Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

wata matsala ko akasin haka saboda suriqa bashi shawarwarin daya kamata harma da taimako idan akwai buqatar yin hakan, yadena yin gaban kansa akan wasu abubuwa matuqar suna raye dominsu har yanzu yaro yake agaresu, ya matuqar jin dad'in nasihohin da suka yimasa kafin yayi madu sallama yawuce gida suna masu sanya masa albarka da addu'ar ALLAH ya albarkacesa da zuri'a d'ayyaba.

Zama mai cike da girmamawa da kuma mutunta juna ke tsakaninsu da Rashida, basuda matsala da ita haka itama batada wata matsala dasu, rayuwarsu sukeyi mai tsabta inganci da kuma nagarta har little Nuraddeen ya cika wata goma aduniya lokacin har yafara takawa Babu inda bai zuwa, yayi wayau sosai gwanin ban sha'awa dashi ga surutu, koda yafara iya magana da gwaggo yake kiran Rashida saboda sunan da yaji ana kiran mai aikin gidan dashi kenan sai yazata itama sunanta kenan yake kiranta dashi, Amma yanayin shaquwa da sabon da yayi da Fatima ita mama yake kiranta shi kuma Dr da Abba yake kiransa saboda tunda suka dawo kusan duka renonsa a hannunsa yakoma, iyakar Rashida dashi bashi nono sai wasu lokutta da idan uzuri ya gittowa Fatima sai tayi masa wanka da gyarashi, hatta bacci wani lokacin awajensu yakeyi ataqaice duk wata kulawa daya dace uwaye suyiwa 'ya'yansu su suke yimasa, kallo d'aya zakayi masa kasan d'an d'an 'yan gayune saboda irin gyaran da yake samu daga wajensu, wata irin mahaukaciyar soyayya sukeyi marar misaltuwa daga shi har mahaifiyarsa, idanko zasu fita sau goma ayini yadinga ihu kenan yana zallo har sai sun tafi dashi, ita abun har mamaki yake bata don ba qaramin shaquwa yayi dasu ba, Babu abunda ma yafi bata mamaki irin kud'in da suke kashikke masa aduk lokacin da suka fita dashi sai take tunanin kamar tad'ora masu hidima sosai akansa, lokacin data roqesu surage yimasu hidima kada abun yayi yawa nan take suka b'ata rai had'e da nuna mata rashin jin dad'insu akan haka, dole tabasu haquri taci gaba da yimasu addu'a suma ALLAH yakawo masu nasu 'ya'yan masu albarka kusa kusa kamar yanda tasaba akoda yaushe.

Hakama dady da ammie suna matuqar son yaron sosai don duk lokacin da Dr zasuje tare suke zuwa dashi, shi kuma baba randa yafara ganin yaron saida gabansa yafad'i saboda yanda ya hango tsantsar kamarsa da 'yarsa da kuma ummanta atare dashi, yadad'e yana tunanin anya wannan yaron ba jininsa bane kuwa?, Amma sanin cewa jikane ga alhaji tunda baisan alaqar dake tsakanin yaron da kuma Dr ba yasa yakama bakinsa yayi shiru daga bayama sai yashiga tambayar kansa taya hakan zai faru tunda yasan kosu waye iyayen yaron?.duk lokacin daya ga yaron sai yaji gabansa na tsananta fad'uwa, ji yake tamkar Rashidarsa ce hakan yasa yafara qoqarin jan yaron ajiki,

Dady ma ranar daya ga little kai tsaye yacewa ammie yana kama da umma tayi dariya had'e da cewa.

"Ikon ALLAH dama haka abun yake, qila idan anyo taliyo yanada alaqa da ita tunda dama mutane 'yan uwan junane idan an bincika."

Basu wani d'auki maganar da muhimmanci ba shiyasa suka barta abakin nan batare da tayi tsayi ba.

Yau da misalin qarfe biyar na marece Fatima tafito riqe da hannun little suna takawa ahankali kamar yanda take tafiya yasha manyan kayansa irin na cikakkun hausawa hadda babbar riga da hannuwa masu clips kai karantse kace babban mutumne, kansa saye da 'yar madaidaiciyar hula irin mai qube d'innan da takalma have cover yayi matuqar kyau sosai har yagaji, murmushi Rashida tayi had'e da cewa Masha ALLAH aranta kafin tace "Haba aunty, uncle fa nawaje yana jira kin tsaya biyewa tafiyar wannan yaron da sai magrib tawuce baku qaraso ba,"

"Eh munji dai, ai SANNU SANNU bata hana zuwa ko my boy."

Taqarasa maganar had'e da d'aukeshi sannan taqaraso wajen tana d'agawa Rashida gira tana dariya had'e da kallon little tace.

"To ya kikaga yarona?."

"Ba kyau, kuma am jealous." Rashida tabata amsa had'e da wucewa gaba tana dariya.

"Lallai ma maman boy, kawai kice dai jealous d'inne yahana kiga zallar kyan dake zuba anan.?"

Saida suka iso suka shiga cikin motar sannan itama Rashida ta shiga sukabar qofar gidan, bayan sun hau titi sunfara tafiya Dr nura ya kalli Fatima yanda tayi kyau ita da little tamkar ace d'anta ne yace.

"Wow..Masha ALLAH, matar yau kincini tukuici, wannan wankan na takwara dole yahau Instagram, yaro sai kace donsa aka halitto kayan nan na hausawa, gaskiya badon kar ace nayi sonkai da yawa ba da nace maman boy kinfi kowace uwa azamanin nan dacewa da kyakkyawan yaro kamar takwarana."

"Kai uncle to ai wannan zancen naka ga mamansa nan azaune ita kad'ai zata iya fahimtarsa amma nikam yanzu haka nahango yaron daya fishi kyau da komai akan titin nan."

"Jealousy jealousy.."

Fatima tafad'a tana dariya.

"Yawwa maman boy yaufa wajen su ammie zan kaiki kugaisa, tun satin can take cewa na kaiki wajensu kugaisa amma ko yaushe sai namanta saboda abubuwa da sukayi mani yawa, Yauma matar ce tatuna mani ganin Ina shirin tafiya can nida takwara shine nace tafad'a maki kigyara sai muje gaba d'aya, Ina fatan bamu takuraki ba ko?"

"Laaa..uncle wace irin takurawa, ai nima matsayin iyaye suke agareni kuma kamata yayi ace tuntuni nayi wannan tunanin na zuwa nagaishesu lura da irin saqon gaisuwar da akoda yaushe suke aiko mana dashi amma rashin kammaluwar cikakken tunani irin nawa yasa nakasa yin hakan, babu komai kuma naji dad'i sosai koba komai naje naga mahaifiyar da tayi sa'ar samun nagartaccin 'ya'yaye kamarku, inada yaqini akan cewa tafi kowa sa'ar samun surukar qwarai irin aunty Fatima kuma nasan tana alfahari da ita sosai.

"Hakane maman boy, mahaifiyata nason Fatima fiye da son da takeyimun, a kullum tana fad'a cewa itace cikar farincikin mu kuma hasken gidana." Yaqare maganar yana kallon Fatima data qura masa idanuwa had'e da d'aga mata gira.

Haka sukayita firarsu har suka isa qofar gidan wanda yayi daidai da shigowar baba yanufi sashen da aka basu.

••• ••• •••
Baffa kam tuni yagama haqura tare da fitar da rai akan komai, yanzu tunaninsa gaba d'aya yakoma akan d'ansa da tunda yatafi baya samunsa awaya kuma shi bai kiraba gashi yanzu kimanin watanni bakwai kenan da tafiyarsa,

Ganin baffa na neman shiga wata damuwar yasa baffa Usman yakoma wajen iyayen matarsa Inna Bilkisu akan zancen auren 'yar yayarta da akayi da baffa mai suna nusaiba, nan take aka fara shire shiren biki nan da sati mai zuwa, fenti marar tsada baffa Usman ya siyo don yanzu bashida isashshin kud'ad'en a hannunsa saboda lalurorin da sukayita fuskanta yasa akaje akayowa baffa awancan gidan inda yake zaune lokacin yana kasuwa, koda yadawo yatarar da anyi fenti kuma anmaida komai yanda yake ya tambayi baffa Usman yafad'a masa cewa ai zancen auren sane yatashi, tabbas yasan yanada buqatar natsuwa ahalin yanzu saidai bayada tunanin ta inda natsuwar zata zo masa, dole yana buqatar taimako takowace irin fuska don haka dole yasawa d'an uwansa ido yayi abunda yakamata wataqil hakan shine zai sama masa natsuwa.

Inna Bilkisu kuwa 'yan kud'in adashinta data karb'a tayiwa baffa magana yaqara mata wasu duk da kuwa basuda yawa tasa aka sawo mata akwati d'an madaidaici ta sayi atamfuna guda biyar masu sauqin kud'i da leshi d'aya mai d'an kyau da takalma kala d'aya da jikka d'aya sai hijab da mayafi shima qwaya d'ai d'aya, foda, turare, sabulu da 'yan sauran kwantsammai da basu taka kara suka kawo ba daidai gwargwado irin kayan auren da aka sani anayi aqauye takai amatsayin lefen da baffa yayiwa yarinyar.

Duk da kayan basuda yawa an amshesu hannu biyu cike da farinciki anata saka albarka.

Baffa Ali kuwa da Inna ruqayya yanda kukasan auren da baffa zaiyi abun kunyane haka sukabi gari duk inda suka zauna basuda tsogumin daya wuce wai baffa zai auri qaramar yarinya tsofai tsofai dashi don abun kunya bai isheshi ba, haka sukayita yad'a wannan maganar har ta zagaye garin, yayinda wasu ke kallon abun ba wani abune tunda ansaba yin hakan a qauyen wasu kuma suke kallon auren amatsayin abun kunyane agaresa.

Wannan dalilin yasa ranar d'aurin auren d'aruruwan mutane na qauyen da kewayensa suka halarci taron d'aurin auren bisa sadaki naira dubu ashirin laqadan ba ajalan ba,

Sosai innna Bilkisu da iyayenta sukayiwa yarinya kayan d'aki daidai arziqinsu kuma suka yima baffa hidima sosai don fitar da ita kunya.

Bayan angama d'aurin auren aka wuce gidansu baffa usman inda yahad'a 'yar qwarya qwaryar walima, abincine jalop da sob'o yasa Inna Bilkisu da qawayenta na mutunci suka dafa 'yan d'aurin auren kowa yaci ya sha yaqoshi sannan suka kama gabansu suna masuyiwa baffa addu'a da fatar ALLAH yazaunar dasu lafiya yabasu zuri'a masu albarka...

Acan cikin gida kuwa Inna ruqayya sai gud'a takeyi tana yadawa Inna Bilkisu magana wai anyi abun kunya an aurarwa da 'ya mijin kishin sauri, da dai sauran suruttan da no zasu iya tunzurata, amma taqyaleta ko cikanki bata cemata ba, dama dai munduwa biyu ka amo..

Bayan anyi sallar la'asar mutanen dake zoma Inna Bilkisu sun watse tajawo d'akinta tarufe sannan taje qofar rumfar Inna ruqayya yace.

"To uwar muneera kizo mutafi yowa yayan mijinki bikon amaryarsa, duk da dai nasan zallar kishi bazai barku ba qaramar yarinya ta aure maki wan miji kuma ko ba'aso dole abata girmanta idan ansan girman manya sai akirata da matar Yaya ko kuma Yaya nusaiba.

Tana gama fad'ar haka tafice tabar Inna ruqayya tana d'ura ashar tare da kumfar baki.

Ana gama sallar magrib 'yan kai amarya suka raka nusaiba har gidan mijinta dake can farkon gari Inna Bilkisu nariqe da hannunta sai faman kuka takeyi, nasiha tasake yimata sosai sannan suka baro gidan yarage daga ita sai Aisha yarinyar baffa Usman da yusuf, suma Inna Bilkisu tace da zaran baffansu yadawo sudawo gida.

Shikuwa baffa tunda aka gama sallar magrib yayi zaunensa masallaci yakasa motsawa ko nan da can, juya al'amarin kawai yakeyi a k'wakwalwarsa wai yau shine da sakeyin aure bayan tsawon shekaru kusan talatin da wani abu da aurensa na farko, abunda ko amafarki bi tab'a kawowa aransa ba.

Baffa Usman na kalle dashi tun d'azu har akayi kiran sallar isha'i, tare sukabi jam'i har aka gama baffa yasake komawa inda yake zaune d'azu ya zauna yana tunani.

"Ikon ALLAH, Yaya a Ina katab'a ganin ango ya zauna yana tunani haka?, Don ALLAH katashi katafi wajen matarka nasan yanzu haka tana can zaune ita kad'ai."

"Usman wlh abunnan nauyinsa nakeji, sai naga kamar maganar dasu Aliyu kefad'a gaskiya ce, wlh abunne da kunya sosai."

"ALLAH ne yahana?"

"Ko kad'an."

"To donme kake jin nauyi ga abunda ALLAH ya halasta maka?, Katashi katafi matuqar baso kakeyi tun yau kafara d'aukar haqqoqan amanar yarinyar mutane da aka baka ba." Shiru baffa yayi kafin yamiqe ya rungumesa yana fad'in.

"Nagode d'an uwana, kayi Mani sutura kala kala arayuwa da bazan iya saka maka ba, a matsayinka na qane agareni kazamemani uba kuma aboki acikin rayuwa, ya ALLAH ka kula da dukkanin al'amurranka dana iyalanka ya shirya mana d'an uwanmu shima yayi maka fiye da abunda kayi mani."

"Amin Yaya, ai wannan shi d'inne ake kira da zumunci, allah yabamu ikon cigaba da haquri da juna."

Shi yarakasa har gida sannan ya juya batare daya shiga ba yana yimasa Saida safe, yana shiga suma su Aisha d Yusuf suka gaishesa tare da yimasa saida safe suka nufi gida..





*ALLAH KAJIK'AN IYAYENMU*👏😭
[11/14, 22:52] Billy S Fari: 🚶‍♀️🚶🏻‍♂️ *SANNU SANNU*🚶🏻‍♂️🚶‍♀️
💎 _Bata hana zuwa..._💎


_WRITTING BY:_ *BILLY S FARI💎*

_DEDICATED TO:_ *BLOOD SISTER'S (AMZAHFAZ)*💋

_BESTOWED TO:_ *ZAINAB AL-AMIN (MOM NA'EEM)* AND *AMINA UBA AYUBA (OUM ASHFAQ)*💞

*DOMIN FARINCIKINKI SISTER SADIYA ZANGO (MIEMAH)*💖

*FATAN ALKHAIRI AGAREKU MOMMAH ME NANA HAFSAT (MISS XOXO) AND MAMANA HAFSAT RANO(OUM AFFAN)*❤️

_Thank you guz for d warmest comment you did on a previous page, all jazakumullahu bikhair, fillah i feel so much appy💃🏼bless to be with you & always proudly to have you🥰_


Page___62💎

Yajima tsaye abakin qofar d'akin kafin ya tattaro d'an sauran kuzarin dake jikinsa had'e da tira qofar d'akin sannan yashiga bakinsa d'auke da sallama.

A tsakiyar gado ya hango yarinyar kwance ta lullub'e da alama bacci ya soma d'aukarta ya qarasa wajen yana qara rafka wata sallamar da d'an be qarfi tayanda zatajishi,

Cikin yanayin baccin dake cinta ta tashi da sauri tana murtsuka idanuwa had'e da amsa sallamarsa, kasancewar akwai hasken wutar lantarki a d'akin yasa baffa qura mata idanuwa yana kallon irin kyawon da ALLAH yayi mata, kallo d'aya zaka yimata ka tsinkayo asalin kyawo 'ya'yan fulani dake tattare da ita, farace tas dake da dogon hanci da kuma manyan idanuwa farare tas da suka d'an zurma d'auke da zara zaran gashi a samansu sai kuma yalwataccen gashin girar daya kwanta luf asaman idanuwannata, bakinta kuwa d'an qaramine dake d'auke jajayen labb'a masu matuqar d'aukar hankali, tanada lotsawa a gefen bakinta(dimple) musamman idan tayi dariya wanda shike qara fitar da tsantsara kyannata, ataqaice dai tubarkallah masha ALLAH amaryar baffa sai sambarka, batada wani tsayi ko girman jiki daya d'ara qananun shekarunta don haka dole baffa yayi mamakin qanqancinta a kansa.

Ganin yayi tsaye ya kasa qarasowa inda take yasa ta sauko daga saman gadon tare da takawa zuwa inda yake ta durqusa tana fad'in.

"Ina wuni baffa?."

Wani irin murmushine ya kuccema baffa da yasa haqoransa bayyana a lokaci d'aya yasa hannu ya d'agota daga duqen da take gabansa ya zaunar a bakin gadon sannan shima ya zaune gefenta had'e da cewa.

"Lafiya klw nusaiba, bakiyi bcci ba."

"Nafarayi sallamarka ta tasheni." Tafad'a tana murza d'ayar ijiyarta.

Shiru yayi na tsawon wasu mintuna kafin can yajuyo qafarsa d'aya akan gadon itama yajuyo da ita suna fuskantar juna.

"Nusaiba kinsan ya nake dake?" Yafad'a yana kallonta, saida tad'anyi jim sannan tace.

"Yakumbo tace matsayin uba kake awajena ingirmamaka hakama kaka dasu baffa sunce kai shugabana ne inyi maka biyayya."

'yar dariya yayi don yafahimci metake nufi, anyimata nasihane data girmamasa saboda dattijantakarsa ta isa ya haifeta komanta zarta haka, sannan annuna mata shugaba take awajenta kasancewarsa mijinta wanda hakan zaisa dole tayi masa biyayya, wannan wata hikimace da nagartaccin iyaye keyi don d'ora 'ya'yayensu bisa turbar yin bautar gidan aure cikin ladabi da biyayya da koma girmama maigida, aransa yaji cewa tabbas yayi sa'ar nagartaccin ahalin mata awannan karon.

Ajiyar zuciya yayi sannan yaciga da tambayarta cewa.

"Me ake nufi da shugaba a gidan aure nusaiba?"

"Mijin gidan." tabashi amsa hankalinta kwance.

Yanda take amsa tambayoyin nasa cike da yarinta duk da dai tana fad'a daidai yasa yaqara gasgata qanqantarta don haka yaci gaba da tambayarta akan abunda yashafi karatun addini, kama daga tsarki da kashe kashensa, arwala, farillai, sunnoni da kuma mustahabbanta, yanda ake sallah da abubuwan data qunsa, wanka da kashe kashensa, banbancin Haram da halat acikin rayuwar auratayya duka saida ya tambayeta, yayinda kashi cas'in da twakwas bisa d'ari batasan komai ba sai 'yan qalilan daga ciki musamman ta b'angaren wanka, anan baffa ya fahimci cewa akwai aiki gabansa don dole tasan wud'annan abubuwan kafin komai yashiga tsakaninsa da ita, koba komai zuwa lokacin tasaba dashi kuma taqara sanin ko meye matsayinsa awajenta.

Yana wannan tunanin ne yaji anbubbugo qofar gida yamiqe had'e da ficewa yabar d'akin dama yanzu yake zancen zuwa yarufe don har qarfe goma tayi.

Yana zuwa yatarar baffa Usman ne a qofar gidan riqe da ledoji a hannunsa ya miqo masa yana fad'in.

"Yaya aini namanta da tsiren amarya har sai dana kwanta kuma nasan baka shiga da komai ba shiyasa nace Bari nafitu nan anguwarmu wajen habule mai nama inkarb'o maka tunda anan dai anguwar kusa banga tukubar mai nama ba, gashi ammafa aro nabaka kud'in."

Yafad'a had'e da miqa masa ledojin yana dariya.

Murmushi baffa yayi yakarb'a.

"A gaida qanen nusaiba, ai gaba d'aya shaf ni namantan da wannan zancen, shine zaka fito awannan daren ai da kabarshi."

"Inaa..ai ba'ayi hakan ba tunda sunna ce."

"Hakane kuma, to nagode sosai ALLAH yabar zumunci, kud'inka kuwa har qari zanyi maka in Sha ALLAH."

Saida Baffa Usman yayi dariya sannan yace.

"Inaaa..kud'ina daidai zan karb'a bana son qari, salon kace ace nabada aron bashi na karb'i ruwa (bashi da ruwa).." haka sukayita raharsu kafin yawuce shi kuma baffa yarufe gida.

A inda yabarta anan yasameta tana gyangyad'i ya ajiye ledojin gefe tare dad'an girgiza kafad'arta, zumbur tamiqe tsaye cikin gigin bacci tanufi qofar fita yariqo hannunta ya shiga toilet d'in dake cikin d'akin yace tayi arwala,

Bayan sunfito yarufa mata mayafinta ya jasu sallah raka'a biyu sannan suka sallame, jawo ledojin yayi naman kazane qwaya d'aya da cire sai lemun Coca-cola na gora guda biyu ya tura mata agabanta yace taci,

Citake tana rufe idanuwa had'e da sandare hannu cikin naman alamun har lokacin bacci nacinta don haka yasa hannunsa tare dayin bisimillah yana d'ebo naman yana tura mata abaki, haka yayita bata idanuwanta arufe tanaci har taqoshi don taci fiye da rabi saboda yunwar da takeji sannan yabud'e coke d'in ya azamata bakin gorarar abaki tafara sha, da sauri tabud'e idanuwa had'e da cire bakinta saboda yanda sanyi da gas d'inta suka shigar mata a hanci.

"Bana shan wannan naqoshi." Tafad'a tana qoqarin zamewa takwanta anan inda take.

Aje lemun yayi had'e da d'agata yaje ya wanko mata hannunta yabata ruwa tasha yakaita saman gadon takwanta ya lullub'eta sannan yadawo ya zauna ya canye ragowar naman yasha lemunsa sannan yafidda ledojin awaje.

Yajima zaune yana tunanin abubuwa uku da suka yimasa kututu azuciya, nafarko rashin sanin halin da Nuraddeen ke ciki, na biyu zancen Rashida da aka tabbatar masa da cewa tadawo na uku rashin sanin inda amininsa yashiga wato mahaifin Rashida. ganin bayada tudun dafawar da zai samun mafita akansu yasa yamiqe yafara salloli yana kwararo addu'o'i akan ALLAH yakawo sassauci acikin jarabawowin rayuwarsu.

••• ••• •••
Baba na wucewa sashensu Rashida nafitowa cikin mota, jitayi gabanta ya tsananta fad'uwa da sauri tayi ta'awizi saboda korar shed'an, dama tunda taga annufo gate d'in gidan gabanta yasoma fad'uwa amma saita laqantashi da kyan gidanne da tsaruwarsa yasa tajin hakan, a hankali takebin ko Ina da kallo har zuwa lokacin da Fatima ta zagayo zuwa inda take tsaye tana d'an d'unguzarta da kafad'a.

"Kai maman boy."

Tafad'a tana d'an harararta.

Dariya tayi had'e da cewa. "A'a aunty barni in kalli wannan aljannar duniya, tunda nake ban tab'a shiga cikin irin wud'annan gidajen ba koda kuwa a mafarki ne saidai in hangosu a tv."

Hannunta Fatima taja tana d'auke da little sukabi bayan Dr nura daya wuce yana murmushi,

"ALLAH kidena wannan qauyancin, idan ba haka ba kuwa nida yarona bazamu sake fita tare dake ba kada ki kofsa mana ko little?." Taqarasa maganar tana dariya had'e da kallonsa.

Dariya yayi tamkar wanda yafahimci metake fad'a yana qoqarin zillewa ya sauka qasa ganin annufo part d'in ammie, dama haka yakeyi duk sanda sukazo yafiso a ajiyesa yashiga da qafafuwansa, haka kuwa akayi ta ajiyesa da gudu yanufi cikin falo tana fad'in.

"Little kadena gudufa?"

Ita kuwa Rashida dariyar gudun nasa tashigayi tana fad'in

"Wayyo ni ALLAH Rashida, wlh aunty yaronnan naki idan naganesa da daddare sai gudu, kingasa kuwa qurqur dashi sai kace d'an aljanu."

'Dago kai tayi tana kallonta had'e da harararta sannn tace.

"Mungode, wato nida Dr mune aljanun ko?, Bari mushiga ai zanfad'awa uncle d'in naki abunda kikace."

Hango ammie sukayi da tuni dr nura daya shiga yasanar da ita zuwan nasu tafito cikin shiga ta alfarma tad'auke little Nuraddeen da sai faman wangalar dariya yakeyi yana d'aga hannuwa.

"Wowwww...Masha Allah, oyoyo maigida, wannan wanka haka gaskiya nasayeshi, iyyeeeee yaron Abba kasha kyau tubarkallah yau nikam auren dakai nakeyi."

Shi kam banda dariya da gwarancin maganarsa da ba'a fahimta babu abunda yakeyi, d'ago kai ammie tayi lokacin da suka qaraso tana fad'in.

"Maraba da 'yata takaina, kice yau tafe kuke da manyan baqi, bisimillah sannunku da zuwa"

Tawuce gaba suna biye da ita har suka qaraso cikin falon,

Bayan sun zazzauna suka shiga russunawa suna gaisheta cikin girmamawa yayinda shi kuma Dr nura kecan gefe zaune riqe da remote yad'ora qafa d'aya akan d'aya yana kallon wani shiri a tv.

Gaba d'aya ammie ta manta dashi sai faman firarta takeyi dasu Fatima suna dariya kai kace ba surukarta ceba idan kaga yanda sukeyi, Rashida kawai ce bata wani saki jiki sosai ba,

"Rashida kisaki jikinki mana, kemafa 'ya na d'aukeki tamkar su Fatima, don haka kid'auka nan gidanku ne har zuwa lokacin da zama zaiyi halinsa tsakanin mu dake kinji ko, koda inafatar ko hakan tafaru zumunci bazai tsinke a tsakaninmu ba ko?"

"Insha ALLAH." Tabata amsa tana murmushi,

Ganin sukayi Dr Nura yataso yana kumbura fuska ya d'auki little dake jikin Rashida yana faman jaye mata mayafi da alama nono yake son sha.

"A'a son Ina zakaje kake qoqarin d'aukar Nuraddeen" don ita haka take kiran little, acewarta wai qara ariqa kiransa da cikakken sunansa yafi akan litte d'in.

"To ammie fita zamuyi tunda yau gaba d'aya kin manta dani ta 'ya'yanki kawai kikeyi."

"Ikon ALLAH, shine kake kumbura fuska haka?"

"Eh mana, Nima ai da umma nan nasan zata kulani dani tunda kin shareni.?"

"To da batanan fa?"

"Nazama so lonely, waima Ina take ne? Yafad'a yana duba gefe gefen kitchen.

"Aw sai yanzu kake tambayarta?, Ina tunda kashigo baka nemeta ba kuma kasan inhar dai tananan bazata barka haka ba idan kazo ko?"

"Wlh shirincan ya d'aukemun hankali, ina tajene ammie?"

"Babu inda taje, zazzab'i ke damunta yau shiyasa baka ganeta ba, Amma dai da sauqi don ban jima dabaro wajenta ba"

"Ya Salam! ALLAH yasawaqe, Bari muje nida maigidanta mudubota."

"To ai shikenan ka kyauta kuwa, kagaisheta idan kunje."

'Daukar little daketa faman rigimar shan nono Rashida tayi kamar bata fahimta ba yayi suka fice, Fatima tad'an harareta sannan tamaida kallonta ga ammie tace

"Kingata ko ammie?, Yaro nason yasha nono tahanasa shida kayansa, sai kace jiqawa zatayi tasha, ALLAH haka takeyi masa ko agida tayi kamar bata san rigimar me yakeyi ba."

"A'a Rashida kidena yimasa haka, yaro fane sosai ina watansa goma akace ko?"

"Eh." Tafad'a a kunyace.

"Haba ai har yanzu yana buqatar ruwan nonon ajikinsa don sunada matuqar tasiri wajen basa garkuwa ga lafiyar jikinsa data qwaqwalwarsa, kidena ganin wannan girman d'an jikin da wayau da ALLAH yayi masa tunda bai shekara ba kina bashi nono isashshe yana sha kinji ko?."

"Ai zakiga wasu yaran da wata tara har sun iya tafiya ga kuma d'an banzar wayo atattare dasu amma sukai har kusan shekaru biyu iyayensu na basu nono batare dasun damuba balle shi dake da wata goma da 'yan satukka akai."

Dr nura kuwa d'auke da litte yanufi sashensu umma yayi sallama a bakin qofar shiga d'akin baba dake ciki ya amsa masa tare da bashi izinin shigowa, koda ya shiga kwance ya iskota lullub'e kanta na bud'e ya gaisheta tare da yimata ya jiki, shi kuwa little wajen baba yanufa ya d'aukesa yan dariya.

"Kai babban mutum wannan gayun dai bazai burge amaryar kaba tunda kwance take tana fama da zazzab'i, abunda kawai za'ayi kabani kayannan naka sai in lallab'a maka ita ta tashi kugaisa." Baba yafad'a d'auke dashi yan gyara masa zaman hular kansa shi kuma sai hannuwa yake turawa cikin babbar rigar yana wasa da ita."

Dariya yaba baba yace.

"A gaisheka alhajin baka jeba, kodai alkhairi zakamun intaro hannu."

Hatta umma dake kwance saida suka bata dariya, batasan meyasa yaron ke matuqar shiga ranta ba, ita dai har ga ALLAH jitake tana yimasa wani irin so nadaban, tana wannan tunanin taji ya hayikke jikinta yana qoqarin leqo fuskarta, shi kuma Dr nura suka fita tare da baba suna gaisawa yana tambyar mike damunta.

Zaune umma ta tashi ta jawosa ajiki tana kallonsa, haka kurum taji tafashe da kuka wanda bako shakka kukan tunawa da 'yarta data hango kamarsa da itane, shin taya wannan yaron ya zamo jinin alhaji bayan jikinta da kamanninsa nafad'a mata akwai alaqa mai qarfi tsakaninsa da ita, wannan shine tmbayar da tashiga yiwa kanta tanaci gaba da kuka.

Acan waje kuwa kud'd'i Dr yaba baba yace yaje yakai umma asibiti adubata saboda bai kamata ta zauna da zazzab'in ba tunda ba'asan meke damunta ba.

Godiya yayi masa sosai sannan yakoma cikin d'akin ya d'auko little daya isko lafe ajikinta yana kallo yanda take kuka.

Bayan Dr nura yawuce ya taimaka mata tashirya yana yimata fad'an tacire damuwa aranta kar azo ace itace keneman yimata barazana a lafiyar jiki sannan suka wuce asibitin.

Basubar gidan ba sai bayan isha'i ammie tarakkosu har part d'in hajia nafeesa don su gaisheda dady tunda a part d'inta yake.

Dr nura yafara shiga kafin su ammie da Fatima su shigo suma yana zaune shida hajia nafeesa da yaranta suna kallon wa'azin shaikh Ahmad tijjani Yusuf a tashar Sunnah tv, dama matuqar

Please Login or Register in order to submit comment