Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dama jiraye take da inna Bilkisu, bangaje nura tayi dake tsaye bakin qofar kamar an dasa yana kallon ikon ALLAH, gaba d'aya saboda yanda gaskiya tayi masa yawa kasa cewa komai yayi sai bin Inna Bilkisu data tallabota tana d'an bubbuga gefen uncinta had'e da kiran sunanta yakeyi.
"To munafuka algunguma, sarkin ashibanci da son yabo, fad'i ba atambayeki ba tsabar kicifi da iyayi ina ruwanki, meya shafeki no aciki ko dake akeyine da zakizo kisamun baki, kinsan me tayi manine da zakizo kisamun baki, Ina yanzu kika jiyo qarar muneera acikin d'akin nan Amma tsabar mugunta Ina kallonki ko ajikinki tunda ba 'yarki bace, sai yanzu don antab'a bare Zaki taso mana da wani migun bakinki kisa mani baki, to wallhi ahir d'inki Bilki da shiga sabgata ko inyi maki rashin mutunci, ni uban waye nasakawa baki da aka tab'amun tawa 'yar." Inna ruqayyace tafad'i haka tare da fitowa tayi tsaye akansu batare data damu da ganin halin da Rashida keciki ba. "Fadeela jeki d'ebo mun ruwa ki kawo inaga yarinyarnan suma tayi."
Da sauri fadeela tabar wajen taje ta d'ebo ruwan takawo Inna Bilkisu ta karb'a ta yayyafawa Rashida. "Mtssssss.. ALLAH ma yasa tamutu idan taso ba abunda yashamun kai iyayenta keda asara bani ba." 'dago kai Inna Bilkisu tayi had'e da kallonta hawaye cike da idanuwanta, kasa magana tayi ta maido kanta had'e da sake zuba ruwa a hannunta tashafawa Rashida, wata irin doguwar ajiyar zuciya Rashida tayi tare da dafe goshinta dake mata rad'ad'i tana fad'in. "Wash.."
"Sannu Rashida." Inna Bilkisu tafad'a tana kallon inda ta dafe goshin nata ya kumburo, sai alokacin nurah ya qaraso wajen idanuwansa sun kad'a sunyi jawur kamar an watsa masa barkono aciki, wani irin zugi da rad'ad'i yakeji kallon halin da matarsa keciki amma yakasa tab'uka komai saboda jin nauyin Inna Bilkisu dake wajen tana kula da ita, had'a idanuwa yayi da ita ta sakar masa murmushin daya tabbata cikin qarfin hali tayisa don takwantar masa da hankali,
"Nura d'auki matarka kushiga ciki, kaga goshinnan nata yabugu kad'an lullunda matashi koya saki, ALLAH yasawaqe kuma yaqara maku hak'uri."

Ya tsinkayo muryar Inna Bilkisu nafad'a cike da damuwa, duqawa yayi da niyar riqota, Inna ruqayya tariqo wuyan rigarsa had'e da cewa. "Ai wallahi baaka isa ba, mutum befi mutum ba balle ka dakarmun 'ya na qyaleka, wuce muje naga ubanme kayiwa 'yar tawa take wancan reren kukan." Ta jasa suka nufi cikin sashensa yana biye da ita, wani irin tuquqi yakeji aransa da badon matar qanen mahaifinsa bace ko wace yau sai ya koya mata hankali, qoqarin miqewa tsaye Rashida tayi hawaye na zubo mata daga cikin idanuwanta Inna ruqayya tayi saurin d'agata had'e da riqota sosai tanufi cikin shiyar tata. "A'a Inna Bilki bana son ganin abunda zai faru tunda tsakninsa ne da 'yan uwansa, kawai ki kaini shiyarki" Rashida tafad'a tana sake goge hawayen dake faman kaida kawo saman fuskarta akaro na ba adadi,
Kiyi hak'uri Rashida in sha ALLAH komai zai wuce." Sashenta tanufa da ita suna kai bakin dangaramar da zaka taka su ahiga cikin d'akin jiri ya sake d'ibarta da kad'an tafad'i, da sauri fadeela tariqota ita da Inna Bilkisu tana dafe da kanta sukaqarasa shiga da ita.

Acan cikin d'akin Rashida kuwa yaya hawwa na can hakince saman kujera tana kallonta, ita kuma muneera na zaune sai faman reren kuka takeyi tana susar kai sai kace wata sabuwar amaryar da akayiwa auren dole, duk abunda akeyi tana jiyosu daga tsakar gidan amma tayi kamar batasan anayi ba, bini bini take juyowa tana kallon muneera dake kuka can kuma sai tayi shiru ta qurawa tv ido tana susar kai tace. "Au munafuka dama kukan na qaryane! Wato anga abunda sai gidan masu kud'i ake gani d'an ba'a saba ba kin baza idanuwa sai kallo kike yi, ja'ira kawai." Ta kaimata dunguri a qeyar kai, sake fashewa da kuka tayi tana cije gefen d'an kwalinta had'e da sosa qeyar kan nata data daka, Inna ruqayya ce tashigo d'akin har lokacin tana riqe da kwalar rigar Nuraddeen tana fad'in. "Wato kasan matar taka bata cikin d'akin shine ka kamamun 'ya ka zalunta to wlh bazan yarda ba, ai kana ganinta ka zame kaje ka auro wata shine yanzu kake nema ka cuceta don baka samu yanda kake soba, wuce muje naga abunda kayimata" muneera naganinta ta taso tanufo inda take tana sake tab'e baki. "Buhun uba me zan gani haka ruqayya, d'an nawa kika shaqowa wuya haka sai kace wanda yayi sata! Uban me yayi maki."
Cikasa Inna ruqayya tayi kafin tariqo mueera tana fad'in. "Aiho dama kina cikin d'akin Yaya hawwa?, Kukan muneera najiyo nazata shikad'aine aciki shine na tasosa agaba yazo ya fad'amun abunda yayi mata gabanta har take wannan reren kukan saboda nasan duk abunda yasata kuka to ba kad'an bane"

Tafa hannuwa Yaya hawwa tashigayi tana sallalami had'e da gyara d'aurin zanenta kafin tace,

"Ke ruqayya sharri zakiyiwa yaron nawa don kinga bayyi magana ba?, shi dake da matan mezaiyi da 'yarki yarinya kamar an tsoma kaza acikin ruwan zafi anfiddata, tsigalalliyar yarinya munafuka kawai da ita, mai yagaggen baki zakuyi masa sharri, to maza kufita kafinna karya mata wud'annan gwalmad'ad'd'in qafafuwan nata."
"Dakata yaya hawwa gaskiya nagaji da wannan cin kashin naki, aci zalin yarinya agabanki bazakiyi magana ba kuma sai kiqara mata da kushe mata halitta, gaskiya nagaji kidena don nima ina son abuta a haka, shikenan daga zuwa tambayar meyayi mata sai kidinga cab'a mani magana..." Bata rufe baki ba ta Nuraddeen yafito a fusace riqe da belt a hannunsa dama tuni tsananin b'acin rai yasa ya shige uwar d'aki yayi zaune bakin gado yana tunanin ko meyi zai yimata ya rage rad'ad'in abunda tayiwa habibty d'insa, babban takaici ma wai shi Inna ruqayya ke zargi akan muneera ko mezaiyi da ita, meye ma zai tsinta ajikinta da zatayi masa wannan sharrin, yana zuwa ya finciko muneera daga jikinta idanuwansa jajir ya jefar da ita a qasa had'e da nuna Inna ruqayya yace. "So kikeyi nafad'a maki abunda nayi mata ko, to bari kigani na nuna maki, bari kiga kome nayi mata yanzun nan."

Jibgar muneera yafarayi da belt d'in yana watsa mata tako ina tana ihu, sheqeqe Yaya hawwa takalli Inna ruqayya data turo idanuwa waje tana kallonsa tace "yawwa qarawa shegiyar, yimata lilis munafukar yarinya kawai, daga mari sai uwarki tabisa da mugun sharri, yita jibgarta sai tagane shayi ruwane?"

Tafad'a tare da rab'awa ta gefensu tayi tafiyarta, qoqarin riqesa Inna ruqayya ta shigayi tana tsigarsa amma da yake zuciyarsa tariga tarufe a fusace ya d'ago kai yana cewa. "Wlh kibar ganin ke matar qanen mahaifinace duk kika matso wajennan saina had'a dake."
Ganin yanda fuskarsa ta sauya yasa tayi gum da bakinta tayi waje tana haragagon neman taimako, duka kam ranar muneera tashashi tun tana ihu har takasa shi kuma yace bazai dena dukan taba har sai lokacin data bar d'akin da qafafuwanta yanda gobe koda wasa akace tashigo shiyarsa bazata shigoba, Inna ruqayya kuwa tayi ihun neman taimakon har tagaji babu wanda yazo ai kuwa tana ta zundumawa mutanen gida zagi wai duk munafukaine sunaji za'a kashe mata 'ya kowa ya qyale,

Inna Bilkisu kuwa ji tayi kamar ta taka tsabar farinciki don koda baiyi komai akai ba ta d'au alwashi akan sai tayi mashi fad'a daya tashi tsaye ya qwatowa matarsa 'yancinta a gidan matuqar shi ba lusarin namiji bane, sai gashi da kanshi yayima kansa fad'a.
Yaya hawwa kuwa dama sashenta tawuce tashige d'aki had'e da haye gadonta ta soma bacci batare data sakebi ta kansu ba, su baffa Ali da baffa Usman su kuma basa gida balle su kawo mata d'auki ,

Sai da jikin muneera yayi tib'is tukuna tafara qoqarin k'watar kanta daga hannunsa ganin babu sarki sai Allah, da jan gindi tafito shiyar Inna ruqayya na tsaye bakin qofar takasa komawa sai faman zunduma masa zagi takeyi, da sauri ta riqota had'e da ida jawota tafito sukayi shiyarsu tana kuka yace.

"Wannan shine abunda nayi mata, kuma kad'an tagani, idan nakoma ganin qafarta cikin shiyata saina maida ita gurguwar qarfi da yaji." Sannan ya juya yakoma ciki,

Toilet ya fad'a had'e da d'ibar ruwa acikin durom d'in dake ciki yafara sakarwa kansa yana sakin wata irin ajiyar zuciya. Yajima aciki kafin yafito ya hau gyaran falon had'e da sharesa tass, feffesa room freshener yayi soboda tsamin da yaji d'akin nayi sannan yanemi kujera mai zaman mutum uku ya kwanta rigingine kansa na kallon silin zuciyarsa cike da matsananciyar damuwa

Acan shiyar Inna Bilkisu kuwa saman gadonta suka kwantar da Rashida, hannuwanta da idanuwanta tashiga duddubawa tana son gaskata abunda zuciyarta ke rayamata akanta tun kwanaki biyu da suka wuce saboda yanda ta canza, murmushi tayi had'e da cewa,
"Alhamdulillah ALLAH kaine abun godiya." har lokacin takasa Dena murmushin da takeyi, kallonta fadeela tayi had'e da cewa, "Inna menene?."

Bata tanka taba saidai kallon Rashidar data koma yi tana qoqarin rufe idanuwanta saboda baccin da take ji, baccinta mai isarta tayi kafin nan tafarko tana jin wata irin matsananciyar yunwa dama d'azun data gama abinci bata samu taci ba saboda tare sukeci dashi shikuma alokacin bacci yakeyi,

Kasancewar koda ta tashi bakowa ad'akin yasa tasauko saman gadon had'e da fitowa bakin qofar d'akin ta saki wata uwar hamma dake nuna ba qaramar yunwa take jiba.
"A'a Rashida har kin tashi?." Inna Bilkisu dake sharar cikin rumfar tasu tafad'a tare da d'agowa tana kallonta.

"Eh inna barka da marece, shara kikeyi?."

"Eh wallahi wajenne ya d'anyi datti ga baffanku yana kan hanyar dawowa ke sanshi baya son datti ko kad'an, ya qarfin jikin naki?"

"Alhamdulillah da sauqi Inna bari na riqa maki."

"A'a ki barshi ai nakusa qarasawa, maza jeki tun d'azu mijinki na ciki nasan ran nan nasa a cunkushe uake yanzu, kuyita haquri har ALLAH yakawo qarshen wannan al-amarin kinji ko."

Duqar da kanta qasa tayi tana wasa da 'yan yatsun hannunta tana murmushi sannan tabar wajen, har takusa shigewa Inna Bilkisu tace,

"Au Rashida." Juyowa tayi tana kallonta taci gaba da cewa "dama nace ki kula da kanki saboda yanzu bake.." Bata qarasa ba saboda hango Inna ruqayya da tayi nafitowa daga cikin d'akinta sai tayi shiru had'e da cewa

"Jeki rashida maya magana dake anjima"

"Mtssss...munafucci kunun kanwa!."

Inna ruqayya tafad'a tana jefo wata tasar Inna Bilkisun data gani cikin rumfarta.

Batace mata qanzil ba taci gaba da shararta ita kuma tawuce shiyarta batare data fahimci kome Inna Bilkisun ke nufi ba.










*ALLAH KAJIK'AN IYAYENMU*πŸ‘πŸ˜­
[8/17, 10:19] Billy S Fari: πŸšΆβ€β™€οΈπŸšΆπŸ»β€β™‚οΈ *SANNU SANNU*πŸšΆπŸ»β€β™‚οΈπŸšΆβ€β™€οΈ
πŸ’Ž _Bata hana zuwa..._πŸ’Ž


_WRITTING BY:_ *BILLY S FARIπŸ’Ž*

_DEDICATED TO:_ *BLOOD SISTER'S (AMZAHFAZ)*πŸ’‹

_BESTOWED TO:_ *ZAINAB AL-AMIN (MOM NA'EEM)* AND *AMINA UBA AYUBA (OUM ASHFAQ)*πŸ’ž

*DOMIN FARINCIKINKI SISTER SADIYA ZANGO (MIEMAH)*πŸ’–

*FATAN ALKHAIRI AGAREKU MOMMAH ME NANA HAFSAT (MISS XOXO) AND MAMANA HAFSAT RANO(OUM AFFAN)*❀️

Page___27πŸ’Ž

Tana shiga Kai tsaye kitchen tashiga ta d'ebo abincin a plate, tun kafin taqaraso cikin d'akin tasomaci saboda azabar yunwar da takeji, kwance ta iskosa idanuwansa arufe amma babu alamun bacci yakeyi saboda yanda k'wayar idanuwansa ke rawa, qasan carpet a bakin kujerar da yake kwance ta zauna tana cigaba da cin abincinta hannu baka hannu akushi, a hankali ya jaye hannusa dake saman goshinsa yana kallonta fuskarta a sake tamkar babu abunda yafaru, abincin dake gabanta ya kalla sannan ya kalleta cike da tambaya, saboda iya saninsa tunda tazo gidan tare suke cin abinci yazu ko kimanin tsawon watanni hud'u kenan, to meye dalilinta nayin haka kenan ko haushinsa takeji ya tambayi kansa had'e da tashi zaunne yana kallonta.
'Dago kai tayi ta kallesa tare da sakin murmushi daga haka Bata cemasa qanzil ba Kuma shima bai cemata ba sai data canye abincin tas had'e dayin gyatsa.
"Alhamdulillah" tafad'a tana lashe yatsun hannuwanta har lokacin idanuwansa nakanta, turo baki tayi yasakar mata murmushi tare da miqewa ya d'auko mata ruwa a fridge ya miqa mata, karb'a tayi tasha sannan tamiqe tare da d'auke plate d'in takai kitchen, tray d'in data had'a abincinsu akai ta d'auko takawo agabansa ta ajiye sannan takoma saman kujerar kusa dashi ta zauna had'e da d'ora kanta saman kafad'arsa. "Malamina ka sauko kaci abinci, nabarka da yunwa ko?." Seda yad'an harareta sannan yace. "Bazanci ba!."

'Dan turo idanuwanta tayi awaje tana qyaqqyaf tasu had'e da cewa, "meyasa?. Abincin da kafiso ne nayifa!"

Taqarasa maganar tana b'ata rai tare da nad'e hannuwanta saman qirjinta, mintsili ya kaimata a kumatu had'e da cewa. "Saboda bakya son naci shiyasa kikaci naki bayan kinsan tare mukeci ko fushi kikeyi da nine akan abunda yafaru."
"Laaaa...wlh ba haka bane malamina, kawai yunwa nakeji sosai shiyasa na fara ci, atunanina ma bacci kkeyi, kayi hak'uri nazuba maka kaci nasan kana jin yunwa kaima."

"E.ehm bazanci ba." Yasake fad'a yana nad'e hannayensa akan k'irji kamar yanda tayi d'azu ya juya mata baya, saqalo hannayenta tayi ga wuyansa ta rad'a masa akunne, "afuwan habibyyy.." taja qarshen cikin wani salo daya sashi juyowar da bai tashiba cike da mamaki don bai tab'a jin takirasa da wani suna ba inba malaminta ba, "me kikace habibty?, Pls sake fad'a naji."

Maqe kafad'a tayi had'e da cewa, "o'oh sai in kaci abincin tukuna zan fad'a har sai kace ya isa" zamewa tayi daga kan kujerar tana dariya ta zubo masa abincin a plate, jallop rice ce tasha kayan ciki da kifi dasu irin baqin kifinnan gasashshe mai d'an karen dad'i, saman kujerar tadawo tana riqe da plate d'in abincin da cokali aciki, d'ebowa tayi a spoon takai masa abakinsa ya juyar da kai gefe,

"Meye?"

"Kifad'a mana." Yafad'a had'e da d'an d'aure fuska, dariya tayi sannan tace, "Shikenan! Nafad'a habiby, habiby, habibyyy.." bud'e baki yayi zaiyi magana ta tura masa cokalin abincin abaki had'e da sakin dariya, murmushi yayi tare da nunata da yatsa. "Ke ko?"

Haka tadinga bashi abaki yanaci har yaqoshi ta tattara kayan takai kitchen ta dawo, miqa mata hannu yayi ya zaunar da ita a tsakankanin kafafuwansa ya turo kansa tagefen wuyanta.
"Habibty!" Yafad'a cikin wata irin kasalalliyar murya, "uhmm, habibyn habibty!." Shiru yayi na wasu mintota yana nazarin irin kalaman da zaiyi amfani dasu wajen bata hak'uri akan abunda yafaru, juyo fuskarta yayi yayi mata kiss saiti inda ya d'an kumburo a goshinta sannan ya sake maida kansa agefen wuyanta yace, "kiyi hak'uri, kiyi hak'uri, kiyi hak'uri bisa abubuwan dake faruwa, nasan cewa ba kad'an kike kauda kanki ga abubuwan da mahaifiyat da kuma wasu 'yan uwan keyi maki ba, kwata kwata banajin dad'insu har ga ALLAH domin ke amanace agareni, nakan tsinci kaina cikin damuwa mai tsanani aduk lokacin da naga ana cutar mani dake, zuciyata na quna inajin wani d'aci a maqoshi domin babu abunda nake so araina duniya fiye da inganki cikin farinciki, zallar hak'urinki da tarbiyarki suke galaba akaina wajen kawar mani da damuwa badon haka ba inada tabbaci akan da tuni zuciyata da kuma rouhina sun daina aiki ajikina saboda kasa jurewa ganin duk wani abu da zai cutar dake, nayarda cewa shi so sa'ane kuma dacene tun a ranar dana had'u dake, domin kin zame mani gwana takowane fanni, a kyau kece gwanata, a hak'uri Banda yake, a iya kula da tarairayar miji kinfi mata dubu, girki tsafta da kawaici sai dai nace Masha ALLAH, Alhamdulillah domin duka nasamu awajenki, na tabbata kece alkhairina na duniya da kuma lahira don haka Ina mai sake baki haquri ga yanayin da muka tsinci kanmu aciki, natabbata wata rana zai zamo labari."
Tunda abubuwannan kefaruwa bata tab'a zaunawa ta zubar masu da hawaye ba sai yau, koshi saboda wani nauyine da takeji azuciyarta taji ya sauka saboda dad'ad'an kalaman daya fad'a mata hakan shine yayi silar zubowar hawayenta batare data shirya ba, wud'anda batasan da wace kalma zata fassarasu ba, na bak'in cikin abubuwan da suke faruwa da itane ko kuma na farincikin soyayyar mijinta dake lunkuwa azuciyarta. hannu yasa ya juyo da ita gaba d'aya suna kallon juna tare da tallabo fuskarta yana kallon kyawawan idanuwanta dake zubar da hawaye, bakinsa ya nufo dashi wajen fuskarta tayi saurin rufe idanuwanta hawayen dake maqale aciki suka samu damar gangaro, jira takeyi taji saukarsa akan nata amma sai taji akalarta sauya saboda harshensa da taji saman fuskarta yana lashe hawayen, sannan yadawo ga bakinta ya sakar mata wani irin french kiss daya sa ta sake lumshe idanuwa tana mayarnmasa da martani.
Sunfi tsawon mintuna biyar ahaka kafin ya zare bakinsa daga nata had'e dasa hannuwa yariqe fuskarta yana kallon idanuwanta d'aya bayan d'aya,

"Habibty kidena zubar da hawayenki domin duk d'igar da zasuyi suna yintane tamkar d'igar ruwan wuta abisa zuciyata, nasan ke jarumace kuma akoda yaushe nasara natare dake don haka kikara hak'uri kafin ALLAH ya yalwata mana mutashi nan kinji ko?"

"Habiby ba Ina zubar hawayene akan abubuwan dake faruwane ba, hawayena na zubane adalilin samun nagartaccen miji kamarka, kalamanka nada matuqar tasiri agareni domin ako yaushe d'auke suke da saqonni masu ma'anar dake gamsar dani irin soyayyar da kake yimani Wanda hakan shine babban burina arayu, bana son wannan haqurin da kake bani domin mahaifiyarka ai mahaifiyatace hakama 'yan uwanka nawane don haka duk runtsi zai jure komai akanka matuqar kana tare dani."

"Habibty bakyajin zafin abubuwan da ake yimaki ne?."

"Inaji mana amma girman soyayyarka bata barin hakan yayi tasiri azuciyata." Tafad'a tare da rungumesa. Rungumeta shima yayi sosai tamkar wanda za'a k'wacewa ita yace.

"I dont want to miss you in my life..., I love you for ever and ever and ever.."
Rashida da wasu kalaman tafahimta wasu kuma bata fahimcesu ba tayi murmushi itama tace "Nima haka." dariya yayi don yanada tabbacin ba duka ta fahimci meya ce ba amma tace itama haka duk da dai dad'ad'an kalamaine yayi bamasu illa ba.

"Habibty kema me?" Yafad'a yana sake shigar da ita ajikinsa sosai.

"Yanda kace mana."
Tabashi amsa atak'aice itama tana dariya,

"Tom nagode gobe kishirya zamu fara lesson in sha ALLAH."

"Ni bana so."

"Ai baki isa ba."

Nuraddeen yafad'a had'e da sakinta yana yimata cakulkuli, cikin mintuna qalilan ya mantar da ita duk wani b'acin rai da takeji azuciyarta.

Rayuwa kenan haka ALLAH ke jarabtar bayinsa da sukayi imani dashi akoda yaushe, baffa dai gashi da rai amma wasu abubuwan sun buwayesa, duk fitinar da akeyi yanaji Amma Babu halin tashi, ahankali yaji damuwa naneman tayar masa da ciwonsa yayi saurin jawo hisnul muslim d'insa yana karanta addu'o'in hammu wal hazan (damuwa da baqinciki) cikin ikon ALLAH yaji komai na gushe masa, Saida yaji yasamu sassauci da salama acikin ransa sannan ya ajiye yaci gaba da ambaton ALLAH.

Bayan sallar magrib su baffa Ali sun dawo don basu shigo gidan ba saida suka gama sallah, baffa ya zayyane masu duk abunda yafaru agidan wud'anda kunnuwansa suka jiyo masa, sosai baffa Usman yaji ba dad'i sab'anin baffa Ali da yace.

"Ni wlh Yaya nazata wani abun mai muhimmancin ne yasa ka tsaidamu gashi tun d'azu yunwa nakeji, ai indai muneera ce da uwarta abunda ma yafi haka zakaji, ni bari inje inci abinci inaga yafimun."
Yana gama fad'a yamik'e ya wuce sashensa, cike da mamaki suka bishi da kallo kafin su ahiga tunanin nemo mafita,

Baffa Ali na shiga ko sannuda zuwa babu inna ruqayya da tun d'azu take zaman dakon isowarsa tace.

"Alhamdulillah muje malan, wlh yau saika qwatarwa 'yata haqqinta akan cin zalun da aka yimata."

"Ke ruqayya fara bani abinci tukuna yunwa nakeji." Yafad'a yana zaunawa saman tabarmar dake shimfid'e abakin qofar d'akin, sanin zai iya birkice mata idan tamatsa masa da zancen yasa taje takawo masa abincin ta ajiye agabansa, ruwa taje ta d'ebo takawo masa jikinta har tsima yakeyi ta zauna tabasa labari,

Yana gamawa tashiga bashi labarin qarya da gaskiya ya mik'e cikin b'acin rai yanufi shiyar Yaya hawwa yana k'walla mata kira, iskota yayi zaune tana cin abinci bisa 'yar barandar dake cikin rumfarta akan kujerar tsugunno ta tsakar gida shima yanemi waje ya zauna.

Saida takai loma abaki ta had'iye sannan yace.

"Ina jinka Ali mike faruwa?"

Cikin kwantar da kai yace. "Haba Yaya hawwa yanzu ace agabanki yaron nan zai kama 'yar uwarsa yayi mata mugun duka baki d'au mataki ba."

"Uwarta taja mata." tabashi amsa atak'aice tanaci gaba da tura lomar tuwonta hankali kwance.
"Koma dai meye ai kamata yayi ace kin hanasa tunda 'yar tawa ba jaka bace kuma ko meye ai kece kika jamata, babban abunda kebani takaici shine keda kikace bakyason yarinyar nan kin tsaneta meye na wuni kullum a d'akinta? Kodai yanzu kin fara amincewa da zab'in barene."

"Hmmm! Ali kenan, wai ku atunaninku zuwa d'akinta da nakeyi na ALLAH ne? Yaro man kaza ai duk wanda yace baya sonka to tabbas har amutu bazai tab'a sonka ba, ai tsuntsu biyune nake jifa da dutsi d'aya don haka ka kwantar da hankalinka, wannan shashashar 'yar taka ita nakeyiwa yaqi amma ita da mahaifiyarta suna neman b'atawa shiyasa na zura idanuwa saboda kada ad'agoni, duk wani shiri nawa ya kammala don gaba d'aya nagama aiwatar da abunda na karb'o wajen malan bakada imani, k'waya d'aya yarage ina kammalasa zakaga aiki da cikawa.."
Yaya hawwa taqarasa maganar had'e da miqewa tana d'auraye hannunta agefen d'akin. dashe hauru baffa yayi had'e da cewa.

"ALLAH yaya hawwa?"

"Naka wasane Ali, an fad'a maka ja da baya tsorone, ai tuni nashirya maka maina tsaf da zan yaqi waccan yarinyar mai kama da miyagun mayu, yanda nakejin natsaneta yanzu bana tunani zan iya d'aga mata qafa har sai tabar gidannan don haka idan harkana son gurinka yacika dole kadakatar da uwar iyayin nan da muneera daga shiga sha'anin Nuraddeen, inba haka ba kuwa to dasu b'ata mun aiki k'wanda na tabbatar na dakatar dasu nida kaina."...












*ALLAH KAJIK'AN IYAYENMU*πŸ‘πŸ˜­
[8/17, 10:19] Billy S Fari: πŸšΆβ€β™€οΈπŸšΆπŸ»β€β™‚οΈ *SANNU SANNU*πŸšΆπŸ»β€β™‚οΈπŸšΆβ€β™€οΈ
πŸ’Ž _Bata hana zuwa..._πŸ’Ž


_WRITTING BY:_ *BILLY S FARIπŸ’Ž*

_DEDICATED TO:_ *BLOOD SISTER'S (AMZAHFAZ)*πŸ’‹

_BESTOWED TO:_ *ZAINAB AL-AMIN (MOM NA'EEM)* AND *AMINA UBA AYUBA (OUM ASHFAQ)*πŸ’ž

*DOMIN FARINCIKINKI SISTER SADIYA ZANGO (MIEMAH)*πŸ’–

*FATAN ALKHAIRI AGAREKU MOMMAH ME NANA HAFSAT (MISS XOXO) AND MAMANA HAFSAT RANO(OUM AFFAN)*❀️

Page___28πŸ’Ž

To shikenan Yaya hawwa yanzu nai magana, amma tuntuni sai zuba idanuwa nakeyi naga matakin da kikace zaki d'auka amma shiru yau gshi kimanin watanni hud'u kenan da kawota. "Kaji dai abunda nafad'a maka koma meye kawai kazuba idanuwa kagani."
Tafad'a tana qoqarin shigewarta d'aki, seda safe yayi mata sannan ya wucewarsa yana ayyana abubuwan da zasu faru idan burinsa ya cika.
Yana fita Kai tsaye waje yayi sai bayan sallar isha'i lokacin har karfe 9 tawuce, yana shiga sashensa inna ruqayya ta sake tarbarsa da maganar cewa yayi "Kai ruqayya matsalata dake rashin hak'uri, yanzu dai ki kwantar da hankalinki munyi magana da Yaya hawwa kuma tace tana nan ta d'aukar mataki akan al-amarin."
"Hmm wane mataki zata iya d'auka akai bayan duk abunda yafaru dasa hannunta itace ummul aba isu tana kallo ya narkarmun yarinya agabanta batace komai ba, Kai nifa wlh nagama gano bata son auren yarinyar nan da yaronta, kaduba yanda take kashe wuni ashiyarta kuma wai don ta Rena mana da hankali tace bata sonta."

"Ashsha ana baki kina roqo, Bari in fad'a maki wlh yarinyar nan Yaya hawwa bata qaunarta tuni taje takarb'o magani wajen malan bakada imani..." Nan ya kwashe duk yanda sukayi da Yaya hawwa ya sanar da ita, lokacin muneera na kwance can acan gefen gado kafin takoma d'an d'akin da take kwana, Inna ruqayyace tace tabari har mahaifinta yadawo taji matakin da aka d'aukar masa na dukan daya yimata, wannan dalilin yasa tayi kwancenta nan ita da qannenta maza su uku ciki harda yusuf tana jiran dawowarsa.

Baffa Ali daya saki baki yanata bata labari kawai sai yaga muneera ta taso tana susar kai tanufo inda suke zaune gefen gado tana fad'in.

"Baffa ni babu ruwana da matarsa kawai so nake ku a auramun shi, wlh baffa Ina son ya nura sosai." Zarar idanuwa baffa Ali yafarayi don bai zata muneera na cikin d'akinba da ko kad'an bazaiyi

Please Login or Register in order to submit comment