Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Sharri, ya sake ciro wani Galan, ya ba Ammie yace kada tayi wasa da amfani dashi.

Ya sake fiddo wata yar Kwalbar mai, yace

"wannan kuma herbal Jelly ne mai ɗauke da , Man Babba, Man Ridi, Man Hulba, Man Zaitun, Man tafarnuwa, Garin Luban, and co da ayatu sshifa' Wannan na Ashman ne, shi ne zai saka mishi nutsuwa ya wargaza Duk sharrin mai sharri, ya kora Aljannu"

Sai kuma Ya haɗa masu da Wani turare yace su dinga ƙonawa da Garwashi, jinnu basua Son hayakin ya kuma Umurce shi da yasa ana Saukar Alkurani ayi tawassali da Karatuni na samun shifa'a, ya Bama Aeeesh nata maganin wanda yafi na Aashman Karfi.

Ammie tayi Godiya Sosai, tace "InshaAllah za'ayi yanda kace Mallam

Suna Komawa Gida Suka fara Amfani dashi, babu Kakkautawa, da turaren nan suka kwana, hayakin Na shawagi a dakin.

tabbas Sihiri Gaskiya ce kuma Magani da Alƙur'ani Waraka ce, Haka yau Aeesh ta tashi cikin dare kanta na juyawa sakamakon Hayakin da take shaka, tana ganin jiri, ta dafe kai ta bude idonta a hankali Ashman ne a kusa da ita Amma gani tayi Fuskar ta ta sauya ta koma na Aareef zumbur ta Miƙe, gani tayi dakin na juya mata.

. Sallalami ta fara, Yi da karanta inalillahi wa ina ilaihir rajiun da karfi, muryarta ya tayarda Aash ya tashi zaune yana Binta da kallo, ta wani rike kanta sai addu'a take maimaitawa.

Ihty Are You okay...?

Ji tayi Kaman Muryar Aareef ne keyi mata gizo da cewa

"Baby are you okay"

A tsorace ta sauka a kan gadon ya nufota da fadin Lafiya, amma Sai ji tayi Muryar Aareef na amsa kowwa a kunnenta.

Kuka ta fashe dashi cikin tsoro

"Sadauki Me nayi maka?, What have i done to You nan ma biyoni kayi?"

Da mamaki Ashman Ya nufota yana ƙoƙarin Riketa, ta Ƙwala kara

"Ka daina Bina....ka daina Bina bana so... Banaso"

"Ihty Meke damunki innalillahi Wainnailayhirraji'un"

Kuka ta fashe dashi

"Aareef Don Allah ka ƙyale kurwata ta huta ,ka fita a zuciyata, ka Fita Rayuwata "

Ta faɗa tanayin baya yayinda kanta ke wani irin juyawa ,tana ganin Dishi Dishi Daga nan Duhu ya Rufe Idonta, ta faɗi ƙasa Sumammiya, a ruɗe Ashman Ya dauko ruwan addu'an don Ya yayyafa mata ,Amma sai me?, Gani yayi Ruwan Ya koma Ja kaman jini.

Yayi saurin Dire Robar a tsorace yana Zaro ido jikinsa duk rawa yake, wani farin kumfa ya ga yana Fita ta Gefen Bakinta, Hankalin shi duk ya tashi Ya rasa ya Zaiyi, Rungumo ta yayi Yana Tofa Mata duk Addu'ar da tazo bakinta, idanunsa Sunyi jazur, so yake hawaye su Zubo ko ya samu natsuwa.

Gani yayi Ruwan na Komawa Fari Yana chanza kala izuwa Jaa Kalanshi na Masa siddabaru, anan Hankalinsa ya dawo jikinsa ya raya a Zuciyarsa Ai wannan Ruwan Addu'a ne babu Wani mara tsarki Da ya isa ya taɓa, Wannan kadanne daga Siddabarun maƙiya, Nan take ya dau Gorar with courage Hannunsa na rawa yayi Addu'a ya bude murfin, ya zuba yayyafa mata ruwan a daidai Lokacin Alhaji Faisal Ya gana Ba Yaransa Umurni Ya ɗauko Masa Sureey sannan Su kashe ƴar Aeesh.

_*Maryam*_ _Saleem_

Wani Zafaffen k'auna sukeyi wa junan su, cikin kwanakin nan, Saleem So yake ya maida Maryam yar Gata kota halin Yaya,Dukda Bata bashi damar Hakan Ba, Sosai Take ƙoƙarin ɓoye sonda take masa Ta nuna Masa baya Gabanta Don Yaji haushi Yayi feeling guilty akan ɗauko tq da yayi a kasuwa, da kin Maidata gida taga mama , amma ance so baya Ɓoyuwa da zarar ta ɓoye Da kansa yake fitowa, Saleem ya koya ma Maryam yanda zata so shi, tun tana jan ajinta har ta daina, don Baya bari tana Komai, a tare suke yin Komai

Zaune yake a kan kujera, Maryam na ƙasa Yana yamutsa mata gashin kanta wai a dole kitso yake mata, suna Kallon Korean Drama The Heirs Season 4, idanun Maryam Nakan TVn Amma Hankalinta baya Kan kallon Yayi pausing Scene din Yana Dubanta, hakan yasa ta sauke kai hawaye na daɗa taruwa a idanunta, ya zame ya zauna a ƙasa kusa da ita yana Dubanta, ita kou taki yarda su haɗa ido, hannu yasa shafo kuncinta, ta Lumshe ido Hawaye Suka Sauko Mata

"Baby Kuka Kuma?, A gidana?"

Sake shagwaɓewa tayi Hawaye suka Cigaba Da reto a Fuskar ta, cikin Ƙanƙanin lokaci ta ruɗarda shalelen Abba, ya shiga Tambayanta me ya faru, saida tayi mai Isarta Sannan Ta dakata Tana share sauran kwallar, shuru yayi yana Kallonta ya ma rasa me zai ce don Sosai Kukanta ya bashi mamaki cikin Turo baki tace

”ni ka maidani gidan Mu, ina son Inga mama na, Ina so Inje prison Inga baba na, Ina so Inga Dana"


Ya Rungumota jikinshi Yana Rarrashi

"Kiyi Haƙuri mostang na tuba na shafa'a ne, idan Ina tareda ke mantawa nake da kowa, I just want to Be with You, only You....always And forever"

Sake kwantar dakanta tayi a ƙirjinshi tana matsar ƙwallah.

"yanzu dai ya isa haka let's get ready Muje Wajen Daddy Sannan Muje Gidan Mama Daga nan sai mu wuce Gida mu dauko Ayyan "

Dadi Ya lulluɓeta bata san Lokacin da ta sake ƙanƙame shi ba tana Murna, ko me ta tuna Oho sai ta taɓe baki tana hararar Ƙirjinsa Murmushi yayi yana ɗan shafa gemunsa a hankali yace

"Tell me you Love me"

Ta kauda Kai , fuskar ta Amurtuƙe ,kallonta yayi yaji gabansa ya fadi, Kenan bata sonshi

Ya girgiza kansa a sanyaye, annurin fuskar sa na Gushewa

A hankali ya furta

"Now I know I'm Alone"

Ya Mike zai tafi, ta riƙo hannunsa idanunta cikeda hawaye

"You are not alone Saleem, I am here with you, you're in my heart and You will always be there forever until the end of time."

Wani dadi yaji, Amma ai duk wannan Shirme ne tunda bazata ce tana sonsa ba, Hannunsa ta murza a hankali, ta datse idanunta tana ƙoƙarin hana hawayenta gangarowa, tayi Shuru , ganin tayi Shuru yasa yace


"You don't Want To be with Me, I feel like am forcing You, am sorry For jumping Into Ur peace 💔 am sorry For marrying You again"

Tayi saurin katseshi da

"Wallahi I want to be with you, I can't do without You , you are my forever"

Wani farinciki ya lulluɓeshi, Dama Tana sonshi take wahalar dashi?, Jin haka ya sa yace bari ya ɗan ja ajinsa ya sake tsuke fuska

Ji tayi ta Bama kanta haushi, meyasa ta bishi, mai yasa bata barshi yayita fushinsa ba?,tanada Pride Amma akanshi Zata iya sauke shi, tana Son Ƙyaleshi Amma Bazata iya ba, ta dube fuskar sa, ya wani daure fuskarsa tamau, _Samun Wuri_ 😠😡😑

"A lokacin da yayana ya rasu, na cire rai da Duniyar nan Gabaki ɗaya, i feel like I don't wanna leave anymore,but I don't know how you do it, you make me want to live forever!".....

Tayi shuru tana Feeling Somehow, ta kasa Sakin Hannunsa muryarta chan ƙasa tace

"I am not Good in expressing Myself"

ta sausauta murya tace

"Ina Sonka Saleem Ina sonka Nasty Doctor, I hate my love for You for a long time, I hate my self loving You without You knowing , ban damu da tsawon Lokacin da na dauka kafin In sanar dake ba, i love only you I want to be with you"


Ta wani kwantar da murya sai tona sirrin Zuciyarta take, Sai kace ba Maryam ba, Queen Of pride.





_Naso na gama Littafin nan a wannan page ɗin, I wish I could do so, but I have Alot To cover, Bazai yiwu na fara Labarin Tiryan Tiryan na takaita shi a ƙarshe ba✍🏼, Hope zaku min Uzuri 😘😍_


Thanks For Understanding
Bintou loves You.

Nayi Gabas 🚶🏽‍♀️


18th Jan ✍️
[1/19, 08:38] Bintou Abdul: _*WUƘA A ZUCIYA*_
_(BLEEDING HEARTS)_

*069*

Kasa magana yayi saboda wani yanayi da ya shige shi, Farinciki ya lulluɓeshi, Jikinsa yayi sanyi Wasu Hawaye suka Sauko masa ,yasan Bai kyauta mata ba , ya daukota a Mall ya Kawota gidanshi , ya Hanata zuwa gida But she love him Bata duba wannan ba, ganin hawayen ta sunki tsayawa yasa ya ruɗe ya Shiga goge mata , cikin sanyin murya mai cikeda shauƙi yace

"I want to steal this moment from my life, store and preserve it in my memory to make it last forever... till eternity."

Tayi Murmushi ta shafo fuskar sa, ya Turo baki yana Shafa cikinsa
Ta ɗage gira Ɗaya

"What Again...?

"I'm hungry"
Ya faɗa kaman ƙaramin Yaro,
Juyawa tayi zata nufi Kitchen da cewa

"Ohhsh na shafa'a , its time for lunch"

ya yamutsa fuskar sa yace

"No no no,kawai ki shirya muje "

da sauri tace

"Give me 15 minutes i'll just get ready"
Murmushi yayi yace

"Bari In shirya nima"
Ya tafi

Ta bishi da ido tana mamakin shi, duk ya bi ya sauya, sai nuna Kulawanshi yake ƙarara a kanta, ta shige nata dakin Don ta kimtsa.

Babu jimawa duk suka fito cikin Matching outfit, yau Shigan ƙananan kaya yayi Yana Sanye yake cikin casual wear Royal Blue shirt ya Dan Kamashi Kadan har Kana iya hango Shatin packs ɗinsa, da tracksuit trouser all Blue da ratsin baƙi, Fuskar sa nanne da da farar transparent eye glasses, ya juya blue facing cap ɗinsa tabaya , itama sanye take Cikin abaya dark Blue Mai ɗauke da adon Black Diamond Stones sai kyalli suke, tayi rolling da gyale shi.

Bintou's Pizza suka fara nufa, Sukayi Order abinci suka ci a mota ,saboda bata ƙaunar cin abinci In public daga nan suka kama hanyar Gidan Mama, tana ganinsu duk sun tsura mata ido she was Expressionless batareda tace komai ba, Maryam Tasan tayi laifi don haka ta saukar dakai shima Saleem galala yake kallonta bata chanza hali ba yanzu ,tana nan a matsayin moster da ya fara gani a lokacin da ya fara Zuwa gidansu Maryam.

Maryam ta gaidata kanta a ƙasa kaman Wacce tayiwa Sarki ƙarya.

Sai a sannan Mama ta motsa tana taɓe baki tace

"Tho fa ke kuma daga ina?ina kika samo ƙatoton Gardin bayanki?"

Maryam Ta Rungumeta tana Murmushi

"C'mon Mama yanzu Baki gane mu ba?


""Ke Ni dalla sake Ni Karki kadani, ba gaki Ja'ira rasa kunya kazar birni ba?, ke gaki Yar daɗi miji Daga cewa zaki kasuwa Sai dai naji kin tare Gidan Miji Babu Aji babu komai, taya Auren Zaiyi Albarka ,kai Kuma lafiya?, Ka wani Kafeni da Ido "

Ta faɗa tana Galla Masa harara,Sai kuma ta riƙe haɓa

",ikon Allah kai kuma haka ka koma zama Kato kaman Dan dambe?"

Kunya ta ishe maryam, Saleem yaja dan guntun tsaki a hankali yace

"She'll never change she hate me"

Ta dubi Maryam Tace

"Fassara Min Me yace"

Maryam Tace

"Cewa yayi Ina wuni "


"Eh maidani yar iska don na nuna Bana fahimtar yare zaki Min taaddanci?"

Maryam Ta juya idonta tanaa dariya, mama ta bita da kallo tana Kallon cikin Idanunta, sannan ta tafa hannu

"Nikam na shiga Uku me nake gani?,Mero kodai ciki gareki....?, Nikam Da na shiga Uku daga fita Unguwa sai Ki dawo da ciki?"

Maryam ta Zaro ido

"Mama Rufa min Asiri"

Shi ma Saleem kallon ta yayi ya saki Murmushi, Tsaye sukayi Maryam Na tuna Rayuwarta a gidan ko ina na gidan dauke da Hotunan Da ZEEYK ya ɗauka ba Tsuntsaye da sararin samaniya, duk sunyi kyau da ka gani zaka gane Wannan snap din professional Photographer ne.

Mama sai Tsokanar Saleem take wai yayi ƙato, ya fice mata a gida gashi sun kasa zama kaman Wadanda akayiwa dukan tsiya akace su biya tara, Maryam gajiya tayi da mitar mama akan Saleem tace

"Na shiga Uku mama, wai ina Ruwanki?"

"Zaki sani ne, ki je ya danneki hanjinki ya fito ta baki ,babu Mai taimaka mikii"

Maryam tace

"Ba Komai ai miji na ne, Kuma ba wani Girma ya fini bai "

"Iyye kin ganki Kuwa? ,Iyakarki in kinyi Wuta ki tsaya a iya ƙirjinsa, a Fadi kuwa sai ya rabaki Biyu baki kai rabin ki ba"

"Kaiii mama Kedai kice mutumin naki yau Ya tsorata ki,My squirrel 🐿 matso mu gwada tsayi da girman jiki"

Ya matso suka gwada, iyakarta Chest ɗinsa ta juya ta dubeshi Kut ita kanta Batayi zaton Haka Yake da Girma ba, ga tsayi, duk tsayinta ya kerata, a hankali ta ƙare masa Kallo ba wani fadi gareshi ba ,but Packs Sunyi occupying Chest ɗinta

Mama tace

"Kin Gani ko?, Ba irin Wannan Ake like mawa ba, ni ku tashi mn akai karka tsotse min Jini"

Saleem Yaja Guntun Tsaki

"This woman is annoying"

Ya sunkuya zai zauna


"Ni tashi min akan kujera zauna chan Kan Tabarmar yan gayu"

Bai tanka ta ba ya zauna kan kujerar yana jan tsaki, Maryam tace

"Mama kin fa takura ma wannan Mijin Nawa , don Kinga yau Bai Kulaki bane?, Wallahi kiji tsoron tankawanshi"

Wayarsa ya fiddo cikin Aljihunsa Yana latsawa Not saying a word, har ta ƙarashi surutanta, tasa Saleemah ta dauko musu Ruwa , ta shimfida Masu Bankararrun kaji tace kada Saleem ya Saki ya taɓa Mata kaza, duban Kajin yayi ta wutsiyar ido Yasha Spices Ga Onions everywhere ,ya taɓe Baki yasan da Gangar Mama tasa Onions don Maryam Ta basu labarin Baya son Albasa.


Wani Yawu ya haɗiye, a ransa yace yau ba Albasa ba ko Tafarnuwa ne sai yaci

Zamewa yayi ya zauna a ƙasa ,yana Fuskartar Maryam Dake shirin Yanko kazan Ta dubeshi da mamaki tace

"Lemme take off the onions"

"No I'll eat it like that"

Mamaki bai tashi Kamata ba Saida taga Ya yago kazar ya haɗa da albasar, ya dangwali yaji yakai baki tana ganin yanda yake yamutsa Fuska alamar yana Receiving irritative taste a tongue ɗinsa, Murmushi tayi a ranta tace Ashe K'aryar Rashin Son Albasa kake.

Itama ta yanko yanda taga ya yanko zata kai baki, ya cahfko hannunta, ya kai Bakinsa yaci kazar harda cizon yatsarta, ta saki Ƙara.

Mama taja tsaki, "mugu ba ance baka cin Albasa ba?, Ko Wata sabon Gulmar ce yau ta tashi?"

Bai tankata ba Ya sake yanko kazar ya kai bakin Maryam, ta Girgiza kai Wai ita a dole kunya take aikou ya sauke hannunsa zai ya kai bakinsa, ta cafke Ya sa mata a baki ta saki Murmushi, mama dai bata tashi ba, sai kular da ita suke tanata sababi basu tanka ta ba, da La'asar sukaje ganin Abba a kurkuku .

Yanda taga Abbanta ta Tsorata sosai , yayi busu Busu, ya wani tara ƙasumba gashin kanshi a hargitse kaman mahaukaci siffanshi ya koma Abin tsoro, tana Ganinshi taki hawaye Sun Zubo mata, innalillahi Wainnailayhirraji'un taketa Faman Maimaitawa har ya iso garesu ya zauna, Saleem ya kauda kai yana Taɓe baki don Ya tsani Daddy, haka baiji ya bashi Tausayi ba.

Cikin Hawaye sosai Maryam tace

"Daddy me Umma na tayi maka ka kasheta?, Me yasa ka kashe Umma me tayi maka?"

Kuka Takeyi sosai ,Daddy ya Rungumota Yana Rarrashi ,Saleem Ya sakar Masa harara

"Kiyi hakuri maryam sharrin Shaidan ne"

Maryam ta ɗago idonta da yayi ja don Hawaye , tace
"Really?, Abba Sharrin Shaidan?, Sharrin Shaidan ne yasa Ka kashe Umma na?"

"Sharrin Zuciyace...kiyi haƙuri "


"Daddy Ina So nasan dalilin Da yasa Ka kashe Umma ,ina so nasan taya ka kasheta batareda ka bar Hujja ba💔💔, Daddy You're wicked, ka lalata Rayuwar mu"

_*Waye Daddy?*_

"Kakan Bamalli da maryam shine Sarkin Zazzau, Dattijo Alhaji Ahmad Bamalli, ƴaƴan Sarki guda biyu ne kachal a duniya, Abban Bamalli shine babba wanda Uwargidansa jikar Sarkin Katsina ta samu cikinsa tun Kafin Aure, Lokacin Ahmad bai Hau mulki ba babu wanda ya sani don ana Saura Sati bikin ya gane, kuma Cikin har ya shiga wata biyu lokacin, a haka akayi auren, bayan anyi Auren sai Suka haɗa baki da Doctor cikin na kaiwa wata bakwai daidai akayi surgery aka ciro abban Bamalli gudun kada a fara kirgan yaushe akayi auren, sai suka ce hawan jini ne yayi mata yawa Kuma zaman yaro a cikinta babban Barazana ce ga lafiyarsu,, Har yanzu babu wanda yasan bata aure aka samu cikin ba, ranar suna yaro yaci sunan Abubakar.

Sai kuma amaryarsa da ya aura bayan Haihuwar Abubakar, itama ta haifa Abban Maryam Sa'eed, Cikin ikon Allah Abban Bamalli ya fita daban daga cikin Gidan kaman Ba ɗan sarauta ba, hakan yasa sarki da Mutanen gidan Suke matukar sonsa ,idan Ka duba Shekarun Abubakar da na Sa'eed Sam basuda wata tazara sosai dukkansu kansu ɗaya, sai dai Kowanne halayyar su baizo ɗaya ba, haka yasa Suka taso babu yabo babu fallasa.

sa'eed ya kasance mutum ne mai tsananin Son Mulki da kuma Son zama sarki ko ta halin yaya, da Farko Sun ɗorawa Abubakar Tarin Tsana ,don Gani suke kaman yana son sarauta ne, amma da suka ga ya fidda Hankali baya damuwa da alamuran siyasa sai suka sassauta masa , Alhaji Abubakar ɗan Flexing ne, bai damu Yayita kwanan Club ba, zaman Gidan Bai dameshi ba, Neman Mata kuwa har abin ya zarce na iyayensa , kusan a tare Abubakar da kanenshi sukayi aure a rana ɗaya aka daura auren Sa'eed da fateemah, sanann Abubakar da matarsa khadeejah Wacce suka gama Gantalinsu a waje kafin Suyi aure *_Note Zina Bashi ce, zina igiyace mai ci da Wuta, In ta fara ci bata tsayawa sai ta cinye Karshen igiyan, zina bashi ce mai bin Dangi ,, In ka ɗauka ko baka Biya anan Ba sai Ka biya achan_*


_*TUNASARWA*_
Ibnul Ƙayyum ya ce duk cikin cututtuka da ke bayan ƙasa babu wani ciwo da yake da wahalar warkewa irin ZINA.

*Imam Shafi'i* ya ce duk wanda ya yi ZINA da Dirhami Dubu, idan aka zo yi da nashi (ƴaƴa ko ƴan uwa) a kyauta za ayi ZINA Dasu tunda sun zo za su biya bashi ne 👌.

Ki duba masifun da za ki jefa ƴaƴan ki mata aciki, domin tabbas duk wanda yayi da ƴar wani sai anyi da nashi, idan kayi da matar wani tabbas Za'ayi da naka.

ZINA wargaza Al'ummah take yi, saukar da fushin Allah da Azabar Allah take yi.

Ya Allah ka sanya mu daga cikin bayin ka masu yawan tuba uzuwa gare ka, ka kare mu da zuri'ar mu daga ZINA.
Amin🙏🙏🙏.


Babu Yanda sarki baiyi ba don Ganin ya tarkato da hankalin shalelensa Kuma babban dansa Abubakar kan sarauta, Amma fir yaki amincewa , Ya maida Hankali kan karatunsa da matarsa, bangare guda kuma yana Neman Matan Mutane

Matar ABUBAKAR Hajiya KHADIJAH Ita ta fara haihuwa ta haifi MUZZAMMIL Wanda akafi sani da BAMALLI (Family name dinsu ne)

hakan Ya bawa Alhaji sa'eed haushi don yaso ace shi ya fara Ɗiga ƙwansa a Gidan ta yanda zai zamanto ko shi bai hau ba, yanada hope akan Ɗansa, saida Bamalli yayi shekara Ɗaya a duniya matar Alhaji Sa'eed ta haifi Zaid ( ZEEYK ) Bayan shekaru Shida ta sake haihuwa inda ta haifi Maryam ,daga nan Bata sake haihuwa ba sai bayan Shekara Uku inda ta haifi ƴan Biyu Ameer Da Ameerah .


Bamalli ya zama Ɗaya tamkar da dubu babban jika ɗan shalele, ya shiga Ran sarki Fiye da tunanin Mutum ya zama Ɗan Gata gaba da baya, hakan ya Haifar da wani Irin Shakuwa mai karfi a tsakanin Bamalli da Kakansa Sarki ,duk inda yabi sonsa ake, hakan ya Haifar da kishi da gaba mai tsanani a tsakanin these two brothers, Da iyayensu , Amma babu Mai nunawa Don A ganinsu nuna Kishi a zahiri Zubar da kai ne.

Da haka Daddy da Mahaifiyar sa sukata kulla wa Hajiya KHADIJAH da ɗanta tsuggu ta karkashin kasa suna yin nasara a wasu,Wasu kuma Su Fadi har Allah ya tona asirinsu ,Mai martaba ya Kori Sa'eed da Babarsa a masarautar kasancewar shi mai zuciya ne kuma mai kafiya akan Hukuncin da ya zartar yasa basu zauna neman Gafara ba suka fice, a wanann Lokacin ne rayuwa ta fara juya Masa baya, bai Haƙura ba Mahaifiyar sa sai zugashi take tana tunzurashi akan Kada ya haƙura da Sarauta duk yanda za'a yi yasan Yanda yayi ya ɗau fansa kuma ya cigaba da neman Sarauta .

bban Maryam Ya Saki Mahaifiyar Maryam Hajiya Fateemah sanadiyyar Wani Saɓanin da suka Samu kuma Tunda Suka rabu bai sake waiwayan ta ba, ya Kuma Bar mata yaransa Duka Su hudun yace babu ita babushi, ita ke wahala dasu Ana nan har ci dasha ya gagareta, wata Aminiiyarta kawar Saude ta nema Mata aiki a gidan su Saleem,Anan Abba Ya ganta yace yana So, Shima Baffa yace yana So, ita kuma ta zaɓi Abba , tace In Bashi ba sai rijiya Hakan ne ya Tunzura Hamza har Yayi mata fyade Ya kuma kashe Yaranta Ameeer da Ameerah Saboda sune shaida a lokacin da yayi mata Fyade, yayi framing Abba dashi a ranar, Kannen Maryam Su Ameer sun raka Ummansu wajen aiki , Abba baya nan anan Anan Baffa ya saita camera yayi amfani da ita a gabansu a take kuma ya sauya Fuskar sa Zuwa na Abba, ya Makala fuskar Ammie da na Hajiya Fateeemah, ɓangare guda kuma yayi Leaking Real Video ɗin a social media, Sai Baffa ya ajiye fake clip din a ɗakin Abba, a inda Ashman Ya shigo yayi playing ya kalla, babu wanda zai iya cewa editing akayi, everything was like Real, Hankalinsa ya tashi Matuƙa, Zuciyarsa tayi ta bugawa da ƙarfi babu Ƙakkautawa,ya fito yana tafiya ko ganin gabansa baya yi, yana Fitowa ya hango Abba Rungume da Aeesh dawowansa kenan Daga Pool (a lokacin Aeesh na Zaune a gidan Abba), idanunsa Sun Rufe, sai yaga Image din Videon na Masa Gizo, gani yake kaman Abba na shirin Yiwa Aeesh Fyaɗe ,ya Kamo wuyar Rigarsa Yana haki ya shakeshi, ya dinga zuba surutai Kaman Zararre, duk wanda ya matssoshi Sai ya kadashi, da ƙyar aka ƙwaceshi, aka shiga dashi Ciki ranga Ranga yana Ganin Sun fita, ya fito a guje ya nufi ɗakin Abba, Amma abinda kunnuwansa Suka jiyo masa yasashi Tsayawa chak, Yana Sauke numfashi, Inna Saude ce keba Saleem Umurnin yanda zasu Ƙona Gidan, idan Amman sa ta dawo, komawa yayi da baya Yanajin Kansa na barazanar Tarwatsewa, yana fita aka Saki Wani uban tsawa ,wanda yayi daidai da faɗuwan sa, bai tashi sanin Komai ba sai Da ake shirin Kai gawar Amma,

Daga nan Gabar tasu ta fara, a fili yake zargin Saleem da kashe mahaifiyarsu, da kuma Zargin Abbansa dayima Mahaifiyar matarsa fyaɗe, da yunƙurin yima Aeesh fyaɗen, a duk lokacin brain ɗinsa ya gifta Kan makamantan a binda ya faru a ranar sai hankalinsa ya gushe Yayita aikata abu kaman Zararre idan ya kama mutum da duka Baya bari har sai Ya suma , gefe guda kuma tsana mai tsanani ya shiga tsakanin Aash da Saleem, Abba na Bashida abokin takara irin Ashman, bashi ya aikata Fyaden ba ,amma ya yarda Ya amince ko don Ashman yaji haushi ya bar masa Aeesh, Son Aeesh da yakeyi daga Allah ne, kuma da gaske yake in An aura masa ita zai zauna da ita.

Gefe Guda kuwa, alhaji Faisal gudun kada su Ameer su tona masa asiri yasa aka kashe su, da ya nema ya rasa Gara kowa ya rasa, aikuwa Kowa ya rasa domin Kuwa a lokacin da Videon Nan Yayi Trending Fateemah ta Rasa kowa nata, dangi duk suka gujeta a cewar ta ita takai kanta, wa ya sani ma ko da gangar ta bari aka yaga mata rigar mutunci, Su Maryam ma kowa ƙyamarsu yake,


Abban Maryam Yaji haushi sosai Don Ta dalilin Haka masarauta suka Kuma datse alakar dake tsakanin Su, Suka kuma haramta ma Daddy Sarautar masarautar Zazzau na har Abada, akayi Appointing yayansa Abubakar A matsayin Sarki mai jiran Gado, yace baya so, ya bar ma Ɗansa Bamalli, Hankalin Daddy ya tashi ganin ta sanadiyyar matarsa Ya rasa sarauta, hakan Ya daɗa Tunzurashi Yaje Har Asibitin da Mahaifiyar Maryam Take jinya sakamakon ciwon Kidney da ta kamu dashi bayan anyi mata Fyaden ya kasheta ,daga Nan ya fara Jan Ƴaƴanta a jiki gudun kada azargeshi burinsa bai wuce yaga Maryam ta girma Ta auri Bamalli ba, don A halin yanzu shi kadai ne hope ɗinsa Tunda yanada tabbacin shi zai hau sarautar nan bayan Ran Sarki, idan Ƴarshi ta auri Sarki shi kuma ya zama surukin sarki

Sarauta Whoo👊

Ta dayan Ɓangaren Kuwa
Bamalli dan gata ba'a tsawatar masa akan komai In yayi, komai yayi daidai ne, baya son Raini, haka Bai yarda na kasa dashi ya rainashi ba, hakan Yasa Yan gidan Duk suke shakkarsa , komai yake so ana masa koda babu sai an nema, bai taba neman wani abu a duniyar nan ya rasa ba ,kama daga kudi Har matar da yake lalata hakan Yasa ya taso cikin sangarta da lalacewa Ya zama Mayen Mata, kun dai san Gidan Sarauta da Iya

Please Login or Register in order to submit comment