Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Wlhy idan Ina Raye Bakida Miji sai UNCLE Haɗaku zanyi tayi har Sai kin Fara Sonshi”

Ohni bintou Yau naga Yarinya da Ƙarfin Hali 🤔

Ko Kallonta Maryam Batayi ba ta zame a ƙasa Ta kife kanta da Cinyoyin ta tana hawaye, Ba kowa ya ja mata wannan dizgin ba sai Yayanta Shine ya kawota Kaduna Ya kuma Nema mata aiki a asibin domin ta binciko masa wasu sirrika, tana kaunar yayanta sosai bai taɓa neman Wata Alfarma a Wajenta ba, wannan Shine na farko, Shiyasa tayi alƙawarin Nemo Masa Komai da Iya karfinta, Tun farkon Fara aikinta a asibitin bata taɓa samun Matsala da Kowa ba sai da Saleem Ya shigo Asibin, a lokacin ne Abubuwa da dama suka fara sauyawa a ratuwarta, domin Kuwa shigowan saleem Cikin Rayuwar ta ne yasa Ta fara Tolerating Wulaƙanci abinda ada Bata Iyawa duk matsayin Mutum Yana mata take taka masa Burki ,Duk Cin mutuncin da yake mata tana Shanyeshi ne kawai don Ta samu ta cika burin Yayanta, a ranar da Ta bar Aiki ma Ta riga ta samo Duk abinda ake buƙata, Shiyasa ta bar aikin , a zahiri ta nuna Rashin Mutuncinsa ne Yasata bar aiki Amma asalin dalilin shine mission Ɗinta da ya cika.

Tun da take saleem Bai taɓa Burge ta ba, Hasalima Tsanarsa takeji matuka , bata taɓa tsanar Dan Adam Yanda ta tsaneshi ba, kuma bata tunanin akwai wani abinda zai Iyayi ma Rayuwarta ya burgeta.

Har Yanzu jin Jinin dake yawo a jikinta take kaman Ruwan maliya Gabaki ɗaya ta ƙagara Ƴayanta yazo suje Renal Unit A ɗebe Jinin Jikinta a sa mata wani.

SALEEM yadade ahakan yana ambaton sunan allah a zuciyarshi da ƙyar ya iya samo kansa.

Tashi yayi ahankali yana dafa kanshi da ke sara masa .

Bude kofar yayi yafita batareda ya rufo kofarba ya ratsa gefensu ya Wuce ko Kallonsu baiyi ba yana jin Saleemerh na masa Godiyan Tsarabar Kayan Marmarin da ya kawo masu, Dukda Bata buɗe ta ga abinda ya kawo ba, Tasan Su ya siyo.

Kamar yasha kwaya haka ya qaraso wajen motarshi ya bude yashiga sannan yarufo ya saka key hannunshi nadan rawa rawa ya tada motar sannan yawani figeta yabar harabar Asibin, yau Ko Office dinsa Bai shiga ba, Ashman Na tsaye Jikin Windownn Office ɗin shi ya ga shigarshi haka fitanshi ma a idonsa.

Girgiza kai yayi a ransa yace
_Yaro yanzu taka wasan zata ta Fara_

Ya zaro waya ya latsa Layin Dr Sabo, yace ya Duba Patients din Saleem ,Bashida Lafiya.

*AREEF*

Tun Randa Idanunsa Suka masa Arba Da Reey Ya rasa Nutsuwansa, Kullum Cikin mafarkinta yake, Tunaninta duk ya addabi Rayuwar sa, sai ya dinga jin yana Son Ganinta, Yana Son Zuwa inda take Amma yana Tsoron Kada Su Sake haduwa Da Aeesh Komai Ya lalace, tunanin Hakan ne yasa ya zama wani iri

A ranar bayan Sallar Azahar suna zaune a dakinsu

Bash na Danne Danne a System kaman Yanda Ya saba, Kamal na Tayashi karanta wasu Mails sun tasa Areef a gaba da tsokana akan wai yaƙi tunkarar wacce yakeso da Saƙon zuciyarsa , ya zauna Sai Azabtar da zuciyarsa yake.

Suna ta tsokanarsa yayi masu banza Sai Danne danne Yake a wayarsa cikin Rauni, yau Kwana Uku kenan Baishaƙi Powder ba, Haka Rabon da yayi Allurar da ya saba Tun Shekaran Jiya , har wani Rawa Jikinsa Keyi ga Damuwan da ya addabi Rayuwarsa, ko ina yaje da batun ayi masa Allura sai ace sai sunga Sa hannun Likita, gashi babu Likitan da ya sani balle ya samu taimako ta wannan Ɓangaren .

Bash ya taɓo kamal cikin tsokana Ya nuna Areef dake kwance Jikinsa na rawa

"See your guy Na igbó he wan take"

Dariya Kamal ya saki

"Omo Charger na Your mate?, shebi I told you say Small pikin no dey do Drug You no listen, Now see wettin you caused For your self, You're Already Addicted ,abege Who go carry you con Take care of you?"

Bash ya janye laptop din Cinyarsa ya zo inda yake, ya dagoshi yana cewa

"Arrow Ga Drugs ta ko ina Saidai In bakason Shaƙa"

Tasowa Areef yayi ,ya Lumshe Idanu Cikin Yanayi irin na masu jin sanyi yace

"Please kamal I need This thing, Zan iya Mutuwa idan ban sha Ba"

Yayi maganar yana wani Kakkame jikin sa haƙoransa na harhaɗewa.

Yanda yayi maganar ne yasa Jikinsu yayi sanyi

Shuru sukayi Cikeda da tausayinsa, kamal ya nisa yace

"Arrow Calm down me zai hana Muje gurin Budurwarka A'isha tayi maka Allurar ,Nasan indai akan Sonda Take maka ne Wannnan Kadan Ne daga Ciki”

Yayi Shuru yana Nazari, Bash ya sake cewa

"Eh Mana , Allah Babe din Nasonshi, Kuma tanada Sauƙin Kai Kawai mu nemota tayi Maka, kaga In ta Amince Shikenan Basai Kudin Mu ya sake Kokawa ba"

Yayi Shuru yana Kallonsu ,yana Tunawa da Irin Cin Mutuncin da yayi mata, yasan Da wuya ta Amince dashi, Amma zai Gwada sa'arsa yayi Amfani da Sonda Take masa Don Samun Cikar Burinsa

"C'mon Johr, Wettin you con dey fear, ABI u forgot say na Shameless Guys we be?"

Inji Bash

"Omo ,let's Go meet MAGA, You no go Loose The thing na 50/50, She go give you True Love Then We go Use am Carry her best Friend away ,ABI no be so"

Murmushi Areef Yayi Ya jinjina kai, ya Gamsu Dasu Lokaci Guda, jikinsa na rawa ya dauko Kwalbar Syrup ya kafe kai ,bai dire ba Saida Ya Tabbatar ya ƙare, take wani Nannauyan bacci yayi awon Gaba dashi .

Yau Medical Surgical Nursing (MED SURG) lecture din da suka yi was very interesting. Sai dai kallo ɗaya zakayi masu Su biyun Ka fahimci Da damuwa a tattare dasu,barin Ma Reey don ita Aeesh dukda akanta abin ya faru Bataji komai Ba.

Tafe Suke A hanyar su Ta komawa Hostel, duk Sunyi Shuru sai tafiya Sukeyi , Chan Sai Reey ta nisa, Ta Kira Sunan Ta

"Na'am "

Aeesh ta Amsa Cikin Sanyi

"Nayi mazari Akan maganar Da kika Gaya Min Ɗazu, Sure I was shocked Shiyasa Na kasa Cewa Komai, But Now Nayi nazari akan Hakan Kinsan Abinda nake zargi?"

Aeesh tace
"A'a Sai Kin Faɗa"

"Kila Da gaske Yake shi din Mijin Ki ne, maybe bayan Saleem ya sakeki an daura muku aure dashi , Kece dai baki sani ba"

Kallonta Aeesh tayi Cikin Rashin fahimta

"Haba Besty Meyasa Zakice haka?,da Anyi hakan Ai da Tuni ya sanar Dani"

"Ya ASHMAN Akwai Mugun Hali na Ɓoye Ɓoye kinsanshi da Zurfin Cikin tsiya,Abinda yafi Wannan Muhimmanci Ma sai Ya ɓoye miki, a gani na don ya ɓoye miki wannan ba abin mamaki bane, Kuma Kinsan Wadanda ya kamata su Sani Ba lallai su gaya Miki ba, ke shaida ce Akan Irin Tsanar da suke Miki"

Lumshe Idanu Aeesh tayi Zuciyarta na Ƙaryata batun Reey

"Wannan Ƙarya ne Besty, Yaya Aash baya So na Koda an Daura Mana Auren Ma tun a gurin Daurin Auren zai Rubuta Min takardar saki"

Tsaki Reey taja Cikin Takaicin ƙaryata ta da Tayi

"Baya Sonki,ya iya saki a ɗakin asibiti ya kulle?"

"Wannan Kuma Daban , Nima Sonshi nake dana biye masa?"

Harara Reey ta wulla mata

"Munafika, Magulmaciya Ki rantse bakya Sonshi"

"Na Rantse Ban taɓa son ya Ash ba, Kawai dai Shaƙuwa ce da Kaunar Jini, Kinsan Ni tunda nake bansan Kowa ba saishi, Shine Sanyin Idaniyata ,Amma nidashi batun Soyayya Babu , Ni Areef nake So"

Banzan Kallo Reey ta watsa mata Cikeda Haushi, tasan Kawarta shashasha ce Amma bata san Cewa She's Dump haka ba sai Yanzu rashin Hankalin Aeesh na bata Haushi Wlhy jifa Wai Areef take so Mutumin da ya wulaƙanta a bainar nasi, ya Wanka Mata Mari Shi take Iƙirarin tana So, Bayan Ga mai Nuna mata So na haƙiƙa a transparent Love da Ko sau daya Kaga Irin Kulawan da Yake bata zaka Gane dimbin Soyayyar da Yake mata.

Takaici ne yasa Reey tayi Shuru don Gani tayi In ta Cigaba Da magana Babu Abin da zai hanata nakadawa Aeesh Na jaki.

Jin Shurun yayi yawa yasa Aeesh tace

"Besty Kinyi shuru"

Cikin Takaici Tace

"Tausayin ki nake ji, ina Tausayin Mijin da zai Auri Second hand , Wanda Wani Ya Gama Lagudawa"

Dukda tasan gaskiya Reey ta fada sai ta samu kanta da jin haushin maganganun da take fada ,ta juyo ta kalli fuskarta taga babu wasa a cikin ta. In a serious tone ta cigaba da cewa

"Duk Namijin da zaki Aura saidai Ya kwashi Raguwan ya Ashman "

Itama Aeesh Cikin Haushi tace

"Eh Din Bakomai , Ai ya saba Gani, Tun ina ƙarama shike min Wank...."

"Enough Abege"

Reey Ta katseta a Fusace

" Ke a ganinki Har wani Abin burgewa ne don Kin sakar ma namiji jikinki yayi Amfani dake?, ba abin Burgewa bane, Abin Kuka ne, Ni na aza Baki San Abinda Kikeyi ba, ashe abin Naki Iskanci ne , Tho ki sani Wlhy kiji tsoron Allah , Ki ƙaddara yarki mace ce Ta biyewa namiji Suka Aikata Abinda ku kuka aikata Zakiji daɗi?, Ki kwatanta Irin Zafinda Zakiji a zuciyar ki da Ƙamshin Azabar Da Allah Zaiyi Muku a nan Duniya, ke shashasha Don Kina jin Abu akansa Sai Ki kasa Controlling Kanki Aduk lokacin da Ya Tado miki da Irin Wannan Abin?, Amma na lura ba Laifin ki bane rashin mafaɗi ne"

Jikin Aeesh ne Ya fara sanyi Hawaye suka Gangaro mata,Dubanta Reey tayi taja Tsaki

"munafuka da zarar An fara magana sai Ki fara kuka, gaskiya dai ɗaya ce da zarar an Gujeta sai ɓata kuma idan Ina tare dake Kin rinƙa jinshi kenan Babu Yanda Kika iya dani dole Kibi gaskiyar ,Wlhy Wlhy A'isha Muhammad Kiji tsoron Allah ,Idan Ma sonsa Kike ki gaya Masa Tun wuri ayi Aurenku kafin ku aikata ba daidai ba"

Haka Reey ta cigaba da Mata Fada kamar Uwarta tana Kuka ta tasa keyarta har hostel.

Ranar haka suka wuni jikinsu da zuciya su babu dadi. Aeesh na tunanin bata kyauta ba data sake mishi Yayi yanda Yaso da Ita, kuma deep inside her batajin Zata iya Kiyaye Abinda Zai sa ta koma Gareshi saboda Tsakanin Jiya da yau ji tayi Abin da takeji akansa ya ninku

Ashman Ya kirata bayan Sun Dawo yafi a ƙirga, Amma Reey ta kasa ta tsare ta hanata sakat tace idan Ta sake tayi Picking calls Din sa Saita Yi Mugun bata mamaki, Ya zama Dole ta koyi yin Nesa Dashi Tun kan abin ya Habbaka.

*Ashman*

Yau Surgeries Sukayi Sosai bai zauna ba ,Sai kusan Hudu na yamma suka Fito, A lokacin ne yayita kiran Aeesh amma bata daga ba ,yayi Tunanin ƙila suna lectures ne Shiyasa Ya Kyaleta da cewar Zuwa anjima zai sake gwada Kiran.

Tarin misscalls dinda ya Gani a wayarsa ce Ya bashi mamaki, Na Abban KHADEEJAH Yafi yawa, Mamaki ne ya Kamashi Tho Kiran me Babanta ke masa?, me zaiyi mai?, Kodai Deejah takai ƙararsa ne? , Lallai Da taga Hauka.

Bin kiran Yayi, bugu ɗaya Ya daga da sallama a bakinsa, Amsa Sallamar yayi ya dora da cewa

"Baba Naga Miss calls ne sir Allah yasa Lafiya"

"Eh Lafiya ,kawai dai ina Son Ganinka ne a gida na, If possible ma kazo yanzu"

''ok No problem Sir"

Daga nan suka kashe wayar bai kawo komai a ranshi ba, yayi Sallah sannnan Ya kama Hanya,Rabonsa Da gidanshi tun shekaran Jiya , Deejah bata Ranshi Shiyasa bai damu da yasan Halin Da take ciki ba.

Ashman kam koda ya shiga gidan, bayan yayi gaisuwar girmamawa ga Alhaji Umar sai ya nuna masa wajen zama.


Hannu Dr Umar ya bashi cikin musabaha suka sake gaisawa, dukda dai Ashman na nuna jin kunyar haka ɗin a matsayin Su na surikai.


“Dr kasan me yasa na kiraka kuwa?”.


“A'a Sir”. ‘Ashman ya faɗa cikin kaɗa kai.


Zama sosai DR ya gyara, ya fara magana idanunsa akan ASHMAN

"Wato nayi Takaici da Dana sanin Baka auren Ɗiyata Alhalin baka san Darajar ta ba ,ashe dama Ba Sonta kakeyi ba ka amince na aura maka ita?"

Ashman da idonsa ya kaɗa ya yi jazur ya ɗago kansa yana Dubansa.


Murmushi Dr Umar yayi na takaici yana cigaba da faɗin,

“Abun mamaki yau Watanni Kusan hudu da Auren ku, Amma ko Hannunta baka taɓa Riƙewa ba"

Cikin mamaki Ashman Ya kada Idanunsa Akanshi, sannan Ya matse idanunsa tare da rumtse hannu, muryarsa a matuƙar kausashe yace, .

“Sir ita deejahn ce ta gaya Maka hakan?"

Dr Umar yayi Murmushin takaici idonsa akan Ashman.

"Eh a halin yanzu Ma tana Gidana"

Zazzafan numfashi Ashman ya sauke yana miƙewa idonsa a matuƙar jazur tamkar ya haɗiyi wuta, yayi ma Dr Umar wani irin Kallo.

"Tho ka gaya Mata ta cigaba da zama a gidan Naka har sai Randa Ta koyi Riƙe Sirrin Mijinta"

Daga nan Ya sa kai ya fice daga Gidan Gaba daya ransa a ɓace.

Har ya dau hanyar Gidanshi sai ya samu Kansa Da Biyawa ta Gidansu haka kawai yaji yana Son Ganin Yar ƙanwarsa Ƙawwama rabon da ya ganta Har ya manta.

Bai yadda Ya fito da ɓacin ran Deejah ba, a bakin Ƙofan Gidan Ya bar Bacin Ran.

Shigarsa yyi, Ganin Yan uwansa Ta ko ina ya saka zuciyarsa tsitstsinkewa, musamman da yayi tozali da tilon ƙanwarsa, He really Missed them, Dukda Basua Sonshi But Yaji Ba daɗi Rashin Zumuncinsu.

Kai tsaye Part din Mazan Gidan Ya nufa Shi Saleem yana zaune kansa a ƙasa saboda ciwon da yake masa, baima san da shigowar Ashman ɗinba.

Ashraff ne ya fito daga Dakinshi yana zuba Ƙamshi Duk gidan Ashraff ya fi su hasken fata, fari ne tas Amma da kadan yafi Ashman, A kyau kuwa ba daga nan Ba ,Kamanninsu da Ashman kaman An tsaga Kara haka halayyarsu iri daya saidai Ashraff yanada Masifa Shi kuma Ashman Akwai Iya Dunƙule zance ,Ga Zuciya Da jan Aji. Ashraff Dan gayu ne na ajin karshe, ballantana kuma yau kamar fitar musamman za'ayi. Shirt da wando a jikinsa Coffee Shirt Mai Layi Layi sai Baƙar wando, kansa babu hula sai gyaran da gashin da ya sha sai daukan ido yake, takalminsa da agogon hannunsa kadai abin kallo ne.

Ya karaso gareshi idonsa a kan Ashman haƙora a washe

''A'Ah Ango Daga ina?"

Harararshi Ashman yayi, yana jinjina tsananin Kamanninsu da Ashraf

"Daga Sama''

"Tsuntsu ka zama"

"No Kaza Nake, Kai Gauro ina zuwa?"

Ashman ya fada yana Kare masa Kallo ganin yasha wanka.

"Me ya shafi kaza Da inda xani ina Ruwanka?"

Ashman Ya ɗago fuskarsa ya Dubeshi Da kallon tuhuma yace

"Kadai bi A hankali don Matan Yanzu basu iya sace zuciya ba, in sun Sace zuciyar basu Barinshi a kyakkyawar Ma'adana, sai Sun sossoke shi da Wuƙa tukunna, sai Su dawo kuna manejin Yankakkkun Zukata"

Ya ƙare maganar Da duban saleem da Ke zaune ya Dafe kanshi, Duban Inda Ashman Ya kalla yayi yana Dariya , sai a yanzu ya lura da Saleem yace

"Meke damun Lititan Mata?, kodai babu Lafiya ne?"

Ashman ya Kauda Fuska daga kallon salem yace

"His heart was Bleeding, da Alama Wata ce ta Sace Masa Zuciya "

SALEEM najinsu yayi kaman Baisan Suna ji ba, But deep down He's dying.

Ashraff ya saki Baki yana kallon Su cikin mamaki yace

"Wacece wannan Da tsautsayi ya faɗa Mata?"

"Wata Renal Nurse ce a asibina"

Saleem Duk da son danne fushinsa da yaketa ƙoƙarin yi hakan ya gagara, sai da ya fallasa Kanshi, ɗagowa yayi A Fusace ya dubesu kaman Zaiyi magana sai Kuma Ya kauda kai sakamakon Sarawan da kansa Yayi masa.

Ashman ya Taɓe baki, ɗakin yayi tsit kaman ruwa ya Cinyesu, Idan Zaka Kasa Kunne sosai Sai ka jiyo Hucin Saleem dake fita cikin zafi.

Cikin Murmushi Ashraff ya zubama Ashman ido yana buƙatar ƙarin bayani daga garesa, amma abin mamaki tamkarma baisan yana yi ba, ya kauda Kai.

Hakanne ya saka Ashraff taɓashi kaɗan.

"Man Gist me, Da gaske Soyayya ce ta maida Saleem Haka?"

Ashman ya ɗan ɗago ya kalli Ashraff da ya Kafeshi da Idanu

"Bro Kana Ganin yanda Ya susuce ya Rasa Nutsuwansa, ya zama Wani iri, He's Slowly Loosing His Self, Ya Zama Tamkar mace"

Ashman ya fada Cikeda Son Fusata Saleem.

Aikam ba Ƙaramin fusata Saleem Yayi ba yau Har shi za'a duba A kwatantashi da Mace?, A rasa me za'a dame za'a Hadashi Sai mace?, Zuciyarsa na tafarfasa da ƙuna, tare dajin tsanar yayan nashi mai tsananin Gaske.

Ashman Ba ma'abocin bada Labari bane, Amma Saboda ya fusata Saleem Sai suka Sami wuri Shida Ashraff , yana Bashi labarin yanda Saleem ya Ruɗe Akan Maryam, Banda dariya babu Abinda Rabeel keyi, Cikeda jin daɗin Moment dinda Suke Sharing da dan uwan haihuwarsa, Kaf Rayuwarsa zai iya ƙirga iya adadin da suka taba zama Sukayi Hira shida Dan uwan nasa, Ashman Bai bar komai ba saida Ya bashi Labarin komai wanda hakan Ba ƙaramin Tunzura Saleem yayi ba.

Sosai Kalaman Shi ke dukanshi, wannan shine karo na biyu da Ashman ya tabbatar masa Da shi mai rauni ne, Amma wannan Karon Ya yarda dashi, Dukda yana Ƙoƙarin kauda Gaskiyar Karayar da Ya keyi akan Mace ne .

Shiyasa
zuciyarsa tayo sama , idanunsa Suka rufe Kalamansu sun gama Makantar dashi sun Kuma kurmantar dashi bayaji baya Gani.

A fusace ya zaro wuƙar dake jikin Apple dake kan Dining ya nuna Ashman da ita, dan zuciyarsa a maƙoshi take, shiyyasa sam yaƙi kula su tun farko.

Ashraff baiyi zaton da gaske Saleem yake ba ,Shiyasa ya Tsaya yana Kallonsu ,saida yaga saleem ya daga Wuƙar zai daɓa masa a ciki.

A gigice ya hankaɗa Ashman gefe sukar da Saleem yayi ya sami bango.

Damkar hannunsa Ashraff yayi da qarfi yayi cilli da wuƙar.

Kiciniyar kwace hannunshi yake cikin rashin Ƙarfi hawayen na Taruwa a idanunsa

"Ka cikani you Brat yau Saina nuna maka iyakan ka!"

Yafada cikin cracked voice.

Tsawa Ashraf ya daka masa Ya rirriƙeshi da ƙarfi, da wani irin Zafi yake jin Zuciyarsa Na Tafasa yana jin Ayau babu mai Hanashi Kashe Ashman Kawai ya huta, akoda yaushe shike sashi Jin Rauni akan Mace, da ƙarfinsa ya kwace riƙon da Rabeel yayi masa

"Leave me alone!" Yafada da iya Ƙarfinsa daidai lokacin da Zuciyarsa tayi wani irin Bugawar da ta sakar masa Kasala.

Fashewa yayi da kuka kaman Ƙaramin Yaro

Sulalewa yayi ya zauna qasa sannan ya cusa kansa tsakiyar kaffafunsa ya Saki wani marayan Kuka mai sauti.

They were shocked , this's Unbelievable da kallon mamaki suka bishi jikinsu duk yayi sanyi,Saleem ne ke kuka?

ASHMAN dukda ya cika da mamakin ganin Saleem na kuka Amma baiji tausayinsa ba ko kadan, yasan Kukan Da yakeyi was Full of Emotions , Koba Komai Burinshi ya cika ya Tunzura shi, kuma Ya tunzuru, Next time he'll get up and be Strong.

Yana Murmushi ya Fice daga Side din, ya Koma Part din su Inna Saude ya Gaishe su daga Nan ya fice daga Gidan Gabaki ɗaya ya nufo gidanshi.

Yana isa Ya baje akan gado, wani Nannauyan bacci yayi awon Gaba dashi..

Ring ɗin wayarsa ne ya farkar da shi da ga nannauyan barcin da yay nisa a ciki, ya janye bargon da ya rufa da ga kansa da ƙyar tare da miƙa hannu saman bed side drawer ya ɗauki ƙaramar wayarsa da ke vibrating.

Ba tare da ya duba wanene ba ya ɗaga kawai ya saka a kunne yana sake maida idanunsa ya lumshe. Tsawon wasu yan Seconds yana sauraren mai maganar da ga can, kafin ya furta "ke kika sani" cikin nutsatstsiyar muryarsa da ke gauraye da barci.

Ƙarƙashin filon ya tura wayar yana sake juya kwanciyarsa hankali kwance, sai faman ɓata fuska yake na jin takaicin katse masa barci da Deejah tayi, Wai a takira ne don Ta Rokeshi yayi haƙuri zata Dawo, Tana Kan hanya ne.

Ture bargon yayi ya fito, ya fada Ban daki yayi wanka, Sannan Ya fada KITCHEN ya girka Abinda zai sa a cikinsa.

Haka nan Ya uni yau cikin FarinCiki, Dukda abubuwa da dama Sunso su ɓata masa Rai, Amma da zarar ya Tuna Cheerful moment Ɗinshi na jiya sai Ya nemi Bacin Ran ya rasa.

Da yamma Deejah ta dawo, Sai rokonshi take Akan ya yafe mata bazata sake yin yaji ba, Ko a jikinsa baima san tanayi ba,

Da daddare bayan ya dawo daga Sallar Isha'i, ya kimtsa cikin shirin bacci baƙar jallabiyarsa mai dogon hannu ce a jikinsa,

Kai tsaye ɗakin Deejah Ashman ya shiga, Abinda Bai Taɓa attempting ba tun Ranar da aka Kawo masa ita a matsayin Amarya.

juyowa tayi ta ɗan kallesa da mamaki ta ɗauke ido.

Yabi dakin Da kallo kafin ya kai dubansa gareta, kallon tausayi yayi mata sannan ya cigaba da takowa cikin ɗakin, jikin bangon ya jingina tare da harɗe ƙafafunsa waje guda ya tura duka hannunsa a aljihun jallabiyar.

*AEESH*

Gabaki ɗaya ta kasa nutsuwa ,har dare bataji Muryar yayanta ba, Gashi Reey ta kwace wayar ta hanata ganawa da kowa.

Saida Ta faki idonta bayan tayi bacci ta dau wayan, ta fito daga Dakin ta Dannawa Ashman Kira.

Alokacin Har ya haye Gado ya Shige bargo yana Latsa waya, Deejah na zaune kusa dashi ta tsare shi da Kallon mamaki, so take ta kwanta, Amma tana Tsoron kwanciya kusa dashi.

Tana fara wani ringing din ya dauka

"Assalamu Alaikum"

Sanyayyen Muryarta ta daki Dodon Kunnensa ,Baisan sanda ya saki Sihirtaccen Murmushin da Baisan Yayi ba ya Amsa Sallamar sannan Ya ɗora Da cewa

"Ikon Allah yanzu fa nake shirin kiranki"

Itama Murmushi ta saki,Cikeda Jin dadi ta Rungume Pillow

"Allah Sarki ai ana Haka idan Munyi tunani iri ɗaya Lokaci guda"

Ta faɗi hakan Feeling so week

"Lafiyan Ki ƙalau kuwa?"

Ahankali ta bude bakinta trying very hard to control her emotion tace

"Eh"

"Kin tabbata?"

"Eh"

"Tho Amma ya Naji muryarki wani iri?, ko wani abu akayi miki?"

"A'ah yayana, Nima bansan Abinda Ke damuna ba"

Kasa jurewa tayi ta fashe da kuka ,voice ɗinsa nasata tajin wani iri emotional feeling na tasomata daga Chan qasan zuciyarta yna zagaye ko ina na jikinta.

Shima hakan take agareshi, kafe kunne yayi heavy Emotions na Taso masa acikin zuciyarshi.

Shuru yayi yana Sauraron Shessheƙar ta Duk Shessheƙan ta jinshi yake har cikin Jinin jikinshi cikin sigar Rarrashi yacs

"C'mon Baby Stop crying, Come over Lemme Hug you"

Shiru tayi bugun zuciyarta na qaruwa sosai, she's feeling somehow, tanajin wani iri sosai, Kukanta ya ƙaru.

Duban sa ya kai kan Deejah da ta tsareshi da Idanu tana Huci da Alama tana sauraron conversation dinsu,ko Bai Fada ba Tasan da Aeesh yake waya,don ita kadaice macen Dayake kira da suna baby

Shiru yayi yana Sauraron kukanta na wasu mintuna sannan ahankali cikin Muryar da ba tasa ba ya ce

"Your lips look so lonely, would they like to meet mine?"

Wani yarrr taji ya ratsa Jinin jikin ta , ta Lumshe idanu ta saki Kasallalliyar Numfashi

At the same Time, take mutuwa ya fado mata a rai, Yanzu da zata Mutu fa ta tabbatar wuta zataje.

Tunowa tayi da cewar annabi saw da yake cewa *_'kada ku kusanci zina'_* sai Ta tuna abinda ya faru a tsakanin su, Kadan Ya rage ya Rabata Da Budurcinta

Nan take wani irin tsoron Allah ya fara shigarta, kukanta ya tsananta, cikin kukan ta fara ambaton astagfirullah, astagfirullah har sai da muryarta ta fara neman dasashewa, banda Dariya Babu Abinda Ashman Keyi, Duk Deejah na daga Zaune tana Jinsa, Zuciyarta kaman tayi bindiga, sai yanzu ta tabbatar ma Kanta cewa bata kai matsayin ya haɗa jiki da Ita ba, tunda Gashi a gabanta yake neman Sumbatar Wata ta waya

Ita kanta Aeesh bata jin me take cewa, Duk Addu'an Da ta fado bakinta Takeyi. Wani sanyin Imani ne taji yana Ratsata

Cikin kuka ta sa hannuna ta shafa fuskarta tana goge hawayenta, tunda ta mallaki hankali nta babu wani namijin daya taba koda rike hannunta ne, Ashman kadai taba ma wannan damar, bata yarda namiji yaga Al'auran ta ba , Kullum cikin shiga Ta kamala take yawo, but Ashman has kissed her kuma ba shine abinda yafi sata regretting ba kamar the fact that he Almost Drive her Dignity Away from from her.

A bayyane take cewa

_I should have control myself but I can't, I am too weak, and soft_








Tho Amaryar Ƙauye kauce min Da gani😎

Nayi Gabas 🚶🏻‍♀️
Bintou ✍🏼

26th Aug
[10/3, 9:56 PM] Solace: *WUƘA A ZUCIYA*

_BLEEDING HEARTS_


*033*


A bayyane take cewa

_I should have control myself but I can't, I am too weak, and soft_

Ya datse ya tsaya yana kallon wayar

Please Login or Register in order to submit comment