Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

fito dasu da niyar zai shiga can cikin gari yabada gidan redio da telebijin asa cigiyar Rashida da baosan ko nawa bane yaciro cikin aljihu ya miqawa baba balarabe tunda har baffa Usman yariga da yakai sanarwar.

"Baba ga wannan aqara ayi amfani dasu, in Sha ALLAH gobe zan dawo."

"Haba! Ina Nuraddeen, Kai dake cikin wannan halin mezaisa nakarb'i kud'inka, kabarsu ko wani abun kayi dasu kaji ko."

"Don ALLAH baba idan har kad'aukeni d'anki tamkar Rashida ka karb'i kud'innan hakan ba qaramin zafi zai rage mani azuciya ba." Karb'a yai sannan yayi masa godiya tare da fatar ALLAH kabayyana masu Rashida aduk inda take kuma yakareta.

••• ••• •••
Baffa kam tun ranar da abun ya faru bai sake waiwayar gidanba kayansa ma saidai yasa baffa Usman ya kwaso mashi su yakoma warsa acan gidan yayi zaunensa, kusan kwana biyu yayi yana zuba idanuwa ko ALLAH zaisa aga Rashi kafin ya d'auki matakin daya qudurce aransa amma har lokacin shiru babu wani bayani akanta, da kansa yaji sanarwar b'atanta da akasa agidan redio kano da sauransu, haka ga telebijin wani maqwabcinsu ya fad'a masa yaga anyi sanarwar hadda hotonta tana saye da hijabi don daga baya baffa ya shawarci nura dake nan zaune tare dashi akai hoton nata, makarantu islamiyoyi dana almajirai duka yakai sadaka ayi masa saukar alqur'ani da addu'a amma ko mai kama da ita babu wanda yazo yace ya gani, hakan yasa ranar tunda sassafe ko Nuraddeen bai sani ba yaje har central policetatio dake can cikin gari yakai report akan b'acewar surukar tasa, tare da zayyane masu wud'an yake tuhuma akai, nan take 'yan sanda sukayo mota biyu suka kama hanyar bebeji tare da baffa da yanzu gaba d'aya zuciyarsa ta qeqashe, Babu wani sauran tausayi tsakaninsa da kowa keda hannu akan b'atan 'yar mutane, ko yaso ya rarrashi zuciyarsa aduk lokacin da yaje asibiti yaga halin da iyayenta ke ciki da Kuma Nuraddeen daya zabge yayi baqi ya lalace saboda tunaninta sai yaji bazai tab'a iya qyale b'atanta ya tafi ga banza ba.

Address d'in gidan yabasu lokacin da suka shigo garin shi kuma yawucewarsa gidansa bayan yatabbatar masu da cewa karsu qyale mutun ko d'aya daga cikin wud'anda ya lisaafa masu. Kasancewar ya zube masu kud'i masu tsoka don gaba d'aya dabbobinsa dake can go ya saida abunsa yasa 'yan sanda karb'ar umurnin daya basu tamkar wani shugabansu.

Adaidai qofar gidan suka tsaida motocinsu da sai faman ruri sukeyi, yaro suka samu sukace ya shiga ciki yace ana sallama da baffa Ali, yaron nashiga sambai ya wuce shiyarsa yace.

"Wai ana yiwa babansu muneera sallama."

Inna ruqayya dake zaune bakin qofar d'aki tana gyaran goro ta d'ago kai had'e da cewa

"Inji waye..?"

"'yan sanda." Yaron ya bata amsa atak'aice had'e da juyawarsa yafice daga gidan, sai alokacin Inna ruqayya ta tuna da taji rurin motar 'yan sanda ai da gudu tamiqe har tana kifar da kwanon da take gyaran goro ta shige d'aki jiki na rawa ta turo qofa....







*ALLAH KAJIK'AN IYAYENMU*👏😭
[8/17, 10:19] Billy S Fari: 🚶‍♀️🚶🏻‍♂️ *SANNU SANNU*🚶🏻‍♂️🚶‍♀️
💎 _Bata hana zuwa..._💎


_WRITTING BY:_ *BILLY S FARI💎*

_DEDICATED TO:_ *BLOOD SISTER'S (AMZAHFAZ)*💋

_BESTOWED TO:_ *ZAINAB AL-AMIN (MOM NA'EEM)* AND *AMINA UBA AYUBA (OUM ASHFAQ)*💞

*DOMIN FARINCIKINKI SISTER SADIYA ZANGO (MIEMAH)*💖

*FATAN ALKHAIRI AGAREKU MOMMAH ME NANA HAFSAT (MISS XOXO) AND MAMANA HAFSAT RANO(OUM AFFAN)*❤️

_😅Gara nafara da dariya saboda you guzs are amazing, just two day's fa nayi babu update kunata qorafi har dasu kira nasha awaya!🤔 to Ina baku haquri sosai kunsan jiki da jini abun sai a slow🤥 nagode da qauna, kulawa da kuma addu'o'inku agareni, jazakumullahu bikhair, ALLAH duka yabaku aljannah da rahamarsa👏 yanzu kam zaku dinga yimani uzuri saboda ba kullum zakuna dinga samun update d'ina ba saboda wani dalilin, taku a kullum mai qaunarku ALBIEN ROUHI❤️_ if u no u know kawai🤪🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️


Page___41💎

Muneera dake gefe zaune tanata kuitar kai ta kwashe da dariya had'e da cewa. "Kaga Inna meye abun gudu don ankira 'yan sanda, ni wallahi bana tsoronsu barima naje nafad'a masu cewa sudena jira saboda baffanmu baya nan" tafad'a had'e da miqewa,

"Ehim. Ehim. Ehim." Inna ruqayya dake can cikin d'aki tana sauraron abunda muneera kefad'a gabanta sai faman dukan uku uku yakeyi tashiga yimata tari alamar kada taje ko ina, amma ita muneera batama san tana yiba don har takai bakin qofar gida, tsaye tayi tana qarema 'yan sandan kallo, su bakwai sukazo cikin kakinsu uku mata hud'u kowane fuskarnan tasa a d'aure babu alamun wasa atattre dasu, tura hannunta tayi cikin kai tana sossosawa had'e da nufo inda suke,

"Sannuku." tafad'a hankali kwance babu alamun tsoro atattare da ita, kallon juna sukayi kafin d'aya daga cikinsu mai suna najida ta kalleta hannuwanta zube cikin wandon dake jikinta na kaki had'e da cewa. "Ke waye Aliyu agidannan?"

"Babu Aliyu acikin gidanmu sai baffa Ali." Muneera tafad'a tana leqen d'an sandan dake tsaye bayan najida yana faman zazzare idanuwa. Wata irin tsawa inspector najida ta katsa mata da alamu itace babbansu gaba d'aya kafin tace, "ke bama son wasa maza shiga kikira mana shi."

"Wlh ALLAH da gaske nakeyi, baffana kawaine keda irin sunan shi kuma ba haka ake kiransa ba."

"Au ko kece muneera?." wani d'an sanda dake tsaye a gefen inspector najida yafad'a yana zare mata ido.

"Laa..wlh nice, a Ina kasan sunan.." Bata qarasa ba inspector najida ta d'auketa da wani kyakkyawan mari had'e da cewa "stupid! Shine kike son rena mana da hankali, Jamil kuyi arresting d'inta." Inspector najida tafad'a had'e da juyawa zata shiga cikin gidan sauran 'yan sandan mata na biye da ita, ihun muneera ne data aza hannuwa akai ya dakatar da shigarsu saboda tirjewar da tayi ganin andamqeta za'a sakata bayan mota tana fad'in, "wayyooo...nashiga uku, Innata fito daga cikin d'aki kitaimakeni zasu tafi dani, wayyo baffa, to kubari ga baffana nan da kuke nema ya dawo" taqare maganar sakamakon hango baffa da tayi rataye da fartanyarsa yana 'yan waqoqinsa, yana hango motar 'yan sandan suna kokuwar tura muneera cikin mota gabansa ya fad'i kan kace me yaji wani fitsari ya tsilgo masa daga cikin wando, wasu yawu masu kabrin gaske yaji sun wuce masa da qarfi kan yaji jikinsa yafara rawa, kasa guduwa yayi daga wajen kamar an dasa shi saida ya hango inspector najida tana nunosa da hannu da qarfi tana fad'in.

"Kofron Ishaq, Jamil, Kabir maza ku kamosa.."
Da gudu baffa Ali ya arta dana kare fitsari nayi masa yawo aqafafuwa sukuma suna biye dashi, ran inspector najida yab'aci sosai ganin suna son b'ata masu lokaci, cikin jarumta tazo ta damqi kan muneera suka nufi cikin gida da ita, ihu take tana yarfi da hannu saboda azabar zafin da takeji dama kanta a tsefe yake fiye da sati uku, a daidai tsakar gida inspector najida ta jefata tana fad'i.

"Oya gwada mana inane d'akin hawwa"
Jikin muneera na rawa tayi hanyar sashen Yaya hawwa 'yan sandan mata biyu na biye da ita, yayinda inspector najida tayi tsaye tsakar gidan tana zarar idanuwa, matan gidan kuwa duk wanda ya leqo sai kaji kararaf yarufe d'akinsa saboda tsoro, 'yan gulma ne kad'ai sukayi qarfin halin bud'e tagoginsu suna leqowa.

Yanda muneera ke reren kuka yasa Yaya hawwa daga cikin d'aki cewa, "karki kuru ki qarasomun qofar d'aki sakaran yarinya, wato har kin manta da tonon sililin da kikasa jwarki tayimun har taja mani saki shine zaki sake kwaso gwalmammin qafafunki kinufo inda nake, to ahir d'inki mai mugun baki kuka ai nike dashi bake ba lalatacciyar banza da wofi." Raf, raf, raf d'aya daga cikin 'yan sandar tadinga buga gambun qofarta na d'aki da qarfi, a harzuqe Yaya hawwa dake faman harhad'a wasu 'yan kud'ad'enta da zimmar komawa wajen boka don taci alwashin babu inda zataje kuma saita rama baqin cikin da Inna ruqayya tayi mata tafito tana fad'in.

"Ga 'yar buhun uban yarinya inayi maki magana zakiyi mani iskanci, wallahi sai in b'atar.." Bata qarasa ba ganin 'yan sanda tsaye cirko cirko suna jiran fitowarta, gabantane yayi saurin fad'uwa amma saita dake.

"Kai lafiya naganku aqofar d'akina da wannan uwar tsakar ranar?, to indai fitina wannan shegiyar yarinyar tajawo ku kalleni da kyau banice na hifeta ba, ku koma can baya inda kuka baro munafukar uwarta nacan." Tana gama fad'ar haka tajuyawarta zata koma cikin d'aki da qarfi d'aya daga cikinsu tajawota tabaya had'e da fizgota da qarfi ta watsota qofar d'aki.

"Ya rasulu manzon ALLAH, ke yarinya anya kinada imani kuwa, ki kalli tsufana Amma kiyadoni awaje? ALLAH ya d'ebewa wannan kakin naku albarka."

Cakumo wuyanta wacce ake kira da blessing acikinsu tayi had'e da cewa.

"Munafuki, kene bakida imani muje zakiyi bayani." Tana turo qeyarta agaba, tirjewa Yaya hawwa tayi had'e dayin tsayenta ta d'ago tana kallon irin tsayi da qibar da blessing keda ita sannan ta duqar da kanta k'asa, cikin sanyin murya tace.

"Yarinya fad'amun menayi zaku tafi Dani, nafa fad'a maku cewa wlh banice uwar wannan yarinyar ba."

Yatsine fuska blessing tayi tana riqe da kunkurun zanen Yaya hawwa tace.

"Inna.."

"Na'am." Yaya hawwa tafad'a tana d'ago kai tana kallonta, hurar hanci blessing tayi sannan tace

"Inna, zanfa zagi uwarki ko inci ubanki anan"

Qwalalo idanuwa Yaya hawwa tayi awaje kafin tace wani abu da qarfin blessing ta izo qeyarta zuwa tsakar gidan inda inspector najida ke tsaye tana muzurai,

"Ina ruqeya take?" Blessing tafad'a tana yiwa Yaya hawwa wani irin mugun kallo da yasa cikinta murd'awa, tun kafin tarufe baki Yaya hawwa tanuna qofar d'akin Inna ruqayya dake rufe tana fad'in

"Gata nan, kushiga tana nan ciki..." tana rufe baki sukaga muneera tanufi bakin qofar d'akin tana bubbugawa.

"Wayyo Inna kifito kice kada suje dani, ni banyi komai ba, don ALLAH Inna kifito kifad'a masu ankusa aurenmu da ya nura kada sutafi dani."
Runtse idanuwa Inna ruqayya dake samn gado ta tattake da bargo tayi tanajin kamar tajawo muneera tayita maka, dukan qofar da taji inspector najida da taje wajen nayi kamar zata b'alla qofar yasata tasowa dole lullub'e da bargo ajikinta tabud'e qofar tana wani rawar sanyin qarya.

Share hawaye muneera tayi had'e da cewa. "Yawwa inna don ALLAH kifad'a masu kada suje dani ya nura yace yafasa aurena."

Cikin wata rawar murya Inna ruqayya yace. "Muneera lafiya?" Irin Bata masan abunda kefaruwa ba tana wani bubbuga haqora da junansu ala tilas ita sanyi takeji.

Tsaki inspector najida tayi tare da fincikota da ita har bargon tanufi qofar waje da ita, sumui sumui muneera tashige rumfar shiyarsu Inna Bilkisu dake zaunenta tana fitar gero tashige bayanta tana fad'in, "Inna Bilkisu don ALLAH kirufan asiri" duk da cike take da haushinsu gaba d'aya shiyasa ko kallon abunda kefaruwa batayi ba, hakan bai hanata cewa

"ALLAH dai ya rufamana gaba d'aya, kidena jin tsoro idan kinada gaskiya ba abunda zai faru dake, idanko dasa hannunki aciki to Ina fatar ayi maku duk abunda ya dace har sai kun bayyana inda yarinyar mutane take." Tana gama fad'ar haka blessing nafad'owa cikin rumfar, ashe taga lokacin da muneera tashiga, "sannu mama." Tace da Inna Bilkisu sannan taje tajawo muneera tana kuka tana susar kai.

"Munafukin qazami, wuce muje." Blessing tafad'a itama tana turo qeyar muneera waje,

"ALLAH ya kyauta." Inna Bilkisu tafad'a tana cigaba da wanke geronta.

Dandazon mutanen anguwane awaje suna kallon yanda ake kokuwa da Inna ruqayya tashiga bayan motar tana tirjewa wai ita batada lafiya, wasu suyi dariya wasu kuma abun yabasu tausayi, wani ne yace

"Ranki shidad'e ai ku ciccib'eta kujefa aciki don bazata shiga ba." Dama cike mutumen take da haushinta wai yaje neman auren muneera shine tayi masa tass har tana kiransa matsiyaci shiyasa abun yayi masa dad'i har yace haka.

Daidai lokacin blessing ta iso wajen riqe da muneera tajefa cikin motar, juyowa tayi fiskarnan tata ba imani ta wanke Inna ruqayya da mari, kafin sululin ya saketa ta d'agata har lokacin tana lullub'e da bargon tajefa cikin mota.

Tana qoqarin hawa bayan motar ne saiga su kofron ishaq sun kamo baffa Ali duk sun bubbuge masa fuska da qafafu ko tafiya baya iyayi saida suka tattallabo hannuwansa fuskarsa a kumbure, ba qaramar wahala suka shaba kafin su kamasa shiyasa sukayi masa wannan dukan, don gudu ya dinga jansu har zuwa farkon gari gidan baffa, basu samu kamasa ba sai acan yana yiwa baffa magiya wai yatuna da wasiyar mahaifiyarsu akansa, wlh shi baisan komai ba akan b'atan Rashida, sosai mganar tayi tasiri azuciyar baffa Amma hakan bai hanasa juya masa baya ba yana goge hawayen da suka zubo masa yace da 'yan sandan da suka shigo sun sheshsheka.

"Kutafi dashi kawai."

Yanajin ihun da yakeyi sanadinyar dukan da suka kaimasa saboda haushin wahalar daya basu da sauri yafito qofar gidan yana zubar da hawaye.

"Baaba kiyi haqury, banida zab'in daya wuce hakan, natabbata da kina raye zakiyi masa hukuncin daya fi wannan saboda kinfi kowa tsanar zalunci da cutarwa" baffa yafad'a had'e da duqewa wajen yana kuka, baffa Usman kuwa dama bayanan shida Nuraddeen suna can yareemawa asibiti dubo iyayen Rashida.

Jefasa shima sukayi kwance a tsakiyar bayan motar tsaknkanin qafafuwan su Inna sannan 'yan sanda maza su biyu suka shiga bayan motar tare da blessing, shi kuma kufron Jamil yashiga ya tayar da motar inspector najida na gefe sukuma sauran matan biyu na kujerun dake bayansu.

••• ••• •••
A b'angaren Rashida kuwa tana samun sauqi sosai saboda cikakkiyar kulawar da take samu agun Fatima har zuwa lokacin da Dr. nura ya dawo, yamatuqar jin dad'in yanda ya isko Rashida cikin qoshin lafiya da yanda tasamu sauqi saboda kulawar da take smu da kuma taimakon Dr. Sani, satinta biyu aka baata sallama don tji sauqi sosai amma jaririnta abun yakoma tsanantar masa duk da sauqin d'aya samu baya, yanzu kam tawatsar da abubuwan da suka faru akanta gaba d'aya basa gabanta saboda tsananin tashin hankalin da yaronta keciki, Wanda yasake jefata cikin matsananciyar damuwa, kullum cikin kuka take tare da addu'ar ALLAH yatayar mata da rayuwarsa saboda shi kad'aine kan gushe mata kewar habiby d'inta da akoda yaushe cikin tunaninsa take, kowane lumfashi dake fita daga cikin gangar jikinta cike yake da d'imbin qaunar Nuraddeen da akoda yaushe ke qara ruruwa azuciyarta.

Tunsu Dr na rarrashinta har sungaji sun dangana, Fatima kuwa duk da haka haka take tasata agaba tasa tayi mata wankan jego duk da dai ba irin na al'ada take yimataba saboda matsalar hawan jinin da tayi fama dashi amma dai takan sa tayi wanka da ruwa masu d'imi sosai da taimakonta, kuma tana tirsasata taci abinci maikyau sosai saboda yaron yasamu isashhin ruwan nono duk da yanzu saidai a matsa mashi nonon a fida saboda gaba d'aya likitoci basa bari aganshi, ganin yanda su Dr suka damu da yanayin da take ciki yasa tarage nuna damuwarta agabansu amma idan tana itad'ai batada wani aikin daya wuce kuka da tunani.
Tashin hankalin da suke ciki na rashin lafiyar yaron yasa gaba d'aya su Dr suka manta da batun tambayar ko ita waye balle har su nemi maida ita wajen iyayenta, sun ajiye wannan har sai lokacin da yaron yasamu lafiya ita kuma tasamu natsuwar da zata basu cikakken labarinta da kuma dalilin daya rabota da gida...







*ALLAH KAJIK'AN IYAYENMU*👏😭
[8/17, 10:19] Billy S Fari: 🚶‍♀️🚶🏻‍♂️ *SANNU SANNU*🚶🏻‍♂️🚶‍♀️
💎 _Bata hana zuwa..._💎


_WRITTING BY:_ *BILLY S FARI💎*

_DEDICATED TO:_ *BLOOD SISTER'S (AMZAHFAZ)*💋

_BESTOWED TO:_ *ZAINAB AL-AMIN (MOM NA'EEM)* AND *AMINA UBA AYUBA (OUM ASHFAQ)*💞

*DOMIN FARINCIKINKI SISTER SADIYA ZANGO (MIEMAH)*💖

*FATAN ALKHAIRI AGAREKU MOMMAH ME NANA HAFSAT (MISS XOXO) AND MAMANA HAFSAT RANO(OUM AFFAN)*❤️

Page___42💎

Ganin yanda hankalin Rashida yatashi sosai akan rashin lafiyar jaririnta yasa Dr nura yanke shawarar d'aukesa daga wannan asibitin zuwa federal hospital dake nan cikin garin borno saboda sunada qwararrin likitoci sosai, kasancewar duk irin aikin da yakeyine kuma akwai sanayya sosai tsakaninsa da likitocin yasa babu wata wahala aka basu takardar transfer izuwa federal hospital d'in.
Nana take suka fara yimasa sabbin gwaje gwajen saboda gano haqiqanin abunda ke damunsa, yanayin yanda yaron keshan wahala tamkar ransa zai fita ya matuqar tayarwa da likitocin hankali don koda akazo dashi asibitin lumfashinsa nafitane da taimakon oxygen d'in da aka ska masa, tsawon sati biyu sukayi a asibitin Amma al'amarin jaririn jiya iyau kuma sun kasa gane takamammiyar matsalar yaron don ko motsi yadena yi lumfashinsa kawai ne kefita, tun Rashida nakuka had'e da tsammanin tashinsa har takai ga cire rai, gaba d'aya yanzu ta dangana tare da cire ran yaronta zai tashi, kullum addu'arta d'aya ALLAH ya sassauta masa zafin ciwo saboda bayada alhakin kowa inba nata na haihuwar da tayi masa ba, ita kuma tayafe masa duniya da lahira, ahalin yanzu tafison idan ba Mai tsawon rai bane ALLAH ya karb'i abunsa da gaggawa akan wannan wahalar da yake sha, ta saki jikinta sosai tamaida al-amarin gaba d'aya ga ALLAH, asibitin ma tadena zuwa Fatima ce ke zuwa sai kuma Dr nura, kullum tana zaunenta gida tana ragema Fatima aikace aikace da girki ita da sabuwar mai aikin da Fatima tasamu, iyakarta idan ana buqatar nono ta tatsawa yaron a fida taci gaba da al-amurranta, tanajin damuwar amma dole ta tirsasawa kanta fidda ita saboda batasan tsarin da ALLAH yayi mata akan yaron ba, idan abunnya taso mata saita zauna ta kwatanta soyayyar da takeyiwa mahaifinsa amma ALLAH ya tsaro rabiwarsu duk da dai ako yaushe tana fatar sake had'uwa dashi nan kusa ba nesa ba,

Yau tunda safe ta tashi cikin wani irin kad'aici da shauqin son ganin habibynta ab'angare d'aya kuwa tausayin halin da yake cikine kwance azuciyarta, zaunawa tayi tayi kukanta mai isarta kafin tamiqe da sauri taje toilet ta wanko fuskarta jin motsin Dr nura da Fatima naqoqarin fitowa daga part d'insa zuwa nata zasuje asibiti, cikin jin kunya take takowa izuwa inda suke kanta sunkuye a qasa,

"A'a maman baby muna qoqarin qarasowa inda kike sai gashi munyi karo dake, hop kin tashi lafiya." Fatima tafad'a had'e da qarasowa tarungumota ajiki,

"Lafiya klw aunty Ina kwana?"

"Lafiya klw ya qarfin jikin naki?"

"Alhamdulillah, Ina kwana uncle." Rashida tafad'a had'e da d'ago kai tana kallonsa.

Murmushi yayi had'e da d'agowa daga dannar wayar da yakeyi kafin yace. "Lafiya klw Rashida kin tashi lafiya?"

"Lafiya klw uncle." Shiru yabiyo bayan gaisuwar taau kafin ya kad'a wayarsa a aljihunsa nagaba yana cewa.

"Yadai?, Rashida ko akwai wata matsala?"

"Eh uncle." Tafad'a hawaye na zubo mata daga cikin idanuwa,

"Subhanallahi! To kuzo mu koma ciki" yafad'a tare da nufar falon dake cikin sashen nasa, da sauri tace.

"A'a uncle tunda fita zakuyi kubari idan kundawo zamuyi magana."

"Ina ai bazai yuyu ba, dama sayayyar kayanki dana baby ne nake son muje daga nan sai muwuce asibiti, Amma yanzu kawai mubar zancen sayayyar har zuwa gobe, kuzo mushiga daga ciki." Hannunta Fatima takamo had'e dasa d'ayan hannunta tana goge mata hawayen dake kwance afuskarta, murmushin qarfin hali tayi mata tana mamakin cewa wai zasuje yomata sayayyar kaya ita da jaririnta, yaron da ba'ada tabbacin zai rayu kuma bayan haka satin daya wuce fa suka sassayo mata kayan sawarta daau hijabi da takalma da ita har yaron to idan ba b'arnar kud'i ba meye nacewa yanzu kuma zasu je sawo masu wasu kayan?,
Har suka isa falonsa Rashida batasan sun isoba tanacan tana jefama kanta tambayoyin da batada amsarsu,

"Zauna." Taji Fatima tafad'a tana qoqarin zaunar da ita akan kujera, kafin itama tanemi waje kusa da Dr tazauna.

Cire madubin idonsa yayi ya ajiye agefe sannan ya shafa fuskarsa yana fad'in. "Ina jinki Rashida meke faruwa."

Tajima tana wasa da yatsun hannuwanta kafin can tasamu tace. "Dama Ina son sanar daku ko wacece ni, saboda Ina son nakoma hannun iyayena da kuma mijina, kuyi haquri bana Rena irin taimakonda kulawar da kuka bani bane, kawai Ina aunayanayin da suke acikine, wanda jikina nabani cewa akwai matsala atare dasu, kamar yanda kuka sani sunana Rashida, ni haifaffiyar kano ce, nikad'ai nake ga iyayena, banida wa ko ya banida qane ko qanwa, muna zaune awani qauye da ake kira yarimawa, nayi aure da mijina dake tsananin sona awani gari da ake cema bebeji saidai nahad'u da matsalar rashin so da qauna daga uwar mijina, qarara tanunawa duniya bata sona bata qaunata, bansan cikakken dalilinta nayin haka ba inba kasancewata bare acikinsu ba, ko kad'an bata qaunata ita da wasu danginsa wanda adalilin hakanne suka nemi salwantar mani da rayuwa har nafad'a ayanayin da kuka tsinceni, namatuqar tsorata da al-amarinta wanda har nakai bana son tuna garin da duk wani abu daya shafesa, bana fata ko burin daidai da rana d'aya yarona ya kusanci koda inuwar garince saboda tsoron kada shima acutar mani dashi ko anemi salwantar mani da rayuwarsa, amma d'imbin soyayyar da nakewa mahaifinsa bazata barni nayi hakan ba, tsananin qaunar iyayena bazata barni in Amin da zuciyata dake raya mani innesanta dasu ba, naroqeku da kusake taimaka mani akaro na biyu ku hannuntani awajensu, inada yaqini akan dukkaninsu basa cikin kwanciyar hankali da walwala akan b'atarnan tawa, nasan kunyi mani abubuwa da yawa da bazan biyaku ba Amma zanso kusake taimakona awannan karon don Allah."

Taqarasa maganar had'e da duqewa gabansu tahad'a hannuwa tana kuka, duk da dai a dunqule tabasu labarin hakan bai hanasu fahimtar matsalar tata daga wajen mahaifiyar mijinta bane, ita tayi mata wannan aikin da Babu ko shakka asirine amma sai ALLAH ya kubutar da ita, d'agota Fatima tayi idanuwanta cike tab da hawaye tace.

"Kiyi haquri Rashida in Sha ALLAH sai ALLAH ya isar maki akan zaluntarki da akayi, tacutar dake tahanyar rabakinda masoyinki wanda afarko na munana masa zato, sannan ta rab'a iyayenki dake tajefasu cikin tashin hankali, in Sha ALLAH, saita tozarta kamar yanda ta tozarta soyayyar dake tsakaninki da mijinki. Kiyi shiru ki kwantar da hankalinki zamu maidaki agaban iyayenki amma don ALLAH kiyi haquri har yaronki ya samu lafiya, ahaka babu inda za'a iya tafiya dashi don haka mubar zancen komawarki har mugaabunda ALLAH zaiyi kinji."

Tafad'a tana d'an bubbuga kafad'arta.

Dr. Nura kuwa d'aukar glass d'in idonsa yasa sannan yace.

"An zalunceki matuqa amma kiyi haquri hakan na rubuce ne a cikin qundin qaddarar rayuwarki, ALLAH yakan jarabci mumini don ya gwada imaninsa, in Sha ALLAH komai zai daidaita, Amma kamar yanda Fatima tace, a matsayinki na uwa kitausayawa yaronki har zuwa lokacin da zai samu sauqi ni kuma zanjena shaidawa iyayenki da mijinki cewa kina hannuna cikin qoshin lafiya saboda hankalinsu ya kwanta kinji ko?"

"Shikenan uncle duk yanda kuka ce, nagode sosai, ALLAH ya saka maku da alkhairi ya arzuttaku da 'ya'yaye masu albaka."

"Amin mman baby don ALLAH kiyi haquri ki kwantar da hankalinki, SANNU SANNU Bata hana zuwa...in ALLAH yaso yaronki zai tashi kuma ki koma hannun iyayenki lafiya."

Fatima tafad'a tana cirota daga duqen da take, yayinda al'ajabin hali irin na Yaya hawwa yasa Dr yakasa motsawa daga inda yake zaune, Anya kuwamatar nan nada imani da zata I salwantar da rayuwar d'anta a irin wannan yanayi na tsohon cikin da suka ganta?, Anya kuwa ita tahaifesa da batayi tunanin halin da zai iya shigaba ta rabasa da jininsa da kuma matarsa da yake matuqar qauna?.
Wud'annan tambayoyin yashiga jerowa kansa yana mai ALLAH yawadarai da iyaye masu tunani da kuma hali irin nata.

••• ••• •••
A b'angaren su Yaya hawwa kuwa tuni aka saki muneera bayan ta amsa masu dukkanin tambayoyin dasukayi mata Wanda ac suka sake samun haske akan bincikensu, sun fahimci batada wani laifi ko sa hannu a b'atan Rashida don haka randa suka cikasati d'aya da kamawa aka saki muneera, tsalle da farinciki ba'a magana awajenta, da zata tafi takalli blessin wacce itace tayi mata mummunan duka kafin afara yimata tambayoyin tace.

"Mai kaki baki jiba." Juyowa blessing tayi fuskarta sake tana fad'in. "Maneera ya akayi?karkaji komai kaje ka sira?" Dashe baki muneera tayi tana susar kanta yadda kukasan maiqeya fuska duk tabi ta kumbure, ijiyarta d'aya tarufe saboda matsanancin dukan da tasha ga lab'b'anta sunyi sutu sutu kamar anjika ganda tace

"Ina tsira anan kin maidani uwa gwaggon biri, kinga dai ni banyi komai ba kika yimani wannan dukan? To su kiyi masu dukan mutuwa wallh, karki raga ma waccan yaya hawwar ita da kanta takai Rashi wajen boka ayi mata kurciya, sukuma su Innata da had'in bakinsu don kawai su auramun

Please Login or Register in order to submit comment