Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya dawo masa Da komai sabo.

*Ashman*

Yana Zaune SADEEQ ya sake Kiransa , Umma na son Magana da Aeesh Kuma cikin Ujila, sbd Jikin ta ya tashi Sosai Daƙyar take iya magana

Bai fahimci halin da Umma ke ciki ba Saida SADEEQ ya Hadashi da ita Video call don Su gaisa Hankalin sa yayi matuƙar tashi da Yaga Halin da take ciki,ko ina na Jikinta Jone yake da na'urori kala kala, kama daga Kanta har zuwa Hannayenta, idan ka ganta a wannan Lokacin sai ka tausaya Mata.

Kashe Wayar Yayi Ya dubi hadarin da Yake taruwa, ya fuzar da iska mai zafi yace

"i think this Girl is a witch, she's a witch, kome nakeyi ita nake gani, eating, bathing sleeping, working anything am doing sai Nayi ta ganinta, i don't know what is wrong with me, but she's is my mind, I've tried my best to get her out of my heart but is not working, Nayi Nesa Da ita But She's Silently Taking Off My breath!, Please Aisha Get off my Life!, Bana Ƙaunarki a rayuwa ta Ki kyaleni Nayi Rayuwa Kaman Kowa, thinking Of you is driving me crazy"

Fitowa yayi Ya Kwala ma Driver Kira.

Da kansa ya buɗe mota ya shiga mazaunin driver, Driver daya ƙaraso ya Durkusa har Ƙasa Jikinsa na Kyarma yace.

“Am Sorry Sir"

Da hannu yamasa nuni da Side din mai zaman banza batareda yace dashi uffan ba.

Driver bashida za6in daya wuce zagayowa ya shiga,Jikinshi babu inda Baya rawa a tunaninsa Laifi yayi ma Ashman yake Son ya kaishi inda za'a hukunta shi.

Da gudu Ashman ya ja motar a dari uku da Sittin, saida suka hau titi sannan ya buɗe baki da ƙyar yace.

“ka Iya Ruƙiyya?"

"Eh Ranka shi daɗe"

Driver ya amsa cike da girmamawa, mamaki fall a fuskar sa.

"Dau Gorar Ruwan nan Ka fara tofa min addu'o'i a ciki, Nasan Kanada yawan Karatun Alqur'ani, inada Tabbacin kasan Abinda nake nufi"

Da tho sale Driver ya Amsa, ya dau Gorar Ruwa ya fara Rera Karatun Alkur'ani Cikin Ruwan.

Kallon Hadarin dake sake haduwa yayi ya Cije lips yana jin Abubuwa na chanzawa a jikinsa sakamakon Sautin karatun alƙur'anin dake Ratsa ko ina na jikinsa, ya kama hanya, cikin salon iya tuƙi ya isa kASU, Zuwa wannnan lOKACIN Ashman Ya Gama Jikewa sharkafff da Zufa, Jikinshi babu inda Baya Rawa ,tuki kawai yakeyi Cikin Fitar hayyaci, garin ya Gama hadewa Za'a iya saukar da Ruwa a koda yaushe.


Hankalin Driver ya tashi kwarai da gaske, dan bai San Abinda Ke damun Ashman ba Alamu dai Sun nuna yana Tattara da Sammu, ko shafin Aljannu ko kuma Taɓin Ƙwaƙwalwa mai Karfi.

Baisha wahalar nemo inda take ba, Map ɗin GPS dinta ne yazama jagoran Nuna masa hanya, da taimakon Driver , Danshi ASHMAN gabaki Daya baya Cikin Hayyacin sa Tuƙi kawai yakeyi Burinsa Ya isar da sakon Ammie kafin Ruwan sama ya sauko.

Fitowar su kenan daga Lecturn Yamma ta gaji Sosai Ga damuwan da take tattare dashi na Rashin Yadda da Areef ya nuna akanta, Sunyi fada da Reey akan Yanda ta damu da batun Areef mutumin da ya lafta mata Mari ya Kuma Furta mata ya tsaneta a baynar jama'a hakan yasa suna Fitowa kowa ya kama hanyarsa.

Parking Yayi ya tura Driver ya kira masa ita, Tayi mamaki Sosai jin wanda yazo nemanta, hakan Yasata je batareda tayi musu ba.

Yana zaune cikin Motarsa ya hango Tahowarta, Take heart beat ɗinsa Ya Chanza ya Fara Rising above Normal

Lokaci daya yar raguwar Annurin Fuskarsa Ta ɓace, Ya daure fuska kaman Bai taba yin dariya ba a Rayuwarsa ,Ya tsani Yarinyar nan baya ƙaunar Ganinta ko kadan ya Tsani abinda zai hadasu waje Guda

Yana Zaune a motar Ya kirawo Driver ya mika masa Wayarsa yace ya bata, Mahaifiyar ta ke son Ganawa da Ita.

hannayenta na Rawa ta karɓa, yana Kallonta ta cikin Motar tayi saurin kara wayar a kunne hawaye na taruwa a idanunta, Sai kuma ta sauke wayar Cikin Rawar jiki, Yana Kallonta ta kunna data da Alama Video call Zasuyi.

Binta da kallo yake idanunsa ya cika da hawaye, duk inda tayi binta yake da Kallo tausayinta na Tsiro masa a zuciya.

Bude kofar Motarsa Yayi a karo na farko, yace ta shigo.

Banza tayi masa ,tayi kaman Bata jishi ba ta cigaba da amsa wayar da takeyi .

Zuciya ce ta taso masa,baya son raini a rayuwa yaga kuma kamar ta koyo rashin Kunya.

Banza yayi da Ita ya Rufe kofar motar sa ya koma ya jingina da Seat din Motar yana Furzar da Huci

Ganin haka yasa Sale driver Ƙarasawa Wajenta yace "Ma'am Oga fa yace ki Shigo Motar"

Daidai Lokacin Network ya Tsinke, Ta bashi wayar, tasa bayan hannu ta share Hawayenta.

"Bashi wayar sa, kace Inada tawa Wayar zan Kir..."

Maganar ta Maƙale Sakamakon Ganinshi da tayi a gabanta.

Ƙamshin Turaren sa ne ya fara sanar da ita tsayuwarsa, ga iskar hadari da ke bada ƙamshin ƙasa.

Bata ta6a sanin tayi missing dinshi har haka ba sai yanzu, jitake zuciyarta na kumbura tana sacewa don shauqi.

Kasa janye idanunta tayi akanshi tacigaba da kallonshi wani emotional feeling na tasomata daga Chan qasan zuciyarta

Shima hakan take agareshi, kafeta yayi da idanunshi kamar zaiyi devouring dinta yana sake jin wani abu Na taso masa daga cikin zuciyarshi.

A hankali iskan hadari ya fara tashi Alamun Za'a iya barkewa da ruwa ako wane lokaci.

Sun kai kusan a minute suna kallon juna kafin Ashman ya kauda Dubansa Daga Kallonta, ya daure Fuska kamar bai taɓa Dariya ba.

Take Hankulan Mutane Ya fara karkata akansu, wasu na Admiring Zallar Matching dinda Sukayi.

Kallonshi tacigaba dayi idanunta na cigaba da kawo kwallar da batasan dalilinta ba harya qaraso gabanta

Sai a lokacin ta sauke idanunsu qasa wanda yayi daidai da digar hawayen idanunta.

Cool voice dinshi taji ya ce
"Come in"

Lumshe idanu tayi Slowly Heart dinta na glowing ta Buɗe Idanunta akansa, ya Allah! Tayi missing komai gameda yaya nan nata, har muryar sa.

Ganin Tana Neman Bata masa Lokaci Yasashi daka Mata tsawa yace

"Hey zaki shigo, ko nai ball dake?"

"Kutt Ji wani irin Soyayya Harda Ball Game"

Daya daga Cikin Masu Kallonsu ta furta.

Ajiyar Zuciya ta sauke, Idanunta tuni yayi ja Jikinta ya fara Kyarma, sai a lokacin jikinsa yayi sanyi bata Son tsawa Ko kadan yanzu nan sai ta nemi ta Birkice .

Meye laifinta don tayi banza dashi?, Atleast She eally cares About him, a Yanda ya wulaƙanta ta a baya yaci ace ta fita daga Rayuwar sa baki daya, amma ta gagara yin hakan, ya kirata kuma ta amsa.

Tsaki yaja yana maida jan lower lip dinsa ciki tareda cijewa gently cike da tausayi ya Kamo hannunta , Undescribable shock ya ratsasu.

"Awwn OMG"
Daya daga cikin yan laɓen su ta furta.

Wani irin Emotional tears Suka digo daga Idanunta, Ta Sunkuyar Dakai kuka mai sauti ya Kufce mata.

Ta fada Jikinshi batareda ta damu da yan tsirarun Mutanen dake Giftawa a wurin ba, kanta ta ɗura a ƙirjinsa tare da cewa

"Ahky"

"Ya Salam This people Wan drive me crazy"

Wani Guy cikin Yan Leke y Furta

idanunsa a rufe a hankali yace

"Ihty" ya faɗa yana sake Hadata da Jikinshi bugun Zuciyarta na tsananta.

Shiru tayi har lokacin jijinta rawa yake, kanta dake ƙirjinsa ta ɗaga idanunta ta sauke a fuskarsa ,Dago haɓarta yayi yana kallon fuskarta hakan yasata saurin lumshe idanunta wanda hakan yaba sauran hawayen damar gangarowa, Murya na rawa ta sake Ambaton Sunansa.

"Ahky"

Tafukan Hannayensa yasa ya tallabo Face ɗinta Cikeda Tsananin tausayinta, bata yarda ta haɗa Idanu dashi ba saima qara gudu da hawayenta sukayi, Shafo fuskarta yayi

"Nine ko?"

Fuska ta kwaɓe tare da ɗaga masa kai hawaye na Cigaba Da tsiyaya daga Idanunta

yace "Am sorry yehr? I don't mean to Make you cry" yafada almost in wishper

Nanma batace komaiba, Haka Idanunta a kulle, ta ki yarda ta Bude ta dubeshi.

"Please open your Eyes"yasake fada amma bata bude ba, Sake Sharo hawayenta dake ta faman Diga yayi.

"Are you angry?" Yasake Furta hakan cikin damuwa

Shiru tayi bata kuma bude Idanunta ba, hannunsa Yasa Ya kara Tarbo fuskarta

"My presence is irritating you ko? ,You hated me ko?,Intafi?" Yaqara tambayarta cikin sanyin murya

Samun kanta tayi da girgiza mashi kai ahankali.

"Then ki bude idanunki please look into my Eyes"

yafada yana janye hannayensa daga Face dinta, hakan yasa tayi saurin faɗawa jikinsa a karo na Biyu, ta saki Marayar Kuka mai narkar da zuciyar mai sauraro.

Murmushi ya suɓuce mashi shima yasa hannu ya sake mannata da Jikinshi Sosai har tana jin Bugun Zuciyarsa a Ƙirjinta.

"Kikikiki Yayyafi Mu tafi kafin Ruwan ya sauko"

Namijin cikin Masu laɓe ya furta hakan, Duk suka watse da Gudu.

Rungumeshi da tayi in Public batareda ta damu da Zirga Zirgan mutane ba ya isa ya ganar dashi yanda Takeji dangane dashi.

Lokaci yayi da ya kamata Tasan Da Aurensa Akanta, ya dace Tasan Matsayinta a gareshi

Qara turata yayi a ƙirjinshi yana sauraron sautin kukanta dake fita ahankali yana Sauraron bugun zuciyarta a qirjinshi

Hadiye wani yawu da ya tokare mshi maqoshi yayi .

Muryarsa na rawa yace

"It ok babe? Stop crying" ya fada softly.

Sake Cusa kanta tayi ajikinshi tana sauke numfashi ahankali tanajin yadda zuciyarta ke swelling in Flying Emotions.

Saitin Kunnen ta ya raɗa mata

"Ke Matata ce, Check the wedding Gift I gave to You, Nasan zaki Yadda dani, Zaki Aminta ki zauna dani..."

Tsawa akayi mai haɗe da Ruwan sama, Wanda hakan yasa Ashman birkicewa.

Da iya ƙarfinsa ya Rabata da Jikinsa yana Numfashi Sama sama.

Ruwan saman da akeyi ne ya sauko da karfi

"Yaya Lafiya?"

Ta tambayeshi a Mamakince.

wani irin firgitaccen zabura ASHMAN yayi cikin tsananin Azabar tsikarin da yakeji a duk ilahirin Jikinshi.

razana yayi ya yunkura da karfi yana wani irin gurnani, ya saki ƙara mai karfi

ganin haka cikin karfin hali da firgici Aeesh da ya Driver sukai saurin riƙoshi tofa masa Addu'o'i.

Ruwan Addu'ar da sale driver ya tofe da addu'a ya dauko ya yayyafa masa.

Da yike Ruwan da akeyi Mai karfine Sosai Kuma Mai haɗe da iska,kafin Ruwan ya diga a jikin Ashman Iskan Ruwan ya tafi dashi.

Aeesh kuwa gaba d'aya jikinta rawa yake Sosai, Kuka Takeyi Sosai harda majina, Gabaki daya jikkkunansu ya Gama jiƙewa da Ruwan da Akeyi.

Zaro Idanu Ashman yake cikin Fitar hayyaci ko ina na jikinsa na Tsikarin shi.

dakyar ya sale ya kamo kansa da hannu bibbiyu da iya karfinshi ya kaishi kasa, ya kwantar da shi a kan cinyar shi dan yadda yake fizge-fizge.

Zuwa wannnan lOKACIN Aeesh was already Out of control, sai tofeshi da addu'a takeyi a hankali kwalla na zuba a idon ta .

Shiko ya Sale yana ruggume da shi a jikin shi Cikin Taɓon Ruwan da akeyi mai ƙarfi gaba ɗaya jikin shi Ya ɓaci da Taɓo, Ruwan Gorar dake hannunsa Ya buɗe ya Zube Gabaki dayanshi akan ASHMAN.

ita kuwa Aeesh cikin kuka mai tsanani taci gaba da cewa.

"Ahky kaine rayuwa ta, ina Ƙaunar ka a rayuwata, kai kadai nakeso ,Kaine komai nawa banida Kowa banida komai, na rasa Komai da kowa a lokacin da nake tsananin buƙatarsu, don Allah Yaya Karka tafi ka Barni, idan Ka mutu nima mutuwa zanyi".

Tana magana ne cikin matsanancin kuka Sosai, bakajin komai a gun sai shashshek'ar kukarta da kuma Karar saukar Ruwan Saman dake sauka Da ƙarfi.

Duk Juriyar Sale ya Kasa rike Kansa, ƙwallah ne idanuwan shi na kan Ashman yana mai wani irin kallo.

Kamo Ashman yayi ya miƙar dashi tsaye da niyyar Maidashi cikin Motarsa.

Baiyi aune Ba yaji Saukar Gigitaccen Mari a kuncinsa

"AMMA!"

Sautin Ashman Ya karaɗe Shurun wurin

Sale bai damu da Marin da yasha Ba, Burinsa ya Kamashi ya shigar dashi Mota.

Ya sake kamoshi wannan Karon Duka ya haushi dashi kamar Mahaukaci yana faɗin

''Saina aika ka inda ka Aika min Amma ta, Sai na kashe ka Zan kasheka kowa ya huta’’

Saurin Karasowa Aeesh tayi ta Rikeshi da iya Karfinta tana kuka.

Wuyanta ya shaƙo da iya ƙarfinsa, ya ɗagata Sama.....

"Ya lalata Miki Rayuwa, Rayuwarki Batada Amfani Saina Kashe ki, Kashe ki zanyi"

Da hannu ɗaya ya dagata sama, yana sake Matse Wuyanta a hannunta.

Waro Idanu Aeesh tayi a galabaice tasa hannu ta Dafe hannayensa Dake Wuyanta tana kakkari Tareda Wulla ƙafafunta on Air.

A Hankali kafafunta suka daina Tsilli, Jikinta ya saki, Dishi Dishi yake gani har duhu ya mamaye Ganinsa yayi baya ya fadi a sume itama ta biyo bayanshi , ta faɗo jikinshi babu Alamar Numfashi a tattare dashi.

"Ranka shi daɗe ! Oga! !, Innalillahi."

Dubansa ya kai kan Aeesh dake kwance luf jikin Ashman d'in a sume babu Alamar Numfashi a Tattare da ita, cikin jin tsoron lamarin ya waiga gaba da baya Babu alamar Mutum ga Ruwan da Akeyi mai karfin Gaske, babu yanda za'ayi ya iya driving cikin Ruwan saboda hadarin dake tattare da yin hakan.

Cikin Matsanancin tashin Hankali ya daga Ashman ya shigar dashi Cikin Motar, ya kuma dawowa Ya daga itama Aeesh ya shigar da Ita, ya tada Mota bayaji baya Gani......✍🏼✍🏼


Nayi Gabas

Share
And
Comment 🙋🏽‍♀️

Bintou ✍🏼

18th August 💙

[10/3, 9:56 PM] Solace: *WUƘA A ZUCIYA*

_BLEEDING HEARTS_



*029*



*POLLOKSHIELDS GLASGOW* _(UNITED KINGDOM)_

"Hmm Sir Rayuwa Kenan, In fa ya kasance Bakada Komai Kaita ganin Wulaƙanci kala kala, Amma lokaci Ɗaya idan Allah ya ɗaga Ka sai kaga Wa'ennan mutanen dake Wulaƙanta ka nason su samu Kusanci dakai, Mu kuma duk sanda Ba'a karɓe mu ba yayin da bamu dashi, saida muka samu Sannan Muka zama mutane tho wannan Alaƙar bamua Sonta, Muma Anzo gaɓar da bazamu so Mutanen da suka Guje mu ba yayinda Bamu dashi"

Tayi maganan cike da fada har y
Tana neman ya shakewa,Buban ZEEYK dake tsaye Riƙe da Camera tayi

"Baby na Let's Go"

Adan rude sir hydar yace

"Please Sureey Don't Go Muna buƙatar Irin ku a Companyn mu"

yayi maganan cikin Tashin Hankali, Wannan shine Best opportunity dinda Yake nema, Opportunity din Work offer da client din Delight Television Authority unluckily sai Allah ya hadashi da client ɗinsa da WHO happens To be his Student Wacce ya Wulaƙanta a lokacin Da suke project, Tasha wahala sosai Gurin shi Don Har saida Yasa ta maimaita shekarar,ta kara shekara daya Akan wanda Tayi.

Yana Tsaye Ƙiƙam kaman Gunki,Har suka bace masa da Gani

Ranta a ɓace ta Fito, sai Faman Huci Takeyi, ZEEYK na biye da ita yana daukan Hoton wajen Office din Hankalinsa a kwance .

Saida Takai bakin Motarta sannan Ta lura babu ZEEYK a bayanta, Tsaki taja sanan ta shiga mota ,ganin Tana shirin Tada motar ta Kyaleshi yasa shi saurin Karasowa ya shiga motar,ya jasu yawuce da ita.

yau gabaki daya Ranta a ɓace yake, A gate din ƙaton Restaurant ZEEYK ya Ajiyeta ,suna fitowa suka shiga ZEEYK yamusu ordern Chips da Youghut , juyar dakai tayi tana kallon premises din Restaurant din yanda iska ke kadawa kaman za'ayi ruwan sama, flowers din premises din sai kadawa suke suna making loving sounds, a Hankali ta fara jin Sauƙin Zafin da take ji a Zuciyarta.

tabata ZEEYK yayi hakan yasa ta juyo dakai ta turo baki tace cikin rauni, ta ɗora kanta a ƙafaɗarsa Tana Shessheƙa.

"A'ah Baby Zaki Fara Ko?"

Ƙara cusa Kanta a ƙafaɗarsa Tayi tana Shessheƙa

"Haba Baby Haba Ba Dole ba, Kana gani Ya ci Min mutunci sannan Kuma a gabanka ya harareni,kana Gani ka kasa cewa Komai 😭,Maimakon haka ma sai banza dani kayi Kana ɗaukan Hoto salon kasa ya raina Ni, Shikenan kuma Ni sai kace wata Mara Gata, Uhm,huhum"

Sai ta sake fashewa da Kukan Shagwaɓa Tana goge fuskar ta a kafadar sa

"Haba Baby wane mutum Bayan Kakkausan gargadin da kikayi mai?..."

"Uhn Nide, Nide Meye Amfanin zuwa Tare dakai?, Naje dakai ne fa don Ka zane min shi sai ka ɓige da Ɗaukan Hoto 😩😭"

"Haba Baby Akan Wannan Kike kuka?, No...No..No...No Ai yau ba Shi ba ko Mugun Dad ɗinki ne babu Abinda zai hana in zaneshi ,Taso Kiga Mu koma Office ɗin nashi ,sai yayi min bayanin Dalilin da yasa ya zama Dalilin Zuban Hawayen Baby na, Don Haka share Hawayen ki Muje"

Ya fada yana Ɗagota ya Goge mata Hawaye.

Dariya mai haɗe da Kuka ta kwashe dashi tana cewa

"Daga baya kenan Jibeshi sai Kace zai iya ,Ɗazu ai ina kallonka ko haɗa ido kasa yi dashi kayi kana gudun kayi Motsi ya kamaka a lungu"

Dariya yayi Shima daidai lokacin aka kawo chips da Youghut din, karba sukayi suka faraci saida Sureey Sai Zuba masa Shagwaɓa Takeyi Yana Rarrashinta.

Da ka gansu kaga masoyan asali,Masoyan da suka Lume a kogin Kaunar juna.

ZEEYK Wato Muhammad Zayn Haifaffen Dan Nigeria ne a nan Kaduna , karatu ne ya kawo shi UK, Inda yake karantar Photography wato Fannin Daukan Hoto, tun Shigowanshi makarantar suka hadu da Sureey, Jin Shi ɗan ƙasar daya da Mahaifin ta ne yasa mutunci Mai Karfi ya shiga Tsakaninsu, Daga nan Soyayya mai ƙarfi Ta kulle, Amma ko kadan Mahaifinta ALHAJI Faisal baya Kaunar Ganinta Tareda shi duk kaunar da yake nuna mata , da zarar ya gansu tare Sai ya nuna mata Bacin Ranshi.

Hira suke cikin kwanciyar hankali, Sai Zolayarta yakeyi tana dariya

Dirar motocin da Sukaji a harabar Gurin babu Ƙaƙƙautawa ne yasa, Sureey waro Idanunta a tsorace

"Innalillahi, ZEEYK Dad ,My dad is here"

Kafin Ta rufe baki ta Hango babban yaron Alhaji Faisal , Fuskar nan Babu Rahama , Wasu Kattin Jagajigan maza na biye dashi

wani irin rawa taji jikinta ya dauka tana binsu da kallo daidai dai dai, daga nesa Ta hango dad Zaune cikin Motarsa Yana Kallonsu ta Glass din motar dake Zuge.

arude ta kalleshi heart dinta nawani irin racing da tunda take a duniya batajin zuciyarta yataba irin gudun nan ba Dad Yasha Yin Rantsuwa Akan Idan ya sake ganinta da wani Namiji sai ya kasheta har Lahira kuma tana hango sincerelity suna maganar a idanunsa.

Komawa bayan ZEEYK tayi, ta laɓe Tana Kuka

"Baby Dan Allah ka dakatar dasu Karkasa Su tafi dani 😭, Wlhy yau Dad kasheni Zaiyi, Wayyo Baby Ka taimaka min zasu kasheni"

daga ta Ƙaton cikinsu yayi sama kaman wata kaya tana Ihu suka jefata Cikin Mota,Suka Rufe suka ja Suka bar wurin.

ZEEYK na tsaye ya kasa aikata Komai don ansha zubar masa Da jini akanta ya Tabbata da zarar Ya saka baki Dad Zai sa A kasheshi har Lahira.

Kai tsaye Gida Suka nufa da ita, Kaman Yanda suka Daukota kaman Kaya haka suka sake Daukota suka dire a ƙatoton Parlorn Alhaji Faisal, Banda Kuka babu abinda Takeyi Jikinta har wani rawa Rawa yake yi sosai

Da Ido yayi masu Alama da su fita, aka barsu daga Shi sai ita

kallonta yakeyi sosai heart dinshi na breaking Kishinta Na daɗa azalzaluwa a Ƙahon Zuciyarsa cikin Fushi ya kira sunan ta

"SURAYYA"
dago fuskarta da hawaye yagama wanke wa tayi jin muryan Dad ta kalli Wanda Take gani a matsayin Abban Nata idanunta tsabagen kuka har kumbura sukayi

Wani irin razanannen Tsawa ya daka mata, wanda ya tilasta mata yin shuru batareda ta shirya ba, cikin Huci ya dora da cewa

"So nawa zan Gargade ki akan bana Son Ganin kinyi Alaka da ko wane namiji?, so nawa zan Gargade ki Akan Banason kina Mu'amala da ko wane irin namiji ne?, na lura Kunnenki Hoto ne Basuji Saina Yanka su, tho Bari kiji in Gaya Miki, daga Yau babu ke babu Fita, And idan Kika sake kika Sa ƙafa kika bar Gidan nan Koda wasa Wallahi Saina Kashe ki, kinji na Rantse"

fadawa jikinshi tayi tafashe dawani irin kuka mai kara tana shesheka.

"Wayyo Daddy, Wayyo Daddy na, Dan Allah ka daina Wannan Maganar, Wlhy na daina 😭, na tuba Ka yafe min Bazan Ƙara ba, Nayi Alƙawari as from today I'll be a Good Girl "

dago kanta yayi ya dubeta Cikin ido

"I don't fucking care about Your tears daga yau na soke Zuwa Aiki, and Idan Na sake Ganin Ku tare Bake Kadai zaki ziyarci lahira ba ,tare zaku ziyarci Lahirar Wlhy kinji na gaya Miki, so be careful"..

Daga nan sai ya fice Fuuu, cikin Matsanancin Fushi .

Tana ganin ya fita taja tsaki, tasa Bayan hannunta ta share hawayenta kaman ba ita ta gama Shara kuka yanzu ba

Cikin taɓe baki tace

"Ai kam Fita ya zama dole, nida Baby Mutu ka raba Takalmin Kaza, Haka zaka ganmu Ka barmu Idan Kai ka tsani ka ganmu a tare iyayenshi na sona kuma saina bishi Mun tafi Nigeria a tare saidai Ka biyoni Chan ka kashe Ni, In Yaso Ka daddatsa Naman Jikina ka Rabar ga Karnukan Nigeria, Mugu Kawai 😒"

*NIGERIA*

Tunda Maryam Tayi Mota ta rage Fita da Bike ɗinta, ta koma Fita da Motar, Amma Tana Fita da Bike ɗinta Dadaddare don fita da Bike daddare na Sanya Mata Nishaɗi ta musamman .

Yau Tare Suka Fito da Saleema,Sun kai Kaji wani Company a motar Maryam.

Driving Takeyi Saleemerh na zuba Mata surutu tana Biye mata.

Sunzo dai-dai Flyover zasu ɗauki hanyar gida danger Traffic ta tsaidamu.

Kusan minti Biyar suna a haka, motoci da dama Sun Tsaya basa motsawa ma.

Kiran wayanta Akayi, Duban screen din tayi, Sunan da ta gani Yasa ta saki Sassanyar Murmushi,. Ahankali tasa Hannu tayi Sliding ta ɗaga

"Hello Daddy na"

Murmushi ta kuma saki tana Sauraron dayan bangaren

''Dad Yaya Zayn baya Sona, ya tsaneni, ya kawoni Inda za'a Kasheni ina nan sai Faman Gana Min azaba Akeyi, da Gata na an maidani Mai kazar Ƙarfi da yaji"

Tayi maganar Cikin Shagwaɓa, Shuru ta Kumayi Tana sauraron Abban Nata, Gani nayi ta fashe da dariya tana cewa

"Kai Abba, Ni tun Yaushe na bar Aiki a asibin?, Kuma ai Ba kowa yasan Ni Nurse ce ba, anfi sanina da Mai kaj.....!"

Kasa Karasawa tayi Sakamakon Tozali da Idanunta yayi da na SALEEM ta Side mirror dinta , yana zaune a Motarsa Sai kallonta Tun da yake yauce Rana ta farko da ya fara Ganin Dariyarta,kullum cikin daure Fuska Take, Sai yaga Dariyar ma yafi mata kyau akan fushi ji yayi kaman Karta daina, hakan yasa ya shagala da Kallonta.

Dubanshi tayi take Annurin Fuskarta ta ɓace ɓat ta zuba masa Harara, sai a lokacin ya lura Da Ashe Kallonta yake,daure Fuska yayi Cikin basarwa ya maida Hankalinsa Akan Hanya .

Cigaba tayi da Amsa Wayar da Takeyi,TAASSSS Sukaji ƙarar Harbin Bindiga kaman Daga Sama.

Ihun Maryam ne ya Karaɗe wurin ,cikin tsananin Razana ya juya ya Dube Side ɗinta ,Daidai Lokacin da wani Saurayi ya ƙwace wayar hannunta ya zuba a guje.....

Buɗe Motarsa yayi, daidai Lokacin da Traffic ta bada Hannu, Ganinta Cikin Jini yasa gabasa yayi masifar faɗuwa ga Kukan da Takeyi dake taɓa masa Zuciya a wurin babu Wanda Yayi Ƙoƙarin taimaka Mata, Da alama basu Masan Anyi harbi ba.

Hankalinsa a matuƙar tashe ya buɗe motar ya Shiga ya ɗan matsar da Ita gefe ,Ya zauna a mazaunin Driver, Sai Kuma Ta Rirriƙeshi tana sakin wani irin wahallallen kuka mai taɓa zuciya ,Damtsen Hannunta sai Zubar da Jini yakeyi,kuka takeyi mai ban tausayi, Tana Riƙe da Wurin Jini gaba daya ya Jiƙata ya Jiƙa suturar dake jikinta, Haka saleem shima Suturar dake Jikinshi duk sun Ɓaci da Jini, Wannan shine karon farko data taɓajin mummunan rauni irin haka a rayuwarta, wani masifaffen zafi da raɗaɗi na ratsata, Hankalin Saleem A matuƙar Tashe yaja Motar ya kama hanyar Asibiti, Saleema Sai Kuka takeyi Cikeda Mamakin Yanda Auntyn ta ke shigewa jikin Bawan Allahn nan tana Kuka, Amma da Alama bata Masan Tanayi ba, tsananin Azabar Ciwo ne yasata haka.

A hankali Jiri ya fara rufe Idanunta, duhu ya fara mamaye idanunta, hakama numfashinta sai tattarewa yake waje guda yana dunƙulewa a cikin ƙirjinta, daga Nan bata sake sanin Abinda ya faru ba.

*AEESH*

hankali take buɗe idanunta da sukayi mata masifar nauyi, taɗan motsa kaɗan tana cije leɓe kafin ta samu nasarar sake buɗe ido da ƙyau a karo na biyu.

Drip Stand dindake Manne a Jikin Gadonta ta Zuba ma Idanu

‘‘Asibiti kuma?’’
Ta ambata a hankali tana waigewaige da kallon ɗakin data buɗe ido.

Kamo hannunta da Akayi ne ya sata maida Dubanta Akanshi.

Ashman ne Zaune a kujerar dake bakin Gadon Da Alama ya jima yana Jiran Farkawanta.

"Am Sorry Ihty, Am very Sorry"

Kalmar da ta fara Fitowa kenan daga Bakinsa,Damuwa ƙarara a fuskar sa, yana sake kamo Hannayenta.

"Yayana Me yasa Aka kawo nan, Banida Lafiya ne?"

Ta tambaya tana ƙare Mshi kallo, Dubansa Yakai Kan Machine din SPO2 dake manne a

Please Login or Register in order to submit comment