Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

be hard for us ,Koda munzo da Hujja ba Lale bane a hukunta su Gwargwadon abinda Sukayi ba, but muma mun kawo Ƙarfin Da zamu Iya daukar Doka a hannun Mu, inada Iko ta ko wane Ɓangare da hannu na Zan Hukunta su, Ki Cire komai a ranki ki tashi mu dauki fansar jinin Mahaifiyar Mu"

Dafata yayi cikeda Ƙwarin gwiwa yacs

"You Are strong , you can do it, I know Kinada ƙarfin Zuciya Zuciyarki bazata Juri kallon Miyagun da suka Maida Mu Marayu A raye suna walwala kaman Kowa ba"

ta goge hawayen fuskarta Cikeda Kwarin Gwiwa tace

"Yeah Am strong, I can do It, Mum's Blood Will never Go unjust"

Sai Kuma Hawaye ya sake Ɓalle mata, Sosai Rarrashinta ya cigaba dayi cikin tausasawa.

A Chan Ƙasar Canada Kuwa Jinin AMMIE fa yaƙi sauƙi, Kullum Jiya iyau ada tana Iya magana duk da bata Iya daga koda yar yatsanta ne ,Amma Yanzu Abin ya daɗa munanta bata iya buɗe Idanunta, bata iya daga Koda yar Yatsar ta ne, Shiyasa yanzu koda An kirasu basu ɗauka, gudun tayarmata da hankali.

Bayan Gwaje-gwaje da Dube Duben da Likitoci suka gudanar akanta, nan take sukayi Referring ɗinsu Zuwa Babban Asibitin Dake chan Ƙasar America.

Sosai Goggo ta tayar Musu da Hankali cewa Da ita Za'aje America, Itace zata cigaba Da Jinyar Ammie, Cikin Dabara SADEEQ yasa Aka maidato su Nan Gida Nigeria Ita da Inna Yathai, a ranar Kou yasha Zagi da tsinuwa kala-kala.

Ashman Dakansa Yaje Har Airport ya daukosu, a ranar Saida Yayi nadamar Zuwa Ɗaukowa da yayi ,domin Kuwa Akanshi Fadanta Ya ƙare, Sai haƙuri Yathai ke bata Amma taƙi ji.

A Ranar Saida gabaki Daya Unguwa suka san Da Dawowan Su Goggo, Kowa yazo Saita bashi Labarin Tashin Hankalin Da suka Shiga a can , Tunda Taje ba'a daura Tukunya anyi girki ba, daidai da yar shinkafa idan zasu ci Siyowa akeyi, ga ƙasar Sanyi Su Kullum cikin yawo da Jigajigan rigunan sanyi Suke.

Ashman da kanshi yaje Har makarantar yayi Surprising ɗinta, ya Kuma dawo da Ita Gida, Tayi Murnar Ganinsu Sosai Amma Labaran faɗi ban tambayeka ba da Goggo ke bata akan Ciwon Ammie yasa Hankalinta ya tashi, Dole ta koma Makaranta Badon ta so ba.

A ranar da ƙyar ta iya Rintsawa Saboda tashin Hankali, Reey ce mai Tausarta da bata Baki

Bayan Kwanaki Uku ZEEYK Dakanshi Ya nemo Saleem don Suje su ya nunashi A wajen Daddy a matsayin mijin Da Maryam zata Aura.

Cikin Shigar Kamala ya taho suka kama hanya har Lagos suka tafi tare wajen Daddy, Daddy Na Ganinshi ya Tuna Mara Mutuncin da Ya kusa marinshi a asibi.

Da sauri Saleem ya karaso gabansa , yana zuwa ya zube akan gwuiwarsa, Ya na roƙonsa yafiya ,Daddy Akwai Zuciya Sosai ga Kafiya ko Kallonsa Baiyi ba ya Dube ZEEYK rai ɓace yace

"Me yaron nan yazoyi a gida na?, fitan Min dashi "

"Dad Shine Wanda Princess ta tsayar Please don't say no"

Salem ya sunkuyar da kansa kasa, a zuciyarsa yana wishing ina ma dai zai iya kuka, maybe in hawaye ya fito masa zai ji sanyi a zuciyarsa, wannan mutumin da yake tsaye a kansa is his only chance to happiness, idan yace yes to shi kam ya samu duk wani buri nasa na rayuwa, in yace no kuma tamkar a saka full stop ne a rayuwar sa.

Daddy ya sauke ajjiyar zuciya Yana Auna masa Mugun Kallo yace

"wannan abin shine Princess Dita zata aura?, wannan Mara Tarbiyyar?, over my dead body, ko bayan raina"

SALEEM ya kuma sunkuyar da kansa yana jin bugun zuciyarsa yana karuwa. Daddy yacigaba da cewa

"Ko ka manta Kalaman Rashin da'ar da ka Gasa min a asibi?, Ka manta Cin Mutuncin da Kamin?, Kace Batada Tarbiyya ban bata tarbiyya ba? Nima banida Tarbiyya like father like daughter!, Tho Mara Tarbiyyar kake Son Ka aura??"

SALEEM yayi shiru Daddy Yace

Tambayar ka fa nake

SALEEM ya dago kai ya kalli daddy da jajayen idanunsa yace

"daddy I have bad temper, babba Bai taɓa marina ba Shiyasa Najishi so strange , but that Aside, Now Abinda ya kawoni shine Auren diyarka nazo neman Aure ne, Maryam ce ta turo Ni, please Karka Hanani ita,Bazan Iya rayuwa babu Ita ba"

da mamaki daddy yace

"ita Maryam dince ta amince maka kazo gurina ka nemi auren ta?"

Saleem ya gyada kansa yace

"yes daddy, kuma Mun sasanta itama tana Sona''

Daddy ya jinjina kai, Ya dauko waya zai kirata kenan Yaga saƙon ta.

_Daddy na Turo maka nama, Ka haɗashi da Karnukan Su Yazeed Please_

Murmushi daddy Yayi ya Maida wayar sa, Ya mika wa SALEEM hannu da niyar ya taimaka nasa ya tashi tsaye, Saleem ya watsa masa harara ya mike,Shifa a Dole Tsohon nan Ya Takura wa rayuwarsa Akan yana Neman Auren ɗiyarsa ne Yaketa faman ja masa Rai ,tunda yake bai taɓa Durƙusa ma wani Ba sai Yau Duk akan Mace , ya dau Alƙawarin daga wannan Bazai sake Juran wulaƙanci ba, idan Daddy ya Sake Ɓata masa Zai fito masa a Mashayin gaske Yaci Mutuncinsa in Yaso ya Hanashi yarshi, mutuwa Zaiyi Ba,koda ya shiga wani Hali na dan wani Lokaci ne, So baya kisa .

Daddy yaji zafin Hararar da Saleem yayi masa amma bai nuna ba, Suna Fitowa Yayima Dogs securities Alama da Ido,Aikam nan take aka kwance Masa Karnuka, Sukaita Binshi da Haushi saida Suka Yayyaga masa Kayan Jikinsa Sannan aka buɗe masa Ƙofa ya Fice da Gudu kaman Zararre.

Tun daga Lokacin Saleem ya dau Alwashin Bazai sake Kulata ba, idan Itace autan Mata a duniyan nan ya haƙura da ita, kuma wallahi sai ya rama Cin Mutuncin da mahaifinta yayi masa.

Yayi matuƙar ƙoƙari sosai wajen Ɓoye yanda yakeji aransa Dangane da Ita, Yayi Ƙoƙari Sosai Domin Kuwa bai sake neman ta ba Duk yanda yakeji a ransa akanta ya Danne Ya Cigaba da harkokin shi kaman Kullum, Dukda Yanajin bazai Iya Jurewa na tsawon Lokaci ba ,Amma Ya sa a ranshi rayuwa da mace ba Nashi bane ,Ƙasƙantar da kai A neman Mace Duk ba nashi bane .

Bayan sati Ɗaya Dakanta ta nemeshi a waya tace yazo Gidan Su na kd tana Neman shi ,yaji Mamaki sosai Amma sai Ya Ɓoye mamakinsa

a lokacin yana Gidan Zaheer (Ƙanin Ghost) _jarumin Littafin Maƙaryaci_

Nan fa Zaheer ya tada Rigima akan Shima fa sai anje dashi, Dole akai shi yaga wacce ta sace Ma Nasty Abokinsa Zuciya.

Slowly yake driving din idonsa a kan titi yana sauraron Zaheer sai Zuba masa Surutai yake

can dai ya ja tsaki ya girgiza kai, speaking calmly yace

"Kai Kafa Isheni ina Kaiwa roundAbout Zan saukeka ka hau Napep ya Koma dakai Gida"

Dariya Zaheer yayi yace
"Yaseen Bazan sauka Ba In Kuma Ka matsa Inbi bayanka in hanata Sauraron ka idan ƙura ya lafa In Zagaya nayi wufff da ita ”

SALEEM ya ɗan Harareshi yace

“maitanka akan mata yasa Ghost ya aura maka Mata uku a lokaci Guda, Dukda Haka baka sajuda ba"

Zaheer ya shafa lallausan gashin kansa cikin dariya yace

"Kasan mene?"

Kallonsa kawai saleem yake yana jiran jin abinda zai ce

Zaheer ya cigaba da cewa

"Tunda ka Saki ƙaddararka ta faɗo cikin Littafin Bintou ka kaɗe, ka Duba Aaryaan Mijin Titi bata barshi ba Saida Tasa Soyayya ta gasashi, Ga Kuma Yayana Ghost uban barazana Shima ba'a Ƙarƙare ba Sai da aka Gasashi , ko Ni danake ƙaninshi bata Barni ba akan Dan Mistake kadan Taso ta Hallaka rayuwata ,tasa Aka Aura min Mata Uku A lokaci Guda, a lokacin ji nayi inama banzo a raye ba, inama Bintou bata Sanni ba🙆🏽‍♂️"

SALEEM dake masa wani kallo ya dakatar da shi ta hanyar cewa

"Me kake Nufi?, Kana Nufin Nima Saina Sha Wahala kenan akan So?"

"Ba wai bane, kaji tsoron Neman Da Maryam ke maka ,Daga Nan naka Labarin ku zai fara"

SALEEM ya gyada masa kai yace

"plss CUT the chapter"

Zaheer zai sake yin magana ya hango me Agwaluma Tsaye a gefen titi, da sauri yace

"Boss please ka ɗan tsaya, I want to get those Agwalumas, Matana biyu nada juna biyu Kuma Suna Mugun Son Agwaluma , Please Wait "

SALEEM ya ɗan kalli Mai Agwaluman ya kara ma motarsa gudu sosai yace

"Allah ya kiyaye,na Daukoka Muje Mu gyara Soyayyata kazo Kana Mn maganar wasu Matan ka, Meye Hadina dasu?, Ni nace ka dirka musu cikin ne?"

Zaheer yace "Toh ka ajiye ni, ai bance Dole Ka yarda Na raka ka Bama, Akan Matana Ni banƙi in Ɓata da Kowa ba Ko wayeshi!"

SALEEM ya kashe Motar ya Parka a Gefen titi, ya Buɗe Masa "A sauka lafiya"

Zaheer yace "yanzu Saleem Sauke Ni zakayi a Tsakiyar Titi baka tsoron Wani Mugun Abu ya Sameni a han..."

"Please Fita Kana Bata Min Lokaci"

Zaheer ya fita Yana bata Fuska, Ko Kallonshi saleem baiyi ba ya tada Motar Ya tafi ya barshi anan, Lallai saleem Ƙarshe ne a fagen rashin mutunci , To Wlhy Zaiyi maganinshi, shima Allah ya nuna Masa Ranar tashi Ya rama.

kofar gidan su Mama yayi parking ,Kai tsaye ya Shiga Gidan babu Ko sallama

Mama na zaune a falo tana ɓarar Dafaffar gyaɗa taji dirar Mutum kaman an jefoshi , a ƙufule tace

"Waye wannan Dalla"

Karasa shigowa yayi batareda Yace da Ita komai ba ya samu wuri Ya zauna Yana harararta

A tsorace ta koma baya ganin sa tace

"Waye wannan?"

Shi dai bai tanka ta ba bai kuma kalli inda take ba,

tace "Wannan dai ba Halin yan Aljanna bane, don kaga ina walha sai kato ya fado min parlor ba sallama"

Ba tare da ya dubi inda take ba yace

"Kina tsintar Gyaɗa dai" rai bace tace "Ya zaka ce ina tsintar Gyaɗa?, Ina nan Zaune Ka ganni da hijabi walha nakeyi ka wani fado Mana Gida babu ko sallama sai Kace gidan jatumin ka"

Dubanta yayi a karo na farko yace

"Ina Matata??"

Tace "Eh Gata A kaina, matarda ubanka ya aura Maka, ya kuma daura min dakonta a ka"

Lallai ma Tsohuwar nan, da Alama rabon ya Koya mata Hankali ne ya Biyo dashi ya kalleta bai ce komai ba,

tace "Maryam din mafa ba Sonshi take ba, Iyayi Da Kafidiri Wai Matarshi?"

Komawa yyi ya jingina da Kujera, ya Lumshe Idanu,Matar nan Na Neman Ƙure haƙurinshi a yau Dinnan,

Ganin Yayi mata shiru bai sa Tayi shuru ba tace

"SALEEM Hamisu kake Ko wa? ,in Aure kake so kaje can Hamisu ya Daura maka, Ni Banida Hurumin Hada aure, ko kai baka san Maza Ke Daura Aure ba mata ba? Ko dai Anyi asarar Kudin Laraba ne?, dan Naga alama Kaman Baka leƙa islamiyya ba"

shi dai bai ce mata komai ba, tacigaba

"Duk na tattara ma yarinyar nan kai Ubanta Ya daura Maka,in Huta da Wahala Nice Nan Na reni Maryam tun tana Tsumman Goyo har Ta girma Tayi wayo, Burinta a kullum ta Zama Likitan Oda ta taimaka ma marasa Lafiya, Burinta ya cika, Amma Saboda Tsabar mugunta kalar naka Kasa aka Koreta a wajen Aiki, yanzu kuma Kazo wai Sonta kake..."

Ta kama baki

"Ohh na manta Kila taku salon Soyayyar kenan, Ba'a shiga tsakanin Masoya ai ko?"

Nan Ma shuru, ya shaƙi takaici Kamar Me, Ƙiris ya rage ya fashe.

Muryar Maryam yaji Kaman daga Sama

"Kai mama daga zuwan mutum kin bi kin Dameshi da Surutu sai kace an gaya miki ke yazo nema?"

Ɗago fuskarshi yayi Ya dubeta, tana Sanye Cikin Shigar Atamfa Tayi daurin ture Kaga Tsiya, atamfar tayi Mata Kyau Sosai.

A hankali ya Lumshe Idanunshi ,ya tuno farkon Haɗuwarsu a Turkish Da Atamfa ya fara ganinta kuma Da irin Ɗaurin nan, A kanta ya fara ganin Irin ɗaurin Dukda ba a ƙasar Hausawa ya fara Ganinta ba, Amma akoda yaushe tana sanye cikin Shigar kamala .

Sake ware Idanunsa yayi akan Innocent face ɗinta a Kallon farko da yayi mata ya haddace Surarta.

Tana da tsaho madaidaici, fuskarta oval shape ce mai dauke da dara-daran idanu kwantattu masu yalwataccen eye lashes, girata kamar an zana. Hancinta dai-dai misali, lips dinta sirara masu kalar pink mai haske da yauƙi a koda yaushe, gashin kanta mai cikane kuma mai tsaho don Ko a yanzu da tayi dauri ana iya hango yanda ta tattaresu a baya, tana da dimples a both chicks dinta masu lotsawa koda magana takeyi ballantana kuma ace tayi murmushi, Skin Color ɗinta Rich Black ne, wadanda Ake ma Laqabi da Wankar tarwada a takaice dai Maryam Tanada Madaidaicin kyau daidai Misali.

Cikin Yar ɗaga murya ta kira BaBa

"Baban su!, Ina Kake Gashi fa yazo"

Nan take baba ya Fito daga Dakinshi Dama Yana jiran Kiran yake.

Har yanzu Saleem Bai bar Kallonta ba, yana Mamakin Yanda Take Shareshi Kaman bata taɓa Saninshi ba, koda yike Su duka biyun haka Suka nuna Kaman Basu taɓa sanin juna ba, Kaman Basu taɓa yin Rayuwa a tare ba.

Muryar Baba ne ya Katse mashi Tunaninshi

"Yaro ya sunanka?"

SALEEM yayi gyaran murya yace
"Sunana SALEEM "

"Daga wace Unguwa?"

"Ban san Sunan Unguwar ba, anan Kaduna Muke"

Baba ya jingina kai ya cigaba da cewa

"Su waye Iyayenka?"

"Babana Likita ne"

"Ko zan Iya sanin kai waye a takaice?"

Kallon Mamaki yayi masa, Sannan ya ɗago ya dubi Maryam Dake tsaye a kansu ,tayi folding hannayenta tana Kallonsu, haka mama Duk sun natsu Suna jin ta bakinshi, a hankali Ya saukar dakai yace

"As I said earlier, Ni Sunana Saleem Khamees Nass Shettima, I am a Drunkard, I don't know who my mother is!, and my father hates me, I am a Psychiatric Patient, I have a bad temper, banida alaƙa da Kowace Mace a duniya, yayyina Biyu ne Maza Sannan Kannina Namiji daya Wato Naseer, babu mace A rayuwana Bansan Rayuwa da mace ba, bansan halaccin Da mace ta min A rayuwa ba, na taɓa aure , a ranar na Saki Matar tun Kamin na Shiga ɗakin....!"

Kowa a gurin sakin baki yayi yana kallon saleem, hatta baba rasa mai zaice masa yayi.

Maryam ta sunkuyar da kanta kasa, Tasan Idan saleem Dinda ta sani a Turkish ne zai aika fiyeda Haka ma.

Duban Baba Tayi tace

"I think he's Loyal He has confidence Kace ya Turo Iyayenshi ayi magana asa Rana nan da Sati biyu”

Tayi Maganar trying to Calm her self down Cox Deep down she's dying, So take ayi komai a gama Batareda Mutuncin ta ya taɓu Ba, ta ƙosa ta gama Binciken da Zatayi Saleem Ya bar Rayuwar ta na Har Abada, ta tsane shi bazata Iya misalta Irin tsanar da take masa Ba, har yanzu bata manta Azabar da ya gana mata a Turkish ba, Amma har yanzu jin Kansa ya kasa sa ya nuna Mata fuskar sanayya, itama Haka yanda ya D'auketa a baƙuwa Haka ta dauke shi a baƙo.

Nan fa Baba ya bashi umurnin ya Turo magabatanshi ayi magana in sun Amince Sai a daura Aure nan da Sati biyu.
Maryam Ta riga ta kashe Baba da Kudade , idanunsa Sun Rufe akan Abin duniya Bayaji baya Gani Batareda Ya duba matsalar da za'a iya Samu ba bayan anyi Auren batareda sanin Mahaifin Maryam Ba ya yanke hukunci.

SALEEM na zuwa gida ya Gayama Abba shifa ya samu Mata, kuma Nan da Sati Biyu yake son a daura Auren, da farko daddy Kin yarda Yayi Amma sai Saleem ya Tada Tsiya yace idan aka Hanashi Aure zai sa yar Mutane a Daka ya kashe fitila kuma dole su karɓi haramtacciyar Goro.

Abba najin haka hankalin Sa ya tashi, yasa Salem baya Alwashi a banza Nan take ya tura aka nema ma Saleem Auren Maryam Aka saka Rana Nan da Sati Biyu, sai kace Auren mara Gata.

A sati Daya ZEEYK ya gama hada lefen ƙanwarsa , da komai kama daga Kayan Daki zuwa Gara, hatta Ruwan da zata rinka sha har na tsawon watanni Uku saida aka kawo basu Buƙaci komai Daga ɓangaren Su Saleema ba, haka koda Sun Kawo maida Masu Sukeyi.

Part daya Na Musamman Aka ware masu, Aka gyarashi sosai.

Maryam Da ZEEYK ne kadai Sukasan tarin Alfarmar da Auren nan zai samar masu, Su kadai Suka san Amfanin shigan Maryam Cikin Gidan, Shiyasa basu damu Daddy ya sani ba, A tsakanin su suka shirya Ko mama bata san Dalilin Auren ba, Amma tana sane mahaifinta Baisan da Auren ba kuma ba'a so ya sani.

RANA BATA QARYA......

Yau ranar asabar ce mai cike da tarihi a rayuwar SALEEM, Asabar da maryam bazata ta6a mantawaba.

3rd September, a ranar da aka daura Auren SALEEM NASEER SHETTIMA DA MARYAM SA'EED SANI.

auren da tazo a bazata,babu gayyata babu Event, a cikin Gida akayi shagali , a gidan su Maryam Kou ba'a mayi shagalin Ba, tun safe Mama ta tasata a gaba sai nasiha take mata, a Tunaninta Aurene na Har Abada.

Da yamma ZEEYK ya Raka Ta Gidanta, Shi kaɗai ya rakata Tareda Jaddada Mata mahimmancin aikin da zataje tayi...

Hanun ZEEYK ta rungume tightly ta lumshe ido, hakan yasa ya maida hankalinsa Gabaki ɗaya kanta.

tadago kanta hakan yasa hawayen datake makalewa suka zubo da sauri ZEEYK ya share mata hawayen yana girgiza kai yace

"zaki fara ko?, Ba kin min alƙawarin Bazaki sake zubar da Hawayen ki ba?, bakisan yanzu kinyi girma ba , Ke fa Amarya cw, stop it princess, I'll be visiting you Inshallah"

fadawa tayi jikin ZEEYK din ta kankameshi sosai tasaki kukan da kyau tana shesheka ta yanda ZEEYK ne kadai zai iyaji take taji Mutuwar Mamy ya dawo mata sabuwa gani take kaman Idan ta shiga gidan bazata Daɗe ba itama kasheta Zasuyi kisan Wulaƙanci irin wanda sukayi ma Mamy.

Hannu ZEEYK ya zura ckin aljihunsa yaciro handky dake kamshin Daddadan turarenshi ya share mata hawaye

Ta kalleshi Idanunta Cikeda hawaye tace

"Yaya Meyasa kake Son A binciko komai cikin sauri?"

Shuru yayi mata,shima ji yake kaman Yayi kukan Ko zai ji sauƙin Abinda ya tsaya mishi a zuciya.

"Saboda Kaima ka kusa Tafiya Ko?"

Shiru yayi mata sai a yanzu Hawayen da suka kasa Zubowa suka wanke masa Fuska

Ta haɗiye yawu tana Shessheƙa

"Kaima Tafiya zakayi ka Barni!, Ni kadai, mamy ta tafi, su jannah sun tafi yanzu kai da Ka rage min Kaima tafiya zakayi!"

Sai Kuka mai Ƙarfi ya kwace mata cikin matsanancin kuka ta cigaba da faɗin

“yaya na idan ka mutu nima binka zanyi, Meyasa Zaka tafi ka Barni, Banida kowa fa, Ni kadai zan rage a duniyar nan"

Magana take tana dukanshi da hannu tana kuka sosai.

Sakin Jikinshi yayi tana dukanshi yana kallonta Yanajin kamar zuciyarshi zata tarwatse.

Jiyake inama zai iya yin kuka da yayi yarage rada din dayake ji a zuciya, da zai iya da ya cire ma kansa cutar dake Damunshi,ya rayu da yar Ƙanwarsa.

*AEESH*

Ta dawo weekend ta Iske ana Shirye-shiryen Biki, ita kanta bata san Saleem Zaiyi aure ba, kuma bata san matar ba, Goggoce ta Feɗe Mata Biri har wutsiya ta ƙara da cewa Ai saleem harda kayan Fadar kishiya Yayi mata, Suna gama Jarabawa sukayi Hutu zai Maidata Ɗakinta, Taɓe baki tayi tace

"Goggo Wasu Lokutan Ko In kina wasu abubuwa sai In rasa Wanene mai hankalin Tsakanin ke da Saleem, Wlhy Halinku daya"

Duka Goggo takai Mata ta kauce tana Dariya

"Ja'irar yarinya Allah sarki uwarki na chan Kwance rai a hannun Allah kina nan kina Ja mata Zunubai, maimakon a ganki bisa darduma kina nafilfili kin taho sai washehaƙora kike, wayasani Ko kece kika hana samun sauƙi? ,Zamani ne Ka haifi yaron da zai Kawo karshen Rayuwarka"

Turo baki Aeesh tayi tace "Ni wlh Goggo Shiyasa nace ba fa baxan sake xuwa part dinki ba har abada"

Goggo tace "Toh kar kizo mana ina Ruwa na ada da babu ke Mutuwa nayi?, Dama Zuwanki baya Amfana min Komai sai tarin baƙin Ciki da takaici, Tsabar baƙin Hali ma Irin Naki a duk lokacin da naga Fuskar Ki kafin na kwanta sai nayi Mummunar mafarki"

Aeesh ta tashi rai ba dadi ta fita tana Jan Tsaki, Ashraff da ASHMAN na xaune parlorn AEESH ta tana Kukkumburo baki, tana kallon Ashraf tace

"Ina yini ya Rabeel?"

Yace "Lafiya lau Aeesh yau ba kuka kenan"

Ashman Ya dubeta ta Wutsiyar ido ganin bata ko kalli inda take ba yace

"Ina yini Ihty"

Kunya taji ya kamata, tasa Tafukan Hannu ta rufe Fuskarta tana dariya.

Murmushi Ashman da Rabeel suka saki a lokaci guda

Ashman yace

“tho Meye na Rufe fuska?, kunyata kike ji?”

Cikeda shagwaɓa tace

“kai yaya Ba kai Bane, shine sai ka Gaishe Ni haba sai ka Uhm Huhum...."

Sai ta sake Rufe fuskar ta.

Tasowa yayi ya kamo hannayenta,

"Mujena nuna Miki wani abu"

Daga nan sai suka fita suka bar Rabeel shi kadai sai dariya yake msu.

Suna Fita ya dubeta yace

"Ihty Meyasa Baki gaisheni ba?"

Turo baki tayi tace

"Ba kaine jiya kace zaka kaini yawo shine baka kaini ba?"

"Auw saboda wannan Ne dama?"

Ta gyada Masa kai

"Aikuwa Yanzunnan Zamuje yawo , Muje ki gani"

Waro ido tayi tace

"Kaii yaya Dare yayi fa?"

"Eh Gidana Zamuje musha hira!"

"Matarka fa?"

Ya dage mata gira daya yace

"Kina Tsoron ta ne?"

Da sauri tace
"Eh Wlhy, tunda ka aureta ta zama like a monster to me, She even Blocked me on media Bata ganina bana ganinta"

Yayi Murmushi

"Tho Ki kwantar da hankalin ki bata Nan"

Aeesh batareda tayi wani dogon Tunani ba Tabishi , kai tsaye gidansa suka nufa.

Suna zuwa yace, zo

"mu zagaya gidan kafin ordern da nayi placing su karasa"

tun daga palo suka fara, ɗaya bayan ɗaya yake nuna mata Lunguna da sakunan gidan harda inda Deejah bata sani ba duk ya nuna mata.

Suna Gamawa akayi knocking Ya Buɗe, Kajin da yayi order ne aka kawo masa, dakanshi ya shiga Kitchen ya dafa musu farar Talia dama yayi stew Ɗazu bayan sun dawo daurin Aure.

Da Kanshi ya baje kajin ya yayyanka kanana akan plate, sannan ya miko mata yace

"ga kazar ki nan, amarya"

Tana dariya innocently ta karba sacastically tace

"thank you angona, it looks delicious".

Murmushin Gefen baki yayi...

Tare suka ci abincin, tare kuma suka ci kazar yana Bata Labarin Yanda daurin Auren SALEEM ya gudana ba kowa ya sani ba, sai kace auren Sirri, tana Sauraron shi sai zuba santi takeyi yana yi mata dariyar Mugunta...

Kafin Su Gama cin Abincin tuni Yanayinta ya sauya,ita kanta bazata Ce ga abinda take ji ba, wasu abubuwa Takeji yana Yawo a Jikinta tun daga yatsun kafarta har Tsakar kanta.

Fuskarsa Dauke da Murmushi Ya karaso ya ruko kugunta ta baya ya hada ta da jikinsa, ya dora fuskarsa a wuyanta yana goga mata sajensa.

tsigar jikinta taji yana daɗa tashi, tayi yunƙurin matsawa amma ya maidata, ta lumshe ido ina jin jikinta yana amsawa, a Hankali tace

"Ahky..."
Taja sunan Chan Ƙasan maƙoshi.

a daidai kunnenta yace "uhmm"

Tace "please Stop...it kana sa Ni jin wasu abubuwa..." yace "uhum" ya daga hannu yana shafa cikinta, tayi sauri ta rike hannun,

Murya na rawa tace "Ash....man" ya sake cewa "uhmm"

"Ina jin Wani iri cikin Jikina"

ya kawo fuskarsa dai dai nata, tayi sauri ta rufe idonta tanajin bugun zuciyar sa har cikin kunnenta.

Chak ya D'auketa tafiya da'ita, ta kasa bude idonta ta kwantar da kanta a kirjinsa Jikinta babu inda Baya rawa, tana ji ya bude kofa ya shiga wani guri Ƙamshin Turaren da ta shaƙa ne ya bata Tabbacin Dakin Deejah ne, don Ɗazu har nan suka Shigo.

Ta dan bude idonta ta gansu a dakin Deejah, ta sake rufe idonta

Murya irin ta maye tace "Ashman" yace "uhmm"

Sai kuma duk Sukayi shiru, bai ce komai ba sai da ya kwantar daita akan gado, tayi kokarin tashi ya mayar da ita baya da jikinsa, fuskarsa babu annuri,Bata ankara ba taji fitar zip dinta, tayi saurin rike rigar tana kara zaro ido Gabanta na fa'duwa.

kuka ta fara yi sosai harda sheshsheka, Tasaba jin Feelings Akan Ashman,Amma Nayau yafi ƙarfin ta, a yanda take jinta a yanzu zata iya mutuwa idan bata samu abinda Jikinta ke nema ba

amma Dukda haka bata shirya ba, tsoro take ji sosai, Babu alamar sassauci a fuskar Ashman kuma da alama ya saka mata wani abu ne shima He's high Amma duk da Haka kallon da yake Binta dashi Is very suspicious, abinda take karantawa a idonsa shine yake kara tsorata ta.

Yar dariya yayi yace "kuka kuma? Tun yanzu? Me kike wa kukan ? I did not even Touch you fah"

yay maganar yana dora goshinsa akan nata, yayi tapping Cheeks ɗinta yace
"me kike wa kuka?"

Tace cikin muryar kuka "tsoro nake ji"
yace "tsoron me?"

Da hannu ta nuna shi, ya kara matseta a jikinshi yace "I promise you I will be gentle, It won't hurt you that much"

wani kukan ta kara saki wannan wane irin Masifa ce?, Da gaske Ashman keyi Yana Son Karɓar Mutuncinta da wayau 😭,

Kuka Takeyi sosai yace

"what now? Me kike so kuma?"

Tace "ni ka Cire min Wannan Abin , inajin wasu abubuwa na yawo cikin

Please Login or Register in order to submit comment