Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yanada matuqar tsinkaya da kuma fahimtar abubuwa da sauri, musamman ga mahaifiyarsa da akoda yaushe yake jinta har tsakiyar ransa, duk da bawata shaquwa bace sosai tsakaninsa da ita saboda gaba d'aya kulawarsa ta ta'allaqane akansu Dr da kuma su umma da ammie, amma yana jinta aransa tun daga lokacin da yasan cewa itace mahaifiyarsa wacce tahaifesa da cikinta, saboda kulawar da yake samu awajensu Dr baisan cewa basune suka haifesa ba sai lokacin da hajia nafeesa taci masa mutunci tare da zazzagesa shida umma, anan ne yagano cewa yanda yake d'aukar ammie amatsayin kakarsa dady kuma kakansa ashe ba hakan neba, umma daya d'auka amatsayin matar dady kawai ashe itace kakarsa, gwaggo kuma itace 'yarta wato mahaifiyarsa basu Fatima da Dr ba,

Cikin natsuwa yace waya b'atawa gwaggona rai haka har ta zubar da hawayen da suka kumbura mani idanuwanta?, d'ago kai tayi ta kallesa sai taji wasu sababbin hawaye sun zubo mata tasake fashewa da wani kukan tare da jawosa tarungumesa, sunjima ahaka kafin tatsaida kukan nata had'e dasa hannu tana share hawayen da suka jiqa mata fuska tana fad'in, kana so kasan wanda yab'atama gwaggonka rai?

Da sauri ya d'aga mata kai yana gogen 'yan hawayen da suka zubo masa sanadiyar kukan da yaga tanayi, wani irin nishi mai sanyi tayi sannan tace dashi, abbanka ne little, abbanka shi yasani wannan kukan da naga kanayi.

Cikin farinciki yamiqe yana dudduba ko ina cikin d'akin had'e da cewa, abbana yadawo ne gwaggo? A ina abban nawa yake?, yaushe yadawo ne gwaggo amma kikak'i kirana?, Abba, abba.., ya shiga kiransa yana qoqarin fita.

Saurin dakatar dashi tayi tana kallonsa had'e da cewa, kadena kiran sunansa don bazai amsa ba, kadena nemansa don bazaka tab'a ganinsa ba kuma kadena tunanin zaka had'u dashi nan kusa kamar yanda nake fad'a maka don bazai dawo ba,

Dawowa yayi ya zauna kusa gareta yana fad'in, Amma gwaggo ke kike bani labarinsa akullum tayanda zuciyata tacika da qaunarsa da kuma son ganinsa da jin muryarsa, ke kika sanya mani tunanin cewa zanga mahaifina nan kusa alokacin da ake shegantani, gaba d'aya mafarkina da kuma muradaina sun ta'allaqane alokacin da zan had'uwa da mahaifina kamar yanda ako yaushe kike fad'amun cewa nan kusane bada jimawa ba amma meyasa yau zaki rusa mani su tahanyar cewa nadena tunanin abubuwan da nake fatan zuwansu gareni akoda yaushe?, duk wannan maganar da yake cikin tausasawa da kuma sanyin murya yakeyi matasu,

Riqo hannunsa tayi tace, nasan ni nasa maka wannan tunanin da kuma shauqin soyayyar mahaifinka dason ganinsa, duk nayi hakanne cike dasa ran cewa zai dawo agaremu, amma sai gashi yau da bakinsa yafurta cewa bazai dawo agaremu ba har abada, yazab'i yarabu damu ya zauna acan wata qasar shida wud'anda yake ganin sun fimu saboda rud'in abun duniya, dakansa yasanya wuqa mai tsananin kaifi ya kashe alaqar dake tsakaninsa damu sannan yayi amfani da kalamai mafi d'aci da kuma quna da rad'ad'i ya tunb'ukemu daga cikin rayuwarsa, don haka a matsayina na mahaifiyarka bana son kasake yimani magana akansa da kuma abunda ya shafesa, ina son ka kashe duk wasu mafarkai naka da kuma muradanka matuqar nina haifeka.

Innalillahi wa'inna ilaihirrajiuun, gwaggo idan nayi hakan meye makomar rayuwata?, Wace sheda zan bayar ga mutanen dake shegantani?, wane irin qwarin guiwa zan samu wajen martabaki a matsayinki na mahaifiyata bayan kinsa sharud'd'a masu matuqar nauyi agareni da zasu hanani tsayuwa ako ina inbugi qirji cewa ni d'an halak ne?,

A razane tamiqe had'e da d'aukesa wani irin zazzafan mari hawaye nazubo mata a fuska saboda jin d'acin kalmar da yayi taqarshe sannan ta nunasa da yatsa tana cewa, ko kayarda ko karka yadda kai d'in d'anane kuma kai d'an halak ne ba shege ba kamar yanda mutane suke fad'a, kuma yazama dole kasa a ranka kuma kayarda da hakan azuciyarka.

Ganin yanda b'acin ya bayyana a fuskarta qarara da kuma tsantsar qaunarsa a idanuwanta yasa yariqo hannuwanta ya zaunar da ita yana share mata hawaye had'e da cewa, kiyi haquri gwaggo idan nab'ata maki rai kuma kiyafe mun, na amince da sharad'inki nafarko amma don Allah kijaye nabiyun, kibarni in rayu da mafarkaina nason had'uwa da mahaifina da kuma muradaina akansa domin zasu tsaya mani wajen yaqar duk wasu kalaman cutarwa akaina,

Hannunta ta aza a kuncinsa had'e da cewa, katabbata haka yarona?, Yace sosai gwaggo, tayi murmushin da iya saman d'eb'enta ya tsaya sannan tashiga labarta masa irin firar da akayi da mahaifinsa kamar yanda talabarta masa rayuwarsa da ita acan baya kafin abubuwa suzama hakan, wani wajen tana fad'a masa tana 'yar dariyar da tafi kuka ciwo wani wajen kuma idan takawo fad'a masa tana hawaye, duk da qananan shekarunsa haka yayita bata magana don yana nuna mata yanayin yanda rayuwa kezoma bawa kamar yanda akoda yaushe take lurar dashi, don kam gwargwado yasamu gatar ilimi da tsantsar tarbiya daga garesu, saida yaga damuwar da take ciki tad'an ragu sannan yajawo abincin daya shigo dashi ya zubata tare da miqa yana cewa, kici abinci gwaggona, jarumar uwa, d'aya tamkar da dubu, linzamin rayuwata kuma hasken idaniyata, kinsan da ALLAH kuma yasan dake shiyasa yake shiga dukkanin lamurranki har yake jarabtarki aci, kiqara haquri in Sha ALLAH ranar cikakken farincikinki nazuwa, ahankali nake maki fatan canye duk wata jarabawarki da qaruwar imaninki had'i da lafiyarki, SANNU SANNU dai Bata hana zuwa..da yardar ALLAH sai kinzamo zakaran gwadin dabi aduniya, Ina sonki sosai mahaifiyata kuma inafatar zakici gaba dayi mani addu'ar cimma mafarkaina domin duk halin abbana shima Ina matuqar sonsa.

Wani irin sanyi taji azuciyarta tare da yima ALLAH godiya daya batashi amatsayi d'anta, ko ahaka aka tsaya ta tabbata batayi asarar auren da qurciya tasata iqirarin sonsa ba ba tare da tasan qalubalen dake ciki ba wanda ayanzu take nadamar yinsa arayuwa.

Bayan kwana biyu dady dasu umma da ammie sukazo gidan saboda tattaunawa akan matsalar don tun ranar bai koma d'auko zancenba sai yau saboda bayason abun ya haifar masu da damuwa tsakaninsa da umma.

Bayan duk angaggaisa dady yayi bayani sosai tare da fad'a masu cewa shi yana ganin atuntub'i magabatansa kawai aji ba'asi idan har abunda yafad'a ta tabbata shikenan sai anemi maslaha aciki, idan zasu sa yadawo ya d'auki matarsa da d'ansa sukoma tacan qasar tareni walillahil hamd, idan kuma sawaqe mata zaiyi shikenan, anan umma takafe kai da qasa tace bata amince da hakan ba, Babu yanda za'ayi su iskesu bayan su yakamata ace sunyi hakan, kuma koma meye suna sane amma suka share saboda basa qaunarta don haka ita kawai aje kotu araba auren faqat shi yafi sauqi, don ita dama bata shirya sake rabuwa da 'yarta ba akaro na biyu. Nan fa rigima takucce tsakaninta da dady tafad'i yafad'i saboda yanda tad'au zafi, anan Dr yacewa umma a musulunce bazai yuyu araba auren ba har sai in akwai magabatansa aciki sunsan da maganar don haka tayi haquri aje can d'in, nanma kasa fahimtarsa tayi had'e da fashewa da kuka tana fad'in, bazasu fahimci yanda abun yake ba don ALLAH subar mata 'yarta,

Hakan yasa Rashida da tun d'azu batace komai ba ta d'aga kai tana kallon yanda mahaifiyarta take kuka tacewa dady don ALLAH indai donta zasuje kada sutafi, tafiso abar zancen domin zuwan nasu ba lallaine yayi wani amfaniba tunda baza'a iya tirsasashi dawoba, aslalima yariga daya fad'awa duniya cewa baisan komai ba game da ahalinsa da iyayensa to meye amfanin cewa sai angamsar da duniya cewa yana dasu tahanyar tirsasa masa abunda bayada muradi ko qoqarin cewa sai anje kotu domin araba auren, Saida tashare qwalla sannan taci gaba da cewa ita tana ganin yin hakan zai iya zama qalu bale agaresa ga wud'anda basu san gaskiyar al'amari ba tunda shi yanzu yazama wani shahararre da aka sani awannan lokacin, za'a iyayin amfani da wannan damar ayi qoqarin tab'a mutuncin d'ansu kuma masu sheganta mata shi su samu qwarin guiwa da wata damar cigaba da walaqantasa had'e da tozartasa, koba komai ita yanzu batada wani sauran buri akansa amma akwai mafarkai da dama da d'anta kedasu akansa don ALLAH kada hakan yazamo mafarin rushewarsu.

Murmushi dady yayi irin nasu na manya domin gaba d'aya kalamanta sun gama bayyanar da cewa har yanzu akwai sauran soyayyar mijinta aranta, koma meye b'acin rai yasa takasa iya jure abunda yayi kuma yagamsu da maganganunta saboda tarin hujjojin da keciki, dama shi babban burinsa amincewar yarinyar amma tunda tabuqaci ayi hakan shikenan ALLAH yasanya alkhairi, nan yanuna mata cewa shikenan baza'aje ba matuqar hakn zai faranta mata rai sannan suka koma gida.

Akan sa'insar da umma tayi dashi saida yayi kwana biyu yana fushi da ita duk da bawai har azuciyarsa bane, kawai yayine don yanuna mata kuskurenta kuma tabashi haquri suka daidaita, tun lokacin dady ya d'auki alwashin saka Nuraddeen acikin addu'o'in sa akan ALLAH ya yaye masa abunda ke kansa ya dawo da hankalinsa ga iyalinsa kodon tarin d'imbin qaunar da take yimasa.

••• ••• •••
Yaya hawwa kuwa kullum cikin addu'a take da kuka ALLAH yadawo mata da d'anta agareta, kullum cikin kiran sunansa take tana istigfari akn abunda ta aikata, baya da haka bata aikin komai sai kuka, abinci ma sai Inna Bilkisu tayi da gaske takeci, tsananin rad'ad'in da takeji akan rashin d'anta har ji take yana neman sa lumfashinta ya d'auke, sai yanzu takejin rashin kyautawarta nasa a salwantar da rayuwar 'yar mutane ashe haka akejin zafi alokacin da aka raba iyaye da d'ansu ko masoyi da masoyinsa, tayi dana sani sosai tare da nadamar abunda ta aikata.

Baffa ma gaba d'aya yamiqa lamurransa ga ALLAH yanaci gaba da addu'a ALLAH ya karkato masa da hankalin yaronsa izuwa garesa yadawo gida, don shima yasamu labarin firar da akayi dashi da abunda yace, Wanda hakn yasashi komawa can wajen shuwa gabannin da suka turasu yace sutaimaka abashi lambar da zai iya samun d'ansa yana son magana dashi, ai kuwa cikin sa'a saiga wani daga cikin wud'anda sukayi karatu yanada contact dashi Nuraddeen d'in aka samu lambarsa a hannunsa donsu cewa sukayi basada ita,

Cike da farinciki baffa ya amshi lambar wayar yaje da ita yasa kud'i masu yawa yawa yakirasa,

Tajima tana ringin kafin ad'aga cikin wata iriyar miskilalliyar murya aka amsa sallamar, muryar da Nuraddeen dake kwance yaji tasashi miqewa zaune yana qoqarin tunano wani abun amma yakasa, shikuwa Baffa sai fad'in yake Nuraddeen meyake faruwa dakai?, Kana lafiya?, Kayi magana mana idan kaine, meyasa zaka zab'i yin bauta awata qasar bayan qasarka data taimaka maka?, shin I tarbiyarka tatafine har ka I manatawa damu iyayenka?, don ALLAH kadawo hakanan kaga mahaifiyarka kuma kayi qoqarin gano inda matarka take, jikina nafad'a mani cewa tana raye aduk inda take, sarawa kansa ya shigayi yana son tunano muryar amma hakan tafaskara saboda wani juyawa da ciwo da kansa keyi, cikin qarfin hali yace, bab..kafin ya qarasa yasaki wata irin qara tare da buga wayar ajikin bango ta watse saidai baffa yaji tayi d'if, yanata faman hello hello daga nan bai qara jinsa ba yasake kiran lambar yafi aqirga amma sai yajita akashe hakan yasa yahaqura yaci gaba da yimasa addu'a kuma yana qoqarin sake gwada kiran lambar akoda yaushe amma kashe

A b'angaren Nuraddeen kuwa nan take alokacin ciwon kai mai tsanani ya rufesa yadafe kan da hannuwa yanata juye juye daga tsayen da yake cikin d'akin saiga wani abokinsa d'an can qasar yazo gidan, shiya taimaka masa ya d'aukesa yayi asibiti dashi, bayan ya farfad'o yafara qoqarin tunano abunda yafaru da muryar da har lokacin sautin amonta yakeji akunnuwansa amma yakasa tunowa, hakan yasa da kansa yasa akayi masa allurar bacci don da kansa yanzu yafara rage shan barasar da yakeyi gaba d'aya, tun daga lokacin yakasa komawa yanda yake saboda qarar sautin baffa dake damunsa a kunnuwa wanda yaja gaba d'aya yanzu bayason abunda zai had'asa da waya balle d'aga kira daga ko Ina, hakn yasama gaba d'aya bai komabi takan wayar tasa data tarwatseba.

••• ••• •••
Haka rayuwa taci gaba da tafiya har zuwa lokacin da little yagama secondary, sau da dama yakan so yayi zancen mahaifinsa da mahaifiyar tasa amma idan yatuna yanayin da take shiga nadamuwa akan haka da alqawarin da yayi mata na bazai koma yimata zancensa ba sai yafasa, ana qoqarin nema masa makarantar da zaici gaba da ita wato jami'a yahad'u da wata kyakkyawar yarinya da ALLAH ya jarabceta da mugun sonsa Mai suna *BATOOL*, 'yace ga yayan mahaifiyar hajia nafeesa dake can garin kano wato mahaifar iyayensa, sun had'une sanadiyar hutun da take zuwa nan gidan dady wajen 'yar uwar tata da take matsayin abokiyar wasanta, tunda ALLAH yad'ora idanuwanta akansa taji duk duniya babu wanda takeso sama dashi, wani irin so takeyi masa da batasan iya adadinsa ba wanda hakan yahaifar mata da yawan zuwa hutu garin saboda shi, tun tana b'oye son da take yimasa har takasa haqura ta bayyana masa, aranar kwana yayi yana juye juye don bako shakka bazai yi qarya ba shima yana sonta, saidai tunani matsayinta ga wacce duk duniya babu macen daya tsana sama da ita saboda yanda take amfani da halshenta wajen cutar dashi da mahaifiyarsa harma da kakarsa yasa yakejin bazai iya soyayya da itaba don gudun kada allura ta tono masa bakin galma...






*ALLAH KAJIK'AN IYAYENMU*👏😭
[11/14, 22:52] Billy S Fari: 🚶‍♀️🚶🏻‍♂️ *SANNU SANNU*🚶🏻‍♂️🚶‍♀️
💎 _Bata hana zuwa..._💎


_WRITTING BY:_ *BILLY S FARI💎*

_DEDICATED TO:_ *BLOOD SISTER'S (AMZAHFAZ)*💋

_BESTOWED TO:_ *ZAINAB AL-AMIN (MOM NA'EEM)* AND *AMINA UBA AYUBA (OUM ASHFAQ)*💞

*DOMIN FARINCIKINKI SISTER SADIYA ZANGO (MIEMAH)*💖

*FATAN ALKHAIRI AGAREKU MOMMAH ME NANA HAFSAT (MISS XOXO) AND MAMANA HAFSAT RANO(OUM AFFAN)*❤️

Page___73💎

Ganin abun zai zame masa damuwa yasa ya miqe yaje ya d'auro arwala ya fara nafilfili yana mai addu'ar ALLAH kazab'a masa abun duk da yafi zama alkhairai arayuwarsa.

Tun daga lokacin yad'an fara d'ad'd'aurewa batool fuska duk da kuwa tarin d'imbin soyayyar da yake yimata atunaninsa hakan shine mafita amma ako yaushe soyayyarta sai qara nitso takeyi acikin zuciyarsa, musamman yanda yaga tana faman bibiyarsa, sannu ahankali batare daya ankara ba yafara bata damar da bai tab'a tsammani ba azuciyarsa, gashi tuni angama shire shiren wucewarsa jami'a wato BUK dake nan cikin kano inda Dr nura ya cikashe masa fannin computer science bisa shawarar mahaifiyarsa da Fatima a lokacin yanada shekaru ashirin da d'aya aduniya, wasa wasa shaquwa mai tsanani tashiga tsakaninsa da batool da sati d'aya yarage mata takoma gida can kano don hutunsu yaqare.

Tunda umma tafahimci alaqar dake tsakanin little da batool ta zaunar dashi tanuna masa cewa yafita hanyar yarinyar kodon su tsira da mutuncinsu tunda yasan Babu wata jituwa tsakaninsu da ita Kuma yasan koba komai yanzu karatune agabansa ba zancen aure ba don haka ya fad'ama yarinyar gaskiya, amma da yake yariga ya kurb'i giyar soyayya duk da qananun shekarunsa sai yanuna mata cewa shifa yana sonta kuma itama tana sonsa don haka shi baidamu da duk abunda hajia nafeesa zatayi ba domin yariga da tunfarko kafin sufara soyayya yaba ALLAH zab'i akan yazab'a masa duk abunda yafi zama alkahiri tsakaninsa da batool, don haka tunda har yaji ALLAH naqara samasa sonta kuma har suka fara soyayya to yatabbata akwai alkhairi tsakaninsu kuma babu abunda hajia nafeesa zata iya sai abunda ALLAH yaso, duk iya qoqarin da tayi wajen lurar dashi qin fahimta yayi don haka saita sanar da mahaifiyarsa tun kan abu yayi nisa.

Fad'a Rashida tayi masa sosai tare da umurtarsa ya ajeyi zancen duk wata soyayya agefe har sai lokacin daya kammala karatunsa domin bayada gatar data fimasa karatu alokacin, kasancewar yana matuqar yimata biyayya tare da martabata acikin duk wani umurni da zata bashi yasa ya amince da maganarta kuma yayi mata alqawarin zaiyi yanda tace matuqar hakan zai faranta mata rai, sannan yanemi alfarmar tabashi izinin sake had'uwa da batool d'in sau d'aya daga nan bazai sake kulata ba dama duk wata mace har sai zuwa lokacin daya kammala, taji dad'i sosai tare da saka masa albarka kafin ta shiga sanar dashi saqon Dr ya barmata cewa ta fad'amasa yaje wajen dady yakarb'o saqo ya ida kammala shireshirensa in sha ALLAH jibi zai wuce makaranta don har anfara karatu satin daya wuce ya amsa mata da cewa anjima da daddare zai tafi, sun jima suna firarsu irinta d'a da uwa kafin akira sallar la'asar yayi arwala sannan yanufi masallaci, ana gamawa ya dawo sukaci gaba da firarsu alokacin harda fatima da yaranta gaba d'aya, Rashida na tsokanarsa wai yazama kiyashe ja abunda yafi qarfinka had'e da labartawa Fatima abunda kefaruwa anata dariya, d'an sosa kai yashigayi saboda jin kunya Fatima tace, Kai qyaleta big son, haushi takeji nakusa zama suruka kafin ita, in sha ALLAH indai batool ce kad'auka har tazama matarka komai daren dad'ewa, ai SANNU SANNU bata hana zuwa....kamar gobene zakaga ka kammala karatunka musha buki, ranar aga b'arin nera awajen Fatima surukar Fatima uwar ango da kanta.

Taqarasa maganar tana dariya, d'an kallon Rashida yayi ta qasan idanuwa data mere baki itama tana dariyar yace, wlh ko mama, ranar saidai su gwaggo surab'e agefe sai inkinga dama kince su shigo adama dasu kuma mama kinsan meyasa nake son batool?, A'a big son sai kafad'a, Fatima tafad'a tana kallon Rashida da alamu tafara gajiya da shirmen nasa da tabiye masa sunayi yace, saboda kawai sunanki da take dashi, kinga sai adinga cemani d'an fa....bai qarasa fad'ar abunda zaice ba Rashida ta d'auki throw pillow d'in dake gefenta ta jefesa dashi tana fad'in, ungo nan marar kunyar yaro yatashi da gudu yana dariya yabar falon, maido kallonta tayi ga Fatima had'e da cewa, ALLAH yaron nan naki idan yayi wani abun har mamaki yake bani, duk wannan shiru shirun nasa da nike gani idan yaganki awaje haka yake sake baki yayita zaro suruttai cike da rashin ta ido sai kace bashi ba.

Ah to! barshi yayi, shida mamansa ne balle ayi masa gori, ni kaina mamakinsa nakeyi, zuwa nan da anjima kuma in kika gansa bazakice shine ba, musamman idan dadynsu na awaje, sai kiga gaba d'aya ya tattaro natsuwarsa waje d'aya, yana matuqar girmamasa fiye da lissafi,

Ai aunty shiyasa in za'a kwana ana kawoma uncle laifinsa bazaya tab'a yarda ba, Fatima tace.

Ai kuwa wlh, yo inama yai laifin balle har afad'a masa ya yarda,

Hmm! aunty kenan!, Rashida tafad'a tana murmushi,

Shikuwa bai jima da fita ba aka kira sallar magrib don haka saida yawuce masallaci yayi sallah sannan yanufi gidan dady, yana shiga batool nafitowa daga cikin part d'in ammie, dama yau tayi mayannu sunfi aqirga part d'in don tagansa tasa bayada wajen zama idan ba canba, cike da farinciki tanufi inda yake tana sakar masa wani qayataccen murmushi, ta qasan idanuwa yake kallonta yana susar gefen idonsa har taqaraso, zagayarsa tashigayi hanuuwanta duka nazube abayanta kafin tadawo gabansa ta tsaya tana qare masa kallo tundaga sama hara qasa, shima kallon nata yashigayi yana 'yar dariya sannan yafara zagayarta kaman yanda tayi masa had'e da cewa, ALLAH bazan yarda ba kishanyemun jini nima sai narama, hakan yasata sakin dariya had'e da d'aga hannu kamar zata dokesa, d'an kaucewa yayi had'e daja da baya, tace, kai ko?, Ina kashigane yau tun safe nake nemanka ban ganeka ba kasa gaba d'aya har bugun zuciyarta na neman tsayawa?, taqarasa maganar had'e dasa hannuwa a qugun tana kallonsa, Saida yasa hannuwansa guda biyu ga kunnuwa yariqe yana d'an yatsina fuska sannan yace da ita, tuba nake gimbiya, yau wajensu gwaggo naje shiyasa baki ganeni ba, amma zuciyata da kuma rouhina gaba d'aya suna nan wajenki, zo muje nafad'a maki wani sak'o kafin dare yayi inwuce.

Kana nufin yauma ba'a gidannan zaka kwana ba?, nida nake son musha firarmu har mugaji sai kuma kace haka!, taqarasa maganar tare da juya baya tana turo baki had'e da qoqarin barin wajen, bayan nata shima yabi yana cemata,

Ke gimbiya!, Ina kuma zakije daga magana,

Dena cemun gimbiya ni, kawai kace mun batool d'ina tunda munyi fad'a dakai, 'yar dariya yakama yimata tare da cigaba da binta yana fad'in.

Kai yaushe kuma akayi haka?, to tsaya mushirya mana,

Inaaa!, tafi kawai.

Shikenan! Bari kawai natafi, kicewa su ammie Ina gaishesu. yajuyawarsa kamar zai koma, da sauri tajuyo tabiyoshi baya da gudu shima yad'an ruga saida yaga yakusan kai bakin gate tana qoqarin cimmasa sannan ya baud'e mata tare da nufar gefen da wasu fararen kujeru suke kakkafe tsakankanin part d'in umma dana hajia nafeesa ya zauna yana dariya, tana qarasowa wajen tayi tsaye kamar zatayi kuka tana kallonsa da sauri yamiqe had'e da qamewa ya d'aga qafa yabuge qasa sannan ya Sara mata da hannu yana fad'in, sorry mah! Bushewa tayi da dariya ganin yanda yawani qame tare da zaunawa saman d'aya daga cikin kujerun har tana riqe ciki, Saida tayi dariyar mai isarta yana kallonta shima yana murmushi sannan yanemi waje ya zauna, cikin wani irin kallon qauna takallesa had'e da cewa. Abu sumayya a gaskiya zakayi kyau da soja sosai, ka ganka kuwa dake qame d'innan?

A'a gimbiya, amma tunda ke kingani ya wadatar, saidai ni bana sha'awar duk wani aiki na kaki saboda bana qaunar duk abunda zaisa nayi nesa da mahaifiyata, karatunnan ma da zanje garinku inyi saboda babu yanda na iyane kuma ita tagoyi bayan hakan da babu inda zanje.

ALLAH sarki, shiyasa nake qara sonka abu sumayya saboda kana matuqar girmama magabatanka musamman gwaggo, ya ALLAH kabani ikon qara qarfafa maka hakan idan munyi aure.

Amin gimbiya, wai nikam na tambayeki?, Cikin kashe murya tana kallonsa tace, Ina jinka Abu sumayya.

Meyasa kike kirana da Abu sumayya?, tunda muka had'u dake ban tab'a jin kin kirani da sunana ba, meyasa?

Shiru ta d'anyi kafin tace, sunanka nada matuqar nauyin da bazan iya kiranka dashi ba, kaga sunan abbanmu ne sannan kuma sunan babban Yaya agidannan so bazan iya kiran sunan gatsau ba, Abu sumayya kuwa da nake kiranka dashi mafarkina ne da kuma burina da nake fatan ya tabbata idan munyi aure muka haifi 'yah Ina son taci sunan sumayya, Ina matuqar son sunan tun lokacin da malamin islamiyarmu yayi mana tarihin irin gwaggarmayar da tasha acikin musulunci, to tun alokacin nak'uduri cewa idan nahaifi 'yata sumayya zan saka mata kuma duk mijin da zan aura komai dad'insa ni da Abu sumayya zan kirasa.

Iyyeee to idan shi kuma baya so fa?,

Saida ta d'an d'aure fuska sannan tace dashi, Dole ma yaso tunda nima naso sunan da yake yimani, murmushi yayi sannan yace da ita,

To shikenan, ubangiji ALLAH yacika mana burinmu na alkhairi, ni kaina inajin dad'in sunan sosai kuma Ina sonsa fiye da yanda kike sonshi, tace dashi ALLAH? Ya amsa mata da sosai kuwa.

Saida suka sha firarsu sosai sannan yabijiro mata da maganar da sukayi da mahaifiyarsa kuma ya tabbatar mata da cewa zaibi umurninta koda hakan na nufin zai mutune, duk inda hankali ke tashi hankalin batool yatashi, nan take tafara girgiza kai hawaye nayimata zarya a fuska,

Don ALLAH abu sumayya kada kayimun haka, Ina tsananin sonka kuma saida kai zan iya rayuwa, don ALLAH kataimakeni kada karabu dani har bayan cikar mafarkaina, idan ba haka ba zan iya lalacewa.

Haba gimbiya, meyasa zaki fad'i haka, taya za'ayi in saka idanuwa inaji Ina gani ki lalace adalilina, yakamata ki fahimceni gimbiya, bawai ina nufin murabu bane, ina so mujingine wannan maganar agefene har zuwa lokacin daya kamata, aduk fad'in duniya ban tab'ajin zuciyata zata iya son wata da sunan aure ba daidai da second d'aya, ke ce kad'ai azuciyata kuma ke kad'ai nakeda wannan buri akanki, amma hakan bazai yuyu ba har saina gama cika burin tawa mahaifiyar.

Amma mekake tunani zai haifar akaina lokacin da muka jingine wannan maganar agefe?, ita fa macce ba iyaye na renonta bane don d'ai su zauna suyita kallonta ko su ajiyeta ba har zuwa lokacin da cikar burin wani zaya gama cika, don ALLAH kafahimci wannan abun da kake shirinyi ba komai bane illa kuskure da kuma ganganci da zai jawo rabuwarmu d juna akowane lokaci, kasani ina sonka tun daga zuciya, jinin jiki, rouhina da kuma dukkanin sassan jikina, Abu sumayya zan iya rantse maka akan cewa kaine bugun kowane lumfashi nawa dake fita daga jikina.

Nasani gimbiya, amma nima Ina so kisani mahaifiyata da

Please Login or Register in order to submit comment