Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yiwa ALLAH godiya akan ni'imar da yayi mana takarb'uwar addu'o'inmu da yayi kaima ya nuna maka naka jinin aduniya, sai gashi kuma ALLAH yayi nashi ikon akansa, ganin hakan yasa naquduri cika wannan niyar tawa ga iyalinsa, nan ma ALLAH bainufi hakan tafaru ba dalilin kasantuwarsu aqarqashin inuwarmu, don haka yau Ina son ALLAH da mala'ikunsa da kuma ku 'ya'yana kuzama sheda ko bana raye na mallaka wannan gidan halak malak ga jikansa don cika wannan alqawarin dana d'aukarwa kakansa cewa zan bashi wannan gidan tun farko,"

"Dady mun sheda hakan uabangiji ALLAH ya saka maka da alkhairi ya lullunka maka da gidan aljannah," Shakur yafad'a yana dariya tare da jujjuya nasa takardun gidan dake hannunsa, duk da dai faruk bai tanka ba da zaran ka kallesa yanayin fuskarsa zai tabbatar maka da cewa baiji dad'in hakan da mahaifinsa yayi ba.

Takarda da biro dady yaciro yayi rubutu akai sannan yafara ba Dr yace yasa hannu shida 'yan uwansa, bayan sun sa ya amshi takardun yamiqawa little dake zaune tamkar andasa shi, banda hawaye babu abunda ke zubo masa saboda ganin irin gatar da dady yayi masa tamkar yanda yayiwa 'ya'yansa, wannan bawan ALLAH wane irin mutunne shi da kokad'an babu qyashi da hasada acikin al'amurransa, yana karb'a yafashe da kuka hannunsa na kakkarwa,

"A'a Dady ban cancanci haka ba daga wajenka, abubuwan da kukayi mana nida mahaifiyata da kakannina kawai sun wadatar don ALLAH kabar takardun gidannan."

"A'a! Little meye haka?, Wannan kyautar tun asali cancantar kakan kace shiyasa tazo hannunka, shi kuma alkhairi danqone idan kayishi watarana zai dawo maka, bamusan me gobe zata haifar ba, abunda muka bayar shine namu wanda Kuma mukayi amfana dashi sharar banzane, rabon bawa kuwa duk inda yake bai wucesa don haka kawai ka amsa kayiwa ALLAH godiya domin shine yabaka ni kawai nazamo silane sai kayi mani addu'ah"

Godiya yayita zuba masa tare da sake miqawa Dr takardun ya amsa ya sanya masu albarka tare da miqo masa yana fad'in.

"Karb'a amma kafin nan bari nima amatsayina na uba agareka infad'a maka irin abunda dady yafad'awa Shakur d'insa, wannan gida nakane halak malak kaje idan akwai gyare gyaren da zakayi kayi kafin lokaci yayi, idanma bakada ra'ayinsa zaka iya sayar dashi kasai wanda kake buqata babu wanda zaice kayi laifi."

Gaba d'aya dady dasu shakur sukasa dariya, sun d'an jima awajen suna tattaunawa akan maganar auren kafin dady yasallami kowanensu yana maijin farincikin sauke wannan nauyin alqawarin daya dad'e dashi acikin zuciya har na tsawon shekaru, faruq baiji dad'i ba ko kad'an amma da yaje wajen ammie yana qunquni ya sanar da ita fad'a tayi masa sosai tare da nuna masa cewa idan mutum ya tallafi bayan wani to shima ALLAH zai tallafi bayansa, alkhairi kuwa danqone baya fad'uwa qasa banza, sucire qyashi da son duniya suyi koyi da mahaifinsu wajen taimakon wanda bayada, musamman shi faruq d'in don ta tabbatar Dr yariga daya gama hawa kyakkyawar turbar mahaifinsa shi kad'aine yamzu kansa ke rawa wani lokacin don haka yatsaya yayiwa kansa fad'a domin duniya ba wajen zama bace, Dole ya sauka daga dokin naqin daya hau ya bata haquri tare da tabbatar mata da cewa zai kiyaye.

Rashida kuwa har gida ta isko dady da guntayen hawayenta tayi masa gdy bisa kyautar da yayiwa little, umma kuwa ba'a magana don haka ta tashi cikin dare tayita zuba masa addu'a bayan tayi masa godiya, gawata kulawa ta musamman da riritasa data qarayi tamakar qwai a faranti.

••• ••• •••
Acikin sati ukun da aka kwashe kuwa banda qara cikakken bincike akan bayanin dasu baffa suka basu uncle h babu abunda sukayi saboda maganar da yayan nasu yazo da ita cewa wai hayar mutanen da sukazo amatsayin iyayen little akayi, sunyi hakanne don qara tabbatar da zancensu baffa akan hukuncin da suka gama yanke shawarar d'auka akan yayan nasu, kafin sukai ga zartar da hakan kwatsam saiga wani Abba yakawowa batul akan shi zata aura nan da sati biyu kuma ba gudu ba ja da baya, wayyo ranar batul qaramin hauka kawaine batayi ba, tayiwa mahaifinta kuka tayi masa magiya kamar ranta zai fita amma yaqi saurararta, kwana d'aya da zancen aka kawo lefe set d'in akwati uku, duk inda ran su uncle h yake ya b'aci don gaba d'aya bai bid'esu ba shi kad'ai ke sha'aninsa.

Haka batul ta dinga kuka tare da isko su uncle h tana riqon qafafuwansu akan kada subari abbanta ya aura mata wanda bata so amma saboda b'acin rai akan abunda yayi masu suka kauda kai akanta, ganin yanda sukayi biris da ita yasa ta iske iyayenta mata tana roqonsu akan su dakatar da mahaifinta kada yayi mata auren dole nan ma suma suka qyaleta, matar uncle Hassan ce da bazata iya jurewa kukan nataba tana hawaye tariqo hannuntata nufi d'akin Abba da ita, yana zaune falo tayi sallama suka shiga lokacin yana waya har dasu qyaqyatawa da alama yanajin dad'in firar wanda suke waya dashi, yana gamawa ya d'ago kai yana kallon matar uncle hassan d'in da hawaye ke kwance a fuskarta yace.

"Lafiya hajia Naga kamar hawaye afuskarki? Meyake faruwa?"

Nuna batool data durqusar masa agabansa tayi had'e da cewa.

"Bakaga wud'annan hawayen na wannan yarinyar ba data kwashe kwanaki tana zubarwa akan abunda kanada ikon tsayar mata dasu tahanyar dakatar da qudurinka sai nawa?, Haba Yaya wannan wace irin zuciyace da kai da bata tausayawa abunda ta dad'e tana iqirarin tana so?, Naroqeka kayiwa ALLAH da girmansa ka amincewa yarinyar nan ta auri wanda take so don ALLAH yaya?"

"Shegen?, Marar asali."

"Kodai waye shi kabarta ta aura, ai ita zata zauna dashi bamu ba, sannan idan ma shegenne to meye laifinsa?, Iyayensa sune masu laifi kuma sune shegun bashi ba, katausaya mata kabata zab'inta."

Saida ya hard'e qafarsa d'aya akan d'aya sannan yace.

"Ni kuma nawa zab'in fa?."

"Ka haqura dashi mana, haba yaya don ALLAH kada karusa mata rayuwa."

Cikin b'acin rai yamiqe tare da katsawa matar uncle h tsawa yace.

"Ke wace da zakice nahaqura da zab'ina da nake ganin shine daidai akan 'yata, tuntuni ban rusa mata rayuwa ba sai yanzu da take ganin duk gatar da nayi mata bata yimata ba saboda tana butulu.?"

Cikin kuka batool ta had'a hannyenta had'e da cewa.

"Abba ba butulci bane nayi maka, abunda zuciyata kawai keso nake qoqarin fad'a maka kamar yanda abaya kafad'a mun cewa in sanar dakai dik wani abu aduniya da naji zuciyata naso zaka nemomin, Abba kayi mani duk wata gata aduniya da nake tunanin babu wani mahaifi da zai iya yiwa 'yarsa ita kuma ban rena hakan ba, ayau Ina sake roqonka a karo na ba adadi daka cikashe mani wannan gatar da kakeyimun tahanyar bani zab'ina, wlh Abba nagartaccen zab'i nayi maka, Nuraddeen d'an halak ne ba shege ba, yanada asali yanada tarbiya da duk wata nagartar mutuntaka, don ALLAH kada kahanani samunsa Abba domin bayan kai shi kad'aine ke iya bani irin kulawar daka bani, Ina sonsa Abba Ina son sa fiye da tunani, hanani shi zai iya dakatar da bugun zuciyata da kuma lumfashi na, Abba kaji tausayina ka aura mani shi ina matuqar qaunarsa sosai."

Taqarasa maganar tana kuka tare da d'ora kanta asaman qafafuwansa daga tsayen da yake, hanb'areta gefe yayi har saida kanta yabugi qarfen center table d'in dake tsakiyar falon yafashe da sauri matar uncle hassan tajuyar da kanta gefe had'e da runtse idanuwa tana fad'in.

"Shikenan, zaka iya kasheta ai 'yar kace kai kake da hasarar hakan," sannan tabar d'akin itama tana sharar qwalla.

Karo tayi da hajia mama ta d'auko abinci a try bakin qofar d'akin taja burki tana share hawayenta tace.

"Yanzu bazaki iya dakatar dashi daga qoqarin illata maki 'ya da yake shirin yiba?, kinfiso kirasata tahanyar biyewa zab'in da mahaifinta yayi mata."

Cikin dauriya don ita kad'ai tasan irin damuwar dake cunkushe acikin azuciyarta hajia mama tace.

"Ai ita tajawa kanta, mezanyi mata bayan addu'a, mahaifintane yanada iko akanta, ni kuma matarsa ce dole inbi duk wani umurni nasa, don haka ALLAH yayi mata magani kuma yarabata da wahala, gadone tariga tayisa, yanda baza'a iya saukar dashi ya sauka ba haka itama baza'a saukar da ita ba ta sauka,"

Tana gama fad'ar haka tawuce ciki daidai lokacin yana fad'in.

"Koda zaki mutu kina dawowa batool ni bazan tab'a d'aukarki naba wanda bayada asali ba, yarage naki kihaqura da zab'inki kibi nawa saiki zauna lafiya, idan Kuma kikace a'a to tabbas hawayenki zasu qare aduniya ba tare da ni nabi naki zab'in ba, shashashar banza da wofi."

Ko kallon gefen da suke hajia mama batayi ba taje ta jere abincin akan dining table tana qoqarin maida qwallanda suka zo mata,

Har zata fita dady yace.

"Zo kifice Mani da ita ad'aki kafin na kakkarya ta."

Dawowa tayi tasa hannu tariqo batool zata miqar da ita batool tariqe qafar Abba d'aya tana fad'in.

"Wayyo Abbana, nice batool d'inka, katuna lokacin da kake sakani dariya idan zaka kaini makaranta Ina kuka kana fad'amun cewa inyi shiru kukan da nakeyi na tab'a maka zuciya!, katuna lokacin da idan aka sakani kuka anan gidan kake cewa da ab'ata mani rai kafison a b'ata maka naka!, Abba ka tuna cewa tun ina qarama kasaba mani da nema mani duk abunda nake so kuma ka riqemun shi yanda bazani tab'a kukan rasa shiba, Abba don ALLAH kada yau da kanka ka nosantani da abundanake so, kada ka bari narasa Nuraddeen domin daidai yake da rasa rayuwata."

Hannunsa yasa yacire hannunta daga riqon da tayi masa ya juya mata baya, haka hajia mama tayita jan hannunta tana kuka tana kiran Abbaaa.

Duk da yanajin damuwa aransa na kukanta amma yafiso yayita saurarensa akan dawwama da zuciyarsa zatayi cikin damuwar aura mata wanda take so da yake yiwa kallon shege da bayada uba.

Ganin abbanta naci gaba da shire shiren auren nata gashi fushin zuciya yasa su uncle h fita batunta yasa batare da sanin kowa ba ta tsere tabar garin tanufi borno, kai tsaye gidan Dr ta sauka wajen Rashida mahaifiyar little don dama tasan gidan, suna zaune ita da Fatima tashiga bakomai ahannunta tana daga ita sai kanta tana kuka, sun matuqar firgita ayanayin da suka ganta don tarame tayi baqi tamkar wacce batada galihu aduniya.

Tana zuwa ta zube agabansu tana fad'in.

"Gwaggo don ALLAH da girmansa kije kiyiwa mahaifina bayani, gwaggo bazan iya rayuwa babada Nuraddeen ba, shi kad'ai nake so kuma zan iya bashi rayuwata, mahaifina, mahaifiyata, baffannina, gaba d'aya sun juya mani baya, sunnkasa karantar zuciyata balle susan irin zafi da qunar da take yimani, kitaimaka kifad'awa abbana kece mahaifiyar little, kafad'a masa mahaifinsa naraye wataqil zai..."

Bata qarasa ba sanadiyar fad'uwar da tayi daga durqushen da take tasuma, kallo d'aya zakayi mata kafahimci irin jigatar da tayi.

Ruwa Fatima ta d'ebo ta yayyafa mata tare da tada ita zaune, d'ago kai tayi tana kallon Rashida da tayi tagumi da dukkanin hannayenta hawaye na zubar mata saboda tsananin tausayin yarinyar, wato haka ita rayuwa ta gada kowane irin mutum da tasa jarabawar rayuwar, ayau taqara jin zafin mahaifin little a ranta domin duk shine silar faruwar wannan abun ga yaronta da kuma wacce yake so.

Ganin batool naqoqarin yin magana yasa tagoge hawayenta had'e da dakatar da ita da hannu, cikin sanyin murya tace da ita.

"Kina son little?" Da sauri batool tashiga kad'a kai kamar qadangaruwa had'e da cewa.

"Eh.."

"Zaki iya zama dashi aduk yanayin da take?"

"Eh?"

"Kingamsu da cewa shid'in d'an halak ne gaba da baya?"

"Eh."

"Wane yaqini kike dashi akansa?"

"Zai kula dani har qarshen rayuwarsa."

"Wace tabbaci zaki bani akan soyayyar da kike yimasa?."

"Ban saniba, amma nasan Ina sonsa domin ALLAH, kuma Ina qaunarsa har zuwa fitar lumfashina naqarshe!."

Wata ajiyar zuciya rashida tayi had'e da cewa.

"Shikenan, share hawayenki, kina sonsa domin ALLAH, shima haka, don haka narantse da wanda lumfashina yake a hannunsa a matsayina na mahaifiyarsa Ina tabbatar maki da cewa matuqar ALLAH nanifin alkhairi acikin aurenku kamar yanda akoda yaushe nake roqa maku to tabbas babu abunda zai hana ku auri junanku, sai dai tabbas bazaku gujewa tsarin qaddarorin da za'a jarabceku dasu aciki ba, girman imaninku da yaqininku ga ALLAH shi zai tseratar daku daga kaidin dukkanin masu kaidi, kisa aranki in Sha ALLAH, ALLAH zai kawowa soyayyarku d'aukin da bazaku tab'a rabuwa ba, ni inajin haka ajikina."

"Yanzu dai ba wannan ba ke gwaggon yara, inashi little d'in? Yakamata akirashi."

Fatima tafad'a tana kallon Rashida.

"Kwana uku kenan shima yana d'akinsa baida lafiya sanadiyar kiran da tayi masa ta sanar dashi halin da ake ciki, na hanasa bayyana hakanne saboda kada yatayarwa da dady hankali, kina ganin yanda shekarunsa keja bai kamata acika kai masa duk wani abu da zai jefasa cikin damuwa ba, mubi komai a sannu ALLAH zai kawo mafita"

Yanda Rashida ke maganar cikin kwarin guiwa shiya dad'a kwantarwa da batool hankali domin itace last hop d'inta akan soyayyarta shiyasa tayo wajenta atunaninta nacewa ita kad'aice zata iya gamsar da mahaifinta, sai gashi tasamu qwarin guiwa da gamsuwa daga wajenta, murmushi Fatima tayi had'e da cewa.

"Anya kina ganin hakan zai yuyu?"

"Sosai kuwa, ai SANNU SANNU bata hana zuwa...."

"Shikennan! Amma dai taci abinci ta watsa ruwa sai a sanar dasu dady da Dr kokuwa?"

"A'a basai anfad'a masu ba, zansa shi da kansa ya d'auketa yamaida ita gidansu."

"Anya Rashida kina ganin hakan yayi?."

"Eh mana, hakan shine daidai."

Bayan tayi wanka taci abinci wanda sharabonta dashi har ta manta Fatima takira little awaya tace yazo tana son ganinsa,ba'afi mintuna biyar ba sai gashi yashigo tamkar a hura sa ya fad'i cikin 'yan kwanaki uku kacal da yayi acikin damuwa, yana d'ago kansaya hango batool d'insa zaune kusa da fatima tana wasa da 'yan yatsun hannunta.

Da sauri yaqarasa wajen gaba d'aya ya manta ko wacece awajen had'e da cewa

"Gimbiya, waya kawoki nan?, ya akayi kika zo nan?, Meya sameki haka gimbiya?."

Kasa maganatayi saboda wani nauyi da takeji, sab'anin d'azu da Bata masan kalaman da take fad'a ba saboda tsananin halin da take ciki,

"Kice dani wani abu mana, dama nasan bazaki barni ba, pls gimbiya kiyi..."

Bai qarasa maganar ba Rashida dake shigowa lokacin tace.

"Rufe mana baki marar kunya, agaban maman taka kake wud'annan suruttan?"

Sai alokacin ma yatuna tana wajen cikin rashin qwarin jiki yaje ya zauna qasan qafafuwanta yana kallon batool qasa qasa.

Murmushi Fatima tayi had'e da cewa.

"Dama na kirakane saboda kazo kaganta ku gaisa, idan kun gama gaisawa sai kaje kawatso ruwa ka d'auki motar Dr ka maida ita gida."

'Dago kai yayi kamar zaiyi kuka Rashida tace.

"What ever the situation is..Dole yau d'innan kaje ka maida ita wajen iyayenta kaji nafad'a maka." Sannan suka miqe sukabar falon yarage daga shi sai ita.....





*ALLAH KAJIK'AN IYAYENMU*👏😭
[11/14, 22:52] Billy S Fari: 🚶‍♀️🚶🏻‍♂️ *SANNU SANNU*🚶🏻‍♂️🚶‍♀️
💎 _Bata hana zuwa..._💎


_WRITTING BY:_ *BILLY S FARI💎*

_DEDICATED TO:_ *BLOOD SISTER'S (AMZAHFAZ)*💋

_BESTOWED TO:_ *ZAINAB AL-AMIN (MOM NA'EEM)* AND *AMINA UBA AYUBA (OUM ASHFAQ)*💞

*DOMIN FARINCIKINKI SISTER SADIYA ZANGO (MIEMAH)*💖

*FATAN ALKHAIRI AGAREKU MOMMAH ME NANA HAFSAT (MISS XOXO) AND MAMANA HAFSAT RANO(OUM AFFAN)*❤️

_Gaisuwa tare da fatan alkhairi agareki, haqiqa kulawarku agareni ta musammance da bazan tab'a iya mantawa daku ba, *NANA RUKAYYA GUMMIEY, DOTA HADIZA ZAINU (KUBRA), NAJIDA ALIYU🐒, MUM NUSAIBA, TEEMAH M SANI, HAFSAT HASSAN USMAN, SA'ARBUKAR RABI'U CE, ABLAH SORPEEEY, UMMUL ADNAN, ZAINAB GARBA FARUK, SHAMA HALLIRU, UMMI ABIL BAITY, XEEEE, JAMILA YUSHA'U* Ina godiya bisa qwarin guiwa da kulawar da kuke yimani dama littafina, fatana amincin ALLAH da kuma yardarsa ya lullub'eku kuma yabaku aljannah da rahamarsa👏Fillah Ina matuqar girmama karamcinku agareni, ngd ngd ngd sosai 😍🤝_

Page___87💎

Abba bai zame ko Ina ba sai tsakar falon hajia mama wato mahaifiyar batool, kira yadinga qwala mata tamkar wacce tayi wani laifin, tafito daga kitchen riqe da ludayin miya da alama girkine take qoqarin qarasawa, kallo d'aya zakayi mata ka hango tsantsar damuwar da take qoqarin b'oyewa daga cikin idanuwanta, wanda ko shakka babu kasan hakan yasata zubarda qwalla ba adadi lura da yanda idanuwanta suka kumbura, cikin sanyin murya yace.

"Gani alhaji lafiya?"

"Bana buqatar jin wannan tambayar daga bakinki, Ina so daga rana mai kama tayau karki sake kisake barin yarinyar nan tashigomin part domin nadad'e da cireta daga cikin 'ya'yana, don haka dole tanisanta da duk wani abun daya shafeni kuma yazamo mallakina, wannan umurnine nafad'a maki, qoqarin sab'ashi kuma zai iya jawo b'annar rayukka tsakanin ni dake, ban haifi d'iyar da zatazo tana walaqantani agaban idanuwan duniya ba kuma har in zauna da ita, wlh bazai yuyu ba, ta zab'i wani akaina duk irin gatar dana bata saboda kawai cikar nata burin, tayi fatali akan cewa wane irin hali zan iya shiga a matsayinta na 'ya tilo mafi soyuwa araina don haka taji tayi duk yanda take so nacire hannuna a al_amurranta, nayi qoqarin ganin nabata gata tare da inganta rayuwarta amma takasa fahimtar hakan, amma shikenan taje, in dai duniyace ta isheta riga da wando, in Sha ALLAH da SANNU SANNU..."

Bai qarasa ba tayi saurin d'aga masa hannu idanuwanta na hawaye tace

"Ya isa haka, ya isa haka nace, bazan ja akan duk wani hukunci da zaka yankewa 'yarka ba, amma Ina so kasani zanyi maka biyayya iya gwargwadon yina amatsayina na matarka saidai Ina roqonka kadaka aibatamun 'yata agabana, domin hakan zai iya jawo duk girmamawa da kimarka da nake gani su zube, idan kace zaka koreta agidanka bazan hanaka ba matuqar zata samu cikar burinta, idan kace indena kulata zan dena matuqar farinciki da kuma addu'a ta natare da ita, amma bazan iya yin shiruba matuqar zaka cutar da ita ta lafuzzan bakinka dake iya aibata mani ita nahar abada agabana domin yin hakan kuskurene kuma illoline masu yawa da zaka jawowa yarinyata, don ALLAH da girmansa kayi haquri kayafewa 'yarka idan zaka iya idam kuma bazaka iyaba Ina roqon ALLAH daya tsare mani ita kuma ya albarkaci rayuwarta yakare mani ita ga shiga dukkanin baqincikin duniya dana lahira, no bana ganin laifin yarinyata kokad'an domin kaine kad'orata akan wannan tarbiyar, don haka fushinka bazaisa na d'au fushi da itaba, saidai zanyi qoqarin dakatar da ita ga dukkanin abubuwan daka fad'a tare da bin umurninka akan wud'anda basu sab'awa ubangijina ba."

Tana gama fad'ar hakan tajuya ta shigewarta kitchen taci gaba da aikinta, wayyo Allah yau ina wuta Abba yakad'ata, tana jinsa yana bambaminsa da fad'ace fad'acensa tayi tamkar ma bata jiyosa ba, don izuwa yanzu yafara kaiwa qarshen haqurinta.

Su uncle h kuwa gaba sukasa batool da little sukayi masu fad'a sosai akan yanda suka tsanantawa kansu soyyayyar junansu dake nema tajefasu cikin mawuyacin hali har suna lurar dasu cewa idan sun kasa jurewa arabasu lokaci na zuwa da ALLAH zai d'auki ran d'aya yabar na d'aya, shikenan sai d'ayan ya kasa rayuwa saboda an d'auke ran d'ayansu? Yakamata su sassautawa ransu yanayin son da sukeyiwa juna izuwa tubalin rayuwa bisa qaddaruwar kyakkyawar qaddara ko akasinta akansu domin hakan shine zaisa su iya canye duk wata jarabawar da ALLAH zai yimasu, kallon batool uncle Hussain yayi had'e da cewa.

"ke kuma ina son kisani cewa kuskurene mai girma bijirewa zab'in iyaye matuqar mai nagartane, haka kaima Nuraddeen taya mai laifi aikata laifinsa shima kuskurene babba domin ALLAH ya haramta sab'awa iyaye."

Gaba d'ayansu banda hawaye babu abunda ke zuba ga idanuwansu saboda jin kalaman dake fitowa daga bakinsa, wani irin tsorone ya ziyarci zukatansu akan rashin sanin ko wane hukuncin zasu zartar masu lura da irin nasihohin da suke yimasu, sun tabbata duk abunda suka fad'a gaskiyane amma taya zukatansu zasu amince sukarb'i wannan gaskiyar dakeda matuqar d'aci azuciyoyinsu, suna wannan tunaninne sukaji uncle Hussain yaci gaba da cewa.

"Sai dai kuma shi fiyayyen halitta kuma annabin rahama yayi mana hani da muyiwa 'ya'yayenmu auren dole sannan yaqara mana da cewa idan wanda muka aminta da addininsa da d'abi'unsa to mu aurar masa dashi, idan mukaqi kuwa hakan zai jawo fitina da fasadi mai girma a doron qasa, bisa wud'annan hujjoji yasa muka zab'i mu aurar daku ga junanku, domin fifita umurnin manzon ALLAH s.a.w akan na yayanmu saboda kaucewa abunda ya tsoratar mana, badon haka ba wlh tallahi kunji na rantse maku koda rayukkanku nafita suna dawowa bazamu tab'a barin ki sab'awa mahifinki ba, bazamu tab'a bari kicutar da zuciyarsa ba saboda ra'ayinki domin muna sonsa fiye da soyayyar da kuke yiwa junanku, saidai son da mukeyiwa manzonmu yasa dole mu ajiye soyayyar da muke yimasa muyiwa ALLAH da mansonsa biyayya."

Kallon little yayi idanuwansa cikin nasa yace.

"Shin ko kashirya kanada muhalli mu aurar maka da batool."

Tun kafin yarufe baki little yashiga kad'a masa kai had'e da cewa.

"Eh uncle."

"Yaushe?"

"Yau..." Little yabashi amsa tamkar anqwato muryar tasa da qarfi tafito, hakan yasa su uncle h sakin murmushin da Basu tashi yiba, ba ko shakka yamatuqar basu dariyar da Saida uncle Hassan yakasa tsaida murmushin nasa yakoma dariya, yana dariyar yace.

"Anya malan Nuraddeen kashirya ayau d'innan? Halama so kake mu d'aura maku aure kawai kawuce da matarka?.

Murmushi ya shigayi yana sosa qeyar kansa saboda wata kunya da yaji ta lullub'esa, baima san ya akayi ya furta hakan ba sai yanzu da uncle ya tambayesa, murmushin itama tayi kanta na duqe qasa tana kallonsa.

Dariya irinta manya uncle Hassan yayi don yana kalle dasu kafin yace.

"To kayi haquri, bazamu d'aura maku aure ayanxu ba domin kada ka d'auka cewa 'yarmu batada gata, batool da kake gani 'yar gatace gaba da baya fiye da yanda kake tsammani saboda haka yanzu kahuta kaci abinci sai kawuce gida, in Sha ALLAH da kanmu zamu nemi iyayenka tunda ka shirya nan da sati biyu sai a d'aura aure idan ALLAH ya yardar mana."

Wani irin murmushi yasaki, lokaci d'aya suka d'ago kai shida batool suna kallon juna tare da yin hamdala acikin zuciyoyinsu, babu ko shakka ayanzu sunada yaqinin cewa sunfara tako matakin nasara nafarko wajen cika burinsu, murmushin itama tayi sannan tamaida kanta qasa, haka su uncle suka cigaba da fira dasu wacce rabinta kusan duk nasihohine masu ratsa zuciya akan auratayya suka yimasu, kafin uncle Hussain yace batool tashiga cikin gida takawo ma little abinci da ruwa, sosai shikam little yasaki jikinsa dasu uncle h sukasha firarsu har tadawo d'auke da tray abinci wanda tanan suka sake fahimtar wani Abu akansa tare da yabawa nagartarsa da Kuma tarbiyarsa.

Tana shigowa su uncle h suka fita sukabar falon yarage daga ita sai shi, Saida tafara zuba masa ruwa a cup yasha sannan tazuba masa abincin a plate ta tura masa agabansa tare da komawa gefe tayi zaune tana kallonsa, tankwashe qafafuwansa yayi tamkar mai shirin d'aukar karatu tare da matsowa da abincin kusa dashi yafaraci, Saida yayi kusan cokali uku tukuna ya d'ago kansa had'e da kallonta yace.

"Gimbiya ke bazakici abincin bane?"

Girgiza masa kai tayi tana kallonsa alamun taqoshi sai shima yature plate d'in dake gabansa had'e da cewa.

"Shikenan Nima naqoshi."

Yafad'a had'e da qoqarin miqewa daga inda yake, da sauri tasauko daga kan kujera tana fad'in

"A'a'ah...don ALLAH kazauna zanci Nima."

"Kin tabbata?"

"ALLAH zanci, kaidai kawai ka zauna kaci naka."

Ta sake turo masa plate d'in abincin agabansa,"

Qinci yayi har saida yaga tazuba nata a plate ta soma ci sannan yayi murmushi had'e da d'aukar cokali yaci gaba dacin nasa,

Bai bar gidan ba sai bayan sallar magrib sannan yayi masu sallama yanufi gidan baba balarabe don bazai iya komawa borno ba alokacin.

Su uncle h kuwa tuni suka kira dady suka sanar dashi zance auren wanda suka ajiye nan da sati biyu, yayi matuqar farinciki dajin dad'i kafin yace yana son subashi dama ya tuntub'i su baba balarabe da baffa idan sun amince da lokacin harma da mahaifiyar yaron kuma sun amince masa da hakan inda sukace yabari da kansu zasu kira baffa su sanar dashi, hakan da sukayi yasashi qarajin dad'i ganin sun martaba wanda shine matsayin mahaifin yaron ayanzu don haka shi sai yakira baba balarabe da Rashida ya sanar dasu komai, ita dai Rashida tasan abunda yafaru tsakaninta da mahaifin batool don haka zuciyarta tashiga kokwanto cewa daqyar idan har da amincewarsa za'ayi wannan auren azahiri kuwa amsawa dady tayi da ALLAH yasa hakan shiyafi zama alkhairi, baba balarabe ma yayi farinciki sosai had'e da addu'ar ALLAH yasanya alkhairi, baffa kuwa amaimakon farinciki damuwace ta sake bijiro masa na ganin jikan nasa zaiyi aure ammababu mahaifinsa alhalin yana raye bai mutu ba.

Washe gari dady yasa Dr yagyara don yana fama da zazzab'i shi bazai iya tafiya ya bashi dubu d'ari yace yaje can kano yasami su baba balarabe da baffa ayanka masu sadaki su biya kafin lokaci yayi,

Bayan

Please Login or Register in order to submit comment