake gefensa tafice da gudu daga gidan tana susar kai...

••• ••• •••
Baba da umma kuwa suna zamansu hankali kwance Babu wanda ke takurasu, gwargwado suna cin mai kyau kuma suna shan maikyau, hakama alhaji naqoqarin ganin ya kyautata masu saboda su samu kwanciyar hankali da natsuwa kuma Alhamdulillah ba laifi sun d'an fara ragewa kansu damuwa, wasu lokutanne kawai take bijiro masu idan suka tuna da 'yarsu sai 'yar matsalar hajia nafeesa dake musgunawa umma tahanyar yawan baqaqen maganganu da tsawar da take yimata duk kuwa da taka tsantsan da takeyi da ita, ga Rashin kunyar da yaranta keyi wanda shike sakesa hajia nafeesa fitina idan aka qiyi masu yanda suke so.

Yauma umma na kitchen tsaye tana jiran albasar data yanka acikin ruwan mai tasoyu sannan tazuba kayan miyan da zata dafa jallof dasu sai ga yaronta d'an shekara goma mai suna Shakur ya shigo, dube dube ya farayi cikin kitchen d'in kafin yace.

"Ke umma zuba mun abinci."

"Yi haquri Shakur abincin bai ida nuna ba."

"Nidai kizuba mun haka zanci."

"A'a bari dai nahad'a maka qanzon nan naturawa (cornflaks) kafin ka qarasa sha nagama kaji ko."

Bubbuga qafa yafarayi zai b'are mata baki da kuka tayi saurin jawo plate ta zuba masa shinkafar data yiwa per boiling gudun kada kukan nasa ya jaxa mata walaqanci awajen mahaifiyarsa,

"Ungo gashi" tafad'a tana miqo masa plate d'in farar shinkafar data zuba man da take soyawa da magi mai star akai yanda zaiji dad'inta ya karb'a yawuce abinsa.

A daidai saman inda dining table ke ajiye yaje ya zauna qafafuwansa na reto a qasa ya fara cin abincinsa hankali kwance ko d'an sauran qarfin shinkafar daya rage tanuna baya ji tunda yunwa yakeji.

Jim kad'an hajia nafeesa tafito cikin wani material mai shegen kyau yasha d'unkin riga bubu waya laqame akunnenta tana takawa d'ai d'ai, da alama wayace takeyi da wata, idanuwa ta qwalalo awaje hango d'an tsakiyar ranta wato Shakur yana cin shinkafar da kallo d'aya zakayi mata kasan Bata dahuba saboda yanda take tsaitsaye, wajensa taqaraso ta d'auke plate d'in dake gabansa tana fad'in.

"Ina zuwa hajia hafsat, zankira daga baya."

"Kai shakur a ina kasamu wannan?."

"Momy a kitchen ne nasamu."

"Waya baka?"

"Umma mai aiki..." Tun kafin yarufe baki tashiga qwallawa umma kira da qarfi, umma najin haka tasan a fusace take.

Tsoron qasqanci da walaqancinta yasa umma fitowa da sauri alokacin da tasake kiranta tana fad'in.

"Na'am hajia, gani."

Jeho mata plate d'in da sauran shinkafar tayi ya bugi goshinta sannan yafad'i qasa duk shinkafar ta wawwatse mata ajiki.

"Har ke waye da zaki bawa yarona abinci gaya babu miya kuma d'anye wanda be nuna ba, ke wace nake tambayarki?" Hajiyar tafad'a a tsawace.

Qasa umma tayi da kanta saboda batajin duk qasqancinta zata iya sa'insa da matar dako sa'ar qanwarta mawiyya batayi ba.

Masifa tashigayi inda taka shiga ba nan take fita ba har tan fad'in umma tadena ganin tagirmeta zata iya zabga mata mari akan yaronta wai so takeyi takashe mata shi shiyasa tabashi d'anyen abinci salon cikinsa ya kumbure masa, cikin fushi tace. "To wlh maza ki tattarata ki kwashe kuma sai kin zauna anan gabana kincinyeta tas kamar yanda kikasa yarona yacita."

Haka tayita masifa da ita har alhaji dake tsaye a harabar gate shida wani abokinsa suna magana yajiyo harshen nata, hakan yasa yayi cikin gidan ransa a d'an b'ace da zimmar yimata magana ya tadda umma durqushe a gabanta tana kakkab'e shinkafar dake jikinta had'e da qoqarin tattara wadda ta zube qasa ita kuma tana tsaye kanta tana faman jijjiga jiki, motsin da taji ya sata juyowa tana kallonsa had'e da cewa.

"Yawwa qwanda daka shigo ka ganewa kanka abunda tayi, irin wannan iskancin da sukeyi kesa kake ganin kamar ina wulaqanta 'yan aiki, farar shinkafa na isko fa taba Shakur ko nina batayi ba salon taja masa wahalar da zata kashesa, musamman idan ta kumbura masa ciki."

"Sai ke kuma kika yimata me?" yatambaya ransa a b'ace."

"Shine da raina yab'aci nawatsa matashi kuma nace ta tattarar dashi ita tacinye."

"Ok. Ni ina wahalar samo abinci ke kina zubarwa qasa, shikenan umma ajiye ki tashi wajen." Yafad'a tare da matsowa wajen ita kuma umma takoma gefe ta makure,

"Duqa ki tsincemun abina tas ki miqomun keda kika watsar dashi." Yace ma hajia nafeesa tare da nufar inda shakur yake zaune.

Sanin halinsa yasa hajia nafeesa duqawa tsince abincin tana hararar umma tana kumbure fuska sai kace wacce aka hurawa mabusa.

Riqo hannun shakur yayi had'e da cewa.

"Shakur d'in baba ya akayi kake cin waccan shinkafar haka?"

"Abba yunwa nakeji kuma umma bata gama abinci ba da nace tazubomun haka sai tace inbari ta had'amun cornflakes shine nace bana so da taga zanyi kuka sai ta zubomun a haka saboda nace zanci."

"Bakasan cin shinkafa have done zata iya kumbura maka ciki ba."

"Abba bazata yimani komai ba yunwa nakeji."

Daidai lokacin hajia nafeesa tagama tsincikke shinkafar tazo tamiqo masa tana faman cika da batsewa,

Murmushi yayi sannan ya karb'a ya ajiyewa Shakur agabansa yace

"Ungo kayi bisimillah ka qarasa canye abinka kaji ko, Amma kada kasake yin haka Babu kyau."

"Alhaji fa yayi qasa." Hajia nafeesa tafada kamar zatayi kuka.

"Eh yaci babu abunda zai yimasa in sha ALLAH, Ina kinsan da haka amma kikace ita tacinye sa ko."

Juyawa yayi yana kallon umma yace.

"Umma kiyi haquri, kuma daga yau bazaki sake yin aiki agidannan ba."

"A'a alhaji kada ayi haka, indai akan wannan ne babu komai zanci gaba dayi, bana son na zaunane waje d'aya, nafi son ind'an dinga mommotsa jikin."

"A'a baza'ayi haka ba, aishi d'an adam daraja ne dashi yakamata ace angirmamashi musamman wanda ya girmeka, walaqanci bayada dad'i ko kad'an don haka kije zanyi magana da hajia fareeda sai ki koma acan b'angarenta inaga zaifi tunda kinfiso kina motsa jikin naki."

"To shikenan alhaji ngd, bari na qarasa wannan girkin."

"A'a umma kibarshi ita zata qarasa da kanta."

Da qarfi hajia nafeesa ta d'ago kai tana kallonsa yayin da umma tafice daga part d'in tana godiya ga ALLAH daya kawo alhaji ya kub'utar da ita daga cin mutuncin da tayi niyar yimata kuma ya yaye mata damuwar zama da ita da kalolin walaqanci da cin kashin da takeyi mata.

Jinjina mata kai yayi idanuwansa acikin nata alamun da gaske yakeyi sannan yace. "Kuma ba wannan girkin kad'ai zaki ida da kanki ba, daga yau nayi maki alqawarin babu wata macce da zata koma zama part d'inki da sunan yi maki aiki har sai lokacin da kika canza kuma kika san darajar mutane, don haka ya rage wajenki kidafawa kanki da yaranki abinci ko karki dafa duka ruwanki, wannan shine hukuncin dana yanke akai, idan kuma kikak'i ji to wlh kinji na rantse bakyaqi gani ba.

Yana gama fad'ar haka ya juyawarsa ya fice, dama tuntuni yake son d'aukar mata mataki akan cin zarafin da take yiwa bayin ALLAHn dake qarqashinta ALLAH bai bashi iko ba sai yau.







*ALLAH KAJIK'AN IYAYENMU*👏😭
[11/14, 22:52] Billy S Fari: 🚶‍♀️🚶🏻‍♂️ *SANNU SANNU*🚶🏻‍♂️🚶‍♀️
💎 _Bata hana zuwa..._💎


_WRITTING BY:_ *BILLY S FARI💎*

_DEDICATED TO:_ *BLOOD SISTER'S (AMZAHFAZ)*💋

_BESTOWED TO:_ *ZAINAB AL-AMIN (MOM NA'EEM)* AND *AMINA UBA AYUBA (OUM ASHFAQ)*💞

*DOMIN FARINCIKINKI SISTER SADIYA ZANGO (MIEMAH)*💖

*FATAN ALKHAIRI AGAREKU MOMMAH ME NANA HAFSAT (MISS XOXO) AND MAMANA HAFSAT RANO(OUM AFFAN)*❤️

Page___57💎

••• ••• •••
Sosai wan saheke Rashida tasamu sauqi zuwa azahar aka basu sallama, kai tsaye gidan Yaya maryam aka nufa da ita duk da baba balarabe yaso ace gidansa zata zauna, Amma ganin yanda Yaya Maryam d'in ta kafe kai da fata lalle wajenta zata zauna yasa ya
haqura tunda itace yayarsa babu yanda zaiyi,

Tunda Rashida ta bar gida yaune karo nafarko da taji tana son had'uwa da mijinta wato habibinta mahaifin d'anta Nuraddeen, suna kan hanyarsu ta zuwa gidan Yaya maryam da yake Dr nura ne ya d'aukosu a mota, Fatima na gefensa riqe da little sai Yaya Maryam da aunty marwiyya da ita Rashida abaya, shi kuma baffa mijin Yaya maryam ne ya d'aukosa saman mashin d'insa suka biyo bayansu, takalli aunty marwiyya tace.

"Aunty ya nura fa?"

Wata uwar harara ta zabga mata had'e da juyar da kanta gefe, ganin haka yasa ta kama bakinta har suka isa gida,

Dr nura nayin parking su baba balarabe dake biye dasu na tsayawa da mashin d'insu, Yaya Maryam ce tafara fitowa sannan aunty marwiyya suka nufi cikin gidan, hakama Fatima itama tafito tare da riqo hannun Rashida dake qoqarin fitowa tayi mata jagora sukabi bayansu,

A can cikin gida aunty marwiyya tafara fad'a tana fad'in. "Yaya wannan yarinyar batada hankali, kinji tambayar da takwyimun a mota wai ina ya nura? Wlh badon batada lafiya ba da saina d'auketa mari don ko sunan garinsu bana sonji balle sunansa."

"Hmmm banni da ita marwiyya Ina jinta, bi izinillahi ko shikad'ai ya rage namiji aduniya bazata koma gidansa ba, ai tunda haka tafaru to ta tabbata komai mahaifiyarsa zata iya yimata saboda qiyayyar da take yimata kuma mu shedane akan haka, shikenan kuma don muna sakarkari sa mubarta takoma masa a kashe mana ita, narantse kozai mutu sai yasaketa tunda ba ita kad'ai bace macce aduniya ba."

"Wannan shine daidai Yaya Maryam, in yaso yaje can uwarsa ta aura masa wacce take so." Aunty marwiyya tafad'a a qufule.

Tana rufe baki suna shigowa, ta sakarwa Fatima murmushi had'e da cewa.

"Wucikke matar Dr." Batare data kalli inda Rashida take ba.

A falo suka shiga suka zazzauna kafin mijin Yaya maryam yashigo shima su Dr da baba balarabe nabiye dashi abaya.

Bayan sun zauna Yaya Maryam tamiqe taje takawo masu ruwa da lemuna masu sanyi da 'yar sauran samosar data had'a da safe da take sayarwa ta ajiye masu,

"Balarabe kutab'a wannan kafin kuwuce."

Saida suka fara tab'a hira ana tayiwa little da Fatima ta ajiye tsakar falo yana faman yimasu qyaqya dariya sannan tamiqe taje ta d'ora masu dahuwar taliya da kifin gwangwani ga 'yar qaramar tukunyar gas cooker d'inta saboda tayi saurin nina, ai kuwa cikin mintotan da basu wuce goma ba ta nina ta zuzzubo a flate ta kawowa kowa, sake d'auko had'ad'd'en zob'onta na siyarwa da takeyi tayi ta kawo masu sannan itama ta zauna tana cin nata,

"Kai amma zob'on nan yayi dad'i yaya maryam ya akeyinsa?" Fatima tafad'a tana sake kai cup d'in zob'on abaki.

"Kai matar Dr Banda zolaya, zob'on na siyarwa?"

"Eh mana, gaskiya kina gyarasa sosai, ai wannan zob'on ko shugaban 'yan hasada yasha dole ya yabashi balle masu so

Please Login or Register in order to submit comment