Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

duk abunda tafad'a akan little ba gaskiya bane, tayine saboda kwad'ayin d'anta shakur ya auri batool da kuma tsanarsa saboda soyayyar da mijinta ke nuna masu shida kakarsa da mahaifiyarsa kuma tayi nadamar hakan don ALLAH ya yafeta, alokacin Abba yayi nadamar d'aukar maganar hajia nafeesa da yayi sosai amma sai zuciyarsa ta nuna masa cewa koma meye ai bai kamata duk irin d'imbin soyayyar daya nunawa 'yar tasa ba ace tagujesa ta bijirewa umurninsa da zab'insa ba saboda son zuciyarta, tazab'i ta b'ata masa don tafarantawa kanta da masoyinta don haka baiga dalilin da zai koma bata wata soyayyar tasa abanza ba, kuma yayiwa ita hajia nafeesar kaca kaca had'e da cewa shi yanzu bayada case da wannan maganar don haka da ita da batool d'in da mijinta suje can suqarasa,

Wannan dalilin yasa hajia nafeesa ta qudiri riqe 'yar uwarta batool hannu biyu tare da kyautata mata tana yimata addu'ar samun daidaituwa tsakaninta da mahaifinta kota rage alhakinta data d'auka kuma ta dinga jan sumayya ajikinta sosai tana kula da ita had'e da cewa adinga kawo mata ita tana tayata reno, kusan ko yaushe cikin sayen 'yan kayayyakin yara take tana aika mata dasu tare da kayan wasa da sauran abubuwa wanda nan take Abu sumayya da gimbiyarsa suka manta da abunda tayi masu, dama ita uwa samnace da zaran kaso d'anta to shikenan ka gama da ita, duk girman laifinka zata iya mantawa dashi adalilin soyayyar daka nunawa d'anta kamar dai yanda suka manta da laifin da hajia nafeesa tayi masu suka saki jiki da ita suna kaimata baby sumayya da zuciya d'aya wanda hakan yajawo shaquwa mai tsanani tsakaninta da yarinyar shiyasa lokacin da yarinyar tarasu tana cikin wud'anda mutuwar ta jigata sosai.

Sunji damuwa matuqa akan rashin yarinyar amma daga qarshe suka fawwalawa ALLAH komai kamar yanda mahaifiyarta batool tayi, bayan watanni bakwai da rasuwarta ALLAH yasake bawa batool wani ciki, murna awajen little kam ba'a magana kai ka rantse kace shine cikinta nafarko, don farincikin daya nuna fiyema da wanda yayi ne alokacin da tasamu cikin sumayya tana tayi masa dariya, tun cikin na qarami idan yafita sai yakira fiye da sau bakwai kafin ya dawo yana tambayar ya unborn d'insa yake har ya tsufa ko gajiya bayayi, musamman da taje scanning d'inta na farko aka tabbatar mata tana d'auke da cikin 'yan biyu duka mata, ai sai kulawar ta sake lunkuwa har zuwa lokacin da zata haihu,.....







*ALLAH KAJIK'AN IYAYENMU*πŸ‘πŸ˜­
[11/14, 22:52] Billy S Fari: πŸšΆβ€β™€οΈπŸšΆπŸ»β€β™‚οΈ *SANNU SANNU*πŸšΆπŸ»β€β™‚οΈπŸšΆβ€β™€οΈ
πŸ’Ž _Bata hana zuwa..._πŸ’Ž


_WRITTING BY:_ *BILLY S FARIπŸ’Ž*

_DEDICATED TO:_ *BLOOD SISTER'S (AMZAHFAZ)*πŸ’‹

_BESTOWED TO:_ *ZAINAB AL-AMIN (MOM NA'EEM)* AND *AMINA UBA AYUBA (OUM ASHFAQ)*πŸ’ž

*DOMIN FARINCIKINKI SISTER SADIYA ZANGO (MIEMAH)*πŸ’–

*FATAN ALKHAIRI AGAREKU MOMMAH ME NANA HAFSAT (MISS XOXO) AND MAMANA HAFSAT RANO(OUM AFFAN)*❀️

Page___95πŸ’Ž

Da lokacin haihuwarta yayi ta matuqar shan wahala don kusan kwana tayi tana naquda a asibiti amma ba haihuwa ba mafarinta, hakan yasa likitocin suka yanke shawarar yimata operation, koda aka fad'a mata kowa yayi tsammanin zata tada hankalinta amma saita nuna babu wata damu don yanzu batada babban burin daya wuce taga an rabata da cikin dake jikinta lafiya, damuwarta d'aya shine mahaifinta, tana kuka takira hajia mama ta sanar da ita taje itama tafad'a masa, kamar dai wancan karon haka yayi yace ALLAH yasa ayi cikin nasara kuma ya sauketa lafiya, hajia mama taso ya amshi wayar yayi magana da ita kota samu natsuwa amma sanin halinsa yasa batayi hakan ba saidai tace mata tariqe wayar kada ta tsinke har taje tafad'a masa yace hakan, wasu zafafan hawayene suka zubowa batool jin muryar mahaifinta da tayi da kuma addu'ar da yayi mata ahankali tace.

"Alhamdulillah!, Ya ALLAH kaci gaba da sanyaya zuciyar mahaifina har sai yaji yayi na'am dani kafin ka amshi rayuwata."

Godiya tayiwa mahaifiyarta tare da roqonta gafara sannan tace koda ba'a fito da ita ba ALLAH ya amshi ranta taroqa mata gafarar mahaifinta kuma tafad'a masa duk tsawon shekaru shidan data d'auka ba tare dashi ba tana rayuwane da tarin d'imbin qaunarsa acikin zuciyarta, wud'annna kalaman nata sun matuqar kashewa mahaifiyarta jiki har saida suka sa tazubar da qwalla amma bata bari ta fahimci hakan ba taqarfaf mata guiwa sosai tare da yimata addu'a ALLAH yasa ashiga lafiya kuma a fito lafiya, cikin jin dad'i batool ta amsa da amin tana maijin wata irin natsuwa atattare da ita.

Cikin iyawar ALLAH ana shiga da batool ko mintuna talatin ba'ayi ba aka fiddo mata da kyawawan yaranta 'yanmata biyu masu matuqar kama da junansu wato (identical twins), both doctors da nurses d'in da suka amshi haihuwar sai ihu sukeyi cike da farinciki ganin girman da yaran ke dasu cikin qoshin lafiya, duk wanda ya kallesu da abinda zakaji yana fad'a,

"Wowww...fine baby's, wow...the baby's are so cute, woooo..so beautiful." Haka sukayita santin kyawon yaran har aka gama shiryasu.

Da aka fito dasu hajia nafeesa ce tayi saurin amsar d'aya, imaan matar Shakur da itama lokacin ke d'auke da tsohon cikinta na farin ta amshi d'aya don wannan karon Rashida bata zoba Fatima kuma tatsaya shiryawa yara zuwa school shiyasa hajia nafeesa da imaan suka zo don yanzu familyn sun d'unke waje d'aya tsintsiya mad'aurinki guda, dama hajia nafeesa kad'aice mai matsala yanzu kuma data shiryu sai familyn yayi gwanin sha'awa, qarami na girmama babba, babba Kuma na mutunta qarami tare da kyautatawa.

Waya hajia nafeesa taciro takira su uncle h ta sanar dasu an sauka lafiya anciro mata yara biyu 'yan mata sak kamarsu d'aya, saboda haka sukawo toshi sun samu takwarori, nan uncle Hussain yace aduba mashi wacce duk tafi tsawon hanci koda itace hassana to itace amaryarsa mai nakakken hanci kuwa ya barwa uncle Hassan sai ya sammata nashi aqara mata dashi shidai bayayi da ita, anata dariya.

Hajia mama kuwa harda sujudush shukur tayi had'e da sadaka lokacin da aka fad'a mata anfito da batool har ta farfad'o, Abbama dai ba'a barsa abaya ba lokacin da aka sanar dashi saida yayi qwallan farinciki yayi saurin sa hannu ya goge don kar agani, yace ALLAH yaraya yabata lafiya sannan yabar wajen, murmushi su uncle h sukayi tare da girgiza kai suna jinjina taurin rai da qarfin hali irin na yayan nasu.

Ko sati ba'ayi ba dayi mata tiyatar tasamu sauqi aka basu sallama, amma saboda taqara samun lafiya aka d'aga sunan sai nan da sati biyu, angon qarni kam saidai ace ALLAH yaraya masa don kallo d'aya zakayi masa yafassara maka irin d'imbin farincikin dake tattare dashi,

Ba'a batun Rashida da umma da ayanzu suke ganin batool tagama faranta masu a duniya tunda ta zamo jigon wanzuwar cigaban farincikinsu da suke tsammanin yankewarsa a shekarun baya da suka shud'e.

Haka su baffa da baffa Usman sunyi farinciki sosai duk da basu samu damar zuwa ba saboda matsalolin da sukasha gabansu amma saida suka aikowa da little dubu talatin sukace yaqara yayi hidima ALLAH ya raya, baffa nason ganin yaran amma babu yanda zaiyi, tsufa yaci qarfinsa sosai had'e da tarin damuwowi, wanda idan yatuna cewa rashin d'ansa akusa dashi shi yahaifar masa da har hakan kefaruwa, ga jininsa aduniya amma babu damar yagansa saidai a hoto idan little yazo ya nuna masa sai yayita kuka yana addu'ar ALLAH kasa yanada rabon bada wannan labarin kafin rai yayi halinsa kuma yarayawa Rashida zuri'arta cikin aminci da kuma kariyar ALLAH.

A wannan karonma a gidan Dr batool takoma saboda kula da yaran tunda acan gidanta ita kad'ai take batada wani mataimaki, Shahida ce mai hankali acikin 'ya'yan gidan kuma tana sudan wajen karatu balle atura mata ita su zauna tare, tana matuqar jin dad'in kular da take samu awajensu umma, hakan yasa tasake sakin jikinta sosai tana renon yaranta har akayi suna akayi arba'in sannan takoma gidanta, Inka ganta bazaka tab'a cewa itace uwar yaran ba don tayi qiba tayi haske ta murmure abunta saboda gyaran da Rashida keyin tsaye tayi mata tamkar ita tahaifeta, haka suma yaran bazaka tab'a cewa 'yan biyu bane saboda girmansu sai ka d'auka kowane daban aka haifesa, rayuwa mai kyau da inganci takeyi da mijinta da 'ya'yanta cikin so da qauna da kuma kulawar juna,

β€’β€’β€’ β€’β€’β€’ β€’β€’β€’
Kuma acikin shekarunne baffa Ali ya bayyanawa su baffa Usman duk aika aikar da sukayi shida Inna ruqayya har sukayi nasarar da bokansu ya kafe Nuraddeen acan qasar malesia kuma yasa mashi tsanaar qasarsa tare da mantar dashi akan duk wani abun daya shafi rayuwarshi ta baya kafin yaje qasar.

Tashin hankali wanda ba'a saka mashi rana, awannan lokaci baffa yayi abunda bai tab'a yiba saboda tsananin b'acin rai, dukkanin qarfinsa ya tattaro yana hawaye yanata kaiwa baffa Ali mari taduk inda ya samu batare da yayi la'akari da girman shekarunsa ba, ko kad'an baffa Ali baiyi yunqurin hanasa ba har saida yagaji yadena don kansa yana fitar da nishi d'aya bayan d'aya, bayan mintuna kad'an yamiqe ba tare daya d'ago kai ya kalli d'an uwan nasa ba yace.

"Ali kacutar da rayuwata da dama Amma ban damu da hakan ba inata yimaka uzuri had'e da bud'e maka fika fikan tausayina ka shige aciki Ina mai yafiya ga duk wani abu da kayi mun, Amma yau Ina mai baka haquri akan cewa kayi mani cutarwa mafi muni da girma da bazan tab'a iya yafe maka itaba har sai lokacin da kaje ka walwale wannan asirin da kayiwa d'ana, idan ba haka ba zan cigaba da rayuwa a matsayin mai d'an uwa qwaya d'aya aduniya batare dana koma sanyaka a matsayin d'an uwana ba, me nayi maka haka dana cancanci irin wannan horarwa awajenka nida d'ana?, Wace irin tsanar muce kasawa zuciyarka da bazaka iya samun koda d'an qanqanen filine azuciyarka da zaka iya yafe mana idan har wani abun muka yimaka alokacin da kasan munada matuqar buqatar juna ni dashi, kasa narayu na tsawon shekaru da baqin cikin d'ana da kuma fushinsa azuciyata?, Tir da halinka Ali tunda har zaka iya duban girman soyayyar mahaifi da d'ansa karabasu, a halin yanzu bakada wani sauran amfani awajena tunda har zaka iya saka wuqa ka datsemun farinciki na tsawon lokaci kuma ka d'auka daga yau ni ba d'an uwan ka bane kuma kaima ba d'an uwana bane."

Yana gama fad'ar haka ya juya yafice, baffa Usman dake zaune gefe ya kallesa had'e da cewa.

"Yanzu kayi farinciki ko Aliyu!? Ka b'atawa zuciyar data shima tana yimaka fatan shiriya da kuma kyautatawa, ka kai haqurin bawan daya jima yana yimaka yafiya da hidima qarshe har kana nema kasa kyawawan abubuwan dayayi abaya su ruguje ga banza."

Jikin baffa Ali a mace yace.

"Usman ka fahimceni, wlh na shiryu na gane kuskurena shiyasa nafad'a maku gaskiya wataqil asamo mafitar da nura zai dawo garemu, kwad'ayin na faranta zuciyoyinku yasa nazab'i nayi kunyar duniya a idanuwanku ko nasamu farinciki asanadiyar naku farincikin, ko kad'an ni ban fad'a maku wannan maganar ba don cutar da zukatanku kuma ALLAH shine sheda akan haka."

Ajiyar zuciya baffa Usman yayi don ya gamsu da maganganunsa had'e cewa.

"Naji, dama ni tun farko Ina zarginku akan haka amma bawan ALLAH can yaqi amincewa da zaku iyayin wani abun akan d'ansa tunda kai jinin sane, sai gashi ka watsa masa qasa a idanuwa kasa zargina yazama gaskiya akanku, maganar gaskiya baku kyauta ba kuma kun zaluncesa sosai."

"Hakane Usman Amma wlh nayi nadama da kuma dana sani, don ALLAH katayani roqonsa ya sake bud'a mani inuwar tausayinsa da kuma yafiyarsa nagane kuskurena."

"Alhamdulillah ALLAH yasa haka Ali amma gaskiya ni bazan tirsasashi akan ya yafe maka bisa hukuncin daya d'aukar maka ba, kayi qoqarin zuwa kuwarware abunda kukayi hakan zaisa ni kuma natayaka roqon yafiyarsa."

Shiru baffa Ali yayi kafin yace.

"Taya Usman?, Wlh yanzu bansan inda wannan malamin da mukaje ya had'a mana maganin da akayi sammun dashi yake ba, shekarun ba kad'an ba don gidan da yayi zama yanzu haka shine akayi sababbin shagunan can masu hawa biyu a farko farkon gari, Abu d'aya zan iya tunawa shine inda mukaje muka binne abubuwan da akabamu na sammun, shi kuma malamin ya fad'a mana cewa idan har wani yayi yunqurin haqo wajen to tabbas tsakanin ni da ruqayya dole sai d'aya yamutu, d'aya kuma za'a azo mashi ciwon da bayada magani sai dai yayita jinya har lokacin da mutuwarsa zata riskesa."

Baffa Ali yaqare maganar yana hawayen dake nuna tsantsar nadamarsa,

"Tirqashi wannan wane irin cacan raine kukaje kukayi da rayuwarku Aliyu don salwantar da kawai ku salwantar da rayuwar rai d'aya? Innalillahi wa'inna ilaihirrajiuun, wannan shi ake kira da murna ta koma ciki, ga kuma qoshi ga kwanan yunwa."

Wani irin kuka baffa Ali ya fashe dashi yana hango yanda rayuwarsa zata kasance a tsakankanin wannan sirad'i mai matuqar kaifi, har ga ALLAH ba mutuwa yake tsoro ba don yanzu ashirye yake daya sadaukar da ransa matuqar Nuraddeen zai dawo ga mahaifinsa da iyalansa, ciwo da kuma jinyar da batada magani su yake tsoron kada sufad'a kansa, Saida yayi kukansa mai isarsa baffa Usman bai hanasa ba don yasan ya cancanci yayi kukan daga qarshe yamiqa komai ga ALLAH yana Mai addu'ar ALLAH yasa suzame masa kaffarar zunubbansa sannan yace da baffa Usman.

"Zanje inyi abunda yakamata domin abunda na shukane zan girba da hannuna, fatana ALLAH yabani qarfin zuciya da kuma imanin da zan aikata hakan! kuma yasa Rashida da Nuraddeen su yafemun abunda na aikata ko bayan rayuwatane."

Duk zafin ran baffa Usman da haushinsa da yake ji yau saida yaji tausayinsa, tabbas SANNU bata hana zuwa...duk shaqiyancin mutum da girman kansa da kuma izgilinsa da sannu zai cimma ranar da zaiyi nadama da kuma dana sanin yinsu, dafa kafad'arsa yayi had'e da cewa.

"Karka damu Ali, ALLAH gafururrahim ne kuma mai tsananin tausayin bayinsa, babu buqatar sadaukarwar rayuwarka bayan katubanma zunubbanka, muje ni zan haqo komeye kuma da yardar ALLAH babu abunda zai samemu."....

_To jama'a kuyafeni idan nayi maku ba daidai ba acikin wannan littafin domin duk yanda mutum yaso yayi abu idan ALLAH bai soba yayi aikin banza, naso gama littafin nan kafin akoma makaranta amma ALLAH bai yarda ba saboda yanayin jiki da jini, don haka kuyi mani afuwa kuyi haquri zan tsaya da rubutunsa saboda gobe zan koma school sai kuma naga yanayin ya karatuna zai kasance, idan akwai yuyuwar inci gaba dayi maku typing d'insa kafin abubuwa su ida kankama zaku iya ganin posting d'ina kowane lokaci, idan kuma babu sai agafarceni har zuwa wani lokacin idan ALLAH yabani dama kuma ya aramun lokaci, Ina qaunarku FILLAH masoyan amana🀞🏻❀️🀝_





*ALLAH KAJIK'AN IYAYENMU*πŸ‘πŸ˜­
[11/14, 22:52] Billy S Fari: πŸšΆβ€β™€οΈπŸšΆπŸ»β€β™‚οΈ *SANNU SANNU*πŸšΆπŸ»β€β™‚οΈπŸšΆβ€β™€οΈ
πŸ’Ž _Bata hana zuwa..._πŸ’Ž


_WRITTING BY:_ *BILLY S FARIπŸ’Ž*

_DEDICATED TO:_ *BLOOD SISTER'S (AMZAHFAZ)*πŸ’‹

_BESTOWED TO:_ *ZAINAB AL-AMIN (MOM NA'EEM)* AND *AMINA UBA AYUBA (OUM ASHFAQ)*πŸ’ž

*DOMIN FARINCIKINKI SISTER SADIYA ZANGO (MIEMAH)*πŸ’–

*FATAN ALKHAIRI AGAREKU MOMMAH ME NANA HAFSAT (MISS XOXO) AND MAMANA HAFSAT RANO(OUM AFFAN)*❀️

Page___96πŸ’Ž

A'a Usman wlh maganin nan nada matuqar had'ari sosai, bazan so wani abun ya sameka ba har yayanmu ya sake shiga cikin wani hali, kaine kad'ai karage masa aduniya da zai kalla yaji sanyi bayan iyalinsa, naroqeka kabarni zanje da kaina in fuskanci hukuncin laifin Dana aikata, natabbata ALLAH baya mayar da tubar bayinsa matuqar sukayi ingantacciyar tuba kuma mai kyawo, idan ko har wani abun ya sameni to nayi imani da cewa ALLAH na nufin ya jarabta nine domin yaga qarfin imanin da nace nayi da kuma tubata idan har na gaskiya ne, saboda haka kabari inje kaji d'an uwana!" yaqare maganar had'e da d'ora hannunsa saman kafad'arsa.

Kusan mintuna ashirin da wani abu sukayi suna rigima akan wanda zaije cikinsu, shidai baffa Usman ya nace shi zaije don ayanzu bai shirya rasa d'an uwan nasu ba tunda har ya tubarwa laifinsa, shi kuma baya cikin wud'anda haqo asirin zai iya cutarwa kamar yanda bokan yafad'a idan har aka haqo abun shi baffa Ali da matarsa da sukayi asirin su zai koma mawa balle wani abun ya samesa, shi kuma baffa Ali yana ganin tunda har yatuba to dole yayi qoqarin gyara laifukan daya aikata da hannunsa da kansa ko zai samu sassaucin hukuntawa daga ubangiji, ya sani ubangijinsa zai karb'i tubarsa amma haqqin wud'anda ya zalunta dolene sai yayi duk yanda yakamata wajen ganin sun yafe masa kafin ALLAH yabarshi.

Dole badon baffa Usman yaso ba ya haqura ganin yanda ya dage harda kuka, amma ya tabbatar masa dacewa Dole tare zasuje koma inane bazai barshi yaje shi kad'ai ba.

Da sauri sauri baffa ke tafiya ko gabanshi ma baya gani saboda tsananin b'acin rai har ya isa gida yana fitar da haki d'aid'ai ya samu gefe da tsakar gidan ya fad'i zube kwance yana kuka, gaba d'aya yau yarasa qarfin zuciya da jarumtar da zai iya hana kansa kuka, Babu abunda yake tunanin in banda lafuzzan d'an uwan nasa, ace kimanin kusan shekaru talatin yana fama da damuwar rabuwa da kuma fushi akan d'an nasa tilo duk ta adalilin kaidi da baqin sammun da d'an uwansa na jini uwa d'aya uba d'aya yayi masa, meye rauninsa a matsayinsa na babba agaresa daya cancanci wannan hukuncin?, Meyayi masa aduniya da bai cancanci yafiyarsa ba har sai ya rabasa da d'ansa na tsawon wannan lokaci?, Wace irin kulawace bai bashi ba aduniya daya zab'i jefasa cikin mummunan hali haka?, Haka yayita tambayar kansa yana tsiyayar da hawaye har ya gaji don kansa ya bari.

kallon baba nusaiba da tun shigowarsa taqaraso wajen d'aya zube kwance hankalinta atashe, yanda yake kukan ya tabbatar mata daba abu qarami bane ke damunsa ba, don haka saita d'auko mafifici ta shiga yimasa fiffita batare da race masa uffan ba har sai da taga yasamu natsuwar da zai iya kallonta, murmushi ta sakar masa had'e da cewa.

"Waye ya tab'a mani adilin mai gidana baban nura abban Rashida har ya karya zuciyarsa haka tasashi zubar da qwalla, kayi haquri da yanayin da rayuwa kanzo dashi na farinciki ko akasinsa, kayarda da wanzuwar qaddara mai kyau ko marar kyau agareka, ka amince babu mai yimaka sai ALLAH domin shine kad'ai ke iya sarrafa zukatan bayinsa, shiga damuwarka daidai yake da rushewar dukkanin farincikin gidannan musamman na wacce ke rayuwa bisa walwalarka da kuma farinciki, idan ni nayi maka laifi kayafeni baban nura idan kuma waje akayi maka kayafesu baban Abba amininsa?"

Duk da yana jin wani nauyi a zuciyarsa da kuma wani abu da yazo ya tokare masa amaqoshi hakan bai hana jin tasirin kalamanta azuciyarsa ba da sukasa nan take yaji wani irin sanyi ya mamaye masa ita,

Murmushin ya mayar mata kamar yanda tayi masa had'e da cewa.

"Me zakiyimun aduniya maman nusaiba da zai b'atamun rai har yasani kuka inba alkhairi ba, kin zamo mani haske alokacin da nake cikin duhu, kin kauda mani kad'aita alokacin dana rasa makusantana gaba d'aya, kin zamo sanyi agareni alokacin da zafi yayi mani qawanya tare da qoqarin share mani hawaye ga dukkanin damuwar dake neman durqusar dani, taya kike tunanin duk tarin wud'annan alkhairan da kikayimun zaki iya yin wani laifi da zaisa hawayena sake kwaranya bayansu, aike 'yar aljannah ce in sha ALLAH maman Rashida, ki kwantar da hankalinki damuwata dai irin ta yau da kullumce kamar yanda kika sani."

"Akan Nuraddeen kenan!"

"Sosai kuwa, saidai awannna karon ta tarin nadamar fushin dana d'auka dashi ba bisa haqqinsa ba, wataqilma fushin nawane ya dad'a jefasa cikin halin da har aka samu yin galaba akansa, ya ALLAH ka yafemun kuma ka yaye masa wannan mummunan hali da aka kad'asa aciki."

Yaqarasa maganar wasu zafafan hawayen na sake biyo masa fuska,

"Amin" baba nusaiba tafad'a tana kallon mijin nata da gaba d'aya tsufa yarufes, furfura tako ina ta cika masa fuska ga tarin jijiyoyi da suka taso masa tako Ina suka bayyana ajikinsa, wata 'yar sanyayyar ajiyar zuciya ta sauke aranta tana maijin tausayinsa, a wannan lokacin yakamata ace yana samun cikakken hutu ne bawai wahala ba, Amma tsabar neman halal d'insa da yake da kuma tarin damuwowi dake cike fal azuciyarsa da mabanbantan qalubalen da yayita fuskanta arayuwa sunsa tsufa yayi saurin bayyanar masa tayanda kallo d'aya zaka yimasa ka d'auka shekarunsa sunfi qarfin gangar jikinsa saboda manyancin da yayi,

Nan baffa yashiga labarta mata abunda kefaruwa, sosai itama bataji dad'in hakan ba amma saboda ta tausasa zuciyar baffa akan d'an uwan nasa tace.

"Ashsha! Gaskiya abun baiyi dad'i ba kam, Amma kayi haquri Kuma ka godewa ALLAH daya kawo qarshen lamarin alokaci d'aya, kaga dai ALLAH ya karb'a maka addu'ar shiriya da kaketa roqawa d'an uwanka sannan kuma zai dawo mana da d'anmu a hannunmu in sha ALLAH don na tabbata Ali yayi nadama kuma tubar gaskiya yayi don haka zai karya koma meye da SANNU SANNU sai kaga hankalin Nuraddeen yadawo gida, kaga kuwa banda godiya babu abunda yakamata kayiwa ALLAH, nufin alkhairansa agaremu yasa ya bayyana mana gaskiyar a fili tafito, da yaso sai yakarb'i rayuwar Ali da matarsa batare da sun sanar da abunda suka aikata ba agaresa kaga kuma shikenan babu yanda zamuyi sai dai mucigaba da haquri har zuwa lokacin da ALLAH yaso karya asirin da kansa, Amma yanzu wannan shiriyar da yayiwa Ali har yatuba ga laifinsa yafad'i abunda suka aikata ita zata haska mana al-amarin sai muga nesa ta matso mana kusa da yardar ALLAH, kayi haquri kayafi d'an uwanka ka jawosa ajiki don yanzu babu abunda yafi buqata sama da haka, shizaisa ya dad'a nadama da kuma dana sani akan abubuwan da suka aikata."

"Maman Rashida nariga da nayi rantsuwa akan babu ni babu shi har sai yaje ya tonikke abunda suka binne shida matarsa, taya zan karya wannan rantsuwar ."

"Haquri zakayi kayafe masa, ai hannunka bazai rub'e ka cire kayada ba, kabari tunda akwai hatsi sai in fiddar maka da kai."

"Maman Rashida.."

"Haba babn nura bansanka da haka ba, kayi afuwa da yafiya ga sabba balle d'an uwanka." Tayi saurin katsesa tana fad'ar hakan cikin sigar rarrashi da ban magana, badon baffa yaso ba ya amince da maganarta saidai ya tabbatar mata da cewa shi bazaiyi kaffara ba kuma bazai fidda kai ba, amma ALLAH yasheda ya yafe masa abunda yayi masa, maganar sulhu tsakaninsu kuwa sai lokacin da suka warware abunda sukayi tukuna, ganin hakan yasa dole itama tahaqura taci gaba salwantar masa da hankali tahanyar dad'ad'an kalamai har saida taga ya sauka daga fushin da yayi kuma yasamu natsuwa sosai sannan tamiqe taje takawo masa ruwan tukunya masu sanyi da abinci yaci yasha ya qoshi ta kaimasa ruwa ban d'aki yayo wanka sannan yanemi waje ya kwanta, ko mintuna uku da kwantawa baiyi ba wani nannauyan bacci yayi awon gaba dashi.

Tare su baffa Usman da baffa Ali suka nufi inda yake tunanin sun binne maganin da aka basu, yawo suka sha sosai amma basu ga wajen ba saboda gaba d'aya anguwar ta canza tunda jiya ba yau ba, kusan yini sukayi suna kaida komo a tsakankanin wajen da baffa Ali ke tunanin sun binne maganin amma ya kasa ganewa don duk anyi gine gine wajen, ko banza shi tun daga ranar da suka binne maganin bai koma zuwa wajenba saidai idan hanya tabiyo dashi ya hango wajen hakan yasa yakasa tantace wajen, wani irin kuka ya fashe dashi had'e da cewa.

"Kaicona nayi asara, na rabe tsakanin d'a da uba kuma na tab'ar da kaina, wayyo ALLAH na nashiga uku bansan meye makomata ba aduniya idan har nakoma ga ALLAH batare da yaron nan yadawo mahaifarsa ba ga mahaifinsa."

Haka yayita sabbatu shikad'ai yana kuka duqe agaban baffa Usman da alokacin wata damuwa ta taso ta lullub'e masa zuciya, ya rasa yanzu ko meye mafitar wannan al_amarin, matsalar sammu kenan, koda za'ayi addu'a to samun warakarsa yana ta allaqane ga karye surqullen da akayi, gashi shida suka aikata b'arnar yakasa gano wajen.

Sunfi mintuna biyar awajen kafin baffa Usman yaduqa ya d'aukowa baffa Ali iccensa(crutch) na qafa da yake dogarawa daya saki lokacin daya durqushe agabansa yana kuka ya miqa masa had'e dasa hannu ya taimaka masa yamiqe shima yana sharar qwalla.

Ji baffa Usman keyi kamar yayita dukansa saboda zafin abunda sukayi amma babu hali dole ya tunda yayi nadama kuma ya tuba, haka suka dawo gida agajiya baffa Usman yawuce shiyarsa Inna Bilkisu takawo masa abinci da ruwa tana yimasa sannu da zuwa, cike da damuwa

Please Login or Register in order to submit comment