Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

amma ganin yanda mahaifin nasa ya tsaresa da idanuwa yasa yaje ya wanko hannuwansa yasa hannunsa suka soma ci, tunda suka fara babu wanda ya koma cewa uffan har suka kusa gamawa, cire hannu baffa yayi ya d'auki ruwan yasha ya yiwa ALLAH godiya sannan yace.

"Nuraddeen ya zancen tafiyarka? Naga lokaci sai sake gabatowa yakeyi"

Da qyar Nuraddeen ya iya had'iye abincin dake cikin bakinsa kafin ya d'ago kai yana tankwashe qafafuwansa yace.

"Baffa maganar tafiyar nanfa ni na haqura da ita gaskiya, bana tunanin zan iya sa qafa inbar qasarnan mahaifiyata na cikin wannan yanayin, bacin haka ma baffa nifa har yanzu bancire tsammanin cewa Rashida zata dawo ba, jikina yana bani cewa duk inda take Ina ranta kuma tana cikin damuwa kamar yanda nake cikinta, bana son lokacin da zata dawo ta isko bana qasar, hakan zai sakata cikin shakku da kokwanto cewa nadamu da b'acewarta, shiyasa kawai nake tunanin gwara inzauna in bawa mahaifiyata kulawa har zuwa lokacin da ALLAH zai dawo da Rashida agareni.

"Nafahimceka Nuraddeen, Kuma nayarda da zancenka, Amma karka manta dama tana zuwa ga bawane sau d'aya arayuwa, sai kuma sa'a idan tasa ALLAH yasake baka wata damar, batun mahaifiyarka kabarshi a hannuna zankula maka da ita har lokacin da zaka dawo, zanyi hakanne don ALLAH da kuma zamowarta uwa agareka amatsayinka na d'a tilo da nake so fiye da komai arayuwata."

"Ita kuma matarka Ina so kayarda dani, na d'aukarma alqawarin zanci gaba dasa anayi maka sauka da addu'a har zuwa lokacin da ALLAH zai bayyana mana ita, zanyi qoqarin fahimtar da ita komai alokacin da tadawo izuwa gareka kuma na sadaka da ita akaro na biyu, na tabbata zata fahimceni tunda yarinyar nada ilimi da kuma fahimta.

Shiru yayi cike da son mahaifin nasa ya fahimci abunda yake nufi, baya son abunda zaisa Rashidarsa taji wani shakku azuciyarta akan soyayyar da yake yimata tahanyar barin qasar alokacin da bata tare dashi, nisawa yayi kafin yace

"Baffa.."

Da sauri baffa ya dakatar dashi tahanyar d'aga masa hannu yana fad'in.

"Shikenan! Na fahimceka ALLAH yasa hakan shiyafi alkhairi, Yana gama fad'ar haka yamiqe zuciyarsa a cunkushe duk da yayi qoqarin hana hakan ya bayyana a fuskarsa amma saida nuraddin ya fahimci hakan.

Toilet baffa ya wuce shi kuma yamiqe ya d'auke kwanon sannan ya Ida gyarawa, yana tsaye baffa yafito ya watso ruwa tare da canza wasu kayan yace dashi.

"To ni zan fita, zanje wajen baffanka akwai mganar da nake son tattaunawa akan mahaifiyarka dashi."

Bai jira jin amsar da zai basa ba yafice don baya son ya fahimci rashin jin dad'insa akan hukuncin da yake qoqarin yankewa kansa wanda yazab'awa rayuwarsa. Zaune Nuraddeen yayi akan katifa yadafe kansa da hannayensa duka yana furta, "Rabbi yassir wala ta'assir."

Yajima ahaka yana tunanin yanda rayuwa tayi masa d'aurin goro tahanyar rasa farincikinsa Rashida da kuma gudan jininsa dake jikinta, a b'angare d'aya kuma tsananin damuwar da yake ciki ta halin da mahaifiyarsa ke ciki dake neman tsaida dukanin al'amurransa, yanzu kuma ga fushin mahaifinsa na nema ya bayyana agaresa ta dalilin hukuncin da yaga yafi dacewa agaresa, miqewa yayi yabar gidan shima bayan yasa kwad'o ya rufesa sannan yanufi police station d'in,

Bai wani sha wahala ba inspector najida tasa aka kaishi inda take don ancanza mata waje saboda yanzu Bata qarqashin kulawar hukumar, tamkar ajiya take a hannunsu shiyasa aka kaita can cikin wani d'aki abayan station d'in daya tab'a gobara ya qone, tun daga kan tagogin wajen da qofofi duk sun qone, haka ma samansa abud'e yake saboda qonewar da rufin yayi, asalima nan jami'an 'yan sandan ke zagayawa domin biyan buqatocinsu na yau da kullum wato fitsari da bayan gida, duk wata rana da iska ko ruwan sama da akeyi akanta suke qarewa gashi an d'add'aureta gudun kada ta tsere, suna nufo wajen Nuraddeen yafara yatsine fuska yana toshe hanci saboda tsananin warin da yakeyi yana bin d'an sandar da kallo Mai cike da tarin tambayoyi har suka isa inda take, da sauri ya saki hancinsa yana zaro idanuwa waje hangota da yayi kwance cikin wajen dake kama da juji hannuwanta da afafuwanta d'aure da gudu ya isa wajenta tare da tallabota izuwa jikinsa batare daya damu da yanayin da take ciki ba yana fad'in.

"Innar mu, innar mu."

A hankali ta d'ago kanta tana kallonsa kafin ta saki wata irin muguwar qarar da tasa baisan lokacin daya saketa ba ya koma gefe, wani qaqari tashigayi kafin yaga anfara juyata cikin qonanniyar dattin dake cikin wajen ana birgima da ita tamkar wata halittar da batada qaffuwa, qananun gilasaiyen dake wajen ne suka shiga yayyanke mata jiki tana cigaba da wata qara mai cike da nuna tsantsar azabar da take ciki, ganin haka yasa yasake zuwa ya tallbota yariqeta yana kuka yana fad'in.

"Kidena innar mu, don ALLAH kidena innar mu kada kijima kanki."

Rungumeta yayi tsam don kada ta kucce masa yana aza kansa bisa jikinta, ganin haka yasa tasa baki ta kaimasa cizo ahannu har saida taciro da naman jikinsa amma yaqi sakinta saima sake rungumeta da yayi sosai yana kuka yana fad'in "kibari innar mu."

Yanayin qugi da gumzar da qarar da takeyi yasa inspector najida da sauran 'yan sandan zagayowa sukayi tsaye suna kallon ikon ALLAH, lallae duk lalacewar uwa uwace kuma baza'a tab'a iya shiga tsakaninta da d'an taba.

Wani yunquri tayi da yasa d'aurin dake hannuwanta faccewa da qarfi ta turesa gefe har saida yabugi jikin bangon wajen ya dawo, 'yan sandan naganin haka suka shigo wajen had'e da qoqarin rirriqeta, ganin tana neman tafi qarfinsu yasa wani d'aya daga cikin 'yan sandan qaqqarfa ya d'auketa kyakkyawan marin da yasa saida ta kife qasa, wani irin kukan kura Nuraddeen yayo kansa had'e da cakumar wuyansa ya kaisa jikin bango ya shaqesa yana fad'in.

"Kai waye da har zaka dakarmun mahaifiya agabana?, Kasan me ake kira da uwa kuwa?, Kasan muhimmancinta ga 'ya'yansa da zaka dokarmun abita?."

Maganar takeyi idanuwansa sun kad'a sunyi jawur ga wasu irin jijiyoyi sun taso masa a goshi yana turo idanuwa awaje."

Jin yafara kakari yasa wasu 'yan sandan dawowa wajen suna qoqarin janyesa amma gaba d'aya su ukun ya turesu yafara kaimasa naushi a fuska da ko ina ajiki, dukansa yakeyi yana fad'in.

"Wayace ka daki mhaifiyata?, waye yace ku d'auremun ita haka?, Akan me zaku kawota anan ita ba dabba ba?"

Duk d'an sandan daya nufosa sai yakai masa duka hakan ya b'atawa inspector najida rai nan take tbasu damar suyi masa duka, ai kamar jira sukeyi suka rufar masa da duka Saida suka yi masa liqis sannan suka qyalesa tace a d'aukesa ajefasa cell.

Ranta a b'ace takira baffa lokacin yana wajen baffa Usman suna tattaunawa akan asibitin daya dace akai Yaya hawwar ta sanar masa da abunda Nuraddeen yayi nayiwa 'yan sandansu duka a police station d'in.

Jikinsu narawa shi da baffa Usman suka nufo wajen kowane da abunda yake saqawa aransa.

••• ••• •••
Kwanan Dr.nura biyu yana rage aikace aikacen daya isko sun tarar masa a asibitin tasu sannan ya nufi anguwarsu umma agarin yarimawa, awannan karon bisa mashin yake tunda baizo da motarsa ba shiyasa batare daya sha wata wahala ba yasamu wani mutum ya tambayesa zancen iyayen Rashida da har lokacin yaga gidan a kulle da kwad'o.

Nan mutumen ya sanar dashi komai har yana d'ora masa da "yanzu haka ina tabbatar maka cewa babu Wanda yasan inda iyayenta suka nufa balle asan halin da suke ciki."

Wani irin jiri ya d'ibesa da yasashi saurin dafe bushiyar iccen dake kusa dashi yana fad'in.

"Hazbunallahu wani'imal wakeel, wannan wane irin mummunan labari ne kunnuwana suka jiyomun."

"Abun gaskiya ba dad'i sai haquri." Mutumen yafad'a had'e da wucewarsa, koda ya d'ago kai daga jimamin da take ciki da niyar yimasa wata tambayar sai yaga har yabar wajen, bai bar anguwar ba har saida yasake tambayar mutum uku don ya tabbatar da abunda nafarkon yafad'a suna bashi amsa iri d'aya da tasa sannan yabar anguwar jikinsa a sanyaye, kwana biyu yaqara kafin yakoma borno cike da tunanin irin amsar da zai baiwa Rashida idan ta tambayesa iyayenta, daga qarshe dai ya yanke hukuncin zai bari har zuwa wani satin idan sunje taganema idanuwanta ammashi tabbas bazai iya fad'a mata ba.

Sosai yayi qoqarin sakin jikinsa lokacin daya koma amma saida Fatima tafahimci akwai abunda ke damunsa, yanda ta tsaresa da tambaya yasa ya sheda mata komai ba tare daya b'oye mata ba tare da shawarar daya yanke, nan take tagoya masa baya tan kukan tausayin Rashida akan halin da zata shiga idan sukaje ta tarar iyayen nata basa nan. rungumeta yayi yana lallashinta don yasan halinta sai takai gobe tan kuka har yakai ga Rashida tafahimci abunda ke faruwa.

A b'angaren little Nuraddeen kuwa yayi wayau sosai don har ya iya zama, sak kamarsa da Rashida ke dad'a fita da kagani babu tambaya kasan yaron tane. Wani irin so takeyi masa marar misaltuwa da yasa Bata qaunar abunda zai sashi kuka ko kad'an, duk Wanda ya kallesa sau d'aya sai yaqara saboda yanayin jikinsa da kuma tsabtarsa shiyasa duk wanda ya gansa sai yayi sha'awar d'aukarsa, a daddafe suka hau yima Rashida Shirin komawa gida ita da little sai murna takeyi, katsar watsar tasamu satin ya qare wani yashigo yakama gobe zasuyi tafiyar don harda Fatima za'a.

Basu suka gyara ba sai kusan qarfe d'aya na rana saboda wasu 'yan abubuwa da Nuraddeen ya tsayayi, shidai Nuraddeen sai binta yakeyi da kallo yana jimamin abunda zata riska idan sunje, Saida yayi mata nasiha sosai akan rayuwa da kuma muhimmancin yadda da qaddara mai kyau ko marar kyau, sannan ya tabbatar mata da cewa sauran maganin little Nuraddeen na cikon wata d'aya daya rage in Sha ALLAH zai karb'a sai ya kaimata idan lokacin yayi tana tayi masa godiya harda 'yar qwallarta, haka ma Fatima tayi mata godiya sosai suka rungume juna kafin suwuce su d'auki hanyar zuwa kano tana murna tana qarawa.

••• ••• •••
A b'angaren su umma kuwa Saida suka kwashe kwana uku suna yawo acikin borno kafin baba yagano Wanda yake nema, haka suke buge yini suna yawon tambayarsa in kuma dare yayi sai suje asibiti su shige cikin majinyata su kwanta da safe kuma su sake fita nemansa har ALLAH yasa suka ganesa, hannu biyu mutumen ya karb'esu bayan baba yayi masa bayanin dalilinsu na zuwa garin saida, sosi ya jajanta masa tare da yimasa addu'ar ALLAH ya bayyana masa inda 'yarsa take, nan yabasu wajen da zasu zauna acikin gidansa acan baya inda d'akunan masu aikin gidan suke sannan yace suyi haquri zai sama masu abunyi nan da kwana biyu, bayan kwana biyu ya tambayi baba in zai iya zaman tsaron wani sabon shagonsa daya bud'e zai dinga biyansa albashi duk wata dubu goma idan ya amince bisa amana da Kuma yardar daya yimasa, nan take ya amince har yana duqawa had'e da yimasa godiya, ita kuma umma d'aya daga cikin matan alhajin taroqa ta dinga yimata aiki duk wata zata biyata dubu hud'u, daga alhajin har baba basuso hakan ba amma nan take umma ta amince da zatayi aikin, acewarta hakan zai d'an d'auke mata hankali da ace tayi zaune ita kad'ai bata komai sai aikin tunanin b'atan 'yarta. Babu yanda suka iya tunda ta amsa zatayi, ajiyar zuciya alhajin yayi kafin ya kalli matar tasa bayan sun wuce yace.

"Hajia nafeesa don ALLAH kada kiyiwa baiwar ALLAHn nan abunda kika saba yiwa sauran masu aikinki, mutanene masu kirki da daraja agarena don haka kada kiwatsamun qasa tahanyar tozartar dasu don suna aiki aqarqashinki, zamane zamuyi dasu nad'an wani lokaci kafin su koma inda suka fito, saboda haka Ina roqonki daki mutuntasu don girman ALLAH kinji ko."

Saida ta yatsina fuska sannan ta mere baki had'e da kallon gefe tace.

"Naji.."

Hajiya nafeesa itace matarsa ta biyu, matada kirki ko kad'an ga son walaqanta mutane matuqar suka amsa sunan talauci atttare dasu kuma suka zamo qarqashinta, shiyasa yaja mata kunne tun kafin aje ko Ina saboda shi mutumne mai dattako, yau itace rana ta uku da umma tafara aiki a sashenta, Babu ruwanta da shiga sha'aninta iya karta tayi abunda tasata ta koma sashenta, kamar kullum yau umma tagama gyaggyara kitchen bayan aikin da tayi saiga baqi hajia nafeesa tayi, sai da aka kwashi mintuna uku sannan ta d'ibi ruwa da lemuna ta kaimasu a falo tare da russunawa ta gaishesu sannan ta koma kitchen, sake kirawota tayi had'e da cewa.

"Umma jeki ki kawo masu fruit"

Saida taje kitchen tabud'e fridge d'in taga babu komai sun qare sannan tadawo taduqa tare da cewa.

"Hajia ba'a samu kawo wasu ba, Kuma naciki sun qare."

Batare da hajia nafeesa ta damuba taje d'aki tad'auko dubu uku tadawo falon tare da jefowa umma kud'in tace.

"Jeki kicewa driver nace ya kaikai inda aka siyo mana kisawomun, kiyi sauri Ina jira yanzu yanzu kinji ko."

"To hajia." umma tafad'a tare da d'aukar kud'in tabar falon.

Tafe suke ita da drivern har suka kai daidai wajen da zata siyo fruit d'in yayi parking acan gefen titin yana nuna mata tsallake inda suke yace

"Umma ki tsallaka acan kice daga gidan alhaji aka turoki, zasu had'a maku duk abunda suka san ana buqata."

"To"

Umma ta and masa tare da bud'e marfin motar tafito tana waige waigen gefe gefe don tasamu ta tsallaka.

A daidai lokacin motarsu Dr nura tazo wucewa yana sauri ganin har qarfe d'aya na rana yayi saboda bayason suyi dare ahanya gashi ko cikin garin basu fita ba......






*ALLAH KAJIK'AN IYAYENMU*👏😭
[11/14, 22:52] Billy S Fari: 🚶‍♀️🚶🏻‍♂️ *SANNU SANNU*🚶🏻‍♂️🚶‍♀️
💎 _Bata hana zuwa..._💎


_WRITTING BY:_ *BILLY S FARI💎*

_DEDICATED TO:_ *BLOOD SISTER'S (AMZAHFAZ)*💋

_BESTOWED TO:_ *ZAINAB AL-AMIN (MOM NA'EEM)* AND *AMINA UBA AYUBA (OUM ASHFAQ)*💞

*DOMIN FARINCIKINKI SISTER SADIYA ZANGO (MIEMAH)*💖

*FATAN ALKHAIRI AGAREKU MOMMAH ME NANA HAFSAT (MISS XOXO) AND MAMANA HAFSAT RANO(OUM AFFAN)*❤️

Page___53💎

Umma na tsallakowa a dai dai tsakiyar titin Dr. Nura na kawowa da sauri ya sakar mata oda yana qoqarin juya starring nasa wanda kad'an ya rage ya bugeta, daga Fatima har Rashida runtse idanuwa sukayi had'e da dafe kai suna fad'in. "Innalillahi wa'inna ilaihirrajiuun."

Ita kuma umma tsabar tsoro duqewa wajen tayi jikinta na rawa, gefe yayi parking had'e da fitowa ganin takasa motsawa daga duqen da take a tsakiyar titin ya nufi wajenta. Kafin ya isa har drivern da sukazo tare yazo ya jayeta ya nufi wajen motar yana masifa da ita,

"Umma kar kizo ki jazamun bala'i, duka duka yau kwanana uku da d'auka aiki agidannan kizo kisa akoreni, fisabillahi idan kinsan bazaki iya tsallakawa ba ai saiki fad'amun, gashi yanzu da kinja mani fitina." Maganar yakeyi kamar zai doketa saboda tsananin takaici, ganin babu abunda yasamu matar yasa Dr nura juyawa yakoma wajen motarsa yana girgiza kai had'e da fad'in ALLAH ya sawaqe, kallon Fatima yayi dake faman jijjiga little Nuraddeen dake kuka saboda tsoron qararsu da yaji ta tadashi daga baccin da yakeyi yace

"Bari na tsallaka nabawa matar can haquri duk da dai naga bataji ciwo ba."

"Haba saurifa mukeyi, tunda ALLAH ya kare kuma ba laifinka bane kawai mutafi ALLAH ya tsare gaba."

"Amin ya amsa yana qoqarin bud'e marfin motar ya shiga sai yaga drivern ya iso wajen masu fruit d'in, fasa shiga yayi ya nufi wajensa ya bashi hannu suka gaisa sannan ya amsa gaisuwar da masu fruit d'in keyi masa dake nuna sun sanshi,

"Amm..don ALLAH kabawa matar can da muka kusan samun tsotsayi da ita haquri, sauri nakeyi amma tunda ALLAH ya tsare naga dacewar nayi maka magana tunda tare kuke kabata haquri."

"Babu komai ranka ya dad'e, ALLAH ya tsare gaba kuma ya kaiku lafiya."

"Amin." Yafad'a tare da miqa masa hannu suka sake gaisawa sanna ya juya yashiga motar ya tayar suka kama hanya shi kuma drivern ya amshi fruits d'in ya tsallaka inda ya ajiye motar tasu, ta glass Dr nura ke kallonsa lokacin daya biyo bayansa don yayi utorn yace da Fatima.

"Matar wai kinsan wani abun, ashema motar gidace, sai yanzu na hango lambar dady dake jiki, kingasu nan sun biyo bayan mu."

"Allah sarki, to ko waye waccan matar?, Inaga dai sabon drive ne dady ya samu, Amma shima bayada mutunci, don me sunzo a mota bazai iya tsallakawa yayi parking acan ba sai dai ya tsaya acan tsallake kuma ya turo matar mutane a wannan babban titi hakan shi bazai iya fitowa ba sai ita."

"Iskanci samarin yanzune, Amma zanyi magana da dad a dinga tsawatar dasu akan tsofaffin mutane, inaga d'aya daga cikin masu aikine hajiya nafeesa ta turo kinsan halinta."

"Zata iya yuyuwa gaskiya, ALLAH ya kyauta." A daidai lokacin da suka tsaya a bakin junction suna jiran traffic tabasu hannu drivern yazo saiti dasu Dr nura ya juyo ya kallesa yana fad'in.

"Kin gashi ko?" Fatima tajuya ta kalli drivern daya qore sautin kid'an motar yana kad'a kai, dai dai lokacin itama rashida ta d'ago kai ta gefenta tana kallon motar da taji suna fira akai, motace mai kyan gaske don zata iya cewa takusa kyn ta Dr.nura ko kuma suzo d'ai, matar dake ciki tajuyar da kanta can gefe take kallo da jikinta yabata kmar ta santa kota tab'a ganinta awani wajen amma rashin juyo fuskarta da tayi yasa takasa tantance haka, tan wannan tunanin ne little Nuraddeen ya tsanyara kukan da ya maido hankalinta agaresa tare da qoqarin turasa cikin mayafinta don tabashi nono, a lokacin ita kuma umma tajuyo fuskarta ta b'angaren tana qarewa yanayin kyawon garin da yanda motocin suka tsaitsaya suna jiran abasu hannu suwuce amma kasancewar glass d'in motar tasu Dr nura tinted ne yasa takasa hango 'yar tata dake ciki tana kicaniyar bawa little Nuraddeen har traffic d'in tabasu hannu, jin motarsu tafara tafiya yasa Rashida d'agowa tare da maida kallonta wajen amma sai taga wayam tuni har motar tajuya ta d'ayan hannun takoma baya sukuma suka miqe hanyarsu tabarin cikin garin.

••• ••• •••
Baffa ya matuqar tsorata da abunda yaji inspector najida tace Nuraddeen ya aikata, sukayita bata haquri shida baffa, daqyar suka samu tabasu belinsa saboda yanda ranta ya matuqar b'aci kafin tace.

"Baba kaja masa kunne don idan ya sake maimaita hakan zamu kaishi a hukuntashi ne saboda babban laifine civilian yasa hannu ya bugi kowane irin kaki, don haka kajamasa kunne, kawai na qyalesa ne albarkacinka daya sai mun ganar dashi kuskurensa"

"To 'yata nagode nagode sosai."

Kallon Nuraddeen da duk yafita hayyacinsa yayi had'e da cewa "tashi muje."

"Babu inda zanje baffa matuqar innarmu na wannan wajen." Nuraddeen yabashi amsa had'e da d'agowa yana kallonsa da ijiyarsa da aka bubbuge ta kumbure.

Cike da mamaki suka bishi da kallo kafin baffa Usman yace. "Haba Nuraddeen, kayi haquri, zamu d'auke mahaifiyarka anan amma kasan komai sai anshirya, kabi komai ahankali insha ALLAH zamu fidda ita nan kuma zata samu lafiya, yanzu haka muna tattaunawa akan maganar ne inspector najida ta kirawomu, kayi haquri ka taso muje kaji ko."

"Baffa bazan iya ba." Yafad'a tare da miqewa zai koma cikin cell d'in baffa ya bishi da kallo, saurin dakatar dashi baffa Usman yayi had'e da cewa.

"Dawo Nuraddeen za'a fiddo da ita kaji!"

Baffa zaiyi magana baffa Usman ya dakatar dashi had'e da cewa "a'a ya kabarshi, inspector najida ya za'ayi kubamu ita." Baffa Usman ya qarasa maganar yana kallonta.

"Bayada matsala baba, dama Bata qarqashin kulawarmu don haka zaku iya zuwa ku d'auketa ko yaushe, Amma d'aukarta akwai had'ari sosai saboda yanayin da take ciki bai kamata ace an d'auketa ankaita cikin mutane ba, wannan kawai shine matsalar."

"To mungode, Kai Nuraddeen kaji abunda tafad'a, me kace."

"Ni zan iya kulawa da mahaifiyata koma a inane, kawai ni bana buqatar zamanta ne a hannun wud'annan mutanen."

Shiru sukayi kafin sufice waje suna tattaunawa akan inda yakamata akaita daga qarshe suka yanke shawarar ajiyeta can gida a d'akinta, ciro waya baffa Usman yayi yakira maqwabcinsu dake jigilar motar haya,

Bayan mintuna sai gashi yazo da motarsa sukaje aka d'auko Yaya hawwa tana kucce kucce, aka sata baya sannan Nuraddeen shima ya shiga ya riqeta, kallon baffa Usman baffa yayi yace yashiga gaba, shi zai biyosu abaya ya shiga suka wuce,

Godiya ya sake yiwa inspector najida sannan ya nemi Mai mashin ya hau yabi bayansu.

Ba qaramar wahala Nuraddeen yasha ba kafin su isa gida don duk ta yakusheshi, haka ma da zasu shigar da ita daqyar da sud'in goshi yasamu yashigar da ita cikin gida har d'akinta don hana kowa ya tab'ata yayi ganin yanda sai ihu da dariya yaran shiya ke yimata.

Baffa na saman mashin ya kira baba balarabe yana tambayarsa jikinsu baba balarabe, nan ya sheda masa halin da ake ciki na b'atansu, baffa yashiga tashin hankali sosai marar misaltuwa yashiga sallallami har ya iso gidan, yana isowa ya tadda baffa Usman tsaye shida baffa Ali yana surfa masa masifa akan don me za'a kawo masu mahaukaciya acikin gida tahanasu bacci ta illata masu iyali, yana ganin baffa ya d'aure fuska had'e da zunduma ashar sannan yabar wajen, baffa dake cikin alhini da damuwan b'atan iyayen Rashida kota kansa bebiba balle yadamu da abunda yayi masa yashiga yima baffa Usman bayanin abunda ke faru.

"Astagfirullah, astagfirullah, astagfirullah ALLAH ka sassauta mana wannan jarabawar dake b'ullo mana d'aya bayan d'aya." Baffa Usman yafad'a yana zabga uban tagumi, ahaka Nuraddeen ya taraddasu baffa yayi masa bayani, awannan karon damuwa tayi masa nauyin da bayada kuzarin yin kuka balle ya zubar da hawaye, gefen baffa ya zauna ya d'ora kansa saman kafad'arsa ko zai samu sassaucin yanayin da yakejin kansa aciki, tabbas ubangiji baya zalunci kuma baya goyawa mai zalunci baya domin yayi hani da hakan, haqiqa halin da mahaifiyarsa ke ciki ta cancanci zama ciki fiye da hakan saboda haqqin wud'annan bayin ALLAH da tayi sanadiyar fad'awarsu cikin wani hali suda 'yarsu,

A hankali ya d'ago kansa yana kallon baffa yace.

"Baffana shin kana fushi da inna ne har yanzu?."

"A'a Nuraddeen bana fushi da ita Amma aduk lokacin dana tuna cewa ita wani sashece acikin rayuwata kuma mahaifiyar d'ana nakanji ba dad'i."

"Kayafe mata Baffa nasan hakan zaisa tasamu sassucin halin da take ciki."

"Ko kad'an Nuraddeen bani tunanin haqina na daga cikin dalilan da ALLAH ke hukuntata domin tun aranar da ALLAH ya wanzar da tsinkewar alaqar dake tsakaninmu nayafe mata dukkanin haqqina dake kanta kuma ALLAH shine sheda akan haka."

Sake maida kansa yayi saman kafad'ar tasa sannan yace.

"Kayi haquri baffana, haqiqa dukanin mumini baya kaucewa jarabawarsa, in Sha ALLAH da sannu quncinmu zai koma farinciki."

"ALLAH ya qaddara hakan Nuraddeen."

Cike da tausayi baffa Usman ke kallonsu, haqiqa ALLAH shi yake fidda farin tuwo acikin baqar tukunya kamar yanda ya fidda Nuraddeen acikin Yaya hawwa, Wanda gaba d'aya kyawawan halayensa na mahaifinsa ne ya gado, sunjima awajen kafin akira sallar la'asar suje suyo SALLAH sannan suka kama hanyar yarimawa.

Gidan baba balarabe suka sauka suka jajanta masa akan abunda yafaru kafin sujuyo sudawo gida.

Da daddare suna zaune sunacin abinci sukaji sanarwar batun tafiyarsu Nuraddeen nan da kwana uku ana masu aqa gargad'insu dasu kasance cikin shiri, Nuraddeen na kallon yanda yanayin fuskar baffa takoma lokacin da aka fara sanarwar har aka gama yana saurare yayi ajiyar zuciya had'e da cewa Allah ya sawaqe.

Cikin kwanaki ukun da suka rage kullum Nuraddeen shike zuwa da kansa d'akin Yaya hawwa da aka kulleta ciki ya bata abincin safe rana da kuma dare, haka kuma yakanyi qoqarin gusar mata da duk wata najasa da tayi da dattin dake taruwa cikin d'akin, Bata barin qazanta ko kad'an atattare da ita koda kuwa tana dukan sane har sai yaga ya tsaftace ta.

Shi kuma baffa tuni suka gama yanke shawarar Kai Yaya hawwa asibitin mahaukata ta uduth dake jahar sokoto wanda tafiyar takama ranar dasu Nuraddeen zasu wuce, shire shire kawai baffa keyi nakai Yaya hawwa asibitin batare daya koma kula zancen maganar tafiyarsu Nuraddeen ba saboda yanda yaga yafita batun abun,

Da daddare awayi safiyar ranar baffa na zaune shida baffa Usman suna fira saiga Nuraddeen yadawo kayansa duk ajiqe sanadiyar ruwan saman da akayi suka yimasa duka, binsa da kallo sukayi har yaje yacire kayan jikinsa ya canzo wasu yazo ya zauna inda suke yana mai saqale hannuwansa waje d'aya ya d'ora akn qirji,

"A'a, Nuraddeen daga Ina kake haka ruwa sukayi maka duka?." Baffa Usman yafad'a yana kallonsa, saida ya kalli mahaifinsa dake qoqarin had'o tea a cup sannan yace.

"Daga wajen bankwana nake baffa Usman."

Miqo masa cup d'in tea daya had'a Mai zafi har yana tururi baffa yayi had'e da cewa.

"Bankwana fa kace Nuraddeen, Ina zaka jene?"

Saida

Please Login or Register in order to submit comment