Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

takwanta har tayi bacci.

Baya ga wannan batada wata damuwa aduniya saboda tana samun kulawa sosai awajen mijinta da kuma ahalinsa, wata irin soyayya Rashida keyimata tamkar ta mayar da ita cikin ciki, duk abunda zai b'ata mata rai Rashida taja kunnen little daya nisancesa ko don halaccin data yimasa arayuwa, tana matuqar jin batool aranta da har wani lokaci take tunanin idan har ahaka akejin sarakanai ma'ana 'ya'yan d'anka arai meyasa ita tata uwar mijin bata so taba? Meyasa tanuna mata tsanar da ko kishiyarka bai kamata ka nuna mata ba don taga ummanta bata tab'a nuna cewa tatsani hajia nafeesa ba duk da irin cin kashin kare da aibatawar da take yimata ita da jininta.

Batool tazama 'yar gata, ba awajen mijinta kad'ai ba hatta su Dr da dady suna kulawa da ita sosai ba'a batun umma data d'auketa tamkar little jikanta, duk abunda ta yayo duniya ita dai akaiwa batool, ammie ma na iya qoqarinta don duk abunda zata yiwa matar faruq to saita had'a da batool da kuma imaan matar Shakur d'and'an hajiya nafeesa.

Ganin haka yasa umma tayi kwad'ayin yin haka koba komai ai dady ya kyautata masu baici ace ta wofantar da nashi ba tana nuna banbanci don itama takan sayi abubuwa wani lokacin tace akaiwa su Fatima da matar faruk wace yarinyarsu ma ta farin mai sunan ammie ana kiranta Islam tana hannun umma tun lokacin da za'a yayeta takarb'eta shikenan sai suka barta nan basu amsheta ba, gaba d'aya kulawarta tadawo tsakankanin ita da kuma ammien, hakan yasa ranar umma tasa ayo mata odar turarukkan wuta da khumra's masu qamshi acan kano wajen wata hamshaqiyar dilan kayan qamshi masu qamshin gaske dake saidasu bisa sassauqan farashi mai suna nana hafsat (miss xoxo) wacce anfi sanin sana'ar tata da sunan da takeyi mata laqani da *YERWA INCENSE* kayanta kam akwai kyau sosai don idan kagane amfani dasu to tabbas qamshi ya aureka duk inda kaje kaida 'ya'yanka, miji kuwa ba zancen zaman fira awaje saboda mararin yadawo gida ya shaqi wannan dadda'an qamshi dake kwantar da hankali da kuma natsuwar zuciya, ( _hajia wannan ba qanzon kurege bane, sai kin gwada zaki iya tabbatarwa, don haka idan kina son hana mijinki fira awaje saboda daddad'an qamshin da kikeyi keda 'ya'yanki da gidanki to kinemi YERWA INCENSE akan lambarsu ta talfo kamar hakaπŸ‘‰ +234 809 521 5215 na tabbata zaki Sha mamaki kuma ki gode mani_ ) son da umma keyiwa kayan qamshinta yasa tasa aka kawo mata bokitayyen turarukkan da kwalaben khumra's d'in don ta rabawa sarakanan nasu, bayan ta kakkasa masu taba shahida ta d'auka taje ta kaimasu sai ta tuna da bata bada na imaan ba wato matar Shakur, da sauri tabi bayan shahida dahar takai bakin gate tana qwala mata kira riqe da bokitin turaren wutar d'aya da kuma kwalaben khumra's guda biyu a leda, muryarta da hajia nafeesa tajiyo yasata fitowa ta zauna akan d'aya daga cikin kujerun dake gefe wajen motocin Abba da alama baqi yayi suka tafi ta zauna tana lallatsar wayarta saboda tsabar gulma.

Batare da umma ta damu da ita ba tunda tariga tayi niya tamiqawa Shahida ledar tana fad'in.

"Ungo wannan mantawa nayi idan kin shiga kin bawa maman islam nata saiki biya ki kaiwa imaan wannan, kice muna gaishesu sosai..."

Ai bata rufe baki ba taji anbuge ledar da qarfi tafad'i qasa, da sauri ta d'ago kai sukayi ido biyu da hajia nafeesa sai wani faman huci takeyi sai kace wacce akayiwa laifi, bata tankata ba ta duqa zata d'auki ledar wacce ga alama kwalaben dake ciki sun mutu tasa qafa ta sake murza ledar bokin turaren ya fashe sannan tashurasu gefe tana fad'in.

"Ho iyayen munafucci da asiri, wane mugun abunne za'a d'auka akaiwa matar d'ana don arabani da ita, meye alaqarki da ita ko ina ruwanki da ita da zaki d'auki abu kice akai mata ban da baqin sheri dake zuciyarki da kuma iyayi.!"

Duk wannan abu dake faruwa ashe agaban idanuwan Abba ne lokacin yafito daga part d'in ammie zai shiga na ita hajia nafeesar ya d'auko wasu takardu ya hango abunda hajia nafeesar tayi, ran umma ya 'baci sosai amma saita qyaleta saboda bata buqatar tanka mata har tazamo silar jawo wata fitina agidan tadalilinta, inda ta shura kayan umma taje tasa hannu zata d'auke sauran don wasu duk sun d'an watse musamman turaren wuta sai taga anrigata, d'ago kan da zatayi sai sukayi ido biyu da dady, lumshe idanuwansa yayi sannan yabud'e yana murmushi had'e da cewa.

"Amaryata wannan wane irin turaren wutane mai qamshi da kuma sanyaya zuciya haka?" Saida ya d'an lakuto damshin ruwan khumrar dake jikin ledar ya sake sunsunawa had'e da rufe idanuwa sannan yaci gaba da cewa "kai! Masha ALLAH, wannan qamshin khumra haka sai kace an tattara qamshin turaren duniya aciki, fad'amun a Ina aka sayeshi kuma nawa nima in siya don na burgeku." Yafad'ai hakan da gangan yana kallon gefen da hajia nafeesa ke tsaye kamar an dasa ta da gefen ijiya.

Yanda yayi maganar yasa umma sakin murmushin da seda haqoranta suka bayyana suka miqe tsaye tare yana riqe da ledar sai qara shin shina yakeyi, Shahida kuwa sai faman toshe dariyar dake son fito mata takeyi aranta tana fad'in wannan tsohon akwai gwamawa mutun takaici, can tajiyo muryarsa yana kiran sunanta da sauri ta qarasa had'e da cewa.

"Na gaisheka tsoho mai ran qarfe, kayi naka kayi ta raggo ka dad'e kayi shekaru adadin yawan gashin rago,"

Dariya yayi had'e dasa hannu aljihu ya qirgo dubo goma ya miqawa umma yana fad'in,

"Ungo wannan asake kawo wasu sai akai mata, ke kuma Shahida ungo wannan ledar kikaiwa imaan d'in kice tayi haquri sun fashe tayi amfani dasu za'a sake kawo mata wasu." Yaqare maganar had'e da miqawa Shahida ledar ta amsa tawuce tana kallon hajia nafeesa da tayi fam tana dariya.

"A'a alhaji kabarshi akwai wasu zan sake bayarwa akai mata, basai ka wahalda kanka da kashe kud'in kaba." taqare maganar tana qoqarin saka mashi kud'in a aljihu, riqe hannunta yayi had'e da cewa

"Maman Rashida kibarsu kije kiyi yanda nace kawai ai hakan shine adalci."

Kafin yarufe baki hajia nafeesa tayo kukan kura kan umma ya zura mata idanuwa yana kallo yaga mezata aikata shima ya aikata mata irinsa sai yaga taja burki ganin kallon da yake yimata tafara zuba ruwan masifa inda take shiga ba nan take fita ba harda fad'in.

"Indai zalunci abunyine yaje yaci gaba dayi, akan tsohuwar mace yabi duk ya susuce ko tsufansa baya gani don kunya Bata ishesa ba agaban jikoki, to wlh in su anbasu sun canye anayin yanda akeso dasu ita ba'a isa ba, munafuccine banxa da wofi ai wannan kinimbibine za'ayi mata."

Cin mutunci kam dashi har umma tayi masu sai wanda tamance saboda zafin kishin abunda yayi mata, gaba d'aya idanuwanta sun rufe ta manta cewa yayi mata jan kunne akan karta sake takoma d'auko masa wata fitina agida baya buqatar haka sai gashi abun yauma takansa ya qare, Saida tayi mai isarta tagama sannan yacema umma tawuce part d'inta ita kuma yace daga nan karta kuru taqara taku d'aya cikin gidansa ta tafi gidansu sai yanemeta.

Wata irin gud'a ta ski had'e da cewa.

"Tafi nono fari, don ko yanzu nafita gidanka bazan rasa mai so ba, don haka takarda ta yakamata kabani ba kace intafi gidanmu ba, kana tunanin wai zaiji baqin cikine don kace intafi gidanmu?, to wlh ko d'aya don ko yanzu kasuwa tawatse d'an koli mai rabonci yaci."

Cikin yaranta ta qwalawa kira tace a d'auko mata mayafinta da takalmi dama wayarta na hannunta, ana kawo mata tasa had'e da cewa.

"To Ina jiran takarda ta mijin tsohuwar..."

Bata qarasa ba ya daka mata tsawa had'e da nuna mata gate yace tafita baya son ganinta...








*ALLAH KAJIK'AN IYAYENMU*πŸ‘πŸ˜­
[11/14, 22:52] Billy S Fari: πŸšΆβ€β™€οΈπŸšΆπŸ»β€β™‚οΈ *SANNU SANNU*πŸšΆπŸ»β€β™‚οΈπŸšΆβ€β™€οΈ
πŸ’Ž _Bata hana zuwa..._πŸ’Ž


_WRITTING BY:_ *BILLY S FARIπŸ’Ž*

_DEDICATED TO:_ *BLOOD SISTER'S (AMZAHFAZ)*πŸ’‹

_BESTOWED TO:_ *ZAINAB AL-AMIN (MOM NA'EEM)* AND *AMINA UBA AYUBA (OUM ASHFAQ)*πŸ’ž

*DOMIN FARINCIKINKI SISTER SADIYA ZANGO (MIEMAH)*πŸ’–

*FATAN ALKHAIRI AGAREKU MOMMAH ME NANA HAFSAT (MISS XOXO) AND MAMANA HAFSAT RANO(OUM AFFAN)*❀️

Page___94πŸ’Ž

Batare data damuba tasa qafa taficewarta daga gidan, waje yanema ya zauna d'aya daga cikin kujerun dake wajen ya dafe kai, gaba d'aya yarasa wace irin rayuwace ga hajia nafeesa wacce batada lissafi da kuma sanin yakamata, ko kad'an bata gajiya da fitina arayuwarta duk kuwa yanda za'a jamata kunne, yana iya qoqarinsa wajen ganin yayi haquri da halayyarta har zuwa lokacin da zata canza amma hakan ya cutara har saida taqure haqurinsa tasa ya aikata abunda bai tab'a aikatawa tun qurciyarsa sai yanzu da manyanci ya kamasa.

Haka ya qarashi tunane tunanensa har yagaji yamiqe yakoma cikin gida yana mai Shan alwashi akan cewa koda zai amince tadawo masa gida saita gane gaba d'aya kurakuran data dad'e tana aikatawa tukuna,

Kimanin watanni takwas kenan da aurensu su little kuma adadin watannin cikin batool, zaune take tamimmiqe qafafuwanta tana faman yatsinar fuska saboda nauyin da cikin yayi mata, gaba d'aya duniyar tayi mata zafi ji take kamar ta fasa ihu, kallon little tayi dake mammatsa mata qafafuwanta alokaci d'aya kuma yana d'ibar wainar fulawa ga cokali yana bata abaki tace.

"Abu sumayya, agaskiya 'ya'yaye na d'auke da haqqin iyayensu sosai, sai yanzu nake jin tsananin rad'ad'in rashin kyautawar da nayi abbana azuciya akan kafiyar dana yimasa, da nabi komai ahankali da yanzu abbana bai haramta mani kusantar saba, wayyo...ni wannan karauniyar ce da akeyimun cikin ciki bana so wlh, Awwshhhh...ya ALLAH kabiya iyayenmu da alkhairi wlh da wahala renon cikin nan sosai,

Tafad'a had'e da d'an muskutawa tana qoqarin jinginawa a jikin kujera, cike da tausayinta ya d'anyi murmushi had'e da cewa.

"Ayya!, Yihaquri gimbiya, dama dole ai zakiji haka, kema ALLAH yabiyaki ya saukeki lafiya, idan summynmu tazo saina qwangare mata kai tunda ta wahalar mun da gimbiyata haka"

'Dan b'ata rai batool tayi tana turo baki gaba had'e da cewa.

"Karma kafara don bazan lamunta ba, yarinya 'yar gwal 'yar baiwa zaka dokanmun ita, ai kuwa da anjimu ko sumayya tah."

Taqare maganar tana shafar cikin nata tana murmushi, murmushin shima yayi mata tare da cewa.

"Kice akwai match agidannn don na lura sumy a partyn adawa zata zomun Kuma bazan yarda ba."

"Shikenan tunda kace haka, damankasan ita zatayi wining match d'in shiyasa kake adawa da ita, ni kama dena kiranta da sumy kana b'atawa yarinyata suna, sumayya take baiwar ALLAH."

"O'oh Anya gimbiya!, to shikenan nadena ranki shi dad'e ummu sumayya ALLAH ya saukeki lafiya."

Ta amsa da amin tana dariya.

Bayan sati d'aya da yin hakan takira mahaifiyarta hajia mama suka gaisa sannan tayi mata batun komawarta gida wajen wankan jego, ai kuwa nan hajia mama tayita yimata fad'a had'e da cewa tayi haquri ta zaunawarta gidan mijinta ta haihu babu abunda zai faru da ita in sha ALLAH tunda tana samun cikakkiyar kulawar da koda itace ke tare da ita iyakar ta zata bata, duk da bata so hakan ba haka ta haqura don kuwa ba k'arya gwargwado babu abunda tanema tarasa a fannin kulawa tun daga kan mijinta har zuwa mahaifiyarsa da sauran natare da ita, sun zame mata uwa da uba kuma sunyi mata gatar da bata tab'a tsammani ba aduniya don haka dole ta haqura da ra'ayinta tabi umurnin mahaifiyarta, haka taci taci gaba da renon cikinta yau ciwo gobe lafiya har watan haihuwarta ya kama,

Ranar tana zaune taga little yashigo kai tsaye yawuce d'aki yaje ya harhad'o mata kayanta cikin akwatuna biyu ya fiddosu falo sannan yakoma ya d'auko mata mayafinta yana fad'in.

"Gimbiya tashi muje.."

Binshi tayi da wani irin kallo dake cike da tarin tambayoyi kala kala da take buqatar ya amsa mata kafin sutafi yayi murmushi had'e da cewa.

"Easy madam! Bafa Saida ki zanyi ba, wannan irin kallo haka ai sai kisa 'yan kayan cikina zubikkewa."

Saida tayi dariya sannan yace. "Ahh.. to! Ba dole ba naga notice tsakar rana bazato ba tsammani."

'Dan matse fuska yayi kamar mai shirin kuka had'e da cewa. "Yana iya gimbiya! Gwaggo tace nakawo mata 'yarta yau d'innan ba sai gobe ba tunda watan haihuwarki yakama bazai yuyu kizauna ke kad'ai agida ba, nace zan ajiye aikina mu zauna gidan tare tace a'a, nace aturo maki Shahida shima tace bata amince ba, kinga kuwa dole na cika umurninta."

"Aw! Akan wannan abun d'an abun kake b'ata rai?, Lallei Abu sumayya kice kashagwab'e da yawa yanzu, Ina can d'in ba baqonka bane tunda bawani waje za'a kaini ba, ni danaso komawa kano gaba d'aya nahaihu can da sai kayi qaqa?"

"Tab inbiki mana!"

"Da kuwa katabbata bita zaizai gaskiya."

Taqare maganar had'e da tuntsirewa da dariya can kawai yaga hawaye na zubo mata dariyar takoma kuka, da sauri yaqarasa kusa gareta ya zauna tare da jawota ajiki yana fad'in.

"Gimbiya menene?" Ta d'ora kanta aqirjinsa had'e da cewa.

"Abbana, Ina son naga Abbana ko sau d'ayane, bana son namutu ban ganesa ba."

"Yaa salaam! Gimbiya meya kawo zancen mutuwa kuma, bazaki mutuba har sai muntarawa Abba jikoki da yawa da zaiyi alfahari dasu, kinsan ko jiya saida likita yafad'a maki cewa kirage damuwarnan da yawa tana tab'a lafiyar babynmu, shine kike kuka yanzu bakya son yafito very healthy ne?"

"Ina so mana, Amma bazn iya dena damuwa akan Abbana ba, Ina so naji muryarsa pls Abu sumayya ko a'ane."

Ganin yanda duk tabi tarikice masa yasa yaciro wayarsa had'e da kallonta yace.

"Idan kikaji muryarsa kinyimun alqawarin zaki dena wannan kukan?"

Da sauri ta d'aga masa kai yayi murmushi had'e da shafo kanta dake saman qirjinsa sannan yakira Abba da d'ayan layinsa na (data) da yake using dashi, don tunda ya gwada kiransa bayan auren sau d'aya suka gaisa yagano shine yadena samunsa daga baya idan yakira, may be ya kulle masa layine ta yanda bazai iya samun saba. Bugu d'aya Abba ya d'aga yana fad'in.

"Hello, hello assalamu alaikum." Can yayi tsaki jin ba'a amsa shiba had'e da kashe kiran, d'ago kai tayi ta kallesa hakan yasa yasake kiran lambar yana murmushi.

"Assalamu alaikum." Abba yafad'a awannan karon tare dayin shiru yana jiran a amsa masa a d'aya b'angaren, jin ba'a amsashi ba yasa ya sake tsinke kiran little yasake kira akaro na ukku.

A hasale abba ya d'aga kiran yana fad'in.

"Wai wayene halan? Idan ba'ada abuncewa kar asake kira, shashancin banza da wofi."

Amai makon ya katse kiran saiya ajiye wayar yaci gaba da fad'ansa yana fad'in.

"Wannan ai shashancine akira waya akasa magana, mutane sun d'auka yanda basada abunyi kowama baya dashi, saika rufesu da fad'a akama srry is wrong nomba."

Dariya batool takamayi ita da little tana goge hawayen da suka zubo mata, azahirin gaskiya taji dad'in jin muryar mahaifinta sosai amma aqarqashin zuciyarta wata irin kewarsa ce ta sake rufeta, tana matuqar son mahaifinta fiye da tsammani saboda tsananin shaquwar dake tsakaninsu abunma ba'a magana, qaddarowar son dake tsakaninta da little tajawo mata rabuwa dashi badon ranta yaso ba, cikin dubaru had'e da so da qauna little ya dinga fad'a mata kalamai masu sanyi da zasu kwantar mata da zuciya har saida yaga damuwar dake fuskarta ta gushe daga nan kuma ya karkata akalarsa izuwa muradinsa har saida suka farantawa juna rai sannan ya taimaka mata tayo wanka tashirya, akwatunan tajawo tasake gyara duk abunda take da buqata sannan yafito dasu yasa cikin mota, tana qoqarin fitowa yaja hannunta suka koma cikin d'aki shima ya d'auko wata jikka ya dinga jidar kayansa yana zubawa.

Turo idanuwanta tayi awaje tana dariya tace.

"Abu sumayya ya haka!, Ina zuwa da wannan uwar jikka haka kake ta loda kaya."

"Tab..ai wlh qafarki qafata bazan zauna ba, mezanyi agidan nima can zan koma ai inada nawa d'akin."

Dariya ta dinga yimasa har tana riqe ciki had'e da cewa.

"Ashe ko kaida gwaggo."

"Eh naji dai, amma bazan zauna anan ba ke kina acan sai kace wani mara gata." Yaqarasa maganar yana kulle zip d'in jikkar suka fice tare yanaci gaba da jinini tana dariya.

Satinta uku da komawa gidan Dr wajen Rashida wanda gaba d'aya duk kulawar daya kamata tasamu Rashida nabata wand idan kagani kai karantse kace 'yartace ba suruka ba, yauma kwance take saman gadon bayan sallar magrib Rashida na gefe tana jan carbinta sai kawai taga ta zabura, da sauri ta katse lazumin had'e da miqewa tanu wajenta ganin tariqe kunkuru,

"Batool lafiya?."

"Wash..gwaggo bayana."

"Subhanallahi sannu ko haihuwarce?" Bata tsay jin amsar da zata bata ba da sauri tajawo wayarta takira little sannan tayi cikin gida ta sanar da fatima."

Kan kace me gaba d'ayansu hankalinsu yatashi suka nufi d'akin da sauri, dur qushe suka iskota gefen gado tana yarfi da hannuwa tana cizon baki, ga wani zufa daya tartso mata alokaci d'aya saboda tsananin azabar naquda, ganin haihuwarce zangu zangu yasa Rashida ta d'auko wata qatuwar leda ta shimfid'a mata tare da zane sabo sannan suka kamata ita da fatima suka maida wajen, tun batool na juriya har azabar zafin ciwon naquda tasa tafara kiran abbanta tana fitar da wani iska abaki,

Wani irin tausayinta yarufe Rashida tunawa da irin yanda azabar haihuwa take da tayi, safa da marwa ta shigayi tana karanto addu'o'in da tasani abaki tare da nema mata sauqin rad'ad'in da take ji, bini bini tajuyo tayi mata sannu fatima kuwa tuni tafita taje takirawo Dr, yana zuwa yasa suka riqota suka kaita a mota daidai lokacin little shima ya iso hankalinsa atashe Dr yace yashiga motar ya shiga sannan yaja suka nufi asibiti bayan Rashida takoma ciki ta d'auka kayan da za'a iya buqata.

Ko mintuna ashirin basuyi da Isa ba batool ta samb'alo qatuwar 'yarta kyakkyawa jawur da ita, ho ho zo kaga murna a wajen little ba'a magana don gaba d'aya bakinsa kasa rufuwa yayi musamman da aka fiddo yarinyar daga d'akin haihuwa Dr yamiqa mashi ita, gaba d'aya kamarta sak da batool d'insa babu ta inda tabarota tun daga kan hasken fata har zuwa kamannin fuska.

Kallon Rashida yayi yana dariya yace.

"Gwaggo kinga yarinyar nan gaba d'aya mamanta ta d'auko ko tayimun 'yar kara nima tayi kama dani."

Murmushi kawai Rashida tayi batare data tanka saba tanajin wani irin farinciki marar misaltuwa na mamaye mata zuciya, soqo Fatima tayi masa akai had'e da cewa.

"Lallai little ashe rashin kunyarka har takai haka ban sani ba, bazaka bamu 'yar ba kakame kariqe sai kace wanda za'a qwace mawa sai kamanninta kake fad'a mana."

"Kema dai kyafad'a, bana fad'a maki baida kunya ko kad'an ba kikace a'a, to ai gashi yau kingani da idanuwanki."

Saida yayi mata hud'uba ya rad'a mata sunanta da tunkafin tazo duniya mamanta ta rad'a mata wato (sumayya) sannan yamiqawa Fatima ita yana fad'in.

"ALLAH yaraya mana sumayya." Had'e da gyara mata d'an bargon da aka nad'ota dashi aciki daya d'an rufe mata fuska.

Baki bud'e Rashida ke kallonsa tare da mamakin rashin ta idonsa kafin taji Fatima tace

"Aikam little kabushe fitilarka, ALLAH dai ya shiryaka, in dai wannan narkakkarce badon kar in saketa tafad'i ba ace kishine nakeyi ai dana sakar maka abukka qasa."

"Mama kice dai kinga zata anshe maki Abba shiyasa kikace haka, dama tunda yafito da ita naga yanata kallonta da alama yagama qyasawa."

Taji muryar abbaty daya biyo bayansu yafad'a yana wasar baki shima, hannu yaba little suka tafe had'e da cewa.

"Congrat real Abu sumayya, ubangiji ALLAH yaraya mana."

"Amin" duk suka fad'a kafin dady yasake dawowa ya fad'a masu cewa batool na buqatar jini sai an qara mata don jininta yayi qasa, nan take suka nufi lab shi dasu abbaty da little cikin sa'a kuwa ana auna na little yazo daidai da nata aka d'ibi leda d'aya aka qara mata,

Sosai batool tasamu sauqi don anata fira da ita 'yan uwa da abokanan arziqi dake zuwa dubata, murna awajensu uncle h ba'a magana suda hajia mama da sauran mutanen gida, abbanta ma da aka sanar dashi saida wani annuri ya bayyana a fuskarsa har zaiyi magana sai kuma yayi saurin d'aure fuska yaci gaba da duba jaridarsa batare daya tanka ba, baiso tankawa ba azancen sai kuma yaji ya tsinci kansa da cewa,

"ALLAH yara itama yabata lafiyar shayarwa."

Wannan addu'ar da yayi tasa kowa jin cewa tabbas nan kusa bada jimawa ba zai daina fushi da 'yar tasa kuma yadawo da ita cikin rayuwarsa kamar yanda take ada.

Bayan kwana biyu su uncle h zasuje dubo batool bayan an sallameta daga asibiti hajia mama tacire kunya agefe tabisu taje tadubo 'yarta da kuma baby sumayya, taji dad'i matuqa ayanda taje ta isko 'yartata cikin kulawa da walwala da kuma soyayyar uwar miji da sauran ahalinsa, kusan yini sukayi acan kafin sufara yunqurin juyowa su dawo gida bayan sun ajiye mata kayayyakin da suka jemata dasu masu uban yawa kama daga kan suturarta data baby, kayayyakin abinci da kayan qarin jini da kud'i masu yawa sukace taqara tayi hidima dasu kafin suna, kuma sauran 'yan uwanta da iyayenta nanan tafe ranar suna sannan suka yiwa Rashida dasu Dr da iyayensa godiya sosai suna masu nuna masu farincikin da sukaji na had'a zuri'a dasu da kuma yabawa qoqarinsu wajen kulawar da sukaba 'yarsu wanda hakan baqaramin dad'i yayi masu dady da dr ba suma, koba komai sun samu natsuwar cewa sun kula da amanar batool da suka basu d'ari bisa d'ari tunda har suka yaba ayanda suka ganta.

Ranar suna kuwa batool tasha mamaki don taga gata kala kala kama daga wajen 'yan uwanta har zuwa 'yan uwan mijinta da nasu Dr abun saidai tace alhamdulillah, anyi taron suna lafiya an watse lafiya na kusa sun koma gidajensu na nesama sun kama hanya saidai fatan ALLAH ya saukesu gida lafiya.

A 'bangaren hajia nafeesa kuwa har lokacin bata saduda ba don tanada abunda zata iya kula da kanta koda babu abunda za'a bata agidansu, Shakur nazuwa akai akai wajenta ya gaisheta tare da abun kyautatawa da ALLAH ya hore masa, yayita qoqari wajen lurar da ita kuskuren da tayi tare da nuna mata cewa yanda take d'aukar umma ba haka suke ba mutanene masu karamci da dad'in zama amma taqi fahimta saima masifar da take rufesa da ita wai shima ambashi ya canye kamar yanda aka yiwa mahaifinsa, hakan yasa ya haqura dayi mata nasihar saidai addu'a da kullum yake yimata akan ALLAH ya ganar da ita, wasa wasa tun ana qidayar watannin da tayi batanan yanzu har takusa shekara amma taqi ta hankalta hakan yasa 'yan uwa da abokanan arziqi aka shiga ba Abba haquri akan yabari tadawo d'akinta tunda ba sakinta yayi ba shima yabuga kai ga qasa yace bazai bari ba har sai tayi hankali, kawai aqyaleta taci gaba da abunda takeyi ai SANNU SANNU bata hana zuwa...lokaci zaiyi wanda idan taji wutar gashinta da kanta zata gano kuskuren da tayi kuma tanemi gyarawa.

_BAYAN SHEKARU BIYAR_

Abubuwa da dama sun faru ciki har da rasuwar 'yarsu Abu sumayya da gimbiyarsa lokacin tanada shekara d'aya aduniya wanda hakan ya matuqar tayar masu da hankali, musamman Rashida da little da suka d'auki son duniya suka azawa yarinyar don little kam har da zazzab'i yayi na tsawon sati d'aya, batool kuwa gaba d'aya ta dangana tabarwa ALLAH ikonsa acewarta shikad'ai yasan dalilin amsar yarinyar, yarinyar nada matuqar kwarjini da kuma shiga ran mutane sosai wanda hakan yasa mutuwarta tagirgiza mutane da yawa, ciki kuwa harda hajia nafeesa da tuni tayi nadamar abubuwan data aikata saboda ba kad'an tasha wahalar zaman gida da tayiba sanadiyar gobarar da sukayi gidansu yaqone qurmus da mahaifiyarta aciki saidai aka tattara tokarta data cinye aka sallaceta aka rufeta, ita kuma gaba d'aya jikinta yaqone fuskarta kawaice bata qone ba itama gefe yafara qonewa aka kaita asibiti da taimakon dady inda daqyar likitoci suka ceto rayuwarta don babu wandama yayi tsammanin cewa zata rayu, sai gashi cikin iyawar ALLAH da yardarsa da take kwana basu qare ba tasamu sauqi bayan takwashe watanni kusan uku tana jinya a asibiti, alokacinne tagane cewa duniya ba abakin komai take ba kuma idan mutum yasan farkonsa da qarshensa to baisan tsakiyarsa ba don kusan duk jinyar tata batool dasu ammie ne sukayi, tayi kuka sosai akan abubuwan data yimasu daga qarshe ta roqesu gafara kuma suka yafe mata umma kawaice bata fiye shiga harkar taba don har ga ALLAH bata son abunda zai jawo mata wani walaqancin awajenta, abunda bata sani ba kuwa shine hajia nafeesa tayi nadama sosai har cikin zuciyarta don har little da Rashida saida tanema gafara kuma takira abban batool tafad'a masa cewa

Please Login or Register in order to submit comment