Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da 'yan watanni shida  da matarshi Hussaina suka fara samun matsala atsakaninsu sanaddiyar Rashin Adalci ƙiri ƙiri da yake nunawa A tsakaninta da Saude dama 'ya'yanta da ta haifa, kiri kiri Sai Ya nuna mata itafa Haihuwan 'ya'yan kawai tayi ,daga Ƙarshe cewa yayi Ta bawa Saude Ashraf wato Rabeel tunda likita ya tabbatar Masa cewa Saude Bazata taba iya haihuwa ba sakamakon Hujehujen dake mahaifanta.

Firr maryam taqi yarda a cewarta Taya zatasha wahalar daukar ciki da rainon ciki ta Sha wahalar Laulayi da naƙuda Shayarwa da raino, Rana ɗaya Ace ta bada Danta ga Wata!, watan ma wacce batasan Mutunci ba Mai saka Mutunci da butulci?,Abu kaman Wasa Wannan Karon Ma Naseer ya dage akan Fa dole sai An ba saude 'da ɗaya tun suna abin a tsakaninsu har yakai kunnen Goggo Mahaifiyarsa dama Baya ganin Girman ta nan ma ba'ayi sa'aba ,Abu yakai Har kunnen Mahaifiyar Su hussaina abinka d dattijuwar Arziki Haƙuri ta bata tareda Kawo mata misalai da ban baki, babu yanda ta iya Umurnin Uwane , hakanan tabi ta Mahaifiyarta Ta bada ɗanta ga Saude.

Daga nan Fitinar ta fara ya zamana Idan ta samu Ciki tun kan ta haihu Zai Raɗa wa Ɗan Suna Idan Namiji ne.

Ana Haka ta Haifo Saleem ,Wannan Karon Ma irin nasu Ashman yayi mata ya karɓe Saleem dinma Daga gareta ya damƙawa Saude, Saida ya bari ta yayeshi Ya ɗaukesu Duka Ya kaisu Turkish Alokacin su Ashman Nada Shekaru Biyu da watanni biyar a duniya A chan ya Aiwatar da nufinsa Batareda Kowa ya sani ba,Suna Turkish har ta sake samun Wani Cikin Nan ma bata sauya Zani ba tun kan ta Haifoshi ya Sa masa Suna Naseer Amma baiyi Alƙawarin badashi ga Saude ba Wannan karon saida ta haifeshi yayi Shekara biyu a hannunta Tayi Kuka sosai kamar Ranta zai fita tun tana Kukan Zahiri har ta koma na zuci 'ya'yanta hudu Amma Daya take Riƙedashi a wajenta Wannan wne Irin Son kai ne?.

A lokacin Shekarun Ashman Shida duk abinda mahaifinsa keyi yana Sane Hakan yasa ya taso da tsanar Mahaifinsa Ya kuma Ɗau Mahaifiyarsa a matsayin Duniyarsa Tunda bashida kowa Sai ita.

Tanaji tana Gani Idan Sunma Saude Laifi Ta sasu a ɗaka tayita bugu, Abduljaleel Auta yafisu Shan wahala tun yana ɗanyen Jinjirinsa Aka Rabasu da Mahaifiyarsa, Iyaka inyayi Kuka tayita Ɗirka Masa NAN tun baya karɓa har ya dawo Yana Karɓa.

Da yaga Ashman Da Saleem Sun fara Wayau ,Sun haɗe kansu In yana Kuka sai Su daukeshi Suyita masa Wasa ,Haka naseer Shima tare Suke Wasa ,Sai ya sauya Masu gida.

Mahaifiyar Ashman da Ashman dinta Shi kadai ,Sai kuma Saude mai reno Da Ashraf, Saleem ,Naseer da Abduljaleel.

Ba Zaɓin Haj Hassana Bne tayi Ta Haifar masa yara yana rabata dasu ba,Alkunya da nasihar Mahaifiyarta ne yasa take binshi Sahu da Ƙafa ko da wasa bata taɓa Kiran Wani ta sanar dashi Halin da ake ciki ba a ganinta yin hakan Tonawa Mijinta asiri ne,Dukda haka Tasha shan kwayoyin hana Shigar ciki Yana kamata, Likita ne Babu hanyar da zatabi da bazai iya ganewa ba, Rana zafi inuwa ƙuna, Gashi ya Rantse komw tayi masa Bazai taɓa sakinta ba.

A chan Turkish Din yaran Suke Makaranta ,Duk yanda Akaso a raba ƴan uwantaka Gamayyar Jini Tafi gaban Wasa Kawunansu duk a haɗe yake tun Tasowarsu.

Da saude taga shekaru naja ya kamata ace ta ajiye nata kwan Koda ɗaya ne sai Ta tada fitina akan Suje Asibiti Ayi mata dashe In vitro fertilization (IVF) ,Ba don Ranshi yaso ba Amma don Shine zaɓinta Hakanan ya Amince Aka Ciri Semen dinsa Aka haɗa Da Eggs dinta Akayi ma wata Baturiya dashe bayan sunyi yarjejeniyar Zasu bata Miliyoyin Kuɗaɗe ,Watanni tara na Cika baturiya ta Sulluɓo Yara Mata sak Uwarsu Wato saude.

Bataso aka samu mata Ba taso a haifo Maza ne amma ya ta iya naka naka ne hannunka baya Ruɓewa Ka yanke ka yar ranar Suna nayi Yara sukaci Zainab da Nafeesah, ana haka Mahaifiyar Ashman Ta ƙara samun Ciki Inda Allah ya nufeta da samun Mace tayi Murna sosai ,Gata Da son Yara Mata shi kanshi Alh naseer wannan Karon yaji tausayinta sosai Ganin yanda tasha wahala Gurin naƙudar ,Bai taɓa Ganin Yanda Ake naƙuda ba sai a Lokacin.

Bayan Suna Suka tattara Inasu Suka Koma Nigeria Kowa yayi murnar dawowarsu har Shagali Na musamman  Aka haɗa Msu, babu Wanda yasan Su Naseer ba 'ya'yan saude bane Daga nan Sai zumuncin Su ya ɗora daga inda ya tsaya.

Saude kam ji tayi sam batajin daɗin Zaman Nigeria Nan ma tada tsiya tayi Akan zata koma Turkish yarda Abba Yayi ta Koma   ita kadai saboda A lokacin ya kusa Kammala Ginin babban Asibitinsa Da yake Ginawa a nan Cikin Garin kaduna yana Ida Ginawa ya damƙama Haj hassana Takardun Tace na ɗanta Ashman ne in ya girma a lokacin yanada Shekaru Goma da haihuwa ,Tun yana Ƙan kaninshi ya taso da Burin Zama Likita ,haj Hussaina Tayi mamaki Sosai Duba da Rashin mutuncin da Yake nuna msu na iya Shekarun da suka gabata lokaci Guda yayi ma 'dansa wannan Gagarumin Kyautar Ai abin da Mamaki.

Tunda Nooriyyah Ta haifi Sadeeq bata sake samun haihuwa ba sai bayan shekaru Goma a lokacin su Ashman Sun dawo Nigeria ,Inda Allah ya nufeta da Haihuwar 'yan Biyu duk mata ,a ranar da ta haihu Faisal ya diro Nigeria da zunmar Auren Rabin Ransa Bayan ya shafe shekaru da dama ya Tara maƙuden Kudade a ranar ya iske Ta haihu.

Yayi baƙinciki sosai ya kuma kuduri aniyar Daukar fansa Ko ta wane hali Satinsa ɗaya a ƙasar yana Jinyar zuciyarsa.

A ranar suna Yara Sukaci Sunan Aisha Humayrah da Kuma Surayyah Ana tsaka da Gudanar da bikin Suna Aka nemi suree aka Rasa Faisal ne ya saceta da Niyyar daukar fansa Kuma Ko babu komai Ganin gudar jinin abar kaunarsa Zai rage masa radadin Rashinta a Zuciyarsa, a ranar ya bar Ƙasar da ita ya nema Mata Nani mai Reno a chan UK inda yake gudanar da harkar Kasuwancinsa.

Aeesh ta taso Cikin Gata na iyayenta dama dangi gaba ɗaya ta koina sonta ake Barin ma Ashman ,Koda aka Yayeta Mahaifiyar Ashman ta Roƙi alfarma Gun ɗan uwanta da ya bata Aeesh ta hadasu da kanwar Ashman wato Hafsah, a tare suka taso Cikin ƙauna da Kulawar yayansu Ashman ,har yanzu Saude na chan Turkish Itada Su Saleem ko Ziyara basuayi Saidai Abba yaje In yana Less busy yaga yaransa ya dawo.

Aeesh nada Shekaru Uku a duniya aka haifo mata Ƙani wato Habeebullah Wanda a yanzu Suke kira Habeeb.

Arzikin Dr Hassan Na Ƙara bunƙasa Yana Ƙara shahara Habeeb nada Shekaru biyu Shima ya mallaki nasa Asibitin Ido anan cikin garin kaduna,A ashekarar kuma Sukaje Wani Gasa a Egypt anan y samu kyautar wata gagarumin Kyauta kyautar companyn Milo daga wani Dan kaduna da ya halacci gasar, Sosai Dr hassan Ya burgeshi yanda Ya cinye gasar ƙasa da ƙasar da Aka gudanar Tsakaninsa da Turawan Wasu ƙasashe.

Yana dawowa Tasa Matsalar Ta fara ,Kyautar da aka bashi ya damƙawa Matarsa Noor Wato mahaifiyar Aeesh.

A lokacin Dangi ya rikice ,Haka kawai gaba da hassada ya shiga tsakaninsu daga nan suka ƙaurewa Zumunci ,Ajman dake chan Kasar Egypt a da yana Leƙowa Amma yanzu ko ɗan Phone call dinnan Ba suayi dashi, A halin yanzu Yaransa biyu duk Sun Girma.

Ana tsaka da wannan Saude ta tattaro Inata inata ta dawo Nigeria lokacin Ashman Ya samu Admission yana Karatu a KASU.

Gabar Dake tsakanin dangi yayi tsamarinda har yakai Ga Suna Gudun Juna Haka kawai rana Tsaka Dr. Naseer ya tattara iyalansa Suka koma kano da Zama, Ashman Dake Kaduna yana karatu Baya komawa gida sai bayan shekara.

A lokacin Ƙaunar dake tsakaninsa Da 'yan uwansa ya tarwatse babu mai ganin Girmansa dukda shine babba ,A fili su Nafeesah ke nuna matsa Tsana bai taɓa nuna ya damu ba tunda yana Tareda su Saleem atleast he's not alone kaman da.

Ana haka Dr hassan da Yar uwansa Hussaina suka tafi Umrah ,Lokacin Ashman ya zama likita, Saleem kuma yana Turkish yana Nasa karatun , rana ɗaya suka dawo ,Ashman ne yaje ɗaukosu a filin jirgi.

Anan Filin Jirgin aka samu wasu marasa Imanin Da suka ƙona Dr Hassan Da Yar uwarsa Hussaina.

Rasuwarsu y gigita kowanne a dangin Dukda Rashin Jituwan dake tsakaninsu ,haƙiƙa Sunyi babban rashi .

Tun daga ranar Gaba mai tsanani ya shiga tsakanin Ashman da saleem sakamakon Abinda ya gani a zahiri yana Zargin Saleem da kashe masa Mahaifiya.

Yaran Baffa Imam uku Sumayya itace babba,Sai Ummulkhayri da Idris, Sumayya tayi Aure Ummulkhari da idris sun gama Secondary sch Suna jiran Admission ne .

*_Back to the Story.._*

Baffa ,Umma da idris aka kashe Mahaifiyarsu kuma Akayi mata illa....

Innalillahi Wainnailaihirraji'un kadai Ashman Ke ta maimaitawa, yayinda Kukan Aeesh ya daɗu, cewa take _"Wlhy Su Bamalli ne, Sune Suka Kashe Mn Baffa na"_

Hankalinsa a matuƙar tashe ya ɗau Makullin Motarsa ya fice ,da gudu ta mara masa baya tna kuka ,Bai hanata ba don bazai iya barinta a gida ita kaɗai ,Motar ya shiga ya tada bai tsaya ko ina ba sai gidan baffa.

Allahu Akbar Baffa imam Allah sarki Umma da Idris ,Allah sarki Ammy Duk zube suke cikin Jini .

cikin wani irin firgita da gigicewa da fita hankalin Aeesh ta tasaki wani irin kara mai firgatar da duk wani bani Adam dake wurin,
juyowa Ashman yayi da ƙarfi ya daka mata tsawa Shima hankalin nasa a  tashe yKe ya ma  rasa ta ina zai fara .

Kasa Shuru tayi tarinka dukan Ashman take a haukace tana,

"Wayyo Allah na wayyo Baffa na Wayyoni Aisha naga ta kaina ,Bamalli me Abbana yayi maka ka kashe shi?,Nice na maka lefi ,Nice na cantanci na Mutu".

sai ƙara ruggumoshi a jikinta  take ta rik'eshi gam tana kuka mai ban tausayi.

'dai bayan daya Ashman ya dinga daukansu yana kaisu Cikin Mota da ƙyar ya samu ya raba baffa da Aeesh.

Shiga motar yayi ya figeshi a guje a lokacin karfe 2:36am.

Asibitinsa Suka nufa Suna tun kan Su iso Yayi Alarming yan sanda so basu samu matsala dasu a hanya ba.

Emergency Unit aka shiga dasu ,nan aka tabbatar da Rasuwar Idris da Ummulkhayri baffa da Ammi suna raye.

Taimakon Gaggawa likitoci suka shiga basu, Cikin Ƙanƙanin lokaci aka samo Numfashin Ammie ,baffa kuwa A saitin zuciyarsa aka daɓa masa Wuƙa Da kyar ya rayu.

Ana sama Baffa Oxygen Wutan Asibitin ya ɗauke abinda bai taɓa faruwa ba a tarihin asibitin.

Ambu bag aka samu akayi ta matsa masa a hanci ko Numfashin nasa Zai dawo Amma ina ko gezau,Gashi pulse Dinsa na bugawa a hankali a hankali.

Banda kuka babu Abinda Aeesh keyi gani take idan baffa ya rasu bazata Yafewa kanta ba, itace silar shigansa wannan yanayi da batayi ma bamalli Alƙawari ba da yanzu Baffa na zaune cikin Ƙoshin lafiya.

Idanunta takai kan oxometer taga Pulse rate dinsa na raguwa da gudu ta Ƙarasa gadon da Aka shimfidashi Ko ina na jikinsa jone da Na'Urori dukda bbu wuta amma ko wanne na gudanar da aaikinsa kadan kaɗan.

Hannunta ta dungule ta kai masa Duka Daidai Saitin ƙirjinsa.

A razane likitocin Suka ɗago......




Pls
Share
And
Comment

Bintou 🐾
June 15th

Nayi gabas🧘🏾‍♀️
[7/18, 9:27 PM] chubby number: *_Wuka a zuciya_*
_(Bleeding Hearts)_

*013*


Hannunta ta dungule ta kai masa Duka Daidai Saitin ƙirjinsa.

A razane likitocin Suka ɗago suka kalleta.

Sake Dunƙule hannu tayi zata Kai masa Wani Dukan Ashman Ya riƙe hannunta tareda zuba mata mari da ɗayan hannun wanda saida taga taurari na yawa a sararin samaniya kunnen ta saida ya bada sautin kiuuuu sannan ta kuma jin yayi dum lokaci d'aya zanen yatsun shi suka taso a farar fatarta tuni fuskar tayi jazir gaba d'aya ta rasa ina take dan marin ya gigitata.

Ba Aeesh ba Hatta doctors Ɗin dake Ƙoƙarin samo Numfashin Baffa Tsayawa Sukayi Ƙyam Sun kasa Motsawa ,Marin Yayi kamada Almara,Ko a mafarki babu wanda zai iya tunanin Ashman Zai iya daga Hannu ya mari Aeesh ba koda wasa.

Tsawa ya daka mata
"Are u out of ur mind ?, Kashe shi zaki yi? ,his heart is bleeding how can u hit an unconscious Patient like that ”

Hannu tasa ta tallabo kuncinta ,wasu Siraren hawaye suka gangaro mata She's Shocked Yau Ita yayanta ya mara,Ko kaɗan Marin bai dameta ba Tasan Baya cikin hayyacinsa je can do worse than that, A halin yanzu Lafiyar baffanta yafi mata Muhimmanci, muryartq har rawa yake gurin Furta

"Sir Gani nayi babu Artificial Oxygen,Ambubag Doesn't help ,And his pulse Rate is Running Down he Really Need an oxygen therapy And at this Stage it's only Cardiac massage that can help"

Dago kai ashman yayi ya kalleta da idanunshi dasuka yi jaa, siraren jijiyoyi jajjaye duk sunfito akan farin idanun.

sosai Aeeesh taji tsoro da mamakin yadda Ashman d'in ya birkice mata tamkar zaiyi hauka bata tab'a ganin baccin ranshi kamar na wannan ranar ba,

Saurin Tanke Idanunta tayi A gigice ,Taja baya Dafe da Kuncinta Cikeda tsananin tsoro, Shi kam babu abinda yake hangowa sai Auren da baffa ya ɗaura masa ,yanason baffa ya rayu ya gayawa Duniya Yayi masa Aure ,yanaso Duniya suji batun aurensa daga Gareshi Shi kadai ne Shaidarsa a wannan Duniyar, babu abinda Yake hangowa Face Chakwakiyan da zai Fuskanta nan idan ya Rasashi.

"Ki Fita ki Jira Mu A waje"

Kalmar da ya iya Furtawa kenan A lokacin da wata Tunani ya faɗo masa, simi Simi ta fice a Dakin hawaye na zirya a kuncinta,Har yanzu tanajin Zafin Marin da yayi mata har Cikin haƙoranta zuwa maƙogwaronta,Gaskiya ta maru sosai 😔.

Yana Ganin Ficewarta ya cire Ambubag Dinda suke matsa masa,Shawarar Aeesh yabi yabi Suka sauya METHOD ɗin Zuwa Cardiac massage,Dukan Zuciyar Baffa yake Jini na fitowa Amma ko gezau baiyi ba.

Hawaye ne suka zubo masa babu abinda yake hangowa a halin yanzu face Rayuwar sa Nan Gaba,Bazai iya Sakin Aeesh ba Ko da Baffa ya rasu Zaiyi iya Ƙoƙarin sa wajen ganin ya Riƙe Amanar da Baffa ya Dora masa.

  cikin Sa'a kuwa Engineers ɗinda suka je  kunna inverter suka yi Nasarar kunna wa haske ya gauraye ko ina.

Take akayi masa Fixing nasal Catheter Cikin sa'a kuwa Numfashinsa ya fara dawowa a hankali.

Cikeda FarinCiki Ashman yayita jero Hamdala a zuciyarshi.

Ɓangaren Aeesh ma haka,daɗi ne ya Cika ta,itama hamdalan tayta jerowa a ranta, tana waje tana Hangen su ta Space din Kofar.

Giftawan mutum ta gaji an wuce ta bayanta kaman Walƙiya,Saurin juyowa tayi A matuƙar tsorace , bayan Mutumin ta hango Sanye yake cikin Baƙaƙen Kaya Ya Rufe Fuskar Sa da baƙar P-cap ya Fice da gudu.

Haka kawai taji Gabanta na Mugun faɗu take Jikinta ya fara Rawa Sosai,Bayansa tabi da gudu Zuciyar ta na harbawa.

Dif

Aka Sake Dauke wutar a karo na biyu Duhu ya mamaye ko'ina ,lokaci d'aya wani irin fargaba da razani da tsoro mai tsanani ya rufeta Amma dukda haka Bata Daina bin inda yabi ba so take ta tabbatar da Abinda Idanunta suka hango Mata ne tabbas Tasan Bayan Mutumin Ta kuma san Footsteps ɗinsa.

Jin Jikinta take kaman ana rufamata d'anyen fata duk zuciyarta ta raunata a hakan cikin kad'uwa da Zafin zazzaɓin da bai ida barinta ba ta ke takawa, Hanyar da ta tabbatar Zasu haɗu tabi Tunda bai daɗa da giftawa ba Tasan Dole sai ya ɓata lokaci Wajen Hawa Elevator,Ko Kuma ya Bi ɓoyayyar hanya Ta Celling Dole dai in ya diko Su haɗe saboda Hanyarce kadai batada Tsaro.

Aikam Kamar yanda ta hasasa tana Sauka Mutumin na Dirowa Daga Cikin Wani hole ta Sama.

Kallon Kallo Aka shigayi tsakanin shi da ita, Wani irin Razana fargaba da tsoro duk suka mamaye ta Idanunta Suka firfito Saboda Tsoro ji wani irin sanyi ya ratsata har cikin hanjin cikinta tsoro mai tsanani ya rufeta, cikin Rawar murya tace

"Sa...dauki...!"

Tafukan Hannayensa yasa ya Rufe mata baki yana Zazzare ido,
gaba d'aya jikinta rawa yakeyi tamkar mazari sai wani irin zaro idanu tayi cikin tsoro

"Shhhh,Don't talk....Relax ....I can Explain"

Ajiyar Zuciya ta Dinga saki A hankali Na tsawon Wasu lokuta har yanzu Jikinta bai daina Rawa ba.

"Neman ki nazoyi, Hankali na ya tashi Da Yayanki yazo Gidana 'dazu yace yana neman ki, Har gidanku naje ance baki nan, Ɗazu Habeeb ya kirani yace Umma tace Baki da Lafiya Yayanki ya kawo ki Asibiti, Bazan iya kwana banga halin da kike ciki ba shi yasa na biyo ki,Tunɗazu nake vulayi securities sun hanani Shiga Shi yasa kikaga ina yawo"

Ita kuwa ido ta zazzaro waje cikin tsantsar firgita da tsoro ga tarin mamakin Aareef, Ko kaɗan bata yarda da zamtukansa ba.

"Ikhty...!, Ihkty......!!, Ihkty...!!!"

Muryar Ashman taji yaja Kwala masa Kira Cikin Wata firgitacciyar Muryar da bata taɓa ji daga Gareshi ba,Murya ce mai Cikeda ruɗu da tashin Hankali .

"Sadauki na Ka ɓuya kar ya ganka"

Ta furta a tsorace tana kokarin kareshi.

"No me zaisa In ɓuya?, What have I done?"

Ya fada innocently But deep down he's dying.

"No Sadauki...!, hide..!"

Ta fada tana Turashi inda ya fito.

Daidai nan haske ya Gauraye ko ina na faɗin Asibitin, Chan ta hango Ashman Tsaye yana Haska hasken Agogon shi Ko zai ganta .

Da ɗan gudu Ta Ƙaraso wajen shi tana Amsawa da na'am.

"Waye Shi? "

Tambayar Da ya sako mata kenan daidai lokacin da ta iso Wajen sa.

Zaro ido tayi a tsorace,Jikinta babu inda baya rawa.

Ido Ashman Umar ya zaro mata tare da buga mata tsawa fuska a yatsine.

"I said who is he?"

Fadawa Jikinshi tayi tana kuka ,Sosai Tsawarsa Ya razanata Duk ilahirin jikinta rawa na rawa.

"Nashiga uku yaya, yaya what's happening ?" Tafada cikin kuka sosai.

Ahankali Ashman ya lumshe idanunshi yana sauke numfashi silently jinta a jikinsa, sautin Kukanta ya doki dodon kunnenshi, take yayi regretting din Act Ɗinshi akanta, he's nervous,Bai kamata ya zarge ta da Wani abu ba don ya jiyo mutyarta tana Mgn ita daya, ya aza da wani take Shiyasa Ya sauya Act dinsa akanta.

Shiru Daren ya dauka babu Abinda kakeji face Ƙarar Sautin Tsuntsaye da Kuma Sautin Ajiyan Zuciyan Ashman mai kamada Shessheƙar kuka, Shi kaɗai yasan yanda yake ji a halin yanzu, ya kasa cetar wanda ya bada rayuwarsa Don Sama masa Future Mai kyau.

Ahankali Aeesh  ta dago idanunta dasuke sheqi saboda taruwa da hawaye yafara a idon da kuma tsananin tsoro, bata saukesuba a koina sai cikin na Ashman da shima ita ya kafe da idanu Hawaye Sunyi Tsilli Tsilli a idanunsa.

Da sauri ta sadda idanun gabanta na faduwa don ba qaramin tsoro taji ba Ganin Hawaye a idanun Yayanta.

Shima sadda kai yayi ahankali yana lumshe idanu yana sauraron yadda zuciyarshi ke halbawa.

Hannunta taja Sukayi Cikin Asibitin

"Innalillahi Wainnailaihirraji'un"

Kaɗai yake maimaitawa a ransa yana ƙoƙarin Ɓoye Damuwarsa a fili.

Dakin da Aka Kwantar da Baffa suka nufa

fizge hannayen ta tayi da k'arfi cikin tashin hankali ganin ya nufi kan wani Mutumi wanda aka masa Complete lulluɓa da farar Qyalle yana k'ok'arin buɗe kyallen.

"No.....!, stop it...!"

Kasa Bude fuskar yayi ,Zuciyarsa Na ƙuna.

"No Baffa Bai Rasu ba, Innalillahi Wainnailaihirraji'un Baffa... No Baffa....! ,N0Ooooooooooooo"

Bubbuga kanta ta shigayi da Bango tana Kuka sosai mai tsuma zuciya batareda tayi la'akari da Dare ne ba, hakan Ya jawo hankalin Likitoci  masu Aikin dare .

shi kuwa Ashman  cikin firgici da tsoron ganin zata yi kisan kai,Zata kashe kanta gaba d'aya jikin shi sai rawa yake yi,
cikin b'acin rai ya fizge hannayen ta Ya jawota tana kuka suka fice daga Asibitin

Direct inda yayi parking Motarsa ya nufa ya tura ta jikin sit d'in ta koma ta bugi jikin marfin motar sannan ta sake tasowa tana k'ok'arin sake rik'e kan motar,Tsawa ya buga mata ta kame ta nutsu Sai ajiyar Numfashi take ta faman Saukewa a hankali a hankali, Firgici ya Gama Gigita mata ƙwaƙwalwarta Gaba ɗaya,Bugun zuciyarta kam Ya dade da sauya fasali ya fara bugawa Abnormally Kuka takeyi mara Sauti ,Yanzu Shikenan ta rasa Baffanta?, Wandaya maye mata Gurbin uba a lokacin da Mahaifinta ya rasu Shike daukar duk wata ɗawauniya nasu,Shi ke msu Cida sha da Sutura dama duk wata hidimar Su ta Rayuwa ,Dukda Ummanta na Aiki tana samun kudaden Shigowa, kuma ana Kawo msu Wani abu daga Cikin Kasonsu na Asibiti da Companyn da mahaifinsu ya bari, dukda haka Baffa bai taɓa gajiyawa akan komai nasu ba.

Wani'dan karamin Ƙwaro ne ya shigo ta Windown kotar,a hankali ya fara yawo Bisa Fuskar Ashman ,tun Ashman bai lura da shi ba har ya Tsaida Idanunsa akan kwaron ,Tsaida Idanunsa keda wuya Sai ji yayi  kwaron Ya shige Cikin idanunsa.

Duhu ne ya mamaye Ganinsa ,ya kasa Controlling Driving dinda yake ,Hannunsa Ya cire daga Stirring Ya Dafe Idonsa da Ƙarfi.

Daidai lokacin da Motar ta bugi Wani gini ,Ƙara Aeesh ta saki a Gigice Ta ƙamƙameshi Daga nan basu Sake sanin Inda suke ba.

******
*Bamalli*

Cikin Matsanancin Sa'a yan sanda suka Bincikoshi cikin Gidan suka Kamashi tareda yaransa, Dama Tuni Iyayensa sun Gudu ,Yan sanda Sunyi arresting Ɗinshi da burin Daukar fansa Ga kowanene y haɗa masa Wannan Tuggun, Yafi Zargin mahaifinsa Don yaga Alamun Rashin Jin dadin Abinda yayi a Fuskarsa.

*Aeesh*

Kiiiii Kwaa

Ƙarar Bigewar Da motar tayi Kadai takeji a Kunnenta.

A firgice Aeesh ta farfad'o cikin k'ara tare da rarumo Umma dake gefen ta,

karan da Aeesh yayi ne yayi dai-dai da farfad'owar Ashman dake Chan Asibiti a razane.

"Wayyo Baffa na, Wayyo Yaa Aash, Wayyo Allah ya kashesu duka Wayyo Allah Na shiga Uku na lalac...."

Saurin Rufe mata baki umma tafi da tafin Hannunta.

Sai a lokacin ta lurada tsirarun Mutanen dake Cikin Kai kawo a ɗakin Wasu na zaune kan gado duk sun zuba mata ido.

Hawaye ne suka ziryo daga cikin Idanunta, " _Shikenan Hasashen ta ya tabbata, Ashman da baffanta duk sun mutu_ "

"Kiyi Haƙuri Yasebo na ,Ko wane Mai rai mamaci ne "

Kankame Umma Aeesh tayi tana Kuka, Shikenan Tata rayuwar tazo ƙarshe Masu bada Gudunmawa Wajen Gina rayuwar Ta sun Tafi Shikenan Baffa da Ya Aash.

"ALLAH yyima Baffanku Rasuwa yau Kwanaki huɗu kenan , Kullum Sai Ashman yazo dubaki Ɗazu ya bar nan Gun bayan ya gama Dudduba Shi"

cikin hard'ewar harce da rawar jiki ta kamo hannun umma ta,Harce a rik'e maganarta bata fita sosai Saboda yadda bugun zuciyarta tayi ƙasa haka muryarta numfashi a cushe Idanun ta  sunyi jazir tamkar rushi cikin in Ina tace

  "Am...mie Ya Aash na Raye?, to Baffa fa?"

Sai Kuma ta fashe da wani matsanancin Kuka mai tsuma zuciya.

Zata iya cewa Tafi kowa jin rasuwar Baffa don Ita kadan Tasan Abinda Ya faru kafin Ya rasu da kuma Abinda ta gani Lokacin da ya rasu.

Gidansu Da Gidan Baffa cike yake da yan'uwa Da abokan Arziki, Tun Da Akayi rasuwar Abba da Kawu Hamza Suke zirya tsakanin Kano da Kaduna kawu Ajman kuwa Baida Labari don a halin yanzu babu mai Layinshi.

Ashman Kuwa Ya samu matsalar Ciwon Ido da gocewar Ƙashin Ƙafa tun bayan Haɗarin da suka samu ,Amma dukda haka Kullum Sai yazo ya duba Aeesh , Shima Aareef Kullum saiyazo Burinshi a halin yanzu bai wuce ta farka Ta bashi Kuɗin Aurensu da tayi masa Alƙawari ba,Don Saida kawu Hamza Ya Sake Jadda da masa Kwana Biyu ya ƙara masa Saboda rasuwar da Akayi.

Aeesh tayi kukan da yafi na rasuwar Abbanta a wannan lokacin kam, hakama babban ruɗanin Ciwon idon da Ashman ya kamu dashi Duk Suka hadu suka Kusa maidata kurman gaske bata uhm bata uh-uhm.

        Ma'aikatan Asibiti da ƙawayenra masu Zuwa dubata sun ɗan tausaya msu a tsakanin nan, dan kuwa kullum sai an samu masu Zuwa kuma babu Wanda zai shigo bada leda ko wani Abun ba tun Abin na burgeta har ya koma Bata haushi don ta lura da Alama Gulma ke kawo wasu, har a lokacin Reey na Asibiti ba'a Sallamota ba, Ko a daren Da abin ya faru tana Chan Asibitin, washegarin ranar da Aeesh ta farfaɗo ta Saci hanya Ta zo gidan, Aikam duk sunsha kuka kamar ba Gobe.

         Bayan kwanaki bakwai na makokin baffa akai addu'ar bakwai, sai aranar ne taga wasu tsiraru a cikin dangi Don har Umma sauda Saida tazo.

  A Ranar Aareef yazo Gidan da ƙyar ta Iya Tashi ta fakaici idon jama'a ta fita.

Yana Tsaye a parking lot jikin Wata Yar mota da ya shigo dashi.

Buɗe mata motar tayi Ta shiga Fuskarta babu yabo babu fallasa.

Zama tayi ta zuba masa ido shima Tsaye yake ya zuba masa nasa idanun

"Bear..!, I did Not Understand Me yasa kazo Asibiti As that same night Randa Aka Kashe Baffa, An suspecting something"

Ta fada straight forward Tana Duban Cikin idanunsa.

"I can Explain...!"

"Explain What Aareef!, Kaine kayi Disconnecting Electrics a Wannan Daren Which hakan yayi leading to his death ,

Please Login or Register in order to submit comment