Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya nunasa da hannu had'e da cemasa.

"Abu sumayya?" Kamar yanda yaji baffa nakiransa dashi.

Murmushi little yayi tare da d'an russunar da kansa qasa yace.

"Eh, Ina wuni?" Fad'ad'a murmushin sa baffa Usman yayi tare da qarasowa wajensa yayi saurin miqa masa hannu tare da yimasa sallama, cike da yaqinin cewa tabbas wannan jinin d'an d'an d'an uwansane baffa Usman ya amsa masa sallamar yana qare masa kallo tare da tunano kammannin Rashida acikin fuskarsa.


Kusan secod biyar suka kwashe ahaka kafin can baffa Usman yayi firgigit kaman wanda yafarka daga bacci yajawo hannnunsa su shiga ciki, tunda suka shigo baffa ke kallonsa har suka qarasa, shidai little sai bin ko ina nagidan yakeyi da kallo kafin can ya ajiye idanuwansa akan baba balarabe, ajiyar zuciya ya sauke yana fad'in.

"Kai wlh ALLAH tsohonnan yau ka wahalsheni da yawa, gaba d'aya ka tada mani da hankali gabana sai fad'uwa yakeyi."

"To ai seyadena yanzu tunda gani kagani cikin qoshin lafiya."

Matsawa yayi inda baffa yake had'e da zaunawa kusa dashi yasa hannu ya dafo kafad'unsa, "sannu kaka, anwuni lafiya?"

"Lafiya klw Abu sumayya, ya kake?"

"Ina lafiya kaka, yanaga kamar jikinka a sanyaye.."

Muryarsa na rawa ya juyo duka jikinsa yana fuskantar little tare dasa hannayensa yariqo fuskarsa dasu yace,

"Farincikine yahaifar da haka jikana tare da samun kyakkyawan albishir daga bakin da bazai tab'ayimun qarya ba akan cewa kai d'in jinina ne, katuna nasha fad'a maka inada wani d'a tafiyarka da maganarka sak irin nasa, har kake tambayata yana ina? Kana so kasanshi katuna,"

Kasa amsa masa yayi saboda yanda yaji gaba d'aya jikinsa ya mutu yana kallonsa, juyowa yayi yana kallon baba balarabe ya jinjina masa kai alamun tabbatar mas da zancen baffan.

"Hakane Nuraddeen, wannan shine kakanka wanda yahaifi babanka, nazab'i nahad'aka da sune batare da sanin mahaifiyarka ba da kuma 'yan uwana saboda gudun lalacewar zumunci tsakanina da 'yar uwata, koba komai ni kaina na sauke wani nauyi da d'an uwana yamutu yabarni dashi aransa,

Little baisan lokacin da wasu hawayen da zai iya kira dana dad'i ba suka zubo masa da sauri yataso ya rungume baba balarabe yana fad'in.

"Nagode d'an tsoho da kazamo nafarko wajen cika mani muradai na da kuma mafarkaina, kayi mani abunda duk duniya Babu Wanda zai iya yimani, ka haska mani rayuwata alokacin da take cikin duhun rashin sanin makomarta anan gaba, ba shakka kakana yafi kowa sa'ar samun d'an uwa aduniya, yayi saurin tafiyane saboda yanada yaqinin cewa goben ahalinsa zatayi kyau a hannun d'an uwansa, nagode maka nagode maka sosai d'an tsohona mai ran qarfe, ka dad'e kayi qarko har zuwa qarshen ahalinmu."

Yasake rungumesa sosai kamar zai tsaga jikinsa ya sakasa,

"Kai meye haka? Meye haka kakeyi lele? Cikani mana kasan ba qwarine da qashina ba yanzu, wannan abu haqqine akaina duk da nasan hakan zai iya haifarmun da matsala, amma nayi farinciki sosai, wannan addu'ar taka bana fatar karb'uwarta domin banaso qarkona yawuce lokacin da zanga jininka, don haka kama dena fatar hakan kaji ko?"

Yaqarasa maganar qwalla nazubo masa a fuska, d'agowa little yayi daga jikinsa yasa hannuwa yagoge masa hawayen fuskarsa yana fad'in.

"Kadena kuka mana d'an tsohona, kayi Abu mai kyau, ka sada yaron da akeyiwa kallon shege da danginsa na uba, ka gyara zumuncina don me da ALLAH zai tsaida rayuwarka ga iya ganin jinina bayan shi yafad'awa manzonsa cewa duk wanda ya kiyaye game da sha'anin zumunta zaiyi masa tsawon rai tare da gyara gobensa?, Natabbata koda baka kai lokacin da nakeyi maka fata ba in Sha ALLAH zaka wuce lokacin da kai kake fata, na dad'e da dason sanin dangin mahaifina, amma yanayin da mahaifiyata keshiga da alqawarin dana d'aukar mata akan bazan sake tambayarta abunda zai sakata cikin damuwa ba shi suka hanani tsaurara son sanin hakan saboda gudun na kaucewa umurninta duk kuwa da shegantani d'in da akeyi"

Miqewa yayi yakoma wajen baffa da duk wata kalma da yake ajewa ke dad'a tunkud'o da fitar hawayenta saboda tausayinsa da yakeji da kuma rad'ad'in kalmar da yaji ana jifarsa da ita, kamo hannuwansa yayi yana murzawa ahankali tare dayin murmushi alokaci d'aya kuma hawaye na zubo masa yace.

"Kakana kaima kuka kakeyi?, Kaida zakayi farincikin bayyanar jikanka agaresa mezai saka kuka Kuma?" Sa hannuwansa yayi akan fuskarsa shima yagoge masa hawayen dake zubowa sannan yaci gaba da cewa.

"Kana kewar mahaifina kamar yanda nima nake matuqar kewarsa ko?."

Girgiza masa kai yayi had'e da saurin rungumesa yana cewa.

"Ko kad'an jikana, kai kad'ai nake kewa da kuma mahaifiyarka, ka manta dashi tunda bayada buqatarmu na tabbata zaka maye mani gurbinsa."

"A'a kakana, zaiyi matuqar yimani wahaka na iya maye maka gurbinsa, kayi haquri kada kayi fushi dashi, duk da Ina son jin muryarsa, Ina son ganinsa, Ina son na rab'i jikinsa nayi fira dashi na fad'a masa damuwata nayi kuka ya sharemun hawayena amma nakasa samun haka saboda yayi nesa damu banyi fushi dashi ba, natabbata SANNU SANNU bata hana zuwa..kamar yanda bamuyi tsammanin zamu had'u da juna ba sai gashi ahankali ba zato ba tsammani ALLAH yahad'a fuskokinmu shima in Sha ALLAH da sannu zai dawo garemu, da kanshi zai cike gurbinsa da kake tunanin zan maye maka da yardar ALLAH."

Wani irin sanyi baffa yaji na ratsa zuciyarsa jin kalaman jikan nasa, d'ago yayi daga jikinsa little yayi saurin maidashi yana fad'in "Rowa zaka yimun bazaka barni naji d'imin jikinka ba?"

Gaba d'aya duk sukasa dariya, baffa ya cikasa yana fad'in nawa kad'ai bazai wadatar da kaiba har sai ka had'a dana wannan kakan naka." Yaqare maganar yana nuna masa baffa Usman da bakinsa yakasa rufuwa saboda farincikin da yakejin kansa aciki, haka little yaje ya rungumesa shima tare da d'an tsokanarsa sannan suka shiga wata firar mai cike da jin dad'i kowannensu naji tamkar karsu fita cikin wannan yanayin, saidai ita rayuwa haka ta gada wani lokaci farinciki wani lokaci baqinciki, Abu d'aya baya tabbata balle sudawwama acikin wannan yanayin.

Sun jima suna shawarwarin yanda cigaban rayuwar zata kasance inda baffa da kansa ya roqi little akan cewa subar wannan zancen a tsakaninsu har zuwa lokacin da mahaifinsa zai dawo, yasani bayada matsala ta b'angaren baffa Usman haka ta b'angaren baba balarabe shima bazai bayyanata ba kodon gudun lalacewar zumuncinsa da Yaya Maryam har zuwa lokacin data buqata, little d'in dai yake tsoron yabud'e sirrin shiyasa yaroqesa, abunda bai sani ba shima kansa baya buqatar fitar zancen saboda gudun b'acin ran mahaifiyarsa har sai lokacin data buqaci ita da kanta tahad'asa dasu sai ya bayyana mata gaskiya, nan yayiwa baffa alqawarin zai riqe wannan sirrin har zuwa lokacin da ALLAH yayi nufin bayyana komai batare da matsala ba tunda dai yasamu wani sashen farincikinsa kamar yanda yake mafarki,

Shiru baffa yayi kafin can yace,

"Saidai yakamata ace Ali yasani tunda shid'in d'an uwana ne bazai yuyu ace na waresa daga sanin hakan ba."

"Idan nima d'in d'an uwanka ne dana isa ga dukkanin abunda yashafeka to nace harshi bazai san komai basai ranar da gaskiya zatayi halinta." Baffa Usman yafad'a cikin b'acin rai.

"Saboda me Usman, karka manta shimafa jinin mune, duk mugun halinsa dai bazamu iya cire jininsa daga namu ba kamar yanda shima bazai iya cire namu anasa ba."

"To nidai nafad'a Yaya, wlh baza'a fad'a masa ba kaji kuma na rantse."

Daga haka baffa bai sake cewa komai ba ya qyalesa, little yayi dariya don yafahimci kakan nasa baiji dad'in hakan da d'an uwansa yace ba.

"To nidai ku taimaka ku gwada mani amaryata, itama ina kewarta Ina so naganta."

'Dago kai baffa yayi yakallesa don ya fahimci kakarsa yake nufi wato Yaya hawwa, aransa yace ALLAH sarki gaba d'aya sak d'abi'unsa na mahaifiyarsa ne, matuqar yasan abunda tayiwa mahaifiyarsa har take buqatar ya had'u da ita to tabbas yacika d'a nagari mai ramakon alkhairi ga mugunta, nan shima baba balarabe yabuqaci yashiga ya dubota ita da baffa Ali suka miqe gaba d'aya suka shiga cikin gidan.

Ita Yaya hawwa saboda tsananin kukan da takeyi ako yaushe yasa idanuwanta gaba d'aya sun dena gani ga yanayin tsufan da taqarayi duk ta nad'e waje d'aya kai ka d'auka ba mutum bace, don ma ALLAH yasa tana samun kulawa gwargwado, tsabar tausayinsa da little yaji da suka shiga harda kukansa, koda suka shiga babu abunda takeyi sai kuka tana kiran nura.nura.nura, da qyar Inna Bilkisu dake zaune gefenta ta rarrasheta sannan tasamu tayi shiru suka gaisa da baba balarabe tare da yimasa yajiki, little kuwa sunan mahaifinsa da yaji tana kira yasa yakasa yin magana saboda kada ta ida rud'ewa idan taji muryarsa tayi tsammanin shine, bayan sun fito ita dai Inna Bilkisu sai kallon little takeyi saboda kamarsa da Rashida gashi har taji zasu tafi ba'ace komai akansa ba, hakan yasa zuciyarta tabata cewa qilan cikin 'yan uwanta ne tunda gashi tare yake da qanen mahaifinta malan balarabe,

A hankali lokacin da suka kawo wajen shiyar da Nuraddeen da Rashida sukayi zama baffa Usman ya rad'awa little a kunne, nan ne mahaifiyarka da mahaifinka suka zauna ka ganshi nan tunda suka barshi sau d'aya aka bud'asa har zuwa yau.

Juyawa little yayi yakalli wajen da kyau kawai sai ya tsinkayo mahaifinsa da mahaifiyarsa tsaye abakin qofar, murmushi yayi tare da shafa kansa sannan suka wuce ta can d'ayar qofar inda baba Ali ke jinya don awancan zaurenne na qofar baya suka zauna shiyasa ma Basu samu wurgewar mutane ba sosai balle asan abunda yafaru.

Suna shiga baffa Ali yayi ido hud'u da baba balarabe dake shigowa bayan baffan Usman da sauri ya noce kansa qasa saboda tunawa da abubuwan daya fad'a masa ashekarun baya, gaba d'aya sai yashiga gashi gabansa yashiga fad'uwa yayi tunanin sunzo ne domin su turkesa akan abunda yafad'a amma abunda bai sani ba gaba d'aya baba balarabe bai fad'a masu maganar daya fad'a masa ba, don yasan idan yayi hakan to zai iya tab'a masu zumunci musamman daya fahimci irin soyayyar da baffa keyiwa 'yan uwansa ta hanyar kalamansa, kawai sai ya b'oye gaskiyar yabar duka laifi akansa don baya buqatar ya lalata zumuncin tsakaninsu da shima yake neman gyara nasa, yatabbata komai daren dad'ewa gaskiya zata bayyana domin ita SANNU SANNU bata hana zuwa...,

Girgiza kai kawai yayi sannan suka shiga gaggaisawa tare da yimasa yajiki, ba qaramar razana yayi ba da yaji muryar little wanda saida hakan ta bayyana qarara a fuskarsa.

Kowanensu yi yayi tamkar bai lura ba har suka gama gaisawa sannan suka fita, tambayar kansa ya shigayi wanene wancan yaron to?, me sukazoyi a gidan?, Kardai ace sun kashe macijine basu sare kansa ba!, Idan kuwa hakane duk d'aukar fansarsu tazamo ta banza domin bahaka suke buqata ba, yafiso labarin nura harma da tarihinsa su shafe adoron qasa tayanda mahaifinsa zaifi jin rad'ad'i aransa.

Saida sukayi sallar magrib sannan baba balarabe da little suka wuce bayan sunje can gidan baffa sun gaisa da nusaiba kuma little yaga qannen mahaifinsa, itama konkad'an basu bayyana mata kowaye little ba duk da yasaki jiki suna fira da ita da yaran sosai Amma kasancewar Bata san Nuraddeen ba balle Rashida yasa bata gano komai ba,

Little da baffa kuwa ji sukayi tamkar garsu rabu aranar saboda wata irin sabuwar soyayyar junansu da sukeji na taso masu.

Haka little wanda gaba d'aya yanzu ya maida sunansa Abu sumayya saboda soyayyar batul d'insa da yake dako azuciyarsa yaci gaba dayin rayuwarsa cikin jin dad'i, yana matuqar taimakawa kakannin nasa guda biyu aduk lokacin da yasamu dama, haka tab'angaren karatunsa yana maida hankali sosai duk da kuwa akwai wud'anda suka fishi qoqari tare da jajircewa hakan bai hanasa qasa a guiwa ba yana iya qoqarinsa na ganin shima yasamu abunda yasamu koda bai kaisu ba, har baya son hutu ya qare saboda farincikin da yake samu awajen kakan nasa, haka ya kammala shekarun karatunsa hud'u a tsakanin b'oyayyiyar gaskiyar da sukayi alqawarin b'oyewa a tsakaninsu har zuwa ranar da gaskiya zata bayyana, Kuma yayi nasara samun kyakkyawan sakamako a mataki na biyu wato second class..

A ranar daya amshi saka makon jarabawarsa aranar yaquduri aniyar zuwa gidansu batool domin ya gabatar da kansa awajen mahaifinta bayan yanemo izini da kuma sa albarkar mahaifiyarsa kamar yanda ta alqawarta masa, Kuma ysha alwashin koda za'a rabasa da rayuwarsa aranar sai ya tabbatarwa da batool cewa shi d'in nata ne ita kad'ai kuma ita kad'ai ya tanadawa zuciyarsa da kuma gangar jikinsa...







*ALLAH KAJIK'AN IYAYENMU*πŸ‘πŸ˜­
[11/14, 22:52] Billy S Fari: πŸšΆβ€β™€οΈπŸšΆπŸ»β€β™‚οΈ *SANNU SANNU*πŸšΆπŸ»β€β™‚οΈπŸšΆβ€β™€οΈ
πŸ’Ž _Bata hana zuwa..._πŸ’Ž


_WRITTING BY:_ *BILLY S FARIπŸ’Ž*

_DEDICATED TO:_ *BLOOD SISTER'S (AMZAHFAZ)*πŸ’‹

_BESTOWED TO:_ *ZAINAB AL-AMIN (MOM NA'EEM)* AND *AMINA UBA AYUBA (OUM ASHFAQ)*πŸ’ž

*DOMIN FARINCIKINKI SISTER SADIYA ZANGO (MIEMAH)*πŸ’–

*FATAN ALKHAIRI AGAREKU MOMMAH ME NANA HAFSAT (MISS XOXO) AND MAMANA HAFSAT RANO(OUM AFFAN)*❀️

_Awannan gab'ar alqalamina bazai iya cigaba da rubutu ba har sai ya miqo saqon gaisuwa tare da jinjina had'e da fatan alkhairi agareku, *AUNTY MAIJIDDA MUSA* da kuma *AUNTY FAREEDA MUHAMMAD ABBAS* Bisa zallar karamci, k'auna da kuma halacci da kuka nuna mani wajen jajircewa bibiyar wannan littafi nawa duk da kuwa irin tafiyar hawainiyar da yakeyi hakan baisa kuka nuna qosawa ko kuma gazawarku ba, kun qara mani qwarin guiwa tare da addu'o'in fatan alkhairi agareni da sukasani himmatu da kuma samun quwwar cigaba da rubuto wannan littafin cikin nasara, Ina yimaku addu'ar dukkanin alkhairan ALLAH su lullub'eku tare da ahalinku, nagode sosai da samun goyan bayanku acikin kowane rubutu nawa, ubangiji ALLAH yatsare mani ku kuma yakula mani daku aduk inda kukeπŸ‘, Fillah! akoda yaushe zuciyata na matuqar yabawa d'imbin karamci irin naku tare da yimaku son so na har abada😍_

Page___83πŸ’Ž

Tana fad'in "Abu sumayya!" Cike da kokwanto hakan aranta har ta qarso da gudu bakin gate d'in, daidai lokacin ya aza qafarsa zai fita taja wani irin burki had'e da tsayawa tana fidda lumfashi d'aya bayan d'aya saboda gudun da tayi.

Cikin wani irin salo takira sunansa tace.

"Abuu.. sumay..yaaa."

Cak ya tsaya da qafarsa had'e da lumshe idanuwa jin dirar sautin muryarta da yanda takira sunan acikin kunnuwansa, a hankali yajuyo da duka gangar jikinsa izuwa gareta suna fuskantar juna, lokaci d'aya idanuwansu suka sarqe suna isar masu da wani saqo dake fassara tsantsar soyayya da adadin kewar da suka yiwa junansa,

Wata irin dariya had'e da kukan farinciki taji sun kucce mata alokaci d'aya ta durqushe agabansa saboda qafafuwanta da taji na gagarar imata tace,

"Wannan wace irin bazatace mai cike da burgewa da kuma qayatarwa Abu sumayya?, Ka qaraso izuwa gareni kafin tsantsar farinciki yasa lumfashina d'aukewa."

Taqarasa maganar tare dasa hannuwanta ta rufe bakinta hawayen farinci na zubo mata a fuska, nad'e hannuwansa yayi akan qirjinsa yana kallonta yana murmushi, duk da ayanayin da ya ganta baiyi masa dad'i ba Amma farincikin ganinta yasa yakasa matsawa kusa da ita saboda nauyin da qafafuwansa suka yimasa, sunfi mintuna biyu ahaka kafi yafara takowa izuwa gareta yana cewa.

"Haba gimbiyar Abu sumayya! Wannan kukan da kikeyi ai saikisa hawayen dake zubowa daga idanuwanki su narkarmun da zuciya, kitashi mana na kalleki da kyau naga ko kin kula mani da kanki kamar yanda kika alqawarta mani kinji 'yan matanaaaa..." Yaja qarshen cikin wani salon sigar lallashi da yasa batasan lokacin data saki dariya ba had'e da miqewa tana rufe fuska.

"Sannu da zuwa annurin zuciyata, farincikina kuma uban 'ya'yanah." tafad'a cikin murmushi tana jifarsa da wani kallo mai cike da tarin ma'anoni kala kala.

Tsabar jin dad'in kalaman da yaji na fito daga bakinta ya sashi d'aga kansa yana murmushi tare da kallon fitillun da suka haskaka harabar gidan, gyara tsayuwarsa yayi idanuwansa na akan fuskarta yana kallonta sanna yace.

"Yawwa uwar 'ya'yana, makullin zuciyata da kuma mabud'inta, Ina fatar dai nasameki cikin amincin ALLAH da kuma yardarsa."

"Sosai kuwa, domin badon amincin ALLAH dake tare dani ba da tuni kewarka da rashinka sun kaini kushewata."

Saida yayi dariya sannan ya d'ago kai yana kallonta yace.

"Godiya ta tabbata agaresa daya tsare mani ke daga zuwa kushe don tseratar da rayuwar Abu sumayya daga fad'awa gararin duniya nahar abada, ya kike gimbiyata?.

"Ina lafiya yanzu tunda gani ga ka kuma."

"Alhamdulillah, nayi farinciki sosai duk da dai naga kamar kinyi k'wabron kula mani da kanki, Ina fatar akwai banbancin kulawar da ajiyar dana baki acikin zuciyarki."

"Babu buqatar tabbatar maka da hakan domin ance labarin zuciya atambayi fuska, ai tsantsar kula da ajiyar kane dake cikin zuciyata ya haifarwa da gangar jikina shiga cikin wannan hali, kaine kawai na shiga taraddadin cewa ka kula mani da tawa ajiyar ko kuwa?."

"Haba 'yan mata!, Ai wanzuwata awannan lokacin tare dake shine zai baki tabbacin cewa naba ajiyarki cikakkiyar kulawa, Alhamdulillah yau na karb'i sakamakon dake tabbatar da na kammala karatuna bayan adadin shekaru hud'u dana d'auka inayi cike da tarairayar qaunarki acikin zuciyata, hakan yasa na gaggauta dawowa agareki adaidai wannan lokacin da zimmar zamowa mijinki ke kuma mata kamar yanda na d'aukar maki alwashi, inafatar zaki amsheni hannu biyu ki maidani a gurbin da tun farko kika bani."

"Kash!..a gaskiya bazaka samu hakan ba domin na dad'e da cireka a wannan gurbin."

Tafad'a cike da zolayarsa tare da d'aure fuska ta juyar da kanta gefe, cikin fad'uwar gaba ya koma ta gefen data maida kanta yana kallonta.

"Kamarya! Ban fahimceki ba gimbiya?, Wai kina nufin kin d'aukeni daga wannan gurbin kin bawa wani.. how? " yafad'a yana tsareta da idanuwansa da suka soma canza kala.

Kwashewa tayi da dariya harda tafa hannuwa tana nunasa, sake d'aure fuska yayi yana binta da wani irin kallo da yasa dole ta tsaida dariyar had'e da cewa.

"Afuwan Abu sumayya!, Ba haka nake nufiba, taya kake tsammanin zan iya cireka ga wuri har in aza wani?, Wannan abune da bazai yuyuba kama dena tunanin hakan."

"Taya tunanina bazai bani hakan ba bayan da bakinki kikace.."

"Don ALLAH kayi haquri da wasa nakeyi.."

Kafeta yayi da idanuwa kafin yayi wata irin ajiyar zuciya ya juya mata baya.

"Pls kayi haquri mana.."

"Em'ehm..ni nayi fushi, dama d'azun kin b'atan rai da kikace natafi bakya buqatar ganina, sonki ne da yayi mun yawa yasa na iya dawowa garemu da kika fito"

"Wayyo...kayi haquri mana, plsss..."

Tafad'a tare da komawa gabansa tariqe kunnuwa,

Dariya ya saki sannan yace.

"Shikenan nahaqura, bari natafi dare ya somayi."

Nan take kamannin fuskarta suka sauya daga farinciki zuwa damuwa.

"Meye gimbiya?"

"Bana son katafi Abu sumayya, gaba d'aya shekarunnan hud'u a jigace na qarar dasu saboda rashinka da kuma ganinka, ka qaramun lokaci mana ko hasken daya d'iga azuciyata zai qara yawan da zai haskamun yau zuwa gobena."

"Kamar ya gimbiya?, So kikeyi na kwana anan ne? Ko bakiga lokaci naqara qurewa bane?"

Saida ya duba agogon dake hannunsa sannan yace.

"Kin gafa har goma da rabi takusa, gashi akwai nisa da inda zanje gidan baffan mamana, in dai akaina ne ki kwantar da hankalinki yanzu kullum muna tare kinji ko?"

"Ka kasa fahimtata ne, Taya hakan zai faru abbana na nema ya aura mani duk wanda yaga dama naqi amincewa, sanadiyar hakan ya sanya mani tsauraran matakai,"

"To kinga ya kamata ace natafi yanzu kamin ya sameni, na tabbata ko yanzu don baya gida shiyasa muka samu wannan damar, don haka kiyi haquri kinji ko?"

'Daga masa kai tayi idanuwanta na tsiyayar da hawaye yacire hankacif daga cikin aljihunsa yamiqa mata.

"Ki share wud'annan hawayen bana son ganinsu."

Karb'a tayi tayi kamar yanda yace sannan tamiqa masa ya karb'a ya mayar cikin aljihu,

"In fad'a maki wani Abu?"

Kad'a masa kai tayi yace "to yi murmushi mana tukuna, idan ba haka ba sai nafasa fad'a."

Murmushin da seda haqoranta suka bayyana tayi shima ya mayar mata had'e da cewa.

"Yawwa gimbiyar Abu sumayya, ummu sumayya, haka nake son akoda yaushe ki kasance, in Sha ALLAH su dady na nan tafe gobe su nema mani aurenki, saboda haka kidena damuwa soon zan d'aukeki izuwa duniyar farincikinDana tanada mana kinji ko?"

Saboda yanda farinciki ya rufeta batasan lokacin da tayi tsalleba had'e dayin dariya tana fad'in "da gaske Abu sumayya?."

"To kijira mana gobe kigani."

Ciro wata leda yayi a aljihunsa ya miqa mata sannan yace

"Ina wayarki?"

"Tana cikin nabaro."

"Ok ungo saka mani lambarki nasan yanzu kin canza layi ko?"

"Eh amma ni ai inada naka, kaje kawai zan kiraka"

"Nima fa na canza layi 'yan matana"

"Eh nasani mana."

Sallama yayi mata sannan yawuce saboda ganin takafe tanada sabon layinsa, wanda yake ganin abun da kamar wuya...

Ai kuwa bai qarasa gida ba sai gashi yaga ankirasa da sabuwar lamba,

Sanin yanda sukayi da ita yasa bai wani b'ata lokaci ba ya d'aga, muryarta yaji tace.

"Kasamu abun hawa kuwa?"

"Eyyeeee ashe da gaske kikeyi gimbiya, nasamu gashi har mun kama hanya."

"To Allah ya saukeka lafiya ya karemun kai daga sharrin qarfe, mutum da kuma aljani."

"Amin gimbiya," yafad'a cike dajin dad'in addu'arta.

β€’β€’β€’ β€’β€’β€’ β€’β€’β€’
A can borno kuwa hajia nafeesa najen qesheqeshin cewa dady zaije nemawa little auren batool hankalinta ya tashi, tasan tabbas ba abunda zai hana dady zuwa sai in baya raye kuma duk yanda zaiyi ya wanke little daga kashin kajin data shafa masa awajen mahaifin batool sai yayi, don haka takasa zaune ta kasa tsaye har saida dady ya shigo, da yake yau zai dawo part d'in nata, ALLAH ALLAH tadingayi yayi sauri yagama cin abincin don ta maganta masa abunda ta qudurta aranta.

Yana kammalawa tace.

"Am Alhaji nikuwa Ina son yin magana dakai idan ka amince."

"Ina jinki hajiya nafeesa, injin dai ko lafiya?"

Yafad'a tare da d'aukar jarida yakoma can saman kujerun dake tsakiyar falon ya zauna, biyo bayansa tayi ta zauna kusa dashi had'e dayin shiru na 'yan mintota be sannan yace.

"Shin kasan ko yaron nan shima son batool yakeyi naji ana zancen zakaje nemawa wanda bayada asali ita."

Kar ya fahimci inda zancenta yanufa amma sai yabasar yana qoqarin bud'o wani shafin jaridar yace.

"Wane yaro kike zancen kuma wace batool d'in." 'dan muskutawa tayi daga zaunen da take sannan tace.

"Shakur mana da batool 'ya gidan kawuna alhaji umar fari dake zaune kano, yanzu hakan yana can kwance baya jin dad'i saboda yaji kana shirin zuwa nemoma wani bare ita gashi shi daya jima yana sonta, wlh alhaji zai iya rasa rayuwarsa akanta, shiyasa nace bari nafad'a maka don ya kamata kaduba wannan al'amarin.

Cigaba yayi da bud'a jaridarsa batare daya tankata ba har natsawon mintota da tagaji tace.

"Haba Alhaji!, Dakai fa nake magana kayi mani shiru.."

"Mts..shin mema kike cewa?"

Duk da ranta ya b'aci haka tasake daurewa ta maimaita masa tanaji kamar ta qwalla ihu saboda abunda yayi mata, ajiye jaridar yayi sannan ya aza qafarsa d'aya akan d'aya yana kallon yanda tacika tayi fam, yasan kad'an take jira yanzu tafitinesa ta hanasa bacci mai dad'i don haka sai yace.

"Shikenan naji, Kuma in sha ALLAH kafin muje zanyi tunani akai, idan naga yafi dacewa da ita shikenan sai ayo maganar dashi, duk da shima yaron da kikacewa bayada asali kakarsa na acikin gidannan kuma a matsayin matata baza'a ce abawa daji gida bai qoshi ba, don haka in sha ALLAH za'ayi abunda ya dace, Ina shi shakur d'in?."

Washe baki tayi saboda taji dad'in yanda haqarta zata cimma ruwa anata tunanin sannan tace.

"Yana can sashensa kwance tun safe ba inda yaje."

"Ok Bari nadubosa."

"Ai daka bari har nan da zuwa safiya, don inaga yasamu yayi bacci yanzu kada atashesa."

Tafad'a gabanta na fad'uwa don bata masan inda yaron nata take ba tana qoqarin dakatar dashi, cigaba yayi da tafiyarsa yana fad'in.

"Eh bara dai nadubosa, ai kamata yayi tun wuri ki sanar dani, yanzu idan har ciwon yayi masa tsanani ya cutar dashi ban sani ba, sai kice a'a." Yasa kai ya ficewarsa.

Da sauri taje ta d'au wayarta takira shakur lokacin yana zaune yana game da wayarsa hankali kwance.

"Kai shashasha, me kakeyi yanzu?"

"Zaune nake Ina game awayana lafiya mom?"

"Maza, maza, kanemi waje ka kwanta kuma katabbatar ka lullub'a, nafad'awa dadynku cewa bakada lafiya saboda kaji zaije nemawa wannan shegen auren batool, shine zaizo dubaka, maza ka kwanta kafin ya qaraso."

"Mom nifa Ina da.."

"dallah rufamun baki sakaran banza, kayi abunda nace kawai."

Jefar da wayar yayi agefe tare da komawa yakwanta saman gadonsa ya lullub'e yana qunquni, kasancewar qofar d'akin abud'e take kuma ga fitila akunne yasa har dady yaqaraso bai sani ba,

Shikuwa dady qunqunin da yakeyi ya tabbatar masa da cewa idanuwansa biyu, shigowa yayi ciki ya tako har gaban gadon nasa ya zauna wajen gefen kansa cikin muryar dake tabbatarwa da Shakur bawasa atattare da mahaifin nasa yaji yace.

"Kai Shakur tashi!"

Aikuwa kamar jira yakeyi yayi zumbur yamiqe yayi zaune tsakiyar gadon idanuwansa wuqiwuqi babu alamun ko ciwon kai yayi balle zazzab'i,

Saida dady yaqare masa kallo sannan yayi murmushi had'e da cewa.

"Meyake damunka ne?"

"Ba.ba.babu komai

Please Login or Register in order to submit comment