Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Goggo tasa baki sannan ta yarda, a Gidan lallen ma Saida Ta nuna halinta don Cewa tayi kar ayi Mata mai kyau a Kwaba mata Hauka ta yanda idan Angon ya gani zaisan asarar kudinsa yayi, Dariya mai Lallen tayi Kawai, sosai aka Rangwada msu mai kyau , da  yamma aka turo kawayen amarya Suma akayi msu.

Duk sha'anin Da akeyi Nuna farinCiki takeyi a fuska amma Allah kadai yasan Yanda  takeji Cikin Zuciyar ta, Da saleem ya san yanda takejin tsanar sa a Zuciyarta da Bai yi murna da auren ba.

ajitayi binda ke mata dadi, she's very lonely gashi babu abokin fira ita kadai ake bari da Ammi.

8:27pm

Dare ya tsala Ko ina shuru

Buga tagumi tayi da hannu daya datayi supporting da bed dinta tana kallon Umma dake kwance Rai a hannun Allah, Goggo da Inna Yathai Sun Tafi duba Kawar Goggo ta yarinta an kwantar da ita, Abba kuma dama Baya kwana a asibitin a gidansa na garin Yake kwana.

Tunawa tayi da Good old days dinta da Ashman inda kullum Every Moment Suna tare koda Basu ganin Juna suna manne a waya.

Tunawa tayi da yadda suke Cin Abinci a tare, komin Dare sai ta jira yazo sannan Take cin Abinci.

Tunawa tayi da yadda yake haquri daita akan Shirmenta ,yayi ta biye mata , Sometimes ma har Tsokanarsa takeyi Don Ya biye mata Suyi ta Shirme.

Tunawa tayi da yadda suke fira,Idan Tayi badai dai ba ya tunasar da ita Cikin gamsassun Kalamai ,Salonsa haryanzu takasa samun mai ta musamman irin nashi kuma haryanzu takasa samun wanda zata saki jiki sosai fira da Dariya kamar shi ,Shima baya Ma kowa dariya sai ita ,idan Abu ya burge shi Saidai Yayi Murmushi.

Tunowa tayi da happy moment dnsu ta Ƙarshe, Ranar da sukaso yin fada da Saleem akan ta.

Tunowa tayi da Ƙamshin da ta shaƙa a Gemunsa, Ƙamshi mai sanya natsuwa.

Batasan murmushi take ba, shes lost in his thoughts as always , Rungume Pillow tayi Idanunta na Sake Kawata mata Siffarshi.

dogone sosai tsayyye kuma cikakke dan yafi Saleem cika,Shi dai ba A murɗe yake kaman Saleem ba, A tsaye yake kyam, Soft hand dinsa da soft lips dinsa take tunani dakuma how warm his soft hand is a duk Lokacin da ya taɓata, cusa kanta Cikin Pillow jin Abubuwa na kara tasomata kaman Zatayi kuka

I miss him, I miss him, I’m missing him

Ta fada a bayyane kaman Zatayi Kuka,Jikinta har wani Rawa yakeyi, Miƙewa tayi Ƙafarta na harɗewa ta shige Bathroom

Ta shiga shower ta sakinma kanta Ruwa tana wani irin sauke ajiyan zuciya tana kuka

_"wayyo Allah, wannan wace irin Masifa ce?"_ 

da kyar tasamu abun ya lafamata ,tafito ta shirya ta kwanta akan doguwar kujera tana addu'a, Amma sai Barcin ya Kasa Zuwa, idanunta sai Haska mata Ashman take, ta kasa Controlling kanta.

Agogon Dake manne a bango ta duba, 9:52, Miƙewa tayi Ta saka hijabinta tazo dai dai Gadon Ammi, Ta manna mata peck a Goshi

"Kiyi Haƙuri Umma, zan Karya Alƙawarin da nayi Miki!, he left without saying Goodbye, Zanje nayi Masa bankwana”

Fitowa tayi ta tsaida Adadaita ta kaita har Gaban Gidan, Securities na Ganinta Suka Buɗe Mata dama Sun santa.

Haske tagani tako ina na gidan Wanda hakan ke tabbatar mata da cewan babu Wanda yayi barci Cikinsu daga Ashman Ɗin Har saleem, bin Gidan tayi Da kallo an chanza komai ya dawo kaman Sabon Gida, Dabadon Tasan Ciki da wajen gidan Ba da tace rusa Gidan Akayi aka sake Masa Gini.

Cikin Sanda Ta shige Part din Ashman gudun Kar Ta hadu da Saleem.

A buɗe taga kofar don Haka tana shiga tasa Lock, Kai tsaye Bedroom Din sa ta Shiga don Ta tabbata yana chan By Now.

Babu Kowa a dakin Amma taji motsi a banɗaki, hakan ya bata Tabbacin yana Chan, Zama tayi Saman GadonSa tana Jiran fitowansa Yayinda take Karema Dakin kallo Komai na dakin An chanza Hatta floor din an Chanza Izuwa Samparin turawa.

Tayi nisa Wajen KalleKalle Tajiyo Muryansa A tsakar kanta

“Who invite u"

Ya fada a kausashe

Saurin Juyowa tayi ta dubeshi sai kuma ta kauda kai da sauri tana Ambaton Sunan Allah, Bata taɓa Ganinshi a haka ba Sai yau, Towel ne kadai daure a kugunsa, sai Kuma Wata yar karama a kafaɗar sa

Taɓe baki yayi ,ya cigaba da tsane Jikinshi da Towel

jallabiya ya ciro a drawer, ya juyo zai saka yaga Ta juya masa Baya, Taɓe baki Yayi ya zura sannan ya kwanta Yajawo bargo ya rufa, Ya kashe Wutar, Zuciyar sa cike da mamakin me tazoyi cikin Daren nan ,bayan tanada Mara lafiya.

Ganin Yayi mata banza yasa taji Jikinta yayi sanyi ,Nan take taji ranta ya jagule, ranta ya 6aci taji ta tsani Kanta Meyasa ma ta biyoshi?.

Jin Saukan Numfashinsa tayi Alamar Barci ya fara daukeshi tayi.

Take wani irin Kuka mai sautiya kufce mata, nan ma yanaji yyi banza da ita.

Jin Kukan yake har Cikin Ransa Gashi kukan Take Bilhakki da iya  karfinta tana neman Shi dewa dagowa ya kalleta

"Lower ur voice Please" Yafada yana satar Kallonta ta Mudubi.

Sake sakin  Wani kukan   tayi,ta kara Volume Akan nada.

Ji yayi zuciyarsa tayi Rauni sosai,bazai jure Jin sautin Kukanta ba,

A  sanyaye lekota  bayanta yace
"Menene?"

Tashi tayi  daga gefen Gadon takoma kan Sofa tana Cigaba da rera kukan.

Girgiza kai yayi,ya saki Murmushin da Ya manta Rabon da yayi Irin shi, ya biyo ta ya zauna a Gefenta

Murya a sanyaye yace

"Ihty Menene?"

Hawaye ne suka sake zubo mata

"Ni ka kyaleni"

Galala yayi yana kallonta yace

"Ni menayi kuma?"

"Ba kaine ka manta dani ba?, ka share Ni Kayi kaman Baka ganni ba?"

tafada idanunta na sake kawo Ruwa

Shiru yayi na wani lokaci yana kallonta saikuma saki Murmushi

"Kece kika ce in Bar Rayuwarki kin Manta?"

To dama mai neman kukane aka jefa da ledar kashi

Jin hakan yasata sake fashewa da Kuka

“jibi za'a daura min Aure ,baka Min fatan Alheri ba, Ka daina Sona Yaya Ka tsanani"

Ta fada hawaye na Ambaliya a Idanunta.

Jikinsa ne yayi Sanyi Sosai,shi kansa Dole ne yasa ya guje ta a tunaninsa Hakan da yayi shi zai samar mata da FarinCiki, Amma ganin Tana Kuka ya tabbatar masa Da irin Kewarsa da tayi, Shi ma wani Iri yakeji a zuciyarsa da zai iya da ya sanar da ita ,ita din Matarsa ce Ko ya samu Saukin Raɗaɗin Da zuciyarsa keyi.

A sanyaye y Daga hannu da niyyar share mata hawaye, ta Ture hannun tana Dukansa a kirji da Iya karfinta tana fadin

"Meyasa Zaka Tafi ka barni?, Meyasa ka manta dani Why...!, why..!!, You jerk"

Riƙe hannayenta yayi, hakan yasa tafada jikinshi tana cigaba Sakin Kukan Amma mara sauti.

Lumshe idanu yayi jinta ajikinshi yasaki sanyayyen Ajiyar Zuciya ya maida hannayen shi bayanta ya rungumeta yana sauke nannauyar Ajiyar zuciya

Itama lafewa tayi a jikinshi idanuwanta a lumshe tana qara Bama Hawayenta damar Gangarowa "Karka sake tafiya ka barni kaji"

Ta fada Cikin Raunanniyar Murya mai ban tausayi.

Sake tapping bayanta a kasalance
"You Are My life I can't Do Without YOU"

Ya yi Maganar cikin whisper a kunnenta, yana Sauke Numfashi a Gefen Wuyan ta.

Jin saukar numfashin shi a gefen wuyanta yasata bude lumssasun idanunta da sauri, ganinta kwance a qirjinshi yana qoqarin cusa kanshi a wuyanta yasata saurin dagowa a dan Razane tana ja baya.

Ɗago rinannun idanunsa da suka Fara sauya Launi yyi, ya diresu a kanta a kasalance, Cikin Wata irin Muryarsa da bata fita sosai yace

"Please Ihty, Hug Me for some Seconds"

Itama kasalance ta ɗago Ta zuba masa Watery Eyes dinta, ta Girgiza Kai a dan Tsorace tace

“bazan iya ba "

"Pleasee.."

Yay mahanar kamar Zaiyi Kuka

Tashi tayi Cikin sauri zata fita, ya kamo hannunta kasancewar a kasalance yake yasashi kasa riqeta,ta zame hannunta tayi hanyar Fita Jikinta na rawa.

“Please Ihty....."

Chak ta tsaya ta kasa Fita jin Muryarsa Tayi ya tsarga Ta koina na Jikinta, gani tayi Ashman bai Chantanci Shariya daga Gareta, Just a single hug ya Biɗa daga Gareta ,And this might be there Last moment Together Bai kamata Ta Hanashi ba.

Juyowa tayi ta dubeshi ya koma kalar Tausayi, zuciyar ta taji ya raunana matuƙa, Wani sabon Kuka ta fashe dashi ta dawo da Gudu ta fada Jikinshi ta Rungume Shi.

Rungumeta yayi da duka hannayensa yana sakin Ajiyan Zuciya tare da shaƙar ƙamshin da ke tashi a jikinta.

A Kusan mintuna biyu suna a haka ,Sannan Ya samu Saukin Nauyin da zuciyarsa keyi, Nutsuwa ta maye Gurbin damuwarsa.

A hankali yasa Hannu ya ɗago Fuskar Ta da mamakinsa Sai gani Yayi ta maida kanta Kirjinshi ta kasa ɗagowa.

Idanunsa ne suka Haska masa Zanen Lallen dake Shinfide a baya da Tafin hannunta.

Sai a lokacin ya tuna da Ashe Amaryar Wani To be ce 🙎🏻‍♂️, Kuma matar sa ta sirri.

Wani abu Yaji ya toshe masa Maƙoshi , A hankali ya sa hannu ya shafo hannun

"Lallen yayi kyau"

Ya furta a hankali.

Sake Shigewa jikinshi tayi ta saki Ajiyan Zuciya batareda ta ɗago ba .

Hannayensa Biyu yasa ya dafe kafadunta ya Ɗagota, ga mamakin sa sai yaga Fuskar ta tayi jagajaga da Hawaye.

Miƙewa Tayi a sanyaye ta gyara zaman Mayafin ta ,Ta Murɗa Kofar ta fice tana share Hawaye.

Binta da kallo yayi har ta fita, ya kasa dakatar da ita.






Nayi Gabas 🚶🏻‍♀️

Bintou ✍🏼
July18th
[7/20, 10:36 AM] Bintou: 🗡️🫀 *_WUƘA A ZUCIYA_*

*021*




Miƙewa Tayi a sanyaye ta gyara zaman Mayafin ta ,Ta Murɗa Kofar ta fice tana share Hawaye.

Binta da kallo yayi har ta fita, ya kasa dakatar da ita.

Fitowa tayi harabar Gidan, Ko ina tsitt kaman Babu Mahaluki dake rayuwa a Gidan, Sai yanzu ta Lura da Ƙarin Motoci Shida Bayan Na Ashman da Saleem dake Parke a parking Lot, Duk yanda Akayi saleem Ne yayi baƙi don Bataga Alaman Kowa a part din Ashman Ba

Cikin sanda ta nufi hanyar gate, Tana Share Guntun Hawayen ta da Hanky.

"Babe"

Muryar saleem Taji a bayanta,

Cakk ta tsaya bugun zuciyarta na tsananta.

"Har Kunyi Ejaculating kenan?"

yafada in a low dangerous voice

"So? Are you this shameless?... Nasan kunya gaba kuka bata ba bayaba amma ban ta6a tunanin Rashin kunyar harta Kai hakaba, Matar da na Biya Sadakin ta Kwanaki Biyu suka Rage a daura auren Ita ke neman Yayana"

Jikinta babu inda Baya rawa yayinda wani daci daci ke ziyartar maqoshinta, ita kadai tasan yanda take ji a Zuciyarta a duk lokacin da ya Alaƙanta alaƙarsu Da Fasiƙanci.

"Are you that Shameless?, Ke har kin isa?"

Yafada yana takowa inda take tsaye Still bata juyoba.

"Da kin tambayeni, Kin Nuna Min Buƙatar ki ko Rounds nawa kikeso zan miki kodan darajar Sadakin Da na riga na bayar, amma it's a shame, an extreme shame ace Matar Saleem, the Whole Aisha herself ta biyo namiji Akan ya biya mata Buƙatar ta koba hakaba?"

yaqarashe maganar cikin rad'a yana kafeta da Rinannun idanunshi kasancewar ya zagayo gabanta suna kallon juna.

Kuka tasaki ,Kallonta yake da jajayen idanunsa yana huci Kallo ɗaya zaka masa ka hango Tsantsar Kishinta a idanunsa.

"Yaya Wlh babu Abinda Ya taɓa Shiga Tsakanina dashi"

tafada tana fashewa da kuka jikinta na rawa sosai

Cije Lower Lips Ɗinsa Yayi da ƙarfi yana jin Wani Zazzafar Kishi na kara taso masa,gyara Tsayuwarsa Yayi ya zura hannayensa Duka Cikin Aljihu Yana Kallon Crying face dinta.

"And What bought u here by this time of the night"

"Sorry... i can explain.."
Ta fada Cikin Rawar Murya

"Explain? Kenan wannan gaskiya ne?, Da Gaske kuna Aikata Abinda nake zargi?"

Yafada cikin Rawar murya yana ƙare mata Kallo From Head To toe , idanunshi sun kada sosai .

Bata Fahimci me yake Nufi ba, tunaninta zargin Sun cigaba da Mu'amala a matsayin yaya da Kanwa Yake nufi, Tunda Dama ya hanata Biye mishi.

A tsorace ta gyada masa Kai Hawaye na cigaba da zirya a idanunta.

"Yes Eh!, ...amma.."

"Ya sallam!"

Inji Saleem yana komawa dabaya  Tareda dafa kai, tashin hankali qarara a fuskarsa , Shikenan Ashman ya Gama dashi.

Yanayin Saleem ba karamin Tsorata ta yayi ba,Girgiza masa kai ta shigayi, ga hawaye na gudu a fuskarta tamkar fanfo,

"Yaya?.. Yaya am sorry, am so sorry"

A matuqar fusace ya ɗago, bai yi wata wata ba ya daga hannu da niyyar shararawa fuskarta mari sai yaji an cafke hannun a iska da qarfi

Aeesh da ta tamke idanunta gamm tana sauraron saukar marin taji shiru Haka yasa ta bude idanun ahankali

Rabeel wato Ashraf tagani tsaye gefenta riqe da hannun Saleem a iska suna bin juna da kallon Kallo.

Saurin Komawa Bayan Rabeel tayi,ta kankameshi jikinta na rawa tana hawaye , a tunaninta Ashman ne .

“AshRaf Sake shi, Saleem In ka isa Mara kunya ka mareta"

Muryar AshMan taji ya fada yana riqo hannun AshRaf daya riqe hannun Saleem dashi.

Ɗagowa duk sukayi suka zuba ma Ashman Ido, Dashima kallonsu yake da Rinannun idanunshi Fuskarsa Babu rahama.

Tayi saurin barin bayan AshRaf ta koma bayan AshMan tana kuka mai sauti.

Saleem sai Huci yake yi kaman zaki

Leƙowa tayi ta bayan AshMan ta kalleshi da watery eyes dinta fuska a marairaice murya na rawa tace

"Yaya Please ka bashi Haƙuri, ka Fahimtar dashi Babu Abinda ya shiga tsakanin mu"

Kallon Mamaki Rabeel ya bisu dashi,ya saki hannun Saleem Yana fadin

"Meke Faruwa ne?, ban gane ba, Saleem Me kayi wa yarinyar nan ne?"

"Bani zaka tambaya ba, Tambayi wanchan fasiƙin ,he deserves the Question"

Kallon mamaki Ashraf yyi wa Ashman.

"Bro Me kayi mata?”

Huci Ashman Ya Furzar Wai yau shi ake Tasawa Akan matar sa tazo wajensa.

Shima Saleem Cije Lips ɗinsa Yayi da ƙarfi, yana Sake kallon Yanda Take makalkale shi, Jin zuciyarsa Yayi kaman zaTa buga

Bata ankaraba taji ya chafko hannunta,ya rabata da bayan Ashman yafara kokarin janta.

Wani wawan bangaza Ashman yayi mashi Wanda har saida yakai qasa sannan ya Wanke shi da Wawan Marin da ta Amsa Kowa ta  ko ina, Tsuntsayen dake kwance duk Suka tashi,Ba Saleem ba, hatta Ashraf dake Tsaye saida Saukan Marin Ya gigitashi .

Babu Shiri ya cika ta ya dafe Kuncinsa dake barazanar Fita daga Mazauninshi.

hannun Aeesh Aash ya damƙa, yana Gyara Tsayuwarsa Muryarsa a kausashe yace

"Na zata idan Mutum ya kai Adult Stage Hankali yake karawa, Ashe ba haka bane akwai Wa'enda Ke buƙatar Na jaki kafin Su gane hanya, Saleem kuskurenka daya da Kayi Gigin taɓa Hannunta, a yau in naga dama Ihty zata iya kwana dakina kuma babu Abinda zai faru haka babu Wanda ya isa ya titseni! a haka kake son a aura maka ita kana Tsorata ta?, Idan Mace na Tsoronka bashi ke Nuni da Kai namiji ne ba, Idan Ka isa Kasa Namiji yaji Tsoron ka,Nuna Jan wuya akan Mace Bashine ba Nunawa Ga namiji dan uwanka shine Jarumta Sha Sha Sha kawai"

"Ashman Wai me ke faruwa ne"

"Bai Shafeka ba!, Ka fara ji da Gaurancin da kake fama Dashi"

Ashman ya fada cikin Daga masa Hannu.

Kasa Motsawa Saleem yyi yana Dafe da kuncinsa Da k'arfi ya cije lips d'insa tamkar zai hudashi da hak'ori, ya daga Jajayen Idanunsa ya zubasu akan Ashman .

"Yaya Ni ka mara?"

"An mareka Idan ka Sake Gigin taɓa ta sai na yanke hannunka".

Ashraf dai Kallon Mamaki ya bisu dashi a mammakince ya sake tambayan su

"Wai Meke faruwa ne?"

Hannu Saleem ya Daga masa

"Dakata Yaya Babu Abinda ya shafeka a wannan batun ,mata ta ce ,kuma inada Ikon zartar da Kowane hukunci akanta in tayi laifi"

"Hukunta ta?,Laifin Me ta maka?, anzo wajen yanzu na Fahimci cewa apart From being Dumb kai baka da Hankali ,Gata , Gata nace gata ka hukunta ta! ,ka tsaya ne?, me kake jira!"

Ashman Ya fada da Kausassar Muryarsa yana bashi ita, Ita kou sai kankameshi take tana Kuka Jikinta babu inda baya bari tashin hankali karara a Idanunta

"Eh nace Gata ka hukunta ta!, Me ka tsaya Jira?, Dan Karamin Mara kunya kawai"

"Kai yaya ,na da daɗe ina ganin take takenka ,Bar ganin Kai Yayana ne, Na lura Kai Irin Yayyin nan ne da basu Kaunar Cigaban kannensu Saboda bakin Hali da Mugunta,Duk wata Alheri da biyo takaina sai kasan Yanda kayi ka lalata ta''

Tsawa Ashman ya daka masa

"Hang it Saleem !, Bar Ganin Ina biye maka ,har yanzu kai ƙaramin yaro ne a wajena, bakafi karfin duka ba, na lura bakasan kara ba, baka san Kawaici ba, Sai Girman kai da izza like Pig"

"Nayi Girman kan, Yaya nayi Girman Kan, Kaima kasan Na isa ne ,nayi izzar idan ka isa Kayi mu gani Na riga na shige maka gaba A'isha Tawa ce..."

"Shut Up Saleem"

Rabeel ya daka masa Tsawa, Nunashi da Yar yatsa yayi Cikin fushi

"You have no courtesy , bakada ta ido, bakada Tarbiyya, yayanka kake gaya ma haka!, Na lura da cewa Wannan Rashin kunyar da rawan Kan da kake taƙama da ita Sai an Sauke maka ita "

Kallon Ashman yayi ,Ya kuma kallon Aeesh dake manne dashi tana kuka

"Sufyaan Me ya faru?

Da k'arfi ya cije lips d'insa tamkar zai hudashi da hak'ori, ya daga Jajayen Idanunsa yana huci ya zubasu akan Saleem batareda  ya Amsa Tambayar da Rabeel yayi masa ba, ya nuna shi da Yar yatsa cikin murya dake nuna k'ololuwar 6acin rai yace

"Idan don Ta Amince zata Aureka ne yasa kake jin kanka kaman wani shege ,Ni Sufyan Naseer nayi maka Alƙawarin Kawo Dalilin da zaisa Batun Auren nan ya tarwatse na rantse"

"Ashman Kai Jahilin Ina ne?, Ina ka taba ganin inda Aka taɓa Shiga al'amarin Neman Aure?"

Inji  Abdul Jaleel da Tun ɗazu yake tsaye yana jinsu.

" Malam !,Saleem ya riga yayi maka nisa ko a addini ,idan an riga an bada Sadakin Yarinya ba'a so ay...."

"Abdul....!, don't interfere, yanzu zasu baka Kunya"

Ashraf ya dakatar dashi

"Nikam keda Masaniya akan Komai, Kuma akan Gaskiya babu Kunyar da zanji"

"Mutumin da yake Cusa kansa inda ba'a sonsa shine jahili, Anayin Aure ne domin samun farinCiki, da jin Dadi na Rayuwa, bawai bakin Ciki ba shaShaSha, Meyasa za'a Aurawa yarinya Mutumin da bata so?, Su Dad Sunyi Son Rai Kuma Wlhy idan Suka sake akayi Auren nan zasuyi nadama, Ba'ayi wa mace Auren Dole ballantana kuma da wanda Takeso, Gashi Tun ba'ayi Aure ba Zargi ya fara shiga tsakani inaga In An daura?"

Inji Ashraf bayan Ya karancesu,cikin Kankanin lokaci ya gano Matsalar da suke fuskanta, Don Kallo ɗaya za'ayi wa Ashman Da Aeesh a fahimci suna Cikin Wani yanayi cikin Fushi da tsawa ya cigaba da fadin

"Abdul Jaleel daka kai har Saleem  idan kun manta inaso In Tabbatar muku da cewa a tsatson Dr Khamis Shettima ,Saida Aka fara Haifan Ashman Sannan Aka haufemu duka, Ko Ni nan da nake tsaye a Gabanku ya bani Awanni Uku,Sannan Baku isa Ku zo mana da son zuciyarku ba and Expect me to accept it, I have the Final say !, don haka baza'ayi wa yarinyar nan Auren Dole ba...!, Yanzu ba anjima ba sai gobe sai na kira Dr na Sanar dashi Duk Abinda ke faruwa,ba dan Gatan daddy ba ko kai ka haifi Daddy sai an Bata maka an samar Mata da FarinCiki  don haka Duk Ku watse Ɓace min Da gani"

Ashraff kenan 'dan Uwan Ashman Da akaso a rabasu Sun Haihuwar Su, amma Gamuwar Jini sai Sake Bounding dinsu yake yi, Blood Is thicker Than water, Halayyansu Daya da Ashman Amma shi mafadaci ne na karshe Kuma bai iya Fushi ba, hakan Ne yasa kanninsa Suke Tsoronsa, Duk Taurin kai Da Jiji dakai irin na Saleem Shi kadai Ke iya tankwarashi, Shima dan gata ne wajen Abba, amma duk Saleem yafisu Gata ,Baiwar da Allah yayi masa na karantar yanayin Mutun Shi yayi Amfani dashi Wajen Gano Matsalar Su dukda Sunki gaya masa ,Amma ya dau Alwashin Shiga lamarin Domin Samar da Adalci a tsakanin Su.

Tsayawa yayi yana kallon yadda Aeesh ke kukan jikinta har rawa yake in the process.

Tsayawa yayi yana kallon yadda hawayen ta ke gangarowa, Hannu Ashman Yasa ya Share mata su, sannan kamo Hannunta, sannan ya ɗago ya dubi Ashraf da ya kasa dauke Dubansa Akan su, Wani irin kallon tausayi yake binsu dashi

"Kai kuma ka fara ji da naka Matsalar Kafin ka shiga Lamarin Masu Shirin yin Aure!, Gauro kawai"

Rabeel binsu kawai yayi da kallo batareda ya iya Cewa komai ba, yana Sakin Guntun Murmushi, yana Kallo har Suka shiga Mota suka fice daga harabar Gidan

Sai yanzu yake wondering why Meyasa ya zurfafa Kansa cikin batun? Meye nashi don bata Son Saleem?, Ina ruwanshi?, Gashi yanzu ya dau alƙawarin da dole sai ya cika Shi.

Wayar sa ya zaro daga Aljihun sa yayi dialing number Abba, bugu ɗaya ya daga, Duk inda yayi zaton  batun yakai yafi haka domin kuwa Abba dagewa yayi akan Ko mutuwa Aeesh tayi sai an daurawa Saleem gawarta Kuma ya gargadeshi akan karya Sake Shiga lamarin, a Dole ya bar batun tausayin Aash da Aeesh ya mamaye masa zuciya.

A ranar Cikinsu Babu wanda Yayi Barcin Kirki,Ashman Da Saleem Harda Aeesh din ,Don Koda Ashman Ya dawo bayan ya sauke Aeesh Saida Saleem yayi Kokarin Attacking dinsa ,Yyi Sa'a Ashman Ya nakada Masa na jaki ya kwantar masa Abinka da hannun Tunzurarre Sai da ya kumbura masa Fuska sannan ya kyaleshi

Washegari Da Sanyin Asuba jirgin su SADEEQ Yayima Nigeria dirar Mikiya, Zuwan bazata yayi  don ada Cewa yayi bazai Samu Zuwa ba,

Murna sosai Aeesh tayi, fada ko kamanta  Irin Farin cikin da Aeesh tayi Bata lokaci ne, Domin Kuwa mantawa tayi da auren Da Ake shirin daura mata a gobe,Kowa ya ganta zai hango Tsantsar FarinCikin da take tattare dashi!, farin cikin da rabonta da tayi Irin shi har ta manta.

Sosai Hankalin SADEEQ ya tashi Da ganin Halin Da Ummansa take Ciki , Baiyi Tunanin Rashin Lafiyarta Ya munana Haka ba, Amma da Likitocin Sukayi Masa Gamsasshen bayani Akan Cigaban da ake samu wajen Sama mata lafiya saiYa dan Kwantar da hankalinsa, Ganin Kannensa Habeeb da Aeesh Cikin Walwala ya yi matukar tasiri wajen kara Kwantar Masa Da hankali,  amma ya kudurta a ransa da zarar an Kai Aeesh ɗakinta zai Bar Kasan tare da ita, Zai kaita Chan Ƙasar da yake aiki ,,Don sunfi nan ingantattun kayan Aiki da kwararrun Ma'aikata Zai  tafi tare daHabeeb ma a can Dama yake nema Masa Admission Na shiga Jami'a.

An fa fara Shirye Shiryen biki tako wane bangare.

Kallo daya zakayiwa shirye shiryen bikin ka tabbatar daya hada da na dan gaban goshi wanda ake ji dashi

Bayan kashe  Kudin da Su Abba suka ma Aeesh SADEEQ ya sake mata mata both kayan daki da kitchen.

Sosai ya narka kudinshi wajen hidimar tilon qanwarshi da duk duniya baida kamarta.

Reey itace jagaba kirjin Biki, Inna Yathai Ganin Babu wanda Ya damu da gyara Amarya yasa ta yunkuro dakanta ta zage  ta gyarata Cikin Kankanin Lokaci amarya ta ciko sharr

Kasancewar Ashman Ya riga da yayi Gargaɗi akan kar ayi Wasu bidio'i Shiyasa Basu wani tsara bidi'o'i ba a bikin saidai chan Ɓangaren Amaryarsa Deejah Tun Monday Suka fara Event Sai Kuma yau Aka taru aka Gudanar da Waleemah.

Abin da yaba kowa mammaki don babu wanda baiyi tunanin irin rakkashewar da za'ayi a bikin ba kasancewar Saleem Dan son Sha'ani ne, Musamman Yake haɗa msu Party a gida Ya gayyato abokan sa Suyi ta shagali, Amma babu wanda Yasan dalilinsa na kin Gudanar da Shagali.

Bangaren Aeesh maQawayenta sun shirya ma bikin sosai suna dokin shi dukda Ba wani Dogon Lokaci Akasawa bikin ba, Amma inkaga yanda  Suka shirya wa Bikin Sai ka rantse sunyi Shekara Suna  Shiri, mita Suka shigayi mata wai ta za'ayi bikin Aeesh Guda ace babu event ko 'daya?, Sai Waleemah? A dole ba don taso ba Suka Shirya Nurses Hours Wanda Zasuyi Gobe bayan an Daura Aure, a Assembly Hall ɗin Asitin Dr Ashman kasancewar Yawancin Kawayenta Nurses ne da Colleagues dinta da Senior colleagues Harda Junior colleagues dinta duk sun Halarta, Ga ma'aikatan Asibitin Dr Aash Suma ba'a barsu a baya ba.

Su Maryam sai wajajen uku suka qaraso su biyar da ita da team Dinta masu Jida kansu

Nan suka hade da Ma'aikatan Asibitin da suka  zo,akara 6arin iyayi, sai a sannan su Reey suka gano dalilin iyayin ta saboda Duk kusan haka qawayenta suke, Kuma babu Yar talakawa Cikinsu.

Nanfa waje ya hargitse da hayaniya ,babu abinda ke tashi dakin sai shewa da surutu Abinka da haduwa Yan mata zallah.

Da dai Aeesh taga abin nasu ba karau ba ne saita sulale tabar musu dakin takoma dakin Ammi, Tayi Shuru, So take tayi kuka ko zataji sauƙin Abinda ke Damunta amma kukan yaki zuwa.

Karfe 4:00 na yamma daidai aka fara tafiya Babban Masallacin Unguwar don Gudanar da waleemar.

Nanfa akafara abinda ya tarasu,    hawaye Sosai Aeesh tayi da Malamar ta fara wa'azi mai ratsa jiki musanmman ga Amarya, tana gwada Mata nauye nauyen daya rataya akanta a matsayinta ba matar aure tana kawo Mata misalai da matan Magabata.

Sosai jikin Aeesh yayi

Please Login or Register in order to submit comment