Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Rabeel,kuma ranar da ta kasance mafi tarihi a Rayuwarta bata taɓa tunanin Sake rayuwa da wani namiji ba bayan ZEEYK Allah kenan, wanda ka shirya rayuwarka da tashi daban Wanda Allah ya tsara zaka kare rayuwarka dashi daban.


Shekara daya kenan Da rasuwar ZEEYK Amma har yanzu yana Nan Manne a Zuciyarta, bazata taɓa mantawa dashi ba, ya zamo kaman katanga da ta kare Zuciyarta daga ganin Kowa sai dai a yanzu Rabeel yana neman ya Ture wannan Katangar ya gina nasa soyayyar a cikin Zuciyarta.

Bayan sati biyu aka ɗaura auren Ammie da Ajmal, da kuma nafeesah ƴar inna saude da Ayman (babban Ɗan Ajmal Angon Ammie), sannan Rihaan Shima da Zee a satin da ya biyo baya kuma akayi na barr Abdool da Hafsah Kanwar Aashman, auren da yabawa kowa mamaki duba da yanda basua jituwa ada, Amma cikin kankanin lokaci Kiyayyar da suke ma juna ya juye zuwa soyayya mai Tsanani, ada yaso ya auri barr Bintou Saboda tun a Law school yake ƙaunarta amma taƙi bashi dama akan Nata dalilin, hakan yasa ya haƙura ya nemi soyayya a wajen Hafsah Kuma ta amince gashi Har sunyi aure.

Ana gama Biki Sadeeq Ya dau Amaryarsa Reey suka koma Canada inda yake aiki, bazasu dawo ba sai nan da shekaru uku.


Daddy Ajmal da Abba suka tara Ashman Da saleem Ganin Har yanzu akwai wani yar tsama a tsakanin su, saleem yaki ya yafewa Ashman Kazafin da yayi masa, Ashman Kuma yaki saukar dakai ya bada haƙuri .

Dukkan Su abu ɗaya ke ɗawainiya dasu wato Girman kai , da kyar Abba ya Rarrashi Ashman Ya Bama saleem Hakuri, Shima Saleem Saida Aka kai ruwa rana Sannan Ya yafe ma sa, muna**kai dama Duk sunyi kewan Juna.

Daddy Ajmal yace tunda An rufe asibitin da suke aiki, ya samawa Ashman ,Aeesh saleem da Maryam aiki a asibitin da yake aiki a Chan ƙasar EGYPT inda ya baro, Zasu fara aiki bayan Sunyi hutun honey moon ɗinsu a Denmark, suna bukatar hutu suyi clearing duk wani Abun da ya faru a baya tsakaninsu da Faisal, Baffa, Saude and All, they need to start afresh a new Place,Suna buƙatar suyi Nesa da k'asar ,su fara Sabon Rayuwa inda ba wanda zasu kalla su tuna wani bakin cikin da ya faru dasu a rayuwa, babu wanda zai cutar dasu da kowane manufa, su gina Rayuwar su cikin Aminci da k'aunar juna.

Aikam anyi Sa'a duk Sunyi na'am da hakan cikin Kankanin lokaci shirye Shiryen su ya kankama

Bayan wata Biyu.

*EGYPT*


Karfe 12:30 na ranar Laraba, jirgin Egypt na ƙasar Denmark ya sauka a babban international Airline na ƙasar EGYPT , kaman Kowace rana Wajen Cike yake da dumbin ma'aikatan Daketa zarga zarga a kowane bangare sannan ga jirage a zube, wanda da alama mutane basu daɗe da sauka ba yayinda wasu kuma ke shirin tashi.

Ta jerin Parsinjojin dake ƙoƙarin sauka daga cikin Jirgin dake wurin, Ashman ya ziro ƙafarsa dake cikin takalmi kalar Ruwar Brown, iska ya kada gashinsa da ya gyarashi cikin Wani style mai kyau , sannan Idanunsa na sanye cikin Bakin gilashi, ya tsaya daga Inda yake cikin yanayin garin Da hada hadan mutane, Murmushi ya ɓalle a bakinsa da wani murmushi mai zurfi wanda ya jima baiyi irinsa ba, lokacin da Aeesh ta zura hannayenta a tsakanin tafukan hannunsa, yanayin Fuskarsa yayi kyau cikin hasken Ranar da ya fito ta tsakanin hazon da ya mamaye garin Gaba ɗaya yana sanye ne cikin wata doguwar Shirt ƙirar kamfanin jeo Siang, Saleem yayi gyaran Murya ta bayansa, wanda hakan Ya fargar dashi daga Shagalar da yayi yana Kallon ƙasar .

"Idan Ka gama kalle kallen ka bamu waje zamu wuce, ''

Saleem daga bayansa ya faɗa ,sai a yanzu ya tuna akwai mutane dake tsaye a bayanshi zasu fito, guntun Murmushi ya saki Ya sauko sannan Ya matsa masu, suka fito Mota yazo ya dauke su zuwa masaukin su, (Gidan Da Daddy Ajmal ya zauna na tsawon shekaru)


Wata daya chur Sukayi suna Zagaye Ƙasar da nunawa matayen nasu kalar salon Soyayya da kulawansu wanda basu gajiya da nunawa a kowane lokaci ,tuni suka mantar da su kunci na rayuwa, Suka gamsar dasu cewa Rayuwa bayan ƙunci yafi daɗi.

Yau ce Ranar da zasu fara aiki a Teaching Hospital Egypt bayan colleague Daddy Ajmal ya kaisu ya zagaya dasu Ta ko ina na asibitin, aka nunawa kowa Office dinshi.

*Aeesh*
tunda ya dawo daga masallaci bai koma ba, Aeesh ta haɗa Breakfast shi kuma yayi ma Noor wanka, sannan ya tsaftace gidan sannan suka ci abinci, sannan Sukayi wanka

7:35
Yana tsaye Gaban madubi sanye cikin Bandghala Suit Ash color, inner fit ɗinshi baƙi Mai ɗauke da Side vent ta baya, short necktie nashi baƙa.

Yana Tsaye yana gyara guntun necktie ɗinsa ya hangota ta mudubi, ta Shirya cikin Unique Ash scrub ɗinta (Paediatric Nurses scrub) , Fuskarta ɗauke da murmushi ta dau Kwalbar turarensa ta fara fesheeshi dashi kaman Zata ƙarar da ragowar Turaren dake cikin kwalbar yana tsaye idanunsa a Lumshe bai hanata ba, Saida ta gaji don kanta sannan ta Dire , ta ƙarasa matse masa wuyar Necktie ɗinsa, tag ɗinsa Dake jikin Drawer ta dauko ta liƙa masa a Right chest ɗinsa sai ta saki murmushi, a bayyane ta karanta rubutun dake jikin tag din

Sufyaan Shettima (mbbs, bds ,ms, mds)


Shima Murmushi yayi, ya Zaro tag ɗinta, ya liƙa Mata a daidai Left chest ɗinta, a hankali ya furta abinda ke rubuce a tag ɗinta

Mrs Aash Shettima (RN,BNSc)


"Nima InshaAllah sai na kamo Rank ɗinka"

Ta faɗa tana Dire hannunta a ƙirjinsa tana wasa da Tag ɗinsa.

Ya gyara mata zaman Yar karamar Nurses hijab ɗinta, slowly ya furta

"Yarinya kafin Ki kamoni kin zama kaka"





InshaAllah a next update zamu gama for real


Nayi Gabas 🚶🏽‍♀️
Bintou 💞💞



*Saleem*

Ƙarfe 07:19am suka fito daga Gida, Saleem sanye da brown notch napel suit mai milk inner fit sai dan necktie dinshi daya matse wuya dashi brown, Maryam na biye dashi tana gyara masa brown wristwatch ɗinsa yaƙi tsayawa da tafiyan da yake, shi nan a dole yayi latti

sanye take cikin Royal blue scrub ɗinkin company ta saman Right chest ɗinta hospital badge ne manne a nan, daga ƙasan badge din kuma tag ɗinta ne mai ɗauke da sunan Mrs Saleem (RM, RnlN ) hannun rigar ƙarami ne kaman Normal nurses uniform Don haka tasa sleeve dogo har zuwa wuyan hannu, Black colour, kafadarta rataye da Black hand bag Wanda tsabar sauri yasa ya zazzago zuwa gwiwan hannunta

" ka tsaya mana"

Ta faɗa tana jan hannunshi, Wanda hakan ya tilasta mishi Tsayawa.

"Nayi latti fa"
Ya faɗa yana ƙoƙarin kara taku ɗaya.

"Nidai Ka tsaya kaga agogon Ma yaƙi ɗauruwa"

Yaja guntun tsaki yana ƙara taku a hankali, da sauri ta biyoshi a shagwaɓe tace

"Durling Please mana"

Ta faɗa da buga kafarta a ƙasa kaman Zatayi kuka, chak Ya tsaya yana kallon Yanda a lokaci guda fuskar ta ta chanza a shagwaɓe.

Baisan Lokacin da yayi murmushi ba shima jin irin sunan da ta kira shi dashi, zai iya Bata award ta fannin Chanza masa suna a every second of her life, Sunan Da yawa ,idan Ya fara nastyness dinshi Sai ta kirashi da *_My problem_* Anjima ta kirashi da My Scorpion, Big brat , squirrel, in kuma yan soyayyar sun matso tace *Honey* _Durling_ , _My Bae_ ,Baby ,Luna , *My Boo* ,Misty,Coco,Willow ,mine, My forever, Lucy ,Angon Mero,Max ,My chicken 😘,Noor hayateey ,Orea Amor, jaaan, pyaaary.

"Na gama Nasty Doctor, muje"
Ta faɗa bayan ta gama ɗaura masa Agogon

Kallonta yayi na tsayin 6secs, sannan ya janye idonsa

" Kika sake na Rigaki Isa office sai kin raina kanki "

ya faɗa muryarsa ƙasa ƙasa,Tayi Murmushi, sannan yasaka hannunta Cikin nasa tace

"Bazama ka rigani ba"

sai wani kuma d'aure fuska yakeyi yana kauda kai yake, a haka suka nufi inda ya parka motarsa.

A tare suka shiga motar sannan yayi starting din motar yayi reverse suka fice daga gidan suna jin ƙarar motar su Aeesh a dayan Part din Alamun suma yanzu zasu fito.

Tafiyar minti sha biyar sukayi suka isa tamfatse tsen Hospital din., Wanda Shigowan su yayi daidai Da Shigowan Su Aeesh

Tun acikin motar take bin motar su saleem din da kallo tana tana Murmushi.

A tare sukayi parking a Inda aka Tanada wajen parking, duk Suka fito a tare , Fuskar Ashman Ƙame cikin baƙar spec, Ya zura hannayensa Duka a aljihu, Aeesh ta zuro hannunta a tsakanin Hannunsa dake zube cikin Aljihu, Saleem da fitowansa kenan ya tabe Baki,a ransa yace yarinyar nan Batada kunya, lallai Allah ya haɗa Yayan nan Nashi da jarabawa, shi shuru Shuru mara son hayaniya , komai nasa a nutse yakeyi, ga jan aji tamkar wani mace, kai ka rantse jinin mulki ke yawo a jikinsa ne tsabar k'asaita da izza, saɓanin Aeesh da ta kasance Talkative kuma mai son hayaniya, Allah kenan In bandashi wa isa ya haɗa wannan haɗin gambizar😍😂

Gyaran muryar da yayi Bayan yayi locking motarsa, hakan yasa Aeesh ɗagowa ta kalleshi, idonsa a kanta, Dan haka Suka had'a idanu, kowa janye nasa yayi cikeda Basarwa, hk kawai Saita Tsinci kanta da gaidashi

“ina kwana”.

Daidai Lokacin da Maryam ta fito daga nata ɓangaren tana shirin Rufe ƙofa.

Saida yaja wasu seconds sannan yace

“kin tashi lafiya?, Ya baby", Aeesh tayi Murmushi tace "tana Cikin Mota"

Guntun tsaki Saleem ya saki
"Ba ita nake nufi ba, the one in ur Utherus"
.ya fada yana nuna Cikinta da yar yatsa, Maryam Tayi Murmushi ganin Yanda Aeesh ta Zaro ido, da Alama Bata san Tanada ciki ba,Ashman ya watsa Masa Wani irin kallo

"Sa'ido"

Ya furta a hankali muryarsa ƙasa Ƙasa.

Idanun Aeesh a waje tace

"Ahky da Gaske inada Ciki?"

Ta faɗa da gaskiyar Mamakinta, Murmushi Maryam tamata, dan ita dariya wannan shagwaɓar da Sakarcin nata ke bata, ko kad'an bata d'aukar kanta as a nurse ba ,ai In wani yaji Wannan Maganar sai ya ɗauka bata da hankali ne.

Sai ta Dube saleem, suka hada ido ta ɗaga masa gira, Sai duk suka kwashe da Dariya a tare

Kallon Maryam dake dariya Ashman yayi

“gulmammiya dariyan me kukeyi ?"

Gaba tayi tana cigaba da dariyar

"Nasty Nace wani abu?*
Saleem Yana Dariya yace

“ko mun faɗa ai babu abinda zasu mana"

Aeesh ta sake duban Aash wannan karon In a serious note tace

"Ahky Da Gaske inada Ciki?"

Ashman ya harareta alamun tayi shiru yaja hannunta suka wuce

Haka suke wuce ma'aikata cleaners da attendants na Rissinawa, Aeesh ce mai ƙarfin Halin ɗaga Masu hannu, tana dan murmushi while Aash , Saleem da Maryam ko kallonsu basu ishesu ba, Ashman ya haɗe girar sama da na ƙasa .


Suna shiga Out patient Department Su Saleem sukayi Gabas, Aash da Aeesh Sukabi kudu Su kai tsaye zuwa Office ɗinshi.

A hankali take bin Office din Ashman da kallo, everything was intact sai wani sanyin ƙamshin da ke tashi tako ina, a hankali ta ɗaya idanunta ta diresu a akan hotonta dake jikin Bangon Office ɗin, hoton da ZEEYK ya dauketa ne,a ranar da suka fara haɗuwa da shi a Kano Road, dukda an dau hoton ne a lokacin da take cikin damuwa ,sai kuma yayi matuƙar kyau Sosai, sai kuma family picture ɗin su a Gefen nata.

A kan table ɗinsa kuwa yar ƙaramar Hotonsu ce itada Ashman, an Daukeshi ne a yayinda take Tsaye a bayansa tana ɗaura masa Surgical Gown fuskarta ce ta leƙo ta bayanshi, yayinda fuskarsa mai ɗauke da Madaidaicin Saje ya cinye hoton, Sunyi Kyau Sosai, Ta dayan Side na table din Hoton Su ne tareda baby, a tsakiya kuma Wani Ƙaton Tag ne mai ɗauke da sunansa Dr Sufyaan Shettima.

Ba ita keda shift da Safe ba, ta zo da wuri ne saboda Ashman Nada surgery da zaiyi ma Wani yaro da aka haifeshi da tsiro a ƙasan cikinshi.

Su Saleem Sunyi Sa'a a department ɗaya aka ajiye su ita tana Gynea ward shi yana consultant office kusa da ward ɗin , the department was so silent and cool babu hayaniya sosai saidai Ihun dake tashi a hankali ta ɓangaren labour ward, ma'aikata kowa a post dinshi sai masu kai kawo suke jefi jefi, wurin sai tashin qamshi mai hade da sanyin ƙamshin ko wane asibiti yake.


Jin anja hannunta yasata dawowa daga duniyar tunanin data Lula, sai yanzu ta lura da ashe sun shigo Office ɗinshi

"Start ur work"

Ya fada da sakin hannunta,Ta rausayar dakai Yamutsa fuska

"Work asin?"

A hankali yayi taku zuwa Wajen table ɗinsa, ya zauna ya ɗora Ƙafarsa ɗaya kan ɗaya yana wani Lumshe idanu.

"Serve ur husband break fast"

"Acici"

Ta faɗa tana jan Kumatunsa kaɗan, sannan Ta fice da sauri tana jinshi yana cewa tayi a hankali Kada ta illata masa embryo, Ta jima sosai Sannan ta dawo, a lokacin kuwa har ya fara attending Ma wasu patients.

Ta tsaya tana kallon bayan Matar dake zaune tana Faman Zubo masa zance,tana masa bayanin ciwonta,Saida yaja wasu seconds sannan ya ɗago ya dubeta, ya mata nuni da ta Dire abin hannunta akan table, turo baki kawai tayi matareda ta ƙaraso ba tayi zamanta a kujerar bayan matar tayi shiru.

Tana gama zayyano bayaninta ya rubuta mata magunguna, tareda Shawarwari yanda zata kiyaye lafiyarta, cikin natsuwa a hankali yake bayanin don Ko Maryam da take kallonsa bazata iya Cewa ga abinda yace ba, da alama Matar taji daɗin shawarar da ya bata, Har zata tafi ta tsaya tace ya bata numbern shi ko gaisawa su rinƙa yi.

Da mamaki yake kallon matar, kafin ya lalubo amsar da zai bata har yaji Maryam tana cewa

"Number na ya kamata Ki ƙarɓa, Am his PA"

Matar ta dubeshi, ya ɗage mata gira Alamar Eh Haka ne, daga Nan bata sake cewa Komai ba ta fice Ranta a ɓace...

Tsaki Maryam tayi, ta raka bayanta da harara a karo na farko da taji ta tsani Aikin Saleem Kenan idan bata nan Haka mata ke tambayan Numbern sa ,shima Kila yana Basu🤔, In kuma baya basu batada tabbacin zai iya kare kanshi daga Makircin wasu.

Shuru sukayi babu Wanda yasake magana bayan ta ajiye masa abin kari, yanata aikin latsa system dinsa Fuskar sa a murtuƙe don ya lura hakan kadai ne mafita a gareshi idan ya sake ya tanka mata a wannan Lokacin, bazasu rabu ta lalama ba.

Kusan mintuna biyar suna a haka, bakajin komai a Office din sai ƙarar AC, ita dukma sanyin ya isheta,sai satar kallonsa take da mamakin wannan halayya tashi, ya mata laifi maimakon ya Rarrasheta,amma ya fuske Kaman Baisan tanayi ba


batareda ya ɗagoba yace
“me yasa kika daɗe?, Ko Nigeria kikaje haɗo Breakfast din?”.

Tsaki taja aranta, kafin tace

"Ward ɗinmu naje kuma Your attention is needed”.

Idanunsa ya ɗago yana kallonta tsabar kishinsa ya hango kwance cikin idanuwanta, baice komaiba ya janye ya maida ga Tray ɗinda ta kawo masa ,ya zuba Coffee Yana Murmushin Gefen baki

"Is it urgent?"
Ya tambaya yana kai Mug din Coffee Baki.

Batace komai ba, sai kawai ta girgiza kai don Tasan in ta buɗe baki kuka zatayi.

murmushi yayi ya kwantar da kai a kujerar shi yayi irin balancing dinnan nashi sannan ya ɗauko sandwich ya Buɗe zai kai baki kenan idanunsa Suka hango jelar Albasa cikin haɗin da akayiwa sandwich ɗin,take ya hade rai, ta dubeshi da mamaki ya juyo mata pizzan hannunsshi idanunta suka haska mata Albasan da ya gani.

yayinda farkon zuwanta fara aikin sa a asibitin Ashman yashiga flashing a kwanyarta ,Tayi murmushin Gefen baki ta jawo Mug ɗinda ya dire ta ƙurɓi coffee ɗin kadan tace

"Then Trash it"


Ya Yamutsa Fuska yana Jujjuya sandwich din a hannun sa, Sannan Ya maida Complete attention ɗinshi gareta yace.

_"Did you know the kind of people that annoy me in the world?,talakawa Masu aiki a ƙarƙashin Mutum Suna iyayi, Masu ɗaurawa kansu Pride idan an Koresu su gayama duniya ba'a masu adalci ba"_

Ta saki Murmushi wanda ya bayyana Fararen haƙoranta, Ko zata manta komai a duniyar nan bazata mantada wannan kalmar ba, baƙar maganar da Ta fara haɗasu a lokacin, Kalmar da yasata kuka kaman Zata Mutu ,kalmar da yasa taji tsanarsa a lokacin fiyeda komai, ta haddace kalaman a kanta kaman Hadda.

Ta saki Murmushi a karo na farko Tun bayan Shigowan ta tace

"Ni kuma You Know the kind of people that annoy me Sune Mutanen Da zasu shaidawa duniya Basu cin abu daga baya a kamasu Suna ci"....

Ta ƙwace sandwich ɗin
"Idan Bakaci bani inaso"

Ya miƙo hannu Zai ƙwace tayi azamar kaiwa baki ta gutsura, da sauri ya matsota daga zaunen da yake batayi aune ba sai ji tayi ya sauke bakinsa akan nata yana ƙoƙarin ƙwace Na bakinta, kan kace me sunyi kaca kaca da wurin, sun bar duniyar Mu ta mutane, sun lula chan wata duniyar.

Yanzu Ta ƙarfi da yaji Maryam tasa ya dawo yana Son Albasa Kodan Muguntar da take masa, a farkon Komawanta gidanshi haka nan zatayi girki da Albasa, ta kuma Yayyankawa a saman a bincin bayan ya dafu, tun Yana Tsincewa har ya koma yana ci....


Ƙwanƙwasa ƙofar da Akeyi ya dawo dasu Duniyan Bil'adama, A hanzarce duk suka Saita kansu ta koma kan kujerar dake facing ɗinsa, shi kuma Ya shiga danna System ɗinshi a zahiri Kowa ya ganshi zai ɗauka wani abin yakeyi, but in Real Bai ma Gama dawowa cikin hayyacinsa ba, a hankali maryam ta bada izinin a shigo , Colleague ɗin Maryam ce, an sake aikota ta Kira Gyneacologist on Call.

Bata ida fadar abinda Ya Kawota ba ya daka mata wata razananniyar tsawa, wanda ya motsa yan hanjin Cikinta, hatta Maryam Dake zaune gabansa Saida Ta Tsorata,jiki na rawa Sistern ta fice .

Tana fita ya jingina kansa a jikin kujera yana sauke numfashi.

"My Nasty...."

Ta ambaci tsohon sunanshi a hankali, ya buɗe idanunsa akanta.

"Please muje ka duba ta, her condition is Shoulder dystopia Tunda kaga an aiko kasan abin yafi ƙarfinsu ne, don Allah ka tashimuje"


"Then ku meye aikin Ku a wajen....?, Quacks..!"

Harara ta Galla Masa, yanda taga yayi maganar Tasan Baiyi niyyar zuwa ba, Ta miƙe a hankali ta Zagayo gaban deck ɗinshi, ta ture System ɗin Gabanshi ta haye kan kujerar, ta Saita idanunta cikin Nasa ,saida ta tabbatar saƙon da take ƙoƙarin aikawa yakai inda aya kamata sannan ta saki Wani k'asaitaccen murmushi , takai hannu tana shafa sajensa zuwa gemu, cikin d'age gira da salon jan hankali tace

"A duk sanda nake gaban table ɗinka Ni Nurse ce a ƙarƙashin ka, but idan na ketaro Table ɗinka am no more a nurse

Sai Ta sausauta Murya
"Am now Oga's Wife"

Kasa Motsawa yayi duk ta gama kashe masa gaɓoɓi da salonta, Ta kama Hannayenshi ta miƙardashi tsaye, ta ɗaure fuska cikin sigar bada umurni tace.

"Let's Go....."

Kamar Raƙumi da akala haka ya bi Bayanta, har Labour ward ɗin, A lokacin har sun ceto yaron , sun karɓi Haihuwar, Daɗi kaman Ya kashe Saleem 💃💃

Yanda ta jawo hannunsa izuwa Labour ward ɗin haka ya ja nata zuwa Office ɗinta, da Daɗin baki ya ɓata Mata Lokacin ta...


Bari Mu leƙa masarauta mana

Rayuwar Deejah a masarauta ya zame mata wani gagarumin abu, wanda bata taɓa zaton Zata tsinci kanta a daula irin Haka ba, ko a mafarki bata taɓa Tunanin Samun Bamalli a matsayin miji ba, ko a da da sukayi Soyayya Tasan Yafi ƙarfinta shiyasa Da suka rabu bata sake waiwayansa ba, Dalili Kenan da yasa ta gaza ja masa aji alokacin da taji ya furta kalmar zai aureta bayan Ashman ya saketa, shauƙi da Zumundi suka mamaye ta, ta kasa haƙuri har sai da ta nuna zumuɗinta a zahiri.

Shima a ɓangaren nasa wani irin so da ƙauna yake nuna mata, yasan ya rasa Aeesh wacce yake mutuwar so, wacce ta tsamoshi daga bahaguwar rayuwar da yakeyi a baya, kafin Rashin ta ya sake maidashi ciki.

Tabbas Allah yayi masa gata, ya damƙa masa Deejah a sabuwanta, wanda hakan Yayi matuƙar bashi mamaki ko a mafarki bai taɓa sawa a ranshi zai auri budurwa ba, saboda ɓatancin da ya daɗe yanawa yaran Mutane.

Hakan Yasa Ya maida Gaba ɗaya Kulawan sa a gareta, baya So yaga tayi ko tagumi ne yanzu zaiji dalili, a halin yanzu da take da ciki sai kulawa da soyayyar da yake mata ya ninku akan nada, ji yake kaman Ya maidata ciki.

Mai martaba yaso yayi Murabus ya bar ma Bamalli karagar, Amma sai yace a'a fa koda zai karɓi mulkin Sai Matar sa ta haihu, hakan Yasa mai martaba ya shirya Masu Tafiya zuwa EGYPT inda Deejah zatayi Ante natal ɗin ta har ta haihu, don Gujewa masu Sharri na Masarautar su.

*_4:00pm_*


Dukkan mai ruwa da tsaki akan wannan masarautar ya hallara a gaban motocin da za'a kwashi jama'a, ana idarda Sallar Subh kuwa aka fara tafiya.

Deejah dai tana d'aki bata fitoba, hakama Bamalli saida ya dawo Sallah sannan yafara shiri ma shi.

Saida kusan kowa ya kimtsa sannan iyayen gayya suka fito.

Deejah ce tafara fitowa, kuyangi Uku Na d'auke jakarta a bayanta, yayinda wasu kuma ke take mata baya, a babban falon sashensu suka tsaya jiran fitowar mai girma Bamalli, uban Gayya.

Tunkan ya fito daddad'an k'amshinsa ya fara isowa, saikuma sautin takun takalminsa da ta biyo baya.

Yana gaba Wani bawa na binsa a baya, Tunda ya fito Kuyangun duk sukayi ƙasa da Kansu, yayinda ya k'araso sai suka zube k'asa suna kwasar gaisuwa, hannu kawai ya daga musu amma ko kallonsu baiyi ba, idonsa akan Deejah wadda itama ta risinar da idonta tana masa kallon ƙasan ido, mai cikeda so da ƙauna.

Ba k'arya yayi matuk'ar k'yau, komai nasa Brown ne,, kuma kayan sarauta ƴan asali, harda rawanin daya kuma fiddo ainahinsa Na jinin sarauta, rawanin ya sakaya sajensa hancinsa zuwa bakinsa kawai ake iya gani, idanunsa .

Juyawa yayi ya kalli bawan dake gefensa, bawan ya fiddo Alk'yabbar dake cikin bag d'in hannunsa , ya warware alkyabbar ya matsa gaban Deejah dake tsaye har yanzu, yayinda kuyangunta ke a dur kushe har yanzu suma.

Matsawa yayi jikinta tamkar zai rungumeta, daddadar ƙamshin turarensa ya cika hancinta ta lumshe idanu, ya sako alk'yabbar ta bayanta, bawan na gefe yanata zuba murmushi don Suna burge shi sosai.

Tamkar sokuwa haka Deejah ta tsaya har Bamalli ya gama saka mata alk'yabbar a jiki, ya juya Bawan yakuma bashi turaren dake cikin jakkar, feshi ya shiga yimata da turaren, zuciyarta sai kaikawo take yi na d'umbin mamaki da al'ajabin wannan salo, tunda ta aure shi babu ranar da za'a wayi gari bazai chanza salon Ƙaunar da yake nuna mata ba, Bamalli kuma salo a wajensa basua ƙarewa Kullum cikin Nuna mata yake, salona soyayya mai narkar da zuciya, kwatankwacin salon soyayyar da ta tsammaci Zata samu a gidan Ashman, Sai gashi Ta samu fiye da haka a wajen Mai martaba Bamalli, mai jiran Gado nan ba da dadewa ba.

Bayan ya gama ya maidawa bawan turaren ya miƙa mata hannunsshi, ta kama .

Haka suka fito a jere, hannunsa Cikin nata Ko kunyar su bayaji, Kuyangi na take musu baya, yayinda Camera men ke bayansu suna zuba musu hotuna.

Motar da Sarki ya bada ita aka bud'e musu suka shiga, Driver ya shiga

Motar ta d'auki shiru tamkar babu wani mahaluki mai numfashi, Bamalli ya zubama matarsa da yake gani duk duniya babu kamarta ido kawai yana kallo, yana Kallon Yanda Ƙaton cikinta ke daɗa girma a duk lokacin da ya dubeta, yayinda hannunsa d'aya ke sak'ala cikin Na ta yana murzayatsunta a hankali.

Itama dai tayi shiru sassan jikinta Na kar6ar saƙoninsa, a iya watannin da tayi dashi ta fahimci Shi din Mutum ne mai sanyin hali, neman Matansa ne da shaye shayensa kawai yaɓata shi

A haka suka Isa har Airport din, suka parka daidai Inda ake ajiye motoci, Wanda ya cika dank'am da motocin da sukayi masu rakiya,

Please Login or Register in order to submit comment