Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dawo.

Fiddo idanu wajeyayi

"What...?"

Ta lumshe idanunta cikeda Ƙarfin Hali cikin marairacewa tace

"Don Allah ka fara sana'a Koda Yar Provision ne ka fara siyarwa ,bana jin dadin ganinka babu Sana'a "

Saida ya buga wata yar tsalle cikin Murna sannan yace

"inshaAllah I'll try my best Inga Nayi hakan Amma wa ya baki mota?"

Taɓe baki tayi ta dafe kanta saboda jirin dake janta

"Mota ta ce, Akwai takardun Ma a ciki?"

"But Why did you gave it to me?"

"Because I don't need it, kafini Buƙatar shi ,Please kafin Mu dawo ina don inga change "

"Ina zakuje?"

"Canada zamuje Dubo AMMIE na"

"Keda wa?"

"Nida Ahky"

Ya kauda kai yana Yatsine fuska

"I hated him "

Ta tambaya tana dan kankance idanun nata

"Why"

"Shima baya sona"

"C'mon Yaya na ne fa"


"Babe Let's Go..."

Muryar Ashman taji yana Kiranta

Juyawa tayi tana Masa waving Murya chan ƙasa yanayin ta mai ban Tausayi tace

"Please kayi Ƙoƙarin cire Reey a ranka kafin Na dawo "

Ya kauda kai Yana cijen lips dinsa, Muryarta kaman na mai shirin yin kuka tace

"I know it's hard But please try as much as u can, I want to be alone in your heart..."

Daga nan ta Juya ta Shige Motar tana hawaye.

Tsaki Ashman yaja

What comes over him da zaisa ya kai matarsa wajen Saurayinta, suna taɗi a gabansa?

A airport Driver ya Sauke su, ya juya bayan Ashman ya sallameshi Shima.


Wannan shine Karo na Biyar da zata hau jirgi Duk sunda zaije duba Abroad Patient dinsa indai bazai jima ba da ita suke zuwa, amma har yanzu ta kasa sabawa da hawa jirgi.

Lumshe ido tayi kaman me bacci bayan Ta saka seat belt ji take jikinta Yayi mata nauyi, gabaki daya Gaɓɓanta babu inda baya ciwo,yana Zaune Kusa da ita ya saka Headphone dinsa, ya kunna karatun Alƙur'ani mai girma.

A iya tafiyan da sukeyi a tare wannan itace best trip dinsu ,Ko wannensu da shauƙi na musamman da tafiyar ta samar masa sanda jirgi take shirin tashi kuwa a razane ta hantsila jikin Ashman gamida 'kan'kanme shi ta tura kanta cikin jikinsa tana kyarma, sosai yaji a jikinsa da irin rikon data masa dan kuwa sakwanni ne da dama suka jiyarci illahirin jikinsa.

Kallonta yake ganin yanda ta wani razana a ransa yana mamakin randa Zata daina tsoron jirgi , baice mata komai ba har lokacin tana nan makale cikin jikinsa wanda ita kanta batasan tayi hakan ba, saida ya bari jirgi ta daidaita a sama kana ya matse 'kugunta cikin jikinsa sannan ya kai bakinsa saitin kunnenta a hankali yake ra'da mata

"Ɗagani?"

Saurin dagowa tayi daga Jikinsa tana Jan gajeren tsaki a ranta , ya maida ta ya haɗa kanta da ƙirjinsa ya Rungume .

Hawaye ne suka sauko a idanun ta, ta rasa Na menene amma tafi alakantashi da na murnar Ganin AMMIE da zatayi

*CANADA*

Suna fitowa daga Arrival driver ya karaso gamida Murmusawa yana fadin

"welcome sir"

gaisawa sukayi kana ya karbi jakan kayansu ya karasa dashi yanda yayi parking mota, bayan ya zuba kayan a boot ya budewa Ashman back seat ya shige ya budewa Aeesh gefen sa gamida gaishe ta itama ya koma mazaunin dreba yajasu zuwa masaukin su.


Suna isa wani irin Nauyayyen barci yayi awon Gaba da ita , bata farka ba sai gabda magrib , sai a lokacin tayi Sallolin da akayi tana barci.

Bata Ganshi a ɗakin ba,jira take ya shigo yazo ya kai ta Asibiti wurin AMMIE duk tabi ta ƙosa, gashi bata ga inda ya ajiye mata waya ba, balle ta kirata sanar dasu Zuwan su.

Abinda bata sani ba tuni Ashman ya dauke wayar,a cewar sa dirar bazata zasu masu,kuma sai ta warke.

Sai raunin da taji ya bushe.

Wanka take sonshi Da Hijab dinta Ta shiga Bayi, tayi hanging dinshi a towel hanger Tana Fitowa ta maida hijabin.

Don tayi Alƙawarin banda Fuskarta ,hannayen ta da kafarta bazata sake bari Yaga Wani bangare na Jikinta ba,har yasa ya sakejin wani abu aknta.

Da Hijab din ta dinga shafa Mai bayan Ta gama ta zura Doguwar rigar barcinta mai shegen Kauri Wanda ta dauko daga kd Musamman don irin wannan ranar da zata kasance ita dashi.

Ta dau bedsheet kenan Zata Shimfida sai ji tayi Kamar an fincike ta an hada da jikin bango, ta takarkare iyakacin karfinta zata yi ihu aka toshe bakinta da hannu.

Tsabar ruɗewa kasa ganeshi tayi jikinta sai karkarwa yake yi kamar mazari. A hankali ta fara nutsuwa sai a lokacin taji kamshin sa. Ta sauke ajiyar zuciya Still jikinta Babu inda baya rawa.

wani tsoron ne ya shige ta,, Me ya shigo dashi dakin? Nan ta fara kokarin kwace kanta daga hannunsa amma maimakon ya sake ta sai ya saka dukkannin jiki sa ya matseta a jikin bango.

Ta saka hannayenta duka biyun ta tattara karfinta tana tura kirjinsa amma ko motsi baiyi ba, kawai sai ta saka kuka mai ƙarfi, ta kifa fuskarta akan kirjinsa tana ta kukanta, a hankali ya sunkuyo fuskarsa dai dai kunnenta yace

"why are you avoiding me?

Shuru tayi ta Turo baki kanta a ƙirjin sa, take hawaye suka wanke mata fuska

"Ni ba kai bane, Ka Rabani da mutuncina gashi Kuma ka dawo kace da Auren ka a kaina Ni dai gaskiya bana sonka ,bana Son ka, ka kaini wajen AMMIE"

Ta sake kecewa da wani irin sabon kuka

ya sa hannu ya dago fuskrata yace "look at me, and tell me ,ki kalli cikin Kice baki sona"

Ya cikata, Sai a lokacin ta samu damar sakin Kukan da ya toshe mata maƙoshi, ta kife kanta a tafin Hannun ta cikin Kuka tace

"Nide ka Fita bana son ganin ka...you're scaring me"









Nayi Gabas 👨🏽‍🍳

Bintou ✍️

25th Oct
[10/27, 10:11 PM] Bintou abdool: *WUƘA A ZUCIYA


_(BLEEDING HEARTS)_



*043*

3days later

4:00pm

Ashman ne zaune a cikin babban guess house din Abba dake Canada , babu wanda ya san da zaman gidan, Abba shi kanshi ya Manta da zaman Gidan , Saboda sau tari Yakan Gina gida a wata ƙasa, idan Aiki ya kaishi especially aikin da zai daɗar dashi, Amma da zarar ya ida abinda ya kawo shi sai ya siyar, ko ya bada Kyautarshi, wannan Ma haka ne tun Aashman na Danƙaramin Likita ya siya gidan, da suka zo wani Gasa a Nan ƙasar Canada ,Sunfi wata suna fafatawa, bayan Sun Dawo Nigeria ya manta makullan Gidan A hannun Ashman wanda hakan KE nuni da ya Mace da Batun Gidan ma gaba ɗaya.

Gida ne mai kyan gaske wanda gabaki daya unguwar babu mai Kyan tsari shi.

zaune yake kan kujera daga shiga sai 3⅓ Armless Shirt ne a Jikinsa, wanda ya bayyana fafffaɗar ƙirjinsa mai ɗauke da kwantaccen gashi mai kyau.

System ne akan Cinyar sa yana Operating, Communicating yake da clients din sa.

Hutun da ya samu a ƙasar Canada shi ya samar masa Da nutsuwar Replying Emails dinsa.

Ajjiye system ɗin yayi, ya jingina da Kujerar sosai haɗi da lumshe idanunshi.

A yanzu jinshi yake Free babu wata damuwar dake tattare dashi, Tun bayan Rasuwar Aammah (mahaifiyar sa) zuciyar sa bata taɓa samun Relief irin na satin nan ba.

Daukar system din yayi cikin Tafiyar sa mai cikeda natsuwa ya nufi bedroom ɗinsa, ya ajiye,

Sannan ya dawo main Parlor , Room dinta ya zuba ma ido ,, tun da suka dawo ta kasa Sakin Jiki dashi, tsoron shi takeji sosai Ga Wani zabgegen hijabin da Ta Daura ma kanta ,ko kwanciya zatayi da Hijab dinta take, Sam Bata yarda su zauna Wuri daya.

Tunowa yayi da Tun bayan Abincin ranar da sukaci tare, bata sake fitowa ba.

A hankali ya miƙe ya Nufi dakin nata, ya tura ƙofar sallama manne a Harshen sa

Kwance ya sameta tana bacci ta takure waje guda alamar sanyi ya keji, domin sanyi ake sosai a garin ga window da AC duk a Kunne,

Girgiza kansa yayi

_Aeesh da son Iska kaman yar china_

Kulle windows din yayi ya kashe A.C ,babu Kyau bacci bayan La'asar saboda haka a hankali ya isa inda take kwance.

Zama yayi gefen gado , sleeping face dinta ya zuba ma ido,har yanzu Raunin da Deejah tayi mata Bai gama warkewa ba, Kullum sai tayi Kukan akan ciwon, ba akan Zafin ba, sai Don takaicin a gaban wanda yake Ikirarin yana sonta aka mata dukan mutuwa, Alhalin yanada Ikon Dakatarwa ,sai yaƙi tankawa saida aka kusa kawo ƙarshen ta.

Kallon Fuskarta yake, tayi wani ja kaman Tomato 🍅, ga hancinta ya ƙara tsini sosai, yasa hannu ya ɗan Shafa fuskar ta , Amma ko motsawa batayi ba, ya ɗan sunkuyo saitin Kunnen ta ya kira sunan ta

"Ihty...."

Nan ma Shuru, Sake Kiran sunanta yayi a karo na biyu

"Ihty....!!"

Nan ma Shuru , tana jinshi ,Amma barcin da Takeyi ya hanata tanka Masa

ganin Ko motsawa batayi ba yasa ya daddage y Kira sunan da ƙarfi

"IHTY....!!!"

A firgice ta farka cikin tsoro, Sai kuma ta fashe da Kuka Don Ba ƙaramin tsorata tayi ba.

Fuskarsa ya shafa zuwa gemunsa cikin wani irin shu'umin Murmushi kafin ya miƙe yana fadin

"Babu kyau baccin La'asar, in kin Gama Kukan Ki dauro Alwala Kizo Muyi karatun Alkur'ani"

Daga nan yayi ficewar sa, Bayansa tabi da kallo, ta Turo baki a hankali tace

_Allah ya isa_

A zuciyarta kuma ji tayi ta shauƙantu da son yin karatun tare dashi, don ta ma manta Rabonta da karatun Alqur'ani in banda na sallah, Tun bayan AMMIE ta hana tarayyan su Ta rage Biye masa suna aikata abubuwa da dama a tare, ciki Kuwa harda karatun Alkur'ani,tafi jin dadin Karantawa tare dashi shine first Qur'an School Dinta Tanada Records din Ƙira'oinsa Da yawa A wayanta wanda ta dauka a sace da wandanda ta dauka Lokacin sunayi tare, hakan yasa yanzu saidai taji Ƙur'an Audio na Abdullahi Abba saboda Muryarsa tafi kama da Na Ashman.

Kaman Yanda Yace tayi hakanan Tayi, bayan ta dauro Alwala ta Sako zumbulelen Hijabin ta , a falo ta iske shi, Ya miƙa mata ƙaramar Alƙur'ani (don tafi ganema karamar), ya dau babbar.

Cikin Nutsuwa Suka sukayi Musaffa daga Suratul ƙaaf Zuwa naasi , basu Suka tashi ba Saida Aka fara Kiraye kirayen Sallar Magrib.

Fita yayi bayan ya dauro Alwala yaje Masallaci ,A hanyar shi na dawowa ya siyo musu Abinci ,ya Mika mata nata kaman yanda ya saba , ta karba tana Masa godiya .

Daddare bayan ya dawo daga Sallar Isha'i ya iske ta a dakin ta, wannan Karon Dirar bazata Yayi mata, don Haka babu Hijab a jikinta saboda zafin Da ya fara busowa, ga window da AC a kulle .

Tana zaune saman Kujera, Novel ne a saman Table tana dubawa, sanye take cikin baby pink Shirt mai gajeren hannu Da pink karamar Hular sanyi ,sannan Straight dark blue jeans, Gefenta Mugs ne cikeda Yoghurt da zarar ta dubi littafin kadan sai ta Kurɓi kadan.

Gyara tsayuwar sa yayi ,yayi folding hannayensa a ƙirjinsa yana kallon Yanda ta ƙara kyau, hutu da kwanciyar hankali sun Bayyana a Tattare da ita.

Jikinta ne ya sanar da ita ana kallon ta, a hankali ta ɗago ta dubeshi, aikam da sauri ta dau Hijabin ta dake saƙale a kusa da ita.

Tana shirin sakawa taji an Riƙo Hijabin , dubansa tayi da Idanun ta da suka fara kawo ruwa, jikinta na wani irin kakkarwa.

"Please...lemme watch you reading "

Girgiza masa kai tayi, hawayen da suka taru a gefen idonta suka ɗigo, yasa ƙarfi ya kwace Hijabin

"Ki daina jin tsoro na, babu Abinda xanyi miki tunda kince bakiso”

"Nide ka bani Hijabi na”

Cukuikuya Hijabin yayi ya haɗa da ƙirjin sa ya rungume

"Baki yarda dani ba ko?"

Ya fada yana tsareta da Mayatattun idanunsa
Ta sunkuyar da kai, bata so yana Mata irin wannan Kallon yana sata jin Wani irin abu na yawo cikin Jikin ta.

A hankali yayi freeing hannayensa , Hijabin ya faɗi ƙasa.

Ya kamo hannayen ta ya riƙe cikin nasa .

"Trust me babu Abinda xanyi miki, ki gwada Ni koda na Rana ɗaya ne"

Ya fada in a seductive way, ta ɗago Idanunta da suka fara ƙanƙancewa tace

"How...?"

"You want me to prove it?"

Ta Gyada masa kai Batareda tace komai ba, ya sunkuyo fuskar sa saikin kunnen ta ya raɗa Mata

"Mu kwana a ɗakina"

Zaro ido tayi cikin tsoro, ya ɗage mata gira ɗaya haɗida cije lower lips ɗinsa

"Yeah ko Baki yarda dani ba?"

A yanda yake mata magana cikin salon kashe jiki, sai taji ta kasa ce masa komai, banda Tsumar da jikinta ya dauka.

Murmushi yayi, yasa hannu ya dau novel din, sannan yasa ɗayan hannun ya miƙar da ita tsaye, baiyi zaton zata bishi cikin ruwan Sanyi ba, Amma da Ya irin raunon da yayi mata Wanda Zaiyi wuya ta bijire Masa idan ya sauya yi mata wannan Birkitaccen salon.

Chan dakinsa ta bishi, ta zauna Gefen gado , shi kuma ya samu wuri ya zauna A ƙasa ya dora kansa kan cinyarta a haka ya fara karanta mata Novel din daga inda ta tsaya da haka har barci yayi awon gaba da ita.

Jin saukar Numfashin ta ne ya tabbatar masa da tayi barci, ya mike ya shige ban daki yayo Alwala ya gudanar da nafila sannan ya gyara Mata kwanciya a kan gadon.

Shi kuma ya kwanta gefenta, zuciyar sa fall da farin Cikin feeling her next to him.

A hankali ya jawo ta Jikinshi, ya manna da ƙirjinsa, tareda Lumshe idanu, shima da haka wani Ɓarawon Barci ya dauke shi

Chan cikin dare around 3:06, taji farka, tajita a jikin mutum gashi gaba ɗaya an sanya hannu an zagaye bayan ta, buɗe idanunta tayi kaɗan ,ware idon ta ƙarasa yi saboda ganinta kwance a ƙirjinsa, gabaki daya Yasa hannu ya Riƙota kaman zai mai data ciki.

Hannunta ta sanya ta cire hannayensa dake Bayan ta,tare da zame jikinta, ta sanya Pillow ta maye masa gurmin ta, tana kallon yadda yake Sauke numfashi Alamar ya danyi nisa a baccin...

hannu tasa ta kunna hasken bedroom ɗin, fuskarda ta kalla bacci yake sosai hankalin sa kwance, irin baccin nan wanda ya jima baiyi irinsa ba, bata san Ashman da Dogon Bacci ba, don a yanda tasan shi ko wane irin bacci yake da zarar an kunna haske yake farkawa.

_Ahto Yajishi da mace dole bacci yayi dadi_

tsaki taja a hankali ta ɗauke fuskarta daga kallonta. takaicin ya kama ta na yanda tayi saurin yarda dashi harta baro bedroom ɗinta tazo nasa.

Miƙewa tayi tana duba lokaci ganin da saura kafin gari ya waye, ya sanya ta fita daga cikin bedroom ɗin tare da kashe mishi wutar ɗakin, Parlor ta koma ta zauna kan a hankali ta rufe idanunta.

Sosai take jinta wani iri, like she's missing something, kadaici na matukar damunta sosai , She missed her family She miss Them Alot, Tunowa Tayi da rabon da taji Muryar mahaifiyar Ta tajima sosai ,gashi kuma a yanzu babu Waya a hannunta ,Ashman ya ƙwace kuma taki tambayansa Balle tayi Sa'a ya bata .

Babu Abokin hira, kullum da ta tashi tayi sallah sai barci tana Tashi sai kallo Ko karatun Novels har Abin ya fara Isan ta, Da ya zo don Tayata hira take tashi ta bar mishi wajen , bama ta yarda zama ya hadasu duk iya yin shi Saidai ya ƙyale ta.

Babu Abinda baya Siyo mata ba cikin kayan Makulashe duk don Ta rage Kadaici dasu Tunda ya lura tsoron sa ma takeji.

Sun zo ƙasar ne domin Su gaida Umma,amma Sun cinye 3days Without even freshing out.

Lumshe idanu ta sake yi trying to force her self to sleep, amma baccin ya ɗauke a idanunta, saboda Baccin da tasha Dazu.

" Ahky Why Did you changed? Meyasa ka zama ɗan Iska?, Why did you ruin Our joy ,meyasa Zaka aikata babban Kuskure a lokacin da nafi buƙatar ka a rayuwa?, Ada na dauka na damu uba Bayan Rasuwar Mahaifina Ashe Mutuwarsa Ita zata maidani Cikakkiyar marainiya "

Numfashi taja cikeda hawaye

"AMMIE kin yi gaskiya ,Kince Bazan gane Ni marainiya bace sai Bayan babu ke, gashi Da ranki ma Madadin Ubana ya Bayyana Mugun muradin sa a kaina kiyi haƙuri AMMIE na sadaukar Da budurcina ga wanda bai dace ba...."

Nan take wani irin Kuka mai ƙarfi ya ci ƙarfinta, Ashman dake tsaye Tun bayan Fitowar ta Ya sauke ajiyan zuciya, jiki a mace ,Aeesh tana Cikin matsanancin Duhu shine hasken da zai iya fidda ta, amma Baya jin zai iya fitar da ita da kalaman Baki, Boxes Guda biyun da ya bata Sune zasu fitar da ita, Ya dau Alwsshin da bakinsa bazai sake wahalar da kansa ba wajen yi mata bayani Domin Ya lura Ko sau dubu Zai dinga nanatawa yana Rokon ta ta amince bazata yadda ba, ya rasa ina Aeesh ta Koyo rashin yadda Da kuma kafiya wanda da Alama shi kaɗai take ma hakan.

Kusan duk A tare suka dauro Alwala Amma cikin ɗakunan su,suka Fara gudanar da Sallah kowanne na Kai kokan sa Gun Allah madaukaki, domin Kuwa adduo'in Mu sunfi karɓuwa a daidai wannan lokacin, a daidai lokacin da Allah da kanshi yake cewa ina Mai neman Yafiya ya rokeni in yafe masa!, Ina mai neman Biyan buƙata in biya masa.

Bayan Ya idar kwanciya yayi saman kujerar dakin duk yadda yaso yyi bacci kasawa yyi, yana nan zaune har aka fara kiran sallah, Cikin nutsuwa ya miƙe tsaye zuwa bedroom ɗinta, Itama ya iske ta zaune kan Sallaya.

Ba tare da ya ce da ita ƙala ba ya fito har lokacin gari bai gama wayewa ba, bathroom ya shiga ya sakarwa kansa shower mai ɗan zafi.

Lumshe ido Ashman yayi a hankali saboda Yadda ruwan yyi masa daɗi a jiki, kashe showern yayi ya ɗaura towel, ya dauko head towel yana dan Tsane Sumansa.

Komawa dakinsa Yayi yana sauke Ajjiyar zuciya ya juya zuwa wajan mirror, cream ya shafawa fatarsa ɗinsa, sannan Ya gyara gashin Kansa, Nan ma Hair cream ya Shafa saida yabi ko ina na Jikinshi da Turaruka kala Kala sannan ya Shirya Cikin wasu kananan kaya panda inner shirt baƙa da Kuma Wata mai Budadden bottons a sama shi Kuma Ash ne ,Kanshi babu Hula Amma gashin nan sai Sheki yake alamun Yasha Gyara.

A parlor ya iske ta tana Kallo, wannan karon babu Hijabin nan a jikinta, tana sanye cikin Kayan Kiya.

"Ina kwana Yaya"

Ta fada tana dan kauda dubanta daga Kallon da Takeyi .

Murmushin jin dadi yayi ya Amsa mata

"Kin tashi Lafiya"

Ta sunkuyar dakai tana wasa da yan yatsun ta ba tareda ta iya Amsawa ba, ajiyan zuciya ya sauke ya dubi Goshinta da har yanzu yake zagaye da Bandage yace

"Jeki Shirya Mu tafi Asibiti "

Wni irin Murmushin murna ta saki tayi dakinta tana tsallen Murna, Bin bayan ta yayi da kallo sai yaji ta bashi tausayi.

*NIGERIA*

KADUNA

Abba fa hankali ya tashi, duk inda yasan zaiga Ashman yaje babu ASHMAN babu Labarin shi, abu mafi tayar da hankali ma shine Wayar sa a kashe yake, gashi Abban Deejah yazo ya zazzage masa kwandon bala'i akan wulaƙancin da Ashman yayi ma diyarsa banda dukan da yayi mata saida ya Korota a gidanshi?, Tho Allah Koma ya zaiyi yaje ya nemo Ashman dole ya bata takardar ta bazai iya cigaba da juran wannan Rashin Imanin ba Akan tilon yarsa.

Ran Abba yayi mugun ɓaci da Ashman ,yaji Kaman ya tsine masa ya huta da zafin da yakeji, amma sai ya rarrashi Kansa bayan zuciyar shi ta ayyano Masa Hukuncin da zartar akansa da zarar Ya dawo.

Baƙin da saleem yayi yasa Gabaki daya hankalin sa ya kau daga Kan Aeesh, Zuwan Su Oukky Yasa Shi zama half husband Saboda Wani irin Kula na musamman da Maryam take bashi, Ko kadan bata so su fahimci Wata ɓaraka dake tsakanin su, Don Idan sun Gano haka Girmanta ne zai zube a idanunsu.

Tare Suka taso da Oukky da Butty tare sukayi makaranta tun a promay,Ohkky da Butty Cousins ne, A makarantar da suke ba'a raba Hostel din maza da na mata Amma akwai banbancin Block Tsakanin Male block da female block ƙofa ce ta raba,Amma tsakar Hostel da harabar duk daya suke amfani dashi.

Tun Maryam nada Shekaru Goma aka kawota Turkish ita kadai, bata san kowa ba tun lokacin mahaifiyar su bata rasu, koda anyi Hutu babu mai kawo mata ziyara dama Kafin Mahaifinta ta rasu Sun Rabu da mahaifin ta, Sakamakon Matsin rayuwar da suka shiga da halin Babu Shine Mahaifiyar ta ta fara Aikatau a gidan Su Saleem, anan ne soyayya mai Ƙarfi ya shiga tsakaninta da Abba ,ganin burinta bai wuce Taga yaranta sunyi Zurfi cikin Karatu ba Shi yasa ya Sa aka sama ma Maryam Da Zeeyk scholarship Maryam aka barta anan Turkish makarantar Su Saleem , Zeeyk kuma aka wullashi chan UK Kannenta Yan biyu Kuma aka barsu a Makarantar Gwamnati anan Nigeria, Batareda kowa ya sani Ba, don ko sau daya Abba bai taba ganin Su Ba, Haka bai bari Saleem Yasan Da zamanta ba,tun farkon Fara Makarantar Su Mahaifiyar su ta Rasu.

Hakan yasa Ya manta da Lamarin su gudun kada A gano alaƙar dake tsakaninsa da Mahaifiyar tasu, Maryam bata san kowa ba, bata saba da Kowa ba sai Oukky da Butty sune abokan tafiyarta, ko a aji Seat dinsu na Kusa da na juna.

Sometimes ma a Gidansu Take spending days dinta, Da haka har friendship nasu yakai tana barin Hostel during holiday ta Kwana a gidan su.

A haka har ta Gama junior Secondary school babu wanda ya taba kawo mata ziyara daga Family dinsu, Dama basu damu dasu ba ,Abban su kuma tuni ya sallama wa duniya su.

A Secondary school Suka hadu da saleem ,san da take junior Class year one, Shi yana Final year Final class , Shine head Student a lokacin, sam jininsu bai haɗu ba ko kadan musamman Yake Ƙago laifi ya dora Mata Don ya hukunta ta don yasan ba bada hakuri zatayi ba, ita kuma Girman Kai ke damun ta Akoda yaushe koda ya Laka mata laifin bata bada hakuri hakanan take zubewa ya mata hukunci.

Ba a Hostel yake ba, tun yana yaro Yake zaman Kanshi dukda Kasancewar Inna saude a chan hakan baisa yaso zaman gida ba, ya tsani duk abinda zaisa ya hada kai da mace, gashi Kannensa mata har biyu Ga kuma uwar su.

Amma saboda ita yake zuwa Hostel Duk in yazo sai yasa yan dakin su sun Wanke bayi, idan kuma yazo ya iske shi a Wanke sai yasa Suyi ma bishiyoyin dake harabar Hostel din wanka Ko kuma su debo ruwa Su wanke Jikin fence na hostel din.

Dukda haka bata taɓa Nuna gazawar ta ba ko a fuska, shi kuma baƙar fatarta ne ke ƙara Buga masa tsanar ta, Ya tsani mace sai guma gata dark skin girl .

Da haka Tayita jurewa har yabar makarantar, tana gama Secondary School ta samu admission duk under Scholarship

Inda take karantar BMSC (Midwifery )sai a lokacin Zeeyk ya fara kawo mata ziyara ,duk a lokacin basu san sanadin rasuwar mahaifiyar su ba.

Oukky shima ya samu Admission Inda yake karantar, theatre art Dama shi ɗan Art ne, Butty kuma sai ya karanci Gynecology.

Saida Tana final year Aka Turo msu video Batareda sunsan wanda ya turo ba, sun Koma Nigeria sunyi reporting case din, Amma sai aka watsar Wai basu da gamdasshiyar hujja ,tun daga lokacin suka duƙufa wajen Nemo hujjar da zasu kama wanda yayi ma mahaifiyar su Kisan Wulaƙanci, ta dalilin binciken da sukeyi ne Zeeyk ya kamu da acute kidney failure daga nan ya koma Chronic , har ta kai Saida akayi cire mishi daya, ga Dayan Ma Ya samu rauni sosai baya iya filtering Waste from the blood sai Anyi mishi dialysis, dukda haka bai daina Neman Hujjar da zaiyi presentating ba, Haka kawai rana tsaka ya kamu da wani ciwo ya zamana baya iya Daga koda hannunshi ne Dole Aka maida shi Nigeria anan Sai lokacin abbansu yasan halin da suke ciki, shine Yayita fadi tashi har Ya samu Zeeyk ya zamu Sauki bayan binciken da Akayi Masa an gano Yana dauke da Brain Tumor Wanda zai iya leading To death at any moment.....

Maryam Bata tashi Sanin Yana dauke da wannan Matsalar ba saida ta Gama karatun ta, hankalin ta yayi matuƙar tashi Sosai _Ga Renal failure ga kuma Brain Tumor_ duk a lokaci daya?.

Wannan shine dalilin da yasa Ta karanci Renal nursing karatu ta fannin kidney (ƙoda) a babban Jami'ar dake Ƙasar.

Anan Suka sake hadewa dasu Butty, Saleem ma a Jami'ar yake karatu a lokacin Bracket shine babban Abokin shi, halayyar

Please Login or Register in order to submit comment