Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tsaishesu yana fad'in

"Dr. don ALLAH ka taimakawa yarinyarnan, haihuwa ce zatayi kuma inaga wannan itace tafari, ga dukkan alama yamatuqar Shan wahala don tadad'e tana labour, yanayinta ya nuna tayi riching final stage da zata iya haihuwa wato 10cm don ALLAH kayi iya qoqarinka wajen taimakonta ta haihu lafiya." Yaqare maganar yana had'a hannayensa waje d'aya, riqa hannunsa Dr yayi yana mai bashi k'warin guiwar cewa zai iya sannan ya wuce batare daya tanka ba.

Safa da marwa mutumen ya dingayi abakin d'akin yana mai addu'ar ALLAH ya sauketa lafiya kafin yaciro wayarsa yakira matarsa. Bugu d'aya ta d'aga had'e da cewa.

"Swthrt har ka isa airport d'in." Cike da damuwa yace

"A'a fatima banma je wajen ba, yanzu haka Ina asibiti.." miqewa tayi daga kwancen da take ta tashi zaune had'e da cewa "swhrt lafiya kuwa? meya same kane? Dama tunda zaka tafi Saida nafad'a maka hankalina bai kwanta da tafiyarnan ba qara kabari sai safiya tawaye ido naganin ido amma ka nace kai sai alokacin zaka tafi." Taqare maganar had'e da fashewa da kuka.

"Haba Fatima meye haka kikeyi? Kinaji na ki saurareni kiji me zanfad'a, Babu abunda ya sameni kawai ansamu matsalace akan hanyata ta zuwa filin jirgin..."
Nan yaciga da yimata bayani dalla dalla sannan takwantar da hankalinta, cike da damuwa yaci gaba da cewa.

"Idan zaki iya munanan _mom maternity clinic_ kiyi sauri kizo kinji ko."

"On my way Dr. In Sha ALLAH." Tafad'a tana goge hawayenta had'e da kashe wayar.

Daidai lokacin shima yasaki wata irin ajiyar zuciya tare da runtse idanuwa saiga likitan yafito da sauri ya nufo inda yake tsaye.

"Dr. Lafiya?." Mutumen yafad'a yana kallonsa cikin tashin hankali, shiru Dr. ya d'anyi kafin ya kallesa had'e da cewa.

"Am sorry ansamu matsala. Dole zaka samana hannu anan." Yajuya wajen nurse d'in dake biye dashi ya karb'i takarda a hannunta yana miqa masa. "Zaka saka hannu saboda dole sai anyi mata tiyata bazata iya haihuwa da kanta ba."

"Kamarya Dr.? Inada tabbaci akan takai adadin yanda ake buqatar ta haihu mezaisa kace Kuma bazata iya haihuwa ba yanzu."

"Saboda yaron baizo daidai ba, ma'ana amai makon yazo takai sai yazo ta qafafuwa aturance muna Kiran irin wannan haihuwa da "breech presentation" wato haihuwar da tazo a baibai ba normal haihuwa ba." Shafa kai mutumen yayi had'e da cewa.

"Innalillahi wa'inna ilaihirrajiuun." Kafin yafiddo wasu i.d card guda uku had'e da license d'insa nazama likita a aljihunsa ya miqa masa da sauri, karb'a Dr. Yayi ya shiga dubawa, d'aya national i.d card d'insa ce, d'aya kuma i.d card d'in dake nuna yana aiki a qarqashin asibitin aminu kano ce dake garin birnin kano, d'ayar kuma shedar cewa shi qwararren likitane a fannin matsalar mata wato (gynicolgy) inda yaga an rubuta Dr. Nura ahmad. 'Dauke da lambobin dake nuna cewa shi cikakken likitane babba a fannin wato (consultant).

'Dago kai Dr yayi yana kallonsa ya jinjina masa kai alamar bashi tabbaci akan abunda yagani, cike da girmamawa Dr. Yasake bashi hannu suka gaisa saboda ganin shi babban sane.

"Don Allah Dr zan iya shiga na taimaka mata?. Nasan insha ALLAH zata iya haihuwa da kanta basai anyi mata tiyata ba." Shiru Dr yayi kafin ya bashi hanya yana nuna masa qofar shiga d'akin, da sauri ya shiga ya tarar da Rashida kwance ta matuqar jigata, nan take yasa handglove batare daya cire kayan dake jikinsa ba ya nufi inda take kwance, Saida yafara zuwa saiti fuskarta yace.

"Kiyi fad'a da kowace irin qadadara ce data fiddoki cikin dare awannan yanayin, ki qoqarta wajen ceto abunda kecikinki inada tabbaci akan komeye zai zamo sanyin idaniyarki, kada kibari qaddararki ta rinjayi nasararki wajen rasa abunda ke cikinki ta hanyar gazawarki, kiyi addu'a kuma ki jajirce kibamu had'in kai in sha ALLAH zamuyi nasarar wannan aikin da zamuyi." Binsa kawai Rashida tayi da kallo batare data iya tanka masa ba hawaye na tsiyaya tagefen idanuwanta, tabbas ba k'aramin tasiri kalamansa suka yimata ba hakan yasa taquduri bayar da rayuwarta ga abunda ke cikinta.

Nan take yafara ba nurses d'in umurnin miqo masa kayan aiki, cikin k'warewa da hikima irin wadda aikinsa ya koyar dashi yafar qoqarin jujjuya yaron da zimmar mayar dashi ya koma daidai, fiye da mintuna ashirin ya kwashe yana abu guda amma hakan ya cutara, kallon irin wahalar da tasha yayi amma duk da haka bata sare ba da sauri yasa hannu ya goge hawayen da suka zo masa tare daba nurses d'in umurni dasu canzo masa kayan aikin da zai karb'i haihuwar ayanda yaron yazo koda kuwa za'a rasa ranshi saboda aceto rayuwarta,

Nan take aka had'a komai yashiga fara aikin cike da addu'ar ALLAH yasa ayi nasara, kusan wasu mintuna ashirin ya kwashe sannan yayi nasarar fiddo da yaron lafiya, yana fiddosa na'ura nagwajin d'aukewar lumfashin Rashida, haka shima yaron tsabar wahalar daya sha koda aka cirosa ko motsi baya yi, da sauri yajawo oxygen d'in dake can gefen gadonta ya harhad'a ya jona mata da taimakon nurses d'in dake wajen....







*ALLAH KAJIK'AN IYAYENMU*πŸ‘πŸ˜­
[8/17, 10:19] Billy S Fari: πŸšΆβ€β™€οΈπŸšΆπŸ»β€β™‚οΈ *SANNU SANNU*πŸšΆπŸ»β€β™‚οΈπŸšΆβ€β™€οΈ
πŸ’Ž _Bata hana zuwa..._πŸ’Ž


_WRITTING BY:_ *BILLY S FARIπŸ’Ž*

_DEDICATED TO:_ *BLOOD SISTER'S (AMZAHFAZ)*πŸ’‹

_BESTOWED TO:_ *ZAINAB AL-AMIN (MOM NA'EEM)* AND *AMINA UBA AYUBA (OUM ASHFAQ)*πŸ’ž

*DOMIN FARINCIKINKI SISTER SADIYA ZANGO (MIEMAH)*πŸ’–

*FATAN ALKHAIRI AGAREKU MOMMAH ME NANA HAFSAT (MISS XOXO) AND MAMANA HAFSAT RANO(OUM AFFAN)*❀️

Page___38πŸ’Ž

Juyowa yayi yana kallon Dr dake wajen tare dashi wanda yakamata ace shine ya karb'i haihuwar ya miqa masa hannu suka gaisa sannan yace.

"Nagode sosai, in Sha ALLAH zata samu lafiya, ayanayin wahalar da tasha dole nasan hakan zata kasance, nayi abunda na Nemo alfarmaryi sauran kuma nagareku." Yaqarasa maganar yana cire handglove d'in dake hannunsa, murmushi Dr yayi yana yabawa qwarewar Dr. nura tare da jinjina masa akan namijin qoqarin da yayi, wanda badon haka ba babu ko shakka saidai suyi mata tiyata gudun abunda zai iya faruwa da ita ko d'anta, solutin nasa yayi shima had'e da cewa. "Weldone sir, sunana Dr sani Bilal Ina zaunene d'aya daga cikin gidajen dake cikin asibitinnan, naji dad'in had'uwa dakai sosai."

"Masha ALLAH sunana.." saurin katsesa yayi tahanyar fad'o masa cikakken sunansa daya gani arubuce jikin i.d card d'insa ta asibiti wato

"Dr. nura shu'aib k'wararren likita afannin matsalolin mata dake aiki da asibitin aminu kano dake garin kano."

Murmushi yayi sannan yanufi gefen da nurses d'in ke gyara babyen har lokacin be koka ba, karb'arshi yayi ya d'aga qafafuwansa sama kansa na qasa yad'an twad'i d'uwawunsa sai gashi ya canyara ihu, murmushi farinciki yayi sannan ya miqa masu shi yana kallonsa, yaron kyakkyawane sosai gashi da girma tubarkallah, kallo d'aya zakayiwa jaririn kafahimci ba qaramin kulawa yasamu ba alokacin da yake cikin ciki, yana wannan tinaninne yaji wata nurse a firgice tace.

"Dr...." Saboda ganin yanda yaron yafara amai yana fizge fizge, da sauri ya qaraso wajen ya karb'esa nan take yagano yaron yasha ruwan naquda, qoqarin zuqe masa su ya shigayi da taimakon Dr sani da gaba d'aya hankalinsu ya tashi, miqa masu shi yayi yace suyi maza maza su kaishi sashen ba jarirai taimakon gaggawa, haka kuwa akayi kafin kace me har sun isa wajen nurses d'in b'angaren suka karb'esa suka fara bashi kulawa kafin likitan dake b'angaren yaqaraso, yana zuwa yashiga duddubasa cikin k'warewa da iya aikinsa.
Bayan komai ya daidaita shima yaron aka saka masa oxygen saboda yanda lumfashinsa ke kokuwar barin jikinsa.

Dr. nura kuwa nurses nafita da jaririn ya nufi inda Rashida ke kwance ya qura mata idanuwa, gaba d'aya kamannunta dana yaron sunsha banban, wataqil shi mahaifinsa yabiyo,

Yafad'a aransa, ficewa yayi daga d'akin yana tura hannuwansa cikin aljihu, sai alokacin ya tuno da wayarsa daya ajiye a can gefen gadon da Rashida take kwance da sauri yakoma ya d'auko, kusan 10missed call yagani Kuma duka na matarsa ne fatima wacce take da tabbacin tashigo asibitinne shine takirasa taji inda take, murmushi had'e da danna lambar ya sake kiranta, bugu d'aya ta d'aga tana fad'in.

"Swthrt kana inane? Tun d'azu kabarni a tsaye." Tafad'a cike da qorafi akan haka.

"Fatima kenan! Yihaquri ki qaraso tanan gyani emergency Ina tawurin tsaye Ina jiranki."

"To." Tafad'a had'e da kashe wayar sannan tanufi hanyar da zata sadata da wurin, daidai lokacin shima yanufo qofar fitowa daga wajen sukayi kicib'is da ita d'auke da kwandon kuloli har dasu qatuwar leda da flaks, zaro idanuwa yayi yana kallonta cike da mamaki yace. "Fatima duk meye haka?" dubon agogon hannunta tayi taga kusan qarfe goma da rabi na safe ta dafe kai had'e da cewa.

"Kayi haquri nadad'e ban qaraso ba ko?, natsaya had'a mata wud'annanne, Ina jarin da aka haifa? tahaihu ko?"

Tafad'a tana gyara zaman mayafinta cike da tausayi yabita da kallo, daga jin cewa ya tsinci maiciki a hanya suna asibiti zata haihu shine Fatima zata had'o wud'an abubuwa haka saboda tsananin son haihuwa da take da ita, ya ALLAH kadubemu da idon rahama muma kabamu namu masu albarka, yaqarasa fad'a aransa yana goge 'yan kwallan tausayinta da suka zubo mata.

β€’β€’β€’ β€’β€’β€’ β€’β€’β€’
Dr nura da Fatima mijine da mata dakeda matuqar kyakkyawar fahimta a tsakaninsu, kalla d'aya zakayi masu kafahimci aurensu auren soyayyane saboda yanda suke matuqar son juna, sunyi aure tun shekaru goma sha uku da suka wuce amma har zuwa tsawon wannan lokaci basu samu haihu ba, Fatima macece mai matuqar son yara amma jarabawa ta ALLAH ko b'atan wata bata tab'a yiba, anyi masu duk wasu gwaje gwajen da bincike bincike don agano dalilin rashin haihuwar tasu amma likitoci sun tabbatar masu dashi har ita duka lafiyarsu qalau basuda wata matsala data hanasu haihuwar kawai lokacine beyi ba, hakan yasa gaba d'aya suka tattara komai akan batun haihuwa suka watsar gefe suka rungumi junansu hannu biyu cikin so da qauna da kuma kulawar juna, fatarsu akoda yaushe da addu'arsu shine ALLAH ya basu masu 'ya'ya masu albarka aduk lokacin daya so kuma yanufa, Dr nura cikakken d'an asalin jahar borno ne amma wasu lokutan suna zama a kano saboda aiki daya kaishi can, dalilin fitowarsa yau tunda asuba shine kiran gaggawar da akayimasa tun jiya da daddare ne cewa ana buqatar ganinsa gobe qarfe takwas na safe akwai matar da zasu yiwa tiyata, shiya yayi asubancin tashi zuwa filin jirgin da zai tashi qarfe biyar na asuba don ya isa dawuri, ashe rabon ya taimaki Rashida a wannan lokacin ya fiddosa.

β€’β€’β€’ β€’β€’β€’ β€’β€’β€’
Wata irin ajiyar zuciya Dr. nura ya sauke had'e da riqo hannunta yace, "Kai fatima daga fad'a maki zancen matar nan zata haihuwa shine zaki tsaya kwaso kaya haka!."

Dariya kawai tayi masa batare da tace komai ba saboda Babu abunda takeso alokacin irin taga matar da yace ya tsinta da babyn data haifa, d'akin da Rashida ke kwance yanufa riqe da hannunta har suka shiga.
A bakin gadon Rashida yaja burki ya tsaya yana nunata da hannu. "Fatima kinga baiwar ALLAH da nake fad'a maki nagani tafito daga cikin wani daji tashigo gaban motata, badon ALLAH yatsare ba dana bugeta gata da tsohon ciki." Cike da tausayi tariqe hannunsa gam kamar zatayi kuka yace.

"Swthrt meya fiddota waje a lokacin gata qaramar yarinya mai qanan shekaru, yanzu haka sharri da baqincikin d'a namiji yasata fitowa, kai walh wasu mazan basuda imani."

"A'a fatima karkice haka tunda bamusan dalilin daya fiddota be daga gida ba, wataqil wata matsalarce daban."

"Hmm! Bazaka gane ba swtht wlh yanzu hakan mijinne yakorota saboda wani banzan dalilinsa, ya ALLAH kadubi maraicinmu."

Tafad'a tana d'aga hannuwanta sama hawaye nazubo mata daga cikin idanuwa, qara matsowa tayi kusa da Rashida taduqo had'e dasa hannu tana shafa fuskarta,

"ALLAH sarki yarinya, ALLAH yatashi kafad'unki, wlh swthrt da ganin yarinyar nan akwai ban tausayi cikin al-amarinta, yanzu I babyn nata yake?"

"Yana can shima anbashi gado bayada cikakkiyar." Yafad'a tare da juyowa yafito wajen tana biye dashi ya zuba hannayensa acikin aljifan wandonsa, kallonta yayi yaga yanda gaba d'aya jikinta yayi sanyi, murmushi yai sannan yaci gaba da cewa "muje can kiga yaron nata, so nake idan kin amince nabar komai ahannunki kafin nadawo nan da zuwa jibi idan yafarfad'o muji daga Ina take, thank God ma nayi waya da Dr qasim can wajen aiki yace anyi shifting theater da zanyi sai nan da 24hrs saboda jinin patient d'in daya hau sosai."

"Babu damuwa swhrt ALLAH yabasu lafiya, idan da imani da tausayi a qirjin bawa ko bakasan mutumba ai katausaya masa, shikuma taimako bakasan ta inda zai yimaka rana ba wataran, na amince Babu wata damuwa akan haka."

"ALLAH fatina?" Dr nura yafad'a yana dariya.

"Sosai kuwa, yanzu kafasa bin jirgi kenan?"

"Eh da motar haya zanje sai inbar maki wannan koda wani abun zai taso, zan kira Salim ya kasance kusa idan kina buqata."

"Noo..kabarshi kasan bama inuwa d'aya da qanennan naka yafiye reni da yawa."

"To shikenan muje kigano yaron."

β€’β€’β€’ β€’β€’β€’ β€’β€’β€’
Baffa kuwa na fitowa daga asibiti kai tsaye gida yanufa ransa duk a dagule, gaba d'aya ya rasa mekeyi masa dad'i aduniya, yana shigowa cikin gidan ya tarar da yaya hawwa zaune a bakin rumfarsu Inna ruqayya takira mai tallar fankasu (na alkama) ta tasashi agaba sai ci takeyi tana dangwala yaji, tana ganin lokacin da baffa yawuce ta gabanta fuskarsa cike da damuwa amma ko kallon banza bi isheta ba, saida taci mai isarta taqoshi sannan tamiqe had'e da cewa yaron ya jirata tana zuwa ta karb'o masa kud'insa.

'Daki ta iskosa zaune abakin gefen gado ya rabka wani uban tagumi yana tunanin ta inda zai fara sanarwa da iyayen Rashida halin da ake ciki, cikin nuna halin ko inkula akansa tace. "Malan bani naira d'ari in biya yaron can kud'insa na fankasu dana ci." Tafad'a had'e da tura yatsa cikin baki tana qwalqwalo wanda ya laqemata a hauru, hannunsa yasa cikin aljihu yaciro d'ari biyu ya miqa mata ta amsa ba gode balle nagode taficewarta, ba'a jimaba tadawo tamiqo masa canjin naira d'ari ya sake miqa hannu ya karb'a yatura cikin aljihu,

"Yawwa nace ina nura take?, Nifa tunda yafitarnan hankalina ba kwance yake ba kar yaje garin neman gira ya rasa ido..."
Ai kafin tarufe baki baffa yamiqe tsaye yana nunata da d'an yatsa had'e da cewa. "Qarya kike, wlh qarya kikeyi kice kindamu da Nuraddeen, wai yanzu ke a tunanin ki ke uwace ahaka? tir da halin uwa ko in haka take, maqaryaciyar banza maqaryaciyar wofi, shashasha da batasan abunda takeyi ba, sakaryar uwa kawai to kitambayeni Nuraddeen damuwa kikayi dashine ko a'a?"

"Ya haka malan sai kace wanda ke jiraye dani daga tambayarka yarona saika rufeni da kwandon fitina?"

"Naji hawwa jiraye nake dake amma idan harda gaske kikeyi kina son ganin d'anki sai kifad'a mani ina 'yar mutane take tukuna, don bana haufi akan cewa duk inda yarinyarnan taje ko aka kaita kinada sa hannu aciki, don haka kifad'amun inda yarinyar mutane take naroqeki da ALLAH."

"Buhun ubannan, lallai malan kace wani abu, meya dameni da wannan yarinyar da har zakace akwai sa hannuna aciki, to wlh kul kar inji..." Bata rufe baki ba ya d'auketa kyakkyawan marin da saida ta birkita, kafin ta taso yaqara mata wani, zuciyarsa na tafarfasa yace.

"Anzo wajen hawwa, ahalin yanzu bana yimaki kallon daraja da kimar cewa ke matatace, baki isa kiyi mani jan kunne ba agabana, ayau kimanta da cewa ni Idris d'innan ne da kika sani mai sanyin hali da kuma haquri, wannan Idris d'in dake gabanki shirye yake daya sallamaki har abada, ahalin yanzu ba duka kad'ai da ALLAH ya haramta miji yayiwa matarsa ba hatta azabtarwar da zata iyasa kirasa rayuwarki na har abada zan iya yimaki saboda zaluncin da nake tuhumarki da aikatawa yarinyar mutane, don haka tun wuri ina fad'a maki kitanadi kalaman da Zaki fad'awa jami'an tsaro idan sunzo takanki don wlh bazan bar duk wanda keda hannu acikin b'atar yarinyar nan ba.

Tsaye Yaya hawwa tayi tabisa da kallo cike da mamaki don ko amafarki Bata tab'a tsammanin cewa baffa zai iya yimata hakan ba, tureta yayi daqarfi daga gabansa da take yawuce yabar d'akin, yanajin yanda tafad'a akan qarfen gado kanta yabuge qum..amma ko juyowa beyi ba balle ya kalleta ya wuce abunsa zuciyarsa cike da tsanarta ,
Shikuwa Baffa Usman yana fitowa daga asibiti kai tsaye tashar mota yanufa ya shiga motar da zata kaishi cikin birnin kano, gidajen redio da telebijin yaje yabada iya kud'ad'en dake hannunsa don asa masa sanarwar b'acewar rashida ta kafafen labarai saida ya tabbatar anyi komai tukuna sannan yashiga motar da zata kaishi qauyen yarimawa, cikin sa'a ya tarar da malan balarabe yazo wajen baba, cike da karramawa suka tarbesa duk da dai fuskarsa ta gama nuna baya cikin yanayi mai dad'i.
Bayan sun gaisane cikin natsuwa yayi masu bayanin halin da ake ciki ya qara masu da cewa yanzu haka shima Nuraddeen d'in yana asibiti rai a hannun ALLAH,

"Innalillahi wa'inna ilaihirrajiuun" kad'ai baba ya iya furtawa daga nan bai koma cewa komai ba saidai sukaga ya b'ingire qasa daga zaunen da yake, ranar baffa Usman yaga tsantsar tashin hankali wanda ba'a samasa rana domin adaidai lokacinne itama umma data shigo d'akin kawo masa ruwa ashe duk abunda baffa Usman ke fad'a taji da kunnenta ne saidai sukaji fad'uwar kofin dake hannunta kan kace me itama tafad'i wajen a some...





*ALLAH KAJIK'AN IYAYENMU*πŸ‘πŸ˜­
[8/17, 10:19] Billy S Fari: πŸšΆβ€β™€οΈπŸšΆπŸ»β€β™‚οΈ *SANNU SANNU*πŸšΆπŸ»β€β™‚οΈπŸšΆβ€β™€οΈ
πŸ’Ž _Bata hana zuwa..._πŸ’Ž


_WRITTING BY:_ *BILLY S FARIπŸ’Ž*

_DEDICATED TO:_ *BLOOD SISTER'S (AMZAHFAZ)*πŸ’‹

_BESTOWED TO:_ *ZAINAB AL-AMIN (MOM NA'EEM)* AND *AMINA UBA AYUBA (OUM ASHFAQ)*πŸ’ž

*DOMIN FARINCIKINKI SISTER SADIYA ZANGO (MIEMAH)*πŸ’–

*FATAN ALKHAIRI AGAREKU MOMMAH ME NANA HAFSAT (MISS XOXO) AND MAMANA HAFSAT RANO(OUM AFFAN)*❀️

Page___39πŸ’Ž

Cike da tashin hankali baba balarabe yaje ya d'ebo ruwa cikin gida aka yayyafa masu, kusan atare suka farfad'o amma babu wanda ke iya magana acikinsu, banda hawaye babu abunda kezuba daga cikin qwayar idanuwansu, ganin haka yasa malan balarabe yaje wajwn nemo mota don akaisu asibiti, yace wa baffa Usman dake gefe ya rabka uban tagumi cikin yanayi mai wuyar fassarawa yajirasa nan da mintota zai dawo.

Kallo d'aya zakayi masu kasan akwai maganganu acikin bakinsu saboda yanda suka qurawa baffa Usman idanuwa Amma Babu bakin magana sai hawayen kawai da zasu iya fassara maka yanayin da suke ciki, ba'a jima ba malan balarabe yadawo da mota da Kuma matarsa d'aya don seda yakoma go ya d'auko kud'i, nan take suka d'aukesu suka nufi asibiti,

Waya baffa Usman ya d'aga yakira baffa yace ya iskosa yarimawa ga abunda ke faruwa yanzu haka suna asibiti, cikin azama baffa yakamo hanya batare daya sanarwa da kowa halin da ake ciki ba, tafe yake yana addu'o'i abakinsa har yasamu mota, tund'azu ALLAH ne kad'ai yasan awane yanayi baffa kejin kansa saboda tunanin yanda zai fuskanci iyayen Rashida ya sanar dasu zancen b'atar 'yarsu ashe har d'an uwansa yaje yasanar dasu, saidai ayanayin daya ce suke ciki yanzu kuma shine babban abunda yafi d'aga masa hankali, har aka iso qauyen yarimawa baffa baisan an iso ba saboda tsananin yanda damuwa tayi awan gaba da dukkanin ilahirin natsuwarsa.

Kai tsaye asibitin ya nufa yatarar dasu baba balarabe da baffa Usman tsaitsaye cikin halin jimami suna jiran fitowar likita, qarasowa wajensu yai jikinsa duk Babu qwari, cike da jin kunya had'i da damuwa yaba malan balarabe hannu suka gaisa, fuskarsa asake ya amsa masa yana mai tambayarsa halin da Nuraddeen ke ciki tare da jajantawa juna akan abunda yafaru, suna nan tsaitsaye likita yafito ya nufo inda suke, tambayarsa suka shigayi ya jikinsu baba da umma yace su biyoshi office tukuna,

Baffa da malan balarabe ne zaune saman kujerun dake kallon likitan shi Kuma baffa usman na tsaye, seda Dr yayi gyaran murya sannan yafara fad'a masu halin da suke ciki,

Sanadiyar tashin hankali da baba yashiga a lokaci d'aya ya haifar masa da ciwon hawan jini wanda ahalin yanzu yakamu da mutuwar sashen jiki ma'ana yasamu (stroke), ita kuma umma sun dubata amma sun kasa gano abunda kedamunta ba abunda take kira inba Rashida ba, wanda hakan yasa dole sai munyi mata gwajegwaje a qwaqwalwarta ko anan ne tasamu matsala.
Wannan shine cikakken bayanin da likita yayi masu akan binciken da sukayi, gaba d'ayansu sun shiga tashin hankali jin abunda likita yafad'a "innalillahi wa'inna ilaihirrajiuun, ALLAH Kai kasan dalilin jarabta wud'annan bayi naka, ya ALLAH ka samasu hak'uri da juriya kuma kabayyana masu 'yarsu aduk inda take." malan balarabe yafad'a had'e da sakin wata irin ajiyar zuciya.

Baffa da Baffa Usman kuwa jin duniyar sukayi gaba d'aya tayi masu k'uncin da suka rasa sanin ina zasusa kansu.

β€’β€’β€’ β€’β€’β€’ β€’β€’β€’
A 'bangaren Nuraddeen kuwa tun safe bai farko ba har sai bayan sallar la'asar, ko daya farfad'o yad'an samu sauqi sosai amma yana tuna zancen b'atan Rashida zazzab'i yataso masa, cikin qarfin hali yamiqe ya sauko daga kan gadon yana yatsina fuska, ganin bakowa wajen yasa yamiqi hanyar fita cikin asibitin don baffa Ali da aka bari ya kula dashi tuni yabar wajen, acan bakin wata bishiya ya hangosa shida wasu yasa andamamasa furarsa hankali kwance yana sha suna fira, bai tsaya bi takansa ba ya wuce gida, tafe take yana harhad'a hanya har ALLAH yasa ya isa gida lafiya, sashensu yanufa ya shiga cikin d'akin, tsaye yayi yana kallon ko ina cike da fatar zaiga Rashidarsa ta iso gare adaidai lokacin, yafi minti biyar ahaka kafin ya duqe wajen yasaki wani irin kuka mai tsima ran duk wanda ke saurare, jin yayi andafo kafad'arsa da sauri yaciro kai yana kallon sama cike da zimmar ganinta amma sai yaga ashe Inna Bilkisu ce, hannu tasa tagoge masa hawayen da suka jiqa masa fuska sannan ta riqosa ya tashi ta azasa saman kujera, cikin sanyin muryar dake nuna tattare take da damuwa tace. "Nuraddeen bazan hanaka kuka ba, domin b'atan Rashida ba kai kad'ai yashafa ba har mu, Amma Nuraddeen Ina so infad'a maka cewa yanzu ba lokacin kuka bane agareka, lokacine da zaka tattaro dukkanin natsuwarka kayi yaqin gano matarka aduk inda take, Ina so kayi amfani da kud'in da kake dasu ahannunka, iliminka da kuma qarfin jikinka kaje kagano matarka aduk inda take, wannan kukan da wani kwanciya duk ba mafita bane agareka, kazuba kud'inka a kafafan yad'a labarai asa maka cigiyarta, kayi amfani da iliminka wajen tsananta addu'a kuma kasa malamai ayi maka, kayi amfani da qarfin jikinka wajen shiga lungu da saqo kadubo matarka, idan ALLAH yayi za'a ganta Ina tabbatar maka da zaka had'u da ita tunda baka zauna ba kaji ko, don ALLAH kadaure duk yanayin da kake jin kanka aciki kanunawa duniya cewa kana son iyalinka ko tana tare da kai ko bata tare dakai, damuwa dolece amma kada kabari tayi tasirin da zata cutarwa da Rashida kai, don na tabbata aduk inda take matuqar tana a hayyacinta kaine mutum nafarko da zatayi fatan kasancewarsa cikin qoshin lafiya da kwanciyar hankali, don haka kayi haquri kuma karb'i qaddararka hannu biyu ta hanyar qarfafa zuciyarka kaji ko?."

"Eh Inna Bilkisu nagode." Yafad'a yana goge hawayen da suka jiqa masa fuska, miqewa tayi tafita tana fad'in, "Ina zuwa.?"

Binta da kallo yayi aransa yana burin inama ace itace mahaifiyarsa, daya rungumeta yayi kukan sosai yanda zata fahimci yanayin da yakeji koya samu sassauci, yana wannan tinaninne Inna Bilkisu tadawo riqe da kwanon abinci da wani kwanon ruwa da damammiyar fura aciki, saida tad'an riqe fuska tukuna ta ajiye masa kwanon abincin agabansa tace

"Maza sauko kaci abinci kaji."

"Bazan iyaba Inna Bilkisu, wlh bana tunanin abinci zai iya shiga bakina bacin bansan halinda Rashida ita da abun cikinta ke cikiba."

"Ungo wannan to kasha, ai haquri zakayi, idan bakaci ba taya zaka samu qarfi ajikinka har ka iya zuwa nemota. kadaure ko rabine kasha kaji ko."
Inna Bilkisu tafad'a had'e da bud'e kwanon ruwan takai abakinsa, awannan karon Babu yanda zaiyi dole yafara tsutsar furar ahankali yana sha tamkar wani jariri, cike da tausayi ta raja'a akallonsa kawai sukaji anbuge kwanon furar yafad'i qasa gaba d'aya tazube, d'ago kai dashi har ita sukayi da sauri don ganin wanda yayi wannan aika aikar, dik da dama gaba d'aya zukatansu sun gama hakaito masu dako wacece, cike da masifa Inna

Please Login or Register in order to submit comment