Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tsorone araina saboda yanda duniyar tamu ta koma."

"Babu komai in sha ALLAH ka gaida iyayen nasu, in sha ALLAH gobe zanzo nadubasu saboda marece yayi yanzu."

"Shikenan Alhaji Amma shi mahaifin nasu ALLAH yayi masa cikawa, mahaifiyarsu kuma anyi nasarar yimata tiyata anciro wasu 'yan biyun" da motar na slow amma alhaji najin haka ya kashe motar yana sallallami kai kace wani shaqiqin sane, yajima yana jajanta abun aransa tare dayi masa addu'a sannan yabar wajen bayan ya bashi complement card d'insa.

Yana barin wajen yanufi inda twins d'in suke zaune agaban motar suna wasarsu hankali kwance yaje yaja hannuwansu ya nufi inda su Abba suke riqe dasu...

Suna isa Abba ya miqa masu hannuwa alamar suje wajensa, da gudu suka isa tamkar sun sanshi ya rungumesu yana kallonsu d'aya bayan d'aya yana jin wani irin sonsu da k'aunarsu nashiga zuciyarsa, kallo d'aya zakayi masu kasan kamarsu sak da mahifinsu tamkar an tsaga kara hasken fatar mahaifiyarsu ne kad'ai suka d'auko, hawaye ne suka zubo masa a idanuwa yagoge had'e da cewa.

"ALLAH sarki batool, Ashe rabon wu 'yannan jikokin nawa yasa kika iya jurewa rabuwa dani bayan kinsan irin tsantsar so da k'aunar da nanuna maki acikin 'ya'yana, wacce har takasa b'oyuwa azuciyata, har kikayi nesa dani ban dena jin wannan qaunar taki araina ba, ubangiji ALLAH ya tashi kafad'unki, ALLAH yabaki lafiya kiga yanda soyayyarki ta dinga lunkuwa a kowace rana cikin shekarunnan da bakya tare dani." Haka Abba yayita suruttansa tamkar wanda yafara zarewa yayinda yaran daya d'ora saman qafafuwansa suke jan d'an farin gashin dake shimfid'e a fuskarsa.

Tuni su uncle h suka kira matansu suka sanar dasu halin da ake ciki wanda nan take family da suka had'u don walimar tarbarsu da Abba ya shirya suka fara koke koke, baran mahaifiyar batool da kad'an yarage itama arasata saboda matsananciyar fad'uwar da tayi a some, tajima kafin asamu ta farfad'o, kuka takeyi sosai tana roqon ALLAH ya sassautawa 'yar tata kuma yajiqan mijinta, nan take duk aka watse jikin kowa a sanyaye, asibitin wasu suka nufa wasu kuma suka wuce gidajensu saboda basu sanar da mazansu ba, kafin kace me tuni asibitin tafara samun halartar 'yan uwa da abokanan arziqin Abba da 'yan uwansa tako ina, duk wanda yaji labarin abunda yafaru saiya zuddarwa da yaran hawaye domin har zuwa lokacin ita batool d'in bata farfad'oba,

Dr sadeeq ne yadawo wajensu uncle akan zancen gawar Abu sumayya da suka buqaci abasu akace sai zuwa gobe idan police d'in da suka tsaya sunzo sunsa hannu, hakan yamatuqar qonawa Uncle Hassan rai da yasa yanata fad'a har saida Abba yabashi haquri shida Dr sadeeq sannan yayi shiru.

Ita dai mahaifiyar batool hajia salmah abu yakashe mata biyu, nafarko damuwar halin da 'yarta ke ciki na biyu kuma maraicin da wud'annan qananan yara har su hud'u zasu fuskanta, tayi farincikin kyauta da kuma ni'imar da Allah yayiwa 'yar tata amma sam damuwa takasa barin haka ya bayyana a fuskarta, ita da mahaifiyar shurahbil ne suka zauna zaman jinyar batool da kuma kula jariranta, yayinda Abba yace matar uncle hussain da kuma abokiyar zaman hajia salmah wacce ake kira da Rabi'atu su zauna gida sukula da yara da hidimar abinci,

Tun daga Abba har su uncle h babu wanda yakoma sakama bakinsa wani abun tun safe, hakan yasa bayan sallar magrib hajia salmah da suke kira da hajia mama ta kallesu had'e da cewa, "ya kamata ace damu daku duka mun fawwalawa ALLAH komai, mudangana da tsarin da yayo mana domin bamusan dalilinsa nayin haka ba, don ALLAH ku daure ku zauna kuci abinci kada kuma wani abun ya sameku."

Wata qatuwar kula tajawo ta mik'awa shurahbil da isowarsa kenan shima yadawo daga masallaci tace, "ungo nan shurahbil je kazubawa iyayenka abincinan suci kuma kaima don ALLAH ka tabbatar ka zauna kaci naka"

"To hajia mama, Ina yarana suke?."

"Kagansu nan har sunyi bacci." Tafad'a tana miqa masa plates da spoons, karb'a yayi had'e da cewa, "yakamata hajia akirawo zainab tawuce dasu gida ta watsa masu ruwa, yau sun matuqar jigata sosai, donma yaro yana yaro ai da sai jikinsu yafad'a masu, amma kingansu nan yau sau uku suna barci suna tashi wannan shine na hud'u."

"Hmmmm! Shurahbil kenan!, ai dolene suyishi, baccin rashine ALLAH dai yajiqan mahaifinsu." ya amsa da amin sannan ya wuce inda ya hangosu acan cikin wata runfa da aka tanada domin patient relatives.

Gaida iyayen nashi yayi tare da qoqarin bud'e kular bayan ya ajiye uncle hussain ya dakatar dashi, "kaje dashi can cikin mota saboda bazan iya ci anan ba sai dai kosu alhaji idan zasu iya su." kallonsa Abba yayi sannan yace,

"Kana tunanin abunda duk baibar kaba zai barmune mu?, Aje dashi duka cikin motar gamunan zuwa." Haka shurahbil ya sake kinkimar kular abincin da plates yakai cikin mota ya d'ibi nasa a plate ya rufe da wani plate d'in sannan yabaro wajen, masallaci yakoma yaci nasa duk da bawani ci yayi ba d'an tsakurane kawai yayi saboda hajia mama data had'asa da ALLAH, badon haka ba bazai iya cin abinci acikin asibiti ba.

Saida ya kwatanta sun kammala ci suma sannan yaje ya d'auko masu lemu da ruwan da a kazo dasu na gora ya kai masu ya kwaso kayan da suka gama cin abincin ya maido wajensu hajia mama.

Sosai Abba yaso yaji takamammen bayani akan lafiyar batool amma hakan ya cutara saboda tsoron yanayin da zai iya shiga, tamatuqar wahala saboda ana gama mata tiyata lumfashinta ya d'auke, kusan likitoci bakwaine suka taru akanta kafin su samo da taimakon ALLAH lumfashin ya dawo, shima d'in da qyar take fiddashi wanda sanadiyar hakanne ake shiga da Oxygen aguje saboda ya taimaka mata, daga lokacin da akayi mata aikin zuwa dare ta shanye tukunya hud'u na oxygen, sai bayan sunga lumfashin nata ya daidaita ne kuma suka fara qoqarin treatment d'in raunin da taji a fuska duk da dai and'an bata emergency care kafin akawota nan. taji rauni sosai sabod duk glass d'in mota ya yanke mata fuska har saida aka ciccire mata wani da ya shige, idanuwanta kad'aine ALLAH ya kare basu samu wata matsala ta sokewa a xahiri ba ko kuma wani internal injury aciki ba, Amma hatta kanta ya bugu sosai wanda Dr odugun ya sanarwa dasu uncle h sai ta farka za'a iya gano cewa bata samu wata matsala acikinsa ba idan anyi gwaje gwaje, kallo d'aya zaka yimata kasan tanajin jiki saboda yanda aka nannad'e mata fuska da bandage ba'a bari kowa yashiga d'akin sai nurses da kuma masu jinyarta suma d'in saida dalili.

Jariran kuwa tunda aka cirosu Dr imaan ta karasu ga nonon mahaifiyarsu suka d'an tsots-tsotsa har yanzu ba'a basu komai ba, sunyi kukan har sun gaji amma Dr tace kawai asa masu drip zuwa gobe tunda har lokacin mahaifiyarsu bata farko ba,

Abba dasu uncle basu bar asibitin ba sai misalin qarfe sha biyu da rabi na dare bayan shurahbil yaje gida ya watso ruwa ya dawo shi da zainab sister d'insa ta d'auki su hassana sannan su Abba suka wuce da ita gida saboda anan shurahbil zai kwana Koda za'a buqaci wani abun....








_*ALLAH KAJIK'AN IYAYEN MU*_πŸ‘πŸ»πŸ˜­
[8/17, 10:18] Billy S Fari: πŸšΆβ€β™€οΈπŸšΆπŸ»β€β™‚οΈ *SANNU SANNU*πŸšΆπŸ»β€β™‚οΈπŸšΆβ€β™€οΈ
πŸ’Ž _Bata hana zuwa..._πŸ’Ž


_WRITTING BY:_ *BILLY S FARIπŸ’Ž*

_DEDICATED TO:_ *BLOOD SISTER'S (AMZAHFAZ)*πŸ’‹

_BESTOWED TO:_ *ZAINAB AL-AMIN (MOM NA'EEM)* AND *AMINA UBA AYUBA (OUM ASHFAQ)*πŸ’ž

*DOMIN FARINCIKINKI SISTER SADIYA ZANGO (MIEMAH)*πŸ’–

*FATAN ALKHAIRI AGAREKU MOMMAH ME NANA HAFSAT (MISS XOXO) AND MAMANA HAFSAT RANO(OUM AFFAN)*❀️

Page___4πŸ’Ž

Suna isa gida zainab tawuce dasu part d'insu yayinda uncle hussain ya ciro wayar batool da aka basu da kuma takardun da alhajin daya kawo su Abu sumayya asibiti ya basu ya mik'awa Abba yana fad'in,

"Alhaji ga wud'annan takardun da wayar fatima"

"Karik'esu hannunka hussain, Amma yakamata ace antuntub'i iyayen yaron nan an sanar dasu halin da ake ciki koba haka ba?",

"Eh hakane gaskiya, dama tun d'azu ake kiran wayar narasa qwarin guiwar d'agawa, bari naba yaya sai ya lalabo lambar wanda yakamata." Mik'a masa wayar yayi ya karb'a tare da fara duba sunayen missed call d'in da yagani saboda yanada tabbaci akan nakusa da su d'inne suka kira, lamba uku ya gani, tafarko ansa gwoggwo, ta biyun kuma sister, sai ta ukun barrister kamal, shuru yayi yana nazarin wacce yakamata ace yakira Abba yace, "malan Hassan lafiya kuwa?."

"Lafiya klw alhaji. Kawai Ina nazarin lambar kdaya kamata inkira cikin ukunnnan da aka yimata missed call dasu, wannan ta farkon Ina tunanin qilan mahaifiyar sace wato surukar ita fatima ta biyun kuma qilan qanwar sace, sai ta ukun wacce nakasa fahimtar waye shi!, gashi dare yayi kada a d'aga masu hankali"

"Malan Hassan kenan! d'aga hankali kuma har na nawa agaresu?, ai tunda suka kirawo wayarsu sukaji basu same suba dole hankulansu su tashi, Ina tabbatar maka da cewa dakyar daga cikinsu in akwai wanda zai iya bacci matuqar Basu samu wani labari akansu ba, ya zamuyi tunda mai faruwa tariga da tafaru, ko ance abari sai gone babu abunda zamu iya canzawa don haka ka kira a sanar dasu shine daidai domin hakan zai sama masu natsuwa koda kad'ance, kaga at least tunda akwai 'yar tazara a tsakaninmu (kano da borno) idan aka sanar dasu tun yau zasu samu tasowa da wuri gobe" Abba yafad'a cike da damuwa, ganin shima gaskiya yafad'a yasa ya danna lambar barrister kamal kasancewar shine namiji aciki kuma shi zaifi iya karb'ar abun cikin kwanciyar hankali duk da dai bai san kowaye shiba, ringing d'in farko bai ida shiga ba yaji yad'aga Kiran da alama jiraye yake da hakan, lokacin shikuma yana part d'insu Abu sumayya don agida d'aya suke amininsa ne sosai wani aikine yakawosa agarin borno shida iyalinsa shine Abu sumayya yabashi wani b'angare daga cikin gidansa ya zauna har zuwa lokacin da zai gama, tunda rana mahaifiyarsa tayi masa waya hankalinta atashe tasanar dashi halin da ake ciki akan rashin samun lambar aminin nasa da takeyi ita kuma ta matarsa idan takira ba'a d'agawa, Nan shima yakira lambarsa bai samesa ba hakan yasa yakira ta batool ita Kuma bata d'aga ba, yanda hankalin mahaifiyar aminin nasa ya tashi tanata kuka yasa d'aya dawo sallar isha'i yawuce wajenta yana rarrashi tare da kwantar mata da hankali amma har tsawon wannan lokacin takasa dena kukan wanda hakanne yasa shikuma yakasa komawa part d'insa wajen iyalinsa,

"Assalamu alaikum" Yaya hassan yafad'a ya amsa masa cikin natsuwa tare da fargabar abunda kunnuwansa zasu jiyo masa, runtse idanuwa yayi cike da rashin sanin ta inda zai fara sanar dashi wannan mummunan awannan lokacin, karb'ar wayar Abba yayi ahannunsa tare da duba lambar sannan yakara a kunnensa had'e da cewa, "da barrister kamal nake magana?." cikin i'ina yace,

"E..e...eh shine."

"Kana magana da mahaifin batool ne wato alhaji Umar fari" wata irin ajiyar zuciya yaji ya sauke had'e da cewa, "Alhamdulilah!." sannan yace dashi, "Masha Allah, Abba ya gidan anwuni lafiya?."

"Lafiya klw barrister kamal, ya.." kafin ya ida abunda zaice cikin zaquwa barrister kamal yace

"Alhaji yasu batool suke!, sun dai iso lafiya ko, saboda tun d'azu muke nemansu awaya bamu samu gaba d'aya hankulanmu sun tashi." Gwaggo najin cewa da mutanen kano ne yake waya ta dakata da kukan da takeyi had'e da kashe kunnuwa tana sauraren yagama waya taji halin da ake ciki, Abba kuwa sai daya nisa sannan yace

"To alhamdulilah don aduk halin da bawa ya tsinci kansa dole yayiwa ALLAH godiya." Wani irin fad'uwar gaba barrister kamal yaji kafin cikin sanyin murya da sarewa yace,

"Hakane Abba injin dai lafiya?."

"Lafiya barrister saidai ALLAH ya jarabcesu dayin hatsari gab da hanyarsu ta shigowa kano, wannan shine dalilin da yasa kika nemesu awaya kuka rasa, wayar batool kuma da muka samu bama cikin kwanciyar hankali tun lokacin shiyasa kukaji ba'a d'aga ba, yanzu haka duk suna asibiti wanda ALLAH mai kyauta da dad'i ya qaddara ita batool d'in saboda yanayin da take ciki anyi mata tiyata don ceto rayuwar abunda ke cikinta anfiddo mata da 'yan biyu macce da namiji, amma shi nuruddin (Abu sumayya) saidai muyi hak'uri domin ALLAHn daya haliccesa kuma yafimu sonsa ya karb'i abunsa." Cikin tashin hankali da kuma razana saboda yanda barrister kamal yaji dirar maganar kamar sakin aradu yasa ya saki wayar tafad'i k'asa yana fad'in "innalillahi wainna ilaihirrajiun, innalillahi wainna ilaihirrajiun" haka yayita maimai tawa na tsawon sakanni kafin ya lura da yanda hankalin gwaggo yatashi cikin rud'ewa tana tambayarsa, "lafiya kamal, meyake faruwa ne, meyasa mu 'ya'yana da kuma jikokina, ka amsa mun kamal meya samesu ne nace?" Sai as lokacin ya tuna da yaran cikin sauri ya daidaita kansa tare da goge hawayen da suka zubo masa yace,

"Kikwantar da hankalinki gwaggo ba wani abu bane." Tare da duqawa ya d'auko wayar tasa da harta mutu,

"Karka yimun qarya kamal kafad'amun halin da suke ciki, dama tunda naji wannan kiran awannan lokaci jikina yabani da akwai matsala, baranma da naji cewa da abbanta kake waya" tafad'a tare da sake fashewa da wani kukan.

Kamo hannunta yayi ya zaunar da ita akan kujera tare da riqo hannuwanta biyu yana kallonta cikin tausayawa yace, "kiyi hak'uri gwaggo bazan b'oye maki komai ba domin waji bine agareni na sanar dake." shuru yayi sannan yaci gaba da cewa "mahaifin batool ne yakira yake sanar dani cewa gab dasu nuradden su shiga kano sun samu accident yanzu haka suna asibiti Kuma a sanadiyar hakan ita batool anyi mata tiyata anciro mata 'yan biyu macce da namiji, don haka suna buqatar addu'ar mu saboda sun d'anji rauni." Sai yab'oye mata zancen rasuwar Abu sumayya saboda tsoron yanayin da zata shiga kafin safe, gashi kuma babu kowa atare da ita sai jidda qanwar nuradden 'yar kimanin shekara goma sha shidda wacce itace batool ke kira da sister, sallallami gwaggo tashigayi tana kuka tana fad'in "Saida nace su haqura da tafiyarnan har sai bayan ALLAH ya sauketa lafiya Amma shauqi da soyayyar mahaifin yarinyar nan yasa suka kasa hak'ura, hazbunallahu wani'imal wakeel, ya Allah ka rangwanta masu halin da suke ciki." Kuka tayi sosai yayinda tunanin halin da zata shiga idan tasan gaskiyar al'amarin yasa barrister kamal Fara zagayen d'akin, message yaga yashigo awayarsa yayi saurin dubawa, still no batool d'ince uncle hussain da yaga Abba yajaye akunnensa shima yana kukan ya karb'a ya sake kira amma yajita switch shine yaturo message kamar haka,

_muyi hak'uri da rashin nuruddin domin dukkaninmu ita muke jira, kuma mugodewa Allah daya bashi wud'anda zasu bishi da addu'ah yaransa duka nanan cikin k'oshin lafiya hadda wud'anda ya bashi ayau bayan shi ankarb'i tashi rayuwar, mahaifiyarsu ce kawai kejin jiki itama rai ahannun ALLAH, da fatar zaka sanarda wannan sak'on ga sauran ahalinsa Kuma sunce gobe in sha ALLAH zasu bada gawar tasa, ALLAH ubangiji yajik'ansa kuma ya gafarta masa_

Awannan karon hatta shi kansa barrister kamal zaune yayi yana sharar k'wallah tare da jinjina girman izza da kuma iyawar ubangiji, yakarb'i rayuwar Abu sumayya alokacin da yabawa 'ya'yansa rayuwar zuwa duniya, ya tsara al-amarinsa tayanda ajalinsa ya riskesa adaidai inda yake so bayan shekaru bakwai, wasu zafafan hawayene suka zubo masa aransa yana cewa, "Tabbas ALLAH baya barin wani don wani kuma duniya ba abakin komai take ba, wanda ya d'auka da zafi zai b'ata lokacinsa batare daya ankara ba mutuwa tazo tayi gaba dashi, kana naka ALLAH yariga daya gama tashi tuntuni, kayita hauka kana qirgawa kanka shekaru batare da kasan mutuwa na gab da d'aukarka ba, kayita hauka kana kumfar baki akan qanqanen abu daga qarshe ALLAH yasa azo azare ranka, lallai duk wanda ya shiryawa zaman duniya to tabbas yayi ganganci domin duk tsawon sjekarun da ALLAH ya ibar masa to da sannu zasu qare mutuwa ta riskesa saboda duk nisan abu da SANNU SANNU yake qarewa, girman iko na ALLAH zakaga yanzune zaka rabu da mutum sai kaji ba zato ba tsammani ance maka yamutu, don haka duk musulmin k'warai dole ya farka yasan cewa ita mutuwa gaskiya ce kuma idan lokacinka yayi duk gimanka, duk matsayinka ko mulkinka zata riskeka aduk inda kake kuma aduk akowane lokaci, babu ruwan Allah da cancantar ka wa'adinka nayi za'a zare maka rai."

_ubangiji Allah yakarb'i rayukanmu Muna musulmi kuma mumunai na k'warai, yajiqan wud'anda suka rigamu gidan gaskiyaπŸ‘πŸ»πŸ˜­_

Yajima awajen zaune har gwaggo ta gama kukanta taje ta d'auro arwala tadawo, kallon agogo tayi taga har k'arfe 1:25 na dare yayi tace

"Kamal katashi kaje ka kwanta iyalinka najira, hak'uri zamuyi murok'i ALLAH da yabasu lafiya kaji ko?" Nisawa yayi tare da cewa, "to gwaggo." Sannan ya tashi zai fita jiki a sanyaye, har yakusa fita ta sake cewa,

"Kamal basu yimaka zancen ko awane hali yaran nasu suke ba?."

"Sunan lafiya gwaggo sunce babu abunda ya samesu"

"Alhamdulillah, to saida safe" tafad'a tare da saka hijabinta sannan ta shimfid'a abun sallah ta tayar...






*ALLAH KAJIK'AN IYAYEN MUπŸ‘πŸ»πŸ˜­*
[8/17, 10:18] Billy S Fari: πŸšΆβ€β™€οΈπŸšΆπŸ»β€β™‚οΈ *SANNU SANNU*πŸšΆπŸ»β€β™‚οΈπŸšΆβ€β™€οΈ
πŸ’Ž _Bata hana zuwa..._πŸ’Ž


_WRITTING BY:_ *BILLY S FARIπŸ’Ž*

_DEDICATED TO:_ *BLOOD SISTER'S (AMZAHFAZ)*πŸ’‹

_BESTOWED TO:_ *ZAINAB AL-AMIN (MOM NA'EEM)* AND *AMINA UBA AYUBA (OUM ASHFAQ)*πŸ’ž

*DOMIN FARINCIKINKI SISTER SADIYA ZANGO (MIEMAH)*πŸ’–

*FATAN ALKHAIRI AGAREKU MOMMAH ME NANA HAFSAT (MISS XOXO) AND MAMANA HAFSAT RANO(OUM AFFAN)*❀️

_Jinjina agareku masoyana, fatan alkhairi da kuma fatan tabbatuwa cikin amincin ALLAH da yardarsa akoda yaushe Kuma cikin kowane hali shine addu'ata agareku, tabbas naga karamci, halacci, yarda da kuma zallar soyayya agareku, nayi farinciki da kuma murna ganin irin kyakkyawar tarba dana samu daga wajenku akowane group wanda hakan yatabbatar mani da cewa nid'in takuce akoda yaushe, ngd ngd ngd sosai ALLAH yadubi zuciyar kowanenku yabiya masa da buqatunsa na alkhairiπŸ‘πŸ» Ina farinciki da kuka nuna mani cewa yanda nake ikirarin cewa ina sonku FILLAH kuma kuna so na FILLAH😍 in sha ALLAH zan zage damtse wajen ganin kun ilmantu kuma kun nishad'antu da wannan littafi,πŸ˜…fatana shine ku juri bina daki daki tare da qarfafamun guiwa, ni kuma in sha ALLAH nayi maku alqawarin da *SANNU SANNU* Zaku samu tarin fad'akarwa da kuma farinciki marar misaltuwa acikin wannan labarinπŸ₯°MUCH LUV FILLAH na wajena😘❀️_

Page___2πŸ’Ž

Aguje matashin saurayin ke tafiya saboda yanda Abba ke faman reren kuka tare da azazzalarsa akan yayi sauri, kusan minti ishirin da biyar suka d'auka kafin su isa cikin garin kano,

Hanyar asibitin suka nufa zuciyoyinsu cike da fargabar abunda zasu riska, suna isa ko daidaita parking basuyi ba Abba yafara kiciniyar bud'e gambun motar da sauri saurayin ya danna lock d'in motar had'e da cewa,

"Haba Abba! Me kake shirin yi hakanne, karka manta babu abunda muke iya canzawa daga qaddarar da ALLAH yatsaro agaremu da kuma sauran bayinsa, kabi ahankali in Sha ALLAH babu abunda ya samesu." ko jin abunda yake fad'a Abba ba yayi sai faman kica niyar bud'e motar yafita kawai yakeyi amma yakasa saboda lock d'in daya saka mata, ganin haka yasa wanda d'azu Abba yakira da hussaini ya dafa kafad'ar matashin had'e da cewa,

"Shurahbil bud'e masa kaji ko!."

"Amma uncle h...." Bai qarasa ba yayi saurin d'aga masa hannu da sauri shurahbil yacire lock d'in ba tare daya sake cewa komai ba suka fito tare da bud'ewa Abba da tuni yakai maqurar b'acin rai da hasala kawai yanayin da yake jin kansa acikine yasa bai tsaya bi takan saba, fitowa yayi har yana neman fad'uwa sukayi saurin riqesa ba tare da sunce dashi komai ba suka nufi emergency ward, girgiza kai shurahbil yayi tare da bin bayansu hannunsa na riqe da 'yan biyun da tunda sukaji tsayawar motar suka tashi daga baccin da sukeyi atare,

Har sun kusa shiga emergency d'an uwan uncle hussain wanda shine hassan Kuma mahaifin shurahbil ya juyo yace, "katsaya daga waje kafin muji halin da suke ciki, idan zai yuyu ma ka koma cikin mota da yaran nan, idan akwai buqatar kazo zamu nemeka."

Babu musu yakoma cikin motar shida yaran tare da ciro wayarsa yajawo game d'in race na motoci yanayi, dama aikinsa kenan aduk lokacin daya kad'aita shi kad'ai, yaran na ganin haka duk suka dawo daga inda suke zaune baya zuwa gaba inda yake zaune suka haye masa jiki suna kallo shi kuma mahaifinsa ya ida qarasawa can cikin emergency ward d'in tare dasu Abba suna tambayar mutanen da sukazo daga k'auyen da accident d'in yafaru, sunfi minti goma shabiyar kafin su samu su had'u da d'aya daga cikin wud'anda suka kawo su Abu sumayya d'in wanda shikad'aine ya tsaya awajen, sauran kuwa tuni suka wuce bayan sunga likitocin sun karb'esu, shima d'in saida wannan bawan ALLAHn yaje yakirawo police tukuna suka amshesu.

Hannu yabasu suka gaisa kafin yace, "kune iyayen bayin ALLAHn da mukazo dasu?." Cikin rawar murya Abba ya amsa masa da "eh bawan ALLAH mune, Ina zamu ganesu ne, suna ina?." Shiru mutumen yayi kafin ya d'an nisa fuskarsa cike da damuwa yace, "likitoci nakan duba su amma suna buqatar addu'ah sosai, shi namijin sun wuce da shi ICU (internatal care unit) ita kuma macen suntafi da ita gyni emergency." Shiru yayi tare da ciro gilashin idanuwansa yasa gefen babbar rigarsa ya goge k'wallan da suka zubo masa sannan yaci gaba da cewa, "dukkaninsu suna cikin wani mawuyacin halin da addu'armu kawai suke buqata, amma har yanzu ina kallon yanayin da naga baiwar ALLAHn nan aciki kafin suwuce da ita, abun gwanin ban tausayi yanda abun dake cikinta ke faman motsi Yana neman taimako yayin da ita d'in takasa d'aga ko d'an yatsanta da zaya iya bashi koda k'warin guiwa ne na second d'aya, Ina addu'a ubangiji yadubi karamci da tausayi irin na uwa alokacin da rauni yasa takasa bawa d'an dake cikinta taimako da yakawo masu tallafi da kuma agajinsa domin ceto duka rayuwarsu."

Wani irin jirine ya d'ibi su uncle hussain jin yanayin da 'yar d'an uwan nasu ke ciki daya sasu ja da baya tare da fad'awa zaune saman kujerun dake bayansu saboda tsananin tashin hankali suna furta kalmar, "innalillahi wainna ilaihirrajiun." dama shi Abba tunda sukazo suka samu suka lallab'asa ya zauna saboda bawata lafiyar qafafune keda shiba balle yajuri iya tsayuwa na tsawon lokaci, lokacin da yaji wannan labarin sai kawai ya sake fashewa da wani sabon kukan da dama tun d'azu yake yin abunsa saboda rashin sanin awane hali gudan jinin tasa take ciki, kalmar shahadar shima ya Fara maimaitawa had'e da cewa, "Amantu billahi, qadarallahu wama sha'a fa'ala." cikin tausayawa mutumen ke kallonsu kafin yace, "hak'uri zakuyi tare da addu'a kuma kusamu ku matsa inda suke nasan gab ake da anemi 'yan uwansu, ni ina kan hanya tane ta zuwana garin minna, dama tsammanin jiran isowarku anan kamar yanda d'an uwana ya sanar mun awaya shine dalilin daya tsaidani anan saboda nasan kuna isowa dole direct nan (emergency) zaku zo, don haka ni zan wuce, ga wud'annan takardun acikin aljihun namijin aka tsincesu" yaqarasa maganar tare da miqawa Uncle Hassan takardun, har zai tafi saiga wani Dr da shine suka karb'i case d'in anan emergency ya iso wajen had'e da kallonsa yace

"Ahhhh, ranka ya dad'e baka wuce bane?"

"Eh Dr sadeeq Amma yanzunnan zan tafi in Sha ALLAH, wud'annan sune patient relatives na mutanen da muka kawo" yabashi amsa tare da nuna masa su Abba dake zaune kamar ruwa yacisu.

"Masha Allah, ranka ya dad'e to ALLAH ya kiyaye ya kuma saka da alkhairi"

"Amin ya rabbhi" yafad'a tare da bashi hannu sukayi musa baha, kallon su uncle h yayi tare da cewa "duk wani abu daya kamata wannan Dr zai taimaka maku insha ALLAH, aminina ne sosai don haka ku kwantar da hankalinku, pls Dr you should consider..." har lokacin suna riqe da hannuwan juna.

"I will in sha ALLAH" yabashi amsa sannan suka yimasa godiya ya wuce, Dr yace sutashi yayi masu jagora zuwa can ICU d'in sannan suje gyni emergency, juyowar da zasuyi wajen Abba sukaga wayam babu kowa a mazauninsa, hankalinsu tashe saboda sanin yanayin da yake ciki suka fara duddu basa acikin wajen basu ganesa ba, cikin tashin hankali suka yiwa Dr bayanin ko wayeshi da matsayinsa ga patient d'in yace, "karku damu, inaga yakasa jurewane yanufi can, kuzo mutafi can d'in."

A b'angaren Abba kuwa kamar yanda Dr yafad'a kasa jure zama awajen yayi hakan yasa yamiqe lokacin da suke magana ba tare da sun lura ba yakamo hanyar gyni emergency

Please Login or Register in order to submit comment