Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ai kinsan Am not a good player ko a kwallon kafa kafin na jefa ƙwallo a raga Sai an Shani sau ɗari, tho mutum mai rauni irina taya zai iya buga Aiki sau ɗaya Ace ƙwallon sa ya Shiga Raga¿?"

Tsaki Taja a zahiri sannan tayi masa Reply kaman hk

"Nima fa da wayau na, dukda akwai datti a ƙwaƙwalwar, ka sani Am a nurse nasan All possible Signs of Pregnancy , By the way Gobe da sassafe Zan zo Gidanka zan Dau kayan da Na ajiye , na fasa Ajiyan_

Daga nan Sai ta maida Wayar Flight mode, ta Goge messages din, ta kwanta ranta a jagule Banda hawaye babu Abinda ke fita a Idanun ta, yanzu idan Ciki ne da ita wa zata ce yayi mata ciki?🤔 Ashman ?, Abin da Kunya mutumin da take gani a matsayin uban ta shine zata nunawa Duniya a matsayin uban Ɗan dake cikin ta?.

_No Aeesh stop Bad thinking babu Cikin da kike dashi_

Ta fada a fili tana bubbuga Kanta

_No it might be Real Am pregnant!_

Sai kuma ta waro ido a tsorace

_No Am not, I saw my period last month_

_Maybe environmental changes ne, ai tunda muka je Canada na fara Kawaɗayi._

_Hmmm astagfirullah Ya Allah ka yafe min bazan sake ba_


Washegari da sassafe suka kamo hanyan Zuwa gidan Ashman Don daukar kaya da kuma wayar ta dake hannun sa har yanzu, Reey Sai masifa take mata Daga Dawowanta Ta cinye tulin Abincin da ta dafa Da daddare, ta kuma Cinye mata kati, tsaki Aeesh tayi ta ja tace indai kati ne tayi haƙuri in ta karɓo wayar ta zata tura mata katin Hamsin ta bankin ta😏.


Zaune suka iske shi a Parlornsa ,Yana Kallon kdrama a system din sa, da ka Ganshi kaga mara Lafiya ,gyara zama yayi tare da ɗaukan ƙafarsa ɗaya ya ɗura kan ɗaya dan Kar ta gane halin da yake ciki.

idanunsa ya zuba mata daga kan light Ash vein dinta wanda ta yane kanta dashi, zuwa kan Doguwar Gown ɗinta Dark Ash dake Jikinta, a hankali kuma ya dawo da idanunsa kam fararan yatsun hannunta ta wanda suke Tsaiye dogwaye a jere gwanin sha'awa.

Itama Kallon shi take ƙasa Ƙasa, tana kallon Zallar Ramar da yayi Harda Ƙashin wuya, ga Idanunsa Da suka ƙara Girma sai Sukayi ciki ciki


taɓe bakinsa yayi tare da saurin kawai da kansa zuwa kan system ganin zata kamasa

Murmushi Reey tayi a zuciyar ta tace

_Manafukai duk Kuyi ku gama munsan Makomar ku_

Kamar yaji abinda tace sai ya kauda dubansa daga system yana Murmushi ,itama Murmushin tayi
Reey ta gaida shi Ya Amsa, sai a lokacin itama Ta gaidashi Amma bai Amsa ba hakan Ba ƙaramin haushi ya bata ba, ta haɗe rai Tama bar kallon shi gaba Ɗaya ,ta maida dubanta kan Kallon da yake.

Murmushi kawai yayi Ya mike ya nufi inda Yayi ajiya, ya kwaso mata Kayan Duka Ya dire Mata ,sannan Ya dauko Sabuwar wayar da ya siya mata Already ya haɗa Mata da tsohon


Ai tuni ta mance da batun gaisuwa da murnar ta ta Rungumeshi tana Tsalle, Reey na gefe sai Murmushi take.

Jin yadda zafin jikinsa ke ratsa mata jiki
Yasa ta raba Jikinta d nashi Cikeda tausayawa tace

"Zazzaɓin Safen ne ko?"

Murmushi kawai yayi mata,

"AM fyn"

"U're not fine Ahky...."

"I said Am fine, Muje in Kai Muku kayan Mota, Driver ya Kai ku makaranta"

Daga nan Bata sake cewa Komai ba, ya kinkimo ƙaton jakar suka Fito, Driver ya buɗe booth ya Saka a ciki.

Reey na shirin Shiga Mota Ashman ya kirata , kuɗi ya irgo ya bata yace Incase Idan food stuff Dinsu ya ƙare B4 ending of the week, cikeda Mamaki tace

"Ai munada food stuffs dayawa at least ko wanda ka kawo mana Jiya kadai zai ishe mu har mu gama makarantar Tunda 1½month ya rage mu zana jarabawar karshe"

Karɓe kudin Aeesh tayi tace

“Kaji Munafuka, Wai ita anan Mai kawaice, tho Ni ban Santa ba, ko kifi in siya da Su"

Murmushi Ashman Yayi, suka shiga Driver yajasu suka bar unguwar gabaki daga, ya gota wani Plaza kenan Ta tsayar dashi babu Musu Ya tsaya , Duban Reey tayi a marairace

"Please Besty ki rakani....ba don Halina ba..."


Harararta Reey tayi

"In ma Zaki shiga Ki shiga Tun wuri kafin lokaci ya ƙure don babu Inda zani"

Tsaki Aeesh taja

“Ai duk laifina ne, Ni na kawo kaina"

Tana Gama Faɗin haka ta shige ciki, ba wani abin arziki ta siya ba, takalmi kawai ta siya ta fito, tana Fitowa sukayi kiciɓis da Maryam da yayanTa Zeeyk


Mamaki ya kamata kai tsaye tace

"Sis M.S Dama kin san wannan Me ƙaton Kan ne"

Murmushi Maryam tayi tace

"Nima ban sanshi ba A hanya na tsinto Shi, Dama kin sanshi ne?"

aeesh tace

"Na taɓa ganinshi Sau Uku, Duk in mun hadu sai ya dauke Ni hoto, ko zaka Musa ne"

Tayi maganar tana zare masa ida, Daga hannayensa yayi alamar surrender

"Nope you're right, meet my Precious Ƙanwa"


"Woww sai yanzu naga kaman Ai"

Cikeda mamaki Maryam tace

"Sis Aeesh Dama kinyi Aure ne babu Gayyata?"

Aeesh ta saki Baki

"Wane aure kuma bayan Sakin da mijinki ya buga min a ranar Farko?, Ai ban sake aure ba"

Jinjina kai Maryam tayi Jikinta a sanyaye, taja hannun Zeeyk suka wuce Batareda ta iya cewa komai ba, da ta tuno abinda ya faru a gabanta a ranar da ta fara shigowa gidan, lallai Akwai Sauran kallo a familyn su Saleem, masu hankalin cikinsu Sune maɓarnatar.

Komawa Motar tayi, Driver yajasu, tambayar da Maryam tayi mata na tayi Aurene?, Sai Yawo yake mata Sun kusa Kaiwa School ta hango Wani me Lemu ta tsayar da Driver tace ya tsaya, yana Tsayawa ta buɗe ƙofar ta fito Jikinta Har rawa Yake ta siyo ta dari biyu, sannan ta dawo Cikin motar tana sha.

Cikin Tarin Mamaki Reey ta dubeta tace

" Yaushe kk fara sha?"

"Au na manta fa Ashe bana sha ko?"

Ta fada tana zuƙo Ruwan Lemun, taɓe Baki Reey tayi zuciyar ta fall da fargaba.


Har suka kai makarantar bata daina sha ba, Driver ya Sauke Su Ya Fara ƙoƙarin Fiddo musu Da kayan, zuwa wannan lokacin Haushi da takaici duk sun rufe Reey.

"Please besty stop it, u're disgracing me"
Marairacewa tayi, ''Please besty Wannan ne last one fa"
Reey ta taɓe baki, saitin Kunnenta ta raɗa mata


"Wallahi Ki gama ciyeciyen ki na tasa Ƙeyarki Muje lab a Miki PT test ,inke ShashaSha ce kin kasa gane Abinda ke tattare dake mutanen Duniyan Ba irin ki bane "


Chak Komai nata ya tsaya Lemun hannun ta ya suɓuce ya faɗi.

*Pollokshields GLASGOW*

6:30pm Alh Faisal na zaune saman sofa watching TV, Sureey ta Turo ƙofa dawowarta kenan daga Television Interview da Sukayi da Wani Shahararren ɗan Film na nan ƙasar Uk wanda Sanayyan sa ta karade duniya gabaki daya.

vest ce a jikinsa da 3Qauter hannunsa riƙe da Wine 🍷 ,da sallama ta shigo Ta rugo ta rungume shi Fuskar ta dauke da yalwantaccen Murmushin nan nata Mara gushewa ,ya ture ta yana Jan tsaki ,ta sake rungumeshi a shagwaɓe tace

"Haba Dad Fushi kakeyi dani?"

Banza yayi mata Idonsa na kan TV,ya sake hade rai

"Dad Ko dai Mutane na sun Fara kiran ka ne?"

Sai a yanzu ya Maida Hankalinshi Kanta, still Fuskar nan Babu rahama a cikinta ,murya a kausashe yace

"Meyasa Zaki sa Number na a Stupid Writings dinki?, Ta ina nake da Alaƙa dashi?”

Marairacewa tayi tana Turo baki

"Haba Dad , Kai ne ka bani Labarin Kuma kace I won't have an end to it, that's why I gave ur line so that mutane Su sani Mahaifiyar Yan biyun Da Aka rabasu tun Infancy stage Zata Rayu, ko kuma Alluran da Mutumin da Ya sace Ɗayar yake sawa ayi mata shi za'a cigaba da yi har Ƙarshen Rayuwar ta?"

Dad ya furzar da huci

"Are You suspecting me"


Zaro Ido Tayi

"Meyasa kake da Saurin tsarguwa?,kaine ka bani labarin fa...ka tuna sanda mentor Dina ya nemi na kawo labari mai kayatarwa....."


Saurin Katseta yayi

"Dakata na tuna"

Ta tsareshi da idanu

"So dad you need to Complete my story"

Daga hannu yayi kaman zai dake ta ta kauce

"Storyn burauba!, Zaki Ware ko saina tattaka ki?

Wucewa tayi tana Gimtse dariyarta, saida ta kai ƙofar ɗakinta ta ware murya tace

"Please dad I need My Mum Alive, don't End the story with sorrow"

tsaye yayi , zufa na yanko masa ta ko'ina, a halin yanzu da za'a gwada BPn sa babu shakka za'a samu Above 280/80mmhg

Da Alama yarinyar nan ta gama sanin komai Dangane dashi, Shiyasa yake Tsoron zamowar ta marubuciya, gashi Tun bata kai ko ina ba Tana neman Gigita shi da yan Kananun kalaman d ta wallafa gata kuma yar Jarida, da zarar Yayi Mistake kadan zai jishi a jaridu.

Cije Lips ɗinsa Yayi, ya kamata yayi wa tufkan hanci,,Dole ya dakatar da likitocinsa Su tayar da Noor ta kama gabanta, tunda ga Yarta a hannunsa Ko a haka ya barta ta wahala, Amma bata ɗanɗana kwatankwacin Azabar da ta gana Masa ba ta dalilin Son da yake mata.

Nan take ya Dau waya ya kira Dr Haleem Yace ya dakatar Da allurar dayake mata, a Fara tunanin sama mata Lafiya.....

*Nigeria*

Tunda Maryam ta rabu da saleem bai sake samun Kwanciyar hankali ba, kallo ɗaya zaka mashi kaji yayi matuƙar baka tausayi, Kullum hannunsa Dauke da charbi yana Istigfari Tun Su Abba basu san Da Tafiyar Maryam ba, har Suka gano dole inna Yathai ta dawo Part dinshi gaba daya tana Kulada Ayyan Dashi Saleem Din.


Saidai Ya koma kan Alcohol Wanda Rabonshi da yaji ƙamshin shi Tun bayan auren su Da Maryam.

8:30pm
Dawowan su Kenan Daga Masallaci Shida ɗan nasa Ayyan Shima ya zama wani iri ,yanzu daddyn nashi ya daina Yi masa Wasa, ya Daina dariya ya daina Siyo masa Icecream da Biscuits, a halin Yanzu inna Yathai wacce yake kira da Granny itace ta maye masa Gurbin Uwa da kuma uba.

Yana Shiga Yaga Ko ina a gyare tsab ko ina sai tashin Ƙamshi yake ,Lumshe ido yayi a hankali Ƙamshin nan na Dada tunano masa da matarsa, a hankali ya taka Ya nufi freezer Ya dauko babban Wine dinshi #7PM ya dauko Cup yana Tsiyayawa a ciki ,still hannunsa dauke da charbi.

Inna Yathai ce ta shigo hannunta dauke da Tray din Abinci ta dire Masa a gaba , tareda Dukawa cikeda ladabi tace

"Gashi yallaɓ......"
Bata ida maganar ba, yasa ƙafa yayi Ball Da abincin take komai ya tarwatse,Glass cups da plates Suka farfashe Tuni Abincin ya malale ko ina.

Ya nunata da yatsa Cikin tsawa yace

"Ke wace irin Fitinanniya ce mara zuciya?, I said I don't wanna See you anymore Leave me Exit from my Life?"

Girgiza kai tayi hawaye na taruwa a Idanun ta

"Sorry sir, but Drugs are not healthy for your life , you're too young For that"

Chak Yaji komai nasa ya tsaya, cikeda Tsananin Mamaki Ya dubeta

“what did you just say?"

Shiru tayi masa Tana Girgiza kanta, Idanun ta cikeda tausayin sa.

Da ƙarfi ya buga Kwalbar wine ɗinsa da bango,nan take ya fashe, Yayi Male Male a ƙasa, taku ɗaya yayi ya shaƙo wuyarta idanunsa Sunyi jazur hannunsa na rawa yakai Half broken bottle ɗin saitin Idonta , da murya kaman Ba nashi ba yace

"Tell me who sent you?, Wa ya Aikoki?,Why are you pretending For All these while?....."

Shuru Tayi masa Cikeda tausayi

"Why......!"
Yayi screaming Kwalbar na Faɗuwa a hannunshi.

Kallonta yayi ido cikin Ido Wannan Karon cikin rauni hawaye na ɗiga a idanunsa Itama Take hawaye suka Sauko mata

“you've been My weakness For a while, a duk sanda na ganki inajin wani irin In my heart,my brain my Soul, my blood... anywhere"

Haɗa hannayensa yayi Alamar roƙo.

"Please Madam No matter who You are I don't care, please Exist Form My Life”

Yana Gama fadin haka ya nufi freezer ya dauko wani Kwalbar giyan, a irin kallon da yaga tana masa, yasan zata Iya hana shi don haka Ko kallonta baiyi ba, ya fice yanaji tana Kwala masa kira Amma yayi Kunnen Uwar shegu ya fice.

Hankalinta ya kai ƙololuwar tashi, dakanta tabishi amma kaman Yayi walƙiya tana fita ta tarasa Inda yabi babu alamar Shi sama ko ƙasa, cikeda tashin Hankali ta dawo ta dau waya ta gaya ma Abba

Abba yace "ai saleem ba Ƙaramin Yaro bane yasan Abinda ya dace, Kuma fitan Dare ai ba yau ya fara ba"


Yana Fita bai zarce ko ina ba sai Wannan Eatery da ya saba Zuwa aduk sanda zaiyi Shayen dare

Yana Zaune aka Masa ordern kaza, aka kawo masa Cups don Sungansa Da guzurinsa, y tsiyaya Abin Kwalbar a ciki, ya yagi kaza zai kai baki wani irin ƙamshi ya bugi hancinsa, Ƙamshin suyan da Bazai taba Manta mai hannunshi ba koda mutuwa yayi ya dawo.

A dan razane ya Miƙe tsaye yana bin mutanen wurin da kallo babu ita babu Mai kamarta.


Da iya ƙarfin sa ya Ambaci sunanta

"Monstang.......!"

Daidai Lokacin da ta ɓillo daga ƙofar fita na Eatery din, as usual kanta Rufe cikin Baƙar helmet tana Sanye cikin leather cardigan Baƙar Snicker ce akafan ta dake sanye da Black socks, ta saka bakin straight trouser, hannunta sanye cikin wani irin hadadden Black hand Sock Mai ɗauke da Hoton Teddy a bayanshi, Hannunta na hagu Riƙe da Key tana ɗan karkaɗawa.

"Maryaaam...!"

Ya sake Kiran sunanta da ƙarfi yana Isa gareta cikin hanzari,airpod ne a Kunnen ta biyu ta kuma ƙure volume ba jinsa take yi ba.

Dirar mutum ta gani a gabanta ,Dagowa tayi daga Tada machine din da take shirin yi kafin ta kauda ido, ta Cigaba da ƙoƙarin tadata tana fadin

"Am sorry Sir ,No chicken for today till...."

cak maganarta ta tsaya da tayi recapping abinda ya faru recently.

Saurin dagowa tasakeyi cikin rashin gasgata da mammaki ta bayyananne.

ji tayi gabanta ya yanke yafadi ganin shi dinne riƙeda hannun Bike dinta ya kafeta da seductive eyes dinshi.

Mutuwar tsaye tayi tana kallonshi cikin waro idanu fuskar ta cikeda mamaki.

Binshi tayi da kallo daga sama har ƙasa.

Golden jallabiya Mai tsantsi ce a jikinsa, Yar sumar kanshi a kwance luff sai qyalli take, sosai yaqara mata kyau kwarjini da haiba

Shima a ɓangarenshi kallonta yake yana jin wani irin shauqin dabe ta6a jiba na janshi yayinda ƙaunarta ke daɗa hauhawa acikin Rugar zuciyarshi.

Jiyake kamar ya saceta ya gudu,ji yake kaman Ya maidata ciki ya sake haifota Don sati ɗayan nan dayai bai Ganta ba gani yake kaman ya Shekara bai ganta ba, Dukda baiga fuskar ta ba Amma a iya structure Nata yaga kaman an chanzata.

Ita tafara janye idanunta akanshi tana haɗe rai

Maida hankalinta tayi kan tada Bike datake wanda ayanzu batamasan ina zata choka Key din ba

Ganin yanda hannunta ke rawa yasa ya riƙo Hannunta a hankali ya Saita key ɗin cikin ramin shi.

Lumshe ido tayi ta sauke ajiyan Zuciya daidai lokacin da tajishi a bayanta, ya haye bayan Bike,ya Saƙalo hannayensa ta baya ya Dire su a Daidai cikinta.


A hankali ya kwantar da kansa a Bayan ta , yasa hannu ya zare airpod a kunnenta, cikin Muryar maye ya raɗa mata

"Drive us wifey"

gaba daya alcohol din da yasha ta zuke karfin saleem Bashida ƙwari ko kaɗan ya sauke mata gabaki ɗaya Nauyinsa a baya ...


Maryam ji tayi kaman yana janye. Jinin jikinta a hankali.......








_Alhamdulillah, a big thanks to my loving fans, friends family and relatives who prayed and texted me And even called Me on phone, Am grateful 😍may God bless you All🤲.

I pray none of u go suffer as I do😔😪 Wlh naga adduoi kala kala am even supprised Taya Kuka sani?

But now Alhamdulillah
Nagode sosai 😍😘


Bintou ✍🏽

Nayi Gabas 🚶
5th Nov.
[11/9, 9:33 AM] Bintou abdool: *WUƘA A ZUCIYA*
( _BLEEDING HEARTS)_





*049*

"Drive us wifey"

gaba daya alcohol din da yasha ta zuke karfin saleem Bashida ƙwari ko kaɗan ya sauke mata gabaki ɗaya Nauyinsa a baya ...

Maryam ji tayi kaman yana janye. Jinin jikinta a hankali..

A hankali bishiyoyin wajen suka kaɗa suka bada wani Sanyi mai shiga jiki.

Yyi saurin cire hannun duka biyun ya riƙe faffaɗan waist ɗinta gam tareda Sakin Ajiyan Zuciya.

Duk ilahirin Jikinta ya dau rawa, Zuciyar ta na wani kalar bugawa tayi saurin Lumshe fararen idanunta , hannun ta na wani irin rawa ta kasa sarrafa Bike din.

A hankali Sanyin dake kada Bishiyoyin ke daɗa ratsa duk ilahirin Jikinta har cikin Jininta sosai ,gaba ɗaya sai jikinsa ya saki, a kasalance a kuma yanayi na son samawa zuciya da gangar jiki nutsuwa ta ɗaga hannunta guda ɗaya tare da dafe nasa hannun dake kan waist dinta, ya sake Riƙeta Gam Kaman Za'a Ƙwace masa Ita.

Rintse idanu Maryam tayi tsigar jikinta na tashi, yunƙura tayi zata tashi ya ƙara sakar mata nauyin jikinsa a baya, idanunsa da suke a lumshe ya buɗe, ya Zame hannunsa daga inda ya sauke su , ya kamo hannayenta ya Dire su a ƙahon Bike ɗinta, Muryarsa a dishe yace

"Let's Go....."

Ta sauke ajiyan Zuciya, Tareda daidaita nutsuwarta Ta tattaro Ƙarfin Jikinta, sannan a hankali ta murɗa Mukullin,ta Tada .
A hankali take sarrafa Abin hawan a kan titi, tanajin Saukan Numfashin sa a Bayan ta har ta kaisu Gida.

Ta danna Horn, Zeeyk ya buɗe, ya bisu da kallo Cikeda Mamaki batace komai ba tayi Parking Tasa hannu ta cire helmet ɗinta, sannan ta dube shi cikin Sanyin Jiki

"Yaya Ka kaishi Ɗakinka ya kwana Zuwa Gobe da safe"

Duban Mamaki yayi mata

"Ban gane ba?, meye hadinki Dashi?, Is he Drunk??"

Daga masa Kai tayi Batareda tace dashi komai ba, saleem Ya same hannunsa daga Ƙugunta, Ya sauka Itama Ta sauka, Hannu yaba Zeeyk Cikin Maye da Niyyar suyi sallama Zeeyk Ya Galla Masa Harara.



"Excurt me To your Room ....let's Go....."


Saleem Ya Fada idanunsa Na lullumshewa.

Duban Maryam Zeeyk Yayi rai bace Ciki yace

"Bai San Hanyar Gida bane?"

Tayi Gaba tana faɗin

"He's drunk Taya zai gane Gidan su?"

Bedroom dinta ta shiga ta turo kofa, ta zauna a bakin gado tana ta cije Lips Haɗi da jan Tsaki ita kadai like an idiot.

Attitude ɗin Saleem yana bata mamaki,Gidan su ya kamata takaishi,Amma ta dau ma Kanta Alƙawarin bazata Sake Taka ƙafarta a gidan nan Ba koda Da kuɗi ne, Ta gommace ta kawo shi Gidansu ya kwana in yaso Gobe da safe ya kama Gabanshi.

sai ta fara wondering what happenned to her? What comes over her?, Meyasa Ta kawoshi Gidansu?, _Meyasa ban tsawatar masa ba?, Meyasa bance ya sauka ba?_

Nan Take ta Bama Kanta amsa

_saboda He deserve That little pleasure from You_ Ya Baki mazauni a lokacin da babu Wanda ya damu dake!,Saleem Ya Miki Abinda Mahaifinki Ya gazayi Miki a lokacin da kike neman Taimakonsa ,Bai kamata Ki barsa ya Kwana a waje cikin Wannan yanayin ba.

Ta saki ajiyan zuciya haɗida Jan Yar karamar tsaki cikeda Jin haushin kanta a fili tace

"Maryam This should be the Last time ooh😏, the Idiot did not deserve More from You !"

Zaid ne ya Turo Ƙofa Bakinsa Daukeda sallama, Amsawa Tayi Ya ƙaraso yaja Kujerar Dressing Mirror ya zauna Yana Binta da kallo Fuskar ta babu yabo babu fallasa.

Turo baki tayi

"Ka tsareni da Ido"

"Ya bazan Tsare ki da ido ba Kinsan Abinda Kikayi?, Wai Tukunna Ma ina Kuka haɗu? Ko ince ina kukaje kodai Kin fara sonshi ne?"

Zaro ido tayi

"Kaii yaya Shine fa Ya hau machine Dina kuma Naga A buge yake shiyasa Na kawoshi Gidan Mu"

"Shi basu Da gida ne?"

"A yanda Yake kake Tunanin Zai Iya zuwa Gida ne?, Ai sai Mota Ta kaɗe shi Ko wani abin Ya same Shi"

"Sai me Ina ruwan Mu?, Wa yace yayi Shayeshaye? Yasan Illar shaye Shaye Amma ya zaɓi Ya lalata Rayuwar sa a banza a hofi, ke kuma Gaki me Miji baki son Abinda zai Illata Shi shine kika kawo mana Shi bayan Kinsan Bama Son Yasan Gidannan"

Maryam ta kauda kai cikeda Jin zafin Ambatan sa da mijinta da yayi tace

"Tho Don Ya San Gidan nan Sai me?, Ina Ba ɗauke Ni zaiyi Da ƙarfi Yace zai maida gidan Sa ba ko?"

Tsaki kawai Zeeyk yaja, ji yake kaman ya kifeta da mari.

Shuru ya ratsa dakin Na wasu lokuta, Sannan ta dubeshi Daidai lokacin da Ya kuma jan tsaki

Ta s
"Meye...?, Baka huce ba?"

Ya kauda kai Ransa a ɓace

"Tho Yi haƙuri Bazan Sake Ba”

Ya Mike yana Fadin

"Gobe zan Haɗu da Kawunshi Barr Hamza, na kusa kawo karshen komai"

Fita yayi tana masa saida safe.

"Sai da safe"

Su Mama basu san da zuwan Saleem ba don Sun riga Sunyi bacci Jiya kafin isowar su, haka Maryam Bata sanar da Kowa ba, tare suka hada Breakfast Saleema Ta jejjera a dinning Maryam Ta wuce ɗakinta don Shiryawa so take ta fita tun Da
kafin su saleem su Dawo ya tadda ta.


Ahankali take saukowa daga stairs din bayan ta shirya cikin shigarta na atamfa riga da skirt Blue mai pattern fari sai manyan zanen Flowers Ash, Tayi kyau sosai Cikin Shigar Yau ma Ɗaurin ture kaga Tsiya ce a kanta.

Ta yane Kafaɗarta da wata ƴar Figigiyar mayafi Ash, Hannunta dauke da car key dinta tana Karkaɗawa a hankali.

Dining ta iskesu, Baba, Zeeyk Harda Saleem Kallo Ɗaya Tayi masa ta kauda Kai yana Sanye Cikin sabbin kananan Kaya, Wadanda Zeeyk Siyo Jiya a inda suka hadu da su Aeesh.

Ta kauda kai a ranta tana cewa ashe zai iya saka kayan Wani, a iya sanin Saleem Ko kyauta baya Karba daga hannun wani a cewar sa Yafi ƙarfin Komai.

Su uku kadai ne a dining din , yana riqe da mug din shayinshi daketa tururi Ya kasa Sha Sai Juyashi yake

Tunda ya hangota daga nesa ya kafeta da idanu harta qaraso dining din

"Ina Kwana Baba"

tafada tanayi kamar bata lura dashi ba, Ballantana tasan Yana kallon ta.

"ina Kwana Yar Baba, kin Tashi Lafiya?" Baba yafada cikin kulawa

"alhamdullilah, yaya Ina Kwana" tafada a takaice Batareda ta dubi Bangaren sa ba, saboda saleem dake gefen sa.

"Irin Wannan Kwalliya Haka ina Zuwa?"

Gyara tsayuwar Jakarta tayi,ta dau Mug Din Gabanshi ta ɗan Kurɓi shayin Sannan Ta haɗa Da ruwa tace

"Masarauta Zani"

Ta bashi Amsa a takaice, sannan Ta nufi hanyar Fita a hanzarce.

Saleem Bin duk wani Motsinta Yake da kallo yana Mamakin Yanda Tabama banza Ajiyan Shi Kaman ba Bil'adama ne ke zaune a wajen Ba.

Har Takai Ƙofar Fita ta Tsinkayi Muryar mama tana cewa

"Ke mero dakata"

Chak ta tsaya Gabanta na Dukan 3/3

"Ina zaki?”

Cikin Sanyin Jiki ta juyo tace

"Zaria zani"

“Ni Ban kai Matsayin da zaki nemi izini a wuri na Kenan ba Ko?"

Sunkuyar dakai tayi, ta girgiza kai

"A'a Umma kawai ....dai na riga nanemi izinin Baba ne"

"Tho shikenan idan Ni ban tantanci ki nemi izini na ba ,sai ki nema a wajen Mijinki"

"Miji kuma mama?"

Inji Maryam tana ɗan zaro ido.

Mama ta daga Kai
"Eh Mijin ki wanda Kuka dawo Dashi gidan Nan Jiya da daddare, gashi Chan... kai Taso ka Bita ku tafi, ku bar Min Gida Malalatan banza, ance Muku Aure wasa ne da zaku rinƙa Fita kuna Yadda Kukaga dama?, Wlhy Na sake ganin ƙafar ki a wannan Gidan Sai na sa an Babballa Min ke, Mara Kunya ShashaSha Kawai, idan zawarci abin so ne saiKi kaso Auren da Hujja Kizo mu zauna tare ,ina kallon ki kina kallo na"

Inji Mama cikin fada don sosai ƙaryar da tayi mata ya ɓata mata rai, wai ashe bai saketa ba take Mata Kallon Sakakkiya, tace tunda Sukayi Aure babu abinda ya shiga Tsakaninsu Ya kuma saketa Batareda wani dalili ba, ta kyaleta tana Fita ne kawai Don A cewar ta babu wata Iddarsa akanta amma sosai hakan ke damunta shima yayan nata Ya goya mata baya, Ganin Saleem agidan yau yayi Matuƙar bata mamaki dukda baidamu da sada zumunci ba, Amma tunda shine Zaɓinta tafiso ta yi zamanta a gidan Auren ta, har Rantsuwa yayi mata yace bai Sake ta ba, ta kuma yarda dashi Saboda Zeeyk na nan Ya kasa cewa komai, da Ƙarya ne nan take zai ƙaryata shi

Shiru Maryam tayi tana kallon mama

Tunda ta dawo gidan ta lura mama Bata kaunar zamanta a gidan.

Ranta a ɓace Ta fice Batareda ta ƙara ce da ita uffan ba,

Saleem Satan kallon Zeeyk yayi da wutsiyar ido yaga hankalinshi nakan wayar hannunshi fuskar nan kamar anmashi bishara da jahannama.

Ya maida Dubanshi Ga baba daketa faman Cusa shayi da Breadi ya miƙa Masa Hannu yace

"Nagode Baba, Allah ya bar zumunci"

Murmushi Baba Yayi yace

"Kayi haƙuri da Ita yarinya ce har yanzu, Allah ya baku Haƙurin Zama Da juna Allah yayi Albarka "

Ya Amsa da Ameen sannan ya

Please Login or Register in order to submit comment