Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da gaske."

Dariya duk suka samata harda Rashida da tun d'azu takasa kai koda cokali d'aya abaki sai faman cakularsa takeyi,

"Hmmm! Yakamata nabiya kud'in zobonnan tunda yasa madam Santi har na tsinkayo ana yimata waigi."

Dr nura yafad'a yana dariya ganin aunty marwiyya na gyarawa Fatima hilon dake bayanta, juyowa tayi had'e da cewa.

"Au..Ashe da gaske yakeyi, kai aunty marwiyya zakija yadinga tsokanata kuwa."

Kallon Rashida baba balarabe yayi had'e da d'aure fuska yace.

"Ke Rashida maza kici abinci kinji ko?" Ganin bada wasa yakeyi ba yasa tafaracin abincin tana b'ata fuska tamkar wacce keshan magani.

Yanda su Dr suka saki jikinsu cikin 'yan uwan Rashida Kai ka rantse kace Abu d'aya suke ko kuma sun jima da sanin juna, hakan Kuma ba qaramar shaamquwa da yarda ta sake shiga tsakaninsu.

Bayan kowa yaci yasha ya qoshi, baba balarabe yayi gyaran murya had'e dayin doguwar addu'a da nasihohi masu ratsa jiki bisa abunda ya faru sannan yarufe dayiwa su dr.nura shida matarsa godiya sosai shida su Yaya Maryam, irin godiyar da suke yimasu da kyawawan addu'o'i had'e da fatan alkhairi har seda suka fara jin kunya, daga qarshe aunty marwiyya tace.

"Mungode sosai Fatima matar nura uwar nura, muna roqon Rabbissamawati wal ardi daya azurtaku da 'ya'yaye nagari masu albarka da zakuyi alfahari dasu duniya da lahira, ALLAH yakareku daga dukknin sharrin abinqi ya lullub'eku da rahamarsa da tausayinsa yayi maku arziqi mai yawa ya share maku dukkanin kukanku."

"Amin ya ALLAH aunty."

Suka amsa cike dajin wani dad'i da sanyi da farinciki azuciyarsu,

Itama Rashida hawaye nazubar mata a idanuwa ta rungume fatima tana fad'in.

"Dukkanin alqawurranku agareni wanzazzune hakama alkhairanku tabbataccine akaina, karamcinku da halacci masu girmane da mizaninsu yakai girman da bazan iya biyanku aduniya ba, amma har zuwa fitar lumfashina zuciyata da Kuma rouhina cike da qaunarku mai tsanani take, duk wani fitar lumfashi nawa cike yake da fatan alkhairan ALLAH agareku da kuma farinciki mai d'orewa, ina roqonku da kada kucireni acikin rayuwarku kada kumanta dani kubani damar da zan iyaci gaba da rayuwata tare daku matsayin 'yan uwa batare da zumunci ya yanke a tsakaninmu ba har izuwa ranar da zan kwatanta faranta maku zuciya kamar yanda kuka faranta tawa data ahalina koda sau d'aya ne."

"Bazamu mantaki ba Rashida, bazamu rabu dake da little ba don kunzamo wani yankin daya sama mana farinciki na wani d'an lokaci arayuwarmu wanda muke fatan yatabbata atare damu har abada" Fatima tafad'a itama had'e da rungumeta tana kuka, kuka sukeyi sosai sai kace wud'anda suka rabu kenan har saida Dr nura ya cewa Fatima ta taso sutafi yana mai mamakin yanda shaquwa mai tsanani haka tashiga tsakaninsu a qanqanen lokaci,

'Daukar little tayi ta sumbacesa agoshi tare da wucewa gaba suka rakosu qin miqasa tayi har saida ta shiga mota Dr nura na Shirin tayarwa sannan ta badashi tana goge qwallan da suka zubo mata, shi kanshi Dr nura saida yaji ba dad'i Amma babu yanda suka iya dole yaja motarsa sukabar wajen.

Su kuma yana tafiya rigima ta kaure tsakanin baba balarabe da yace a dole akira Nuraddeen da ahalinsa asaanar dasu yayinda sukuma su aunty marwiyya sukace atafau bazai yuyu ba, daga qarshema Yaya Maryam bugawa Rashida tsatsauran Jan kunne tayi akan karta sake koda mafarkine tayi tunanin zata koma gidan Nuraddeen tunda mahaifiyarsa bata sonta.

Shikuwa baba balarabe duk da Yaya Maryam na sama dashi haka yatabbatar mata da cewa dole sai yasanar da Nuraddeen anga matarsa saboda haqqinsane kuma har lokacin tana aqarqashin igiyar aurensa, hakan yasa suka rabu baran baran, rayuwakan kowanensu a b'ace.

Yana komawa gida yashiga Kiran lambar baffa data baffa Usman Amma shiru kowace switch up, hakama ta Nuraddeen yakira yafi a qirga itama akashe saboda bai fara anfani da sabon layin daya siya acan.

Hakan yasa hankalinsa tashi sosai marece nayi yanufi garin bebeji, yana isa yaci karo da baba Ali ya tsaya yana tambayarsa, sunjima suna magana kafin baba balarabe yabar wajen jikinsa a sanyaye, wata 'yar iskar dariya baffa Ali yayi sannan yawuce yana fad'in "da sannu duk sai kun gane kurenku har ita wacce sanadiyar b'atanta aka rufemu nida iyalina aka yimana dukan mutuwar da gangar jikinmu takasa d'auka"

Kwana baba balarabe yayi yana juyi akan abunda baffa Ali ya sanar dashi duk da dai wani b'angaren na zuciyar tasa bai yarda da hakan ba.

••• ••• •••
Su Baffa kuwa a maimakon kwana d'aya da zasuyi agarin sokoto sai da sukayi kwana biyu saboda shawarar da wani likitan yabasu akan sukai marar lafiyarsu kware shine abunda zaifi masu sauqi, hakan yasa suka sake kwana d'aya acan har saida suka gama shirya duk abunda yakamata acan asibitin kware suka biya kud'in da za'a basu mota da jami'an lafiyar da zasu d'aukota sannan suka juyo zuwa gida bayan sun bada address d'in da za'a tura masu motar nan da kwana biyar, gaba d'aya wayoyinsu sun mutu saboda rashin charji da basuda wannan ne dalilin da yasa baba balarabe yayita kiransu bai samu ba.

Saida suka iso zamfara don dama motar da zata ajiyesu acan sai daga nan su shiga wacce zata kaisu kano suka shigo kafin motar da suka samu ta kano ta cika suka shiga masallacin dake cikin tashar sukayi sallah sannan suka samu wani saurayi ya ara masu chargarsa sukasa wayar baffa charji, minti talatin sukayi sannan motarsu tacika lokacin baffa har yasamu d'igo biyu a 'yar wayar tasa qirar kamfanin itel mai madannai.

Mintuna biyu yayi da kunnata kiran baba balarabe ya shigo.

Cikin natsuwa baffa ya d'aga had'e da amsa sallamar da yayi masa sannan suka shiga gaisawa.

"Am dama wata magana naji cewa Nuraddeen yabar qasar nan shine nace bari nakira naji shin ko gaskiya ne.?"

Wani irin nauyi baffa yaji Amma bayada wata hanyar da zai iya basa amsar tambayar da yayi data wuce eh ko kuma a'a, tamkar baffa nagabansa ya duqar da kai had'e da cewa.

"Eh malan balarabe hakane amma..." Kafin yaqarasa baba balarabe ya katsesa ta hanyar cewa.

"To madallah, shikenan nagode." Had'e da kashe wayarsa, duk inda ransa yake in yayi dubu ya b'aci, Ashe akwai ranar da Nuraddeen zai nuna irin wannan halin ko inkula agaresu adaidai lokacin da suka rasa 'yarsu a hannunsa, Ashe har yanada qwarin guiwar da zaya iya barin gari acikin yanayin da yake kuma har yatafi batare daya yimasu sallama ba?, Me suka yimasa da suka cancanci haka daga wajensa? Ai koba komai ana bankwan saboda ba'asan halin rai ba, kuma ai yakamata ace ko don kaucewa zargi yazo yayi masu bayani, wud'annan tambayoyi sune suka dinga Kai da komo acikin zuciyarsa da kuma qwaqwalwarsa, rashin samun amsar sune yasake tunzurasa sosai,

Ransa ab'ace yanufi gidan Yaya Maryam yakirata tare da zayyane mata duk abunda kefaruwa, dama tayi mamakin ganinsa shida jiya suka rabu baran baran da ita sai gashi har yana fad'in ko mijin Rashida naso ko baya so duk inda yaje dolene ya saketa, kuma dole duk wata alaqa dake tsakaninsu su datseta koda hakan na nufin zasu mayar masa da d'ansa a hannun sane.





*ALLAH KAJIK'AN IYAYENMU*👏😭
[11/14, 22:52] Billy S Fari: 🚶‍♀️🚶🏻‍♂️ *SANNU SANNU*🚶🏻‍♂️🚶‍♀️
💎 _Bata hana zuwa..._💎


_WRITTING BY:_ *BILLY S FARI💎*

_DEDICATED TO:_ *BLOOD SISTER'S (AMZAHFAZ)*💋

_BESTOWED TO:_ *ZAINAB AL-AMIN (MOM NA'EEM)* AND *AMINA UBA AYUBA (OUM ASHFAQ)*💞

*DOMIN FARINCIKINKI SISTER SADIYA ZANGO (MIEMAH)*💖

*FATAN ALKHAIRI AGAREKU MOMMAH ME NANA HAFSAT (MISS XOXO) AND MAMANA HAFSAT RANO(OUM AFFAN)*❤️

Page___59💎

Baffa, baffa, baffa ga aunty tadawo, abunda Yusuf kefad'a kenan har ya isa bakin qofar shiga gida, karo yaci da mahaifin nasa wato baffa Ali shida Dr. nura dake qoqarin barin wajen fuskarsa a cunkushe babu alamun walwala atattare da ita, kad'an yarage Yusuf yafad'i garin kallon Dr nura daya ga yanufi inda su Rashida suke, da sauri ya riqo hannun baffa Ali yana jansa had'e da nufar inda ya gasu Rashida yana nuna masa wajen da hannu, gaba d'aya Yusuf ya rud'e ya manta da cewa ba mahaifinsa yakamata yasan da dawowar taba sanin irin matsayin da take dashi awurinsa.

Baffa Ali kuwa binsa yayi har suka isa wajen lado mai kalanzir, lokacin kuwa har su Rashida sunbar wajen saboda irin amsar da Dr nura nura yazo masu da ita,

"Lado Ina aunty?"

"Kai yusuf wace aunty kuma?."

"Haba lado! Anan fa nabarta ita da wata mata, nan wajen!." Yaqare maganar yana nuna masa inda suka tsaya.

"Aiho nan naga sunbi suda wani mutum." Lado yafad'a yana d'aure ledar daya zubawa wata yarinya kalanzir.

Dagudu Yusuf yabi hanyar baffa Ali shima yabi bayansa don yatabbatar da da hakan,

Suna kawowa su Rashida naqoqarin shiga mota ya shiga qwala mata kira.

"Aunty, auntyyyy.."

Juyowa tayi tana goge hawaye harya iso wajen, da sauri baffa Ali yab'oye bayan wani kango yana hangosu don kada taganshi.

"Aunty ina zaki tafi kuma, kizo muje gida don ALLAH, ya nura nason ganinki shida su baffa da Inna bilki, kowama nason ganinki munyi kewarki sosai don ALLAH kizo muje kinji aunty."

"Yusuf me zanje inyo agidanku Bayan wanda nazo don shi gaba d'aya yabar qasar, zantafi Kuma bazan sake dawowa acikin gidanku ba saboda bakwa sona." Tafad'a tana kuka tare da juyawa zata shiga motar, riqe hijab d'inta yayi shima yana kukan yace.

"A'a aunty muna sonki don ALLAH kada kitafi."

Hannunta tasa tacire hannunsa daga riqon daya yiwa hijabinta sannan tafad'a cikin motar Dr. Nura yaja sukabar wajen.

Kuka Yusuf keyi kamar ransa zai fita had'e da nufar hanyar zuwa gidan baffa, da sauri baffa Ali yafito daga mab'uyar daya shige yatare gabansa had'e da kamo hannunsa,

"Kai Yusuf ina zakaje ne acikin daren nan?"

Ya tambayesa had'e da d'aure fuska yana kallonsa.

Cikin sheshshekar kuka Yusuf yace.

"Gidan baffa zanje."

"Kaje kayo ubanmi acan?."

"Zanje infad'a masa Aunty tadawo amma ta tafi kuma tace bazata sake dawowa ba."

Saida ya sakar masa wani mugun ranqwashi akai sannan yace.

"To uban waye ya aikeka? idan Auntyn tadawo qanwar uwarka ce kota ubanka da zakaje kasanar dasu tunda tace bazata koma dawowa to meye naka aciki.?"

Qoqarin bud'e baki yayi don ya bashi amsa sai Kuma yayi saurin rufewa da hannunsa sanadiyar yanda ya murd'e masa kunne so had'e da cewa.

"Karka sake inji kafidda wannan maganar waje kaji nagaya maka, inba haka ba yanda Yaya hawwa ta b'addata kaima haka zansa a b'adda kai, kaga shikenan baka ba ganin kowa naka wata qilama kamutu gaba d'aya ahuta, shashashan yaro kawai, har kamanta akanta akaje aka kullemu ni da mahaifiyarka, babu kalar azaba da kuma dukan da bamu sha ba ahannun 'yan sanda kuma duk ta dalilinta, to bari kaji duk kasake naji wannan maganar abakin wani sai nayi maka d'an banzan duka kuma wlh kadena cin abincin gidana kenan har kamatu, shegen yaro da bansan halin waye kad'auko ba, maza kawuce gida kafin in jijjimaka anan"

Sosai Yusuf ya tsorata dajin kalaman da baffansa ya fad'a masa don haka yanufi gida yana kuka kamar ransa zai fita, kasa shiga d'akin mahaifiyarsa yayi yakoma saman barandar part d'insu ya Nuraddeen dake rufe ya had'a kai d guiwa yanaci gaba da kukansa, tun qarfe takwas yake zune wajen yana kuka har wucewar goma da rabi nadare kan kace me tuni zazzab'i ya taso masa ya fara rawar sanyi, Inna Bilkisu ce tafito zata zagaya bayi tagansa wajen a kwance had'e da cewa.

"Kai Yusuf lafiya kazo nan ka kwanta ko sanyin nan bakaji?, Maza tashi kawuce d'aki kar mura takama ka"

Ba tare data tsaya sauraren amsar da zai bata ba tawuce bayi don yin lalurar data fiddota, koda tadawo ta tarar har lokacin yana a wajen kwance ko motsawa baiyi ba daga inda tabarshi

"Ikon ALLAH, wai bakaji me nace maka bane Yusuf.?"

Tafad'a tare da qarasawa wajen tana d'agosa, yanda taji jikinsa ya gashe da zafi sai faman rawar sanyi yakeyi yasa tayi saurin rungumosa ajiki tana daddafa kansa.

"Subhanallahi, Yusuf dama baka lafiya shine kazo nan ka kwanta."

'Dago kansa yayi yana qoqarin yimata magana saiga baffa Ali ya shigo shida baffa Usman, ai yana ganin haka da sauri yaqarasa wajen yana fad'in.

"Kai Yusuf mekakeyi wajen? Ko munafuccin ne kaima zaka koya." Ya zata maganarce yake fad'a mata,

Inna Bilkisu najin haka tacire Yusuf daga jikinta had'e da zaunar dashi saman barandar tanufi inda mijinta yake tsaye yana jinjina irin kalaman da d'an uwansa ke alqanta iyalinsa dasu, shi kuwa baffa qiiiii...yaja hannun Yusuf har yana neman fad'uwa yana fad'in.

"Wannan yaron anyi mai kunnen qashi, ina dai kasan abunda nace maka shine zakazo nan kasaki baki don rashin jin magana" hed'e da jefasa saman gadonsu d'an bono bayan sun shiga d'aki,

••• ••• •••
Dr kuwa banda tunanin kalaman da baffa yafad'a masa babu abunda yakeyi, wannan wace irin rayuwace muke ciki aduniya?, Wanda ma kayarda dashi alokaci d'aya sai ya sauya maka, ancuci yarinya kuma ankoma ana binta da sharri, a iya saninsa inzai tuna Rashida tafad'a masa cewa mahaifin mijinta na qaunarta Amma sai gashi maganganun daya fad'a masa akanta sunsha banban da irin kalaman daya dace afad'a ga wanda ake so, saita madubinsa yayi yana kallon yanda hawaye ke tsiyayowa daga cikin idanuwanta dake rufe ya saki wata irin ajiyar zuciya, tabbas ta cancanci tayi kuka ba kad'an ba, ko kad'an bazai hanata tayi shiba awannan karon saboda abubuwan sunyi mata yawa, a qaramcin shekarunta bai kamata ace tafuskanci irin wud'annan damuwowin ba donma Allah yataimaka ansamu jininta yakoma normal da tuni qila zuciyarta tabuga, duk da dai bai sanar da ita gaskiyar abunda yafaru tsakaninsa da baffa Ali ba daya nuna masa cewa shine mahaifin Nuraddeen, kawai dai ya fad'a mata cewa ance baya nan yabar qasar.

Tare suka shiga gidan da ita lokacin da suka iso yaya Maryam na tsaye tsakar gida tana jijjiga little da sai faman kuka yakeyi tun d'azu.

Miqa hannunta tayi ta karb'esa kanta naduqe aqasa batare data bari sun had'a ido da yaya Maryam ba data zuba mata ido tana kallo.

'Daki tawuce, su kuma suka tsaya suna gaisawa da ita,

"Sannu Dr har kin dawo.?"

"Eh ya gida yaya Maryam."

"Gida Alhamdulillah Dr, kunbarni da yaro sai faman tsula Mani kuka yakeyi?"

Murmushi yayi had'e da cewa.

"Afuwan ai gamu mun dawo, dama kwana biyu Fatima tadameni da zancen ta shine nace bari muzo dubata sai gashi munci karo da ita, ganin babu alamun walwala atattare da fuskarta yasa nace bara muje da ita wani wurin taraka mu, I fatar za'ayi mana afuwa bisa wannan kuskuren?" Yafad'i hakanne saboda yasan ran Yaya Maryam b'aci zaiyi idan tasan gaskiyar inda sukaje.

"Ba komai Dr, ai kaga Fatima gaisawa kawai mukayi tabi bayansu saboda sukad'ai tadamu dasu"

Shiru yayi na tsawon wasu 'yan sakanni kafin yace.

"Amm! Dama yaya maryam cewa nayi yakamata ariqa kwantarwa da Rashida hankali saboda yanayin damuwowin da suka tarar mata azuciya don kar takoma shiga wani halin, nasan kuna qoqari sosai tunda gashi naga cikin kwanakinnan tacanza ba kamar yanda muka zoba saboda yanayin natsuwar da tasamu, amma don ALLAH aqara bata kulawa, sha'aninta akwai bantausayi aciki sosai."

"Ikon ALLAH!, Ai dama nasan dole qara tace zata kai wajenka Dr tunda muna ganin mutuncinka, yakamata ace rashida ta fahimci abunda muke guje mata faruwarsa saidai takasa gane hakan..."

Nan takwashe komai tafad'a masa akan abunda yafaru ba qari balle ragi, sosai Dr yashiga rud'ani daya auna maganganun guda biyu, da wud'anda baffa yafad'a masa da kuma na yaya Maryam yagano akwai wani abun aqasa wanda ba daidai ba, ko meye kuma ALLAH kad'ai yasani."

Haquri yabata tare da sake roqonta a lallab'ata in Sha ALLAH da sannu zata fahimcesu sannan ya koma bakin motarsa yana jiran fitowar Fatima.

Rashida kuwa saida taba little nono yasha ya qoshi Fatima na gefenta tana dad'a bata haquri tare da rarrashinta sannan tamiqa mata shi ta kwanta saman qatuwar katifar dake cikin d'akin nata, anan maganganun da suka faru tsakaninta dashi a daren ranar suka shiga dawo mata a kwakwalwa, tabbas ita ta qarfafa masa yin wannan tafiyar kuma ko kad'an hakan da yayi ba laifi bane, Amma meyasa ya aikata hakan batare daya sanar da iyayenta ba.? Meyasa baiyi tunanin abunda zai iya faruwa ba akan wannan kuskuren da yayi, kamata yayi ace ya fahimci cewa komai na duniya kan iya sauyawa idan aka samu sauyin al'amurra, kama daga ra'ayi, buqata, lafiya, wajen zama da kuma yanayi na yau da kullum, gashi yanzu yaje yabar baya da qura, babbar damuwarta shine rashin sanin har tsawon wane adadin lokaci zai d'auka kafin yadawo.

Jitayi Fatima nafad'in "maman boy zamu tafi, yana waje yana jirana, don ALLAH kimaida al-amurranki agaresa kidena kukannan bayada amfani, ga wannan wayace uncle d'inki ya siya maki zamu rinqa magana, akwai lambata da tashi aciki kuma na saka maki ta yaya maryam data aunty marwiyya saiki kirasu, kada kiyarda inkira injita akashe, ko yaushe ina son ki kasance tare da ita kinji ko?."

'Daga mata kai tayi sannan tajuya zata tafi tana d'auke da little.

"Au! yau babu rakiya maman boy?"

Ta juyo tana kallon rashida dake qoqarin tasowa alokacin. Har bakin mota ta rakata tare da yiwa Dr.nura godiya sosai tamiqa mata Little sannan suka wuce...

_Darasi: 'yar uwa ki guji aikata laifi komai qanqantarsa domin bakisan iya adadin mutanen da Zaki iya cutarwa ba ta dalilinsa, wanda hakan kad'ai na iya zamowa dalinlin tsanantar hukuncinki awajen ALLAH, domin shi mai yafe haqqinsane amma banda haqqoqan rayukan da kika cutar, laifi d'aya yaya hawwa ta aikata akan rashida amma mutane da yawa sun cutu adalilinta, ciki kuwa harda qaramin yaro (yusuf) dake fuskantar damuwa da kuma barazana ta dalilin hakan._






*ALLAH KAJIK'AN IYAYENMU*👏😭
[11/14, 22:52] Billy S Fari: 🚶‍♀️🚶🏻‍♂️ *SANNU SANNU*🚶🏻‍♂️🚶‍♀️
💎 _Bata hana zuwa..._💎


_WRITTING BY:_ *BILLY S FARI💎*

_DEDICATED TO:_ *BLOOD SISTER'S (AMZAHFAZ)*💋

_BESTOWED TO:_ *ZAINAB AL-AMIN (MOM NA'EEM)* AND *AMINA UBA AYUBA (OUM ASHFAQ)*💞

*DOMIN FARINCIKINKI SISTER SADIYA ZANGO (MIEMAH)*💖

*FATAN ALKHAIRI AGAREKU MOMMAH ME NANA HAFSAT (MISS XOXO) AND MAMANA HAFSAT RANO(OUM AFFAN)*❤️

Page___58💎

Shiru Yaya Maryam tayi na tsawon daqiqu uku kafin tace.

"Hakan shine daidai, dama abunda nayita qoqarin lurar dakai kenan ka kasa ganewa, to amma batun cewa za'a mayar masu da yaro don yanke duk wata alaqa dake tsakaninmu kabarta don ni gaba d'aya bana buqatar jinmu yakoma zama atare dasu tunda basa da zuciyar imani."

Sun jima suna tattaunawa kafin yabar gidan har lokacin yanajin d'aci akan maganganun da baffa Ali yafad'a masa.

••• ••• •••
Baffa nagama waya da malan balarabe yakalli d'an uwan nasa ya sakar masa murmushi cikin qarfin hali sannan ya juyar da kansa gefe, yana maimaita innalillahi wa'inna ilaihirrajiuun aransa.

Dafa kafad'arsa baffa Usman yayi had'e da cewa.

"Meke faruwa ne Yaya?"

"Abunda Nuraddeen yayi gudun faruwarsa." Yabashi amsa had'e da juyowa suna fuskantar juna.

"Kayi haquri Yaya, dama dole hakan zata faru, mu auna kanmu a matsayinsu mugani, don haka dole zamu lallab'asu har su fahimcemu, ayanayin yanda damuwowi sukayi masu yawa kamarmu, abune mai wahala su iya riqe fushinsu alokacin da sukaji labarin tafiyarsa musamman idan sun jine daga bakin daya kasa yimasu kyakkyawan bayanin da zayasa sufahimta, shi kuwa rashin bayani acikin kowane al'amari shike haifar da husuma da kuma aikin dana sani, don haka dole muyi haquri har zuwa lokacin da zasu fahimcemu."

"Shikenan Usman, amma duk da haka mufara jaraba zuwa wajensa idan mun sauka."

Awa hud'u ta d'aukesu kafin su isa kano, ana ajiyesu tasha suka sake shiga motar da zata kaisu qauyen na yarimawa, cikin qananan daqiqu suka isa sukaci sa'a kuwa yana zaune bakin gida yana arwala suka yimasa sallama, bai amsa ba har saida ya gama arwalarsa ya d'aga kansa sama yayi addu'ar da akeyi bayan gama arwala sannan ya kallesu fuskarsa a sake ba yabo ba fallasa ya amsa masu salamar.

"A'a malan Idris, malan Usman sannunku da zuwa yanzu kuke tafe?." Yafad'a yana qoqarin ajiye butar da yayi arwala agefe, kallon baffa Usman baffa yayi kafin suji ya sake cewa.

"Kai Hassan kushiga ciki ku kawo ruwa a butoci magrib taqaraso ana batun tada sallah."

"Am sannunku da zuwa bari naqarasa masallaci kafin ku iso liman na batun tayarwa."

"To shikenan!"

Baffa yafad'a cike da mamaki a fuskarsa.

Basu sake Shan mamaki ba sai da suka fito sallah suka tarar da tabarma an shimfid'a a qofar gida da kwanonin abinci,

"A'a malan Usman ya akayi kukayi tsaitsaye? bisimillah kuzo kuzauna mana,

Gaggaisawa suka shigayi kafinsu baffa sufara qoqarin canza maganar izuwa asalin wacce takawosu, Amma ga mamakinsu sai sukaga kawai yajawo kwanoni abinci yana fad'in bisimillah malan idris muci abinci ko."

Babu yanda suka iya saboda yanada matuqar muhimmanci agaresu da bazasu iya yimasa musu ba, wanke hannayen su sukayi sukasa suka fara cin abincin tare har suka qare,

Bayan sun kammala, baffa yace.

"Don ALLAH malan balarabe kayi haquri ka sauremu, nasan an aikata maku ba daidai ba, amma kuskurene da babu wanda ya isa ya kauce masa, tabbas Nuraddeen yabar qasarnan saidai bada son ransa ba, nine natirsashi ganin yana shirin ruguza rayuwarsa, kuma dama ce wacce yasamu tun kafin wud'annan matsalolin su faru, ganin ba lallai bane ya sake samun wannan damar ba kuma ga yanayin da yake ciki yasa daya tirje akan babu inda zaije saboda yana tsammanin dawowar matarsa garesa wanda abune gaibi akan dawowarta yasa natilasta masa zuwa koya fita daga cikin halin damuwar da yake ciki."

"Hmmm malan Idris kenan!, Ai bance kunyi wani laifi ko kuskure ba, meye laifinku don kunyi qoqarin inganta rayuwar d'anku?, Meye laifinku don kunyi abunda zai sakaku cikin farinciki?, Ba kuda wani laifi don haka kumanta da komai, fatana d'aya muma ALLAH yabamu ikon d'aukar darasin da kuka koyamana muma mu inganta rayuwar 'ya'yanmu kamar yanda kukayi koma fiye da hakan.?"

Duk iya qoqarin da sukayi wajen ganin sun lurar dashi ya fahimci gaskiya hakan ya cutara daga qarshema cewa yayi.

"Don ALLAH da girmansa malan usman mubar wannan magana kada tajawo rugujewar sauran mutuncin dake tsakaninmu, d'anku dai ALLAH yabashi ilimi mai albarka mukuma ALLAH yatsare mana 'yarmu aduk inda take yabata juriyar shanye duk wani abu da zai nemi duqufar mata da farinciki."

"Amin" suka amsa masa dashi bayan sun sake bashi haquri sannan suka wuce zukatansu a dagule.

Bayan suntafi yakira Yaya Maryam lokacin tana zaune itada Rashida tana bawa little da sai qara wayau yakeyi nono,

"Na'am balarabe ya akayi? Duk lafiya dai kuke ko?"

"Lafiya klw Yaya, dama iyayen yaronnan mijin Rashida ne sukazo bada haquri...."

"Kaga rufemun babinsu bana son ji, ai Ina mumuka haifi aburmu kuma muka bashi aurenta ko! don haka yanzu mun raba, ko suna so ko basa so yazama dole yabawa Rashida takardar ta, bazata koma gidansa ba ko mutuwa zaiyi, shashancin baza da wofi." Yaya Maryam ta katsesa tana masifa,

Wata irin zabura Rashida tayi had'e da miqewa tsaye da kad'an little yafad'i, Yaya Maryam tayi saurin riqosa had'e da kashe wayar tana binta da wani mugun kallo mai cike da tarin tambayoyi, hankalinta atashe takalleta tana fad'in

"Mekike fad'a haka gwaggo!," da yake da haka suke kiran sunanta sannan taci gaba da cewa.

"Wai wa ake zancen zai sakeni?, Duk fa iya adadin kwanakinnan dana d'auka zuciyata cike take da mararinsa, idanuwa da kunnuwana cike suke da son ganinsa da kuma jinsa, kawai nayi shirune saboda kada kuga rashin kunyata tayi yawa amma Ina son na had'u da mijina, shine kuma kuke cewa sai ya sakeni?, Meye laifinsa?, Wne zunubin ya aikata da za'ayi yunqurin rabashi da ni?"

"Ungo nan marar kunyar yarinya." Yaya Maryam tafad'a had'e dayi mata daqquwa tanaci gaba da cewa.

"Ke wane zunubin kika aikata da uwarsa ta rabaki dashi, kin ganemun shashashar yarinya da batasan ciwon kanta ba, to bari infad'a maki wlh munfiso kimutu atare damu muyi maki sallah murufeki da mumaidaki gidansa uwarsa ta sake halakar mana dake, don haka tunwuri kiciresa aranki matuqar kina son muzauna lafiya dake kinji nafad'a maki."

"Haba gwaggo! Haba gwaggo wannan wani irin tsattsauran hukuncine zakuyi mana, inada yaqini akan tunda wannan jarabawa tasameni shima t yake cikin irin tashi jarabawar, don ALLAH kada kura bamu kodon yaronnan." Taqarasa maganar tana kallon little dake hannun ita Yaya Maryam d'in had'e da fashewa da kuka, har ga ALLAH Yaya Maryam taji tausayinta, Amma Babu yanda ta iya, wannan ita kad'aice hanyar da zasubi su kub'utar da 'yarsu daga sharrin uwar mijinta, wacce itama tanacan cikin mummunan yanayin da basuda labari akai, cikin dakewa da qarfin hali tace.

"Rashida kawai kuhaqura da juna, yaro kuma Allah shizai rayashi ko bakwa tare don haka kibi umurninmu kizauna lafiya."

Wani kukan ta sake fashewa dashi had'e da durqushewa qasa

Please Login or Register in order to submit comment