Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Shi kuma ya cigaba da fadin

"Ina so In kyautata miki ta hanyar abinda Hannaye zasu iya Ɗauka su baki, da inada wadata da zan iya mki alƙawari da zan iya maidaki sarauniya, Saidai a yanzu da iya wadatar Kalamai nake da ,tho zanyi miki Alƙawarin yin Amfani da iya Kalaman da nake dashi Insa kiji Kanki tamkar Sarauniya"

Shuru ya ɗan yi na dan Lokaci Yana Kallon Kyakkyawar fuskarta dake dauke da tsadaddar Murmushin ta

"An bani Aurenki,Ko ince an bani izinin cigaba da neman Aurenki, Amma matsalar itace Sun bani nan Da gobe in Kawo kaya Da Sadaki Dubu dari da Hamsin,Ni ban taɓa Ganin inda akayi haka ba "

Ɗagowa ta yi da sauri hawaye suka silalo mata,Ita kanta tasan Ko siyarda Aareef akace za'a samu Dubu dari da hamsin ba ballantana Kudin kaya.

Aareef irin Ajebon nan ne Masu Shiga ta manya Amma basuda ko sisi Abinci ma Sai Abokansa Sun nemo yake samu yaci.....

Ganin Hawayen dake silalowa yasa hankalinshi Tashi

"Pls Wipe ur Tears ki Rufa mn Asiri,  sorry amma ni bada wata manufa na Gaya miki ba, But...I will do my best don Ganin Na samu Koda half Daga Cikin Abinda aka bida ne nakai musu Zuwa Goben....."










Bintou ✍🏼
Nayi Gabas

June 4th

Comment
And
Share🙏🙏
[7/18, 9:25 PM] chubby number: 🫀🗡️ *_WUƘA A ZUCIYA_* 🗡️🫀
(Bleeding Hearts)


*010*
Ɗagowa ta yi da sauri hawaye suka silalo mata,Ita kanta tasan Ko siyarda Aareef za'a yi ba za'a samu Dubu dari da hamsin ba ballantana Kudin kaya.

Aareef irin Ajebon nan ne Masu Shiga ta manyan mutane Amma basuda ko sisi Abinci ma Sai Abokansa Sun nemo yake samu yaci.....

Ganin Hawayen dake silalowa yasa hankalinshi Tashi

"Pls Wipe ur Tears ki Rufa mn Asiri,  sorry amma ni bada wata manufa na Gaya miki ba, But...I will do my best don Ganin Na samu Koda half Daga Cikin Abinda aka bida ne nakai musu Zuwa Goben....."

"Idan Kuma Ban Samu ba ,Sai in Roƙesu da Su ƙara bani dama Koda nan Da watanni Biyu ne lokacin Saura Wata Uku bikin, In Kuma hakan bai samu ba Sai Mu gudu muje wani Gurin a daura mana aure daga baya sai Mu dawo kinga tunda basu yadda ta lalama ba zasu Amince"

Chak hawayenta ya tsaya,Galala tayi tana kallonshi babu ko kyaftawa yayinda kalamanshi kemata amsa kuwa akunne.

Shima kallonta yatsaya yi yanason ganin reaction dinta.

Ga mammakinshi saiyaga tasaki murmushi mai sauti haɗe da digar yar guntun Hawaye ,ta janye idanunta daga kanshi tana chuckling don She can't believe What he's saying, She's  total Speechless.

Murmushi mai ciwo yayi ganin yadda take Murmushi mai haɗe da Kwalla kuma tayi masa Shuru, Shima shuru yayi don ya lura babu Abinda take buƙata a daidai Wannan lokacin Samada silence hakan ne kadai zai iya ba Zuciyar ta da Kwakwalwarta damar natsuwa na dan wani lokaci.

Cije Lower ɗinta Tayi ta furzar da Huci,Duba ɗaya zaka mata ka fahimci Tsantsar damuwar dake tattare da ita .

"What did.... or what Are You ohh..."

Magana take sonyi Amma ta rasa Me zatace, Tabbas Idan da gaske Aareef ya tura Manyansa Gidansu kuma su suka  Bashi wannan Option ɗin lallai Akwai Matsala babba, a iya saninta su kawu Basu taɓa ba Saurayi Zaɓi daga Bayan Ya cimma abinda yake so ba, tabbas tasan Wannan Salon a Rabasu ce Aka ɗauko da Alama sunyi bincike akan Aareef sun San bashida wadata Shi yasa Suka bashi zaɓi.

Ajiyar zuciya ya sauke yana kallon yadda take kokari wajen ganin tare hawayen dasuka cika idanunta daga zubowa.

Yasan yadda takeji, she's in pain, Serious pain,Shi shaida ne akan irin son da take masa ,Rabuwa da ita babbar barazana ce a Garesu,  kallo daya zaka masu kagane hakan.

Cikin kwantar da murya wanda yafi kama da rad'a yace

"AM sorry baby Nasan Ban kyauta ba, Tabbas Bai kamata Nayi tunanin na dauke ki Mu gudu ba At the first place, Ba Laifi na bane ... Na kasa Sarrafa kaina ina miki wani  irin  son da babu Abinda zai iya kwatantawa duniya Adadin ta ba , A kowane daƙika na rayuwata ,Sonki yakan ƙara Daɗuwa ne so adadin da bazan iya misalta miki ba"

Dan Dakatawa yayi yana dubanta itama shi take kallo jiki a sanyaye

"Nasani banida wani Abin Alfahari, da Tunani wanda ya wuce Ke, akoda yaushe Sonki yakan ƙara Daɗuwa ne aduk lokacin da na tuna ki koda na second ɗaya ne, Nasan Soyayya Alkhayri ce Amma ni nayi dace da Samun Masoyiya kamarki ,Mai sona Don Allah koda Wannan Hukuncin itace Sillar Da zata Rabamu dake karki manta Dani.."

"A'a Aareef No..!,a'a bazamu Rabuba,Don Allah ka daina faɗin haka zamuyi aure mu haihu ,yaranmu Su hidimta mana In mun tsufa"

AEESH ta faɗa cikin kuka, Kauda kai yayi yana Furzar da Huci mai zafi

"Am sorry Aeesh ,I can't do this, I can't keep pretending Anymore Bazan iya Samun Abinda suka Biɗa  Kafin Gobe ba"

"No Arrow Don't say that"

"Dole in faɗa miki Gaskiya, Koda na samu Kudin Taya kike tunanin zan Samu Sauran Na shagalin biki?, Shagalin biki Aside,Daga Ranar da aka Aura Min ke Cinki shanki Suturar ki Lafiyarki da ma sauran ɗawainiyarki duk zasu dawo Kaina taya Nida bana iya ciyar da kaina zan ɗauka wa kaina Wannan Aikin?,Bazan so ki cutu ba, ke din Mutumiyar kirki ce mai raunin Zuciya, baki Tantanci Na barki ba ,Amma ya na iya Kashedi mai tsanani aka mn’'

Yana Gama faɗar haka Ya miƙe tare da Gyara tabarau din Shi

"Habeebty"

Ya kira Sunanta cikin Sanyin murya.

"Sai wata rana , I love you''
Ya fada in whisper

Kasa Motsi tayi Tunda ya fara magana ta zuba masa ido She can't believe Hearing these From him sai wata rana! Take ta maimaita wa a ranta , Jikinta babu inda baya karkarwa, Tanaji a ranta bazata iya sadaukar da Sonda take ma Ashman ba,Koda wasa bazata iya rabuwa dashi ba ,ya zama Wani Sashi na jikin ta ya mamaye ko ina a zuciyarta, Zata iya sadaukar da Komai Don Ganin ta cika msu burin su koda zata sadaukar da duk abinda ta mallaka a duniya ne.

Jan kujera yayi yana ƙoƙarin ficewa yaji ta riƙo Rigarsa ta baya

"Aareef me yasa zakayi saurin karaya?, ashe dama Duk sonda kake ikirarin kana mn duk na Ƙarya ne?, Ashe da Gaskiyar Reey na cewa Kai din mayaudari ne?, Meyasa zaka mn haka?,Don Allah Aareef kar ka rabu dani,idan ka rabu dani Mutuwa zanyi"

Wani deep numfashi yaja Yana jin zuciyarsa na zafi

"Idan Kuɗine dalilin da yasa kake son Rabuwa Dani zan baka iya adadin da kake buƙata a iya rayuwarka Zan Baka komai nawa Amma don Allah karka Barni Ka kai musu komai su sa mana Rana, koda Munyi Aure na yarda zan dau dawainiyar kaina Ba sai ka Mn Komai ba, zan sa Yaya Aash ya sama maka Aiki a Companyn Sa , Please.. Please Aareef"

Ta fada Cikin Kuka sosai mai ban tausayi, kallo ɗaya zaka mata ka gane bata cikin hayyacinta gabaki ɗaya .

Kamewa Aareef yayi a tsaye Tunda tafara yaji kamar an zaremasa lakka daga cikin jiki taji jikinshi yayi lakwas , bugun zuciyarsa ta daɗu, yau Shi ake So haka?, Abinda bai taba tunani  ba .

saurin juyawa yayi ganin hankulan mutane ya fara karkatowa kansu yasashi Kamo hannunta Suka fice daga Wajen ,Tunda take yau ne Rana ta Farko da namijin da ba Muharraminta ba (bayan Ashman) ya riƙe mata hannu.

A yanzu dinma don Hankalinta ya gushe ne bata hango komai sai  Rabasun da Ake shirin yi ,ta tabbata wajen su kawu yaje sune kuma Suka dasa masa Wannan Danyen Zabin don sunga bashida kuɗi kuma bashida hanyar su.

Napep ya tayar msu ya kaisu har Gaban Gidan Su Aeesh aka sauketa, a Napep kuwa Banda kuka babu abinda takeyi, Shima kasa rarrashinta yayi ko kadan bashida kwarin gwiwan furta mata wata Kalmar a halin  yanzu Zai iya cewa Yafita shiga tashin hankali ɓoyewa kawai yayi.

Tayi Sa'a har ta dawo Umma bata dawo ba ,Dama Kano taje Abba ne ya aiko mata Saƙon Yana nemanta cikin gaggawa.

Tana shiga kai tsaye dakinta ta nufa ,tayi wajen gadonta da gudu ta fada akai.

kukan da bata iya a lokacin da Arrow yake mata magana ba ya kufce mata.

Jitayi kamar su Abba sunyi nasarar rabata da Arrow din ma.

Wannan wane irin abu ne? Ko kadan bata taɓa kawoma ranta zata iya samu matsala irin wannan a soyayyarsu ba.

Tariga ta yanke hukunci zata fidda kudaden Account ɗinta Ta ba Aareef ya Biya kuɗin in yaso ko bayan Auren su in ya samu sai ya biyata,

bata ta6a tunanin zata iya Bama saurayi kuɗinta yayi Hidimar Auren su ba, ita kanta idan aka gayamata ita  a da qaryatawa zatayi,kwatakwata Watannin Su biyu da haɗuwa, yau sati biyu da Amincewa da Soyayyar sa kawai lokaci daya ta makance a soyayyarshi makantar da bata tunanin zata ta6a bude ido nan kusa.

Reey ce tafado mata arai, sotake ta kirata ta gayamata komai ko zataji sauqin abinda takeji ko kuma tabata shawarwaru kamar yadda tasaba

Amma saita tuna bazata taɓa goya mata baya ba

Ringing din wayarta ya katse ta daga tunane tunanen datakeyi

Wani sanyi taji a zuciyarta tun kafin ma ta duba mai kiran.

Ganin zata tsinke yasata saurin dauka ta daga kiran ta kara phone din a kunne bayan tayi iya qoqarinta na gyara yanayin ta don batason ya fuskanci halin datake ciki ko kadan batason ta saremashi gwiwa shima.

Saida suka gaisa sannan tun daga yanayin Amsa Sallamarsa yasan akwai matsala cikin zumudi yashiga tambayanta, kukan da take Kokarin Ɓoyewa ne ya kufce mata

"Yaya Wai aure za'a mn😭"

Dariya ta bashi Sosai ya saki Murmushi mai sauti.

"Tho Meye na kuka?"

"Yaya Aareef fa..."

Sai ta kasa ƙarasawa Sakamakon kwaɓar da Zuciyar ta tayi mata.

"Me Aareef yayi"

"Ba komai Kawai, I feel somehow Wai ni aka sa ma rana"

"Ayyah, Are You free?"

"Eh"

"Kizo Gidana Abba na nemanki"

Zaro ido tayi

"Yazo Kd ne?"

"Eh harda Umma duk suna nan"

Zaro ido tayi ta Rufe baki da tafukan hannayenta

"Nashiga Uku, Chewa zasu yi in rabu da Aareef ko?"

Katse wayar Ashman yayi yana Murmushi.

Ya ɗago ya dubi Umma dake ta faman Murmushi Itama yace

"Gatanan Zatazo nan bada jimawa ba"

Gyaɗa kai tayi Abba yace

"Allah Sarki Aeesha ta, yarinya mai hankali gata da son Zumunci Amma Allah ya haɗata da Muguwar Uwa mai baƙar hali ”

Murmushi Umma tayi Ta ginjina kai tace

"Yaya Kai kanka ka sani Ni ban raba Zumunci ba,Illa dai nayi Abinda Ya kamata ,Kai bakada Alhakin Bayarda Aisha ako wane irin yanayi kawu Imaam shike da hurumin Bayar da ita"

Tasowa Abba yayi Cikin hargagi yana Faɗin
"Noor Ni kike Gayawa Wannan Maganganun Ni tsarar Wasan Ki ne?"

Ashman dake tsaye Ransa na sosuwa yace

"No Dad Please Stop it ,kufa ba Yara bane"

Daidai nan Saƙo ya Shigo wayar Abba dake hannunsa.

Buɗe sakon yayi yana Huci, jikinsa ne ya hau Rawa bayan ya kama karance saƙon, Hularsa ya dauka A gaggauce yake faɗin

"My attention is needed Urgently"

Kafin Suyi wani yunkuri har ya fice,hadari Sosai ne a sama da alama bazaa jima ba ruwan sama zai sauko, bai duba hakan ba ya Fito hankalin sa a tashe ya tada Motarsa ya Fice.

*AEESH*
  Tunda ta fito aka fara iskar hadari Aka  hankalin ta yaqi kwanciya ,saboda bata Ƙaunar Bugun Ruwa Ko kadan Da zarar ruwan ya doketa zata kwanta ciwo.

Sai duban hanya take taga ta inda mai Napep  zai 6ullo amma Shiru kakeji.

Hankalinta ne ya ida tashi lokacin da aka kece da ruwa, hankalinta yayi masifar tashi ta samu gefen wani gida ta kafe.

Tun tana daukar abin wasa har abin yafara bata tsoro, tun tana keƙe babu Napep gashi anƙi agama ruwan har taji bata iya wannan haqurin.

Hakan yasa tafito cikin ruwan tareda yar lemar ta da ta fito dashi saboda hadarin da taga ya haɗu Gudun fadawa hannun ƙaddara, takawa ta farayi har ta Fito bakin titi Abin mamaki babu Napep ko ɗaya a titin .

Cikin Ƙanƙanin lokaci har Ruwan yayi mata dukan tsiya, take Jikin take ta soma Rawan sanyi haƙoranta har wani harɗewa Suke.

Garin Tsit Babu Alamun Motoci dukda Kasancewar titine.

Tana Tsaye anan tana waiwaye ji tayi kaman ta juya ta koma gida dukda tazarar dake tsakanin inda ta baro.

Tunda ta shigo unguwar taji zuciyarta ta chanza bugu

Kalle kalle tashiga yi zuciyar ta na gudu.

Jin sautin tahowar motoci taji sun tsaya yasa zuciyarta ta qara gudu fiyeda kima.

Kai tsaye Gabanta Motocin Suka tsaya, motoci Uku ne banda Sautin Kida babu abinda ke Fita a motocin Gabaki ɗaya Sun karaɗe anguwar da Amon su.

Tsoro da firgici ne ya kamata kasa Motsa wa tayi jikinta na Kakkarwa.

Buɗe ƙofar motar farko Akayi Bata ga Fuskar Wanda ya fito ba ,daga nan bata sake sanin meke faruwa ba.

*_Some hours later_*

Dishi Dishi ta fara Ganinsu,Saida ta kulle idanun Sannan ta bude daya A hankali ta waresu dukka Akan bangon ɗakin.

Zumbur ta tashi a gigice tana Ambaton Sunan Allah, A Hankali take bin Dakin da Ido, Babban bedroom ne mai ɗauke da Kayan Alatu na Mata Duk inda Dakin mace ke kaiwa Wajen haɗuwa Dakin karshe ne wajen haɗuwa, Komai irin Kalar da takeso Exactly Dream Room dinta.

ta kasa Tuna Komai Wani irin Dumm taji kanta yayi mata,duk iya kokarinta na Son Tunano Abinda Ya faru ta kasa.

Riƙe kanta da ya sara mata tayi da Karfi tare da  runtse idanunta da Ƙarfi tanajin Zazzaɓi zazzaɓi sakamakon Dukan da Ruwan sama Da ya daketa.

Turo ƙofar yayi ya Shigo hannunsa Riƙeda Sigari yana Zuƙa.

A razane ta miqe Zaune tana Zaro ido Kirjinta na Bugawa Cikin Dimaucewa

"Bamalli...!"

Ta furta a tsorace.

Ya zuƙo sigarin hannunshi ya Feso mata a fuska ya ɗage mata gira ɗaya cikin Salon Yan duniya yace.

"Kinji mamaki Ko? ,Tho haɗiye Mamakin ki ,yau 8th June 2022, Shekaru Huɗu daidai da yarjejeniyar Mu, A yau zan Angwance haka Ranar da kema zaki Amarce according to Yarjejeniyar mu, As u know Everything Is Written”

"Enough!" Ta katseshi tana numfashi ahankali ahankali, idanunta na forming din ruwa.

"Ni na faro komai and now I end it!" Tafada cikin shaking voice

Ajiyar zuciya ya sauke yana kallon yadda take share hawayen dasuka cika idanunta suna zubowa.

Dariyar Wulaƙanci ya kwashe dashi batareda yace komai ba ya nufi kofa yana cigaba da Dariyar saida ya kai bakin ƙofa Sannan ya dakata Hadi da juyowa

"Ki biyoni muje, baki na parlor ke kadai ake jira"

Ko motsi bata yi ba bin fuskarta yayi da kallo Yasan yadda takeji, she's in pain, kallo daya zaka mata kagane hakan Amma ai ita dakanta ta kawo Shawarar Su kulla yarjejeniya Babu musu kuwa ya biye masa ,Ayau kam babu wanda ya isa ya hana shi cika Burinsa akansa.

Haɗiye hawayenta tayi ta Sakko daga kan gadon ta bi bayanshi tana Sharar hawaye ,Ayau kam taga ta kanta da tasan zai ɗau zancenta da Muhimmanci haka da Bata yarda ta tanka ma lamarinsa ba.

A babban Parlon Gidan mai kamada Gari Guda yaja burki ya tsaya Bin Parlon tayi da Kallo.

Abba, kawu Imam (Yayan Mahaifinta), da wasu dattijai Biyu zaune tare dasu bisa sofa.

Ko ina na Parlon Kawace da Abubuwan Ado irin wanda ake kawace eventplaces irin Location ɗin biki ko  sha'ani, Idanunta ta kai kan Tulin Abubuwan da Aka tile a ƙasan Rug sai Kuma bundles ɗin kuɗaɗe rafan yan dubu dubu.

Lumshe idanunta tayi ta sake budesu akan fuskokin Su Abba da sai yanzu ta tabbatar ba mafarki takeyi ba

Qara wara idanun tayi ganin the shock of her life

"Abba, Baffa...!

Dagowa duk sukayi suka fara binta da kallo .

"Baffa na.."
Aeesh ta faɗa  cikin kuka kana ruga ta fada jikinshi

Kuka tafashe dashi tana qara Qanqameshi

"wayyo Baffa na! Baffana Wlhy bada gaske nake ba,nayi hakan ne don na ceci rayuwar Reey daga mugun kudurinsa akanta,  Please Help me baffa, take me out of here, zai kasheni, Wai Aurena zaiyi ..." tafada cikin fitar hayyaci jikinta na rawa sosai

Dago fuskarta yayi cikin taffukan hannunshi yana bin fuskarta da kallo

"Aeesh, look temperature ɗinki yayi high Bakida lafiya ne?"

Ya faɗa yana tapping gefen wuyanta da bayan hannunsa

"meya sameki?" yafada cikin raunin murya

Fashewa tayi da wani kukan tana sake komawa jikinshi ta Qanqameshi.

"Baffa Ya akayi kasan Sun sace Ni?,Don Allah muje ka rabani da wannan baƙin Gidan"


Fashewa masu tsaron sa sukayi da Dariya banda Bamalli da fuskarnan ke a murtuke, ga hannunshi dayake riƙe da Sigari yana cigaba da busawa

"silent!!" injishi cikin quluwa don shi bega abin Dariya ba anan , yaƙosa a ɗaura msu Aure ya dau matarsa su bar ƙasar

(Ni BINTOU Kou sakin baki nayi ina kallon Ikon Allah )

Tsit wajen yayi Aeesh kau qara shigewa jikin Baffa dake kallon Bamalli tayi tana rufe idanu cikin Tsoro.

Takowa Bamallo yayi ya nufosu

Ganin Hakan yasa Baffa miqewa tsaye da Aeesh dake jikinshi still ganin Bamalli ya tunkarosu yasata saurin komawa bayan Baffa ta lafe zuciyarta na cigaba da bugawa.

Qarasowa yayi gabansu nan aka shiga kallon kallo tsakaninsu.

Tabarsa ya zuƙa ya Fesar a Fuskar Baffa haɗeda tofe fuskarsa da Wani mugun yawu

Kawu ya Lumshe ido Zuciyarsa na ƙuna.

Bamalli yayi pointing face din Baffa dake malale da yawu yace

"Wannan itace Farkon Abinda ya fara haɗani da ɗiyarka,ko ince ɗiyar yayan ka!, kallon farko da ta Mn tofeni da yawu tayi"

Cikeda tsoro Aeesh ta Qara lafewa a bayanshi, tana kwantar da kanta bisa bayanshi

Cikeda rashin imani da tausayi Bamalli ya cigaba da fadin

"Yauce Ranar da muka tsara nida ita zamuyi Aure,Aure kuma na sunna kamar yanda Al'ada da addinin Musulunci ya koyar damu , Nasan Duk zakuyi mamakin Haka ko ku dauke Ni a matsayin mara Hankali,Amma kafin nan Bari in baku takaitaccen labari Akan Abinda Ya faru Shekaru hudu da suka gabata a rana mai kaman ta yau a lokaci kuma a yanayi irin na yanzu wato Moment after rainfall.

*Four years back*

Ni muzzammil, Wanda akafi sani da Bamalli ɗan Babban Gida ne, iyayena ba matsiyata bane basu san kalmar ba ma family din mu sunada Alaƙa da sarautar Zazzau a halin yanzu kakana shine Sarkin Zazzau

ni kadai allah ya ba iyayena adon haka na mayar da dukiyoyinsu tamkar nawa ina facaka dasu aduk sanda naso.


8th June 2018
Kaduna State Polytechnic

A ranar nayo tsintuwa,yar budurwa ta fakewa Ruwan sama, a lokacin naji na Kwadaitu da ita boys Dina sun fahimci hakan daga yanayin kallon da nake mata,So babu bata lokaci suka ɗaukan Mn ita Suka kai Mn Office din malam garba a lokacin shine malamin da ke daure Mn Kugu ina bura ubana yanda naso, kuka take tana Rokona na Taimaketa karna ɓata mata rayuwa Amma banida imani dama Nafison irinsu, Raping virgins is my passion their tears is My joy ,idan suna Ihu jinake kamar Ana buga Mn tamburan sarauta Sauti mai matukar dadi, My victim was lucky that day ,kamar daga Sama Aeesh ta Faɗo Office din ,a lokacin ina gab da yin aika aika,a lokacin banso na Daina ba don gabaki ɗaya hankali na bayajiki na,janye ta tayi ta ta cire hijabinta ta lulluɓeta ,Ashe Kyawun da na gani jikin yarinyata nafilace ta Aeesh itace ta gaske, take naji na Kwadaitu da Aeesh itama take na fara kokarin Afkawa su biyun abinka da Gushewar Hankali.

Nasha bugu Nasha Cizo daƙyar na samu ma iya Kaita ƙasa.....


❤️❤️



Nayi Gabas😉

Comment
And
Share


Please 😌

Bintou ✍🏼
June 9th...
[7/18, 9:25 PM] chubby number: 🗡️🫀 _*WUƘA A ZUCIYA*_ 🗡️🫀
_(Bleeding Hearts)_


*_Wannan Shafin naku ne Maman Khaleel, Jummai hudu, Safiyya na bebe, Spinky da Ma sauran Team Ashman don Nasan Yau Sai kunba Mutumiyar kyauta ta musamman✊🏻😂_*



*011*

Nasha bugu Nasha Cizo daƙyar na samu ma iya Kaita ƙasa.....

Ganin haka yasa  ta fara kokarin Kwatar kanta ,Amma Inaa Da iya karfina nake ƙoƙarin Cinma burina, Kafin wani lokaci Duk ta gama Fita daga Hayyacinta ya zamana batada Ƙarfin kwatar kanta.

Stain Naga Ni a Jikin skirt dnta ,hakan yasa na tabbatarwa Kaina bata sallah Ashe.

Na kwadaitu dasu Sosai bazan Iya haƙuri ba, Komawa nayi kan ɗayan banaji Bana Gani kaman daga Sama naji kalaman yarinyar Nan cikin Kunnena tana cewa

" _Kai a ganinka Tilasta Mace da Ɓata Rayuwar ta Wani Abu ne?, Jarumta shine Ka Karkato Hankalin Mace kuyi Komai da son Ran Kowanne a cikin ku, wise Men knows their limits, and smart Men knows that They have none ,Give a girl the right shoes and she can conquer the world_ "

Ko kadan Ban Fahimci Inda zancenta Ya dosa ba ,Amma Nasan It's a challenge For me as a man To rape a girl Real Men Doesn't Rape ,Kaman An zare Mn wani Mugun Abu haka naji a lokacin, na nemi Sha'awar Na Rasa.

Takowa Gabanta nayi nace
"Kina Nufin tilasta mace bashine Jarumta ba?"

"Kwarai Kuwa,Kayi Aure That's what Real men do, Duk Shaƙiyyancinka ,da Rashin Imaninka Zaka Zama Mai faɗa a ji a gidanka Zaka Juya mace yanda kaga dama ,Zaka bada Umurni abi Ko ba'a so idan kayi Aure sai yanda kayi da mace dole tayi Abinda kake so kuma cikin Mutuntawa,ko a waje ma girman ka da darajar ka zasu daɗu"

Sosai kalaman ta suka Ratsani,Amma ko kadan Ban Sauya daga yanayin da Fuskata take  Ta rashin imani ba ,hakan yasa ta tsorata a tunaninta ban haƙura ba ina kan Bakana na ɓatanci ga rayuwarsu, kaman daga sama sai naji tana cewa

"Idan ka gyale mu Muka tafi ,Nayi alƙawarin Ni zan Aure ka”

A mammakince na juyo na kalleta ta ɗaga Mn gira

"Eh ka ƙyale mu ,mu tafi Na dau Alƙawarin Zan Aure ka After Four Years"

In takaice muku zance a ranar kamar ta Asirceni haka nan na ƙyalesu Suka tafi bayan nasa tayi Signing yarjejeniyar Mu Ƙawarta ma tayi Signing A matsayin shaida, ya faɗa yana Miƙawa Baffa Takardar.

Ya ƙara da cewa Tun daga Ranar na dainawa Yanmata fyaɗe,dukda ba karamin Wahala Nasha kafin na daina Gabaki daya ba amma na haƙura ,A iya tsayin Shekaru hudun nan na bada Rayuwata ne ga Neman Tarihi da Asalin Gidan Su Aeesh Na gano ita din yar Gidan manya ce Tanada Tarbiyya Sosai,Shekaran Jiya naji Labarin an saka ranar Aurenta da wani Sa'ar guy din ɗaya da ba'a rigada Anyi Auren ba Nasan Komai Da Anyi Auren kuwa kasheshi zanyi har Lahira wlh.

Dan Dakatawa yayi ya zuƙi tabarsa ya fesar sannan ya Nuna Dattijai Biyu dake Zaune kusada su Abba yace

"Wannan Mai farar Rigar Mahaifina ne,Mai Shadda Blue kuma ƙanin Mahaifina ne,Ga yayan Mahaifinta Baffa Imam Wanda Suke Kira Uncle Imam, har Gida na aika a taho Mn dashi ,Sannan wannan Abba Naseer Mahaifin Ashman ɗinki, Shi ban Sha wahala Wajen Samoshi ba, da ƙafarsa ya Tako yazo Nan ,saƙo na tura masa Akan Wani ɓoyayyen sirrinsa da bayason kowa ya sani,nayi ikirarin tona masa Asiri Idan baizo ba That's how it Happens Within a short Time"

Y ƙarashe Maganar Da Tumurmusa Guntun tabarsa.

Shi Abba  kallon Bamalli yake idanu waje kamar zasu fado daga socket dinsu ,tashin hankali qarara a fuskarsa, he can't believe yau wani yasan ɓoyayyen Sirrinsa da yake ɓoyewa ba ma wannan Ba ,babban tashin hankalin sa Shine Aurenda za'a daura da masoyiyarsa .

Kada mata kai Baffa Imam yayi yana murmushin takaici sannan ya kamo hannunta ya riqe

"ina iya bayar da komai saboda ke amma bazan iya bada ke ba saboda koma menene, You Are my life ,Ke Amana ta ce ,Ni kadai nakeda Alhakin Aurar dake, Ki kwantar da hankalinki bazan Bashi ke ba Bazan taɓa yafewa kaina ba idan na bada ke ta wannan hanyar Bazan taɓa rayuwa cikin farinciki idan kika kasance a karkashin Wannan Mara imanin ba , Kiyi hqr my daughter,bakiyi Laifi ba You did it To save Your dignity, mutuncinki yafi Komai ,a halin yanzu nine ya kamata na kareki daga cutarwa da dukkan rayuwata Bazan Bada ke ga Marar Tausayi ba"

Sake fadawa jikinshi Aeesh tayi tana kuka sosai tana girgiza kai, she can't believe abinda Kunnuwanta ke jiyemata, kodai mafarki takeyi? ,Ta aza idan Baffa Imam yasani Tsine mata zai yi tabi duniya saboda a ganinta Sakarci tayi.

Bubbuga bayanta Abban yashiga yi yana rarrashinta sannan ya dagota yayi cupping fuskarta

"ya isa hakanan Daughter, you are safe " yafada cikin murmushi

Ganin da gaske Baffa yake bazai bashi auren Aeesh ba, Sai yabada Umurnin a ɗaure masa Baffa,babu

Please Login or Register in order to submit comment