Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yace a'a tabari yafara watso ruwa tukana sai yaci abincin shida d'an uwansa.

Shi kuwa baffa Ali zaune yayi bakin rumfa ya aza kansa saman iccen da yake tokarawa (crutch) yana kallon shiyar tasa kaca kaca ba wanda ya gyara asalima Inna ruqayyar bata nan tana wajen yawon baransa, gaba d'aya sai yaji ya muzanta awajen wasu zafafan hawaye nazubo masa afuska, tunani ya shigayi lokacin da yana Alinsa yanda Inna ruqayya ke nan nan dashi sai gashi yau ya rasa madogara, gashi da ransa Amma komai nagidansa yafi qarfinsa, abinci ma sai in Inna ruqayya tabashi shi ko yusuf idan yaje yanemo ya kawo masa, amma ita ko mutuwa zaiyi bata bashi acewarta tunda yasamu damar da zaije yayi bara ataimaka masa amma yaqi to ita kam bazata sake ci dashi ba yana zaunensa gida, haka yayita tunane tunanensa har baffa Usman yafito wanka Inna Bilkisu ta shimfid'a masu tabarma acan zaure takai abincin da ruwa ta ajiye masu had'e da 'yar redion da baffa Usman ke sauraren labaran duniya,

Kallonsa yayi had'e da cewa.

"Ali taso muje muci abinci ko?" Ya d'ago kai ahankali had'e da cewa.

"Naqoshi Usman, ko kad'an bana sha'awar cin komai yanzu."

"To taso muje can ko kuma nazo nakai maka ruwa kaima ka watsa ko karage gajiyar kafin ruqayya tadawo."

"A'ah bari dai in shiga ciki." Yafad'a yana tsille da qafa yana qoqarin shiga cikin rumfar, saurin d'auko masa iccen da yake tokarawa dashi baffa yayi had'e da taimaka masa ya daidaita shi sannan yace.

"Ali kacire damuwa mu zauna mu natsu musamo mafita, damuwar da kake qara cilla kanka aciki bafa zata haifama komaiba sai wahala, tunda dai har kayi nadama to kayi Imani da qaddararka mai kyau da marar kyau, in Sha ALLAH zaka samu mafita."

Nan ma kukan ya sake fashe masa dashi saida yayi daqyar yasamu suka koma zauren, Inna Bilkisu dake tsaye gefe ta shiga girgiza kai cike da tausayinsa, Wai yau alin da tasani ne fitinanne da hatsabibanci ke russunawa duniya haka, lallai rayuwar duniya ba komai bace kuma batada tabbas ko kad'an, sanin yana matuqar son fura yasa tashiga d'aki ta d'auko dawon da tasaye d'azu tunda taji yace bazai iya cin abincin ba ta dama masa takai masa acan zauren ya d'ago kai cikin sanyin murya had'e da cewa.

"Sannu balkisu, nagode ALLAH yasaka maki da alkhairi."

"Amin ya rabbi, ka d'aure kasha furar ko kad'an ce, ba a biyewa damuwa azauna da yunwa domin had'uwa sukeyi waje d'aya su illata mutum."

Har zata fita yakira sunanta tadawo, ya sake fashewa da kuka tare da roqonta tayafe masa abubuwan daya yimata don ALLAH, da yake mace ce mai raunin zuciya nan take sai itama tafashe da kukan tana fad'in.

"Ali nayafe maka duk abunda kayi mani wanda kasani da wanda baka sani ba duniya da lahira, kuma Ina roqon kaima ALLAH ya yafe maka ya dawo da hankalin iyalinka agareka ta zauna ta kula dakai kaima."

Girgiza kai kawai yayi don yasan inna ruqayya bazata tab'a hankalta ba sai ranar da duniya ta hankaltar da ita, "nagode sosai Bilkisu ALLAH ya albarkaci yaranki yakaresu da rud'in duniya."

Da ita har baffa Usman suka amsa da amin sannan tabar wajen, kallonsa baffa Usman yayi had'e da cewa.

"Ali idanfa kana tuna abubuwan da suka riga suka wuce to tabbas ka dingi kuka kenan har iya qarshen rayuwarka, Ina baka shawara kayi haquri ka godewa ALLAH daya ganar dakai kafin lokaci yaqure maka."

Saida ya goge kwallan da suka zubo masa sannan ya saki wata ajiyar zuciya had'e da cewa.

"Dole na zubda hawaye Usman, wallahi aduk lokacin da naga kuna hidima dani da yaran nan dake wajenku duk irin cin kashi da kuma mutunci da nayi maku sai naji waninirin nauyi da kunya sun dabai bayeni, nacutar daku amma gashi kunata kyautata mani, wlh da mutane zasu gane da sun daina cutarwa ga mutanen dake Shire da kyautata masu, don wannan abun da kike yimani shine mafi girman horon da kuke hukunta zuciyata dashi, zaifi sauqi ace cutar da mutum akayi kamar yanda ya cutar da adinga binsa da kyautatawa da kuma alkhairai domin yafi shiga kunya da nadamar da zuciyarsa zatayita d'awainiya da abubuwan daya aikata."

"Kamanta da komai, ni babu sauran zarginka ko kuma tsanarka araina, fatana ALLAH yayafe maka laifinka kuma yabamu mafita, din natabbata shi kad'aine zaisa yaya yasake baka damar jingina dashi akaro na biyu duk da dai tsananin b'acin rai yasa yakai ga yanke maka wannan hukunci amma inada yaqini akan zai sauko kuma ya yafe maka shima."

"ALLAH ya qaddara hakan, Amma girman laifina na cancanci hukuncin da yayi mani kuma koda ya gagara yafemun bayada laifi." Yaqara fashewa da wani kukan.

Haka sukaci gaba da maganganunsu baffa Usman naqara yimasa nasiha akan illar biyewa son zuciya da kuma sharrin duniya da rud'in shed'an har aka kira sallar magrib sukayi arwala suka wuce masallaci, bayan angama sallah baffa Usman yamiqe had'e da kallon baffa Ali yace.

"Bari naje wajen Yaya naga halin da yake ciki ina tsoron kar shima yashiga damuwa irin yanda kake ciki!"

"Shikenan bari nad'an gincira kafin akira sallar isha'i, seka dawo."

"To madallah, amma karka kwanta domin babu kyau bacci tsakanin sallar magrib da isha'i, annabinmu yayi hani ga hakan, zaifi kazauna kiyita yimasa sakati da zikiri da kuma hailala har akira sallar ko kuma ka d'auko qur'ani kayi tilawa, bari namaza naje na dawo."

Yana kaiwa nan yafice da sauri don baya son ya rasa jam'i shi kuma ya d'auko qur'aninsa yafara tilawa kamar yanda d'an uwansa ya shawartai.

Koda baffa Usman yaje gidan baffa ya iskoshi tsakar gida 'ya'yansa duka sun zagayesa anata fira ana dariya, murmushin jin dad'in ganinsa haka babu abunda yasamesa yayi had'e da qarasawa ciki yana fad'in.

"Allah ya taimaki uban d'iya yaja da tsawon rai." Yana wani d'aga hannu tare da dudduqawa kamar yanda fadawan sarki keyi gaba d'aya duk sukasa dariya hadda baffa tare da miqa masa hannu sukayi musabaha sannan yace.

"Ai kaine uban d'iya malan Usmanu ko yau kabar mani d'iyan baka so."

"Inaaa.. Yaya nakai ga manyan d'iya haka tubarkallah kace in barmaka, ai Abba kawai ne banayi shida aka yimani rashin kara akansa."

Gaishesa suka shigayi d'aya bayan d'aya yana amsawa kafin akawo ga Abba yamiqa masa hannu yana fad'in.

"Assalamu alaikum baffa barka da dare." Lokacin yanada shekara goma sha biyu.

Dariya baffa yayi had'e da kallon baffa Usman daya kama hannunsa yariqe gam yana dariya yace.

"Aminina kenan, gaisuwarsa ba irin tasu bace."

Nan shima Baffa Usman yayi zaunensa akaci gaba da firar dashi har aka kira sallar isha'i yamiqe da sauri had'e da yimasa sallama sannan yabar gidan, yaso yayi masa maganar baffa Ali amma yanda yaga farinciki kwance afuskokin gidan yasa yafasa don kada yarusa masu shi izuwa damuwa aransa yana yabawa 'yar 'yar uwar matar tasa data iya gusar da yanayin damuwar da yayan nasa yafita dashi d'azun alokaci d'aya, tabbas Babu abunda yakai matar qwarai samun kwanciya da cikakkiyar natsuwar namiji aduniya..

Bayan anqare sallah duk suka nufi gida suna tafe suna shawara akan maganar da baffa Ali yafad'a cewa ya samu mafita akan maganarsu ta d'azu, Inna ruqayya zasu tuntub'a tunda tare sukayi komai da ita ya tabbata ita bazata manta wajen ba, damuwar d'aya ce shine daqyar in zata amince tagwada masu wajen tunda tasan sharad'in da malamin tsibbon nasu yabayar, daga karshe dai baffa Ali yace abarshi da ita zai san yanda za'ayi ta gwada masa don kai tsaye idan aka fuskanceta da maganar bazata yarda ba, da haka suka shiga shiga ya tadda ita zaune tsakar d'aki da gani bata dad'e da dawowa wajen baran ba ta bubbud'e qafafuwa ta zube kud'ad'en da tasamo tana qidaya, sallama yayi har sau biyu bata tanka shiba sai da yayi ta uku tukuna ta d'ago kai cikin tsiwa irin ta fitinannun tsofaffin matannan tace.

"Kai nifa Ali ba nison tsarguwa, dolene amsa sallamar koko dai dolene, in banda gulma baka tashi dawowa ba sai yanzu da kaga ina kikkimtsa abunda ALLAH yabani, to ALLAH yasani idan ma da biyu kayi ko shishi (sisi) bazan baka ba, badai bazaka bara ba? To ni kuma bazan baka shishi (sisi) naba, in shigowa zakayi ka shigo bana son talla kawani hankad'e mani labule, dama haqoranta wasu duk sun fita shiyasa bata iya fad'an sisin da kyau take cewa shishi, batare daya tanka taba ya wucikkewarsa ya zauna gefen gado yana kallonta har tagama qidayar kud'inta sannan tajawo wata leda taciro lemu da biredi sai kuma nama atakarda tahauci abunta, qille bata raga ba har saida ta cinyesa tas batare data sammashi ko kad'an ba sannan tabuga gyatsarta tamiqe tana yimasa habaice habaice, dama shi kota bashi bazai karb'a ba don yasan haramun ne tunda roqa tayi ba bata akayi ba, kuma shi roqo baida kyau awani nassima an haramta yinsa inba da wata babbar lalura ba.

So yake ya d'auko mata zancen amma ganin abubuwan da takeyi yasa yarasa ta inama zai fara, can dai yayi qarfin hali ya daure cikin yanayin da bazata kawo komai ba yace

"Nikuwa ruqayya wai a inane muka binne maganin nan.", juyowa tayi daga kan gadonta data haye had'e da cewa.

"Lafiya kake tambayata?, Ina ai tare mukaje ko?"

"Eh wlh, shaf namanta ko inane, kinsan anyi gine gine a wajen sai nake ganin kamar anginesa.?"

"Hehehe ai nasani, tuntuni nake roqon ALLAH yasa wani ya gine wajen yanda shikenan babu yanda za'a iya tonesa amma har yanzu wajen na nan fili ba'ayi gini wajen ba, shiyasa kullum nake sa ido awajen kar wani d'an ta tsinanniya yaje yatone manashi muboni mu lalace."

Cikin wani farincikin daya kasa b'oyuwa a fuskar baffa Ali ya taso daga d'an kishin gid'awar da yayi had'e da cewa.

"Da gaske ruqayya?, Kai Alhamdulillah wlh naji dad'i, a Ina ne?, Wane wajene ruqayya."

Binsa tayi da wani irin mugun kallo da zai tabbatar maka data fara zargin wani abu akansa kafin tace.

"Kai Ali, kallanni nan Kar nake kallonka, wato kaje 'yan iwan naka su lallashe maka baki don kawai sun taimaka ancire maka wannan 'yar qafar taka data gama rub'ewa shine kakeso a tonikke maganin, ka manta da wannan karon ba qafa zaka iya rasawa ba rayuwarka ko tawa gaba d'aya ko?, to wlh saidai su mutu bazan fad'i inda wajen yake ba, ban shiryawa mutuwa yanzu ba don haka kaji dashi can dakai dasu d'in, iyyeee! Wato sun turoka tunda karasa qafa d'aya bari su ida sallama rayuwarka don baqar mugunta da mugun nufi, to aniyarsu tabisu wlh, na maji dad'i daka mance don Ina baqin cikin lalacewar rayuwarka yanzu Ali, kazama raqumi da akala sai yanda akayi da kai wato?."

Taqarasa maganar had'e da fashewa da kuka tanaci gaba da cewa.

"Allah ya isa ga idrisu, da usmanun da baliksu, da waccan tsinanniyar ta tsallake (baba nusaiba) da waccan mokad'ad'd'iyar tsohuwar data nad'e waje d'aya ita Bata mutuba ita Bata rayuba, duk ita taja mana shiga wannan rayuwar da muke ciki yanzu data haifa tsinannen d'an daya zama silar guntule qafarka, wlh indai Ina raye su dashi har abada sai dai su haifo wani."

Shiru baffa Ali yayi yana kallonta cike da b'acin rai da wata irin tsanarta da bazai iya kwatanta adadin yawanta azuciyar saba, wato ita ba'ayi mata ALLAH ya isaba ita keyi har tana tsine masu, murmushin da yafi kuka ciwo yayi tare da cewa.

"Duniya ce tafi bagaruwa iya jima ruqayya, yanzu ke ko aya bazata isheki ba ganin yanda nakoma nida Yaya hawwa kisan cewa annabi ya faku? Yakamata wannan qiyayyar da tsana da kuma d'aukar fansa ta tsaya haka, yakamata kimanta da komai kitubarwa ALLAHnki kamar yanda mukayi nida yaya, kiroqi bayin ALLAHn nan da muka zakinta suyafe maki kafin ta ALLAH takasance akanmu, ni daine abokin tarayyarki acikin wannan adawar da mukeyi, Kuma natubarwa ALLAH don haka kema ina roqon ki d'aki tuba mutaru mugyara laifin da muka aikata ko ALLAH ya dubemu da idanuwansa na rahama."

"Ali! Kanka d'aya kuwa, shin kaji me kake cewa?, to narantse maka da ALLAH indai don yaron nan yadawo kake yimun wannan wa'azin to wlh tuba ba yanzuba,"

Arazane baffa Ali yace.

"A'uzubillahi minashshaid'anir rajim, ruqayya idan baki tuba yanzu ba yaushe kike son tuba?, Kin manta da rayukanmu ba ahannunmu suke ba, kafin kituba ALLAH zai iya zare rayuwarki, Haba don ALLAH kiwatsar da wud'annan makaman yaqin naki idanko ba haka ba zamu farraqa tsakanin ni da ke don yanzu ni nagane gaskiya da kuma kuskuren dana tabiye maki muna aikatawa."

"Ahaf, kanka akeji ni bacci nakeji, indai kuskurene ai kai nabiyewa har nayi shi ba kace kabiye mani ba."

"Naji tunda ni kika biyewa to nagane gaskiya kema kigane gaskiyar don ALLAH kifad'a mani wajen da muka binne maganin, in Sha ALLAH Babu abunda zai samemu, idan ma yasamemu ai kinga zamu mutu muna masu baraa'a daga laifukan da muka aikata, ko banza ai dama zamu mutu ba tabbata zamuyi ba aduniyar."

Tsabar batada lokacinsa duk wannan surutan da yakeyi saidai yaji hansarinta, bubbuga kafad'arta yayi yana cigaba da roqonta amma tayi biris dashi tamkar da dutse yakeyi.

Haka dai suka kwana babu wani Abu daya samu daga wajenta, da safe ma yadinga roqonta amma fir taqi tankasa ma balle yasamu amsa daga wajenta hakan yasa ransa b'aci sosai yarufeta da maseefa akan lallai lallai saita fad'a masa ko kuma yau babu inda zata fita da sunan bara yakama bakin qofar ya tare, hakan ko kad'an bai girgiza taba balle yasa tadamar da kanta saima cigaba da shirinta da tayi hankali kwance tana gamawa tanufi bakin qofar had'e da cewa.

"Jaye kabani waje ko in ingijeka kasan qafa d'aya ke gareka."

"Ni zaki ture ruqayya?"

"Kana wasa, to Bari kagani..."

Ai kafin takawo baffa Usman dake fitowa daga cikin d'aki don tun jiya yanajin yanda suka kwashe da ita ya qaraso aguje yana fad'in.


"Kul...wlh karki kuskura ki ingije Mani d'an uwa ko hukuma tashiga tsakaninmu, shashasha sakarya da batasan ciwon kanta ba."

Yaqare maganar tare da jaye baffa Ali gefe dake faman qwalla, zata fice tana suruttai yace.

"Karka batta ta tafi, ita kad'aice mafitarmu kuma tunda arziqi bazaisa tafad'i komai ba akaita ga hukuma dole su zasusa tanuna wajen da kansu, don ALLAH Usman kada kubari tafita ku kira ko 'yan sandane...."


Ai kafin yaqarasa rufe baki Inna ruqayya najin yace 'yan sanda ta arta dana kare duk da bawani gudu bane tunda tayi tsufan da batada qarfin da zatayi gudun sosai.

Tunda tafita bata sake dawowa gidan ba har aka buge kwana hud'u saboda tsoron kada 'yan sanda su kamata, kullum saidai taje can wajen wani shago cikin tasha takwana, baffa kuwa dama koda sukaje masa da zancen d'aukowa Inna ruqayya 'yan sanda cewa yayi a'a su qyaleta bayason 'yan sanda sukoma shiga sha'anin gidan saboda ya fahimci hakan naqara rura wutar tsana acikin zukatan 'yan uwa wanda dama yanadaga cikin matsalar data haifarda sasu d'aukar fansa akan d'ansa Nuraddeen don haka aqyaleta, yana nan yana addu'a kuma yasa ayi masa sosai idan da rabon zaingana da d'ansa to ko yaushene zai dawo garesa, hakama ya sanarda little komai yace yatashi tsaye da addu'a sosai akan mahaifinsa in sha ALLAH zai dawo nan kusa bada jimawa ba, little yayi kuka sosai daga baya yakoma ga ALLAH yana fad'a masa damuwarsa, kullum cikin sadaka yake ga gajiyayyu tare da taimakon mabuqata da nufin ko meye ALLAH ka yayewa mahifinsa.

Shi kuwa Yusuf dama baya nan balle yasan meke faruwa, yana can wajen karatunsa a.b.u zaria a matakin qarshe duk da baiso ma cigaba da karatun ba saboda atunaninsa yayi girman da daqyar in zai iya amma baffa yace dole sai yaje yayi saboda yarage masa ganin matsalolin dake cikin gidan da damuwa kuma yasamu ingantacciyar rayuwar da idan yayi aure bazasu samu matsaloli sosai ba tunda yanada iliminsa.

Baffa Ali kuwa ko ajikinsa rashin dawowarta gida don yanzu ko ganinta baya sonyi balle yanemi sanin inda take, muneera ma batasan wainar da ake toyawa ba har aka buge wud'annan kwanakin hud'u,

Ita kuwa Inna ruqayya abunda bata sani ba ashe wasu 'yan iskan tasha na nan nayi mata kallon mahaukaciya suna dakonta ko yaushe, haka wata qatuwar mota duk marece sai tayi parking inda take zama an miqo mata kud'i kusan dubu uku, wannan dalilin yasa taqara yin zaunenta acan aganinta idan takoma gida bazata samu wud'annan kud'in da masu gidan arziqi kamar yanda take fad'a suke bata ba.....






*ALLAH KAJIK'AN IYAYENMU*πŸ‘πŸ˜­
[11/14, 22:52] Billy S Fari: πŸšΆβ€β™€οΈπŸšΆπŸ»β€β™‚οΈ *SANNU SANNU*πŸšΆπŸ»β€β™‚οΈπŸšΆβ€β™€οΈ
πŸ’Ž _Bata hana zuwa..._πŸ’Ž


_WRITTING BY:_ *BILLY S FARIπŸ’Ž*

_DEDICATED TO:_ *BLOOD SISTER'S (AMZAHFAZ)*πŸ’‹

_BESTOWED TO:_ *ZAINAB AL-AMIN (MOM NA'EEM)* AND *AMINA UBA AYUBA (OUM ASHFAQ)*πŸ’ž

*DOMIN FARINCIKINKI SISTER SADIYA ZANGO (MIEMAH)*πŸ’–

*FATAN ALKHAIRI AGAREKU MOMMAH ME NANA HAFSAT (MISS XOXO) AND MAMANA HAFSAT RANO(OUM AFFAN)*❀️

Page___97πŸ’Ž

Yau baffa Ali na bacci yadinga ganin kansa a inda suka binne maganin shida Inna ruqayya wai yanata tonon wurairai ita kuma tana masifa dashi tana rufewa, yana kaiwa bayan wani ginin wasu shaguna da akayi kusan qwara ashirin jere da juna yafara tonon wajen tana turesa sai ya tashi yaje yaci gaba da tono wajen ita kuma ta sake turesa haka sukayi tayi yana tonon wajen tana hanasa, can yaga kamar wata bulala daga sama ta sauko a laftawa Inna ruqayya ajiki tafad'i awajen some shi kuma yaji sautin muryar da bazai iya tantance kowaye ba ance yaci gaba da tono wajenne zai cimma maganin da yardar ALLAH.

Firgigit sai ya farka daga baccin da yakeyi yaga ashe mafarkine yakeyi amma aransa yatabbatar da wannan wajen da akace ya tone shine inda suka binne maganin, bako shakka isharace akeyi masa kuma da yardar ALLAH kome zai faru yau sai ya tone wajen, goge zufan da yabi duk ya jiqe masa jiki ya shigayi yana karanto addu'o'i a bakinsa don mafarkin yamatuqar tayar masa da hankali, gashi lokacin qarfe uku nadare balle yaje ya sanar da d'an uwansa, dole ya haqura yakoma ya kwanta yanata istigfari da hailala da kuma tasbihi daga kwancen da yake har aka kira sallar asuba, yana jin baffa Usman ya qwanqwasa masa qofa ya amsa tare da jawo iccensa (crutch) wanda yake dogarawa yamiqe yanufi bakin qofar yabud'e yafitoa.

Bayan angama sallar asuba ya zauna masallaci yayita tasbihinsa har rana tafito sannan yanufi gida, yana kaiwa bakin qofar gida ya tarar da baffa Usman shida baffa suna magana wacce akan d'an uwannasu ne baffa Usman yake roqon yayi haquri ya yafe masa, nan yafad'a masa cewa tun ranar da abun yafaru ya yafe masa amma baya buqatar alaqar komai tahad'asa dashi ko shekara nawa za'ayi har sai sun warware qullin da sukayiwa Nuraddeen.

Baffa Ali na kawowa baffa ya miqama baffa Usman hannu sukayi sallama yabar wajen tun kafin ya ida qarasowa, binsa kawai yayi da kallo sannan ya qaraso wajen ya miqawa baffa Usman hannu suka gaisa fuskarsa cike da damuwa, ganin haka ya shiga kwantar masa da hankali har yake sheda masa cewa ai d'an uwan nasa ya yafe masa dama yafad'a masa b'acin raine yasa yayan nasu fushi dashi har ya d'au matakin daya d'auka akansa, gashi yanzu ya sauko abunda kawai yarage sukoma su rarashi Inna ruqayya tahaqura hakan shine zai ida daidaitawa tsakaninsa dashi.

Baffa Ali yajima yana zubarda qwalla kafin ya d'ago kai ya sanarda baffa Usman labarin mafarkin da yayi jiya had'e da cewa.

"Na tabbata wajenne Usman kuma zanje na tono wajen in Sha ALLAH, roqona d'aya agareka idan nura da Rashida sun dawo kace su yafemun, suyafemun abunda nayi masu, nayi nadama sosai, bansan abunda zai faru ba, zan dawo koko ta ALLAH zata kasance akaina."

Duk inda jikin baffa Usman yake yau saida yayi sanyi sosai, yamatuqar ji tausayin d'an uwan nasa domin gaba d'aya ya sare ma rayuwarnan ta duniya, yayi tuba taubatan nasuha tare da miqa wuyansa gaba d'aya,

Qarfafa masa yayi tayi sannan yace sushiga cikin gida su, bayan sun gama karyawa sukayi arwala tare sannan suka nufi wajen tono inda maganin yake,

Gaba d'aya zuciyar baffa Ali ta dake haka ya dinga shiga cikin juji har suka isa bayan shagunan, runtse idanuwansa yayi don yatuno daidai wajen kamar yanda ya gani a mafarki sannan yabud'e a hankali yanaci gaba da taku har ya isa wajen, kallon baffa Usman yayi had'e da cewa.

"Kaga wajen nan in Sha ALLAH.."

Bai jira amsar da zai bashi ba yafara saran wajen yana, wasu irin sautukka ya soma ji kala kala Wanda azahirin gaskiya d'aya d'ago kai ya kalli d'an uwan nasa shi bayajin komai, hakan yasa yaqara cire tsoro aransa shima yayi kamar baiji komai ba, sannu ahankali yafara cin karo da wasu abubuwa masu kama da mutane aciki suna yimasa gizo a fuska cikin ramen wani irin hayaqi ya turnik'e wajen had'e da wari Mai mugun d'oyi, jiri ne yafara d'ibarsa amma cikin qarfin hali yaci gaba da tono wajen har yakai ga qullin maganin, ji yayi kansa ya wani sarawa duniyar najuya masa yafara karanto addu'o'in faya sani ga baki, wata irin dariya yaji ansaki mai qarar gaske had'e da amsar addu'ar da yakeyi anaci gaba da karantawa. "Muma musulmi ne kamarka, muna sallah muna addu'o'i don haka baza kaci galaba akanmu ba har sai ka amshi saka makonka daidai da laifinka, bazamu barku ba kamar yanda kuka nememu to tabbas sai alqawarin ALLAH ya tabbata akanku kamar yanda mummunar makomarsa zata tabbata akanmu." Yaji an fad'a cikin kunnuwansa tare da kecewa da wata irin muguwar dariya, kan yace wani abu yaga wata baqar mummunar halitta cikin sigar wani baqin hayaqi tana fitowa daga cikin ramen tare da nufatosa daga zaunen daya fad'i tun d'azu dafe da kansa, da sauri yasa hauyar dake hannunsa ya ida ciro maganin wanda kusan tare suka fito da wannan halittar ta lullub'esa sai dai baffa Usman dake gefe yaga iska Mai kamar guguwa tana nad'ed'e niya cikin jikin baffa Ali dako ganinsa bayayi sai dai muryarsa da yajiyo cikin wahalalliyar qara yana fad'in "Usman ka fiddo ashana ka qona wannan qullin maganin kuma kafasa tukunyar dake cikin ramin nan."

Cike da tsoro jikin baffa narawa yafiddo ashana dama sunzo da ita ya cinnawa maganin sannan yasa hauyar yaje cikin ramin ya faffasa tukunyar dake ciki bakinsa d'auke da addu'a yanayi yana kallon iskar data nad'id'iye baffa Ali, Yana gama fasa tukunyar yaga iskan yawani cure waje d'aya tare da duddun qulewa yayi can gefen daji yana gudu da qarfi shi kuma baffa Ali yashe awajen ko motsi bayayi wasu quraje duk sun feshikke masa tun daga fuska har zuwa tafin qafa, da sauri ya jefar da hauyar agefe ya qarasa wajensa jikinsa na rawa ya tallabosa yana jijjigarsa yana kiran sunansa amma ko yatsansa baya motsi, cikin qarar murya yace.

"Ataimakeni..."

Ko baki bai rufe ba sai ga mutane sun iso wajen, ganin yanayin da suke ciki yasama wasu shakku akan meya kawosu wajen, qilama wani abun zasuyi ALLAH ya mayar masu da abunsu don haka suka tafiyarsu, mutum biyu kad'aine suka tsaya suka riqowa baffa Usman baffa Ali aka tallabosa zuwa titi sannan suka tari napep aka sashi ciki baffa yayi masu sannan mai napep d'in yaja suka nufi asibiti dashi, tun kafin ya qarasa isa yakira baffa ya sanar dashi komai.

Baffa na tsaye gefen gado yayi saurin zaunawa saboda wani irin jiri da yaji ya d'ebesa.

Istigfari ya shigayi ALLAH yasa son kansa baisa asanadiyar rayuwa d'aya ba surasa har rayuka biyu, a wani gefe na zuciyarsa kuwa hamdala yayiwa ALLAH da akaci nasarar tono maganin yasan koba komai in Sha ALLAH d'ansa zai dawo hankalinsa kuma ya tuna dasu.

Kamar antsikaresa yayi saurin miqewa yabar gidan ya nufi asibitin da baffa yafad'a masa cewa can suka nufa.

Yana isa ana fitowa da baffa zuwa d'akin da zanyi jinya na 'bangaren maza wato (male medical ward) don har angama dubashi babu abunda ke damunsa, 'yar doguwar sumace kawai yayi sai qurajen da suka feshikke masa a jiki kuma Alhamdulillah ya farfad'o daga sumar har ansa masa drip bacci ya d'aukesa.

Zuba masa idanuwa sukayi suna kallo cike da tausayinsa, tabbas duk bawan da ALLAH keso yakan nufesa da tubamawa kura kuransa kuma yaqara masa da jarrabawa don tabbatar da imaninsa, fatansu d'aya shine ALLAH ya yafi kura kuransa albarkacin tubar da yayi kuma taubatan nasu da tasashi sadaukar da rayuwarsa don jadda tubarsa ga ubangijinsa.

Sudai likitoci sunyi masu bayanin babu wata matsala kuma in sha ALLAH kurajen dake jikinsa ma zasu b'ace saboda na

Please Login or Register in order to submit comment