Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

duk Wanda yagani yasan yau Sarki mai jiran gado zai bar ƙasar , kodan tsaro Na musamman da wajen ya samu tundaga farkon Layin har Wajen parking


Driver da personal guard ɗinsa suka fito, ba'a bud'e su Deejah ba,saida aka kira sunansu sannan aka bude mata kofa ta fito

Ya rankwafo bayan ya buɗe mata ƙofa da k'asaitacciyar muryarnan tasa mai had'e da izza yace "muje".

Saida ta murmusa sannan ta zura hannunta Cikin nashi ta fito,Kowa saida su Deejah suka birgesa, abin akwai tsantsar birgewa da sha'a a cikinsa, tsabar kulawa yake bata a gaba kowa babu ruwansa da Jama'a cikin Takaitaccen lokaci jirginsu ya harba zuwa Chan ƙasar Egypt inda zasuje su ƙarashi cin Amarcinsu,har ta haihu achan, tareda wasu daga cikin ma'aikatan ta masu tayata wasu ayyuka a gida .


Thou fah, ga Aeesh , Aash Maryam da saleem Ga kuma Bamalli duk a EGYPT.


Bayan Wasu watanni Aeesh da Maryam suka haihu a rana ɗaya, duka maza zokaga murna wajen angwayen ƙarni musamman amma takamo hanya daga Nigeria tazo ganin Yan jikokinta, ranar suna yaron Ashman yaci sunan Saleem inda Aeesh tasa masa Sunan _*Habeebee*_ sunan da Saleem yayi Forcing ɗinta take kiranshi ada , ɗan saleem kuma ya maida Sunan Ashman, yayi masa inkiyan da Aash junior.


Ina Aareef 🤔😅😅😅

*AREEF*
Tunda Reey tayi Aure ya tabbatar yayi 2/0 babu Aeesh da kudin ta da yake Kwadayi, kuma babu Reey da yake mutuwan so , Gashi yanzu duk a tsarge yake tun bayan lokacin da akayi shari'ar Aeesh a kotu gani yakeyi duniya na kalloshi a matsayin mayaudari kuma mazambaci, Wanda tun daga ranan yayi Nadaman Kai ƙaranta wajen yan sanda, sai ya kuma Rungumar shaye shaye wanda a halin yanzu cinyar hannunsa ya ruɓe yake fidda Wani Ruwa mai shegen wari, idan Ya shiga wanka in zai goge ruwan Pampas na yara yake siya ya ƙulle wajen bayan ya wanke, ya kumayin wani allurar, Amma dukda haka ba'a Hour ɗaya panpass din ke jiƙewa Yayita wari, Ya koma kaman Zautacce, Shayeshayensa ya fara taɓa mai ƙwaƙwalwa, Kuma dukda abinda yakeyi bai fasa neman Mata ba don Ya riga ya saba neman Mata ya shiga jikinsa ta yanda bazai iya yakice shi ba,

_Ɗaga cikin Illar zina,idan mutum ya sabar ma kanshi baya iya yakisheshi a Rayuwarsa sai In Alllah ya nufeshi da shiriya_

Akwai Ranar bazai taba mantawa ba, ranar da ta zama rana mafi muni a rayuwarsa *Ranar Nadama* , da yayi Shayeshayensa ya bugu, ya shigo gidan Ummansa,tana ɗaka anan ya bita yayi mata Fyaɗe a zatonsa Matarsa ce.

Innalillahi Wainnailayhirraji'un

lallai tur da wannan halin zai kai ka ga aikata babban kuskuren da tunaninsa kadai zai iya saka ka hallaka, A ranar ce yayi nadamar yin Shaye Shaye a rayuwar sa.

kullum yana zaune inbanda Sallah da Istigfari baya komai sai addua da Rokon Allah Ya yafe masa kurakuransa, kowa ya tsane shi ya tabbata da za'a basu wuka ace su kasheni da sun aikata masa mummunan kisa, domin kuwa kaca kaca zasuyi dashi, Babu ɗan halal ɗin dake Son ya raɓeshi, kowa yaji abinda ya aikata dole ya ƙyamace shi, .Dole suyi Allah wadai da irin rayuwarsa, Umman sa kuwa Bayan Abinda Ya faru da ita, ta tuno da abinda ya shuɗe a Rayuwar ta, ta take umurnin mahaifiyarta Ta bi Faisal ya lalata mata rayuwa ta sanadiyyar Bayyanuwar cikin Aareef Zuciyar Mahaifiyar ta tabuga ta mutu, bata tashi nadama ba Sai yanzu da Rayuwa ke gaɓar garata, a lokacin da ɗan shegen da ta haifa yayi mata fyaɗe 😭💔....


_Allah ya tsarkake jinin Halal daga ire-iren wannan Fasadin, abune mai mautuƙar wahala Wanda aka sama ta tsarkakakken Jini na halal ya aikatama Mahaifiyar sa Fyaɗe_

_Ya Allah yanda muke Alfahari da Iyayenmu a bisa samar damu Ta hanyar Halal da sukayi ,ya Allah kasa ƴaƴan mu suyi Alfahari damu Fiyeda yanda Mukayi_

Sarah kuwa gani takeyi dama ta sameta da zata haɗa gasa masa zafi, tunda Yayi kuskuren Rabata da Mutuncinta tayi Alkawarin ƙarar da rayuwarsa a cikin ƙunci,bai tsaneta ba sannan kuma bawai yana sonta bane, sai dai abunda ya sani shine sha'awarta da yakeji shi ya janyo hankalinsa a gareta , babu sai zallan sha'awa , ta haihu inda ta haifa mai Namiji ,mai Kamada shi sak, tace ɗan shege bazai sha Nononta ba, ko kallon arziki bai samu a wajenta ba, ranar suna Yaro yaci Sunan Muhammad Giath Sunan Mahaifin Aeesh, Ana kiranshi da Hassan inkiyan mai sunan , Duk yayi haka ne don ya faranta Mata.

Ummansa ce ta karbi Hassan tuni ta aka bawa wata ƙawarta Salame ta fara shayar da shi , tabbas tayi nadama, sunyi nadama.

A lokacin da Faisal yaji Labarin An kama ma'aikatan sa, hankalinsa ba ƙaramin Tashi yayiba, nan da nan Ya tattaro Armys dinsa Suka taho Nigeria kai tsaye Gidan Umman Aareef ya nufa, burinsa yayi ido biyu da ɗansa, yana Ganinshi ya rungume shi yanajin Tsananin Ƙaunarsa na Ratsa shi takoina, nan take ya raba Dukiyan sa uku yaba Aareef kashi Biyu, maƙudan Kudaden da shi kansa baisan adadin su ba, Sannan ya nufi Gidan Ammie Ammie ya damƙa wa Mijinta sauran Kashi Ɗayan da ya rage yace gadon Ammie ne, sannan ya tafi batareda ya nemi yafiyar kowannensu ba, a cewarsa baima Kowa laifi ba, ya yarda ya buga game kuma sunyi Nasara, yayi 2/0, babu Ammie, fansar da ya dauka ma duk Sun Ruguje, Baiga Amfanin Rayuwarsa Ba, bazai iya rayuwa cikin duniyar nan ba alhalin Wacce yakeso yake rayuwa saboda ita tana rayuwa da wani cikin kwanciyar hankali ba.

Bayan Kwana uku aka tsinci gawar Faisal a rafi bayan Ya chakawa zuciyarsa wuƙa, ya faɗa rafin with His bleeding Heart..

Wasu gani Suke kaman Komai suka aikata daidai ne, wasu gani suke kaman Allah Bai musu adalci ba a duk lokacin da ya jarabesu da wani ƙaddara, Wasu basu yarda da ƙaddara ba,So suke Rayuwar su ta tafi yanda suka tsara , da zarar an samu Ɓaraka sai Su fara ganin Laifin Mahalicci...

Ƙarshen Faisal Kenan....✍️

Allah ka azurta mu da neman Yafiyanka kafin Mu mutu🙏🙏

BAYAN SHEKARU HUƊU.

*_Aareef POV_*
Tun rasuwan faisal hankalina ya tattaru yakoma kan juya kuɗin da Faisal ya bani, asalima ƙasar CZECH naje na karo karatu, na Cikawa Aeesh burinta na Son Ganin nayi karatu ,dukda a halin yanzu tayi min Nisa, amma shawarwarinta da burikanta akaina su Suka zama jagora Wajen gyara Rayuwata, nabar Shaye Shaye bayan Ya taɓa ƙwaƙwalwata an kaini asibitin Masu jinya na ƙasar czech, asibitin su ba kaman na gida Nigeria bane don Haka nasha matuƙar wahala a hannunsu, na jima sosai kamin Na dawo saiti don Ƙyamata sukeji dubada irin Smelly discharge ɗinda nayita zubarwa a lokacin, daƙyar suka shawo kan Matsalar bayan An narkarda maƙudan Kudaɗe.

mahaifiyata ta rasu watanni hudu da suka gabata, Hassan ya koma wajen Ammie don duk duniya banida Ahali sai ita, Hassan ya komaɗan saurayi babu inda baya zuwa, yasan Ammie kuma itace mahaifiyarsa don haka yake gani...

Sarah taƙi barin Rayuwarsa, kullum cikin facaka da duniyar sa take, gashi kaman an msa asiri ya kasa sakinta, abun duniya yayi masa yawa ,ada babu abinda baiyi ba don ya samu kudi gashi Allah ya kawo masa har inda yake amma babu Kwanciyar Hankalin da zai kashe su, ga wani jarababben son Aeesh da radadin rasata da yakeji a cikin zuciyarsa burin sa kullum shine ta dawo ya ganta ko sau daya ne ya sake rokon gafararta ko zai samu rangwame akan Azabar da yake sha a tsaitsaye,

Kudinsa yasa Ƴan mata suka fara rushing akansa, anan Ya lalubo wata A'isha ya aura itama albarkacin mai sunanta taci don yanzu bayaji baya gani Aeeshce a gabansa, duk wata mace a bayanta take, a ranar da ƙyar ya iya fita ɗaurin auren don Aljannun Sarah Tashi Sukayi suka nakaɗa masa na jaki bayan sun keta Babban Rigar da ya ɗinko musamman don yasa a ranar Daurin aure, Babban bakin cikinsa shine Aishan da ya auro bai sameta a budurwa ba akasin Aeesh wacce yake da tabbacin a lokacin da take taredashi burinta bai wuce ta damƙa masa Mutuncin ta ba, gashi Aishansa Batada wadataccen ilimin Addini

_innalilahi wainna ilaihi rajiun_

wannan balai da me yayi kama,yanzu kullum sai ya tuna da Aeesh ya zubar da hawaye, Allah Sarki tana chan tareda Mijinta Suna jin daɗi, idan sarah ta kunsa masa wani bakin cikin sai ya fice mata a gidan gaba ɗaya yanzu kusan Kullum sai iskokan ta sun Tashi tun yana Tsoronta har ya ware suka fara dambe dasu amma So tari yafi shan Wahala akanta.

Yafison A'isha Amaryarsa akan Sarah saboda tana Son ɗansa Hassan, ga sanyin Hali irin Na Aeesh, Amma Matsalar ta ta farko shine tanada kazanta, da rashin kamun kai , ita kou Sarah Saida ta Nadi Dukiyarsa Sannan ta fara nuna masa Asalin Kalarta na mara kunya kirikiri take dura masa ashar da ƙazafi a duk inda taga dama,har Kunyar shiga jama'a yake don In sunyi faɗa ya fita sai ta biyoshi har inda yake ta yarfa shi, Gashi ya kasa hakuri da ita dole in abinsa ya motsa yake lallaɓata ya samu ya rage zafi don Amaryarsa A'isha nada severe body odour tsabar kazanta har tsutsa sun fito mata, Sarah da kanta ta bar gidan bayan ta tara abin duniya ta bar A'isha da Hassan, bayan ya karbo shi a wajen Ammie.

Yanzu wani irin Girma yake bata , ta maidashi ɗanta ,ta zame masa family , amma koda wasa bata taɓa haɗa su Da Aeesh a wya ba gudun Abinda zaije ya dawo.

idan yafita gun aiki haka yake zama yayi uban tagumi yana tunanin kazantar Aishar sa wanda a yanzu Shine kadai matsalar sa, dabara ce tazo masa a hankali ya fara Siyo mata Mayuka, turaruka da sabulan da zasu Rage mata Wari da Kazantarta, aikou a wata daya ta dawo Mutum Kaman Kowa😀😄😄😆, a hankali farin ciki ya fara dawowa cikin Gidansa,bayan Yasha baƙar azaba.

Maganin Kwadayayyen mayaudari kenan💁🏻‍♀️


Bayan Wasu Shekaru 9:24pm
*EGYPT*

A hankali motarta ya danno kai sannan cikin nutsuwa motar ta nufi parking Lot, ta parka

Kaman Kowace rana a kowane lokaci Wajen Cike yake da dumbin ma'aikatan Daketa zarga zarga , da kuma Marasa lafiya masu shigowa da Masu fita ta kowane bangare sannan ga motoci a zube a parking lot da tarin Security, wanda da alama wani babban Bako Sukayi .

A hankali ta Ziro ƙafarta ta fito, Fuskarta ta haska tsakanin Street light da ya haska gaba ɗaya wurin, Black beautiful skin Ɗinta yayi reflecting da hasken Da ya haska ta fuskar ta.

Saida ta rufe ƙofar sannan Ta juyo Gaba ɗaya
Mrs Sufyaan RN BNSC msc phd ,abinda na gani kenan a Badge tag ɗinta ,wanda hakan Ya tabbatar min da ta cigaba da karatu bayan zuwansu egypt.

Saida Ta Bari Maryam ta dawo daga afternoon shift ɗinta, ta bar mata yara sannan Ta samu damar tahowa dan Ashman na asibiti tunda safe aiki ya riƙe shi...

A hankali ta ta juya ta bude bayan motar, ta Fiddo wani basket,ta Kashe motar sannan ta zare makullin.

Har yanzu tana nan Yanda Take Aisha Muhammad ihtyn Aash, babu abinda ya sauya daga gareta na kamanni saidai maturity da natsuwa da suka Dada bayyana a Fuskarta.

Cikin Natsuwa ta nufi Department ɗin da take aiki, ta karɓi shift a wajen mai Afternoon don a asibitin zata kwana night takeyi sannan ta Shigo don duba Yara marasa lafiyan dake jibge a ward ɗin...

"Mrs Sufyaan, help me Feed the patient on Bed 007"

Muryar Ɗayan Afternoon nurse dake Shirin tafiya ya gifta ta kunnenta, cikin natsuwa ta nufi wajen Da aka tanada wajen Ajiye folders din Marasa lafiyan, ta duba File ɗin Bed 007, Maryam Muzzammil Ta Gani, gabanta ya faɗi, Da alama New admission ne, Jikinta na rawa ta duba Condition ɗinta, Mild traumatic brain Disorder ,ta Furta a Hankali, sannan Ta duba prescribed Diet ɗinta, ta Kira Cafeteria line aka kawo mata abincin da ta bukata, sai a sannan ta fito zuwa makwancin yaran, a bed 7 ta tsaya tana duba yarinyar Mai kamada wanda ta sani.

"Maryam Muzzammil"

Ta furta tana zama akan kujerar Kusada ita.

"My dad call me baby"

Yarinyar ta faɗa Fuskarta akan Tab ɗinda take dannawa.

Aeesh tayi Murmushi, lokaci ɗaya yaji Yarinyar ta burgeta, okay .

"Baby stand up Zo muci Abinci"

Babu musu yarinyar Ta mike zaune, sannan A Hankali Aeesh ta fara bata Damammiyar cornflakes da tasha Madara a baki, tana Karɓa, jefi jefi Aeesh na janta da surutu Yarinyar na biye mata, saida ta shanye tass sannan Yarinyar ta koma ta kwanta a rigingine ta Cigaba da Buga game ɗinta, yayinda Aeesh ta Koma wajen sauran yaran Tana duddubasu...

Hayaniyar da taji ya fara tashi daga dakin ne yasa ta dakata daga abinda takeyi, ta juyo tana duban Mutanen dake shigowa, gani tayi an rirriƙe Maryam amma sai kwacewa take tana Wani irin jijjiga .

Kaman daga Sama taji ɗaya daga Cikin ƙattin matan da suka shigo tana nunata da faɗin

"Wannan Itace quack ɗinda ta Bata Abinci ko?"

Gabaki ɗaya yaran da suka shaida hakan Suka amsa da Eh.

Tana tsaye kwakwalwar ta ta kasa tantace mai ke shirin Faruwa ko ince Meke faruwa a daidai wannan Lokacin.

Tasss taji Saukan Mari a kuncinta, Wanda ya dawo da ita cikin hayyacinta , ta dafe kuncinta da sauri don Babu Shakka marin ya ratsa ta, jinta ya tafi hutu na wucen gadi, Dishi Dishi take ganin Matarda ta Mareta da alama masifa take zazzagawa, ganinta bai dawo ba saida Taga matar na shirin fita janye da hannun yarinyar, Tarin Mutanen da suka rakota na biyeda ita.

A hankali wasu zafafan hawaye suka sauka akan fuskar ta, ta saba shan Mari akan Aikinta daga Iyayen yaran zuwa Yan uwansu amma bata taɓa gazawa Ba kullum burinta ta aiwatar da aikinta, tunda ta zama Nurse Kullum Burinta tayi iyaka ƙoƙarin ta wajen kare lafiyan Alumma bata son Wani hayaniya ya shiga tsakaninta da Relatives dinsu, amma wannan Karon batajin Zata iya bari a mareta a banza, cikin Tsananin Fushi ta fito, tanajin yaran na dariya ƙasa ƙasa, Office din Ashman Ta nufa, ta chanza kaya zuwa Baƙar jallabiyarta datazo dashi, tasa bakar hula, bata ɗaura Dankwalin ba sai ta ɗaura a ƙugu, ta fito a fusace, tana fita ya dawo don haka ya hango Ficewarta, yabi Bayanta.


A lokacin har an cusa yarinyar cikin Mota, matar na shirin Shiga motar Aeesh ta taɓota, tana juyowa Aeesh ta sauke mata Mari a Fuskar ta, wanda yasa ta gigice tayi baya.

Aeesh ta tako gabannta cikin Dakakkiyar muryarta da alamar Gargadi tace

"Mu Nurses ba ƴan hayaniya bane ,mun samu ingantacciyar Tarbiyya daga Uwa Florence Nightingale, a yanzu Ni ba Nurse bace, Uniform Ɗinma na cire , idan Da shirin Dambe kikazo a shirye nake"

Ta fadi hakan tana Dunƙule Hannunta, matar tayi tsaye dafe da kunci tana maida numfashi don ba ƙarya ta maru.

"A'isha Muhammad"

Taji an kirata daga bayanta, koda ace ta mutu ya dawo muryarta bazasu gaza Gane Muryar BAMALLI ba, da mamaki take kallonshi har ya tako Gabannta shida matarshi wanda mamaki ya hanata gane Fuskar ta, daidai Lokacin Ashman Ya iso wurin, Shima a mamakince kallon matar bamalli Mulki da sarauta sun Ratsata, tana sanye da Golden Alkyabba yayinda bamalli ke Sanye da Kayan Sarauta, dogarai sun Mamaye shi.

Yayinda bamalli ke kallon Aeesh da tarin mamaki haka Deejah ke kallon Aash itama da Mamakinta, jikin dogarawan Na rawa suka Nufo Aeesh zasu kamata bayan Matar nan ta zayyane masu Abinda Ya faru a tsakanin su.

Da mamakinsu sai Bamalli ya Dakatar dasu, sannan yasa aka kawo masa yarsa Maryam Muzzammil ,ya kallo Aeesh yace tabbas Ya yarda Fyaɗe da ɓta ƴaƴan mutane ba abune Mai kyau ba, a gaban Idanunshi akayima ƴarsa Fyaɗe a lokacin tanada Shekaru uku a duniya, bayan An shaƙa masa Sinadari mai Kasalar da mutum, ta dalilin Haka ta kamuda Firgici Mai tsanani wanda ya haddasa mata ciwo a kwakwalwarta mai tsanani.

Rayuwa kenan Duk abinda ka aikatawa ɗan wani sai anyiwa naka, Bamalli ya tabbata alhakin Yaran da yake ɓatawa ne yabishi, don Bazai iya ƙirga iya adadin Yaran da ya ɓata ba, gashi Ya faru akan Tilon ƴarshi da yakejin duk duniya babu kamarta.

*A gurguje*

Sun koma Nigeria bayan sun Kwashe shekaru Biyar a EGYPT, A ranar da zasu bar Asibitin sunsha kyaututtuka kala kala, Aeesh da Aash Sun Samu award na musamman From Fellow staffs as The Best Professional Couples na Wannan Shekarar, While Saleem da Maryam ma suka taho da nasu kyaututtukan, Sun dawo Nigeria bayan Sunyi kewan ƙasarsu na tsawon shekaru, a lokacin har su Reey Sun dawo.

Ƴaƴanta biyu Umaymah da miqdaad, a yanzu amintakan dake tsakanin su ya wuce tada don har ta kada kan ƴaƴansu, Tare suke zuwa makaranta kuma suyi Spending Weekends a tare, a halin yanzu Noor Tanada shekaru Shida yayin Da Saleem (Habeebein Aeesh) yakeda Shekaru uku a Duniya.

*_Friday_*
Da yamma.
Dawowansa kenan daga gidan Abba Ya kai su Noor suyi Spending weekend dinsu achan, ya faɗa Bathroom ya don yayi wanka, ya sakar ma kanshi Shower

A hankali ta turo Kofar bayin, ta shigo , ya juyo yana dubanta,gashinsa mai tsantsi ya Manne a fuskar sa kaman leda.

ya saki Ƙasaitaccen Murmushin dake ƙara Ma fuskarsa annuri a koda yaushe, kafin Ta karasa Shigowa Ashman Ya jawota jikinsa, ya zagaya ta da dukkan hannayensa, a hankali idanunsa ya sauka akan fuskar ta.

"Yau tamuce"

Ya faɗa muryarsa ƙasa ƙasa, nan take jinin Jikinta ya sake daukan Dumi yana neman Tafarfashewa nan Zuciyarta ya fara melting with Emotion, Tayi kewarsa kaman babu Gobe, Satinsu hudu kenan Da dawowarsa Nigeria Amma basu samu lokacin juna yanda ya kamata ba, hayaniyan yara da Ƙiriniyarsu duk tasha kansu ga Ƴaƴan Reey dake Spending Weekends a gidansu in sun haɗu Masha Allah.

Ta ɗago Fuskarta kadan, karan hancinsu ya hadu waje guda sannan Ta miƙa hannu ta zagaye Wuyansa.

Da hannunshi ya lalubi ƙasan Cikinta sannan yace
"Babyna fa?"

Ta shagwaɓe fuska

"Yunwa yake ji"
Ta faɗa tana kunna Shower a hankali ruwan ya fara ɗiga akansu yana jiƙasu

K'asaitaccen murmushi Aash yayi, a kan la66ansa ,Aeesh ta nutse cikin jikinsa wanda yake haɗe da kamshin Sabulun wanka da turare tana jin Natsuwa na Ratsata ta ko'ina

Tare sukayi wankan suka fito, Suna fitowa suka hangi wayarta dake gefe yana ruru, Reey ce da sauri ta dauka, Reey tace Ta turo Driver yanzu Zai Kawo su Umaymah ai da sauri Aeesh tace bata bukatar visitors Itama ta gaji, a barta ta kasance da nata mijin ayau.

Bata jira cewar Reey ba ta katse wayar, tana Katsewa wani kiran ya sake Shigowar da Sunan Mother inlaw da sauri ta jawo hijab ɗinta ta Saka, Ashman na ganin yanda tayi, sai tabashi dariya, har kiran ya tsinke wani ya ƙara shigowa ta daga tana gyara Fuskarta.

Amma maimakon taga Fuskar inna Yattai kaman Yanda tayi tsanmani sai Fuskar Noor ta bayyana

"What...!"

Aeesh ta furta cikin ranta tanaji kaman Ta fito ta cikin wayan ta kwada Mata Mari a fusace tace

“Ina Amma...."
Noor ta turo Baki a shagwaɓe kaman Zatayi kuka, Ashman ta leƙo kansa yana kallonta ta cikin wayan yace

"My baby me ya faru?"

Tana jin Muryar Daddynta ta fashe da kuka

"Daddy Kazo ka kaini Gida, Ni gida zan koma"


"Calm down, c'mon Tell me, me ya faru, wa ya tabaki?"

"Ayyan ne ya ƙwace mun icecream ɗina"

Ta faɗa da majina jage jage a fuskar ta.

Aeerah kenan Uwar ƴan ƙorafi ga tsiwa da Tsaurin ido saɓanin ƙaninta Saleem Da ya kwaso wani ɓangare daga Cikin Halayyan Mai sunan Wato Saleem, ta wani ɓangaren kuma ya debo kadan Daga na Aeesh.

Ayyan dake kusada ita yana jin komai ,Ya leƙo fuskar sa, ya rankwashi Kanta sannan Yaja kunnenta ya murɗa,

"Daddy kasan Abinda tayi?, She beg a stranger For the icecream"

Aeerah tasa kuka, Aeesh ta daka mishi tsawa

"Cikata da ƙaton kanka anan , yaro da mugunta kaman ubansa"

"Kyan da ya gaji ubansa"
Ashman ya furta hakan cikin sigar raɗa, ta Harareshi ya Kanne mata ido ,tasa karfi ta tureshi, ya faɗi ta Gefe yana dariya.

Sannan ta maida hankali kan Noor dake kuka.

"Mummy wlh I don't beg , Junior Aash (Ashman ɗan Saleem) gave it to me"

"Yimin shiru! Kwadayayya kai kuma na sake ganin ka rankwashe ta saina hallaka, will apologize to her now ko saina makeka?"

Tafada cikin zaromasu idanu ta cikin Waya, yanzu yanzunnan daga Barinsu gida har sun Ja mata magana.

Turo baki Ayyan yayi, saida ya sake rankwashinta sannan Yace

"Am sorry"
Yana gama fadin Haka ya arta a guje yana dariya, Noor tabi bayanshi da gudu, saura ƙiris wayar ta fadi Saleem Mai bin Aeerah yayi saurin taro wayan da cewa

"Oppa, Ihtyn Oppa...! granny na Kitchen tana mana ɗan wake, ku zo kuci"

ya faɗa yana nuna hanyar Kitchen, Aeesh tayi Murmushi tace

"Habiibi Drop the phone I'll call Granny anjima"

Dif ta Kashe wayar, ta juya kanta ga mijinta da ya faɗa chan Gefe, ya zura hannayensa a cikin Gashinta ya haɗa goshinsu

"Switch the phone off"

Muryarsa ta fito a shagale kaman na maijin bacci, Murmushi mai taushi ya suɓuce mata.

ya janyota jikinsa sannan a hankali ta rufe idanunta a daidai Lokacin da ya Sunkuyo da fuskarsa kan Nata, wani shock ya ziyarcesu a lokaci ɗaya, Lips ɗinsa masu Taushi suka ɗagata cikin gajimare .

Idanun Aeesh suka ciko da kwallar farinciki, a yan shekarun da basu wuce yan yatsun hannunta ba a baya bata taɓa Mafarkin Zata kasance tareda shi cikin Farinciki mara datsewa ba, sai gashi Ashman Ya dinke rayuwarta da Farinciki, ya mamaye kewayenta da Soyayyarsa ,bazata gaji da godewa Allah ba akan wannan baban Falala da yayi mata ba,bazata gaji da nuna Farincikinta a gareshi ba ,Gata da ƴaƴan sa har biyu da kuma cikin Dake shirin zama ɗa na uku a cikin ƴaƴan su, sai ta daga idanunta ta dubeshi yana tsaye Yana share mata ƙwallar da ta digo saman Fuskarta.

A lokaci guda Kwakwalwarta ta hasko mata wani lokaci a baya,a lokacin da ta fito daga hostel tana ɗauke da Cikin Noor tayi dare a ƙofar Gidan Aareef tana neman gafararsa Amma yaki ya bata dama.

A hankali ta lumshe idanunta, Ƙwallar da suka cicciko a idanunta suka gangaro saman Kuncinta, ta manna ƙirjinta da nashi ta yanda duk suke iya jin Bugun zuciyoyin juna, Muryarta a kasalance tace

"Hayateey Your heart and mine are forever one!, no more bleeding Hearts"

*Sureey*

A hankali ta Dire Biron dake hannunta hawaye suka gangaro mata, ta jingina kanta a Bayan kujerar da take zaune nan take Bacci mai nauyi ya dauketa cikin barcin taji Muryar ZEEYK yana faɗin

"Baby Hope I have completed the missing Puzzle"

Tayi firgigit ta buɗe idanunta, fuskar Ashraf dake tsaye Gabanta ya fara rikidewa izuwa izuwa kamannin ZEEYK ,fuskar nan tasa Mai ɗauke da murmushi akoda yaushe, sake buɗe idanunta tayi ,ta diresu akan na Aashraf dake Faman Sakin Murmushi, Tun ranar da idanun ta suka fara sauka akansa a matsayin Mijinta taji hotunan kowane Namiji ta ɓata a idanunta, bata Ganin kowa sai shi, shi kaɗai.

Ta kalleshi A lokacin da ya sake daga idonsa Ya kalleta, zuciyarsa ta Narke cikin tsananin So da ƙaunar ta, ya Dire Littafin dake Hannunsa ya dubeta da murmushi a fuskar sa

"Uhkty kinyi ƙoƙari matuƙa da kika iya rubuta tarihin Rayuwar mu duka a littafi ɗaya, Amma sai naga kaman Kin manta abu"

Ta kalleshi da mamaki, yacigaba da fadin..

"Kin manta baki gaya mana yanda akayi saleem ya samu hujjojin da ya kama Abban Maryam dashi ba, kuma taya akayi yasan yanda Abban bamalli ya kashe Kawu Imam"

Sureey tayi Murmushi tace

"Ban manta ba ai a bayyane yake ,Abba shi ya ba salee Duka hujjojin tunda Yana nan akayi komai kuma shi ya ɗauke CCTV evidence dinda ya kasance babban hujja,sai ya mikawa Saleem dan Maryam ta koma gareshi”

"Shi kuma Hamza ya ƙarshen shi ta kasance?"

Bata ida bashi amsa ba Zaid da Bintou suka shigo a guje, Nabeelah da Ameen (yaran da ta haifa masa) suka biyosu da Pillows Suna wasan Jifa.

Ashraf ya buɗe baki zai Dakatar dasu Sureey ta kwada masa Pillow akansa, ya bita a guje ta gudu tana Kyalƙyale Dariya


*THE END*

Tammat bihamdulillah,

Alhamdulilah,
Alhamdulilah
Alhamdulilah


Na sadaukar da littafin Wuƙa a Zuciya ga duk wanda ya karanta shi. Ina fatan duk wanda ya karanta yaji dadi ko kuma ya karu da wani abun to yayi min

Please Login or Register in order to submit comment