Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

a wuyanta.

"Please Don't Leave Me..."

Ya faɗa Cikin Raunin Murya mai ban tausayi.

Kwantar dakanta tayi a bayanshi tana Sakin numfashi a hankali.

Reey Dake tsaye Tana Kallonsu ta share Kwalla, Sosai Duk suka bata Tausayi,Ko wannensu akwai Muhimmin Abinda yake ɓoyewa dayansa Kuma ba don Komai bawai fadin ne bazasu iya ba, Amma Akwai Muhimmin Abu da ya Shiga Tsakanin Sirrin Zukatan Su subiyun.

"Babe''

Muryar Salem suka ji Kaman daga Sama.

Da iya Karfin ta ta ture Ashman Ya faɗi ta baya.

Saurin miƙewa tayi tana Toshe Bakinta da tafukan Hannayenta Gabaki daya Jikinta cira yakeyi

"Don Allah..ya..ya Saleem Ka...!"

Saurin dakatar da ita yayi da cewa

"C'mon babe Kukan me kikeyi?, Wa ya taɓa min ke?, abinci Na siyo Miki Nasan babu Abinda kika ci Tun da safe Muje Inyi Serving ɗinki da hannuna zakici Ko"

Saurin gyada masa Kai tayi, mamaki ya kama Ashman da Reey, Tun ɗazu Suke fama da ita akan taci abinci amma ta kasa ,Babu yanda Basuyi Ba amma ko kallon Abincin Batayi ba,Sai gashi Daga zuwan Saleem har ta Amince zata ci.

Basu tashi Tsinkewa da lamarin Ba saida sukaga ta Nufi inda Saleem Yake ta karɓi ledojin hannunsa tana faɗin "bari in Taimaka maka da wannan"

Ko kallon Inda Suke batayi ba Tayi hanyar Shiga Ciki ,Zuwa wannan Lokacin kuwa zuciyar Aashman Ya gama kaiwa Wuya, a fusace yaja Wuyan Rigar Saleem Ta baya Hakan yasa babu shiri Ya juyo.

Wani irin Huci yake yi idonsa a matuƙar jazur tamkar ya haɗiyi wuta,muryarsa a kasashe yace

"What have u done to her "

Hannunsa Yasa Ya Cire Hannun Ashman dake rike da bayan Rigarsa ,Yayi masa Alama da ido kan Ma'aikan dake kai kawo a harabar Gurin.

Gyara Tsayuwa ashman yayi yana Kafeshi da Idanu

"Ka wani kafeni da Idanu me zan ce maka?, kaide ka jira isowan Abba Baffa dasu Goggo gobe zakaji Komai Daga Garesu AM sure u gonna recieve the Shock Of ur life see u Then...."



Ya karashe Maganar Da shigewa Ciki Aeesh na Biye da shi, Wani Irin Kuka Reey Ta saki mai ban tausayi, Shikenan Saleem y asirce mata aminiya,yayi nasarar Raba dangantakar dake tsakanin Su😭.










Eid Mubarak 🙏

Allah ya maimaita mana🙏🙏


Comment
And

Share☺️

Nayi Gabas 🚶🏻‍♀️

Bintou ✍🏼

July 10th😉
[7/18, 9:30 PM] chubby number: 🫀🗡️ _*Wuƙa a Zuciya*_🫀🗡️

_(Bleeding Hearts)_


*018*
"Ka wani kafeni da Idanu me zan ce maka?, kaide ka jira isowan Abba Baffa dasu Goggo gobe zakaji Komai Daga Garesu AM sure u gonna recieve the Shock Of ur life see u Then...."

Ya karashe Maganar Da shigewa Ciki Aeesh na Biye da shi, Wani Irin Kuka Reey Ta saki mai ban tausayi, Shikenan Saleem y asirce mata aminiya,yayi nasarar Raba dangantakar dake tsakanin Su😭.

Staff cafeteria Suka nufa ,Da zuwansa Wajen Kowane Ma'aikacin da yazo Cin abinci ya tarkata inashi ya nashi ya bar Wurin Gudun Wulaƙanci, bai taɓa zuwa Wurin ba, Amma sun Tabbata a yanda Fuskar sa ke a haɗe yau marasa Mutuncin sa ne suka motso.

Fitarsu tayi masa Daɗi sosai ,baisha wahala wajen ganin taci Abincin ba tunda dama Yunwa takeji Sosai , Tsoron dake Zuciyarta ya kara taimakawa wajen ganin bata bar komai Cikin Plate din ba.

Tunda ta fara ci yake Kallonta har ta gama ta Ture Plate din tana yunƙurin Amai.

Yamutse Fuska yayi cikin taɓe baki yake cewa

"Kika sake Abincin nan ya fito to ki tabbata zai koma don Wlhy sai kin lashe shi tassss”

Itama kauda kai tayi tana yatsine fuska.

Hasken wayansa ya Kunno mata screen Ɗin wayar.

Hotunan dazu ne ,hannu na rawa ta karɓi wayar Tana dubawa, tabbas Saleem Ƙwararre ne wajen daukar Hoto Saida Ya daidaici Yanayinsu kamin Ya dau hotunan.

Hoton Farko wanda yayi msu randa Ashman Bashida lafiya ,a yayinda yake manna mata Lip kiss ,Amma yanda Ya dauki hoton Babu wanda zai yarda Ba na baki Sukeyi Ba,ya dau Hoton ne dai dai Lokacin da bakin shi ya taɓa Lips dinta , Fuskar ta A Lumshe lokacin,Hannunsa saƙale a bayanta.

Dayan hoton Kuma, Babu Riga a  jikin Ashman Sai men Vest, ita kuma  babu Dankwali a kanta Tana Kwance a ruwan cikinsa,sai Rigar da tasa yyi kamar bargo,half shot yayi Msu daga Fuskar su zuwa kafaɗarsu, ana ganin Hotunan za'a gane Ashman saboda Gabaki Daya fuskarsa Bai Boyu ba, Aeesh kuma in ba Kyakkyawar sani kayi mata ba bazaka ganeta ba ,kuma kallo ɗaya zakayi ma Hoton kayi tunanin Wani abu Suke Aikatawa saboda Gabaki dayansu Hankulansu basa jikinsu a lokacin.

Hannu yasa ya karɓe Wayansa yana Murmushi

"Nasan a halin yanzu Ji kike kaman Ki Soke Ni na mutu Ki huta, tsanar da kike Min ya gaza Ɓoyuwa a kwayar idanunki,haka nima Ƙaunar da nake Miki ya Gaza ɓoyuwa a idanuna, Ki kalli cikin Idanu na zaki ga Soyayyar kice ta dabaibaye su, Ban san soyayya ba ,ada ban yarda da soyayya ba ko wannan Soyayyar da akeji ta uwa da 'da Ni Saleem bansan shi ba, Bana jin komai dangane da tawa uwar wasu Lokuta ma jinake kamar na Maƙureta ta Mutu, Na tsaneta bana Kaunar ta, amma Tana sona, tana Son FarinCikina"

Dan dakatawa yayi ya Furzar da Huci

"Inajin Manazarta na cewa mace nada Daraja ,Ni sam banga darajar da mace ke gareku ba,Kun zo duniya kuna karkashin namiji Gabaki daya rayuwarku Zaku ƙarar da ita ne akan Namiji bakuda yancin kanku har sai Kun koma ga Mahalicci!, Ina daraja ga wanda zata rayu a ƙarƙashin ka!, Tunda nake mace bata taɓa burge Ni ba, Hasalima Ƙyama kuke bani ,Naga matan turawa da dama masu Aji da irin ki marasa aji ,Matsorata da masu dakakkiyar Zuciya sunsha Kawo min Hari akan In kulasu Amma ko kallo basu Isheni ba, Baƙaƙen mata Basua burgeni ko kadan amma kallon Farko da nayi Miki a hoto Sai naji Kin tafi dani, Aeesh I don't know why am telling u this Amma Kinyi Nasarar Jawo hankali na akanki"

Sai muryarsa Ta ɗan yi rauni

"A ranar da na fara ganinki da Ƙyar na iya Rintsawa Na kosa Gari ya waye na sake Ganin kyakkyawar Fuskar ki, Amma daga bisani sai na gano ke ɗin ƙaruwar yaya na ce"

Saurin Ɗagowa Tayi ta dubeshi da jajayen Idanunta da suka koma kamar wuta

"Please ka daina alaƙanta Ni da wannan kalmar ,babu abinda ya taɓa shiga tsakani na shi, Shaidar zina ba Karamin Abu bane "

"Na sani...nasan Babu Abinda ya taɓa shiga tsakaninki da Aash, Amma ke bakida wayau duk inda aka hankada ki nan Kike zuwa Sam bakida Tunani, Ashman kuma yana da wayau sosai a yanda kike biye masa zai iya saki ki biye masa ku aikata abinda ba haka ba, Ki daina ganin kinada masu Sonki dayawa, ki kiyayi alfahari da yawan Masoyanki koda sun kai yawan gashin kanki domin kuwa daga lokacin da Rayuwar ki ta ɓaci anan ne zaki tabbatar da cewa kanki sanko ne tass ba gashi, Kowannensu guduwa Zasuyi su kyaleki, Ni kaina saida na samu tabbacin Ashman baiyi lalata dake ba sannan Nace zan Aureki,Amma da na tabbatar da cewa Ashman yayi lalata dake wlh duk Sonda nake miki na barki kenan Har abada I can't share my woman With someone Else"

Ya ƙarashe maganar da Kallonta Cikin Idanu, shuru yayi na wasu seconds sannan ya cigaba da cewa

"Banyi zaton zan sameki cikin sauƙi ba ,Amma Kasancewar ki sokuwa Ya taimaka min Matuka  ,you're so dull that kin kasa gane ina Rayuwarki ta dosa, kin kasa banbance ra'ayin ki da abinda Zuciyarki keso, Duk inda Rayuwa Ta hankaɗaki nan Kike zuwa bakya tunanin future dinki, tayaya zaki iya tunanin Future ɗinki bayan babu abinda ke Cikin Rayuwar ki Sai Shashanci?, shashancin Da Ashman ya raineki dashi?   ,Bana da burin Auren Sokuwar mace burina na auri mace mai Dakakkiyar zuciya mai Ra'ayin kanta, Amma Don't worry Kasancewar ki da saleem zaisa Kiyi hankali"

Jin tayi shiru yasashi daga kai ya Dubeta,Gani yayi tana shaƙuwa sosai kaman Zata shide.

Taimakon gaggawa Ya shiga bata, Sannan ya dau waya ya kira Emergency unit take aka kawo mata agaji,Cikin Kankanin Lokaci Aka shawo Kan Abin Amma ganin tana buƙatar hutu  yasa suka bata bedrest.

Saleem Bai Saba Zama waje daya ba Shiyasa Yaji Gabaki daya yau ya Takura sosai, Yana ganin ta samu Barci ya fice a asibitin gabaki daya,Daga nan bai sake dawowa ba.

Gabaki daya Ashman bai san abinda ya faru da ita ba saida ,Dr Hilal yake tambayanshi ya Aeesh da jiki , Sai a lokacin Yake ji waita ci abinci yasa ta chucking hakn yasa aka bata gado.

A ranar Habeeb ne kaɗai ya kwana da Umma,Ashman Kuma ya kwana da Ita a dakin, Cikin dare ta farka da zazzaɓi mai zafi Banda kuka babu Abinda Takeyi Gabaki daya hankalin Shi yabi ya Tashi , yasan bata Son Allura Amma Babu yanda ya iya lafiyarta ya fiye masa Komai .

Haka nan yayi Mata Allurar,Ta debo mata Ruwa a kettle da Wani yar garamin Bowl Yasa tayi Alwala tayi sallah a zaune tana idar da Sallolin Ta bingire da barci bata farka ba Sai da safe , lokacin har Ashman ya tafi masallaci jinta tayi garau , Itama sallar tayi, Ta daɗe tana Roƙon Allah yaba Ummanta lafiya kafin daga bisani ta Roƙeshi akan ya Sawwaƙe mata Damuwar da take ciki ya zaba mata Miji na gari.

Ban ɗaki ta fada tayi wanka ,sannan ta zura baƙar sabuwar Jallabiyar da ta gani gefen gado ,Umma ce a ranta tun ɗazu, Allah Allah take ta Gama taje ta duba ta .

Ashman ne ya shigo dauke da ƙaruwar Basket da wata yar ƙaramar Leda.

Kallo ya bita dashi

"Ina zaki?"

"Umma zan Dubo"

"Daga Wajenta nake taji sauƙi sosai Nayi mata Allura , Please kar a bata Komai Yanzu na lura She's allergic To the drug Za'a iya samun matsala.

Murmushi kawai tayi masa ta raba gefensa ta fice ya bita da kallo yana ayyana abubuwa da dama a ransa ,yaji dadin Ganin ta murmure taji sauƙi sosai Dama yasan Shock ne yasata cikin wane hali jiya gefe guda kuwa tunanin Sauyawan da tayi yana cigaba da cin Ransa, Jiya da ƙyar ya iya Rintsawa don Al'amarin Saleem ya fara Tsorata shi, Ya lura ba ƙaramin So yake wa Aeesh ba ,Gashi da Gaske aurenta yake son yayi.

Yana Son ya fitar da Sirrin dake ransa Amma ya kasa,Ashman mutum ne mai Zurfin Ciki sosai Duk yanda kake dashi Ba lale bane kasan cikinsa ba ,Saboda yana ganin Idan Shi ya kasa Riƙe sirrinsa har ya bayyanama wani Koda wanin Ya wulaƙantashi Ya bayyana Sirrin ga wani Bazai ga laifinshi ba, shi kansa ya kasa kare Sirrin shi da kansa Taya wani zai iya adana masa Shi!.

Yana Ganin kaman babu Wanda zai Amince da maganar Aurensu Illa ma kara makansa bakin Jinin da Zaiyi cikin dangi, babu Mai kaunarsa Kaf Family dinsu sai Baffa Imam da Umma sannan Ƙanwarsa  Hafsah(qawwama)  da yanUwansa maza (Su Abdul ,Naseer da Ɗan Uwansa)  ,Amma kama daga kan Abbansa Har Kawu Hamza da matarsa Da dansa Abdul babu Mai Kaunarsa ,Jira Suke Suga Aibunsa Su Ɓata shi, A halin Yanzu babu Abinda yafi Maida hankali akai Samada Nemo shaidun da zai Dogara dasu, a lokacin koda sun ki amincewa babu abinda zai Hanashi daukar matarsa ,Tun WasheGarin ranar da Baffa ya rasu ya tafi Station din yansandan da ya kirawo don Su kama Bamalli Don Su zame masa Shaidu kuma abin dogaro tunda su kadai ya sani ,Amma abin mamaki Sai ce masa Akayi duk Allah ya karɓi rayuwansu Bayan Mummunar hadarin Motar da sukayi Cikin wannan daren, an Shigar da kara akan Al'amarin Tareda Na Rasuwar Baffa, kuma har yanzu Ana Gudanar da bincike kan Dalilin rasuwansu.

A wannan Lokacin Hankalinsa Yayi matuƙar tashi Sosai, yaje Gidan da Aka daura auren Yafi a ƙirga Amma babu Kowa Cikinta ya kuma tambayi maƙota amma sunce suma basu taba ganin Mai gidan ba.

Har ya sadakar Ƙila babu rabon zaman aure a tsakanin su 😌, Amma ganin Bamalli da yayi jiya yasa mishi Kwarin Gwiwa da kuma kwaɗayin Son yar Auren gidan baƙin da aka daura masa.

murmushi yayi wanda ya bayyana loɓar kumatunsa duka biyu, yaja yar Gemunsa a fili ya furta _Kaine Ango ,Mijinta Na har Abada Inshallah_  Aash Mijin Aeesh. 🤭


Tana shiga Dakin Ta tarar Da Habeeb zaune a gefen Umma yana bata shayi a baki , Saurin karasowa Tayi Ta karɓe Mug din tana faɗin

"Ah yaro ka girma ,Ka iya Jinya Tho bari in Taya ka"

Shaff ta mance da Kashedin da Ashman yayi mata na cewa Kar a  bata Komai Yanzu sai zuwa anjima.

Kallo yabita dashi a mamakince

"Ji matar nan ba Ance baki jin dadi bane?, Da daren Jiya nazo na tarar kina barcin wahala"

Zama tayi ta cigaba da ba Umma Shayin Cikin sanyin Murya tace

"Ni dama lafiya ta Ƙalau ,Allah Sarki Umma jiya War haka Muna  tare Muna Breakfast,Allah kenan Allah ya baki lafiya Umma"

Ta karshe maganar Hawaye Na taruwa cikin Idanunta.

Murmushi Umma tayi da kyar ,Babu inda ke iya motsi a jikinta Gabaki daya Jikinta ya kumbura sakamakon Ciwon Odar da take fama dashi,Idan ka ganta dole ka tausaya mata, Ba ƙaramin Juriya sukayi ba wajen Danne Hawayen su don Sun lura Tayi farinCiki da ganinsu Cikin walwala.

Dr Hilaal Ne ya shigo ya dubata ,yana Cikin Dubata Ta fara jijjiga farin Kumfa na fita a bakinta, Cikin Ruɗewa Likitoci suka bazama akanta ,bayan Wasu lokaci Dr Aaryaan Yafito yace

"Gaskiya Madam ta samu Matsala sosai ,Ta haɗa abinci bayan an mata Allurar dake saurin Reacting ga masu irin ciwon nan nata Hakan yayi Sanadin Shigarta cikin mawuyacin hali, wanda a yanzu zata dauki tsayin Lokaci batareda ta san meke Faruwa cikin Duniyar ba, kuma koda zaku fitar da ita kasashen duniya bazata samu ta farka nan kusa ba"

Sabon Kuka Aeesh da Habeeb suka saki, Cikin Tsananin Tausayinsu Dr Ya fice ya basu Guri ....

Karfe Goma daidai Motar su Abba ta dira a Kaduna ,Kai tsaye asibitin suka nufa..

Suma sosai hankulansu yayi matuƙar tashi da ganin Yanayin da Umma ta shiga, Abba har ƙwalla saida Yayi  ,yana matuƙar Son ƙanwar tasa Amma haka kawai Rana tsaka yaji duk duniya babu wanda ya tsana kamarta.

Goggo kuwa Kuka Wiwi takeyi da hawaye harda Majina, Cewa take idan Zasu sun Koma su tarkato mata kwarmatsanta ita dakanta Zatayi Jinyar Diyarta.

Kawu Hamza da matarsa kuwa Suna gefe sai Yatsine yatsine Sukeyi da Alama basu so ganinta a haka tana Numfashi ba.

Mai Aikin Goggo (Inna Yathai) Wacce ta dage akan Sai tabisu ,Itama share hawaye take a fakaice.

Umma Saude Kuwa cewa tayi bazata biyo su ba, Zata zauna da 'ya'yanta mata, in sun dawo ta zo In Kuma Allah bai Nufa zata gaishe ta ba ,Saitazo Ta'aziyya don saleem Ya kirata ya zayyana mata Cututtukan dake Damunta ,Kuma masu Irin Lalurar ta Na dan Jimawa kafin Su Warke, Majority dinsu ma Mutuwa sukeyi.

Da shike Amenity inda aka kwantar da Ammi Ciki da Parlor ne (Ada Consultant Room me) sai daga baya aka maidashi Amenity.

Nan suka baro Umma a Ciki suka fito Parlor suna Hira ,Aeesh da Habeeb na gefe Sun zuba Masu Idanu sai kallonsu Suke, Abba kou sai Kallon Aeesh yake yana jin Sonta na Dada Ninkuwa a ransa, amma da ya tuna Saleem Dan Gaban Goshi Shi zai Aureta Sai yaji Dan dama dama ko babu komai baiyi asarar Ƙaunar da yake mata ba, Tunda Cikin Yaransa wanda Yafiso a cikinsu Shi zai Aureta.

Ashman Ne ya Shigo da sallamar sa ,Turus yyi a bakin Ƙofa Ganin Duka ahalinsa a cikin dakin.

Goggo ce ta mere Baki cikin yar Masifa take cewa

"Kaga ja'iri,Ka tsya bakin ƙofa,kasa Muna shaƙar Gurɓataccen iskan Asibitin ku, wayasani koshi Nuratu ta shaƙa yasa Ta Shiga wani Hali don Naji Mai dogon Wuyan Nan yace Da safen yau idon Ta garau ”

Shigowa Ashman yayi yana cewa

"Kin manta Iskar Guba Muka kunna ta shaƙa..."

Bankado Kofar da akayi ya Hanashi Ƙarasawa,Ya gwara Kai da bango.

Saleem Ne ya Shigo Fuskar nan a murtuƙe Tamau kamar wanda aka aiko wa sakon Mutuwa ,Hannunsa na dama Riƙe da Mug din Coffee Sai tiririn zafi yakeyi.

"Abba Me yasa kazo mana da wannnan ƙaramar "

Ya fada a fusace yana Nuna Inna Yathai da yar yatsa.

"Nice Nan , Nice na taho da ita ,Ita kadai keda imanin da zata iya tayani jinyar Nuratu"

A fusace ya ɗago yana watsama Goggo wani irin harara, yanda idanunsa sukai matuƙar jazur hakan ya kuma ɗagamata hankali taja bakinta tayi shiru

Kallon banza ya watsa ma Inna Yathai

"Ke matsiyaciya!"

Sai alokacin ta dago ta kalleshi suka haɗa ido wani Irin Faduwa gabansa Yyi hakan yasa shi kauda kai batareda ya iya cewa komai ba.

"Saleem, Baka maraba da zuwana ne?"

Nanma shiru Saidai bebari ya sake Kallonta ba.

Narke fuska tayi cikin Raunani Zatayi magana Ashman ya rigata

"Saleem, why are you giving her tough time? Meyasa kakeda riqo?, Meyasa ka tsaneta?, Nasan tayi kuskure ada da ta shiga gonar ka But menene Laifi don Mutum ya nuna kulawarsa Akanka?, Ta nuna Kulawarta akanka ka Nuna ka tsaneta ta fita harkarka Meyasa Kaima bazaka fita nata harkar ba?,  izuwa yanzu ya cancanta ace ka san Matsayin ta agidan Ya Wuce na yar aiki She's like a mother to us"

"Dakata Maan, Ka daina alaƙani da wannan Matar Kowa ya tsaya a matsayin shi, Itafa ba kowa bace face Yar aiki , Kaskantacciyar Yar Aikin tsohuwar Gidan Mu, batada daraja a gurina Ko kadan , Don Allah baiwar Allah ki taimakawa Rayuwata ki fita bana son ganinki"

Ya fada Cikin Ɓata baki yana kauda kansa gefe.


"Saleem.."

"Look woman, please get out, why zakizo kina irritating dina? ,Abba Is either ta Fita ko Ni In Fita "

ya fada cikin Fushi yana kallon Abba.

"Look Woman, this's a family moment please get out"

Inji Abba

"Out or I Call the security"

Saleem ya karɓe

"Yanzu Saleem Innar mu kuke kora? Harda kai Naseer?, Ka manta ko ita wacece?, Ka manta taimakon Da tayi mana a rayuwa?, Ka manta alfarmar da yasa ta zama yar aiki na?, Yanzu Ita zaka kora don Kaniyar ka?"

Cewar Goggo

"Mum Babu yanda na iya This's family moment Bai kamata taji tattaunawan muba"

"Da kai da Pami Din naka na hada Naci Kaniyar ku, Ita din ba dangin Mu bace?, ko so kake in tuna maka Sanadin zamanta a gidan ka a matsayin yar aiki?"

"Ada kenan unma, that's past tense, yanzu nasan kinfini sanin matsayinta awajena, and don't forget Zancen Auren Yaran mu zamuyi, nasan kina sane da hakan bai kamata wani Bare yaji mana Sirrin mu ba, so please she get out before I throw her up"

Shiru tayi takasa cewa komai sai kallonshi datake ga hawaye sai bin fuskar ta ,Itama inna Kukan takeyi Jikin Ashman yayi mugun sanyi ko kadan bayajin Daɗin Wulaƙanta Baiwar Allah nan da Sukeyi So suke tayi zuciya tabar aiki a gidansu,Amma taƙi barin gidan , Kullum cikin Wulaƙanta ta suke ,amma ko da wasa bata taɓa nuna abin ya dametaba sai Yau, Ganin Hawaye a Idanunta ba ƙaramin Taɓa zuciyar sa yayi ba yaji kamar An soka masa wuƙa a zuciya.

A hankali take takawa har ta fice, yabita da kallon tausayi .

Tsaki Saleem yaja Ya kurɓi Coffee ɗinsa ya samu Wuri ya zauna, Ya dora kafa ɗaya bisa daya, Yana binsu da kallo ɗaya bayan ɗaya idanunsa na Sauka akan Aeesh y saki wani Ƙayataccen Murmushi wanda yasa gabanta faɗuwa , Ko kadan bata kaunar Kaddarar da zaisa Su hada Hanya da saleem gashi kuma zaman Nan ya hadasu.

Wuri Ashman Ya samu nan kusa da Aeesh Ya zauna.

Abba ne ya fara magana Bayan ya buɗe da addu'o'i ga mara lafiya sannan Ya dora da cewa

"Ashman dakai Da Saleem Mun Gama ShiryeShiryen Komai na Auren ku ,Saidai Muyi Fatan Allah Ya kaimu lokacin"

Saurin Ɗagowa Ashman Da Aeesh Sukayi suna Duban Abba da mugun Mamaki.

"Dama Saleem Zaiyi Aurene ban sani ba?”

“Eh ,Yar Uwarka zai Aura A'isha ”

Waro idanuta tayi,Kunnenta har wani kadawa sukayi jin the shock of their life

_*Aure kuma!*_ zuciyarta tayi exclaiming .

"Mun rigada Mun Gama shirya komai har IV gasu ku Gani idan Da Mistake sai Mu maida a gyara''

Inji Baffa yana Fiddo Ƙaton Envelope daga Jakarsa

Dagowa Ashman yayi yana kallonsu da jajjayen idanunta in shock

"Abba ban Gane ba, Yaushe Kuka shirya auren Saleem ban sani ba?, ita Ikhty dakanta tace tana Son Saleem?, ya Batun Auren ta da Aareef?, kar ka manta har kudin Auren ta ya kawo maku!"

Dakatar dashi Abba yayi da cewa

"Babu abinda yaron nan ya kawo, Raina mana wayau Yayi niyyan yi Tun randa mukace ya kawo kudi bai sake Dawowa ba, Tun Lokacin Saleem Yace Yana so , mu kuma muka bashi izinin neman Soyayyarta idan ta amince Shikenan , cikin Ikon Allah yanzu Sun Sasanta Duk suna Son junansu bayan wannan Me zamu jira?"

"Abba Auren Aeesh da Saleem bai Halalta ba, Already Aeesh matar Wani ce"

Dagowa Aeesh tayi tana kallon Ashh jin yadda yayi magana sai gani tayi shock ne written all over his face, sai taji jikinta yayi sanyi,tashin Hankalin ta ya daɗu akan Nada Me saleem Ke nufi da ita ne?, Babu Abinda ya taɓa hadata dashi Ballantana tayi Tunanin kila ta taɓa yi Masa laifine Shiyasa Yake son ya aureta don Yayi ramuwa.



"I.. Don't get you matar wacece?"

inji Baffa yana kallon Ashman cikin son gasgata abinda kunnuwanshi suka jiye mashi

Shiru yayi yakasa cewa komai sai hucin da yake Fitar wa ta hanci ta baki

"Me kake nufi da Ita din matar wanice, I don’t get you"

Abba yasake fada

Hadiye wani abu daya tattaru a maqoshinahi yayi sannan tace

"Aeeesh Mata t......"

Sai Kuma yayi shiru ya na haɗiyar zuciya, Ya kasa yarda ya furta abindake zuciyarsa.

Ganin yayi shiru yana huci

"Son are you ok?" inji Abba yana Binshi da kallon mamaki.

Shima baffakallon rashin fahimta ya yimashi

"Yau 9days Ya rage ,daurin Aure kawai za'a yi , a gidanka saleem zai zauna kafin ya ƙarashe Ginin shi" 

Gaban Aeesh yashiga harbawa ahankali ta cigaba da kallon Abba batareda tasan na cewa ba, Kalamansu Masu kamada Garwashin Wuta kam sai Sake Circulating Sukeyi a Tsakar kanta ,bAbu wanda yafi tsaya mata a rai sai Inda Taji sunce Aareef bai bada kudin Auren su ba, Me Aareef ke nufi?,kenan duk kudin da ta bashi a banza?, Me yayi dasu Tho?, Da yanzu ya bada da Ko kusa Saleem bai shigo Rayuwarta ba , da yanzu Maganar Aurenshi da ita akeyi, Meyasa Zaiyi mata haka?,Meyasa zai ci Amanar ta bayan Ta damƙa masa Dukkan yarda?, Meyasa Meyasa?"

Hawayen tausayin kanta ne suka zubo mata, Tana tsananin Son Aareef fiyeda Tunanin Mai tunani bata jin zata iya rabuwa dashi ,Dukda abinda Yayi mata bata ji sonsa ya ragu Cikin ranta koda na digo daya ne

"Waiii kekam Amarya me yasaki Kuka? ,haba sai kace wacce za'ayi wa Auren Dole?"

Inji Goggo don a tunaninta da gaske soyayya Saleem da Aeesh Keyi.

Tasowa Saleem Yayi ,Ya ajiye Mug din hannunsa ya zauna a Gefen Aeesh na hagu, yana satar kallon Ashman Dake zaune a side dinta na dama.

Saurin Share Hawayen ta tayi tare da kallonsa, ganin ita yake kallo sai tayi Saurin Sunkuyar da kanta tana Kuka mai sauti.

Saleem ya wani murmushi wanda shi kadai yasan Ma'anar Abinsa yana sake tsatstsarenta da idanunsa farare tas, a hankali ya furta,

“Inasonki da yawa Aisha ta, Ko kadan Bana son ganin Wannan Hawayen naki, A duk lokacin da na gansu ji nake kamar wanke Zuciyata kike da ruwan Maliya, gara dai nayi na mallakeki kusa dani na huta da Distance ɗin nan da ace na Aureki yanzu nasan abinda zanyi Miki In Hana  Hawayen ki zuba”.

Ya ƙarshe maganar da kai hannu fuskarta da niyyar goge mata Hawaye, ,ji yayi an riƙe Hannun nashi da karfi.


Gaba ɗaya jijiyoyin Kan Ashman sun mimmiƙe ruɗu-ruɗu, numfashinsa sai kaikawo yake saboda tsabar fidda Huci mai tsananin Zafi.

Ya runtse idanunsa tare da matse hannun Saleem, muryarsa a matuƙar kausashe yace

"Don't you Ever try that Rubbish, da kayi Kuskuren Taɓa fuskar ta ta sa kayi mamakin yanda zan daddatsa yatsunka na watsa ma karnuka"

Tsawa Abba ya daka msu, haka yasa shi Sakin Hannunshi yana Huci, Shima saleem Din Huci yake yi yana Kallon Cikin Idon Aaah,idanunsa sun sake kaɗawa sunyi masifar yin jazurr, jijiyoyin kansa sunyi ruɗu-ruɗu.

habeeb sai sharar ƙwalla yakeyi ganin tashin Hankalin da Yar Uwarsa ke ciki ga mahaifiyarsu a kwance Amma Suna zancen Aurar da Yar uwarsa ga wanda bai san darajar Mace ba?, wannan Wane irin Rashin imani ne?.

Ɗagowa Aash yay yana kallonsu, dagani kasan shima kukan zuci yakeyi, ya maida dubansa ga Abba Cikin Bacin rai idanunsa

Please Login or Register in order to submit comment