Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ga jikin jaririnta daya matuqar tsananta wanda tuni tace Dr nura yayi masa hud'uba da sunan mahaifinsa wato Nuraddeen sunan da kuma yayi daidai dana shi Dr nuran. Hakan baqaramin dad'i yayi masu ba duk da basuda tabbacin cewa yaron zai tashi amma sunan da aka rad'a masa yaqarasa su jin wata irin matsananciyar qaunar yaron aransu, lallashinta suka shigayi da bata baki akan tayi haquri tunda har tasan gidan iyayen nata dana sauran 'yan uwanta da mijinta har sai yaronta yasamu lafiya sai su kaita har gida, koba komai zuwa lokacin sunada tabbaci akan ansallami iayen nata aduk asibitin da suke kuma yayi mata alqawarin zaici gaba da bincika mata inda suke kafin lokacin da yaron zai samu lafiya, idan ALLAH yasa angasu koda yaron bai warke ba sai yasa ayi masu transfer sukoma can dashi acigaba da jinya.

Batada wata madafar data wuce mata haka don bazata iya guduwa daga hannunsu ba bayan duk d'imbin alkhairin da sukayi mata ita da d'anta da tuni tanufi wajen iyayenta da 'yan uwanta domin sunada buqatar suganta su san halin da take ciki, musamman habibynta da akoda yaushe jikinta nafad'a mata cewa yana cikin wani mummunan hali,

Yaya hawwa kuwa tasha azaba kala kala kafin tabud'e baki tasanar dasu inspector najida cewa itace tayi sanadiyar b'atan Rashida saboda baqin asirin da takaita wajen wani boka akayimata, kuka takeyi tana basu labarin abunda yafaru saboda tsananin azabar da take ciki, gaba d'aya qanana yatsunta na dama da hagu anqire mata su, haka akaifun manyan yatsun qafafuwanta duk an cire matasu sai jini sukeyi, ga ijiyarta d'aya da suka jimata ciki wadda ALLAH kad'ai zaisa taci gaba da gani da ita.

Hatta blessing da take arniya Saida ta tsinema Yaya hawwa, wani qaton kulki dake hannunta tabugawa yaya hawwa akai takife qasa asume, cikin rashin tausayi blessing tace. "Shege me zuciyan duse kamutu dan iska."

'Daga mata hannu inspector najida tayi had'e da cewa.

"Noo...kibarta blessing, dole munada buqatarta saboda zamuje da ita acan qauyen da bokan yake idan tafarfad'o shima akamosa, hakan zaisa musan inda yarinyar nan take tunda shi yayi asirin, ita daga yanzu amfaninta yaqare wajen sanin inda yarinyar take tunda batada wata masaniya akai, zadai muyi amfani da ita mukama bokan nata yazo hannunmu."

Tana gama fad'a tajuya tabar wajen cike da jinjina tsantsar rashin imani irin na Yaya hawwa.





*ALLAH KAJIK'AN IYAYENMU*πŸ‘πŸ˜­
[8/17, 10:19] Billy S Fari: πŸšΆβ€β™€οΈπŸšΆπŸ»β€β™‚οΈ *SANNU SANNU*πŸšΆπŸ»β€β™‚οΈπŸšΆβ€β™€οΈ
πŸ’Ž _Bata hana zuwa..._πŸ’Ž


_WRITTING BY:_ *BILLY S FARIπŸ’Ž*

_DEDICATED TO:_ *BLOOD SISTER'S (AMZAHFAZ)*πŸ’‹

_BESTOWED TO:_ *ZAINAB AL-AMIN (MOM NA'EEM)* AND *AMINA UBA AYUBA (OUM ASHFAQ)*πŸ’ž

*DOMIN FARINCIKINKI SISTER SADIYA ZANGO (MIEMAH)*πŸ’–

*FATAN ALKHAIRI AGAREKU MOMMAH ME NANA HAFSAT (MISS XOXO) AND MAMANA HAFSAT RANO(OUM AFFAN)*❀️

_Alhamdulillah for d unlimited bless anytime ya rabhπŸ‘ hi sister's gaisuwa tare da fatan alkhairi ga d'aukacin masoyana kuma masoyan littafin SANNU SANNU... Ina yiwa kowa BARKA DA SALLAH tare da fatan anyi sallah lafiya,πŸ₯° ubangiji ALLAH ya maimaita mana kasa ni daku munyi tarayya acikin d'imbin ladaddaki da gafarar ALLAH dake cikin wud'annan kwanakin da suka shud'e,πŸ‘πŸ’ƒπŸΌ ALLAH kajiqan dukkanin iyayenmu wud'anda suka rasu da wud'anda keraye Kuma kabasu aljannah da rahamarka damu baki d'ayaπŸ‘ Ina fatar zamu d'ora daga inda mukatsaya kuma zaku bani 'yan barka da sallah ta tunda rowar nama tasa kun b'uya ko leqowa bakwayi a group balle atuna da littafin SANNU SANNU sai yanzu da kuka cinyye abunku,πŸ₯°πŸ˜… SANNU SANNU fans group 1&2 ina jiran 'yan barka da sallahtaπŸ˜…πŸ˜…πŸ˜…hohoho..ku kwantar da hankalinku kud'i nake so ni ba nama ba don naga wasun ku sun fara hararata, to bashi nake so ba amma dai kuci ahankli ko ince wacce duk ta zaqe da yawa ALLAH yasa tafara z....πŸƒπŸ»β€β™€οΈπŸƒπŸ»β€β™€οΈπŸƒπŸ»β€β™€οΈπŸ€£πŸ€£πŸ€£πŸ€£ahhh to bandai iyar ba balle ace Billy tayi muguwar addu'a. *LUV YOU ALL FILLAH* ❀️_

Page___46πŸ’Ž

Tun da sassafe baffa yakira inspector najida tayi masa bayanin bayanan da suka samu a hannun yaya hawwa tare da tabbatar masa da cewa yau d'innan zasuje da ita har dajin da bokan yake shima aka mosa, matsala d'aya basuda tabbacin kamosan zaisa asan inda yarinyar take tunda harkace ta shed'anin aljanu, kawai zasuyi hakanne don yazama izina uma tudun da zasu dafa wajen ganin sun kauda masu munanan halaye irin na Yaya hawwa da bokan, saboda Haka ta shawarci baffa da kawai atashi tsaye da addu'a in sha ALLAH ALLAH zai bayyanata, sosai baffa yaji dad'i akan matakin da tace zasu d'aukar masu, ad'aya b'angaren zuciyarsa kuwa halin yaji yasamu wata 'yar qaramar natsuwa don yanada tabbaci akan yanda Rashida tayi riqo da addininta ALLAH bazai tab'a Bari acutar da ita ba, saidai idan yaso ya jarabce tane daga cikin jerin qaddarorin daya tsaro mata arayuwa, godiya yayi Maya sannan ya kashe wayar, daidai lokacin Nuraddeen yafito wanka riqe da d'an qaramin towel yana goge jikinsa, kallonsa baffa yayi cike da tausayi lokacin daya hau shirya kansa kafin yace.

"Nuraddeen Ina zakaje ne haka tunda sassafe?."

"Yarimawa." Yabashi amsa ataqaice yana qoqarin zura rigarsa ajiki, "ehmm!..to Bari na shirya sai muje dama Ina son inje dubo aminina, jiya da muka had'u da malam balarabe akasuwa take fad'amun cewa har anba iyalin tasa sallama, kwana biyu banje ba saboda akoyaushe idan muka had'a idanuwa dasu tausayinsu kanjefani cikin matsananciyar kunya da damuwa, maganar gaskiya mahaifiyarka Bata kyauta ba, ta matuqar cutar da rayuwar wud'annan bayin ALLAH."

"Zan nema Maya tafiyarsu baffa, ALLAH kayafe Maya Kuma ya shiryar da ita damu baki d'aya, jarabawar innar mu ce tazo mata ahaka wacce dukkaninku bamu wuce tab'a awurin ALLAH, fatanmu d'aya ALLAH karya jarabcemu ta irin hanyar da aka jarabtata," ajiyar zuciya baffa yayi yana kallon Nuraddeen, tabbas gaba d'aya halayensa na sanyin hali ya d'ebo amma anan harya zartasa tunda take kallon son zuciyar mahaifiyarsa a matsayin kuskure da jarabawar rayuwa, sab:'anin shi dake kallon abun a matsayin mugunta, rashin imani da kuma rashin tausayi, murmushi yayi yana godema ALLAH daya bashi d'a k'waya d'aya tamkar da dubu kafin yace.

"Amin Nuraddeen, bar na watso ruwan nima, idan baffanka yazo kace masa yajirani sai muje tare ko?"

"To baffa" yafad'a had'e da zaunawa gefen katifar dake cikin d'akin yana d'aure zaren takalminsa daya saka yanzu, azahiri idan ka kallesa cikin natsuwa zaka fahimci fuskar a sake take ba yabo ba fallasa amma acan cikin zuciyarsa akwai d'imbin miki da damuwa a cunkushe da ita, yana nan zaune baffa usman ya shigo shida Yusuf d'auke da kayan karin da aka Saba kawo masu, da sauri Nuraddeen yamiqe yana gwadawa baffa Usman gefen katifar daya tashi akai tare dasa hannayensa ya dafa kafad'un Yusuf yana fad'in.

"Sannu da zuwa baffa, Ina kwana antashi lafiya?"

"Lafiya klw Nuraddeen, Ina zuwa da wannan snyin safiya haka?"

Baffa yafad'a yana qoqarin zaunawa bakin gadon yana kallonsa, Saida ya d'an sosa qeyar kansa sannan yace, "zanje yarimawa ne nadubo jikin umma da baba.

"Af! To Masha ALLAH, dama shirin da nayo kenan saboda jiya dasu nakwana araina, kwana biyu dani har Yaya bamu samu muka leqosa ba, shiyasa nace idan nazo zanyi masa magana idan yanada dama sai muje anjima, ga Bilkeesu can itama ta dage akan lalle yau da ita zamuje don ta dubosu."

"Eh shima naji yace zaije, yashiga wankane ynzu amma yace kajirasa" yafad'a tare da jan hannun Yusuf suka fita, firarsu da mintota baffa yafito ya kimtsa sannan suka gaisa da d'an uwansa kamar yanda suka saba ko yaushe sannan su Nuraddeen suka dawo shida Yusuf suna tafe Yana yimasa firar maganganun daya ji su baffa Ali nayi aranar akan zancen korar Rashida cikin gidan don ya auri yayarsa muneera, tuni Nuraddeen yagama sadaqarwa da anhalakar masa da Maya wanda inba ubangiji ba Babu wanda ya isa yace yasan inda take, murmushin da yafi kuka ciwo yayi had'e da rumqe hannun Yusuf sosai sannn yace.

"Yusuf me kake tunani akan auntynka Rashida, za'a ganeta kuwa?, tana raye ita da abunda ke cikinta ko kuma..."

Bai qarasa fad'aba sakamakon k'wace hannun da yasufa yayi tare da tsayawa agabansa yana d'aga yatsa had'e da cewa. "Kada kace komai Yaya, ai ba'a yanke qauna da rahamar ALLAH, muci gaba da addu'a in Sha ALLAH za'aganeta kome daren dad'ewa kuma da yardar ALLAH suna cikin qoshin lafiya duk inda suke."

"Yusuf waya fad'a maka haka?."

Nuraddeen ya tambayesa cike da mamakin kalaman dake fita daga bakinsa, riqe hannunsa Yusuf yayi sannan yace. "Inajin baffa Usman da Inna Bilkisu nafad'a akoda yaushe kuma suna addu'a shiyasa nace haka don nasan addu'ar iyaye karb'ab'b'ace."

"Tabbas hakane yusuf ALLAH ya karb'a mana addu'o'inku baki d'aya."

"Amin Yaya, wai yaushene zaka wuce?"

"Ina fa?"

Nuraddeen yafad'a cikin rashin sani don yama manta da zancen tafiyar tasu, Yusuf daya qura masa idanuwa yana kallo yace "baffa Usman yace zakaje malesia wajen qaro karatu."

"Oh! Kash ai namanta, in Sha ALLAH zuwa wani satin zamu fara tashi."

"Zamuyi kewarka Yaya sosai, yanzu ma da baka gida bkaji yanda muke kewar kana balle kamar qasarnan, no bana so katafi gaba d'aya ma." Dariya yayi yana shafa kansa had'e da cewa. "Nima bana so Yusuf saboda tunanin auntynka, Amma idan har Ina so damuwar da nake ciki ta rage dole sai nayi nesa da duk wani abun daya zamo silar rabani da ita wannan shi kad'aine zai ragemun zafi da sililin da nakeji azuciyata" da wannan firar suka qarasa shiga cikin d'akin baffa na qoqarin jawo kayan karin da suka zo masu dasu, zuwa yayi ya karb'a ya had'a masa tare da ajiye masa agabansa sannan shima ya had'a nasa yaci, bayan sun kammala baffa yad'ibi cikin kud'in da yazo dasu jiya sukaje shida baffa suka samo shatar mota bus akaje da ita qofar can gidan baffa Usman yashiga yace Inna Bilkisu tafito sannan ta sanarwa da mutanen gidan duk mai son take gano mahaifan Rashida sufito aje, ai kuwa kafin kace me motar tacika harda maqwabta, wasu zasujene don yiwa Nuraddeen kara, wasu kuma gulmace zata kaisu, Amma duk da haka baffa da Nuraddeen sunji dad'in yanda 'yan uwa da abokan arziqin suka nuna masu karamcin zuwa suyo dibiyar.

β€’β€’β€’ β€’β€’β€’ β€’β€’β€’
A can borno kuwa kuwa ganin yanda jikin yaron Rashida ya qiya yasa dr. Nura tunanin karb'ar masu sallama su koma gida agwada maganin hausa ko ALLAH zaisa adace tunda nan ankasa gano takamammiyar matsalar yaron, cikin sa'a kuwa daya yiwa likitocin bayani suka fahimta aka basu sallama suka koma gida, ranar Rashida taqara shiga tashin hankali ganin yanda d'an qaramin yaro da bayada alhakin kowa keahan wahala, Babu abunda yafirgitata irin ganin yanda yake fizge fizge yana wani abun, hakan yasa tafara wani tunani aranta Wanda aqasan zuciyarta take neman ysarin ALLAH akan faruwar hakan, da marece Dr nura yaje yakirawo wani malami yazo dashi nan gida saboda yaduba yaron, ranar kam sunsha mamaki ganin abubuwan da malmin keyi masa wanda Fatima dake riqe dashi tausayinsa yasa takasa saidai shi Dr. Nura d'in ya karb'esa, addu'o'i ya dinga yiwa yaron yana tofawa aruwa had'e da watsa masa a fuskarsa da jiki shikuma yaron na wani irin kuka mai matuqar tsima rai sosai, duk lokacin da malamin ya watsa masa ruwan addu'ar sai ya kwanyara ihu tare da fashewa da kuka mai tsananin qara, hakan yasa Rashida dake d'aki ta daddad'e kunnuwanta da filo saboda yanda takejin kukan nasa har cikin ranta takasa jurewa, aguje tafito tanufi falon Dr. Nura inda suke zaune, Kai tsaye tashiga ciki ko sallama babu tare da karb'ar jaririn a hannun Dr nura tad'orasa asaman kafad'arta tana kuka, had'a hannayenta tayi waje d'aya tana ja da baya had'e da cewa.

"Malan don ALLAH kabarmun jaririna haka, zan iya jure rashinsa kamar yanda najure rashin mahaifinsa, zan iya yin haqurin ganinsa acikin halin da yake ciki kamar yanda nahaqura da rashin sanin halin da mahaifana keciki amma bazan iya jurewa wannan kukan nasa ba, domin jinsa nakeyi har cikin zuciyata da kuma rouhina, sannin akwai abunda akeyi masa yasa nakeji tamkar cutar dashi ne akeyi, kayi hak'uri malan don ALLAH kaje..." Cike da b'acin rai dr. nura ya taso ya nufo inda take zai karb'esa tace.

"Don ALLAH uncle kabarmun yarona, ka sallami malaminnan kace yatafi."

"Rashida Anya kina cikin hankalinki kuwa? Duk haqurin da kikayi na tsawon wata hud'u yaronnan baya tare dake batare da kin d'aga hankalinki akansa ba sai yau zaki kasa jurewa, karki manta kowace cuta aduniya tanada magani, Kuma ALLAH ya halasta anemesa, don haka miqo munshi kafin na sab'a maki."

"Uncle kukan nasa tamkar yana fita da lumfashina ne, idan zanci gaba da saurara zan iya rasa Raina, shi kad'aine farincikin daya yaragemun aduniya don ALLAH kubarmun shi kada shima narasa shi."

"Rashida.." Dr nura yafad'a da a tsawace ransa na neman b'aci. Sake dafe kan yaron tayi da hannunta tanajin yanda yake kukan zuciyarsa nabugawa da sauri saur, tasowa malamin yayi daga inda yake zaune ya dawo inda take tsaye yace.

"Shikenan ya isa koma can ki zauna." Adarare tabi ta gefensu ganin yanda ran Dr yad'an b'aci,

Bayan ta zauna malamin yaje gabanta ya zauna shida Dr nura, har lokacin yaron na rungume ajikinta tariqe sosai tamkar za'a k'wace mata shi, kallonta malamin yayi na tsawon mintuna kafin yace.

"Kece mahaifiyar sa." Kasa amsa masa tayi saidai ta d'aga masa kai idanuwanta na tsiyayar da hawaye.

Jinjina kai yayi kafin yaci gaba da cewa.

"Shin antab'a fad'a maki cewa kinada aljanu.?" Nan ma girgiza masa kai tayi da sauri cike da fargabar abunda take tsammanin zai iya fitowa daga bakinsa, kallon Dr nura yayi had'e da cewa.

"Wannan jaririn da kake gani tun yana ciki aljanu ke tare dashi, sunso su hallakasa ko Kuma su shiga jikinsa amma Allah ya sha makance shi da hakan, shine suka shafesa ba tare da sun iya samun nasarar shiga jikinsa ba, wanda nake tunanin su wud'annan aljanun kamar na mahaifiyar tasa ne, Amma sai gashi tace ba tadasu kuma natabbatar da hakan saboda yanda alamom suka nuna batada su, nan Dr nura yayi masa bayanin abubuwan da suka faru da ita dalla dalla har zuwa lokacin daya tsinceta kamar dai yanda tayi masu bayani a farko,

"To malam inaga wannan dalilin shiyasa sukabi ta wannan hanyar don su cutar dashi yaron tunda sun kasa shiga jikin mahaifiyarsa ko cutar da ita."

jinjina kai malamin yayi had'e da cewa.

"Tabbas hakane, kuma da yardar ALLAH, da qarfin ikonsa shima dole su barshi ta hanyar addu'o'i da magungunan da zan baki kafin suyi galabar shiga jikinsa gaba d'aya. Sannan zamuyi masa karatun al-qur'ani wato (ruquya) don kauda duk wata barazana da suke sonyi wajen shiga jikinsa."

Miqewa tayi ta d'orawa Dr. Yaron ajiki sannan tamiqi hanyar fita tana goge hawaye, a yanzu gaba d'aya ta gama gamsuwa da bayanin da malamin yayi don haka ta amince da duk abunda za'ayi masa kuma zata jure hakan.

"Dawo ki d'aukesa." Dr. nura yafad'a yana kallonta.

"Jeki." Malamin yafad'a ganin lokaci na dad'a qurewa, karb'ar yaron yayi yace yaje yayo arwala, bayan yadawo shima malamin yaje yayo tasa duk da yanada tabbacin yanada ita, nan take yafara yiwa jaririn ruquya, wani irin kuka yaron ya fashe dashi bayan tun d'azu ya dena kukan, tun yanayi da qarfi gidan ya karad'e da kukansa har ya farayi ahankali, itama tacan b'angaren Rashida da ita har fatimar kuka sukeyi jin kukansa da sukeyi har yadena, ganin sukayi jikinsa gaba d'aya ya saki tamkar wanda bayada rai lumfashinsa nafita ahankali, da alama baccine ya d'auki jaririn sosai, ajiyar zuciya malamin yayi had'e da cewa.

"Alhamdulillah, inaga in Sha ALLAH anyi nasara, dama ba shigarsa sukayi ba, sun shafesa ne kuma muna sa ran yanzu zasu qyalesa idanma basuyi hakan ba to inada tabbaci akan ayar ALLAH zata qona mana su tare da sauran maganukkan da za'a kula dayi masa amfani dasu."

Cike da jin dad'i Dr. Nura yamiqa masa hannu yana murmushi yayi masa godiya sannan malmin yace yabishi ya karb'o maganin da za'a fara yiwa yaron amfani dasu.













*ALLAH KAJIK'AN IYAYENMU*πŸ‘πŸ˜­
[8/17, 10:19] Billy S Fari: πŸšΆβ€β™€οΈπŸšΆπŸ»β€β™‚οΈ *SANNU SANNU*πŸšΆπŸ»β€β™‚οΈπŸšΆβ€β™€οΈ
πŸ’Ž _Bata hana zuwa..._πŸ’Ž


_WRITTING BY:_ *BILLY S FARIπŸ’Ž*

_DEDICATED TO:_ *BLOOD SISTER'S (AMZAHFAZ)*πŸ’‹

_BESTOWED TO:_ *ZAINAB AL-AMIN (MOM NA'EEM)* AND *AMINA UBA AYUBA (OUM ASHFAQ)*πŸ’ž

*DOMIN FARINCIKINKI SISTER SADIYA ZANGO (MIEMAH)*πŸ’–

*FATAN ALKHAIRI AGAREKU MOMMAH ME NANA HAFSAT (MISS XOXO) AND MAMANA HAFSAT RANO(OUM AFFAN)*❀️

Page___45πŸ’Ž

Zaune inspector najida take saman kujerarta ta office ta jingina kanta a jikin bayan kujerar idanuwanta arufe tana jujjuyata a hankali, gaba d'ya ba abunda keyimata yawo a kwakwalwarta irin abubuwan da Yaya hawwa ta aikata, tambayar kanta tashigayi, wace irin rayuwace muke ciki yanzu?, Wane irin son kaine mutane suke cikinsa?, Meyasa mutane ke aikata zunubi adoron qasa tamkar wud'anda basada zuciya da d'igon tausayi atare dasu?, Haqiqa bakomai yajawo wud'annan abubuwan ba face zallar rashin imani da kuma tsoron ALLAH, tabama kanta amsa tana mai jin tausayin rayuwar Rashida tunawa da tayi da irin yanayin da tabar gida, nan take taji tsanar Yaya hawwa tarufeta har tanajin tamkar taje tarabata da lumfashinsa naqarshe saboda wannan abun data aikatawa qaramar yarinya 'yar cikinta.

Tajima zaune ahaka kafin can tajawo waya takirawo baffa, kusan kira biyar tayi masa amma bai d'aga ba saboda wayar na gida yabari tana chaji shi kuma yana kasuwa yaje kai sauran 'yan dabbobinsa da yakeson saidawa yaqarawa Nuraddeen kud'in akan zancen tafiyarsa don yau sati biyu ya rage tafiyar tasa, tuni yayo screening da sauran abubuwan daya kamata da taimakon baffa Usman daketa qarfafa masa akan tafiyar saboda yanda qarara yanuna baya da buqatar tafiyar tunda baisan halin a ina Rashidarsa take kuma awane hali take ciki,

Ganin takirasa har ba adadi bai d'aga ba yasa ta ajiye wayar agefe tare da d'aukar file d'in wani case dake gabanta tana daddubawa,

Shi kuwa Baffa bai samu yabaro kasuwar ba sai gab da magrib, tafe yake riqe da ledar kud'in daya saida shanayensa guda biyu da tumaki uku da suka rage masa aduniya, bayansu yanzu baida komai sai rayuwa da kuma gona k'waya d'aya da iyayensu suka barmasa ta gado, kasancewar yanzu yanajin babu wani abu da yai masa saura arayuwa na farinciki yasa yazab'i ya saida abunda ya rage masa saboda ya tallafawa d'ansa tilo aduniya wanda ayanzu shikad'ai ne farincikin daya rage masa aduniya sai kuma d'an uwansa baffa Usman da akoda yaushe yake jib'intar al'amurransa. sauri sauri yake tafiya yana sake rumqe ledar kud'in kamar wanda yasato har ya iso gida ya tarar da Nuraddeen zaune saman 'yar barandar d'akin da suke kwana ya rabka uban tagumi, babu abunda yake tunani kamar halinda mahaifiyarsa da matarsa ke ciki, gashi ita mahaifiyarsa tayi masa shamaki tsakaninta dashi alokacin da yake matuqar buqatarta akusa dashi duk kuwa da mugun halinta, ita kuma matarsa nisan tashin da akayi da ita yasa gaba d'aya natsuwarsa da komai nasa sun qaura daga garesa, a kullum bayada wani aiki daya wuce masa tunaninta dake neman ya zautar dashi, abun har yakai idan bacci yakeyi mafarkinta yake riqe da jariri sunata kallonsa suna kuka, idan kuma a farke yake haka zai dinga ganin tana yimasa gizo riqe da jaririn suna kuka, lokaci guda har abun yakai ga koda yaushe cikin jin qarar sautin kukan jaririn nayi masa yawo a kunnuwa a kowane lokaci sai ya zamana kullum bayada aiki sai kuka da tunaninta, gaba d'aya abubuwan da suka faru bayan watanni biyu da satikka da suka wuce sun sake dawo masa sababbi fal azuciya tamkar yanzu suka faru, yanayin daya shiga awannan lokacin sai ya zamana ya lunka wanda ya shiga a baya sosai, musamman daka kalli Nuraddeen zaka fahimci yanda alokaci d'aya yazama wani irin zautaccen mutum, bayada wata magana data wuce matarsa da jaririnsa, gashi lokacin tafiyarsa sai gabatowa yakeyi dad'a yi, hakan yasa su baffa dagewa wajen yimasa addu'o'i tare da nema masa taimako agun malamai har ALLAH yasa yafara dawowa hayyacinsa, wannan dalilin yasa suka sake jajircewa akan zancen tafiyarsa qasar waje wajen qaro karatun cike dasa ran cewa idan yayi nesa da qasar gaba d'aya hakan zai taimaka masa wajen rage tunani kuma yasama masa natsuwa,
Sallama baffa yayi har kusan sau uku amma Nuraddeen baima sanma yayi ba balle yasan da shigowarsa har saida ya qaraso kusa dashi ya dafa kafad'arsa, firgigit Nuraddeen ya farko daga duniyar tunanin da yakeyi had'e da kallon mahaifin nasa da nan taje fuskarsa tanuna rashin jin dad'in yanayin daya iskosa aciki, murmushin da iya lab'b'ansa ya tsaya yayi had'e da cewa. "Baffa sannu da dawowa, tun d'azu nake dibon dawowarka naji shiru, nama zata kuna can tare da baffa Usman."

Saida Baffa ya zauna daga qasa gefensa fuskarsa cike da damuwa sannan yace. "A'a Nuraddeen, kasuwa naje na saikar da 'yan sauran dabbobin da suka rage, dawowata kenan yanzu inata sallama amma naji shiru baka amsan ba, maganar gaskiya naji matuqar damuwa awannan yanayin dana iskoka, gaba d'aya banji dad'i ba."

Yafad'a tare da fashewa da kuka, da sauri Nuraddeen yadawo gabansa ya durqusa, "Don ALLAH baffa kayi haquri kayafeni, kada kabari zubar wannan hawayen naka yasake jefani cikin wani mawuyacin yanayin, ka gafartan baffa zanyi qoqarin fitar da komai araina amma baffa kayimun uzuri dole sai ahankali hakan zai kasance."

Jawosa baffa yayai ajikinsa ya rungume sosai hawaye nasake kwararo masa afuska, wata irin qauna da soyayyar d'an nasa yakeji na ratsa dukkanin sassan jikinsa da kuma rouhinsa. Ahankali yabud'e baki yace,

"Kayi haquri Nuraddeen, yanayin da kake ciki iyayenta sunfika shigarsa, Amma baka yanda bayin ALLAH nan suka haqura ba, suka yarda da jarabawar da ALLAH yayi masu saboda qarfin imani, ka qoqarta kaima kazama mai koyi dasu kuma ka rarrashi zuciyarka in sha ALLAH ubangiji bazai barku ahaka ba zai faranta zukatanku da suka kasance cikin qunci da baqin ciki komai daren dad'ewa, shin zaka iya tuno mani da abunda annabi yaqub (A.s.w) yafad'a lokacin daya sake rasa d'ansa bilyamin bayan ya dad'e da rasa d'ansa annabi yusuf (a.s.w) a cikin suratul yusuf ayata tamanin da uku (83)?."

A hankali Nuraddeen ya d'aga masa kai, cirosa yayi ajikinsa yana saurarensa, cikin qira'arsa mai dad'i yayi ta'awizi da basmala sannn yafara karanta ayar kamar haka.

_Qala bal sawwalat lakum anfusukum amrah, faswabrun Jamil, asallahu anya'atiyani bihim jami'ah, innahu huwal alimul hakim_

Ma'ana annabi yaqub yafad'a alokacin da 'yan uwan annabi yusuf suka zo masa da zancen bilyamin yayi sata a misra anriqesa (a.s.w) yace.
_"Γƒ'a, zukatanku sun qawata wani al'amari agareku. Sai haquri Mai kyawo,akwai tsammanin ALLAH yazo mini dasu gaba d'aya (Yusuf da d'an uwansa.). Lalle ne shine masani, mai hikima."_

Ajiyar zuciya baffa ya sauke had'e da kallon Nuraddeen yace. "to ina son kaima kafad'i hakan tare dayin imani da tattara dukkanin yardarka ga ubangiji, Inada yaqini akan cewa komai tsawon dad'ewa kaima ALLAH zai dawo maka da matarka da kuma d'anka, kamar yanda aka dawowa annabi yaqub da 'ya'yayensa biyu daya rasa alokacin dabai tab'a tsammani ba."

Cike da soyayya Nuraddeen ke kallon mahaifinsa kafin yace.

Baffa _"Fa swabrun Jamil, asallahu anya'atiyani bihim jami'ah, innahu huwal alimul hakim_"

Yaqaresa ayar had'e da rungume baffa yana jin wani sanyi azuciyarsa.

Murmushi baffa yayi shima yana mai godewa ALLAH da duk tsananin jarabawar da suke ciki bai rabasu da imaninsu ba sannan yamiqe yashiga cikin d'akin ya adana kud'in kusan dubu d'ari biyune da hamsin, yana fitowa ana fara kiraye kirayen sallar magrib yace.

"Nuraddeen mutashi muyi harma, kaji ankira sallah."

Miqewa Nuraddeen yayi ya zubowa baffa ruwa abuta shima ya zubama kansa sukayi arwala sannan suka nufi masallaci,

Bayan sun dawo ne suka tarar da baffa Usman bakin qofar gida riqe da ledar kwanonin abincin data zama dole kullum sai yasa ankawo masu daga gidansa ko kuma yazo da kansa yakawo masu, da sauri Nuraddeen yaqarasa wajensa had'e da gaishesa sannan yakarb'i abincin yayi cikin gida, fuskar baffa sake taqaraso wajensa shima yamiqa masa hannu suka gaisa yana fad'in, "agaida malan usmanu baban Nuraddeen sannu da zuwa kazo adaidai don yanzu nake tunanin inkiraka awaya."

"To gani nazo, ALLAH yasa kan wasu nerorine zaka bani in take." yafad'a cike da raha,sun jima suna zolayar junansu abun gwanin sha'awa kafin su qarasa shiga cikin gidan, inda suka hango tabarmar da Nuraddeen ya shimfid'a masu suka nufa suka zauna tare da aza wata sabuwar

Please Login or Register in order to submit comment