Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kuma duk hassadar mai hasada bai isa ya canza abunda ALLAH ya qaddaro ba sannan shi son kai baya tab'a kai mutum ga nasara, sannan kuma tabbas shi naka sai naka amma dad'in zama sai bare, yarinya dai tashigo gidan mijinta kuma ko ba'aso dole akirata da matar Nuraddeen, uwar gidansa kuma uwar 'ya'yansa suruka a wannan gida, masu had'e had'e da kuma qulle qulle sai su canza dabara domin ruwa kam ya riga daya qarewa d'an kada..sai ayi sauri acanza dabara, yarinya dai ALLAH ya mallaka mata Nuraddeen a matsayin miji domin shi tariqe tun farko kuma shi zai tayata fad'a su ko 'yan baqinciki sai dai su mutu don nagaba yariga da yayi gaba."

Tana gama fad'ar haka tawuce d'akinta tana jin wani sanyi aranta, koba komai tasamu zuciyarta ta rege nauyin da tayi mata akan maganganun da suka ta cab'a mata ita da Yaya hawwa.

Wani irin mugun ashar matar Baffa Ali ta lailayo mata had'e dayin kukan kura tanufi wajen qofar d'akinta tana rafkar mata gambu.

"Bilki, Bilki, Bilki tsakanina da ALLAH tun wuri ki kama kanki ko in tata maki rashin mutunci, ki kama bakinki kafin inyi maki wankin babban bargo agidannan, yo da kike zancen ruwa ya qarewa d'an kada ai bakiga k'arshen wasan ba, in dai nice ruqayya matar Ali gadanga tunda kika shigarmun hanci wlh saina nasa zaman gidannan ya gagare ki dake har 'yar koron taki da aka kawo, kwad'a yayyiyar banza da wofi anga yarinya masu maiqo shine za'a maqale mata, to daga ke har ita sai nasa kun kuka da kanku."

Tana gama fad'a ta banka gambun qofar da qarfi cike da jin haushin rashin tanka mata da batayi ba tajuya tabar wajen, Yaya hawwa najinsu daga kwancen da take taja tsaki had'e da cewa.

"Sakarkarin banza duk kuyi ku gama zan dawo takanku, don da d'ai d'ai zanyi maganinku acikin gidannan."

Ita dai Rashida tun tana kukan har ta dangana ga ALLAH tayi kwancen tana tunanin wannan sabuwar rayuwar da zata fara a d'aya b'angaren tana sauraren firar dasu salame da kareema keyi, muneera ce tafad'o cikin d'akin ko sallama babu tayi tsaye qiqam tana raba idanuwa batare da takalli wud'anda ke wajen ba da alama itama rashin mutuncin tazoyi saboda yanda take bud'ar hanta, sudai su salame na kallonta basuce da ita uffanba ta rab'a tagefensu tanufi uwar d'akin, kallon kareema salame tayi ta d'auke fuskarta tana kallon muneera dake qoqarin hankad'a labulen ta d'aure fuska had'e da cewa,

"Ke malama Ina zuwa?"

Juyowa tayi cikin ba'acin rai itama had'e da cewa "to sa'idanawa masu barci da ido d'aya Ina ruwanku da inda zani, Ina dai amaryar nan ba 'yar uwarku bace balle kuce zaku hanani shiga"

"Bashi aka tambayeki malama ba, amsa zaki bamu ba rashin kunya ba don kinsan nan gidanta kika zo" kareema tafad'a a tsattsaye, tsaki muneera tayi had'e da kutsawa tashiga cikin d'akin Rashida na kwance saman gado fuskarta lullub'e da mayafin da aka rufo mata tasa hannu ta yayeshi da qarfi, da sauri Rashida tamiqe zaune tana kallon muneera dake riqe da mayafinta data cire, idanuwa muneera ta qura mata tana kallon gashin kanta daya zubo har gadon bayanta sanadiyar jawo mayafin da tayi ribon d'in ya cire, kyakkyawar fuskarta ta qurawa Ida kafin can kamar an tsunkureta ta zabura had'e da cewa,

"Au yihakuri fa na manta ke amarya ce Saida lallab'awa.." mere baki tayi sannan tafara takawa tana qarewa d'akin kallo kafin ta maido hankalinta gareta,

"Dama kece ya nurana keso? kece ya zab'o a matsayin mata bayan yasan Ina qaunarsa, dama kece kika zamo katangar data shiga tsakanina dashi Kuma har kika datsemun duk wani mafarki da kuma burin mallakarsa dana dad'e inayi, kika wargazamun farinciki tare da sani zubar da k'wallah acikin kowane dare?, Hmmm to kinyi kuskure yarinya a wud'annan qananan shekarun naki baki kai matsayin da zaki mallaki ya nura naba kuma na hak'ura, domin na d'au alwashin shid'in mallakina ne ni kad'ai, kid'auka wannan auren jeka nayi kane kukayi saboda dole kirabu dashi ko kina so ko bakyaso, mallakina ne shi Kuma ki kalleni da kyau kigani nice daidai shi saboda nid'in 'yar uwar sace kuma jininsa don haka d'an uwa sai d'an uwa badai bare ba."

Taqarasa maganar tana wani kallon sama da qasa irin ita wayayyiyar nan , sai alokacin Rashida ta d'ago kai cikin mamaki tana qarewa muneera kallo wacce tun shigowarta data kalleta ta aza itama cikin matan gidanne saboda yanda taganta ajeme cikin wata kod'ad'diyar atamfa wacce duk da itama a qauye take bazata iya ko gugar leda da ita ba, sak kamar muneera irinta 'yan matan qauyennan ne da suka jima basuyi aure ba ga wasu uban qassan wuya da suka taso mata fuska cike da jar foda, kallo d'aya zakayi mata kasan cewa ba yarinya bace zata kai shekaru 20 aduniya ga matsalar qauyanci da rashin wayewa da suka taru suka sake jemeta waje d'aya sai kace wacce tashekara aru aru d'in nan, watanni ne tsakaninta dasu kareema wanda hakanne yasa babu wata girmamawa tsakaninta dasu sai reni, shiyasa da sukayi mata magana bata sauraresu ba hakan yasa salame tamiqe taje d'akinsu ta d'auki wayarta takirawo Nuraddeen ta sanar dashi abunda ke faruwa dama yana bakin gida baiyi nisa ba sai gashi ya shigo da sauri, yana shiga kareema na qoqarin shiga uwar d'akin saboda yanda taji tana yab'a mata maganganu da sauri yariqo hannunta yace tawuce, abakin qofar shigowa taci karo da salame tadawo zata shiga tariqe hannunta tana fad'in.

"Muje salame ai yayan yadawo, barta dashi." Wucewarsu d'akin mahaifiyarsa da tagama had'a masu 'yan abubuwan da zata basu tana fad'a suzo suwuce gidajen mazansu dare yayi don har ankira sallar isha'i, nan suka fara bata labarin abunda kefaruwa tace.

"Hmm! ALLAH dai ya kyauta, Amma ni wlh har yarinyar nan tafara bani tausayi, koni nan dana girmeta nesa ba kusa ba ya naqare da matsalar Yaya hawwa da ruqayya da kuma rashin kunyar yaransu inba Nuraddeen da Yusuf ba, sukad'aine nake jin sanyinsu amma kaf gidannan babu wanda keda ragi, sudai iyaye kishi suke dani gashi kowacenmu da mijinta balle ace ai saboda haka, sukuma yaran iyayen ke lalatasu shiyasa Amma banda haka har ina za'ace muneera ta isko matar yayanta tana yimata rashin kunya, zumuncine da yariga ya lalace saidai ALLAH ya kyauta."

"Hakane inna, amma kema da alifinki? Kidena biye masu balle shiga harkarsu, inaji d'azu kin dawo kina maidawa Inna ruqayya da maganganu ai kinga hakan bai dace ba, ka kyale mutum duk abunda zaiyi tunda dai kasan adoke bai isa ya dokeka ba amma saikiyita biye masu ana fitina." Kareema tafad'a ranta a d'an b'ace, shiru Inna Bilkisu tayi tana nazarin kalamanta don tasan gaskiyane tafad'a kawai dai abun da ciwone shiyasa bazaka iya haquraba wataran, muryar salame taji itama tana fad'ar.

"Eh Inna ALLAH gaskiya kareema tafad'a don ALLAH kidena biye masu, kinsan abun fad'i agarinnan baya k'arewa, kuma mu kece mutuncinmu da kimarmu agidajenmu, da wani abun yafaru agidannan akaji dasa bakinki ba zamuji dad'i ba, don ALLAH kiqara haquri dasu wata rana sai labari"

"Shikenan, ALLAH yaganar damu kutashi kutafi" tabasu amsa atak'aice.

Acan sashen Nuraddeen kuwa tsaye yana qoqarin shiga yaji maganganun muneera sun dakar masa kunne a lokacin da take cewa d'an uwa sai d'an uwa badai bare ba da sauri ya qarasa shigi ciki tare da fizgota ya jefota falo yana fad'in "uban waye ya fad'a maki d'an uwa sai d'an uwa, itama yanzu 'yar uwace awajenmu tunda na aurota na kawota a gidan nan don haka maza kifice kibani waje ko in tattaka ki awajennan wawiya kawai da bata iya magana ba" turo baki tayi tana susar kai had'e da cewa,

"Kai ya nura nizaka yiwa walaqanci akan wannan 'yar yarinyar.." kanta yayo da gudu tafita ta tsaya bakin qofar d'akin tana cigaba da fad'in

"Wlh ALLAH ya nura ni bazan yarda ba ai kasan ina sonka sosai shine kaje ka auro wannan abar.." Bata rufe baki ba cikin tak'a biyu ya cimmata a bakin qofar d'akin had'e da sakar mata wani mugun rank'washi akai, ihu ta saka tare da dafe kanta tabar shiyar aguje tana kuka, rumfar d'akinsu ta shige tafad'i qasa tana murje murje da qafafuwa tana wayyo Inna zai kasheni, aguje tafito d'akin tanufi wajenta yanajin haka ya koma Uwar d'akan Rashida na zaune a gefen gado kanta qasa idanuwanta na zubar da hawaye, durqusawa yayi a gabanta tare da tara hannusa hawayen dake neman saukowa daga idanuwanta suka sauka akai, cikin rashin jin dad'in abubuwan da suka faru yace,

"Habibty kuka kikeyi?" Shiru tayi tare dasa hannunta akan hanci taja majina sanna a hankali ta d'ago kai tana kallonsa, ganin yana qoqarin saka idanuwansa acikin nata yasa tayi saurin maida kan qasa, magana yaci gaba dayi cikin tattausan lafuzza,

"Habibty kidena wannan kukan bana so, akwai basosa masu girma da kike bina wajen rarrashin zuciyarki daga abubuwan da nine silar data b'aci har ta tinzira kyawawan idanuwannan naki fitar da wud'annan tsadaddin wayen, kiyimun afuwa kada kisa zuciyata tayi mani tsattsauran hukunci akan haka, kinfi kowa sanin tarin qaunar da nakeyi maki azuciyata saboda haka gada kibari shaid'an da sharrin zuciyar wasu yasa maki kokwanto ko wani shakku akaina, muneera yarinyar baffa Ali ce, tana matuqar sona amma ban tab'a jin qaunarta azuciyata ba shiyasa tazo tana maki wannan haukar, kiyi haquri daga yau nayi maki alqawarin bazata sakeba kinji?."

Saida ta share hawayen da suka jiqa mata fuska tana sake jan majina sannan tace

"Amma meyasa ka aureni bayan kasan tana sonka.?"

"Saboda ke kad'ai nakeso habibty, ke kad'aice keda mallakin dukkanin wani sansani dake cikin zuciyata, gangar jikina, zuciyata da Kuma rouhina duka mallakinkine babu wani qanqanen fili daidai da k'warar zarrah da zan iya baiwa wata aduniya, Wannan dalilin shiyasa ban aureta ba."

"Amma ai 'yar uwarka ce, inaga kamar ita tafi dacewa ka aura." Murmushi yayi tare da kamo hannuwanta biyu ya riqe yana murzawa a hankali yace.

"Idan ita 'yar uwatace ke Kuma rayuwa tace habibty, shin da d'an uwa da rayuwa wayafi dacewa ace mutum yariqa da kyau da kuma muhimmancin da zai zamo masa abokin zama"

"Rayuwa mana"

Ta furta ahankali tana murmushi, murmushin shima yayi had'e dasa yatsa ya lakutar mata hanci yana fad'in

"Gud gel" Da sauri tasa tafin hannayenta tarufe fuskarta, "yawwa bari naje nadawo yanzunnan kinji habibty, kada kisake kuka daga wannan lokacin saboda yau ranar farinciki ce agaremu."

Kad'a masa kai tayi sannan yafice daga d'akin bayan ya d'auki makullan shiyar tasa dake gefen bedside d'inta, yana fita yajawo qofar yasa makulli had'e da juyawa zai bar gidan, yanaji Inna ruqayya matar baba Ali na zage zage harda fad'in.

"Lallai nura ya lalace yanzu ya dakeki akan bare, kina 'yar uwarsa zai walaqantaki akan matarsa lalle dole Yaya hawwa tasan abunyi, ke ya dokeki?"

Tasake nana tawa tana d'agowa muneera kanta, murmushi yayi tare da kad'a kai sannan yawuce abunsa, ita kuma tab'are baki tare da nunawa inna ruqayya tsakiyar kanta,

"Yishiru taso muje wajen yaya hawwa, wlh yau sai ranar nan tazamo masu ranar bak'inciki, yishiru nace maki" taja hannunta suka nufi sashen Yaya hawwa lokacin tana zaune bisa abun sallarta Bata dad'e da gamawa ba, kukan muneera da taji yasa yasa tayi tsaki tare da ajiye tasbahar hannunta gefe kai kace tasan ALLAH tana tofe addu'a had'e da shafewa a fuska.

"Ke.ke. lafiya aka zomun qofar d'aki ana mani reren kuka sai kace munafukar amarya!." Tafad'a tana lunke sallayar had'e da komawa saman gadonta zata kwanta,

"A'a Yaya ai kwanci bai ganeki ba saboda waccan itace munafukar amaryar da naji kina fad'i, fisabillahi ace daga kawo yarinya yau har tajawa yarinyarnan duka awajen d'an uwanta don tana muna fuka...zonan nuna mata inda ya dokeki muneera don bazan yarda ba."

"To sakaryar uwa mai malalaciyar 'ya yanzu akan d'an rank'washin da yayi mata akai zaki zomun kawo qara don rashin mutunci ko nace takakka."

Yaya hawwa tafad'a tana kallon Rashida da tawani duqo Kai tana nuna mata da yatsa tanaci gaba da reren kuka "ke dallah rufemun qaton bakinnan naki kamar rijiya kona ci ubanki, ca nake uban waye yakaiki shiyarsa har ya rankwasar maki kai." turo baki tayi tana susar kai had'e da cewa.

"To ba amaryar naje gani ba, shine nake jamata fad'amata ni 'yar uwarsa ce Kuma ni nake sonsa..."

Bata k'arasa ba Yaya hawwa ta kwatseta tana fad'in "maza fitarmun d'aki shashasha mai gwalmammin qafafuwa ke kuma da bakisan abunda kikeyi ba kika kwasota kuka iskeni ko yanayin da nake ciki bakya tunani ke tama 'yarki kikeyi, to idan kinfita kijamun qyaurena zanyi lokacinsu su kuma."

"Amma Yaya hawwa ya zakiyi mani haka?"

"Kije kafin dukkanin damuwata taqare akanki rakkiya."

Afusace tafita tare da rafko qofar d'akin tana suruttai jar ta iso shiyarta, tun tana tsammanin wani zai tankata har tagaji tahaqura saboda rashin samun wanda ya kulata.

••• ••• •••
Acan b'angarensu umma da baba kuwa tun cikin mota yaya Yaya maryam ta gargad'i kowa akan kada atada zancen abunda yafaru saboda kada atayarwa mahaifiyarta da hankali, haka da akazo qofar gida saida tasake gargad'insu, kasancewar itace babba yasa kowa kama bakinsa aka shiga ana fatan Allah yasanya alkhairi, aunty marwiyya kuwa da zata tafi Saida tacewa umma "to aunty bawai kinnrabu da 'yarki ba Kuma shikenan, a'a tashi tsaye zakiyi wajen yimata addu'a da nema mata kariya wajen ALLAH daga sharrin miyagu da mahassada." Gaban umma ne yafad'i tace.

"Marwiyya injin dai ko lafiya kika fad'i haka.?"

"Lafiya klw aunty kinsan dai halin gidan yawa dole baza'a rasa gutsiri tsoma aciki ba, amma babu komai." Wata ajiyar zuciya umma ta sauke duk da dai bata natsu da amsar da tabata ba had'e da cewa.

"Shikenan marwiyya, Allah yatsare da tsarewarsa amma addua'a dama ai baza'a dena ba, ngd sosai Allah yabar zumunci, ki gaida mun da alhaji."

"Amin aunty zaiji in sha ALLAH, ALLAH yahutar da gajiya."

"Amin seda safe a gaida yara." Tunda tafita umma taji ta kasa samun natsuwa har baba yadawo, cikin gajiya had'e da nuna kasalar dake tattare dashi yafad'a gefen gado yana fad'in.

"Wayyo ni bawan ALLAH." Murmushi tayi jiki a sanyaye had'e da mik'ewa takoma ta gefensa ta zauna tana d'an mammatsa masa k'wandunansa,

"Sannu da hidima malan."

"Sannu mamn Rashida ya gajiyar taku hidimar.?"

"Alhamdulillah, saidai Ina matuqar kewar yarinyata sosai."

"Naga hakan atattare dake amma ya zamuyi tunda ita mace dama 'yar gidan wani ce, ni kaina ina kewarta sosai, ki kwantar da hankalinki addu'armu kawai itace ubangiji ALLAH yabasu zaman lafiya."

"Amin ya gaffar."

Tafad'a tana goge 'yan qwallan da suka zomata.

••• ••• •••
Nuraddeen nafita yanufi wajen masu saida naman kaji dana rago ya siyo namansa na kaza sannan yasa akayo masa d'aurin naman rago guda biyu, da gorar fresh yaghouth guda biyu, uku wajen baffa yanufa ya kaimasa qulli d'aya sannan yanufi sashen Yaya hawwa bakinsa d'auke da addu'a, tura gambun yayi ahankli daga can kwance tace

"Waye?"

"Innar mu nine yafad'a yana qarasowa cikin d'akin, gefe ya zauna tare da gaisheta ta amsa daga kwancen da take batare da ta taso ba, shiru yayi na mintoto kafin yace

"Innar mu ga wannan?" Ya ajiye ledar abakin gadon,

"ALLAH amfana." tafad'a tana qyaren d'ayar ledar dake hannunsa,

"Saida safe innarmu." Yafad'a tare da miqewa ya nufi qofar fita, har ya aza qafarsa tace,

"Miye wannan a d'ayar ledar?"

Shiru yayi yakasa Bata amsar don baisan me zaice mata ba,

"Dawo itama ka ajiye."

"Innar mu.."

"D'auka duka biyun ka b'acemun da gani" tafad'a a fusace, cike da mamakin mahaifiyar tata ita dako bud'a abunda ya kawo mata batayi ba amma tace a ajiye mata duka, duk ya zatayi dasu, dawowa yayi ya ajiye ledar sannan yace.

"Kiyi hak'uri innar mu seda safe" sannan yafice kamar zaiyi kuka, gashi gaba d'aya duka kud'in ya kashe naira d'ari biyu kacal ta rage masa, tsaye yayi bakin rumfar yana tunanin yanda zaiyi ya samu wasu kud'in gashi abokanansa duka sun shige Kuma bazai iya iske baffa yace masa yabashi kud'i ba bayan duk wannan jidima daya yimasa, yanke shawarar zuwa ya siyo naman d'ari biyun yayi ko kuma idan abule Mai naman ya amince ya karb'i bashi har gobe don bazai iya koma mata babu komai a hannu ba, daidai ta wajen d'akin baffa zai wuce yaji yakira sunansa, shiga yayi had'e da cewa.

"Gani baffa lafiya."

"Lafiya klw Nuraddeen, wai wannan tsumuiniyar da kakeyi ta lafiya ce kabaro yarinyar mutane ita kad'ai zaune, daga Ina kake yanzu kuma Ina zakaje?." d'an sosa kansa yayi had'e da cewa,

"Daga wajen innar mu nake baffa yanzu zan dawo bajimawa zaniyi ba." Yaqare maganar yana kallon agogon hannunsa saboda lokacin tashin abule ya kusa, daga cikin idanuwansa da Kuma yanayinsa baffa ya fahimci komai, aransa ya tabbatar da cewa Yaya hawwa tayi tsiyar don zata iya komai don ta quntata masu awannan ranar, "tashi katafi" yafad'a yana mai addu'ar ALLAH yaganar da ita, har zai fita sai Kuma baffa yace,

"Yawwa Nuraddeen zo d'auke ledar nan naman nan yayimun qarfi bazan iya ciba."

"Amma baffa mai taushi nace yasa maka bansan ya akayi yasa mai qarfi ba."

"To nidai naci d'aya hakanan ALLAH yayi albarka d'auka katafi dashi." d'auka yayi don yasan halinsa baya son gardama yaji yace.

"Had'a da madarar nan tayimun sanyi sosai naga har qanqara gareta, gobe kasiyomun fura da nono nafi gane masu."

Shiru Nuraddeen yayi don yagama fahimtar mahaifinsa ya gano komai shiyasa yayi haka,

"Baffa ka ajiye ko zuwa gobe sai asake dafa maka, ita madarar Kuma dama kamar nono take tahuce sai kasha."

"A'a d'auka tafi dasu nace maka" dole ba yanda zaiyi ya d'auka had'e da yimasa saida safe ya fice, baffa na kallonsa ya koma cikin gida batare da ya fitar daya tashi yiba, murmushi yayi yace, "ALLAH ya kyauta sannan ya komawarsa ya kwanta, sashensa yabud'e ya shiga tare da karanta addu'a ya rufe.

Koda ya shiga ya tarar har tayi bacci ya ajiye ledar hannunsa had'e da nufar inda take kwance da alama sallolin magrib da isha'i tagama bacci ya d'auketa, hannuwansa yasa ya tallabota tare da cire mata hijabinta ya dinga hura mata iskan bakinsa a fuska, ahankali tafara bud'e idanuwanta suka sauka saman fuskarsa ai kamar wacce aka mintsila tayi saurin zamewa daga hannunsa tana tattaro hijabinta tana rufe jikinta, murmushi yayi daga duqen da yake tare da cewa "tashi muje ki wanko bakinki a toilet." Yaqare maganar had'e da mik'ewa ya riqo hannunta suka nufi toilet d'in tana biye dashi tana kallonsa, bata tab'a kula da kyan da ALLAH yayi masa ba sai yau...








*ALLAH KAJIK'AN IYAYENMU*👏😭
[8/17, 10:19] Billy S Fari: 🚶‍♀️🚶🏻‍♂️ *SANNU SANNU*🚶🏻‍♂️🚶‍♀️
💎 _Bata hana zuwa..._💎


_WRITTING BY:_ *BILLY S FARI💎*

_DEDICATED TO:_ *BLOOD SISTER'S (AMZAHFAZ)*💋

_BESTOWED TO:_ *ZAINAB AL-AMIN (MOM NA'EEM)* AND *AMINA UBA AYUBA (OUM ASHFAQ)*💞

*DOMIN FARINCIKINKI SISTER SADIYA ZANGO (MIEMAH)*💖

*FATAN ALKHAIRI AGAREKU MOMMAH ME NANA HAFSAT (MISS XOXO) AND MAMANA HAFSAT RANO(OUM AFFAN)*❤️

Page___19💎

Cike gidan yake maqil da 'yan uwa da abokanan arzik'i na nesa dana kusa da suka zo taya umma da baba murnar aurar da 'yar tasu tilo, duk wanda ka kalla awajen kasan cewa cike yake da tsantsar farinciki saboda yanda fuskokinsu ke d'auke da annuri anata gudanar da buki wan shagali.

Fuskar baba cike da fara'a ya shiga cikin gidan bakinsa d'auke da sallama yana rarrab'awa ta gefe gefe saboda yanda gidan yacika maiqil da 'yan buki sai faman shiga raha akeyi wasu na shiga wasu nafita, duk inda yabi sai faman gaishesa akeyi ana tayashi murna tare da ALLAH sanya alkhairi, da qyar ya samu ya shiga ciki had'e da nufar wani d'aki da suke ajiye kayayyaki aciki yasa wata tobashiyarsa ta kirawo masa umma dake can tsakar gida tasha adonta cikin wani had'ad'd'en leshi wanda saika duba da kyau zaka iya gane itace, yajima zaune cikin d'akin yana tunanin shikenan yau zai rabu da 'yarsa tilo da yakeji har cikin qoqon ransa kafin umma tasamu takuccikke daga baqin dake dad'a shigowa tanufo inda take, a jigace tashigo cikin d'akin tana fad'in, "ai sai kuyi babu wanda zan sake d'ebowa abinci in zaku tashi kuje kud'ebo da kanku ku tashi, ai Kuma 'yar takuce bani kad'ai nahaifeta ba balle kubarni da aiki, don haka ni nagaji bazan qara yimaku wani abunba, shikenan daga kara saiku barni da aiki."

Murmushi baba yayi yana kallon fuskarta sannan yace, "haba uwar amarya, wannan irin fad'a haka da kikeyi halan keda wa."

"Nida matan balarabe mana, su daya dace ace suke tarbar baqi suna kai masu abinci shine sunka koma gefe kowace ta hakince sai kace tukane suna kiran akawowa wance da wance abinci, sun barni ni kad'ai ke hidimata sai kuma fareeda 'yar wajen yaya maryama."

"A'a'a to wannan maganar tafi qarfina tsakaninki ne da qannenki ba Mai shiga tsakani, ni dama zancen kai amarya ne yakawoni kinga gari ba guda ba.." kafin yaqarasa tayi saurin cewa,

"To ai sai anyi sallar la'asar za'aje ko kuwa?"

"A'a, bayin ALLAHn nan sun roqi alfarmar abasu amaryarsu su wuce da ita don gaba d'aya suka zo d'aurin auren tare da motocin d'aukar amarya, don haka kishiryata in sha ALLAH yanzu zasu wuce da abussu"

"Amma malan bamuga 'yan biko ba haka zamu miqa masu ita kamar..."

"Haba maman Rashida kada kice komai da yanzun da anjima duka d'aya ne, kuma shi biko ai al'adace ba addini ba don haka kiyi hak'uri tunda har iyayensa maza sukayi magana tamkar sun turo bikon ne, aje ashiryota gamunan muna jiranta muyi mata hud'u ba sai suwuce."

Jiki a sanyaye umma tafita tamkar wacce k'wai ya macewa a ciki, duk tsawon kwanakinna bata tab'a d'aukar cewa tabbas zata rabu da 'yar tata ba sai yanzu, cikin k'arfin hali tanufi d'akin da Rashida ke ciki kwance tana kuka bayan andawo da ita wajen wanka ita da 'ya'yan malan balarabe qanen mahaifinta su uku, sunyi lallashi har sun gaji sun qyaleta suna ganin umma tashigo duk suka mik'e suka fita, dai dai wajen kanta umma taje ta zauna tare dasa hannuwa ta d'ago kanta, cikin kuka tafad'a ajikinta tana sheshheka, ko kad'an umma ba tayi yunqurin hanata ba domin itama kanta kukan ne yazo mata, saida sukayi mai isarsu sannan cikin muryar dattako umma tafara yimata magana har lokacin tana jikinta.

"Rashida kuka bai kamaceki ba, domin wannan ranar farinciki ce agareki da kuma mu iyayenki da Allah yabamu ikon ganin mun sauke d'aya daga cikin haqqoqanki daya d'ora mana kuma ranace da kika dad'e kina jiran zuwanta don haka kinatsu ki saurari abunda zan fad'a maki amatsayina na mahaifiyarki." Share hawayen da suka sake zubo mata tayi sannan tasa hannuwanta ta tallafo fuskarta tana share mata qwalla had'e da cewa.

"Rashida! Ina so kibud'e kunnuwanki kiji abunda zan fad'a, gidan aure da kike gani ba wajen zaunawa kace zaka huta bane ko kace kayisane don kasuwanci, wajene na gwaggar maya don meman lada da kuma aljannarki, shi gidan miji wajene da zaki jajirce wajen nunawa duniya nagartar gidanku da kuma ahalinki, duk wata kima da darajarki annan ne zaki tabbatar da ita ta hanyar nuna kamalarki ga ahalinda zaki riska ku zauna dasu, mijinki shine aljannarki kuma shine farincikin ki na duniya da lahira, haquri da kike gani shi ginshiqine na tabbatuwarki isashshiyar mace awajen mijinki, shi kuma ladabi da biyayya sune zasu zamo maki tubalin da zai mai dake kasaitacciyar mace awajen mijinki, girmama iyayensa abune da zai qara maki kwarjina da tarin soyayya azuciyar maigidanki, kauda kai kuma da iya dad'ad'an lafuzza ga 'yan uwansa shi zaisa su soki har su zauna dake lafiya, kwanciyar hankalin da zaki bawa mijinki ita kuma jigoce ta yalwatuwar arziqinsa, kyautatawa da yin alkhairi ga mutane shizai jawo maki girmamawa ga manya da yaran da kike tare dasu, kiriqe ALLAH, ki guji abun hannunki, kibi mijinki kiyiwa mahaifiyarsa biyayya tamkar yanda kike yimani ga duk abunda bai sab'awa ALLAH ba, rashin kunya, tsiwa da sakin baki acikin mutane sukan xubarwa da mutum kima da daraja don haka ki nisancesu, Ina mai roqonki da duk k'arfin tsanani da wahala kada kid'aga harshenki akan na mijinki, idan son samune kada ki zalinci kowa kibari ke azalinceki da SANNU SANNU ALLAH zai yi maki sakayya, shi khairan da sharran duka 'yan aikene duk inda ka aikesu za suje kuma su dawo maka, kiyi k'ok'ari kishuka alkhairi don ki girbesa, kizama mai haquri da juriya sannan kizauna da kowa lafiya, kiriqi tsafta nasan kinada

Please Login or Register in order to submit comment