Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta hangoshi chan tsakiyar daki ,Saida ta qaraso sannan ta kira sunan shi a hankali

"Yaya?"

Bude jajjayen idanunshi dasukayi masa nauyi yaayi ya kalleta saiya tashi zaune a kasalance.

Qarasowa Aeesh tayi ta zauna itama daf da shi.

"Yaya lafiya?"

"Yanzu kika zo?"

"Eh, meya samekane? Ji idanunka, ga muryar kama?, ciwon ne?"

"Baby Am Fine"
yafada yana kallonta.

"Kamar ya? Kallo daya za'a yimika asan babu Lafiya,Your eyes are Red, fadamin menene"

Girgiza kai yayi alamun babu komai,Fuskar nan ta koma abar tausayi kaman Karamin Yaro.

"Yaa Saleem ne ko?"

Nanma girgiza kai yayi

"Ko Auren ne?"

Murmushin takaici yayi sannan yace

"Baby please, nace babu komai, bana jindadi ne, kaina ke ciwo"

yafada yana dafe kai.

"To Allah ya sauwaqe taso muje Parlor kasha magani ka kwanta"

Murmushi yayi yasa Hannu ya dan ja Kumatunta Cikin Sigar Raɗa yace

"Cheer up Babe ,Am Kidding Daga Barci na tashi"

Ya ƙarashe Maganar yana Komawa Ya kwanta da Baya.

Mayafinta ta Cire ta ajiye saman Sofa,Sannan Ta kwanta Kusa dashi.

Kusan a tare duk Suka saki Ɓoyayyen Ajiyan Zuciya.

Qurawa ceiling kawai sukayi kowa da nasa tunane tunanen, yau Kwanaki Uku kenan da bataji daga Bakin Aareef ba,Ko ta kirashi baya Dagawa ,Tun randa ta bashi Kudaden Nan ya rage Bata Kulawa kamar Da ,Sosai Damuwa cika mata Kwakwalwa.

Ɓangaren Aashman Kuwa Tunani Yake akan Nauyin Auren Aeesh dake Kansa Gashi babu wanda ya Sanda Auren Hasalima Ya rasa wa zai fara tunkara Da batun ,Idan Ya Gaya ma wani shin zasu yarda?,ta ina Zai fara?,Gefe guda Kuwa Tashin Hankalin sa na daɗuwa da ya tuna bikinsa Saura Two weeks Jiya Abba ya aiko masa da IV, ya ma Rasa Suwa Zai gayyata ta ina Zai fara?.

"Yayana..!"

Sunanshi da Ta kira ne Yasa ya juyo face dinsa ,Itama juyo face dinta tayi suka Fuskanci Juna

Daga mata gira daya yayi mata tare da sakin murmushin gefen baki.

Janye idanunta tayi tareda sadda kai cikin rashin sanin abin yi,Kallon da yayi mata ba ƙaramin kashe mata jiki yayiba.

Dakin ya dau Shiru da Dan wani Lokaci bakajin sautin Komai sai na Iskar ACn dake Ta faman Aiki,

A hankali ta matso dab dashi har suna shaqar numfashin juna, idanunshi cikin nata

Dukda yadda takeji na yanayin kusancinsu ta danne tace

"Yaya baka Son Deejah ko?"

Cikin rad'a yace

"I love her"

Ji tayi wani Katon abu ya soki zuciyar ta,Irin sukar nan Mai tarwatsa Jijiyoyin Zuciya nan take.

Tunowa tayi da Nata Aareef din Yanzu ya rage nuna kulawa kamar da, Haka kawai taji Wasu zafafan hawaye sun Gangaro mata.

Murmushi ya qaqaro Wanda bekai zuciba Still idanunsu cikin juna

"Ko dai Kishi kikeyi?"

Ya fadi hakan yana Karantar Mood dinta.

Saurin Janye Idanunta tayi daga Gareshi ,banza tayi masa Tun tana hawaye harta fara shesheka ahankali.


Jikinshi yayi sanyi Sosai, ya rungumeta Itakuma kamar abinda take jira kenan saita fashe da kuka dakusashiyar muryarta.

Bubbuga mata baya yafara yi cikin sigar rarrashi yana cewa

"Shhhh ya isa hakanan, please stop Yi Haƙuri kanwata, Pls Sorry Yaya bazai Sake Tsokananki ba"

Girgiza mashi kai kawai ta iyayi hawaye na gangaro mata tana Cusa Kanta Gefen Wuyanshi, Cikin Kankanin lokaci ta jiƙa masa Gemu da Hawaye.

Har a lokacin bai Daina Bata haƙuri,Tun Shigowar ta ya fahimci tana Cikin Damuwa kukan da takeyi Shi kadai zai iya rage mata raɗaɗin Kunar da Zuciyar keyi .

A hankali ta fara Sakin Ajiyan Zuciya tana Goge Fuskar ta A ƙirjin sa, bai hanata Ba har Ta gama ,Sai Kuma ta maida Fuskarta Daidai Gemunsa.

Wani cool qamshi takeji mai sanyin gaske wanda hakan yasa taji ta fara Samun nutsuwa Sosai don dama ita ma'abociyar son qamshice.

A hankali yasa Hannu ya ɗagota Sai Ta Ƙamƙameshi tana Komawa,Mamaki ya Kamashi don Irin hakan Bai taba haɗa su da itaba .

batagaji da shaqar qamshinshin Gemunshi ba.

Maida hankalinshi yayi kan gashin kanta da Ya zubo ya malale Ƙirjinsa.

“ihty What's Going on?"

Yafada under his breath tana dorata akan qirjinta tareda rungumeta Gabaki ɗaya

Gyara Kwanciyar ta tayi a jikinsa tana Sauke Ajiyan Zuciya a hankali, hakan Ya tabbatar masa Da ta fara Barci.

Fuskar ta Ya kure da kallo hakan Barci ya daukesu batareda sun saniba....


Saleem Yana Chan Dakinsa Tareda Abokansa suna Celebrating Birthday ɗin daya Daga Cikin abokan su, Sun san Halin Ashman Sarai baya son Hayaniya shiyasa Basuyi Shirmensu a part din shi ba Suka tattara Suka Nufi Dayan Ɓangaren.

Sai bayan Magrib taron Abokan suka Watse ,dawowa yayi Bayan ya Gudanar da Sallar Magrib, Yyi mamaki sosai ganin Aash bai fito ba, Ya saba Ganinshi a sitting Room dinsa yana dan latse latse a system ɗinsa,ko Sallar Magrib baya tunanin ya fito yayi.

Hakan yasa yayi tunanin Leƙashi yaga ko lafiya.

A bakin Kofa yaci karo da Jakarta, Mamaki ya Kamashi me Ashman Zaiyi da Jakar mace?, a iya saninsa Ashman Bashi da Lokacin mace bai taɓa Ganin ya kula mace ba koda Sune suka kawo kansu!.

Haɗiye mamakin sa yayi ya Cusa kai Cikin Dakin nan ma da Takalmin ta yayi Arba a Gefe guda,mayafinta kuma yashe a kasa..............










Thofa

Me kuke Tunanin Zai faru?


Yau akeyinta, sainaga ruwan comments zanyi typing, idan basu gamsheniba kuma zakuji shiru.


Nayi Gabas 🚶🏻‍♀️

July 1st

Bintou ✍🏼

♡ ㅤ   ❍ㅤ     ⎙      ⌲
ˡᶦᵏᵉ  ᶜᵒᵐᵐᵉⁿᵗ   ˢᵃᵛᵉ   ˢʰᵃʳᵉ
[7/18, 9:28 PM] chubby number: 🗡️🫀 *_WUƘA A ZUCIYA_*🫀🗡️
[B l e e d i n g. H e a r t s]


*016*



Haɗiye mamakin sa yayi ya Cusa kai Cikin Dakin nan ma da Takalmin ta yayi Arba a Gefe guda,Nan Gabas Kuwa Mayafin ta ne ke Harararsa.

Idanu Saleem ya ɗago yana kallon dakin sosai, ya lashi leɓensa na ƙasa daya bushe fuskar nan tasa Dauke da Murmushin Nan Tasa Ta yan Duniya a ransa yana Cewa

_Lallai Maan kasan kan Duniya,  Ni dama nasani rashin Auren ka da wuri ba banza ba_

idanunsa ne suka sauka kan ASHMAN dake Kwance a ƙasar Rug Rungume da Wata Bacci Suka hankali Kwance da Alama babu Wata damuwa a tattare da Su hakan yasashi Tunanin wannan Bashine karon su Na farko Ba, da alama Sun saba.

Ko kadan Baiga Fuskar yarinyar ba ,Saboda yanayin Kwanciyar ta, Ta kife kanta ne akan Ƙirjin Ashman Gashin ta ya rufe Gefen Fuskar Ta.

Taɓe baki yayi a fili yake faɗin
_a zahiri ku nuna Kunfi kowa sanin Allah amma a baɗini kunfi shaidan sanin Kan tsiya_

Yayi maganar yana Juyawa Zai fita,Har yakai Bakin Ƙofa Adhan din wayar sa Ta fara Ruri, lokacin Sallar Isha'i yayi.

Sautin kiran Sallar ne yasa Ashman yayi firgigit, dai-dai lokacin Aaeesh Itama ta farka a gigice Tayi Yunƙurin ɗago kanta, Saurin dafe bayanta yayi ya Maidata Jikinsa hakan yasa Ta sake komawa tayi lamo.

Hakan ya saka Saleem dakatawa ya fasa Fita,saurin kallon inda suke yayi , Lokacin Ashman na ƙoƙarin ɗagota.

Karaf ya tsinci idanunsa a kansa, Ashman ya watsamasa wani kallo mai kama da gargaɗi.

Saleem Tsayuwarsa ya gyara har ya zura  hannayensa daya cikin aljihun jeans ɗinsa ruwan toka,Dayan Hannun kuma Riƙe da Wayarsa Yana masa Hoto a sakaye, ƙamshin turarensa na cigaba da addabama ƙofofin hancinsa,

ɗan furzar da huci Ashman yayi yana cigaba da tsatstsareshi da idanunsa masu ban tsoro, gasu sunyi jazur alamun yana tattare da ɓacin ran Shigan Masa daki da Saleem yayi batareda ya nemi izini ba.

Girgiza kai kawai ya iyayi don saura kadan yayi exploding,da kallon Tarr dinda Saleem ke masa.

Kuramashi idanu Ashman yayi sannan ya girgiza kai yace

"Uban wa ya baka Izinin Shigan Min Daki"

Dariyarce ta kufce mashi batareda ya shirya ba yayi saurin sa tafin hannu ya toshe baki yana yi sosai Cikin Son ƙunsa masa Bakin ciki.

Ran Aash a ɓace sosai Ya  kalle Saleem da jajayen idanunsa cikin matuƙar tsawa yace

"Get out! Of my sight ...Get out! Get out idiot!"

Maida wayar Hannunshi Saleem yayi cikin Aljihu yana dariya sosai .

Ganin abin nashi bana qarewa bane yasashi yunƙurin Miƙewa, Aeesh ta dawo Dashi ta hanyar Dafe kafaɗarsa.

Fita Saleem yayi yana cigaba da Kyalkyalewa da dariya sosai, yana fita Aeesh tayi tsalle ta tashi daga Jikin Ashman ta koma Gefe tana zazzare ido, Tun Shigowar Saleem Ta farka tsoro ne ya hanata ɗagowa, har yanzu bata bar tsoron Abinda zai kai ya kawo akan Hoton Da ya daukesu Kwanaki ba.

Murmushi Yasakar mata "kin farka?" tadan yamutse fuska tace

"Am Scared"

Wani irin binta yayi da kallo ganin yadda ta shagwa6e fuska kamar wata baby doll yanajin kamar ya cinyeta don So.

"Hmm babu Abinda Zai faru Tashi Kiyi sallah naji kiran sallahn Magrib".

Murmushi kawai tayi sannan ta tashi tana cewa

"Bari in Fara wanka Tukunna"

Ta juya batareda jiran amsar saba tashiga takawa cikin takunta mai cikeda da nutsuwa ta shige Bathroom.

Binta yayi da kallo qasa qasa ,wani Shu'umin Murmushi ya kufce masa ya maimaita *Bari in Fara Wanka* a ransa yana Mamakin Me hakan ke nufi.

Maida hankalinshi yayi kan agogon Bedside dinsa 8:30pm ya gani Zumbur ya miƙe yana Ambaton Innalillahi Wainnailaihirraji'un duk zaton shi Sallar Magrib ake kira Yanzu a rayuwar Ashman bai taɓayin Barcin Asara Irin Wannan Ba.

Tashi yayi ya Fita, Bathroom Ɗin dayan dakin ya shiga Shima yayi wanka sannan Yayi sallolin a chan ,Yana Idar wa ya fito, Fitowar sa Yayi daidai da Fitowar Aeesh .

Saurin karasowa tayi idanunta na kawo ruwa, idan Ammi tasan nan tazo Har takai warhaka Ai ta banu, Ina zata sa kanta don kunya?.

"Ahky Pls take me home,na Shiga Uku ,Yau Kashe Ni Umma Zatayi"

"Ihty Calm down Bazata yi Miki komai ba, Cire Hijab din ki Sa mayafinki mu tafi."

Komawa tayi ta Sanyo Mayafin da tazo dashi ko jakarta bata Dauka ba ta fito cikin hanzari, yayi gaba tabishi a baya Tana Hawaye sosai .

Kai tsaye Parking Lot ya Nufa ya anan Sukaci karo da Saleem.

Idanu suka tsurama juna da ga shi harsu, tuni idon saleem ya kaɗa yay jazur tamkar an hura barkono, jijiyoyin kansa sunyi wani irin fitowa ruɗu-ruɗu cikin matsanancin Fushi da kishi  ya nufosu yana cewa

"Ke dama haka kike!, Bakida Tarbiyya?”

"Meye haka Saleem Are You out of your Mind?"

Gaba ɗaya jijiyoyin Kan saleem  sun daɗa mimmiƙewa ruɗu-ruɗu, maƙoshinsa sai kaikawo yake a wuyansa saboda tsabar haɗiyar busashshen yawu mai ƙona zuciya.

Ya matse idanunsa tare da rumtse hannu, muryarsa a matuƙar kausashe yace,

“ba Tun yau na fara zargin Kuna aikata Alfasha ba ,Amma gani da Ido ya Kore Min Kowace tantama"

Shaƙo kwalar Riganshi Ashman yayi da sauri, ya Fizgo shi da d'an karfi

"Don't you dare Say that on her ok?! Idan Zaka Yi sukarka da zargin ka Duk ka tsaya akaina"

"Really?, da gaske Aren't you Even Ashame Of ur self?, sleeping With a young Teanager That is Young Enough To be Your Daughter"

"Enough Saleem!"

Ashman ya dakatar dashi a matuƙar kausashe sake shaƙo wuyanshi.

“Enogh for What? Ashman Enough For what?,kai baka Isa in soke ka da aikata Alfasha Ba,Baka isa Ba, Inada hujjar da zan Iya Dakusar dakai!,zan Nunawa Duniya  Ɓoyayyar Fuskar ka Saina Tona maka asiri duniya Tasan  Ko waye kai”

Da ƙarfi Ashman ya sake Shaƙoshi ,Ya ƙume kansa da Jikin glass ɗin Mota ,Hakan yasa Motar ta ɗan yi Kara.

Cikin kakkausar murya yace,
"Saleem na baka Daga Yanzu zuwa Wayewar Gari Ka nunawa Duniya, Idan ka isa In ka fasa Kai na ɗan Halak bane"

"And Ni Saleem Naseer Zan Nuna maka na cika ɗan Halak...."

"N0Ooooooooooooo Pls yaya Saleem kayi haƙuri ka ƙyale Mu ,Mu tafi is not What u think”

“Shut up Let him be,Yayi Duk abinda yaga dama ”

Ashman ya dakatar da Aeesh daga rokonsa da yakeyi,Sannan ya cika masa wuya yana cigaba da faɗin

"Idan baka tona ba kai ƙaramin Ɗan Iska ne"

Ya ƙarashe maganar da hankaɗe Saleem Ya Fadi nan Gefe ,ya buɗe motar ya shiga Itama Aeesh Ta shiga a matuƙar tsorace Jikinta babu inda baya rawa , tsoronta Allah tsoron ta kar Saleem ya tona mata Asiri ,dukda bata san dame ya dogara ba Amma Confidence dinsa Ya tabbatar mata da akwai abin da ya taka.

Tada Motar yayi,ya dan Zuge glass ɗin Motar ƙasa, ya kalli Saleem da har yanzu yake yashe a ƙasa Cikin kakkausar Murya yace

"Kar ka manta Kaine Silar Rasuwar Mahaifiyata ,Ni ba tsarar wasan ka bane"

Yafada 6acin rai sannan Ya figi  motar ƙarfi Tun kan Ya iso security Ya buɗe masa Ƙofa ya fice da gudu.

Bin bayan Motar Da kallo saleem yayi Rai a ɓace yana Ji kaman ya bisu da nasa Motar ya bigesu Duk su mutu ya huta.

Furzar da iska Aeesh tayi ahankali tana komawa ta jungina da kujerar motar Hankalin ta a tashe, Hankalin ta duk ya koma gida Yau kam Ammie sai ta yankata ta soya ta da Man jikinta.

Shi kou Ashman ko kadan bai bari rashin Kunyar Saleem  Ya dameshi ba,Bayaso Batun Ya dameshi ko kadan,Yasan Kansa Idan Yasa Abin arai Babu mai iya rabashi da Saleem A yau Dinnan Don zai iya karyashi.

yana Fitowa Ya  watsar Da batunsa, Hasalima A yanzu ttunaninsa bai wuce ya wanke damuwar da ya gani a Fuskar Matarsa Ba, yasan cikin Damuwar akwai Fargabar Hankalin umma da zai tashi na Rashin Dawowanta da wuri ba, gefe guda kuma yunwar da takeji ya kasa Ɓoyuwa a Fuskar ta, ko kadan Aeesh bata wasa da cikinta duk yanayin da zata shiga bata yarda Ta kasance cikin yunwa.

Ji yayi da So samu ne da ba yanzu zasu koma gida ba, restaurant yaso suje suyi having dinner tare In yaso In sun Koma Gida suce sun Tsaya yin Night duty ne a asibiti ,sanyin Garin ne yasa ya maidota Gida, jiyake baison abinda zaisa surabu daidaida second daya, soyake su dawwama ahaka har abada, Amma da ya Tuna Shi kadai yasan Kullalliyar Alaƙar dake Tsakanin su sai yaji Jikinsa yayi sanyi sosai .

Jin motar ta dauki shiru yasashi kunna disc din motar, kira'ar Sheikh Abdullahi Abba zaria Karatunsa na Suratun-Nisa'i ,Tana Matuƙar Son Kira'arsa ,daddaɗar Kira'ar yafara tashi ahankali amotar.

Lumshe idonta tayi tana Sauraron Sautin dake Fita cikin nutsuwa yana Dada Sanya mata Natsuwa duk a lokaci Guda.

Wani ajiyar zuciya Aeesh ta sauke ganin sun shigo layinsu .

A bakin gate din gidan yatsaya yana sauke ajiyar zuciya.

Dan jimm tayi kamar bazata motsaba saikuma ta sa hannu zata bude murfin kofar tajita gamm.

Juyowa tayi ta kalleshi taga shima ita yake kallo.

Murmushinshi ya sakarmata mai kyau yana dagamata gira daya.

Marairaice Fuska tayi Kaman zata masa kuka

"Don Allah yaya Ka buɗe min,Ammi zata min faɗa"

"Babu Abinda zata maki"

Kauda kai tayi Cikin kuluwa wanda hakan yasashi sakin wani murmushin.

"Ka budemin kofar" tafada batareda tajuyoba

"Bacin Ran duk na menene?"

Yafada yana kallon qeyar data juyamashi

Shiru tayi batace komaiba kuma bata juyoba.

Shima shirun yayi yana aikin kallonta.

Ganin batada niyyar juyowa ko tasake magana yasashi sakin murmushi mai sauti yace

"Alright , i don't mean to annoy you, Muje Na Ba Ammi haƙuri, So now smile”

yaqarasa ahankali kamar mai rada.

Saurin Juyowa tayi a fusace

"Don Girman Allah kar ka biyoni, don Ƙaunar ka da Annabi Muhammad (S.A.W) ka Buɗe min Kayi Tafiyar ka bana so ,Banaso Ka buɗe min"

Ta faɗa cikin Rawar Murya irin ta mai shirin Fashewa da kuka.

Yanda tayi maganar yasa Jikinsa mutuwa sosai, Qara kai hannun tayi a handle din motar ta murda dukda tasan bai budeba.

Jiki a sanyaye shima yakai hannu anashi gefen idanunshi akanta yayi unlocking din kofar.

Ganin haka yasata bude motar tazira kafarta daya zata sauka.

Cak ta tsaya jin an riqomata hannu.

Tsayawa tayi daga yunkurin saukar baterada ta juyoba gabanta na faduwa.

"Are You Sure You Are Okay?"

Shiru tayi kuma bata juyoba.

"Kin hanani Binki,Kin haɗani da Fiyayyen halitta wanda Yafi Min komai da kowa, Nasan Umma Zatayi miki faɗa Sosai ,Banaso ranki ya ɓaci ta dalilina ,Zan Tafi Amma ki tabbata zan dawo Gobe da sassafe don Na wanke ki"

Shiru tayi bugun zuciyarta na daɗuwa sosai, she's feeling somehow, tanajin wani iri iri sosai.

"Ina SON....KI"

Ya fada Emotionally still riqeda soft hannunta.

"Please fr...ee Me"

tafada Cikin kasala muryarta nadan cracking.

Shiru yayi yana kallonta na wasu mintuna sannan ya Cikata a hankali.

Kamar jira take yasaki sai tayi saurin sauka daga motar tayi gaba da Gudu batareda ta juyoba don ko rufe murfin kofar batayi ba.

Binta yayi da kallo cikin wani yanayi harta shige sannan ya sauke ajiyar xuciya ahankali.

Yadan dade anan sannan yafito ya zagayo yarufe kofar, yakoma mazauninshi ya  tada motar yabar kofar gidan cikin Nauyin Zuciya.

dakyar Aeesh tasamu tashige gidan tana tafiya tanajin kafaffuwanta na dan harhardewa Jikinta babu inda baya rawa.

Wani irin abu takeji wanda batasan taƙamaimen menene ba, sosai take jin Kalaman Ashman na Ratsa Ko ina na jikinta ,har yanzu Bata Dainajin Amon muryarsa a kunnen ta ba, Duk Takawar da Zatayi sai kalamansa sun dawo mata *Ina Son Ki*  ga dumin da hannunta ke yi haryanzu kamar yana cikin nashi.

Tsayawa tayi bakin kofar shiga tana qoqarin daidaita nutsuwanta,Ko ina na Parlon yayi duhu Alamun Sun yi bacci ko suna shirin yi.

Hasken Wayarta ta kunna ,Wara manyan idanunta tayi ganin har 9:46pm yayi.

Yanzu me zata cema Umma ya tsaidata har wannan lokacin?, Ina zatace taje?, wasu zafafan Hawaye ne suka Gangaro mata ,Ganin qara 6ata lokaci take yasa ta daidaita Natsuwarta, ta Danna Kararrawar Ƙofar.

Ba'a wani dau lokaci ba aka bude kofar

Ido hudun dasukayi da Ammi yasa qirjinta bugawa tayi saurin sunkuyar dakai cikin fargaba.

Wucewa ciki Ammi tayi batareda ta kulata ba hakan yasa itama tabiyota ciki kamar kazar da kwai yafashemawa aciki gabanta na dukan Uku Uku kaman zata faɗo Daga Ƙirjinta.

Saida ta ida qarasowa ciki taga ashe harda Habeeb a falon.

Gabadaya taji ta daburce don tafiyarma Gagararta yake nemanyi.

Da ido Habeeb yayi Mata Alama da  _Yau kin kaɗe Gun Ammi_ Yana Dan Karkada harshe.

Hakan yasa ta ƙara Tsurewa tsoron da takeji yafi nada Innalillahi kadai take Maimaitawa cikin Ranta.

Muryar Ammi taji tana cewa

“Ga Abincin ki chan kan dinning idan kun gama ku kashe Min wuta"

Tayi maganar tana shigewa Dakin ta.

Saurin karasowa Wajen Habeeb tayi tana cewa

"Habib Me ya faru?, ya naga umma bata ce komai ba?"

"Ke Shurun da tayi ba banza ba, Wlhy yarinya duka zakisha tun ɗazu muketa Kiran Layinki Baki daga ba"

"Innalillahi Wainnailaihirraji'un na shiga Uku"

Dan Dakatawa Habeeb yayi yana dan Shaƙar Ƙamshin dake tashi a jikinta.

"Tare Kuka fita da Uncle Aash ko?"

Waro ido tayi shi kuma ya cigaba da faɗin

"Between You And him who hug Who?, kamshinnan yayi yawa"

Ya faɗa yana Kanne mata ido ɗaya.

Saurin Rufe mshi baki Tayi da tafin hannunta tana zare Ido.

"Kai Meye haka? ba Ƙamshin Turare bane”

Dan jada baya Yayi yana dariya.

"Na sani ai Ba ƙamshin turare bane warin turare ne"

Tsaki taja Hankalin ta a tashe,Ta cire Mayafin ta Sai yanzu ta tuna ta baro Jakarta Achan.

Abinci taci Ta shige ɗakinta ta kwanta Takusan raba dare tana tunani da Fargabar hukuncin da Ammi zata zartar akanta Tasan Shurun da tayi ba banza ba, kafin daga bisani barci ya sadado ya saceta.

Ɓangaren Aashman da Saleem ma haka ko da Ashman ya dawo Ko kallon Part din Saleem Baiyi ba ya shige nasa Part din ,Duk Tunanin Abu ɗaya ya hanasu barci Sai Chan Tsakiyar dare Barci ya sacesu.......

Washegari tun da Asuba Ashman yayiwa Gidan Dirar Mikiya, kaman yanda Yayi Alƙawari zuwa yayi Yaba umma Haƙuri ya kuma kawo mata yar jakarta da ta manta.

Ko kadan Umma bata nuna Masa Komai a fuska ba ,Amma wannan karon Tayi Alƙawarin kawo karshen komai.

Tun Da Aeesh taga Yanayin Fuskar Ammi Tasan Bata haƙura ba, Habeeb ta sama ta roƙe shi akan ya rufa mata Asiri suje su ba Umma haƙuri a tare da ƙyar ya yarda ya bi bayan ta bayan ya ja mata rai.

Zaune suka sami umman tana yankan farce ,A tare Suka zube kan Gwiwowinsu kansu a ƙasa.

Kallo ɗaya tayi Msu ta kauda kai,

"We're Sorry Mum"

Suka fada a tare

Binsu tayi da kallo nan take jikinta yadauki rawa.

Shima Habeeb kasa yake kallo fuskarshi fall mammaki zuciyarshi na bugawa.

"Sorry for What?" Suka ji muryarta tsakar kansu.

Kasa dagowa sukayi yayi kallon ƙasan da suke yi

"Ammi... munsan Munyi laifi But we're Sorry"

inji habeeb cikin kwantar da murya

"Laifi? Kenan Tasan Abinda Tayi?, After i warned her"

Tafada cikin sanyin murya tana kallonsu most especially Aeesh data kasa dagowa, idanunta sun sun yi rau rau sosai.

"Tell me Aish, dama keda Maan Soyayya kukeyi?, saurayinkine?  Ina Kukaje jiya? Dama ban isa na Hanaki abu ki hanu ba ?"

Shiru Aeesh tayi don tama rasa da wacce tambaya zata fara, gashi bawani karya ta iya shiryawaba.

"A'isha kinyi shiru, kin san waye Ashman kuwa? Har yanzu na kasa gane Alaƙar dake tsakanin ku,Ki gaya Min Gaskiya !Meke tsakanin Ki da ASHMAN ,A'isha or... are you hiding something from me?"

Sunkuyar da kai Aeesh tayi cikin Raunanniyar murya tace

"Umma babu Komai a tsakanin Mu"

"So Why Are you hanging out With him?, Nan da Sati Biyu zai Angwance ya kyaleki, ya kamata kema Ki koyi Nesanta kanki daga Gareshi ,I know it's not that Easy tun yarintanki bakida Kowa sai Shi, but Try as much as possible Kiyi avoiding kanki daga Gareshi ,Kema Aure Zakiyi nan bada Jimawa ba ,Kuma mijinki bazai Ji dadi ba Idan Yana ganinki tare dashi akoda yaushe,nasan Kina ƙaunar Yayanki Amma Pls Ki taimakeni,ki tayani kare Mutuncin ki, Ki dubi maraicinki ki taimaka min, Kinsan Kaf Duniyar nan bakida Kowa saini sai dan Uwanki da kuma Allahn dake Dafa mana akan Komai ,Kawunku Imam yayi nashi kafin Allah ya karɓi ransa Nima ki taimaka Min Ki bari nayi nawa Kafin Allah ya karɓi nawa Rayuwar, Idan Na tafi babu wanda zai iya Rike min Ku daga Ashman Har Dan uwan nawa, Nafiki sanin Halin rayuwa, Don Haka ba Abin mamaki bane Idan Allah Ya karɓi Rayuwana Ashman Ɗin da kika like mawa ya juya muku baya nasan tabbas Ba abin mamaki bane, duba da yanda Mahaifinsa Da sauran Yan uwansa da ma danginku gabaki ɗaya suka Juya Min baya bayan rasuwar Mahaifinku,Aish don Allah ki kiyaye..."

Sai Kuma Muryarta tayi Rauni sosai Hawaye Na taruwa a cikin Idanunta,Kuka sosai Aeesh da Habeeb Keyi, Ammi ta taɓo Masu Tabon Da suka fara mancewa Dashi, Ammi ta tunasar dasu Su ɗin fa Marayu ne basuda Kowa sai Mahaifiyarsu,Kuka sosai sukeyi harda shessheka, Dagosu Ammi tayi ta rungumesu Cikeda Tsananin ƙaunar yaran nata.

Tun daga Lokacin Aeesh ta dau Alwashin Rage mu'amala da Aash dole Ta koyi nisanta kanta dashi a halin Yanzu FarinCikin mahaifiyarta yafi Mata komai.

Da daddaren Ranar Aareef ya kirata,tayi mamaki sosai don Rabon da Suyi waya , ya kusa sati Sun sha Hira Sosai sai Guraren karfe Biyun dare Sukayi Sallama kowa ya ajiye wayar Cikeda begen Juna.

Bayan Kwanaki Biyu, Aeesh Na asibiti taga Kiran Habeeb ,Mamaki ya kamata don Ɗazu da safe ma saida Suka yi faɗa kafin ta fito.

Daga Wayan tayi tana wani yatsine fuska kaman yana gaban ta

"Ya Akayi ne"

Hankalinsa A tashe yake faɗin

"Sheettty Kizo Umma ba lafiya"

Waro ido tayi Cikin Daburcewa tana faɗin

"Ammi...!, me ya sameta?"

"Ban sani ba ,Tana nima gani Nayi ta fadi Bayan Ta fito daga Ban ɗaki"

Ya fada Cikin dasasshen Muryansa da tasha Kuka.

Hanyar Fita ta nufa Tana Sallallami, Tana Fitowa Tayi karo da Reey ,Tarota tayi tana cewa

"Besty Lafiya?, ina zaki?, me ya faru"

"Ammi ...Ammi "

Abinda ta iya Furtawa kenan Sannnan ta Nufi gate da Gudu,Itama Reey Binta tayii mugun Gudu tana Ambaton Sunanta,Amma ina Ko Juyowa batayi ba.

Securities na ganinsu Suka buɗe musu kofa Duk Suka Fita, Cikin Sa'a Kuwa tana Fita mai Napep na sauke wata mara lafiya a bakin Gate , Gabaki dayansu suka shige Napep ɗin Reey ta gaya masa inda zai kaisu wato Gidan su Aeesh dukda Bata san Abinda ke faruwa ba amma tasan Ammi nada Nasaba da shiganta Wannan halin.

Reey ce take Masa Kwatance har suka Iso Bakin Gidan ,Da Gudu Aeesh ta shige ciki tana kuka Reey tabi bayanta, Hankulan su yayi matuƙar tashi Da ganin yanayin da Ammie ke ciki, da taimakon Habeeb da Aeesh Aka kamata suka Sata a Napep Sai Asibiti.

A tsiyace Napep din tashigo harabar asibitin,Ta faka Nan take Reey ,Habeeb da Aeesh Suka riƙo Ammi ,Already  Doctors da nurses duk sun fito nurses din riqe da dan gadon nan na gurgura marassa lafiya .

qoqarin tattarota Sukeyi amma sun kasa saboda rawar da jikinsu yakeyi ,Kuka Wiwi Aeesh keyi Kaman Cewa akayi Ammi ta rasu.

Ganin Hakan yasa Nurses matsowa suma da taimakonsu aka fiddo Ammie da ta koma  kamar gawa don idan bama lura kayi ba sai kace ma bata numfashi kwatakwata.

Akan gadon aka dorata sannan duk aka shiga turata dagudu aka nufi cikin hospital din.

Duk inda suka wuce sai mutanen dake kai kawo wajen sun tsaya suna kallonsu don ganin yadda ake gurguro gadon ,Nurses na Binshi dagudu,Hakan kadai ya isa ya nuna cewa koma wa ke saman gadon yana cikin very critical condition,Kuma Ba ƙaramin Mutum bane.

Emergency room suka nufa, tun kafin su qaraso aka bude masu

Please Login or Register in order to submit comment