Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sauri, kasancewar dama tana fashin sallah yasa batabi takan kiraye kirayen sallar magrib da akeyi ba tayi kwancenta, ita kuma umma kota kanta batabi ba tad'auki butarta tayo arwala sannan tawuce d'aki ta tayar da sallah.

Can misalin qarfe tara nadare bayan baba yadawo sun gama tattaunawa da umma sannan yayi mata bayanin cewa ai bayan sun gama dubiyar da sun kajene aminin nasa ya bijiro da maganar nemawa d'ansa auren Rashida ashe cikin ikon ALLAH ganin da yake yimata a makaranta yaji yana sonta tun kafin inyi masa magana sae gashi yafad'awa mahaifin nasa cewa ya nema masa aurenta." nan dai ya fayyace mata yanda komai yafaru, ajiyar zuciya tayi had'e da cewa "Alhamdulillah, aini sai yanzu nasamu natsuwa, amma tunda kabarni nake wasu wasin wannan al-amarin tare da taraddi jin kace nan da sati biyu za'ayi auren, amma yanzu Alhamdulillah, ALLAH yatabbatar mana da alkhairi, naji dad'i kuma nayi farinciki sosai ai malan idi mutumen kirkine da kowa zaiyi sha'awar had'a zuri'a dashi, ubangiji ALLAH ya bashi lafiya kuma yasa ayi munada rayuwa."

"Amin ya rabbi, ai don ma bakiga yaron ba, ALLAH dai ya tabbatar da alkhairi, tashi kije ki kirawomun ita" cike da farinciki umma tanufi d'akinta ta tsaya abakin k'ofa tana fad'in "Rashida, Rashida.." jin bata amsa ba yasa taqarasa cikin d'akin, kwance ta hangota saman katifarta, kallo d'aya tayi mata tasan da cewa ba bacci takeyi ba kawai idanuwan natane kad'ai a rufe, matsawa jikin katifar tayi had'e da cewa,

"Ke Rashida lafiya kikekuwa?" Firgigit tabud'e idanuwanta had'e da saukar dasu akan nata, "lafiya kike?" Tasake maimaita mata akaro na biyu, qoqarin miqewa zaune tayi had'e da sauko da k'afafuwanta k'asan katifar sannan tace,

"Umma kainane yake yimun ciwo."

"Ashsha shiyasa yau najiki shiru tunda kika dawo makaranta baki fito ba balle kid'auko abincinki kici, daure kitashi mahaifinki nakira inyaso daga can sai kici abinci kisha magani kinji ko" Kai tad'aga mata ita kuma tajuya tabar d'akin tana fad'in

"ALLAH yasawaqe ciwon kai kam ai babu dad'i"

Ko minti biyu umma batayi da zaunawa ba Rashida itama tashigo cikin d'akin tajawo hular hijab d'inta ta lullub'e mata rabin fuskarta tanemi gefen qofar d'akin daga ciki ta zauna, "Baba ina wuni andawo lafiya?" Tafad'a tana gyara hular hijabin zuwa kanta."

"Lafiya klw Rashida, lafiya kike kuwa?" Kafin tace wani abun umma tace

"Au kagafa na manta infad'a maka ba tajin dad'i, na iskota kwance shine dana tambayeta take fad'amun kanta ke ciwo don tunda suka dawo islamiya banga tafito waje ba balle ko abinci tasamu ta d'auka taci."

"Subhanallahi, injin to da sauqi" yafad'a yana kallon Rashida

"Eh da sauqi baba," tafad'a tana goge zufa a goshinta, wani d'an guntun tsaki yaja had'e da cewa

"Matsalar ku kenan mata baku fiye kula ba wani lokacin, shiyasa ake ganin sakacinku yayi yawa ace mutum nada d'a yaga yayi awa kusan biyu a d'aki bai fitoba kuma bazai je yaduba halin da yake ciki ba sai mai faruwa tafaru kaji ana fad'in ai kuwa tun d'azu najishi ko najita shiru ad'aki ashe kaza da kaza yafaru bamu sani ba, to meye amfanin hakan? Kin jita shiru amma kin kasa dubota kiga ko lafiya take sai yanzu da nace ki kirawota, ALLAH ya kyauta"

"Ayi hak'uri malan in sha ALLAH za'a dinga kula"

Hannunsa yamik'a gefensa a qarqashin pillow dake kan gadon ya d'auko kud'in da yakarb'a a hannun umma ya mik'awa Rashida had'e da cewa,

"Ungo wannan ki k'irgamun su nawa ne?"

Mik'o hannunta tayi yana makarkata ta karb'a sannan tafara k'irgawa d'aya bayan d'an shi kuma yana kallonta, saida tagama sannan ahankali ta d'ago kanta tace,

"Dubu ce guda hamsin" murmushi yayi had'e da cewa, "ban fahimta ba"

"Ina nufin naira dubu ce sau hamsin " girgiza kai yayi cike da takaicin dubu hamsin ma 'yarsa bazata iya fad'a daidai ba, wannan wane irin rayuwace, kallonta yayi yanaji kamar ya maketa kafin yace,

"Rashida kenan, ai bahaka ake fad'aba, naira dubu hamsin zakice a hausance kinji ko?."

'Daga masa kai tayi tare da sake mik'a masa kud'in,

"A'a kiriqesu a hannunki, nakine mallakinki duniya da lahira" d'ago kai tayi tana kallonsa cike da alamar tambaya atattare da ita,

"Eh, kud'in kine na sadaki da aka bayar kuma a musulunce bai halatta kowa yayi amfani dasu ba idan ba keba koda kuwa mune saboda hak'k'in k'ine shiyasa na hannunta makisu a hannunki duk abunda kike so kiyi dasu, mudai munfita hak'k'inki koba haka ba?" Yaqare maganar yana kallon umma, jinjina masa kai ita Kuma tayi alamar tabbatar da zancensa.

Muryarta na rawa tace "Babu abunda zanyi dasu baba don ALLAH ku karb'a umma"

"A'a kirik'e hannunki abunda babanki yafad'a shine daidai kinji ko?"

"Umma nifa babu abunda zanyi dasu, baba.." dakatar da ita yayi had'e da cewa, zaki iya ba ummanki ta ajiye maki, tashi kitafi ALLAH yayi maki albarka"

Mik'awa umma kud'in tayi sannan tamik'e zata fita, har ta aza k'afarta abakin k'ofar mahaifin nata yace,

"Rashida bazaki tambayi ko wanene na zab'a maki ba?"

"A'a baba, babu buqatar hakan domin nasan bazaka tab'a yimun zab'in daba daidai ba." Tana gama fad'ar haka tafice idanuwanta na hawaye, tabbas tasan takamu da soyayyar malaminta amma bazata iya yiwa mahaifinta musu ko kuma gardama akan zab'in da yayi mata ba, kawai zatayi k'ok'ari ta yakisheshi aranta kafin lokacin auren.

Shikuwagogan naka matsuwa yayi safiya tawaye yaje makarantar saboda yaga sahibarsa, wacce ke Shirin zamowa matarsa kuma uwar 'ya'yansa, cikin daren yaje yasiyo mata waya k'irar tecno L7 saboda ya dinga jin muryarta duk da dai gaba d'aya wannan satin zai ganta har yagaji.

Tunda sassafe yatashi yayi wanka sannan yaje wajen mahaifiyarsa ya gaisheta tare da cemata zai wuce, ciki ciki ta amsa mata saboda fushin da takeyi dashi akan zaije ya auro masu bare, cikin sanyin murya yace,

"Inna har yanzu fushin kikeyi dani?"

"Ai dole inyi fushi da kai nura zaka jawo mani abun kunya."

"Kiyi hak'uri inna da kin fad'amun tun farko bakyason in auro maki bare agidan nan da bazanyi ba, amma yanzu kinga su baffa sunyi magana bai kamata ace anwatsa masu qasa a idanuwan duniya ba."

"Aiho shiyasa ni kuma aka watsamun qasar, shikenan tashi katafi."

"Taya zantafi inna fuskarki ahaka, kiyi hak'uri don Allah kiyafemun, natabbata idan kikaga yarinyar kema zaki sota kamar yanda nake sonta" Saida ta sheqe da wata dariyar shaqiyanci kafin tace,

"ALLAH natuba kayafemun ni hawwa, ai har abada bazan sota ba, kaidai tashi katafi ALLAH yatsare hanya."

Jikinsa ya matuqar mutuwa dajin kalamanta amma babu yanda ya iya saboda ALLAH shine shedar yanda take jin soyayyar yarinyar bazai iya rabuwa da ita ba, fatanshi dai ALLAH yasawa inna sonta kamar yanda yake sonta,

"Me kake tunani haka!" tafad'a a d'an tsawace da yasashi saurin mik'ewa tsaye yana fad'in

"Natafi."

"Adawo lafiya," tafad'a tare da mik'ewa ta rakosa har bakin qofa.

Adaidai bakin k'ofar fita gidan bayan yaje wajen mahaifinsa shima sun gaisa yafad'a masa zai wuce ya had'u da qannen mahaifin nasa baffa Ali da baffa Usman kamar yanda suke kiransu, duqawa yayi har k'asa ya gaishesu, baffa Usman ne yafara amsa masa kafin baffa Ali dake gugar bakinsa da ashuwaki ya tofar da yawu agefe yace,

"A'a malan nura zaka tafi"

"Eh baffa Ali nama yi latti sosai yau gashi inada daraai qarfe takwas naga har bakwai da rabi tayi"

"Eh gaskiya kama tashi katafi, ALLAH yatsare hanya."

"Amin baffa Ali nagode."

Har yafara tafiya yakira sunansa ya juyo zai dawo inda suke yace

"A'a basai kadawo ba, cewa nayi to adai kula kasan halin mata kar ake kabiyewa shashancinsu suhanaka yin abunda ya kaika kaji ko?" Shiru yayi yana nazarin kalamansa kafin yace, "to baffa Ali in Sha ALLAH." Sannan yawuce cikin sauri.

Girgiza kai baffa Usman yayi had'e da kallonsa kafin yace "Yanzu kai Ali meye amfanin abunda kayi, karkamanta yaronnan d'anka ne bai kamata kana yimasa abubuwan da basu dace ba gudun kada yadena ganin girmanka da kimarka, kaga daga lokacin fa girma yafad'i."

"A'a meye rashin dacewa anan, gaskiyafa nafad'a masa, zamu saki yaron namune sagaga alalata mana shi acan"

"Ikon ALLAH, yanzu Ali aganinka har abun yakai ga mata ke lalata maza?"

"Ahaf nawa akayi, ba shiyasa qara mutum ya nemawa d'ansa mata acikin dangi ya huta ba, Amma meye amfanin kwashe kwashe awaje."

"Oho!.. yanzu nagane inda zancenka yayi, wlh kaji tsoron ALLAH kabar yaronnan yazauna lafiya da mahaifiyarsa, meye amfanin sonkai Ali?, Tunda yaron nan yakawo wacce yakeso don me da baza'a haquraba abarsa?" "Mtssss..." Baffa Ali yaja tsaki tare da barin wajen yana suruttansa.

Malan Idris kuwa duk da yana cikin damuwar maganganunda baffa Ali yayi masa hakan bai hanasa fad'ad'a fara'ar saba alokacin daya iso makarantar, Kai tsaye ajinsu Rashida yanufa saboda yanda yake mararin ganinta, duk da itama tana son ganin nasa hakan bai hanata b'uya a qarqashin kujeraba alokacin data hangosa saboda yanda take son samawa kanta mafita tahanyar yakicesa aranta, dube dube yafarayi lokacin daya iso qofar ajin batare daya damu da malamin dake ciki yana yimasu mathematics ba yayinda itako banda fad'uwa babu abunda gabanta keyi,....







*_ALLAH KAJIK'AN IYAYENMUπŸ‘πŸ˜­_*
[8/17, 10:19] Billy S Fari: πŸšΆβ€β™€οΈπŸšΆπŸ»β€β™‚οΈ *SANNU SANNU*πŸšΆπŸ»β€β™‚οΈπŸšΆβ€β™€οΈ
πŸ’Ž _Bata hana zuwa..._πŸ’Ž


_WRITTING BY:_ *BILLY S FARIπŸ’Ž*

_DEDICATED TO:_ *BLOOD SISTER'S (AMZAHFAZ)*πŸ’‹

_BESTOWED TO:_ *ZAINAB AL-AMIN (MOM NA'EEM)* AND *AMINA UBA AYUBA (OUM ASHFAQ)*πŸ’ž

*DOMIN FARINCIKINKI SISTER SADIYA ZANGO (MIEMAH)*πŸ’–

*FATAN ALKHAIRI AGAREKU MOMMAH ME NANA HAFSAT (MISS XOXO) AND MAMANA HAFSAT RANO(OUM AFFAN)*❀️

Page___14πŸ’Ž

Cikin rashin amincewa da zancen malamin Yaya hawwa tace,

"Haba malan, cike fa da yarda da aminci muke kawo buqatunmu zuwa gareku, sai kuma ace da kanku zaku wargaza wanan yardar da muke da ita akanku, wlh no bana son ya auri yarinyar nan don ALLAH kasake dubawa ko akwai yanda za'ayi" jinjina kai ya shigayi yana kallon gefe gefensa kafin yafara kiran wasu kalar sunaye, yajima yana suruttansa kafin yasake baje duwatsun dake gabansa, d'ago kansa yayi fuskarsa a d'aure yace da ita "d'auki d'aya" hannunta narawa tad'auka ta mik'a masa ya jawo wani tray dake cike da qasa ya ajiye agabansa, tsakiyar tray d'in ya aza dutsin tare da yin rubutu saman qasar, ya kwashe fiye da mintuna biyar yana abu guda sai faman zufa yakeyi, can ya shafe rubutuna yayi tare da d'ago kansa yana nuna Maya qasar dake cikin tray yace, "duba nan kigani"

Tana dubawa taga hoton Nuraddeen shida Rashida lokacin daya riqe kunnuwa yana bata hak'uri, da sauri tadafe qirji tana fad'in "nashiga uku ni kuluwa, malan kaga abunda yaronnan keyi agabanta tun ba'aje ko ina ba, don ALLAH malan kayi wani abun, bazan iya jurewa ganin haka ba"

Murmushi malamin tsibbon yayi kafin yace "fiye da haka sai kingani, kawai kitashi kitafi, bayan auren kidawo masan abunda zamuyi amma wannan bazamu iya komai ba" Babu yanda zatayi dole tamiqe jiki ba k'wari taji yace

"An buqaci ki ajiye kud'in sadaka kafin kitafi"

Cikin jin zafi da takaici tabud'e jikkarta taciro naira dubu uku ta ajiye masa sannan tafito kamar zata tashi sama tana fad'in, "wannan ai shi ake kira da asara, maqaryacin banza da wofi meye bazai yuyu ba aduniya, ai wlh banda wancan shashan Aliyun daya kwatanta mani wajenka kuma yace aikinka sha yanzu magani yanzune babu abunda zai kawoni nan don nasan dama bakomai irinku suka iya ba, malan bakada imani shiyafi dacewa da wannan aikin nazo nan nayi asarar kud'ina ga banza." Har ta isa gida fad'a takeyi tana qarawa saboda jin zafin kud'inta da aka amsa ga banza kuma ba'ayi mata aikin da take so ba, nafef na ajiyeta tabud'e jikka taciro kud'i taci karo da baffa Ali daya fito daga masallaci, yana hangota ya washe baki had'e da nufo inda take yana fad'in "sannu da zuwa Yaya hawwa" rufe jikkarta tayi had'e da banka masa wata irin muguwar harara sannan tace, "kasallami mai napep d'in nan acikin kud'ina" tawuce abunta, babu yanda ya iya tunda ta tafiyarta dole yaciro wata damuqaqqar d'ari biyar ya miqawa mai napep d'in yace, "ungo bawan ALLAH cire kud'inka kabani canji" mai napep d'in na amsa yatada kekensa had'e da cewa "ai ahaka na d'aukota."

"'Darin d'in."

"Eh wlh, don ma bance da hamsin ba wannan tsayin da aka sani." Yana gama fad'a yaja kekensa yabar wajen, da sauri baffa Ali ya cimmata daidai qofar shiga gida yana fad'in "Yaya hawwa wud'an ne kud'i kuma kike biyata da kika sani asarar miqa kud'in da nake dasu gaba d'aya, shi kuma tsabar rashin mutuncin wai har nera d'ari ya karb'a, kuma wlh ita kad'ai ce gareni yau ina zancen nakai ad'an silala mana wake da mai sai gashi anrabani da ita."

"Ai ni be burgeni ba don ba haka naso ba, so nayi ya karb'i d'ari biyu a hannunka, idan kahanashi ciko yacire hularka yaje da ita"

"Yaya hawwa meyayi zafi haka?, ALLAH baki haquri, yanzu dai mu ajiye wannan maganar, ya kikaga malamin inadai komai angama ko?" Kallonshi tayi had'e da yaqe hauru hakan yasa shima yasaki murmushi azatonsa andace, ji yayi tace

"Anko dace Ali, ai har an rabasu yanzu kawai ka qaddarama har ya auri 'yarka ya gama"

Sake washi baki yayi yayi had'e da cewa "ai nafad'a maki aikinshi Sha yanzu magani yanzu, dako kinata faman kunfar baki ga inda za'ayi maki maganin matsalarki cikin sauqi." Saida tad'aure fuska sannan tajuyo tana kallonsa ido cikin ido ranta ab'ace tace,

"Eh nako gani Ali, amma ina tabbatar maka da cewa nima cikin sauqi nima zaka biyani kud'ina da kasa nayi asararsu ga banza ga wofi, saboda rashin mutuncin Ali ni zaka yaudara, ka turani wajen matsiyaci talaka da baisan komai ba akarb'e mani kud'i ga banza kuma ace abunda nake so baze yuyu ba, to wlh kaji narantse maka kud'ina ko sisi bazaiyi ciwon kaiba saika biyani" tana gama magana tawuce abunta, tsaye baffa Ali yayi yana kallonta cike da mamaki kafin yayi hanzarin bin bayanta, "Yaya hawwa nifa ban fahimci me kike nufi ba"

"Oho! Ni ba abinda ya dameni kaji nafad'a maka saika biyani kud'ina ko in d'ibesu ajikin waccan gwalmammiyar 'yar taka kona rage zafi."

"Haba Yaya hawwa, meyakawo zancen 'yata anan, don ALLAH kiyi shiru kada afahimci abunda ke faruwa." "Meya dameni ko anji, d'a dai nawane kuma nace bana buqatar wacce za'a aura masa amma anqi afahimceni, to Ina ruwan mutum da duk matakain dana d'auka, kaga ni kaje duk yanda zakayi kahad'o mani kud'ina in koma wajen malan bakada imani, nasan shi kad'aine ke iya maida abunda bazai yuyu ba ya yuyu."
( _wal iya zubillah, yya haww kam kinyi nisa kina buqatar addu'a, duk wani mai sab'o yakan b'oye baya son kowa yasani amma ke qarara kike nunawa mutane ke bakya tsoron ALLAHn da yayiki ma balle d'an Adam, ubangiji ALLAH ya shiryeki da duk masu hali irin naki_).

β€’β€’β€’ β€’β€’β€’ β€’β€’β€’
Da gudu taqarasa cikin zauren nasu tare da tsayawa tana fitar da nishi ahankali, murmushi tayi had'e dasa hannuwa tasake rufe fuskarta, "Alhamdulillah" tafad'a tare da sake leqowa tana hangosa daidai lokacin daya miqawa yaron ledar sannan ya juya yakoma tahanyar da suka biyo, da sauri takoma itama cikin gida tana fad'in "wai kodai mafarki nakeyi?" Daidai lokacin ta k'araso tsakar gidan umma najin me take fad'a tace "meye kuma kike tambayar ko mafarki kikeyi." Cikin farinciki taqaraso inda take zaune tana gyaran wake tace, "Babu komai ummata"

"Anya Rashida?, gaskiya da walakin goro acikin miya wannan farinciki da naga kinayi" kafin tarufe baki sai ga yaron da malan ya aiko yayi sallama had'e da cewa, "wai gashi inji malan idris yace abawa Rashida" kallon yaron umma tayi sannan tamaido kallonta ga Rashida data sunkuyar da kai qasa, murmushi umma tayi sannan tamik'a hannu takarb'i ledar had'e da cewa, "kace angode." Har yajuyazai fita umma takirasa ta warware hab'ar gefen zanenta taciro naira hamsin tamiqawa yaron tace, "kace masa angode kaji ko."

"Kibarsu umma ai har yawuce nagode." Yaron yafad'a tare da ficewarsa da gudu"ikon ALLAH, kaga yaro mai tarbiya, ubangiji ALLAH yai maka albaraka kaji.!" Acan cikin zauren ya amsa da "Amin" sannan yaficewarsa, juyowa umma tayi tana kallon Rashida dake duk'e tana tayata tsince waken, tanaji zatayi magana da sauri tamik'e tana cire jikkarta dake kafad'arta tashige d'aki don tasan babu abunda umman tata bata sani ba, ita dai umma abunma dariya yaso yabata wai yau Rashidar tace dajin kunya, "ALLAH ka sake shirya mana" tafad'a sannan taci gaba da gyaran wakenta, acan cikin d'aki kuwa Rashida kasa tsaida kanta daga murmushin da takeyi tayi tafad'a akan katifarta tare da mulmulawa tajawo pillow tarungume tana dariyar da umma bazata iya jiba ta runtse idanuwanta had'e da furta "I luv you malamina, I luv you Nuraddeen"

Saida tagama sabbatunta tukuna ta tashi tacire uniform d'inta ta sanyo doguwar riga tafito don taya mahaifiyarta aiki, sosai umma ke kallie da sauyin walwalar da 'yar tata ta samu tare da farincikin da take ciki wanda bako shakka tasan abunda take tsammanin rasawane akwanakin baya tasamu tabbacin samunsa, dariya tayi cikin tsokana da nuna cewa bata san abunda ke faruwa ba tace

"Rashida nikuwa wai meye tsakaninki da wannan malamin naku daya aiko maki da saqo d'azu, gashican ma akan kujera na ajiye har babanki yadawo" Saida tayi dariya sannan tace

"Kai ummata ai kunsan komai?"

"A'a nikam ban san komai ba amma dai yanzu abani labari insha, don naga alamar farinciki ya banbanta ranar yau data sauran ranaku ukun da suka gabata, fad'amun meye sirrin 'yatah." Dariya ta sakeyi had'e da cewa.

"Kai ummata, nafahimci komai nakeyi kina sane dashi qyalewa kawai kikeyi."

"Eh mana, ai duk uwa takan banbance tsakanin farinciki da kuma damuwar 'ya'yanta, wasu lokutan kawai tanayin shirune har zuwa lokacin da take tunanin gazawa zata iya bayyana atattare dasu, awannan lokacinne take zamewa jigo kuma garkuwa agaresu har zuwa lokacin da jarumta zata zamo mabayyaniya agaresu. Duk da ban takura kiba wajen sanin halin da kike ciki, akoda yaushe nakan roqi ALLAH d'aya gaggauta yaye maki damuwarki kuma ya matso maki da farinciki marar misaltuwa Kuma alhamdulillah yau natabbata ubangjina ya karb'amun"

"ALLAH sarki umma, tabbas ubangiji ya amsa maki addu'arki ga 'yarki don kuwa ya yae mata damuwarta Kuma yasakata acikin farincikin da baya misaltuwa, ada bana iya banbance soyayya da shaquwa sai ranar da malam idris ya furta kalaman soyayya agareni, aranar ne nasan meye so kuma meye shaquwa, na fahimci gaba d'aya soyayyata da Rabe koda na auresa babu so da qauna aciki shirmene kawai nakeyi gashi najayewa kaina damar da zan iya zab'ar wanda nake son rayuwa dashi tahanyar bawa baba zab'i akan duk mijin daya auramun, hakanne ya jefani cikin matsananciyar damuwa da kuma rashin madafa har nake tunanin farincikina yatafi kenan har abada, ashe bansan cewa wanda yakawo sadakina kuma nake kallo a matsayin zab'in da mahaifina yayi mani shine wanda zuciyata keso, nan take na yankewa kaina hukuncin nesanta kaina da muradin zuciyata saboda insamu damar yiwa mahaifina biyayya, aqoqarin yin hakan ne malan Idris ya walwalemun zare da abawa har nafahimci cewa shine wanda yakawo sadakina kuma shine wanda zan aura" taqarasa maganar tare da miqewa tana kwashe kwanonin data gama wankewa, murmushi umma tayi sannan tace,

"Ikon ALLAH, ai abunda baki sani ba tun kafin mahaifinki yasan alaqar dake tsakaninsa da mahaifin yaron ya yanke shawarar bashi aurenki, kuma ranar juma'ar daya je makarantarku wannan maganarce takaishi wajensa amma saboda ALLAH yariga ya tsaro komai yanda yake son yinsa si gashi kafin yasanar masa da cewa yabashi auren 'yarsa shi da kansa yafad'awa iyayensa anema masa aurenki"

"Tabbas ALLAH shikeyin al-amarinsa ayanda yakeso akuma lokacin daya dace, domin aranar ne nima malan Idris yafurta cewa yana sona wanda aranarne kuma nace baba yazab'amun duk wanda yakeso zan aura."

"To kingani yanda komai yafaru cikin sauqi, kece kawai kika wahalar da kanki, da ace ranar kin sanar dani komai to da bakisha wahala ba, ubangiji ALLAH yatabbatar da alkhairi atsakaninku."

"Amin ummata" tafad'a tare da rungumeta, girgiza kai umma tayi had'e da nad'a mata hannu abaya tace

"Ja'irar yarinya ni cikani tunda ke kin zama ruwa biyu, yau kunya gobe rashinta, ALLAH ya shiryeki" haka suka cigaba da aikace aikacen gidan abun gwanin sha'awa tamkar ba 'ya da mahaifiya ba saboda yanda umma ta sakar mata fuska tabata damar yin fira da ita sosai saboda tasamu damar nazartar kalaman 'yar tata acikin maganganun da sukeyi.

Bayan la'asar baba yadawo yaci abinci ya huta umma ta d'auko masa saqon da malan idris ya aikowa Rashida dashi, karb'a yayi had'e da bud'ewa yaga kwalin wayane da kuma wata leda daban, sa yayi aka kirata yace taciro wayar yagani taciro tana wani sissinne kai yace tabud'e kwalin,

Wayace qirar techno L7 sabuwa dal harda charger d'inta da earpiece, karb'a yayi yaduba had'e da kunna wayar yaga har layi akwai ciki yace "To ki kula Kuma kiji tsoron ALLAH, ubangiji ALLAH yatsare kuma yasanya albarka" sannan ya miqawa umma itama tasa albarka tamik'a mata, Sai da suka yimata jan kunne akan matsalolin waya da kuma rashin alfanun da take jawowa idan mutim baiyi tak tsantsan ba sannan suka sallameta, har zata wuce baba yasake kiranta had'e da cewa d'auki wannan ledar ki wuce batare daya damu da sanin ko menene acikin d'ayar ledar ba, umma ce tace "malan to kaduba sauran kayan?."

"Indai ke kinduba alhamdulillah ya wadatar."

"A'afa nikam mezai sani bincikarsu batare daka gani ba!."

"To k'yaleta can dasu bazai wuce 'yan turarukka bane da sauransu, Kuma kema kinsan nasha yimaki irinsu ko kuwa?" Yaqarasa maganar cike da tsokana yana yimata dariya, murmushi kawai tayi had'e da kauda kai gefe tana k'ara gyara zamanta.

Aikuwa kamar baba yasani koda Rashida tabud'a ledar turarukkane guda uku sai tarkacensu sweet da cingwam, sosai taji dad'in kyautar don ba qaramin son sweet take dashi ba,

Bayan sallar magrib baba yashigo ya leqa d'akin Rashida had'e da cewa takula da gidan zasu fita sannan yaje yacewa umma tafito suje, dama d'azu sunyi magana akan bayan magrib zai kyaita taga kayan d'akin daya siyawa Rashida idan sunyi gobe sai akwasosu,

Basu jima da fitaba wayar Rashida tafara ruri wanda har saida yasa taji tsoro, kasancewar tana yawan amfani da wayar ummanta yasa duk tad'an San wasu abubuwan amma wasukam saiya zauna zaman koya mata saboda bata sani ba, gashi ita wayar daya sawo matama touching ce ita kuma tafi iya mai keypad, ta dad'e wayar na ruri kafin tasamu daqyar ta d'aga,

"Assalamu alaikum." Tafad'a kamar mai koyon magana kafin taji ta d'aya b'angaren an amsa mata da, "wa'alaikissalam d'alibata, ya akayi baki d'aga watar da wuri ba"

"To malamina ban iya bane, ko yanzu ALLAH ne yataimakeni hannuna yakai inda ake d'agawar badon haka ba saidai ta qaraci kukanta tagama" tabashi amsa kai tsaye ba tare da wata kunya ko shayi ba, saida yayi dariya sosai sannan yace

"Kai d'alibata, sedai kice naqarashi kirana nagaji nagama, oh ni Nuraddeen ya zanyi da d'alibata?"

"Haquri zakayi tunda ba tason bokon." Tafad'a tana dariya.

"Hmmm ALLAH dai yakai damo ga harawa, boko kam ai kamar kinyishi kingama..."

"Tirqashi! Ashe kuwa akwai 'yan kallo, Allah yabani kon koya to."

"Amin, ya kike?."

"Lafiya klw malamina."

"Masha Allah, haka nekeson akoda yaushe kunnuwana sudinga ji, ya baba da umma duk suna lafiya?"

"Eh suma lafiya klw yanzunnan suka fita."

"Allah yadawo dasu lafiya."

"Amin."

Shirune yabiyo bayan gaisawar tasu kafin yace,

"Rashida nifa har yanzu nakasa samun natsuwa wajen tabbatar da wane irin so kike yimani, sai nake ganin kamar zuciyarki bata yarda da soyayyar da nake yimaki ba."

"Meyasa kace haka bayan Kai tsaye n nuna maka raunin da zuciyata tayi saboda yanda zantuka da kuma kalamanka suka narkar da ita, kamata yayi ace nice nake shakkun haka saboda banida wata nagartar daya kamata ace na cancanci samun soyayyarka."

"Hmm d'alibata kenan! Ai ita soyayya Bata dubin nagarta ko kuma dacewa da cancanta, kawai had'uwar jinice da kuma zukata da ALLAH kehad'awa lokacin daya so, karki sake tunanin cewa baki cancanci soyayyata ba domin hakan zi iya tarwatsa mani zuciya, Ina so koda zamuyi aure ya kasance mungamsu da qaunar da muke yiwa junanmu ta yanda bazamu tab'a bari wani abu yashiga tsakaninmu ba balle har wata rana aganmu arana ko kuma muyi yunqurin rabuwa da junanmu, Ina matuqar sonki da qaunarki wanda natabbata hakn daga ALLAH ne, zan tsaya maki wajen ganin nariqeki hannu biyu batare da nabari kin koka ba."

"Hmm! Malamina ai wannan abune mai wahala matuqar mutum naraye, zanyarda akan bazaka sakani koka waba amma indai wannan rayuwarce da wataran farinciki wataran Kuma baqin ciki to dole zan koka tawani b'angaren, babban burina shine ace

Please Login or Register in order to submit comment