Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tabi bayansa ya ajiye ledojin abincin da suke hannunsa ,tana shirin zama ya rigata zama a bakin gadon.

Ta harareshi a fakaice, ta zauna a ƙasa, idanun ta akan Ledojin da ya shigo dasu.


saukowa yayi daga gadon yana bude ledar abincin da akayi sealing dinsa a cikin Medium container, sai lemuka wanda bata taba ganin irin suba amma basu da sanyi ya ajiye a gefe


Ji taji yawunta ya tsinke kuma dama yunwa take ji da gaske, a hankali ta matso kamar wadda ake jana da mayen karfe ta gyara zama, ta dauki cokali ta fara ci dadin abincin yana ratsata.

Zagewa tayi ta na cin abincin Cikeda Yunwar dake tattare da ita, babu zato babu tsammani Kawai taji ya Janye abincin Daga gabanta

Dagowa tayi kaman Zatayi kuka ji tayi kaman ya janye Numfashin ta, ya harare ta

"Wanda yayi miki ciki shi ya kamata ya ciyar dake bani ba"

Ya Fada cikeda hawaye

"Yaya Don Girman Allah ka bari in ƙara koda Loma ɗaya ne."

Ta fada cikin Hawaye

idanunta wanda sukai jaa ya kalla, yana ganin yanda take jan numfashi, kafin ya taɓe baki

"I wonder how you feel comfortable With the pregnancy!, Karama dake!"

Yaja tsaki cikeda takaici sannan ya saki Wani sihirtaccen murmushin gefen baki Wanda yafi kama da na mugunta yace

"Karkiyi tunanin Cikin nan zaisa na haƙura dake"

Take taji bugun zuciyarta na tsananta Dubanshi tayi a firgice, yan hantan Cikin ta suka motsa,

"Ni saleem ba'a kasani a gasa, da ace na bar mashi ke na Gommace na Aureki na ajiyeki a matsayin Hoto, Koda Bazaki Min Amfanin komai ba, na gummace na Sakaki a bola Kodan na ƙuntatawa Maan"


Yafada still murmushi a fuskarsa, kasa cewa komai Aeesh tayi sai Zufa dake tsattafo mata Hawaye Na Bin fuskar ta, banda rawa babu Abinda Jikinta keyi tsoron Saleem na Cigaba da shigar ta.


Daga gira daya yayi still yana kallon yanda Hawaye ke Diga a idonta, Tsoron sa ya bayyana Ƙarara a fuskar ta ,murmushin kuma bebar fuskarshi ba yace.


"Ɗaga min Rigar naga Cikin Wata nawa ne?"

Ja da baya tayi Jikinta na karkarwa

"Ɗaga min nace"

Ya daka mata tsawa

Girgiza kai tayi idanunta na saukar hawaye

"Please Yaya kayi haƙuri Bazan sake ba"

Yayi saurin dakatar da ita
"Come again... !"

"Please yay...."

Ya sake dakatar da ita

"what's my name?...."

Ya fada yana Kallon yadda ta rufe idanu, sai kuma sharr hawaye ya shiga zubu mata daga cikin Idanunta.

"Habeeby....!"

Ta furta kaman mai raɗa, Murmushin da baiyi niyyar yi bane ya subucemashi yadan kawar dakai yanayi.

Har yanzu idanunta a Lumshe suke suna fidda ƙwalla.

A hankali ya matsa inda take ,baiyi wata wata ba ya ɗage Rigarta.

buɗe Idanunta tayi hawaye har lokacin bai tsaya mata ba,ta daga hannu zata Riƙe hannunsa da yake yunƙurin kaiwa Cikinta, ya riƙe hannun nata.

Yasa Hannunsa ɗaya yana Yawo dashi a saman Cikinta na dan wani lokaci, kuka Takeyi sosai saboda azaba, gani take kaman Saleem so yake ya fiddo ɗan dake Cikinta da ƙarfin Tsiya.

Da iya ƙarfinta take ƙoƙarin kwatar hannunta, Numfashinta na haɗewa waje guda har yana iya jin yadda ƙirjinta ke ɗagawa sosai.

A hankali ya cikata, ya sauke Hannun daga kan cikin,ya kalli Fuskar ta da tayi Shemeshame da Hawaye da majina sai Numfashi takeja sama sama.

ya ranƙwafa daidai fuskarta yana sauke numfashi da wata kalar Murya yace

"Four months pregnancy.....!"


Saikuma ya sake matsowa dab daita har suna shaqar numfashin juna, idanunshi cikin nata yace

"Ina ƙaunarki koda baki yarda ba, kuma har yanzu akwai Igiyoyin Auren mu akanki,ba barazana zan miki ba, Na miki tanadin Rayuwa bayan Kin haihu sannan nayiwa Dan Cikin ki tanadin Akasin haka a matsayin hukuncin Aikata fasadi da Aurena"

Ya fada yana kwashe Abincin da ya zuba mata, ya maidasu cikin Ledar da ya shigo dashi, sannan ya fice Ransa Fess Koma komai ya huce Kaɗan daga cikin takaicin Abinda sukayi masa itada Ashman.

Binshi tayi da kallo harta fita, tana kuka wani irin tsanar sa takeji azuciyarta, wai me ta tare masa ne?, Me yasa yake Son takurawa Rayuwar ta ne?.

Tun tana hawaye harta fara shesheka ahankali.

Zafi takeji acikin zuciyarta kamar ana ruramata wuta, ga wata zafin abinda Aareef yake mata Jiya har yanzu ya kasa barin zuciyarta, ga takaicin Ammie ta dawo kuma ya kasa ya tsare ya hanata zuwa ganinta , Gashi babu mai iya fahimtar lamarin ta,Ashman dake supporting dinta Akoda yaushe baya nan abubuwa da dama sun taru sun cunkushe mata.

So taga Aareef ta bashi haƙuri, don tasan Ransa ya ɓaci jiya kuma duk laifinta ne, da a lokacin da yace bayida lokacin ta ta haƙura da bata ƙara ma kanta wani laifin a gurinshi ba.


Taci kuka sosai, babu mai rarrashinta, da haka wani wahalallen Bacci yayi awon gaba da ita .

****


Da sallama suka shigo,Binsu da Kallo Barr Hamza yayi har suka ƙaraso, Zeeyk ya zauna sannan ya maida kallonshi kan Maryam data hade gabass da yamma na fuskarta yana mata kallon Sani, bata zauna ba a tsaye ta tsaya.

Tsit office din yayi babu mai niyyar motsawa kowa ya zubama kowa idanu kawai.


Ganin sun kusan 5mins babu mai niyyar magana yasa Zeeyk dake zaune Kujerar dake facing dinshi yadanyi gyaran murya

Shima Barr Hamza Gyaran murya yayi yace


"Akawo coffee ko drinks?"


Murmushi maryam tadan saki tana kallon zeeyk

"No, mun gode, amma ba zama yakawomu ba bare ayi maganar refreshment ƙara muka kawo maka"

tafada tana maida kallonta kan Barr Hamza

"You're highly welcome Mr and Miss ko zan iya Sanin Me ya kawo ku?"

yafada cikin sakin fuska idanunsa akan Maryam.

Ganin yadda ta kafeshi da idanu yasa yayi dan murmushi wanda yaqara mashi muni a idonta sosai

Mika mishi hannu Zeeyk yayi suka gaisa sannan ya dora da cewa

"sunana Zaid Sa'eed Na ji labarin ka ,ance Duk murdewan case indai na Shari'a ne da zarar An zo wajenka an gama"

Kawu ya gyada kai

"Babu Shakka"

Maida kallonshi zeeyk yayi akansa sannan yace

"Nima Nazo da wata Murdadden case Shekara da shekaru ana fafatawa akai Amma an kasa samun Nasara"

Ya cije Lips ɗinsa yana kallon Baffa, ji yake kaman ya hau kansa yanzu yayta duka ,kauda dubansa yayi daga gareshi sannan ya cigaba da fadin

"Wata mata ,yar talakawa, bazawara ce, yaranta Hudu tana Aiki a gidan Masu kuɗi , Maigidan nada mutunci sosai , ya dauki nauyin Komai na Rayuwarta dana 'ya'yanta Boom kwatsam Sai soyayya Ta Wanzu a tsakanin Su da nace soyayya ina nufin Mai karfin nan Wanda har Takai iyaye manya sun Shiga zancen"

Gaban Kawu ya fadi, dama ya zargi hakan tunda yagansu,fuskar Maryam sak dana uwarta.

Lura da yanayinFuskar sa ne ya ba Zeeyk kwarin gwiwa ya cigaba da fadin

"Amma saidai kashh, Ashe Ɗan uwansa Shima Yana Sonta, kuma yayi yayi tasoshi taƙi, hakan yasa Ya Kawo ƙarshen Abin, Tunda bai Samu ba Kowa ma ya rasa"

Kujerar kusada shi Maryam ta ja, ta zauna ganin Labarin Is going interesting, ta Dora ƙafa daya kan daya tana karantar yanayinshi.

Zeeyk ya ce

"Barr ka gane Abinda nake nufi Ai"

Kawu ya Girgiza kai

"No nikam ban Gane yaren ba Kamin dalla dallah"


"Good...!Yayi Mata fyaɗe, yayi mata Video, Sannan yayi Editing ya saka Fuskar ɗan uwan nasa wanda yake sonta, da wannnan Yayi framing Ɗinta yace mutuncin ta shine ta Amince ta aureshi ko Ya turawa 'ya'yanta Ko kuma ta Biyashi Miliyan Ashirin Don ya goge Video kuma ya haƙura da ita Har abada"

Ya fada cikin Dauriya don ba ƙaramin rawa zuciyarsa keyi ba, ya Lumshe ido sannan ya ware su akan kawu.

"But guess What she choose?

Kawu Yayi Murmushin Mugunta, Zeeyk yace

"Sai zaɓi ta Biyashi dukda batada hanyar Samun Maƙudan kuɗaɗen, bataso Abinda yayi Mata ya taɓa mutuncin ƴaƴan ta, tanada ƴaƴa mata tasan idan ya Saki Videon nan har abada Duniya bazata taba ganin ƴaƴan ta da mutunci ba, dukda Ba laifinta bane, Mutumin Lawyer ne babu damar takai karanshi yafita kuɗi da Iko kuma batada hujjan da zata kare kanta ,Kwana uku ya bata rak Yace ta nemo 20M if not Zai ɓata Image dinta a Idon Duniya , Barrister ya daureta da jijoyoyin Jikinta har yana mata barazanar kisa ,Batareda tayi dogon Tunani ba, ta siyar da Kidney Ɗinta Abu Mafi daraja a jikin Dan Adam"

Lumshe ido Maryam tayi, tana jin wani irin zafi a zuciyarta, ta maida Hawayen da ya taho mata.

Barr Hamza Yayi kuri yana kallon Zeeyk , wani irin Murmushi na mugunta manne a fuskar sa ,Batareda ya damu ba ya cigaba.

"Da ya gane Siyarda Odarta zatayi sai yasa aka ɓata daya daga ciki, aka siya ɗaya....duk don Ta haƙura ta amince mishi ,Babu wanda yasan ta Siyarda Oda, Daga ita sai Shi Sai Mahalicci, tun daga wannan Lokacin Ta fara ciwo a tsaitsaye a hankali odar da aka lalata ya fara Shafar lafiyanta,da aka kaita asibiti aka gano hakan ɗan ya bata nashi Odar ya zamana Yana da guda, ita kanta bata san anyi haka Ba,bata ma san An sa mata oda ba,a haka ta cigaba da Rayuwa kuma maganar Aure Ba'a fasa ba, Har Saka ranar Akayi bikin saura Sati ɗaya biki Aka ce Amarya tayi hatsari ta rasu”

Dan dakatawa yayi yana kallon kawu don ganin reaction dinshi, sai gani yayi still yana bin Maryam ne da kallo hakan yasashi cigaba dacewa

"Barr Hamza Da Kaji labarin nan Wa ka fara Zargi a ranka?"

Dubansa kawu yayi Murmushi dauke a fuskar sa yace.

"Ba kace hatsari Sukayi ba?, Ai babu zargi a Batun hatsari"

Zeeyk ya koma yayi balancing Akan Kujera yana Jinjina tantiranci irin na Kawu

"Woww bravo, Amma ya kake gani Idan Ance wacce ta rasu bata Shiga mota Ba a ranar, meaning bata cikin Motar akayi hatsarin?"

Kawu yayi Murmushin gefen baki idanunsa akan Zeeyk

"Anan Ne layin Zargin Zai fara"

Miƙewa Zeeyk yayi, ya zura hannayensa cikin Aljihu, ya cije Lips dinshi a hankali.

"Ashe ka gane!"

Ya fada yana Takawa ta baya

" Allah inaso kasa Lawyern ya maido 20m dinda ya karɓa a hannun Matar, sannan Kuma Ya biya odar da yasa aka lalata Kafin ajega wanda ya Rabata da Rayuwarta ”

Ya daga hannayensa Uku

"Kwana Uku na baka...!"

Maryam ta dau jakarta ta rataya, sannan ta Gyara Zaman Shade dinta

"Na gode Barr Hamza"

Kawu yace

"Nima Nagode sosai maryam Bamalli Mrs Saleem"

Dubansa tayi da mamaki a fuskar ta

"Kunyi mamaki Ko?, amma dai da alama Kun manta abu guda, Wannan Lawyern ba Irin kowane Lawyer bane a ƙasar nan, Basirarsa ta zarce ta kowa shiyasa ake Ganinshi Na daban a ko ina"

Duban Zeeyk yayi a wulaƙance

"Kai kuma magana kaman Mai Rayuwa anan Gaba, ka manta 2months kachal ya rage maka a wannan rayuwar?, Taya kake ganin zaka ja dani mai guaranteen Shekaru ashirin nan kusa"

Maryam ji tayi hawaye sun wanke mata fuska, bata Son a tuna mata Yayanta ya kusa mutuwa.


Shikou Zeeyk fuskar sa Normal Zuciyarsa cikeda wutar dake ruruwa na daukar fansa yace

"Barrister nifa ban Ambaci Suna ba, banyi identifying Mai kaifi ba... Amma da Alama Baka san Tasirin photographer Ba, Wanda yayi specializing Akan Computer,mai yiwuwa Dukkanmu Jikunamu manne suke da camera bamu sani ba, Mai yiwuwa Duniya gabaki ɗaya suna ganin Mu, ka kiyayi Mutum irina Malam Hamza Shettima "



Yana kaiwa nan, sannan ya kalli Maryam da kallo da kallo daya Zakayi mata ka hango tarin ƙiyayya, yadan yimata murmushi sannan yafita, tabi bayanshi.

Binshi dawani disgusting kallo Barr Hamza yayi har suka fita, hantar cikinsa na kaɗawa da alama Kwantacfiyar abinda ya yanka ya birne shi ke shirin tashi.....✍🏼



Suna fita Maryam ta dubi Zeeyk da Murmushi a fuskar ta, tareda Maƙalallen ƙwalla tacce

"Gaskiya Yaya kayi Ƙoƙari , Now what Next....!"

Murmushi yayi

"Inason Kidney Guda Uku , daga Yanzu zuwa Gobe da safe"

Maryam ta zaro ido

"Kasan Ko nawa ne Kidney yanzu kuwa?"

Fuskar sa a haɗe ya dubeta yace

"Nafiki sani, ko kin manta Nima kidney Ɗaya gareni?"


Kauda dubanta tayi daga gareshi tanajin zuciyarta na mata wani irin suya, ji take kaman ta koma Ta farka cikin Barr Hamza, Tayi masa muguntar da yayiwa mahaifiyarsu.

Zeeyk yayi gyaran Murya yana ciro car key suna

"Yanzu ba wannan Ba, a ina kike Ganin Yafi dacewa Da ayi Surgery a garin nan?"


"Asibiti mana"

"Yup I think Asibiti zaifi, cus anan ne Akai ma Mum Aiki"

Ya fada Daidai lokacin da ya shige motarsa, itama shiga tayi ya ɗan yi jim na wasu seconds sannan cikin jimami yace.

"Ba kowa ya kashe Mum ba sai Daddy, mahaifin Mu nidake shine yaje har Asibiti ya karasa ta"

Ya cije Lips ɗinsa Yana jin zafin abin a zuciyarsa idanunsa Suka kaɗa.


Muryar sa a raunane yace

"Idan na tuna Video da aka Turo mana lokacin kina yarinya sai inji na tsani rayuwa, Barr Hamza sent a video to us, mum was naked, stark naked, it was the most Creepy and ugliest sight I have ever seen in my life, tana ihu tana neman Agaji amma saboda kyekyashewawn na zuciya irin nashi yayi raping dinta, Ba raping dinta kadai ya yi ba, Saida Yayi mata Video ya kuma yaɗa shi bayan Rasuwarta, mutane fiyeda Miliyan uku ne suka gani a lokacin Our mum.... imagine....!".

Hawayen baƙin ciki suka sauko masa, yasa bayan hannu ya share hadi da jan numfashi

"Bayan wannan yayi niyyar ya dauki ranta ne gaba daya ,bazan iya rabuwa dasu ba, na rantse sai na daukan Ma Mum fansa koda shine ƙarshen Abinda zanyi a wannan rayuwar sai na dauki fansa akan Mahaifina, mahaifin Saleem da ɗan Uwansa ,jinin Mum bazai tafi a banza ba"


Sosai Maryam take kuka kaman ranta zai fita, shima duk dauriyan sa kasa riƙe hawayen sa yayi, har yanzu idan yayi Duba fake YouTube account dnda Baffa ya Buɗe sai yaga Videon mahaifiyar su, a lokacin da yake mata fyaɗe Ya kuma ɓoye fuskar sa.


Wannan Abin idan ya tuna ba ƙaramin tada hankalin shi yakeyi ba.

*ASHMAN*
Sanye wata hadaddiyar yadi plain navy Blue ɗinkin jampa da wando mai kyau wacce ta ƙara haska skin ɗinta sa , flat shoe ya saka.

Ya dubi kanshi ta Mirror Murmushi yayi wanda ya sanya fuskarsa lomawa yana shafa sajensa da yayi masa gyara irin na Ashraff, Hularsa ya kwama sannan ya fesa turare.

Murmushi kawai yake saki yana jin dadi zai ga ihtyn sa.


*Saleem*

Sai Safa da marwa yakeyi a asibiti , tsakanin Dakin da aka kwantar da Aareef zuwa dakin da aka kwantar da Aeesh, Tsoron shi kada ta gane yana asibitin.

Bash ne ya fito daga ɗakin da Aka kwantar da Aareef yana yar waƙe waƙe

"Kai zonan"

Saleem ya kirashi.

Bash ya nuna kanshi

"Wai dani kake?"

Ran Saleem ya ɓaci yace

"Kako san Dawa Kake magana?"

Cikin Rashin nuna damuwa Bash yafd

"Na sani mana!, Da mutum Dan mutum jikan Mutum mana"

Daidai lokacin da Nurse tazo giftawa Zata shiga ɗakin Da aka kwantar da Aareef

""Keh wannan a wane Unit Yake aiki a asibitin nan?"

Ya fada yana dakatar da ita

"Ba ma'aikacin mu bane, gurin Baƙonka na Emergency Clinic yazo "

Tsaki yaja yana huci
"Ashe ba kowan kowa bane!"

Ranshi a ɓace yace

"Ya Fita daga Asibitin nan, Get out...!"

Ya juyo Kan Nurse din cikin gargaɗi yace

"Ke kuma daga yanzu bana so in sakeji wani Yazo dubashi koda babarsa ce, idan kuma kika sake Wani ya Ganshi Tho a bakin Aikinki....."


Maganar sa ta Maƙale masa ne ganin Shigowan Ashman a natse cikeda ƙasaita ransa a ɓace.

Yana ganin saleem yaja burki aka shiga yiwa kuma kallon kallo.

Cikin dan Rudewa saleem ke kallonsa,Shigarsa irin na Ashraf amma kallon Da yake masa sai yaga kaman Ashman.

Kauda dubansa yayi daga gareshi a hankali , yayi wucewar sa, yabar saleem da mamaki a ransa.

Zaune ya iske ta a bakin Gado tana matsar ƙwallah, zama yayi kusa da ita,ya kamo hannun ta a Tsorace ta dubashi Sai kuma a hankali Tsoron ya rikide ya zama mamaki.

Bakin ta na rawa Tace

"Ahky.......!"

Wani irin wannan Runguma tayi masa, Idanunta ya cika da hawaye

"I miss You....i miss You"

Sai ta fashe da kuka harda Shessheƙa, ɗagota yayi ya share mata hawaye Take yaji Ɓacin ran daya shigo dashi ya ware.

Ɗazu yana fitowa daga gidansa ya hadu da kamal shike sanar dashi abinda ya faru da Ita, harda Dukan da Saleem Yayi ma Aareef din yanzu ma zuwa yayi ya dauketa daga Asibitin, su tafi gida , Already ya riga ya kira Inna Yathai yace ta fahimtar da Ammie cewa Aeesh matar sa ce, ya tabbata idan Ammie ta yarda babu wanda zai hanashi Matarsa.

"it's okay ihty bazan sake Tafiya na kyaleki ba"

ya faɗa yana share mata hawayen fuskarta, kallonsa tayi yaja hancinta yana Murmushi yace

"Bari na gaisa da baby na"

Murmushi Tayi, ya Duƙa ranta cikeda fargaba har yanzu Cikinta bai daina zafi ba, Abinda saleem yayi mata ba ƙaramin azabtar da ita yayi ba, a hankali ya Janye rigarta sama yasa hannu ya shafa Cikinta da ya fara yin tudu kadan, cikin wani irin shauƙi ya Kai bakinsa ya sumbaci cikin Cikin Murya yace

"Hy Baby mai kamada Mummyn shi"

Ji yayi tana Dariya ,da mamaki ya ɗago yana kallonta

Cikin dariya mai haɗe da hawaye tace

"Wai me kamada Ni, meyasa baka So Yayi kama da kai?, Saboda kasan kai mummuna ne ko😂"

Tayi Maganar Cikin dariya sosai,tsayawa yayi yana kallon yanda take dariyar da ka gani zaka gane na ƙarfin hali ne.

Shima Murmushi yayi yace

"Eh naji din, Ni mummuna ne, ke kuma matar Mummunan"

Hararar wasa tayi masa

"A'a Ni ba Matarka bace"

Shuru yayi yana kallon ta na wani lokaci , jikinsa yaji yayi sanyi , a sanyaye ya kira ta

"Ihty...."

Ta dubeshi Batareda ta amsa ba saboda yanayinda taji Muryarsa

"Wai har yanzu Baki yadda da Auren Mu ba?,Dama duk zaman da mukayi baki yadda dani ba?"

Taɓe baki tayi

"Na yarda dakai mana , yardar ne ma yasa Na baka jikina har na Dauki cikinka wanda bana Shakkar nunawa Duniya Ubansu"

Shuru yayi Yana Jinjina shashanci irin nata, take ya Tunano labarin Da kamal ya bashi

Dubanta yayi cikin sanyi yace


"Listen ihty...!

Sai kuma yayi shuru Yana ganin Image din labarin da kamal ya bashi ɗazu, taya zata yarda da Aurensu alhalin tanayi wa wani irin shegen Son Nan, duban cikin Idanunta yayi da Idanunsa da suka kaɗa

"Badon ina matuƙar kaunar ki ba, da tun a ranar da zamuje Canada da kikace in kaiki wajen sakaren saurayin nan naki da alokacin na Kasheshi, da Alokacin na Raba Kansa da gangan Jikinshi, But Now inaso ki sani Idan na sake Ganinki dashi, i wll rip off ur neck wlhy and I mean it"

Dubanshi Tayi d Mamaki

"Yaya Kisa fa kace"

"Eh bayan na Kasheshi, bazan bari a a suturta gawansa ba, bazan bari ayi masa sallah ba, Sanann zansa a tarwatsa taron bakwai ,in an birne shi bayan kowace kwana biyu Sai naje kabarinsa na tultula masa fetur"

Ya fada Cikin Huci idanunsa yana zare mata firgitattun idanunsa, tsoro ne ya kamata tunda take bata taɓa ganin sa cikin Wannan yanayin ba, lokaci daya ya canza daga Yanayin farinciki ya burkice kaman wani mai aljannu, Kuma ayanda yayi maganar tana hango iya gaskiyarsa a iya kalaman sa.

Ransa ɓace yace ta sako hijabi su tafi, a yanda yayi mata magana tana ganin Idan ta Musa babu abinda zai hana ya daddakata a yanda take Ganinshi ya koma Tamkar dodo, sam fushi baya masa kyau .


Bash na fita ya kira Aareef a waya ya gaya masa yanda sukayi da saleem , Yace duk yanda za'a yi yasan yanda Zaiyi ya gudu saboda saleem Bashida Imani.

Hankali tashe Aareef ya Fito daga Ɗakin da aka kwantar dashi cikeda fargaban sake haduwa da saleem, dai dai Lokacin da da su Aeesh suka fito .


Ashman ne ya fara Hango Aareef Ya haɗiye wani Kishi da ya taso masa ji yayi kaman Ya shaƙo wuyarsa ya aika shi inda ba'a dawowa.


Hannun ta dake Cikin nashi yaji ta zame, yabi hannun da Kallo, sannan a hankali ya daga kansa ganinta yayi chan Gaban Aareef.

Chak ASHMAN ya tsaya da tafiyan da yake shirin yi, yabita da kallon Mamaki koda Kamal ya bashi Labarin Abinda ya faru ƙaryatawa yayi ,yasan bata iya son Abu ba, Amma baisan Sakarcinta Akan So har yakai ga haka ba


"Sadauki na, me kazoyi a asibiti?, Me ya kumburar da Fuskar ka?, Kayi hatsari ne?"

Ta fada cikin kulawa kaman Zatayi kuka.

Hararar ta yayi cikeda jin haushinta yayi gaba,ta sake shan Gabanshi idonta na tara ruwa.


"Don Allah Aareef Ka yafe min, Fushinka a gareni Azabtarwa ce"

Wani irin damƙa taji anyi wa Hannun ta, ta kwace da ƙarfi ta tare gaban Aareef dake shirin barin wajen

"Don Allah Sadauki ka saurareni"

kafin ta Ƙarasa magana taji saukar mari a Fuskarta ta hagu.

A gigice ta ɗago kai ta dubeshi fuskarsa tayi masifar jaa


Hannu ya Kuma ɗagawa zai kai mata wani a gigice Aeesh ta ƙanƙamesa tana fasa wani irin kuka mai ƙarfi.

Wannan itace karo na biyu da Ashman ya taɓa yi mata mari irin wannan Ranar da Baffa ya rasu da kuma yanzu.

Marin yanzu ya Gigita ta sosai ,Dukda Ashman shi ya raine ta, faɗa bai taɓa yi mata ba, in zai hukunta ta saidai ya hukunta ta da Halinta, balle duka sai marin ya Zamewa aeesh wani firgitaccen abu sosai ta gigice ta ƙankameshi sosai tana sakin wani irin kuka .
















Nayi Gabas 🚶🏼‍♀️🚶🏼‍♀️🚶🏼‍♀️

Bintou✍🏼✍🏼


Nov 14


[12/7, 8:23 PM] { Queen_Hernah }: *WUƘA A ZUCIYA*
( _BLEEDING HEARTS_ )



*052*


Aareef na tsaye yana auna masa kallon mara wayau, a ransa yana cewa

_Kana namiji ka kasa gayawa Mace Kai Mijinta ne?,Macen ma sakaryar nan Aeesh!_

Ashman na tsaye idanunsa yayi jajur yanayin yadda yake sauke numfashi da sauri zaka san ran maza ya ɓaci, jijiyoyin kansa sun fito sunyi raɗa raɗa ,da ƙarfi ya Rabata da jikinsa ,ta fashe da kuka cikin Tsananin Tsoro da fiegicewa bata Taɓa ganin shi cikin wannan Yanayin ba, sai huci yake kaman Zaki.


Kallon gargadi yayi ma Aareef sannan ya damƙi hannunta yana Huci ya fice, da ƙarfi ya buɗe motar ya jefa Aeesh cikin Motar.

Dr Aaryaan na masa magana bai saurare shi ba balle ya bashi amsa ya shige motar zuciyar sa na tiriri da ƙarfin gaske ya fizge motan ya bar harabar Asibitin

Aareef da Bash na ganin Ficewanshi suka sauke yar gajeruwar ajiyan Zuciya, don su ma ba karamin Tsorata sukayi da lamarinsa ba.

Tafe suke a mota baka jin komai Sai sautin Kukanta,sai shan zuciya take alamun taci kuka sosai take ciwon cikinta y dawo sabuwa kafin Su isa gida ta jigatu Zufa ya gama jiƙata tako ina ,Shi kou sai huci yakeyi takaici duk ya cikasa duk muƙurƙusan da Takeyi bai masan tanayi ba, da wani irin Gudu yake jan Motar har suka isa gida.

Yana gama parking ya Buɗe ya fice Batareda ya jira Fitowan ta ba, ya kulle kofar yayi gaba, yayi nisa ya juya yaga bata biyoshi ba ji yayi kaman yayi banza da ita, sai wata zuciyar tace ya dubata, ya koma, zaune ya iske ta a motar ta haɗa gumi ta riƙe cikinta sai juyi take tana Kuka sosai.

da ɗan sauri ya riƙe hannunta, Aeesh wacce take jin kamar zata mutu ta sake fashewa da kuka da faɗin

"Ahky.... Ahky zan mutu wayyo cikina

Gam Aeesh ta matse hannunta dake cikin nasa, kafin ya ɗaura ɗaya hannun saman Cikin ta ya shafawa yama rasa me zai ce, Jikinta zafi kaman garwashi

wani irin tausayin ta ya kama shi, duk a sbd dashi ta shiga cikin wannan halin kafin yayi Mgna yaga ta saki kuka tare da zabura tana wani irin kalar ihu ta rirriƙeshi tare da faɗin

"Wayyooo Ahky zan mutu Am dying Wayyo cikina"

Tuni ya mance haushin da ta bashi ,da wani irin sauri ya shige motar tare da sanya hannunsa gaba ɗaya ya jawota jikinsa ya ƙanƙame ta yana sakin ajjiyar zuciya.

"Ba zaki mutu ba Ihty"
Ya fada shima kaman zaiyi kukan gaba ɗaya ya rufe ta da ƙirjinsa yana jin yadda zuciyarta ke Bugawa zafin Jikinta na gasa shi a hankula,ya sake rungome ta tsam a jikinsa a hankali yake shafa cikin nata ya saita bakinsa daidai kunnanta Yana Karanto adduo'in da suka zo bakinsa ,Hankalinsa yayi mugun tashi,ji take kaman Ana sossoka mata wuƙa a cikinta, sai yanzu takejin zafin Jagwalgwalon da Saleem yayi mata.

Ji yayi tayi shuru ta kwanta Luff a ƙirjinsa alamar Ciwon ya lafa,sakin ajiyan zuciya yayi yaja hannunta, suka fice a motar tana Share ƙwalla

Sai matse hannunsa Takeyi alamar tana azabtuwa, suna Shiga ciki Motar Abba yayi Parking a harabar Gidan

Zaune suka iske Ammie a Parlor Itada Inna Yathai da Matar Baffa da Alama suna zantawa ne mai mahimmanci

Da sallama ya shigo suna shigowa sanyin AC ya bugeta a bakin

Please Login or Register in order to submit comment