Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

umma tare da d'oko masu jiku_ kunansu, miqa hannu umma tayi takarb'i d'ayar ganin sunyi masa yawa saboda yanayin yanda yake tafiya tunda ba lafiya yacika ba yayi saurin wucewa yana fad'in. "A'a kedai d'aga qafarki muje."

Suna zuwa akasa kayansu bayan mota suka shiga drivern ya tayar da motar suka bar tasha, suna hawa titi had'e da kama hanyar tafiya baba yarufe idanuwansa had'e da sakin wata irin ajiyar zuciya, kallonsa umma tayi itama tana ajiyar zuciyar tare da aza kanta saman kafad'arsa tana karanto addu'ar tafiya yayinda mutum ya hau abun hawa, wacce tafito daga bakin mafificin halitta kuma ya tabbatar mana da cewa duk wanda yayita alokacin daya hau abun hawansa zaiyi wata tafiya to ALLAH zaikaresa da ga sharrin duk wani abunqi dake cikin tafiyar da sharrin qarfe ko kuma had'ari, zai sanya tarin alkhairai masu d'imbin yawa acikin tafiyar tasa da yardar ALLAH.

_"ALLAHU AKBAR, ALLAHU AKBAR, ALLAHU AKBARU subhanallazi sahhara lana haza wama kunna lahu muqrinin, wa inna illa rabbina lamunqalibuun, allahummah Inna nas'aluka fi safrina hazal birri wattaqwa, waminal amali ma tarda, allahummah hawwan ala safarana haza wad'wi Anna bu'udahu, allahummah antasswahibu fis safri, walkhalifatu fil ahli, allahummah inni a uzu bika min wa'thaa'issafri, wa kaabatil manzwari, wasuu'il munqalabi fil mali wal ahli."_

Domin samun fassarar wannan addu'ar zaku iya duba littafin hisnil muslim, addu'a ta tis'in da shida (96) don nemawa kai kariyar ALLAH daga sharrace sharracen miyagun mutanen dake kan hanya da kuma munanan had'urran da sukayi yawa alokutan tafiye tafiyenmu,

Tana addu'ar hawaye nazubo mata a fuska, hannu baba yasa yagoge mata had'e da cewa.

"Kinsan inda muka nufa yanzu?"

Girgiza masa kai kawai ta iyayi tana mai tunanin yanda duniya tajuye masu daga farinciki Mai yawa na bayan shekaru zuwa baqincikin da basusan iya adadin lokacin da zasu d'auka dashi kafin yabarsu,

"Jahar borno muka nufa kuma Alhamdulillah akwai wani babban mutum dana sani acan abokin alhajin da nake saro takalma a shagonsane ana cemasa alhaji shu'aibu maiglass, muna yawan had'uwa dashi idan yaje wajensa ni kuma naje kaimasa kud'insa in amso takalmi, yanda alhajin kejin dad'in mu'amalar kasuwanci dani yasa wata rana ya had'ani dashi muka gaisa har yake fad'amun ai aminin sane yana zowa daga borno me shima yayi sayayar kayan glass nayin qofofin zamani, to tun daga lokacin duk yazo in muka had'u sai yayi mani alkhairi don babban mutumne sosai, kinga idan munje sai munemi gidansa kafin musamu inda zamu zauna.

"Shikenan duk da dai mutum bashida tabbas amma tunda ba muda wata mafitar ALLAH yasa hakan shiyafi zama alkhairi kuma yakaimu lafiya."

"Amin, ki kwantar da hankalinki in Sha ALLAH babu wata matsala."

"ALLAH yasa." Tafad'a tana share qwalla a idanuwanta.

••• ••• •••
Baffa Ali kam yayi sanyi sosai akan abunda yafaru, yayi dana sani mai yawa akan biyewa harkar mata da yayi wacce ta jefasa cikin halin qaqa nikayi, yayi nadamar shiga al'amurran Yaya hawwa Amma duk da haka yana jin tsanar baffa mai tsanani azuciyarsa bisa abunda yasa akayi masa shida iyalinsa a matsayinsa na d'an uwansa, hakan yasa tunda suka dawo yafita harkar kowa yana rayuwarsa shi kad'ai, baruwansa da kafatanin mutanen gidan acewarsa suma munafukaine tunda aka kasa samun wanda zaiyi belinsa acikinsu, had'uwa dubu kuwa idan zasuyi da baffa bazai d'aga Kai ya kallesa ba balle yasa ran zai gaishesa, dama dama baffa Usman yakan d'an saki jiki dashi sugaisa yawuce shima d'in ba sosai ba, Kuma hakan ko kad'an bai dami baffa ba saima addu'ar neman shiriya daga ALLAH.

Muneera kuwa tuni ta manta da babin ya nura rayuwarta takeyi kamar ba itace muneerar dake faman kukan son ya nura dare da rana ba, Amma tasha alwashin bazata tab'a sure ba inba saurayin birni d'an kwalisa ba irin ya nura, shiyasa takeci gaba da yiwa maqwabcinsu da yace yana sonta walaqanci kuma Inna ruqayya tagoyi bayan haka, saidai duk da haka yanzu basuda bakin fitowa tsakar gida suyi tijara kamar yanda suka saba gudun kada a mayar masu da jawabin abunda baffa yasa akayi masu wanda ita kanta tana kallon baffa amatsayin azzalumi wanda yaci amanar d'an uwansa, dama mai hali baya fasa halinsa.

••• ••• •••
Dr. Nura kuwa tunda safe yaso yin tafiyarsa zuwa kano amma yanda yaga Fatima takwana da tana fama da ciwon kai wanda dama lokaci zuwa lokaci yana taso mata yasa yafasa tafiyar, gashi sai kiransa akeyi wajen aikinsa akan wani emergency daya taso na gaggawa, Babu yanda batayi dashi ba akan yatafi kodon issue d'in Rashida amma ya kafe akan matuqar ba sauqi yaga ta samu ba babu inda zaije, hakan yasa tayi qarfin halin tashi taje tayo wanka tare da kiran mai aikinsu tace takawo mata abinci taci, bayan taci ya d'ebo mata magani tasha, a maimakon takoma ta kwanta sai tawuce part d'inta, zaune ta isko Rashida a palour rungume da little Nuraddeen tagama dama mashi madarar (NAN) da ake had'a masa da ita zata bashi.

"ALLAH sarki aunty yanzu nake cewa idan nagama bawa yaronki madara zanje naduboki da jiki, injin da sauqi ko?" Rashida tafad'a tana qoqarin d'aurama little Nuraddeen dake qoqarin kamo fidan madarar abun tare abinci idan ya zuba awuyansa, murmushi Fatima tayi had'e da miqa hannu takarb'esa tana yimasa wasa sannan ta zauna takarb'i fidan tana bashi madarar, har kusan qarfe sha d'aya da rabi Nuraddeen yaji tsit har lokacin Fatima bata dawo ba, part d'inta yanufa ya iskota kwance little Nuraddeen nasaman cikinta yana bacci ita kuma da Rashida na zaune suna kallon wani wa'azi a tsahar sunnah tv, a daidai bakin qofa ya tsaya yayi gyaran murya yana kallonta kafin yace.

"Iyyeeeee lalle kinsamu sauqi madam, shine kika barni acan Ina jiran tsammanin dawowarki ashe kuna nan keda maman baby kuna kallonku, ikon ALLAH, to wannan wace irin jinyace nakeyi, ga marar lafiya anan ni kuma mai jinyar anbarni acan."

Ahankali ta tashi zaune don kada little Nuraddeen yafarka tana kallonsa had'e dayin murmushi tace.

"To ai laifinka ne, nafad'a maka nasamu sauqi amma baka yarda ba ai yanzu ka ganewa idanuwanka ko?"

"Eh to! Yanzu kam ai nayarda." Kallon Rashida da kanta ke qasa a sunkuye yayi had'e da cewa.

"Mman baby Ina kwana antashi lafiya, tunda yau tunanin takwarana abban takwara bazai bari agaisheni ba."yaqare maganarcike da tsokana.

"Laa..uncle jirafa nakeyi kugama magana sai nagaisheka, Ina kwana ya jikin aunty." Rashida tafad'a had'e da d'ago kai tana dariya.

"Lafiya klw, auntynki kam aike zan tambaya tunda kinsa ta wartsake."

Murmushi kawai tayi tare da maida kanta qasa ba tare da tace komaiba yace.

"Madam tunda naga kin samu sauqi kuma akwai sauran lokaci bari kawai nawuce ko kuwa?"

"Gaskiya kam."

Fatima tafad'a tare da tasowa tabi bayansa sab'e da little a kafad'arta,

"ALLAH ya kiyaye uncle." Rashida tafad'a tana kallonsu cike da burgewa, itadai a kullum rayuwar ma'auratan na burgeta don akwai fahimta sosai a tsakaninsu, hakan na yawan sa tanajin sha'awar kamanta irinta da habibynta amma da zaran ta tuna da mahaifiyarsa sai tayi saurin kauda wannan tunanin aranta.

Akan gado ta ajiye little ta taimaka masaya shirya tsaf ta sake d'ebo masa breakfast ta tsaresa ya sakeci sannan tace.

"To ranka shidad'e ALLAH ya kiyaye kuma yasa Kati tafiyar sa'a, kaje lafiya kuma kadawo lafiya tare da kyakkyawan albishir d'in had'uwa da iyayen maman baby, duk da inajin damuwa idan natuna zan rabu da kyakkyawan qaramin maigidannan nawa" taqare maganar tana kallon little Nuraddeen dake baccinsa hankali kwance, jawota yayi ajikinsa had'e da cewa.

"Ki kwantar da hankalinki insha ALLAH muma namu natafe ga ALLAH kinji ko matar?"

"Ina fatar ganin wannan ranar akoda yaushe."

Sumbatar goshinta yayi sannan tasake sab'a Little Nuraddeen a kafad'a ta rakasa har bakin gate hannuwansu na sarqe da juna, dama tuni yakira qanensa ya fitar da motar waje yana jiransa, shi zai kaishi tasha ya hau mota sai yadawo mata da motar gida don dama yadena zuwa da ita tun lokacin da little na asibiti saboda tunanin ko wata matsalar zata taso da za'a buqaci motar,

Saida taga tashinsu sannan ta d'aga masa hannu had'e da komawa gida,

Suna isowa junction d'in da zasu juya su shiga tasha motar su umma na sauka, lokacin qarfe sha biyu saura minti biyar na rana, har zai shiga junction d'in dr.nura yace ya tsaya ya karb'o masa swan water gora biyu awani shago dake wajen, parking qanen nasa yayi agefe tare da rage glass d'in motar, adaidai lokacin su kuma su baba suka fito daga cikin tashar suna qoqarin tsallakowa titi zuwa d'ayan hannun da motar su Dr nura tayi parking....


*ALLAH KAJIK'AN IYAYENMU*👏😭
[8/17, 10:19] Billy S Fari: 🚶‍♀️🚶🏻‍♂️ *SANNU SANNU*🚶🏻‍♂️🚶‍♀️
💎 _Bata hana zuwa..._💎


_WRITTING BY:_ *BILLY S FARI💎*

_DEDICATED TO:_ *BLOOD SISTER'S (AMZAHFAZ)*💋

_BESTOWED TO:_ *ZAINAB AL-AMIN (MOM NA'EEM)* AND *AMINA UBA AYUBA (OUM ASHFAQ)*💞

*DOMIN FARINCIKINKI SISTER SADIYA ZANGO (MIEMAH)*💖

*FATAN ALKHAIRI AGAREKU MOMMAH ME NANA HAFSAT (MISS XOXO) AND MAMANA HAFSAT RANO(OUM AFFAN)*❤️

Page___51💎

A qoqarin su na tsallakowa zuwa d'aya b'angaren baba na tallabe da jakunkunan su umma tamiqa hannu zata karb'i d'ayar dake sagale a kafad'arsa ganin yanda yake tafiya daqyar saboda yawan da suka yimasa tana fad'in.

"Malan kenan! ALLAH kafiye qarfin hali da yawa, miqo wannan jakar ko itace in riqa maka tunda sunyi maka yawa." Maganar takeyi tare da qoqarin karb'ar jikkar ahannunsa har lokacin suna a tsakiyar titi kai kace cikin gida suke hankali kwance, wata motace tashigo ta junction d'in aguje tana yimasu oda amma saboda hankalin su gaba d'aya baya akan titin ba suma kula da zuwan nata ba balle suji odar da akeyi masu. abunka da mutumen qauye ba ruwansu da tunanin ai nan birnine akwai banbancin dake tsakanin titunansu dana qauye.

Ganin motar na tunkarosu ka'in da na'in inda yasa dr.nura dake kallonsu tun d'azu ta cikin glass d'in motar yayi saurin fitowa tare da rugawa ya jayikkesu da qarfi, cikin tashin hankali duk suka saki jakunkunan nasu tsakiyar titi gabansu na matsanancin fad'uwa, yana jayesu motar na wucewa aguje kamar iska wacce kad'an ya rage ta buge Nuraddeen garin taimakonsu.

Kallo d'aya zakayi masu kafahimci tsantsar tsoron daya ziyarto zukatansu alokaci d'aya, binsu yayi da kallo cike da takaici kafin yakoma yakwaso jakunkunan nasu dake tsakiyar titi.

"Haba baba!, shifa titi da kuke gani ba gidajenmu bane da zamuyi yanda muke so akai ba, wajene da ke cike da barazanar d'aukar duk wata rayuwar da tayi kuskuren gittawa akai ba daidai ba sanadiyar ababen hawan dake kai da komo akansa, yanzu da wani abun ya sameku wani hali kuke tunanin zaku jefa halinku aciki, don ALLAH baba kudinga duba tituna dakyau idan zaku tsallaka saboda akwai banbanci tsakaninsu da naku na karkara."

Ya qarasa fad'a ransa a d'an b'ace yana miqa masu jakunkunansu.

"Kayi haquri yaro, injin bakaji ciwo ba."

Umma tafad'a tana goge 'yan guntayen hawayen da suka zubo mata.

"A'a baaba, Amma dai adinga kula saboda gujewa qananan had'urra da manyansu."

"Mungode bawan ALLAH daka taimakemu, badon haka ba da mun afkama abunda mukayi qoqarin gujewa, mungode sosai da wannan taimakon da kayi mana, ALLAH ya saka da alkhairi yayi maka albarka."

Baba yafad'a yana kallon Dr nura daya shiga duniyar tunanin muryar umma da yaji, tabbas yatab'a jin mai irin muryar nan tata amma a Ina ne? shine ya kasa tunawa.

Daidai lokacin qanensa ya qaraso wajen riqe da gorar ruwan guda biyu a hannunsa daya siyo masa, "Yaya lafiya?."

Ya tambayesa yana kallonsu umma had'e da yatsine fuska, halinshi kenan aduk lokacin da zai had'u da talaka saboda yanda yaqi jininsu, shiyasa basa wani shiri da yayan nasa da matarsa ko kad'an, don tsakaninsu da talaka d'an jimmane da d'an jummai injisa.

"Ba komai, muje."

Dr.nura yabashi amsa had'e da wucewa yana kallonsu, bayanshi yabi ummat nayita sa masa albarka suka nufi tasha ya ajiyesa sannan yajuya ya maida motar tare daba Mai gadi makullin motar yaba Fatima sannan yawuce gida.

••• ••• •••
Ana gama sallar asuba bayan rana tafito bab balarabe ya gyara tare da fitowa yanufi kitchen inda uwargidansa ke ciki tana had'a abun karyawa.

"Subhanallahi, hajia har yanzu baki gama had'a abun karinnan ba?, Kinfa sani babu kowa atare dasu kuma akwai magungunan daya kamata susha da safennan bayan sunci abinci, tun jiya saida nafad'a maki haka amma ace har qarfe takwas na nema tayi baki gama had'awa ba, kinsani badon wannan ba da tuni ni nabar gidannan natafi nadubo ya d'an uwana ya yatashi da jiki." Yafad'a ransa a d'an b'ace yana qoqarin rufe mab'allan gaban rigarsa, juyowa tayi had'e da gaishesa sannan tace.

"Kayi haquri, na samune yarannan sun jiqamun gawayin da zanyi amfani dashi seda nakoma had'a itacen murhu, amma kad'an yarage na kammala sai naba Hassan shida Hussain subiyo bayanka dashi."

"Mtssss.." tsaki yaja had'e da ficewa yabar gidan yana fad'in. "ALLAH ya kyauta."

Ya matuqar shan mamaki lokacin daya isa qofar gidan yaganta kulle da kwad'd'o, maqwabtansu ya aika akayo masa sallama da maigidan ya tambayesa su yace shima baisan inda suka jeba, yafi qarfin Rabin awa abakin qofar gidan yana tambayar mutanen dake anguwar tasu amma wanda duk ya tambaya amsar d'aya ce shine basu sani ba, kan kace me qofar gidan tacika da mutanen anguwar ana ta'ajibin ina su baba suka shiga, shi kuwa baba balarabe banda aikin Kiran wayar baba da umma babu abunda yakeyi, cike da tashin hankali yake kiran lambarsa idan ya jita akashe sai ya kashe yasake kiran ta umma amma duka Babu wacce yayi nasarar samu, waje yanema ya zauna yaci gaba da sake gwada kiran nasu cike dasa ran cewa awannan karon zata shiga,

Dafe kansa yayi da duka hannayensa tare da fad'in. "hazbunallahu wani'imal wakel."

Duk mutanen dake wajen sun matuqar tausaya masa ganin yanda hankalinsa ya tashi alokaci d'aya kowanensu nafad'in albarkacin bakinsa akan tafiyar baba batare daya sanar da d'an uwansa ba, duk dako mafi yawancinsu sun san dalilin da yasa suka aikata hakan.

Baki suka dinga bashi kafin sufara watsewa d'aya bayan d'aya ya rage daga shi sai su Hassan da hussaini da basu jima da isowa wajen ba d'auke da kwandon abun karin da aka had'o masu da flaks d'in ruwan zafin tea. Sai Kuma maqwabcinsu dake gefe zaune shima yana gwada kiran wayar baba.

Auntynsu gaba d'aya Yaya maryam baba balarabe yakira ya sanar da ita abunda ke faruwa nan take ita da mai gidanta suka iso wajen cikin tashin hankali suma, nan ya shaida mata abunda yafaru jiya da iyayen Rashida sukazo wanda yake tsammanin shine dalilin da yasa suka yanke shawarar barin garin saboda baqinciki da quncin da suke ciki.

Fashewa tayi da kuka tana fad'in "Amma wannan mata ta cucemu ta rabamu da 'yarmu da kuma d'an uwanmu, ubangiji ALLAH ka isar mana, ALLAH ka isarwa Rashida da iyayenta."

Kasa cewa komai baba balarabe yayi sai jinjina kai da yakeyi, haka Yaya maryam taci gaba da kukanta tana yiwa Yaya hawwa ALLAH ya isa bisa rusa masu farinciki da tayi, wata irin ajiyar zuciya maigidanta ya sauke kafin yace.

"A gaskiya wannan baiwar ALLAH tacutar da mutane da yawa kuma in Sha ALLAH haqqoqansu bazasu barta ba, yanzu Kai balarabe duk ka tambaya nan maqotansa basuda wani labari akan inda sukaje ko wani saqo da suka bari kafin sutafi.?"

"Na tambayesu Yaya sunce basu san komai ba akan tafiyar tasu, ni ina tunanin tun cikin dare sukabar garinnan." baba balarabe yafad'a yana murza goshinsa saboda ciwon kan da yaji yana nema yarufesa,

Kallon Yaya maryam yayi dake shartar majina tana dannar wayarta da alama itama gwada kiransu takeyi yace.

"Yaya maryam kidena wahalda kanki bazaki samesu ba, nakira yafi a qirga amma ban samesu ba."

To yakamata asa ab'alle gidan ko za'a samu wani saqo da suka bari don natabbata bazasu tafi haka ba har sai sunbar wani saqon," maigidan Yaya maryam ne yafad'i haka tare da zuba hannayensa a aljihu.

Maqwabcin su sake gefe zaune baba balarabe yayiwa magana da ataimaka masu da wani abun da zasu iya b'alle kwad'on dashi, cikin gidansa yashiga yake ya d'auko zarton ya kawo masu, kallon babban d'ansa da zai wuce da alama gona yayi had'e da cewa.

"Qasimu zoka taimaka kayanke masu kwad'onnan."

Baba balarabe yafara shiga bayan anyanke kwad'on sannan Yaya maryam Mai gidanta na biye dasu abaya, tsafa suka isko gidan babu alamar an hargitsa komai aciki kafin sutafi, Yaya Maryam tashiga dudduba ko ina cikin d'akin ta hargitsesa amma basuga komai ba, sallamar aunty marwiyya data shigo tana reren kuka tasata fitowa tsakar gidan dasu baba balarabe ke tsaitsaye, kuka takeyi had'e da lailayo miyagun addu'o'i kala kala tana yiwa Yaya hawwa, rarrashinta suka shigayi da bata magana kafin su yanke shawarar fara nemansu a tashoshin motar dake cikin qauyen nasu da zagaye.

Wani yarone yayi sallama had'e da cewa. "Wai mai mashin yace yana jiran matar da yakawo takawo mashi kud'insa" sai alokacin aunty marwiyya ta tuna da aibata sallami mai mashin d'in ba, kawai yana ajiyeta ta tahowarta, nera d'ari baba balarabe yaciro ya miqawa yaron tace a'a yabari taje dakanata, a tsakiyar zauren gidan jikkarta takucce tafad'i wajen saurin taje ta sallamesa tare da bashi haquri, tana duqowa ta d'auki jikkar idanunta sukayi tozali da takardar da baba yarubuta duk an tattaketa.

_KUYI HAQURI ZAN NEMEKU ADUK LOKACIN DA NAGA DACEWAR HAKAN, DAGA 'DAN UWANKU BASHAR"_

Shine abunda ta gani a qasan takardar da har tayi nufin wucewa tabarta, da sauri ta d'auka tana kakkab'e qasar dake jiki ta koma cikin gidan bayan taba yaron kud'in yakai masa tace yabashi haquri,

"Balarabe, balarabe."

Tadinga kiransa tun kafin takai cikin tsakar gidan tana gyara mayafinta da jikkarta dake nema su sub'uce mata.

Kad'an yarage suyikaro dashi a daidai bakin qofar shigowa tsakar gidan da sauri yaja baya yana fad'in.

"lafiya marwiyya ko sun dawo ne?"

Takardar ta miqa masa hannunta narawa ya karb'a yana binta da kallon mamaki kafin ya maida kallon nasa ga takardar, saida ya karanceta tsaf sannan ya d'ago kansa yana kallon aunty marwiyya,

"Waya baki?" Ya tambayeta don ya tabbatar da rubutun dake ciki nad'an uwan nasa ne.

"A tsakiyar zauren nasameta ajiye a qoqarin d'auko jikkana data fad'i wajen saurin in sallami mai mashin."

Juyawa yayi yana kallon Yaya maryam dake tsaye ita da maigidanta suna jiran jin ba'asi tare da takawa ya isa wajensu, cikin raunin muryar dake tabbatar da irin sanyin da jikinsa yayi yace dasu.

"Wannan itace abinda mukayi tsammanin Yaya bashar zai barmuna muketa nema kuma Alhamdulillah gata mun samu." Da sauri Yaya hawwa takarb'i takardar don gaba d'ayansu sunyi boko saidai baiyi wani zurfi ba daga bakin sakandirene suke ajiyesa, wannan dalilinne yasa abaya baba ya kafe akan sai Rashida tayi karatu sosai saboda alwashin daya d'auka akan cewa zurfin karatun da bai samu yayi ba zaisa 'ya'yansa suyisa kosu nawane.

Karanta takardar Yaya maryam tafarayi da qarfi kamar haka.

_Assalamu alaikum 'yan uwana, fatan alkhairi mai yawa da kasancewa cikin amincin Allah arayuwarku har zuwa lokacin da ubangiji zai sake had'a fuskokinmu daku, haqiqa samun 'yan uwa kamarku abune daya isa mutum yayi alfahari dashi har iya qarshen rayuwarsa, Ina Mai godiya agareku bisa kulawa da d'awainiyar da kukayi nida iyalina, mungode ALLAH yabaku aljannah da rahamarsa, nasan alokacin da kike karanta wannan takardar kuna cikin halin tashin hankali da damuwa saboda rashin sanin inda muke, Ina roqonku daku kwantar da hankalinku, muntafine bisa Imanin cewa hakan da mukayi shine mafi alkhairi agaremu, shine hukuncin da zai sama mana sauqi da rad'ad'in abunda mukeji aranmu, don haka muna roqon addu'arku akoda yaushe, nagode 'yan uwana Ina alfahari daku, musamman balarabe daya zamemani ginshiqi arayuwa,_
_KUYI HAQURI ZAN NEMEKU ADUK LOKACIN DA NAGA DACEWAR HAKAN, DAGA 'DAN UWANKU BASHAR_

Kusan atare sukayi ajiyar zuciya gaba d'ayansu kafin Yaya tace.

"Assha bashar, meyasa zakayi haka?, Meyasa zaka jefa kanka da iyalinka uwa duniya don gushewar farincikinka? duka wannan damuwar tasu akan Rashida ce, to gashi sun gudu sunbar garin, idan ALLAH yakuma nufi farincikin nasu dawowa agaresu shikenan sun sake nisanta kansu dashi?."

"Lalle kam Yaya sun ragon azanci duk da dai bamusan ya suke jiba, amma muyi masu addu'a kamar yanda ya buqata, ALLAH yasa rabon had'uwarsu da 'yarsu ne ya fishshesu." Baba balarabe yafad'a yana sake sakin ajiyar zuciya akaro na ba adadi.

Sosai ganin takardar yad'an sa sun samu natsuwa, sun jima agidan suna jajanta abun kafin sufito baba balarabe yabayar asawo masa wani kwad'on ya kulle gidan dashi, bayan ya kulle ya miqama yaya maryam makullan tace yabarsu hannunsa kafin suyi tunani akan abunda ya dace suyi tunda baza abar gidan haka ba.

Sai da mijinta ya goyata ga mashin d'insa suka wuce sannan yaraka aunty marwiyya bakin titi itama tahau mashin, suna wucewa shima shima yawuce yana maijin duniyar tayi masa wani iri daban.

••• ••• •••
Duk wani bayani daya kamata boka yayima su inspector najida yayi masu shi ba tare daya basu wata wahala ba, anan ya tabbatar masu da cewa shima baisan inda baqin aljanin daya turawa Rashida ya kaitaba, ataqaice ma shi aljanin baiyi nasarar shiga jikinta ba kuma ma yanzu baya tare dashi saboda anqoqqonasa ya bijire masa, shi kansa yanzu tsoronsa yakeji saboda yanda yake cutar dashi tare da azabtar dashi, koda inspector najida takira baffa yazo Police station d'in tayi masa bayani, ya matuqar jin dad'in cewa aikin shed'anunbaiyi tasiri akan Rashida ba, dama shi yanada matuqar yaqini akan hakan saboda riqon ibadarta, abunda kawai baiji dad'in jiba shine rashin sanin inda suka kaita lokacin da sukaci nasarar d'auketa, addu'a yayi had'e da roqon ALLAH ya gaggauta bayyanata.

Nan yasaka hannu akan ayi releasing case d'in akayi komai aka gama, har ya juya zai tafi inspector najida tace.

"Baba ya batun Inna hawwa.?"

"Ku saketa kawai." Yabata amsa atak'aice tare da juyawa yabar station d'in.

Har ya tare abun hawa zai hau sai kuma ya juyo ya dawo wajen inspector najida, koda ya shigo office d'in kanta na duqe tana ida cike sauran information d'in daya kamata kafin ya ajiye file d'in inda ya kamata.

A hankali ta d'ago kai ta kalli baffa tace. "Baba ya akayi?"

"Akan maganar hawwa ne, Ina so ku ajiyeta kafin nasamo asibitin da za'a kula da ita, koba komai ta haifamun d'a wanda nake alfaharin samunsa aduniya." Rufe file d'in dake gabanta tayi ta ajiye biron data gama rubutu sannan ta d'ora hab'ar bakinta akan hannuwanta data had'e waje d'aya tana kallonsa, murmushi tayi sannan tace.

"Baba kanada zuciya mai kyau, haqiqa da maza zasu kasance masu duba alkhairin matansu komai qanqantarsa arayuwa koda sun rabu dasu, to ina da tabbaci akan mata bazasu wahala aduniya ba sosai, haqiqa kayi qoqari ubangiji ALLAH yasaka maka da alkhairi."

Murmushi baffa yayi had'e da cewa. "Amin 'yata nagode ALLAH yayi maki albarka ya d'aukaki acikin al-amurranki,"

"Amin" ta amsa masa had'e dajin dad'in addu'arsa....








*ALLAH KAJIK'AN IYAYENMU*👏😭
[8/17, 10:19] Billy S Fari: 🚶‍♀️🚶🏻‍♂️ *SANNU SANNU*🚶🏻‍♂️🚶‍♀️
💎 _Bata hana zuwa..._💎


_WRITTING BY:_ *BILLY S FARI💎*

_DEDICATED TO:_ *BLOOD SISTER'S (AMZAHFAZ)*💋

_BESTOWED TO:_ *ZAINAB AL-AMIN (MOM NA'EEM)* AND *AMINA UBA AYUBA (OUM ASHFAQ)*💞

*DOMIN FARINCIKINKI SISTER SADIYA ZANGO (MIEMAH)*💖

*FATAN ALKHAIRI AGAREKU MOMMAH ME NANA HAFSAT (MISS XOXO) AND MAMANA HAFSAT RANO(OUM AFFAN)*❤️

Page___52💎

Baffa nashiga gida ya tadda Nuraddeen yafito daga wanka yana shiryawa, cike da girmamawa ya tarbesa tare da karb'ar ledar daya shigo da ita ga hannu yana fad'in.

"Sannu da zuwa baffa."

"Yawwa Nuraddeen, barka da rana wanka akayi?."

"Eh baffa, Ina son inje dubo innar mu ne."

Batare daya tanka saba yawuce bakin katifar dake cikin d'akin ya zauna.

"Nuraddeen zubikke abinda ke cikin ledar nan awani kwano kazo muci yunwa nakeji"

Acan gefen d'an madaidaicin durom d'in dake cikin d'akin Nuraddeen ya d'auko wani kwano cikin kwandon da suke kife kwanonin abincin da suke amfani dasu yazo ya d'auki ledar ya zube soyayyar doya da k'wai d'in dake cikin ledar daya zo da ita yana fad'in.

"Ya akayi haka baffa?, Ga abinci nan Inna Bilkisu ta aiko yusuf ya kawo tund'azu."

"Ai nasani Nuraddeen, wannan ina fitowa daga police station ne nagata ana siyarwa saita burgeni nace bari nasiyo mana."

"To baffanmu, ALLAH yasaka maka da alkhairi." Nuraddeen ya qarasa maganar had'e da ajiye kwanon agabansa, saida yafidda ledar ya saka cikin shara tukuna sannan ya dawo ya d'ebo masa ruwa cikin durom d'in yazo ya ajiye agabansa, har zai juya baffa yace.

"Zo zauna muci mana, ko kaci wancan d'in ne."

Azahiri baiya jin cin abincin

Please Login or Register in order to submit comment