Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dady zazzab'ine kawai" yafad'a cikin rawar murya yana b'ab'b'ata rai, d'aure fuska dady yayi sosai had'e da cewa

"Ok. To meye alaqarka da batool qanwar mahaifiyarka, naji ance kamar kana sonta, meye gaskiya?"

Har zaiyi magana dady ya nunasa da yatsa yana zaro masa idanuwa. "Ka tabbatar kafad'amun gaskiya, idan nace gaskiya Ina nufin magana qwaya d'aya tilo wacce batada tabiyu, samuwar ta biyunta kan iyasa na d'auki mummunan mataki akanka, Ina saurarenka!"

Wani qugi Shakur cikinsa yayi don yasan halin abban nasa, idan yace abu to tabbas zaiyisa, wani irin zufane ya keto masa ya shiga sharewa tare da kallon mahaifinnasa yace.

"Dady maganar gaskiya ni bana son batool, asalima bamu fiye jituwa da ita ba, mom ce ke matsamun akan innemi aurenta saboda dani tafi dacewa ba little ba, nayi qoqarin nuna mata banison yarinyar saboda cin mutuncin da take jawowa tana yimani amma taqi ta fahimta, Dana matsa matsa mata da zancen sai tace idan har nakoma musa mata akan maganar zan fuskanci fushinta, shiyasa kawai nahaqura Ina qoqarin cusawa zuciyata yarinyar."

Murmushi dady yayi had'e da bubbuga bayansa sannan yace.

"Gud, kanada wacce kake so yanzu?"

"Eh dady, amma mom bata son na aureta."

"Wacece ita?, kuma meyasa bata sonta?."

"Qanwar matar ya faruq ce dady, sunanta hafsat amma ana kiranta iman, mom Bata sonta ne wai saboda ammie tunda yayarta surukar tace." Tsaki dady yayi saboda gaba d'aya alamurran hajia nafeesa ba komai acikin Inba tarin hauka da shirme ba, bata tab'a tanadar qwaqqwarar hujja cmai ma'ana sai shirme,

"Katabbata yarinyar na sonka kamar yanda kake sonta?" Dady yafad'a yana kallonsa.

"Eh dady."

"Shikenan! Koma ka kwantawarka, Kuma katabbatar kayo arwala ka kashe fitilar d'akin kafin ka koma kaji nafad'a maka."

"To dady nagode saida safe."

"ALLAH yatashemu lafiya, ubangiji yayi maku albarka."

"Amin dady" Shakur yafad'a tare da yaye bargon daya lullub'a dashi ya sauko daga saman gadon tare da wucewa toilet yana maijin wani sanyi aransa, dama duk abunda yake yiwa batool mom d'insa ke sashi, shi kuma sai yana amfani da wannan damar don ya tunzura batool taqara tsanarsa aranta yanda koda ance za'a had'a aurensa da ita bazata yarda ba.

Koda dady yakoma bai cema hajia nafeesa komai ba yayi shirinsa na kwanciya ya kwanta yana mai addua'ar ALLAH yatashesa lafiya.

Da sassafe yakira faruq qanen dr, yace yaturo masa lambar mahaifin surayya matarsa, bayan yaturo masa sukayi magana mai tsawo sannan yakashe yakira dr, shima nan sun d'an jima kafin yakashe yafad'a toilet yayo wanka.

Misalin qarfe 9:30 na safe dady yagama shirin tafiyarsa kano yashiga sukayi sallama dasu umma da ammie sannan yadawo itama hajia nafeesa sukayi sallama batare daya nuna mata komai ba, so take ta taddo masa da zancen amma ayanayin da tagansa ciki sai tad'auka haqartace ta cimma ruwa.

Koda yafito tana biye dashi ta rakoshi Dr da faruq na tsaye bakin mota suna jiran fitowarsa don tare zasu fita tawani galla masu harara aranta tana mai jin kamar takamo su tashaqe tsabar tsanar da tayi masu.

Kai tsaye gidan iyayen matar faruq suka nufa su uku lokacin mahifinta shima yakirawo 'yan uwansa su uku sun iso suka nemawa shakur auren hafsat (iman), iyayen nata sun tarbesu hannu biyu kuma sun amince da maganar don seda suka tambayeta tace eh tana sonsa sannan suka bashi ita, yarage sadaki da sa rana yarage, saida sukayi masu godiya sosai sannan suka baro gidan suna yabawa nagartar sarakanan na faruq.

A bakin titi suka ajiye faruq su kuma suka kama hanyar kano.

Suna Isa misalin qarfe uku na rana suka nufi gidan baba balarabe kai tsaye suka samu anhad'a masu 'yar qwarya qwaryar liyafa don dama yasan da maganar.

Bayan sunci sun sha sun qoshi baba balarabe ya d'auko masu zancen mahaifan little ta b'angaren mahaifinsa inda ya nuna masu bai kamata aje nema masa aureba bada suba saboda haqinsu ne, asalima sun fisu qarfi dashi, nan dai yazauna ya labarta masu duk abunda yafaru da yanda yahad'asa da dangin mahaifina nasa tacikin sirri, sun matuqar gamsuwa tare da fahimtarsa, kuma sunyaba masa bisa qoqarin da yayi inda suka d'aukar masa alqawarin cewa suma zasu riqe wannan sirrin batare da sun bari umma da Rashida sunji ba har zuwa lokacin da gaskiya zatayi halinta, anan yake sanar dasu cewa ai yariga daya fad'amasu baffa zancen yanzu haka shi little yana can tare zasu dawo dasu.

Ana kiraye kirayen sallar la'asar su baffa suka iso gidan baba balarabe, sunji dad'in yanda ya nuna muhimmancinsu acikin sha'anin tare da yimasa godiya sannan baba balarabe ya gabatar masu dasu Dr.

Yauma baffa seda yayi kuka yanata sakawa Dr albarka bisa taimakon da yayiwa Rashida da kuma gudan jininsa little alokacin da suke matuqar buqatar sa, hakama suka taru shida baffa Usman suka dinga yiwa dady godiya har saida yafara jin kunya don kusan duka sun girmesa, musamman baffa, Dr kuwa shidai mamakine ya ishesa da aka nuna masa baffa amatsayin mahaifin baban little wanda yasan ranar da sukaje qauyen shida Rashida bashine sukayi magana dashib amatsayin kakan little, asalima gaba d'aya baya cikin su biyun don haka sai yafara tunanin tabbas akwai wata aqasa acikin al_amarin Wanda su Basu sani ba, koma dai meye shi Wanda yagani tabbas yanada nasaba dasu don ga kamanninsu da shi nan, yana wannan tunanin ne suka miqe zasu tafi can gidansu batool d'in, saidai awannan karon qin binsu yayi saboda aganinsa su hud'un sun wadatar a matsayinsu na manyan iyaye agaresa.

Dady shike jan motar sai baffa Usman a gefensa, baba balarabe kuwa da baffa suna baya sannan suka bar qofar gidan tare da nufar unguwar sharad'a phase 1.

Dama tuni little ya sake kiran batool ya jaddada mata zancen zuwan iyayen nata don itama ta sanar da nata iyayen, cikin farinciki batare da wani shakku ko shayi ba taje ta iske su uncle Hassan da Hussain lokacin suna zaune tare da mahaifin nata da ko kallo bata ishesa ba a harabar gidan tasanar dasu,

Murmushi uncle Hassan yayi had'e da cewa.

"To yaushe!"

"Yanzu uncle h."

Tafad'a tana dariya tare da kallon mahaifin nata, tsabar takaicinta da irin fand'arewar data yimasa yasa yayo kanta da niyar mammaketa da sauri suka rirriqesa ita kuma taruga da gudu cikin gida.










*ALLAH KAJIK'AN IYAYENMU*πŸ‘πŸ˜­
[11/14, 22:52] Billy S Fari: πŸšΆβ€β™€οΈπŸšΆπŸ»β€β™‚οΈ *SANNU SANNU*πŸšΆπŸ»β€β™‚οΈπŸšΆβ€β™€οΈ
πŸ’Ž _Bata hana zuwa..._πŸ’Ž


_WRITTING BY:_ *BILLY S FARIπŸ’Ž*

_DEDICATED TO:_ *BLOOD SISTER'S (AMZAHFAZ)*πŸ’‹

_BESTOWED TO:_ *ZAINAB AL-AMIN (MOM NA'EEM)* AND *AMINA UBA AYUBA (OUM ASHFAQ)*πŸ’ž

*DOMIN FARINCIKINKI SISTER SADIYA ZANGO (MIEMAH)*πŸ’–

*FATAN ALKHAIRI AGAREKU MOMMAH ME NANA HAFSAT (MISS XOXO) AND MAMANA HAFSAT RANO(OUM AFFAN)*❀️

_Gaisuwar yau ta musammance zuwa gareku masoyan amana, *SADIYA ZANGO(MEAMAH), TEEMAH GABS, NUCEEY BEBEJI, MARYAM MANSUR D/WAZIRI(OUM IMAAN), AUNTY MURJANATU (JAANATU), HAIFA BASHIR, ASIYA ALIYU(UMMU SAUDA), REEDERH MALESIA, AUNTY SHAFA ABU KAURA, JIDDAH ALK'ALI, MMN SSS, KHADIJA RUQAYYA* matuqar zan d'ora alqalamina da zimmar fara rubuto ko sau dubune to tabbas bazan iya kammala saba har saina tuna daku had'e da yimaku fatan alkhairi saboda yanda akoda yaushe kuke amfani da tsadaddin lokutanku wajen bibiyar littafaina, hakan yasani jin cewa kud'in na musamman ne kuma 'yan amanata da bazan tab'a iya mantawa daku ba, Ina miqo gaisuwata had'ee da yimaku addu'ah ALLAH yacika maku dukkanin zukatanku da haske mai yawa da zai yimaku jagoranci izuwa aljannatul firdaus, INA MAKU FATAN ZAMOWA CIKIN AMINCIN ALLAH DA KUMA YARDARSA AKODA YAUSHE🀝_

Page___84πŸ’Ž

Subhanallahi Yaya wai meye haka?, Shekarunka fa jasukeyi kadena biyewa yarinyar nan saboda duk abunda tayi kaine sila kuma kai ka d'orata akai, don haka yazama dole kayi haquri da yanda halinta take ko kuma da kai har ita kudinga ba juna wahala.

"Meye laifin da nayiwa yarinyar nan da gaba d'aya take son maidani wani shashasha, meye zunubina agareta da bazata hakura da zab'inta ba tabi nawa?, meyasa?, Ko don taga na nuna mata soyayya fiye da sauran 'yan uwanta shine zata nemi tozartani da gwada mani iyakata, ni zatayiwa taurin kai da kafiya don akan wani banza dabata san ainahin ko waye shiba?, To wlh tallahi hassan nafiso in kakkaryata nazubata akwandon sharah dana aura mata wannan yaron da bayada asali."

Cikin b'acin rai uncle hussain ya sakesa daga riqon daya yimasa had'e da cewa,

"Ai shikenan, jeka gata can ka kakkaryata in kaga dama ma karabata da lumfashinta yaya, wai har kamanta lokacin da muke lusar dakai illar soyayayar da kake gwadama yarinyar nan, kamanta yanda gaba d'aya kanuna mata fifiko fiye da sauran 'ya'yanka daka haifa sai kace su bakai ka haifesu ba?, kamanta yanda kai tsaya kafad'a mana cewa babu abunda zata bid'a aduniya ka hanata shi matuqar kana raye?, To wlh anzo wajen! Saboda tu tana qaramarta kasaba mata da yimata duk abunda take so koda kuwa ba daidai bane, katuna anan cikin gidan kake nuna ba 'yan uwanta kad'ai ba hattamu dake matsayin iyayenta zaka iya haqura da duka ra'ayinmu dama naka ra'ayin kabi nata, ahaka tarayu bisa turbar da kake buqatar tarayu da ita, shine kwatsam alokaci d'aya zakace ta canza, kaima kasan abune da bazai tab'a yuyuwa ba, koda kuwa zai yuyu to bata hanyar wannan tsanar da kuma tsaurarawar da kake yimata ba, ka lallab'ata kamar yanda kayi tun farkon tasowarta wataqil ALLAH zai taimakeka tacanza koba duka ba, da kake zancen kafiya da kuma taurin kai ai jininka keyawo ajikinta badon haka ba qila data sauko tabi naka ra'ayin."

Yana gama fad'ar haka yabar wajen ya wuce part d'insa kamar zai tashi sama, hajia shafa matarsa na kitchen tana girkin abincin dare yakira sunanta da sauri tafito saboda yanda taji muryarsa cikin b'acin rai.

"Ki qara abinci saboda zamuyi baqi."

Haka kawai yafad'a yajuya yawuce d'akinsa ransa ab'ace, sosai idan batool d'in tayi wani abun yake son hukuntata amma daya tuna yanda mahaifinta yanuna masu zai iya samun matsala da kowa akanta da irin yanda ya sangartata sai yaji yakasa, saboda kwatakwata batada laifi, kome tayi shiya jawo da hannuwansa don haka yake zuba mata idanuwa matuqar abun bazai cutar da itaba don kawai yayan nasu ya d'auki darasi kuma yagane illa da kuskuren daya aikata abaya ko don nan gaba ya kiyaye.

Abba kuwa kallon uncle Hassan yayi had'e da cewa.

"Kaji me d'an uwanka kefad'a mun?, Kaji maganganun dake fitowa abakinsa akaina, meye kuskuren da nayi da zaiga laifina?, Waye baya son d'ansa?, Waye baya buqatar ririta d'ansa da kuma nuna masa gata idan hakan tasamu da zaiga laifina cikin kulawar dana bawa batool?"

"Ashsha wannan shine laifin naka yaya kai kuma ka kasa fahimta!, A al'adar malan ba haushe yarinya najin nauyin tunkarar iyayenta da maganar za'azo neman aurenta, Amma saboda sangartawar da kayiwa batool da nuna mata duk abunda tayi daidaine shiyasa bako kunya tazo kai tsaye tafad'a mana kuma agurinta wanan daidaine ba wani abuba, don haka ni atawa shawara ka lallab'a yarinyarnan hakan zai iyasa tafahimci me kake nufi."

"Au kenan kaima kana goyon bayanshi kenan?, Ya zauna yafad'a mani magana sannan kaima kabiye masa?, Shikenan naji na b'ata batool, nayi alqawarin zanyi qoqarin gyarata tahanyar zab'a mata wanda yadace da ita tayanda gobenta zatayi kyau, don haka wlh kaji narantse kada 'yan iskan da suka zo mani gida, kaje kafad'a mata cewa takirasu tasanar dasu ni mahaifinta nace kar inga kowa agidana."

Sheqeqe uncle Hassan ya kallesa kafin yace.

"Tunda kaine mahaifinta kamar yanda kafad'a mezai hana kaje da kanka ka sanar da ita, kasani muna matuqar girmamaka da kuma yimaka biyayya Amma hakan bazaisa mu walaqanta mutane ba don sunzo neman abu wajenmu tunda ba gadon iyayenmu bane, alqawari d'aya zanyi maka shine, bazamu bayar maka da 'yaka ba tunda baka buqatar hakan."

Yana gama fad'ar haka shima yabar wajen.

Safa da marwa Abba ya shigayi a qarqashin 'yar rumfar dake gefen harabar gidan tasha tayils da kujeru na alfarma, bini bini ya kalli agogon hannunsa tare da bakin gate d'in, gaba d'aya yakasa zaune kuma yakasa tsaye, yaqi komawa part d'in nasa yana dakon isowarsu, yaci alwashin ko suwaye suka zab'i maida yaron da akace shegene izuwa d'ah don a yaudaresa tahanyar aurar masa da 'yarsa sai yasasu sunyi nadamar zuwa gidan, ji yakeyi gaba d'aya baya buqatar wakilcin 'yan uwan nasa shi da kansa zaiyi abunda yake ganin shine daidai kuma shi zai sama masa salama azuciya.

Aikawa uncle Hassan yayi aka kirwo masa uncle Hussain ya fad'a masa abunda yayan nasu yace da kuma shi amsar daya bashi, shiru uncle Hussain yayi zuciya na cinsa kafin yace.

"Kace ya rantse kar wanda yashigo masa gida?"

"Eh, yanzu banma san ko meye abunyi ba.?"

"Ka qyalesa ai gidan ba shikad'ai keda shiba, sannan 'yar tasa ma da yake zance muma munada haqqi akanta don haka zasu shigo kuma tabbas dole yayi kaffara."

"A'a hussain kada kayi haka, muqyalesa mana, bana son mubiye masa har yakai ga yayi wani rashin mutunci da zai shafi ita yarinyar, saboda idan ya walaqantasu kamar ya kafa mana wani mummunan tarihine agida, mutane zasuji shakkun koma dawowa gidannan da sunan neman aure kaga kuwa maganin ayi kar afara."

"Shikenan Hassan, amma matakin da zan d'auka naqarshe kar kace komai akai, idan zuciya Yaya ke taqama da ita ai duka Abu guda yayimu dashi don haaka jeka ka shirya ance suna isowa, zansa ayi yanda yakamata."

"A'a hussain.."

"Don ALLAH katafi hassan nasan meya kamata kuma nafahimci abunda kake nufi, bazanyi abunda zai jawo zubewar kimar gidannan ba, kawai jeka ka gyara kafin su iso."

Kallonsa uncle Hassan yayi don yasan indai zuciyace to d'an uwan nasa yadama yayan nasu ya shanye, shi kanshi yanada ita amma ba irin tasu ba sai idan ankaishi bango yake nuna tashi, murmushi yayi sannan yace.

"Shikenan uban d'iya, ALLAH ya huci zuciyarka."

Dariya uncle Hussain yayi sannan yakoma part d'in nasa.

Qarfe biyar nabugewa motarsu dady natsayawa qofar gidan, Abba kuwa sai raba idanuwa yakeyi yana jiran yaga shigowarsu, abunda bai sani ba kuwa tuni Uncle Hussain yasa aka yimasu shimfid'a a qarqashin inuwar fulawowin da sukayi rassa ajikin katangar gidan daga can waje, qatuwar darduma aka shimfid'a tare da kujeru qattunan timatimai irin na sarauta d'in nan yasa aka qawata wajen dasu sannan yasa aka kai abincin aka shirya masu da lemuna da ruwan goruna masu sanyi, duk anyi hakanne ba tare da sanin Abba ba saboda ta wancan d'ayan gate d'in da ba'a fiye bud'ewa ba dake ca qarshen gidan uncle yasa akabi da kayan Kuma suma tacan sukabi suka fita, kallon wajen uncle Hassan yayi ya kwashe da dariya had'e da cewa.

"Banda fitina irin na yayanmu da rufin asirinmu zai samu wannan tonon silili awaje kowa sai yagama da ganinmu, gaskiya wannna abun baiyi dad'i ba duk da dai konan d'in ba laifi ma fake da sunan shan isaka."

Murmushi uncle Hussain yayi had'e da cewa, "Ai duk laifinka ne da kake neman abisa ahankali, wlh indai Yaya ne sai anyi wuta da wutane dashi sannan za'a daidaita, Ina girmamawa awannan sha'ani ai andaiji kunya in anjita."

Haka suka yita firarsu suna dariya har zuwa yanzu dasu dady suka iso, cike da girmamawa suka taso suka tarbesu tare da yimasu iso zuwa inda shimfid'ar take, yanayin su baffa da baba balarabe da suka gani baisa sukaji komai aransu ba balle surena arziqinsu sukuma hakan da suka gani an ajiyesu awaje Bai kawo masu komai arai ba, dady kad'aine ransa yaso bashi wani abu amma sai ya basar, cikin mutuntawa da karrama juna suka gaggaisa kafin uncle Hussain ya mammatso masu da kayan abincin yana fad'in.

"Bisimillah."

"Murmushi baffa yayi had'e da cewa Alhamdulillah, mungode sosai amma aqoshe muke."

"Haba alhaji ai ba'ayi haka ba ko ruwane yakamata kusha kafin mushiga maganar abunda ya taramu anan, akace baqonka ai annabinka ko kuwa?" Uncle Hassan yafad'a duk sukasa dariya.

Dady yafara d'aukar ruwa ya tsiyaya a cup tare da lemu yasha sannan suma su baffa suka sha, hakan kuwa baqaramin dad'i yayiwa su uncle Hussain ba.

Cikin tausasa murya da girmamawa duk da kuwa dady ya girmesu yayi masu bayanin abunda ke tafe dasu cewa sunzo nemawa d'ansu ne izinin neman auren 'yar wajensu batool daya had'u da ita acan gidansa lokacin da taje hutu wajen matarsa hajia nafeesa, saboda bawani sanin dady sukayi sosai ba suna dai yimasa kallon sanine yasa sai alokacin suka gane cewa ashe shid'inne mijin hajia nafeesa 'yar qanwar tasu da suke qoqarin tunano inda suka san fuskarsa.

Bayan yagama yimasu bayani uncle Hassan ya sauke ajiyar zuciya had'e cewa.

"To masha ALLAH, kaga ashe kai surukin mune, munata faman laluben inda muka sanka duk ta dalilin rashin qarfafa zumunta, lokacin da kuka iso naso na ganeka amma a Ina shina manta tinda andad'e ba'a had'u ba, zumuncinne yanzu sai ahankali mutane bamu cika bashi muhimmanci ba."

'Dan russuna kai dady yayi had'e da cewa.

"Wlh kuwa, abubuwane da sukayi yawa gashi ba gari d'aya ba saidai ayita haquri."

"Eh da haka kuwa, ALLAH yayi taimako."

"Amin ya rabbi alhaji."

"To alhamdulillah munji abunda ketafe daku kuma munji dad'i da har ALLAH yasa d'anku yaso jininmu, kaga zumunci zai qara qarfafa idan ALLAH ya daidaita abun, saidai wani hanzari ba gudu ba, kinsan ita maganar aure anfiso ayita bisa kan gaskiya da gaskiya, ni da kuka gani tare da d'an uwana annan, qannene ga mahaifin ita wannan yarinya da d'anku keso, ita kuma matarka ya nuna dady, 'yace ga qanwarmu kasani uwa d'aya uba d'aya duk muke ba inki bawai, don haka bazamu b'oye maku gaskiya ba maganganu sun zo mana ko ince sunzo Kai tsaye ga kunnuwan mahaifin yarinyarnan cewa yaronku bayada asali wanda hakan yasa mahaifinta har yayi mata tsakani dashi bayan yasa anyi masa bincike acan garin antabbatar masa da cewa yaron nan bayada uba, kuyi haquri kada kuga nayi maku cin fuska, muna so musan sahihancin maganar ne don shi yayan namu yakafe akan bazata auresa ba sai gashi kuma yarinyar ta sanar damu zancen cewa zakuzo nema masa aurenta, hakan yasa mukayi tunanin zaunawa musaurareku don jin gaskiyar zancen."

Wani irin dimmmmm...baffa yajiya aransa duniyar ta shiga jujjuya masa saboda kalmar da yaji cewa wai jikan nasa shegene bayada uba, badon ALLAH yasa yana zaune bane to da Babu abunda zai hanasa fad'uwa adaidai wannan lokacin, wasu zafafan hawayene suka zubo masa a fuska da sauri yasa hannu yagoge yanajin wani qunci tare da takaicin d'ansa aransa.

Dady kuwa gabansa ne yafad'i jin kalmar da duk duniya mutum d'ayane yaji nayiwa little ita wato matarsa hajia nafeesa wacce baya tantama akan komeye yafaru itace ta assasashi.

Ganin duka yanayin da suka shiga yasa uncle Hussain jin badad'i aransa Amma ya za'ayi dolene suyi haka don susan yanda zasu kamo bakin zaren, cikin tausasa kalamansa yace.

"Ina nemawa d'an uwana dani kaina yafiyarku idan maganganunsa sun tab'a maku zuciya, har ga ALLAH ba muna nufin zamu yimaku walaqnci bane don kunzo neman alfarma wajenmu, a'a kuyiwa maganar kyakkyawar fahimta akan muna so kai tsaye mu binciki sanin kowaye yaronku tawajenku saboda munyarda daku, kuma Ina zaton ko a misulunce hakan ba laifi bane, idan bakwa buqatar hakan kuma to muna baku haquri tare da cewa kubamu d'an lokaci kafin muje muyi bince akai."

Da sauri baba balarabe yace.

"A'a babu buqatar hakan, asalima godiya yakamata muyi maku dakai tsaye kuka fuskancemu da wannan magana batare da kunje waje wurin neman sanin gaskiyarta ba, ni sunana malan balarabe qane ga mahaifin uwar yaron, Ina zaunene awani qauye da ake kira yarimawa, wannan kuma ya nuna baffa sunansa malan Idris Aliyu wato mahaifin baban yaron tare dashi kuma akwai qanensa malan Usman Aliyu, su kuma suna zaunene a qauyen bebeji, shi ya haifi uban wannan yaro da ake shegantawa ni kuma amatsayina na qanen mahaifin mahaifiyar yaron ni nabada aurenta a hannun wannan qanen mahaifin babansa bisa sadaki naira dubu hamsin, zaku iya zuwa atsakankanin wud'an nan qauyukka guda biyu kuyi bincike akan munda maganar alaqarmu don tabbatar da hakan."

A yanayin da yake yimasu bayani duk daqiqancin mutum dole yafahimci cewa yana fad'in gaskiyar zancene daga qarqashin zuciyarsa.

A hankali baffa ya d'ago kai tare da fara basu labarin dalilin da yasa aka jingina jikan nasa da cewa shegene, tun daga farko har zuwa qarshe batare daya b'oye masu gaskiya ko d'aya ba har yana zubar da qwallah, dady me ya d'ora masu cigaban labarin daga qarshe yakira Dr. yace yazo maza maza yana son ganinsa tare da bshi address d'in inda zai iskosu, ba'a jima ba saiga Dr ya iso dady yace ya sanar dasu kowaye little da mahaifiyarsa, kallonsu yayi d'aya bayan d'aya yace

"Meke faruwa dady?, Bazasu bashi auren tabane har sai an bayyana masu abunda yafaru akan mahaifiyarsa?, Ganinku bai isa ya gamsar dasu ko waye Nuraddeen d'inmu ba?, Idan ko hakane inaga babu buqatar hakan saboda babu yaddar da zata jawo auratayya a tsakani."

"Ya isa, kayi abunda nace maka." Dady yafad'a in a serious tone, ganin babu wasa a fuskarsa yasa yafara labarta masu halin daya tsinci mahaifiyar little har zuwa lokacin data had'u da iyayenta agidan mahaifinsa, anan dady yafad'a masu yanda akayi har yasan mahaifin Rashida wato kakan little, lamba da address d'in abokinsa da marigayi ke karb'ar takalmi awajensa Wanda nanne yahad'u da baba yabasu yace suje wajensa suqara yin bincike akai.

Gaba d'aya duk inda ilahirin jikin uncle Hassan da Hussain yake saida yayi sanyi, sosai kunya da dana sanin tambayoyi da kalaman da sukayi masu tarufesa, sun matuqar tausayawa rayuwar baffa tare da jinjinawa qarfin imaninsa haka sun girmamawa karamci irin na surukin nasu wato dady da d'ansa, da za'a samu irin wud'annan mutanen aduniya to tabbas za'a zauna lafiya cikin wadatuwa da ni'imar ALLAH.

Muryar baffa Usman suka jiyo yana fad'in.

"Little dake son yarinyarku ba shege bane kamar yanda kuka jiyo daga bakin qananun mutane dake yiwa alamari hawan qahura, su zauna akai suyi sharhin abunda basuda masaniya akai, mune iyayen babansa kuma da izininmu yaje karatu waje, qaddarawar ALLAH da kuma jarabtawa da wanzuwar alqalamin qaddara akan yaronsa tahanasa dawowa qasarsa zaku iya zuwa can ma'aikatar ilimi a b'angaren qananan malamai dake da rauni data taimaka musu ku bincika don kutabbatar da hakan domin ita taturasu qasar, bamu fidda rai da dawowar mahaifinsa ba a kowane lokace kmar yanda bazamu dena cigaba da rayuwarmu ba har sai lokacin da ALLAH ya dakatar mana da ita, Kuma in Sha ALLAH kusa ko nesa zai dawo garemu don tabbatarwa da duniya cewa d'ansa ba shege bane da yardar ALLAH."

Cikin sanyinyin murya uncle Hussain yace.

"Kuyi haquri, kuyi haquri, shikad'ai zamuce, damu bawai mu muka sheganta yaronku bane, kawai munfad'i abunda mukajine daga bakin wasu, amma yanzu mun gamsu da bayaninku d'ari bisa d'ari, dama haka ubangiji yace,
" _yaa ayyuhallazina amanu injaa akum fasiqun binaba'in fatabayyanu antusibu qauman bijahalatin fatusbihu ala maa fa'altum nadimuun_" ma'ana
" _yaku wud'anda kukayi imani!, Idan fasik'i yazo maku da wani babban labari, to, kunemi bayani, domin kada kucuci wasu mutane acikin jahilci, saboda haka ku wayi gari akan abin da kuka aikata kuna masu nadama_,
Shiyasa dashi yayan namu yayi nasa binciken mukaga yadace mu tuntub'eku da maganar kamar yanda ALLAH ya umurta don kaucewa aikata abunda zamuzo muyi nadama akai kuma alhamdulillah bamu d'auki wani matakiba koyin abunda zaisa muyi nadamar abunda muka aikata, don haka a matsayinmu na iyayen batool mun ba Nuraddeen dama yaci gaba da nemanta har zuwa lokacin da zamu sake waiwayarku akan batun aurensu,"

Cike da farinciki baffa ya d'aga hannu sama yayiwa ALLAH godiya sannan suka had'a baki shida dady dake murmushi sukace.

"Bakomai mungode, mungode sosai ALLAH yatabbatar da alkhairi."

Nan suka shiga musabahar hannaye kowanensu fuskarsa na nuna jin dad'in yanda abun yakasance, suna qoqarin tafiya aka kira sallar magrib, don haka uncle Hassan yaroqesu akan subari sai sunyi sallah sunci abinci sannan sutafi, haka kuwa akayi anan saman dardumar baba balarabe ya jasu limanci sukayi sallah sannan sukaci abincin, cikin qanqanen lokaci suka saba da juna har sukayi musayar lambobi sannan suka wuce cikin yaba nagartar juna da fahimta.

Suna wucewa Abba na isowa wajen kamar zai tashi sama, kallo d'aya sukayi masa dariya ta soma kuccikke masu da sauri suka gintse,

"Nagode da maidani d'an iska da kukayi a matsayina na yayanku, wato ni Ina can zaune ina jiran isowarsu ashe ku har kunyi mani yanda kuke so sai dai cikin anguwa atareni ana tambayar halama yau baqi nayi?, Yau kun nuna mani cewa ba bakin komai nake ba agareku kuma ban

Please Login or Register in order to submit comment