Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

πŸ’Ž _Bata hana zuwa..._πŸ’Ž


_WRITTING BY:_ *BILLY S FARIπŸ’Ž*

_DEDICATED TO:_ *BLOOD SISTER'S (AMZAHFAZ)*πŸ’‹

_BESTOWED TO:_ *ZAINAB AL-AMIN (MOM NA'EEM)* AND *AMINA UBA AYUBA (OUM ASHFAQ)*πŸ’ž

*DOMIN FARINCIKINKI SISTER SADIYA ZANGO (MIEMAH)*πŸ’–

*FATAN ALKHAIRI AGAREKU MOMMAH ME NANA HAFSAT (MISS XOXO) AND MAMANA HAFSAT RANO(OUM AFFAN)*❀️

Page___80πŸ’Ž

Kyakkyawar tarba su baffa sukayiwa baba balarabe da yake shi kad'ai yaje bada kowa ba, a can gidansu baffa Usman aka share zauren aka yimasa shimfid'a baffa yaba d'aya daga cikin yaran gidan kud'i aka siyo masa ruwa masu sanyi sosai tare da fura da nono Inna Bilkisu tadama masa fura aka kawo masa, tunda baba balarabe ya zauna idanuwansa ke qasa yakasa had'asu da nasu baffa saboda tsananin kunyarsu da yakeji saida baffa Usman yayi gyran murya had'e da cewa.

"Malan balarabe ya hanya da kuma kasuwa? Kwana biyu dad'a mun datse zumuncin dake tsakaninmu, har qara shi Yaya kuna had'uwa kasuwa dashi amma nikam ai bana iya qirga adadin shekaru ba sharabonmu da juna."

'Dago kai yayi suka had'a ido da baffa yaji wasu hawaye sun kwararo masa ga idanuwa saboda tausayinsa yanda yaga tsufa yataso masa ga rashin mataimaki atare dashi, alokacin d'aya yaji haushin kansa na biyewa zuciyarsa bisa yarda da abunda aka fad'a masa wanda bayada tabbaci akai kuma ya hau, gashi sanadiyar hakan yazamo silar rushewar wani sashen farincikin bawan ALLAH n nan bisa rubutacciyar qaddarar da ALLAH ya tsaro akansa, murmushi baffa yayi yana kallonsa had'e da cewa.

"Ashsha malan balarabe meyayi zafi haka?, duk wani tsanani da kake gani aduniya ai yana tare da sauqi, kafad'a mana dalilin zuwanka anan domin wannan kukan naka zai iya jefamu cikin wani rud'ani da kuma tashin hankali."

Saida yasa hannu ya share hawayen da suka kwanta masa afuska had'e da jan majinan dake neman toshe masa kafafen shaqar lumfashi a hanci yana sake qoqarin danne wasu hawayen dake neman zubo masa sannan cikin sanyin muryar dake nuna tattare yake da nadama da damuwa yace.

"Da farko ina so nafara baku haquri bisa abubuwan dana aikata maku ashekarun baya bisa son kaina da kuma sharrin zuciya dana biyewa, haqiqa nayi dana sanin yin hakan tun bada jimawa ba awancan lokacin sai dai aqoqarina naganin nagyara wannan kuskuren da nayi sai kuma nasake b'atawa don kub'utar da zumuncina da tsoron rasa abunda muke tunanin shikad'ai yarage mana aduniya da zai rage mana rad'ad'in wani sashe da muka rasa arayuwarmu...."

Nan baba balarabe yashiga basu labari tun daga abubuwan da suka faru alokacin da d'anuwansa da iyalinsa sukabar gari har zuwa dawowar Rashida da rigimar da sukayi da Yaya Maryam da aunty marwiyya akan sanar dasu dawowar Rashida da da yace zaiyi da kuma abunda yafaru lokacin da yazo garin domin sanar dasu da komawar Rashida acan garin da aka tsinceta da had'uwarsu da mahaifanta sanadiyar zuwansu gano d'an data haifa lokacin data yayesa, da rasuwar mahaifin nata washe garin ranar a qoqarin sa na zuwa wajensa har ya yahad'u da hatsarin da yazamo sanadiyar rabasu dashi da tsatstsauran hukuncin da yayar tasu tayanke alokacin da yayi yunqurin cikawa d'an uwansa burinsa da abunda ya sake fusatata na rashin dawowar Nuraddeen da yanda sukayi da umma mahaifiyar Rashida saboda lafuzzan da taji yafurta qarara a tv cewa bayada iyali har dai zuwa qarshen duk abunda yasan yafaru wanda shine yazamo silar b'oye masa duk wata gaskiya da yayi, daga qarshe yace.

"Wannan yaron da kagani ranar atare dani, yaron da kake matuqar kyautatawa, yaron da qarfin jini ya sanya shaquwa da kuma soyayya mai tsanani tsakaninka dashi acikin d'an qanqanin lokaci ba kowa bane face jikanka, jinin d'anka Nuraddeen kuma d'a ga Rashida, shine wannan cikin data b'ata dashi har muke kokonton yana raye ko akasin haka, ALLAH yanufa tahaifesa kuma har ya girma batare da mun bari kun sanshi ya sanku ba, sanadiyar karatun da yakeyi anan jami'a wajena yasa nayanke shawarar had'asa dakai kasanshi yasanka a matsayin kakansa, Ina roqonka da kayi haquri kayi mani afuwa bisa b'oye maka wud'annan abubuwa da nayi tun farko dakayi bibiyar sanin hakan, ALLAH shine sheda duk tsawon shekarunnan da aka kwashe ina rayune cike da qunci da damuwar hakan azuciyata, nayi kuka nayi da nasani yafi aqirga amma nakasa samun rangwamen nauyin da nakeji azuciyata har sai yau da ALLAH yabani ikon fad'a maka, wataqil hakan nanufin cewa nima zan amshi tawa jarabawarce tahanyar rabuwa da 'yar uwata kamar yanda ta alqawarta, koma dai meye ashirye nake da nakarb'i duk wani sauyin rayuwa da zaizo mani matuqar hakan da nayi zai kawo maka wani sassaucin qunci da damuwar daka dad'e dasu acikin azuciyarka."

Hawaye nazuba a idanuwan baffa Usman yace.

"Hak'ik'a kun cika mafiya son kanku da yawa kuma ko kad'an bakuyiwa yayana adalci ba bisa fad'i tashin rayuwa daya dingayi wajen nemo maku 'yarku da kuma bimata haqqinta, yayi kukan safe, rana dare a sanadiyar b'atanta, yarasa duk wani abu daya mallaka ta sanadiyar b'atan 'yarku, farin cikinsa da walwalarsa gaba d'aya duk saida yayi bankwana dasu ta sanadiyar b'atan 'yarku, meyasa zakuyi masa hakan bayan ya kasance mai tsananin kamanta adalci agareku?, Yarabu da matarsa, dukiyarsa, d'ansa, d'an uwansa, da duk wani farinciki nasa aduniya saboda kawai yaga ya qwatowa 'yarku haqqinta, amma shine ku kuka zab'i cigaba da cutuwar da zuciyarsa ta hanyar b'oye masa gaskiya alokacin da 'yarku ta bayyana agareku wanda natabbata da kun sanar dashi da yasamu craguwar damuwarsa kaso 99 bisa d'ari, haqiqa kune mutane mafiya son kai dana tab'a gani aduniya, maganar gaskiya bakuyi masa adalci ba kuma kun cutar dashi da yawa sai...."

Saurin dakatar dashi baffa da shima hawayen yakeyi yayi ta hanyar d'aga masa hannu had'e da cewa.

"Kar kace haka Usman, awani b'angaren sunada gaskiya d'ari bisa d'ari a matsayinsu na iyaye, kuma ko nine su zan d'au mataki fiye da hakan, saidai bazan d'auka akan iyayen mijin 'yar tawa ba, tsatsauran matakin da zan d'auka zai kasance ne akan shi mijin nata shi dake da iko akanta kuma na d'auki duk wani hukuncin da nake tunanin shine zai zamo maslaha tsakanina dasu don in late 'yatah, sai dai shi tunanin kowa da kake gani daban yake aduniya kuma babu wanda yafi qarfin kuskure, haqiqa naji ba dad'i ga yanda wud'annan abubuwa suka kasance, musamman rashin aminina da nayi aqoqarinsa nazuwa ya bayyana mani abunda yakeda tabbaci akan cewa narasa natsuwata akansa, Amma babu komai tunda babu yanda na iya dole nayi haquri kuma nagodewa ubangijina daya sama mani wani aminin daga jinina da zan riqa kalla a matsayinsa ina jin sanyi duk da rashinsa agareni babbar illace sosai arayuwata..."

Kasa cigaba da maganar yayi saboda kukan dayaci qarfinsa adaidai wannan gab'ar, haqiqa ALLAH shiyake halittar bayinsa kuma yadubi zukatan da suka dace da juna sai yajefa soyayya mai tsanani a tsakaninsu, tunda yake bai tab'a had'uwa da mutum wanda ALLAH yasanya masa soyayyarsa arai ba kamar baba mahaifin Rashida, yana matuqar sonsa ba ga zuciyarsa kad'ai ba hatta sassan jikinsa da kuma rouhinsa, sai gashi kwatsam arana d'aya mutuwa tayi masu yankan qauna a lokacin da suke matuqar buqatar junansu, ya tabbata da yanada rai bazai bari hakan tafaru ba, hatta d'ansa daya zab'i yayi nesa dashi yanada yaqinin cewa da yana raye duk hanyar da zaibi wajen ganin yadawo dashi agaresa sai yabi don tunkud'e masa duk wata damuwa da zata ziyartarsa, gashi sanadin rashinsa aduniya damuwowi da yawa sun nemi su durqusar masa da rayuwa, donma ALLAH yabashi jajirtaccen d'an uwa daya tsaya masa, badon haka ba da tuni shima yarasa tashi rayuwar.

Saida yayi kukansa mai isarsa sannan ya d'ago idanuwansa da sukayi jajir yana kallon baba balarabe yace.

"Nayafe maka komai meye kayimun kaida 'yan uwanka, tasiri da girman soyayyar dake tsakanina da d'an uwanka bazai iya bari nariqeku azuciya ba tunda har ka iya takowa kazo kanemi yafiyata had'e da sanar dani gaskiyar abubuwan da suka faru, haqiqa naji dad'i da hasashena yazamo gaskiya Abu sumayya ya kasance tsatsona, tabbas nagartaccin iyaye suke haifar da nagartacciyar zuri'a kuma babu tantama uwa tagari ita kad'ai ke iya haihuwar d'ah nagari, a nagarta naga jinina atattare dashi a b'angaren kamanni, tarbiya, tausayi da kuma sanin yakamata sak nahango mahaifiyarsa rashiday atare dashi, Ina so ka kwantar da hankalinka akan abunda 'yar uwarka tace, zumunci abune mai girma kuma bazan bari naku ya lalace ba ta sanadiyata ba duk da dai shi hankalin mata yasha banban da namu saboda qarancin tunani da suke dashi amma ni har ga ALLAH banga laifinta ba kuma kaima da kabi umurninta banga naka ba anan, domin shi bin nagaba bin ALLAH ne mun riga da mun taso bisa tarbiyar da iyaye sunka yimana akan muyiwa manyanmu biyayya shiyasa ka gagara bijire mata, ba ita kad'ai ba hatta nidana haifi Nuraddeen naji zafi da rad'ad'in kalaman daya furta nacewa baisan komai ba akan maganar iyayensa da kuma iyalinsa, don haka banga laifinta ba nacewa sai lokacin daya dawo sannan za'a bayyana dawowar Rashida da abunda ta haifa, domin ko an bayyana hakan kafin yadawo bayada amfani tunda baya nan kuma bazai yuyu muriqeta tazauna zaman jiransa ba tunda bashi kad'aine namiji ba aduniya, gayanda kuma abubuwa suka faru akan Rashida ta b'angarenmu dole aji tsoron dawo da ita da abunda tahaifa awajenmu don kada asake qoqarin salwantar da ita da d'an nata kamar yanda akayi abaya, don haka nayi maka alqawarin zanci gaba da b'oye wannan gaskiyar har zuwa lokacin da yaji zai iya dawowa garemu."

"A'a malan Idris kada ayi hakan, asanar dashi komai inaga hakan zai iya karkato dashi yadawo gida." Baba balarabe yafad'i hakan tare da riqe masa hannu.

Murmushin da yafi kuka ciwo baffa yayi had'e da girgiza kai sannan yace.

"Hmm malan balarabe kenan!, Karabu da d'an yau kawai, ada zuciyata na kokonton cewa Nuraddeen zai iya d'aukar dogon lokaci da ransa da lafiyarsa da kuma hankalinsa ba tare damu ba, amma tunda aka d'auki tsawon wud'annan shekarun bai waiwayo muba bayan nakirasa kuma yaji muryata har ya ambaci sunana yaji irin tashin hankalin da nake ciki na rashin dawowarsa amma ya kashe wayarsa saboda baya buqatarmu ya kuma toshe duk wata hanya da zamu iya samunshi nacire wannan kokonto da kuma tabbacin da nake dashi akai, wanda yayi hakan tawace hanya kuma kake tunanin zamu iya sake samunsa balle har mu sanar dashi?,"

Kallon baffa Usman yayi da tun d'azu yazuba masa idanuwa shima yana kallo saboda mamakin kalamn dake fita daga bakinsa, yatabbata idan shine bazai tab'a yafe masu ba akan wannan abun da suka yimasa amma shi alokaci d'aya ya yafe masu har yana qoqarin b'oye laifinsu ya bayyana na d'ansa, a gaskiya qarfin imanin yayan nan nasa yayi yawa, yana wannan tunanin ne yaji yace.

"Kaga d'an uwana nan, Babu wahalar da bamuyi ba wajen ganin munsamu hanyar da zata sadamu dashi Amma hakan ta faskara, haka nakoma tamkar wani mahaukaci kullum riqe da waya a hannuna Ina qoqarin kiransa ko ALLAH zaisa in samesa amma hakan ya cutara kuma ina tsammanin shine yaqi bada damar da hakan zata yuyu saboda yasamu duniya da wasu mutanen da yake tunanin sun fimu."

"Haba Yaya kadena fad'ar hakan?, Wlh nasan ba haka kurum yaqi dawowa ba, wannan abun akwai sharrin shed'anu aciki."

"Hmm Usman kenan, sharrin shed'anu ko kuma sharrin zuciya?, ALLAH dai ya yaye masa abunda kedamunsa amma mudena azawa shed'an da shed'anu laifukanmu akoda yaushe muma kanmu muna aikatasu da kanmu da kuma saninmu sai mufake da cewa shed'anne ko kuma akasin haka, nayi imani akan cewa innamal a'amalu binniyat."

Wud'annan kalamai na baffa su suka fahimtar da baffa Usman cewa izuwa yanzu ran d'an uwan nasa yafara b'aci game da rashin dawowar d'an nasa wanda alamu sun nuna bai yarda cewa wani yayiwa Nuraddeen wani abuba daya shafi magani ko sammu, amma shi zuciyarsa d'ari bisa d'ari tayarda baya bisa hankalinsa kuma ba kowa yake zargi ba sai d'an uwansu, don haka dole yaqara tashi tsaye akan matsalar ko ALLAH zaisa adace awannan karon duk da dama ko yaushe cikin addu'a suke kuma yanada yaqinin tana karb'uwa ijaba kawai ce bata sauka ba....



*ALLAH KAJIK'AN IYAYENMU*πŸ‘πŸ˜­
[11/14, 22:52] Billy S Fari: πŸšΆβ€β™€οΈπŸšΆπŸ»β€β™‚οΈ *SANNU SANNU*πŸšΆπŸ»β€β™‚οΈπŸšΆβ€β™€οΈ
πŸ’Ž _Bata hana zuwa..._πŸ’Ž


_WRITTING BY:_ *BILLY S FARIπŸ’Ž*

_DEDICATED TO:_ *BLOOD SISTER'S (AMZAHFAZ)*πŸ’‹

_BESTOWED TO:_ *ZAINAB AL-AMIN (MOM NA'EEM)* AND *AMINA UBA AYUBA (OUM ASHFAQ)*πŸ’ž

*DOMIN FARINCIKINKI SISTER SADIYA ZANGO (MIEMAH)*πŸ’–

*FATAN ALKHAIRI AGAREKU MOMMAH ME NANA HAFSAT (MISS XOXO) AND MAMANA HAFSAT RANO(OUM AFFAN)*❀️

Page___79πŸ’Ž

Saida little yagama zagaye kasuwar sannan yasamu daqyar yagano hanyar da zai komawa shagon nasu, lokacin har qarfe sha biyun rana tagamayi, a wahalce ya dawo tare da fad'awa akan kujerar rubar dake ciki yana fitar da nishi a hankali, kallonsa baba balarabe yayi had'e da cewa.

"Ina katsaya ne tun d'azu naketa faman jiran dawowarka kazo ka zauna ka karya najika shiru, ga abincin nan dana anso maka har ruwan tean sun huce gaba d'ai"

"Bari kawai d'an tsohona, gaba d'aya nan agajiye nake ga yunwar cikina ta isheni, gaskiya kasuwarnan da girma take, ai kad'an yarage in b'ace ALLAH ya taimaka nadawo kan hanya."

"Kace ashe ka kuru?, Ai nazata kanacan wajen malan idris d'in ne?"

"A'a, ai tund'azu nabaro wajensa ina zazzagayawa cikin kasuwar saboda na d'ebe qeyar idanuwana, Amma dattijon nan gaskiya yakamata ace yazauna gida ya huta saboda ya manyanta sosai, halama bashida manyan 'ya'ya mazane suka barshi haka yana faman shan wahalar rayuwa?."

Saurin kauda zancen baba balarabe yayi had'e da d'auko masa biredi da wainar qwai yamiqa masa yana fad'in.

"Ungo nan nidai kaci abinci kar qwalsa(ulcer) ta kamamin kai, ga ruwan tea nan saika had'a dasu haka nan ka kora"

Yafad'a yana miqo masa cup d'in.

Karb'a yayi had'e da cewa.

"Bari naci biredin kawai ya isheni."

Miqewa baba balaraben yayi tare da d'aukar sauran kayan had'in tean daya sawo ya mayarwa mai tiredar shayin yace yabashi lemu mai sanyi da ruwa a maimakonsu da yake mai tiredar na sai dasu duka saboda masu buqata idan masu sayayyar kaya sunzo masu sannan yadawo ya kawo masa ya had'a dasu yaci abinshi ya qoshi.

Baba balarabe na ganin qarfe d'aya har da mintuna tayi yaciro d'ari biyar yamiqawa little had'e da cewa ya tashi yawuce makaranta tunda yace sunada lectures, sallama sukayi dashi sannan yamiqe zai tafi yana fad'in.

"Zan dawo tanan idan mun tashi zuwa qarfe shida na marece."

"A'a kabarshi sai kuma wani jiqon saboda daqyar mukai k'arfe shidan?"

"Kashh!...gashi kuma nacewa dattijon can ya aiko akirani idan zai tafi sai nariqa masa kayan,?"

"To saidai kayi haqura har zuwa wani lokacin don suna ma riganmu tashi saboda ba'a gari d'aya bane su samu su isa gida dawuri."

"Shikenan bari naje!"

Har yayi nisa sai kuma yadawo had'e da cemasa,

"Bari dai naje nafad'a masa kada ya aiko kuma asamu bana nan, kasan bakyau karya alqawari ko kuwa?"

Ya wuce batare da yajirayi jin amsar da zata fitowa daga bakinsa ba,

Yana zuwa ya iskosa tare da wasu manyan mutane da sukazo sayen kajin har angama cinaki sun bashi kud'in yana qirgawa, sallamar da yayi tasa baffa juyowa yana kallonsa kafin yayi qoqarin qarasa qidaye kud'd'in ya sallamesu sannan yamaido hankalinsa ga little d'in daya nemi waje ya zauna.

"A'a lele kadawo?" Baffa yafad'a yana kallonsa had'e da tura kud'in cikin aljihu, Saida little yayi murmushi sannan yace

"Eh kaka, dama zanwuce makaranta me yanzu saina tuna nayi maka alqawarin cewa ka aika akirawoni idan zaku tashi zanriqa maki kaya, shine nace bara nazo na sanar dakai kada ka aika saboda tafiya zanyi, Ina fatar hakan ba damuwa ko kaka."

"Ikon ALLAH, to nikam meye abun damuwa anan, ai nasaba karaka wani damar da kanka kaji."

"A'a nidai kam bana son yanda ka manyanta haka kana d'aukar wud'annan abubuwan, don ALLAH kasamu wud'anda zasu dinga riqa maka zuwa titi ko biyansu ne sai kadinga yi?"

Shiru baffa yayi yana kallonsa irin yanda yanuna damuwa qarara a fuskarsa tabbas yasan dole akwai wani abu b'oyayye tsakaninsa da wannan yaron, haka kurum baza'a samu irin wannan tausayin ba har sai in akwai alaqa mai qarfi tsakani,

"Shikenan jikana in Sha ALLAH bazan d'auka ba, zan riqasa akaimun duka abakin titi Ina biya."

"Yawwa kaka, hakan yafi gaskiya, bari intafi lokaci na qulewa ALLAH yaqaro kasuwa."

"Amin ya rabbi."

Har zai tafi baffa yakirasa had'e da cewa,

"Yarona yau kafara ganina amma kana matuqar tausayina da kuma girmamani, ko meyasa haka?"

"Nima ban sani ba kaka, Amma nasan shi tsoho na kowane, yanada kyau ace duk inda yake angirmamasa ko badon wani dalili ba?"

"Hakane, to shikenan nagode sosai, amma zaka tafi baka fad'amun sunan kaba?"

Shiru yayi na tsawon wasu daqiqu tare dayin murmushi da alama wani abun ya tuna sannan yace

"Kaka sunana Abu sumayya."

"Abu sumayya.? Kanada aure ne?" Ya maimaita sunan cike da mamaki.

"A'a kaka, Ina dai son akirani da sunanne saboda wani dalilin amma sunana na gaskiya..."

Bai qarasa ba sakamakon wayar baffa da tayi qara yayi saurin cirota daga cikin aljihunsa had'e da d'aga masa hannu alamun ya tsaya don yasamu ya amsa kiran, kasancewar kiran daga gidane wajen iyalinsa nusaiba yasa yabar wajen zuwa can gefe inda babu hayaniya sosai ya d'aga kiran, shi kuwa little naganin haka ya shiga duba agogon hannunsa yaga lokaci na neman qurewa gashi akwai tazara sosai kafin yasamu yakoma gida har yayi zancen shiryawa ya wuce makarantar, wani saurayi dake nan gefe zaune da alama yaron baffane dake taimaka masa ya kalla tare da cemasa"

"Dan ALLAH idan kaka yadawo kace masa nawuce saboda nakusa makara."

Gyad'a masa kai saurayin yayi sannan shi kuma yawuce yana d'an d'aga qafa saboda yasamu yayi saurin isa da wuri.

Baiyi mintuna biyar da barin wajenba baffa yadawo yana tambayar saurayin ko ina yake? ya bashi amsa da cewa ai yawuce yace afad'a masa cewa sauri yakeyi yakusa makara shiyasa.

Ba haka baffa yaso ba don yaso ace yasan ainahin sunansa ko don mutuncinsa tare da kulawar daya bashi, amma duk da haka in sha ALLAH zai tambayi baba balarabe yafad'a masa tunda shi kullum suna tare a kasuwar.

Da lokacin tashinsu baffa yayi yasa masu yin dako suka d'aukar masa kwandunansa suka kaimasa bakin titi inda zai samu mota ya biyasu kamar yanda yayiwa little alqawari sannan ya d'auki kaji uku cikin sauran kajin da suka rage masa yanufi shagon baba balarabe dasu da niyar yabashi aba little amma ga mamakinsa sai ya isko shagon arufe da alama har ya rigashi tashi, Bai kawo komai aransa ba yawuce abunsa duk da aransa ba hakan yaso ba saboda dama wasu lokutan akwai lalurar da zata iya tasowa ya rigashi tashi ko shi yarigashi tashi, duk da dai su sunfi rigansu tashi saboda yanayin sana'ar tasu da kuma gari daba d'aya ba.

Baffa na isa gida bayan yawatsa ruwa yaci abinci yashiga labartawa matarsa nusaiba zancen saurayin daya gani d'an gidansu baba balarabe muryarsa da tafiyarsa sak ta Nuraddeen d'insa, kallo d'ayazakayi masa kaga banbancin farincikin daya samu yau fiye dana kullum, yaqare zancen yana fad'a mata cewa tabbas duk yanda akayi wannan yaron jininsa ne, amma zai tuntub'i balaraben yaji gaskiyar maganar don shidai jikinsa yabashi hakan.

Murmushi tayi itama fuskarta d'auke da farinciki saboda ganinsa cikin yanayin da tadad'e tana son ganinsa aciki tace.

"To kodai jita jitar da Yusuf yafad'a maku ashekarun baya gaskiyane cewa sunga yarinyarsu?"

"To banida tabbaci akan haka sai naje natuntub'esa tukuna, ada na musanta zancen na Yusuf saboda atunanina bazai yuyu ace anga yarinyarnan kuma akasa sanar damuba a matsayinmu na iyayen mijinta, koba komai muma munada haqqi musan halinda take ciki duk da mungaza wajen nemota, amma yanzu ganin yaron nan jikina yabani kamar akwai wani b'oyayyen al-amari da fushin zuciyar da nayi yasa nakasa saninsa."

"To koma dai meye ALLAH yasa hasashenmu yazamo gaskiya."

"Amin, maman Rashida, Ina suka shigane suda aminina."

"Sunje gidan baffansu gano Inna hawwa? Shikuwa amininka yana d'akinsa yana bacci." Tafad'a tare da qwallawa bashar da suke kira da Abba kira. Amsawa yaron yayi had'e da shigowa da gudu dama tund'azu ya matsu yaji kiran nata saboda yasan amininsa yadawo kuma tabbas yazo masa da wani abun.

"A'a Abba meye haka! Bazakayi tafiya ahankali ba sai kaje kajima kanka ciwo kabar mutane da wahala."

"Nadena Babar mu." Yaron yafad'a tare da nufar inda baffa yake yana dariya, hannu yabasa suka gaisa yana fad'in.

"Sannu da zuwa baffanmu kasiyo mana alewar?".

"Yawwa aminina, nasiyo maka kai kad'ai bada kowa ba." Rungumesa yaron yayi yana kallon nusaiba dake d'an harararsu cike da tsokana tana b'ata rai tace.

"Sufa 'yan matan nawa?, Adenafa yimasu 'yan ubanci akan aminin marar jin magana." taqare maganar tare da kaimasa ranqwashi akai, b'ata rai yayi zaiyi kuka baffa yace.

"Qyale babarku, 'yan matan nata ai sunyi girma da yawa baza'a basu ba, badon yayanku da baya nan ba da yanzu na aurar da Rashida itada zainaba, kaga narage maka abokan takara, ya rage daga asiya sai Bilkisu ko?"

"Yaya zai dawo baffa in Sha ALLAH ko?"

"Eh aminina kunadai yimasa addu'a ko?"

"Eh baffa." Yaron yafad'a baffa yaciro sweet da biskit d'in daya siyo masu yabashi nashi sannan yace yaje yajirasa a waje sutafi gidan baffa Usman.

'yan maganganu suka qarasa da baba nusaiba sannan yafito yariqa hannunsa suka nufi wajen baffa Usman da shima yanzu ya manyanta sosai,

Sun jima suna fira dashi akan zancen da yasanar da baba nusaiba na yaron daya gani tare da baba balarabe daga qarshe suka yanke shawarar zasuje masa a mutum su sake tuntub'arsa zancen Rashida don susan gaskiyar lamarin.

Baffa Ali kuwa ba'a maganarsa don tun shekaru biyar da suka wuce yaje gona maciji ya saresa a qafa har sau biyu, babu maganin daba'a nema masa ba amma ba'a dace ba, gaba d'aya qafar ta sundule masa baya zuwa ko nan da can, a d'akinda baffa yayi jinya ashekarun baya anan shima yake jinya, gaband'aya yayi baqi yarame amma babu wani sauyi da aka samu na halinsa, kullum cikin baqinciki yake na zaman da yakeyi waje d'aya baya zuwa ko Ina, duk iya taimako da kulawar dasu baffa keyi masa baya gani kullum cikin tsinarsu yakeyi, shi baya iya fita ya bid'o idan kuma sun kawo masa Inna ruqayya sai tace baza'a amsa ba tafiso tafita tayo bara da takarb'i abin hannunsu gori yayi masu yawa nan gaba, haka kuwa akeyi, bakunya ba tsoron ALLAH take Jan muneera sufita bara tana fad'in ataimaka mata mijinta ne ke cikin mugun yanayi gashi yabarta da d'iya, 'ya'yanta sunyi fad'a har sun gaji amma taqi bari, Yusuf da har ya girma shima yayi fad'an da rarrashi da ban magana Amma takasa fahimtarsa, idan yaje yayo 'yar buga bugarsa yanemo yakawo masu sai tace baya isarsu, haka ya haqura ya zuba masu ido duk da bai dena abunda yakeyi ba, in safiya tawaye haka zata kama hanya ita da muneera sufita bara tana yimata jagora basa dawowa sai bayan la'asar, abinci ma sai Inna Bilkisu ta samma baffa Ali dake jinya yayita qorafi an bashi kad'an ko yace badon ALLAH aka bashi ba, Kuma hakan bai hana yaci, Inna Bilkisu saidai ta kallesa tagirgiza kai domin tuni tagama d'aukar darussan rayuwa aduniya, acewarta ita yanzu batada lokaci inba nata qara neman kusanci ga ubangijinta ba saboda yanda shekaru sukaja, Amma su ko yaushe mugun nufi, qyashi da kuma hassada basubar zuciyarsu ba, halin da baffa Ali ke ciki idan shi mai hankaline ya isa yad'au darasi aciki domin qarara isgilin da yayiwa d'an uwansa ne ALLAH yamaido masa akansa amma yakasa fahimtar hakan, don ma ALLAH yataimakesa da samun d'a irin yusuf dake da matuqar jinqai da tausayi, akoda yaushe shike tare dashi yana bashi kulawa daidai gwargwado duk da baya yaba masa daga tsiga sai zagi da kuma ganin la'ari.

β€’β€’β€’ β€’β€’β€’ β€’β€’β€’
Baba balarabe kuwa tun ranar da yadawo kasuwa zazzab'i mai nauyi yarufesa, Saida yayi sati biyu bai koma leqawa kasuwa ba saidai su Hassan da hussaini suje, hakan yasa su baffa basu samu yin magana dashi ba, sunso iskosa gida da maganar amma da sukaji zancen bashida lafiya sai suka fasa, little kuwa gaba d'aya karatu ya d'auke hankalinsa, bayada wani lokacin zuwa kasuwa sai baka rasa ba kuma duk yaje sai yashiga wajen baffa, baffa na matuqar jin dad'in irin kulawar da yaron kebasa wanda hakan yaqara saka masa son sanin kowaye shi,

Wata irin shaquwace sosai tsakaninsa da

Please Login or Register in order to submit comment