Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

su tazo daya Amma Fa shi Bracket akwai son Mata, Cikin Yan matan sa akwai Nicky da Sayrah kawayen Maryam ta dalilin yan matan Nasa Yasan Maryam don Ko kadan bata sake mishi Fuska ,Shi kuma hakan ne yasa ya da fata sonta, da ya fada Ma Saleem



Nayi Gabas 👨🏽‍🍳

Comment
And

Share fisabilillah 😍

Bintou ✍️

26th Oct
[10/27, 10:11 PM] Bintou abdool: *WUƘA A ZUCIYA*
( _BLEEDING HEARTS_ )


_Bintou_ ✍🏽

*044*



Cikin Yan matan sa akwai Slimzy da Ruth kawayen Maryam ne na Ƙud da ƙud don Ko Lectures Zasu tare suke zuwa

Ta dalilin yan matan Nasa Yasan Maryam Amma Ko kadan bata sake mishi Fuska ,Shi kuma hakan ne yasa ya da fara sonta.

Wata rana Sun fito Lectures Sukaci Karo da Bracket da saleem Sun dawo daga Demonstration block Zasu shiga Lectures , anan Bracket yake nuna mishi Maryam Dama ya daɗe da bashi Labarin ta, taɓe baki yayi Batareda yace komai ba.

Zaman Saleem Shi kadai a gidansa ya fiye masa komai Shi yakeyi wa kansa komai tun yana ƙarami, shi daya yake rayuwarshi a Tangamemen gidan Da Abba ya sake Mishi sai dai su Naseer su kawo mishi ziyara Abokan sa kuma da sunzo yake kadasu Guess Room, Bai Yarda wani aboki yazo gidan sa Yayi hour daya ba kaman Yanda baya bari su kwana.

Lokacin da Maryam ta shiga Semi final year , University din ta samu wasu sauye sauye, aka kori Scholarship Student a Hostel kuma gwamnatin ta daina Biyansu Allowance ta kuma daina ciyar dasu,Ta shiga Tsaka mai wuya ta rasa ya zatayi? A lokacin har ta haƙura.

Domin kuwa ta gayama Abbanta yace babu ruwan shi bashi ya Kaita ba, shi da so samu ne ma a koreta a makarantar ta dawo kasarta da Zama , haka Zeeyk a lokacin shima yana fama da tasa Matsalar takudin makaranta don Shima An cireshi daga Cikin yan scholarship.

Babu Yanda ta iya, haka nan ta kwashe kayanta ta baro Hostel Tana shirin Komawa Gida Nigeria Allah ya haɗata da saleem , Shine ya Taimaka mata, ya maida ita Gidanshi da Sharadin zata Zauna a gidan ne a matsayin Mai aikinshi, Kuma bazata taba masa Gardama ba Akan Akan Dukkan buƙatar da yazo mata dashi.

Batareda tayi dogon Tunani ba ta Amince, saboda burinta a lokacin bai wuce ta Samu matsugunni ba,bata son ta rasa Karatun ta.

Rayuwarta a Gidan Saleem ya Zame mata tamkar Zaman kurkuku ko nace, Rayuwarta a gidan ta zama tamkar Rayuwar Sarki da baiwa, Rayuwa ce ta matsi da Rashin 'yanci.

Ya maidata tamkar jakka, Da Aikinsa da na Abokansa Duk ita keyi, batada time din kanta tana tashi da safe da aikinshi zata fara, kuma ta gama da nashi
Itace take Tashinshi da Asuba, Ta Zuba mai Ruwan Alwala, tana Zaune har Ya gama Alwalar, ta shimfida masa Darduma, nan ma tana zaune har ya idar.

Yana Idarwa take Dangwalo Mai Abin Wanke baki ta Miƙa masa Brush Yayi wanka, Saifa ya shiga wanka take samu tayi nata sallar ,Sannan Ta shige kitchen Tayi Masa Breakfast .

Normally Breakfast dinshi a weekdays Shine Sandwich da Black coffee ,During weekends kuma Nigerian Lipton da fried Irish with Small chicken.

Idan ta sake tayi Missing wani abu a wajen Girkin Tofa a ranar Ta shiga Uku, zataga Cin Mutunci kala-kala Aiki zaisata Tun safe har rana.

Shi yake ciyar da ita saboda University sun daina ciyar dasu ,kuma ya Cigaba da biya mata Wasu Xpensis dinta, Saleem Yayi PHD a rashin imani, bashida tausayi ko kadan Especially Akan mace, ance kukan mace na sanya Zuciyar namiji tayi rauni ,Amma banda na saleem Shi burin shi Yaga Kukan Mace , Sometimes ma da gangar yake mata wasu abubuwan Don yaga Raunin Ta

Amma ko da wasa bata taɓa Nuna mashi gazawarta ba,a kullum fuskar ta a hade take babu yabo bbu fallasa Amma bazaka hango Fushi ko ɓacin Rai a cikinta ba, koda kyauta yayi mata duk kankantarsa karba take ta masa godiya.

hakan ba ƙaramin Bakanta ran Saleem yakeyi ba shi yafiso idan ya Wulaƙantata Tayi yelling at him ta nuna masa fushin ta, tace ta haƙura ta daina zama dashi, ko kuma yaganta tana Kuka har Allah Allah yake Wata ran Ta masa Laifin da zai kaisu ga dambe, Amma sai ta nuna bamata da lokacin wannan.

colleagues dinta Kallon wani irin kallo Suke mata, Suna Alaƙanta ta da jaka mara Zuciya, a lokacin sam bata damu ba, gani take what people think about her doesn't matter, Since no body knows her story ,No body know the Hidden figures behind her story.

Bai san Sunanta na gaskiya ba, kuma bai damu da ya sani ba, Ko wane suna yazo masa Dashi yake kiran ta, Sunan Animals Dama Sunayen da basu dace ba Ita kou koda me ya kirata Amsawa takeyi cikin girmamawa, ya lura Tanada Isa tana kuma ji da kanta da kuma girman kan dake damunta .

He wonder why she's so proud of herself Talaka da ita, jin kanta yayi yawa, me take dashi? Metake taqama dashi?

Idan kyau ne akwai wadanda suka dameta suka shanye a kyau suna binshi yana Wulaƙanta su Su nuna masa fushin su, akwai unique ladies na Turkish Masu Cikar diri wadanda saita raina kanta agabansu suna neman ko kallo daya ne yayimasu amma basu isheshi kalloba, Suma yana Wulaƙanta su Su kumayi faɗa dashi.

Mace bata taɓa Raɓarshi Tayi kwana biyu ba tareda ya sata hawaye ba ,in kou batayi Kuka ba sai ya sa ta raina kanta ,amma sai gata tayi More than 5mounths baiga Tayi ko tagumi ba, mace bata ta6a nuna halin ko-in-kula dashiba kamar yadda takeyi, wasu ma dying suke dan suji ya furta koda kalma dayace garesu amma this one she don't even care ko zai shekara Yana Magana Kan ta a ƙasa .

Bai taɓa sanin akwai talakawa masu girman kai da jida kai ba sai akanta, yasaba wulaqanci ana burauba hakan yasa yakejin zamanshi da ita wani iri, idan tanuna she didn't care about his act sai yaji kaman Ya mutu, tanata rayuwar Takeyi kaman Bata ma san yanayi ba, Shi ke Wulaƙanci And again Shike suffering Akan Act ɗinsa gani yake it's an insult to him ace kamar wannan yarinyar Yar talaka yar Aikinsa na nuna bata damu da wulaƙanshinshi ba, kaman Wasting effort ɗinsa yakeyi don ya takura ma rayuwarta.

Yawan Zuwan Su Oukky gidan ne yasa Suka ƙulle da Bracket ,Wanda yake ganin kaman Saleem Yayi masa kwace ne, Don duk sanda Yazo gidan basu Rabuwar Arziki dashi.

Watannin ta biyar a gidan Lokacin yana shirin yin Project dinsa, yayi choosing topic din IVF INVITRO FERTILIZATION (Dashen Ciki), kuma bayan yayi rubutu Dole zai samar dashi Practically .

A lokacin sai ya rage Muguntan da yake mata, Don a ganin shi Wasting effort ba Nashi bane, zaiyi trying another way da zai muzanta ta ta yanda zataji ta tsani kanta.

A lokacin tayi wani rashin Lafiya ,Ciwo tayi sosai kaman Bazata rayu ba, Tayi More than a week Bata San inda kanta yake ba, shi ya Kaita asibiti haka shike jinya,sai yayi amfani da lokacin Wajen Daukan egg dinta, shine ya haɗa da nashi Semen din Akayi dashe a mahaifar wata bazawarar Baturiya Gravida 8, (Mai haihuwa takwas) bayan ya biyata makudan kudade .

Maryam bata San komai ba dangane da wannan Lamarin, cikin Sa'a Kuwa matar ta dau ciki, dayaga haka sai ya rage Matsanta mata.

Ya fara Sakin Mata fuska yana janta da hira dukda Haka bata wani Sake masa sosai.

Tsabar Shu'umanci irin na saleem, tun bata kulashi saida yasa Ta fara Kulashi, tana Biye mishi Abinda ko a mafarki Bai taɓa tunanin zai tabayi ma mace Murmushi ba sai gashi In Yana tare da ita har dariya yanayi, itama sai ta biye mishi Amma fa baya ganin Murmushin ta da Arha ,duk Inda yace abi nan take bi, A wannan Lokacin ya rage mata wasu ayyuka kaman tashinsa sallah asuba da kuma sashi bacci ,sai ya ƙara mata Manyan Ayyuka idan ya fito wanka ita ke shafa masa mai, ta gyara masa gashi, ta zaban masa kayan da ya dace ya saka .

She should have stand her ground ta nuna masa limit dinsa. Amma ta barshi kusan komai nasa tare suke yi, shi ba muharraminta ba sannan ga strong attraction da ya fara shiga tsakanin su, a lokacin da ya gama karatun zaman Gida yakeyi, yana Jiran Result da Kuma Project dinsa🤰.

Koda fita zasuyi da Matching Outfits Akoda yaushe hannunsu manne da juna Nunama duniya suke kaman Da gaske su Couples ne, amma a waje da zarar an shigo Cikin Gida relationship zai koma Like Boss and maid, shine ya tsara Mata hakan, Sai ya zamana kullum Suna Hanyar fita ,Sune wannan Club din gobe Birthday party jibi wedding Party,gata wannan Mall din , Citta Play center, sai ya zamana basu samun Time din zaman Gida, da zarar ta dawo daga School take binshi su fita ,tarayyan Ta da saleem ya sama ma Yan mata da dama Baƙin ciki akanta Kusan matan Turawa da Rashin iya Ɓoye kishi, a fili suke nuna mata Sun Tsaneta.

Dariya kawai Takeyi a ranta tace _Da kunada Idea kan yanda na tsaneshi da ko kusa bazakuyi kishi dani ba, A halin yanzu shi uban gida na ne, Da zarar na Gama karatu zan Tafi In bar maku shi_

A hankali ya fara Shafa mata nashi Halin dama Turawa sunce character is contagious, Dama saleem Bai Iya samun Wuri ba yanzu abubuwan da suke aikatawa a wannan Gidan ko a mafarki akace maryam zata aikata something like that zatace karya ne, Ya maidata tamkar kanwarsa ta jini bayajin kunyar Yin komai a gabanta, itama bata nuna ta damu ko ta kwaɓar masa Hugs and body contact Kam ba'a Magana ko a gaban waye dama kuma ƙasar Turai babu ruwan wani da rayuwar ka ,babu mai kawo mata Ziyara balle asan Halin da take ciki.

Abinda Bata amince masa ba shine, taɓe taɓen nan na yaran Zamani, ina ma yaga Fuska shima sai ya kama kanshi yake rage zafi da Rungume Rungume.

Kafin shekara ta zagayo wani irin shaƙuwa ta Musamman ce ta shiga tsakanin su ,a lokacin Baturiya ta jima da haifo musu santalelen dansu, ya kaishi Gidan marayu bayan ya saka mishi sunan Mahaifinta Sa'eed Amma yana kiranshi da Ayyan, har zuwa wannan Lokacin bata sani ba.

today is her graduation day, Ranar da ya kamata ya zama na fari ciki a gareta.

Yau ta fito ranta a ɓace sunyi faɗa da Friends dinta su Slimzy akan Bracket yau Saida ta nuna musu Asalin Halinta Ta cire rigar Mutunci tayi musu ta tass, Asalin Halin ta da tayi keeping just to make peace yau Saida Aka kaita bango.

Bata taddashi a gida ba, don Haka sai ta shiga Gyaran Gidan, Tayi mopping ko ina Sannan Ta saka Turaren wuta a Electric burner Tayi Socketing dinshi, nan Take ko ina ya haure da daddaɗar Kamshi, tana tsaka da Jona Turaren ya shigo ko kallonta baiyi ba ya shige dakinsa, itama yanda ya nuna bai ganta ba, haka ta nuna bata ma san ya shigo ba.

Tana Gamawa ta nufi kitchen don Sama ma kanta abinci, Message ne ya shigo wayarta , ta duba saleem ne Yace ta kawo mishi Something Liquid.

Tsaki taja A ranta tace Like king kana Chan kana bada Umurni anan.

tadauki tray ta bude fridge tafiddo drinks biyu daura akai da Cups biyu ta debi snacks ma sannan tafito kitchen din tanufi falon shi.

haka kawai taji beating din zuciyarta na chanzawa, She feels very nervous and uncomfortable Ranta da ke ɓace.

Koda takai bakin kofar saida tadanyi jimm na some seconds kaman wannan shine karonta na farko da zata shiga dakinshi.

A hankali ta daga hannu ahankali tayi knocking sannan ta tura kofar bakinta dauke da sallama.

A natse ta ƙarasa ciki Kanta a ƙasa da wata iriyar kasala ya kafe kofar da idanu .

Lumshe idanu yayi akanta ya bude jin wani sanyi na ratsa zuciyarshi tunda ya haɗu da ita yakejin irin wannan Sanyin Amma tayau ta zarce ta kullum.

Tana Direwa ta Miƙe zata fita, ya kira sunanta a kasalance

"Monstang"

Juyowa tayi Batareda ta yarda ta hada ido dashi ba

"Sir..."

"Bazan iya sha ba"

Ta fada cikin narkar da murya.

Duban shi tayi duba na ban gane ba, yace ta bashi da kanta bata Musa ba ta zauna Ta zuba a cup ta kai bakin shi, sai ya girgiza kai Wai ba irin haka ba so yake ta fara sha Sai ta bashi mouth to Mouth , Iyye🙄

Da farko banza dashi tayi , kaman bataji shi ba, Sai Ya sake maimatawa Nan ma banza tayi masa ta kai Bakin Cup din Bakinshi Batareda tace Komai ba.

Ƙin bude bakin Yayi ya zuba Mata ido cikin jin haushin kansa da ya zubda girmansa ya nemi Such aThing a wajenta bai taba neman abu ya rasa ba a rayuwarsa, bata isa ta zama History breaker dinshi a Koda yaushe ba.

Itama ganin yaƙi buɗe bakin Sai ta dire cup din ta miƙe zata fita.

Ya wani jawota ta fado jikinshi riƙeta Gam Kafin ta an kars ya haɗe 👄 wuri ɗaya, Riƙeta yayi da iya ƙarfinshi itama da iya ƙarfin ta take ƙoƙarin kwatar kanta amma ta kasa, Saboda saleem Mutun ne mai wani irin karfin da Ko namiji dan uwansa ya ma irin wannan riƙon Sai yaji a jikinsa ballantana ita da take mace Mai rauni ,Taji gaba ki daya Ƙarfin ta ya ƙare, Ta sake mai komai banda hawaye babu abinda ke Diga a Idanunta, sakewan da tayi shi ya ƙara birkitashi ya fara Fita a Hayyacinsa, Daga nan Sai ya fara yunƙurinyi mata fyaɗe da Ragowar ƙarfinta ta laluba ta dau Glass Cup Dake dauke da Fresh juice ta fashe shi akanshi, nan take ya dawo Hayyacinsa Wani matsanancin Zafi Ya ziyarci kwanyarsa take Gurin ya fashe jini Ya fara fita.

Kasa Motsi tayi, ta Kife kanta a cinyarta Wani irin kuka mai karfi yaci ƙarfinta, Miƙewa yayi Cikeda jin haushin Kansa ya bar Mata dakin Jini na Diga daga kansa.

Tunda ya fita bai sake dawowa ba, har dare

Tunda take Bata taɓa shiga tashin Hankali kwatankwacin irin na yau ba, ta kwanta amma ta kasa bacci.

So Saleem thinks was that tough ? A tunanin shi itama kalar sauran matan ne?, he think he can Use her anyhow. Wato ni nice Maid Dinshi so yake ya maidani ƙaruwar shi?, me yake takama dashi a wannan Rayuwar?

Tunawa tayi da Yanda rayuwake garata tun bayan Rasuwar Mahaifiyar ta, Mahaifinta da Family dinshi duk sun manta dasu, can You Imagine a lokacin yayan din Mahaifinta shine Sarkin Zaria gaba ɗaya a wannan lokacin?, A halin yanzu zata iya cewa batada Kowa sai Yayanta Zain da kuma Cousin dinta Wanda shine Mai Kiranta a koda yaushe, Idan yawonshi ya Bigoshi ƙasar yakan Kawo Mata ziyara Wato muzzammil (Bamalli) , bayan Su batada Kowa sai Saleem.

Har 3:27 babu Saleem babu Alamar shi, baccin kuma yaki zuwa.

Sai ta mike ta fara abinda ta cikin dare , ta tashi ta fara gaya wa Allah kokanta, tayi adduoi sosai akanta A karo na farko sai ta sako Saleem cikin addu'ar ta, tana nema mishi guidance na ubangiji.

Sai a lokacin ta fara wani tunani ko bashi da iyaye ne? Daga ita harshi zaman Kansu Suke babu mafada , Ba Aiki yakeyi ba Amma Kullum sai yaji Alert , bata tabajin yayi maganar iyayenshi ba.

addu'ar iyaye itace addua mafi inganci a gurin 'ya'yansu, saleem baya samun wannan, shi kansa baya yiwa kansa da kansa addu'ar , da zarar ya idar da Sallah Yake Tashi babu istigfari Ballantana Taga yayi Karatun alƙurani.

Duk adadin zaman da tayi dashi ta lura baya barin sallah ,Kuma ya iya larabci yana Kuma da Ilimin Islamiyya daidai Gwargwado Akwai lokacin da taji Yana waya da Naseer ,da Larabci suke maganar yana Masa nasiha harda jan ayoyi, tayi mamakin ina ya koyi Karatun Arabi bayan Gashi nan dai shatara shatara bashida Alƙiblah .

Ta jima tana adduoi tana Gamawa ta kwanta akan sallayar tayi baccina.

Da assuba ta tashi yayi sallah, har ta koma zata kwanta taji still ranta babu dadi

Tunanin Abinda ya faru jiya take, hawaye Suka sauko mata, ta sa hannu ta shafo fuskarta ta goge hawayenta, zuwa kan lips dinta da suka kumbura, tun da ta mallaki hankalinta babu wani namijin daya taba koda rike hannunta ne until she met him, and he has kissed her today ,And even tried rape her , hannu tasa ta share hawayen ta Daidai lokacin da ya Turo kofa ya shigo as usual babu ko sallama

Bata dago ta dubeshi ba ta gane shine don Ƙamshin Turarensa ma ya sanar da ita.

Shuru sukayi babu Wanda yayi magana cikinsu, Almost 2mins Yana Tsaye akanta , kukan yaron da taji ne yasata duban Shi da mamakinta sai yaro ne a hannunshi, Yaron sai wasa Yake Abinshi, abu mafi ban Mamkin ma shine Yaron Kama yake da ita kaman hoton ta sanda take yarinya.

Ta kalleshi shima kallonta yake fuska a daure, he looks very sad

Tace"what happened?"

Nan take ya gaya Mata matsayin Ayyan a wajenta, Saleem baya karya duk Girman abu fada yake, he don't care how you feel ko bayan Ya Fada

He keep it to the world that he's a monster, Ranta ya ɓaci Hankalin ta ya tashi ta nuna mai bata yarda ba Kuma bazata raini Dan shege ba ,har asibiti Sukaje inda aka tabbatar da cewa Baby dai Dan su ne, ya Kuma nace akan Sai ta karbi Yaron, sosai rayuka suka ɓaci, har takaisu ga fada Kaman yara Ta biya thugs Suka masa shegen duka dukda haka bai dandara ba, Dole so yake ta karbi Yaron.

Babu Shiri ta kwashe kayanta ta dawo Nigeria, a gidan Kawar Mahaifiyar ta ta sauka a lokacin Mahaifinta shine Minister Of health .

Watanta daya a Nigeria Aka tsige shi , sai a lokacin ya waiwayo ta ya Bata hakuri akan Rashin Kulawan da ya nuna mata Siyasar sa ce ta ɗauke mishi hankali bashida Time na kansa ballantana na iyalensa, _Hmmm Wai siyasa!, kenan ya Gommace ya Rayu yana Gina rayuwar wasu alhalin Ga nashi chan a wata kasar suna bauta_

Amma You know tsakanin da da uba , nan take ta yafe masa amma fa tace bazata koma gidanshi ba, a barta da mama Sunfi sabawa , dakanta ta Roki Dad dinta da ya Zuba ma baba (Mijin Mama) ya zuba mishi kaji a Keji, Haka kuwa akayi Tangamemen wuri yasa aka ware a gidan Ya zuba mashi kaji, kullum Sai yasa an Yanka ta sarrafa da daddare nayi sai takai Eatery Tana dawowa taba baba kudin da haka Ta siye Zuciyar Yan gidan ta zama tamkar yar gida itama.

Har zuwa lokacin Zeeyk nachan ƙasar U.K ya gama Karatunsa inda ya karanci Fannin Photography, a nan yake Kulada lafiyar sa, da yaga ta dawo sai ya fara tunzurata akan Daukar fansan ran mahaifar su, Shi da kansa Ya nema ma Maryam Aiki a asibitin Ashman saboda anan Mahaifiyarsu ta fara Jinya kafin a Kaita babban Asibitin Abba Inda daga nan bata sake fitowa ba.

Ta dauka Ta rabu da saleem kenan na Tsawon rayuwa Sai ta kuma haduwa dashi a Asibitin a matsayin Senior Gynea doctor na department Dinsu.

Haduwar su taso ta tado mata da abubuwa da dama But she keeps her courage, pride and dignity Ta nuna kaman bata taɓa ganinshi ba sai a ranar, wannan Karon ba Boss and maid bane Worker and co'worker ne.

Shima Da yaga Haka sai ya kama kanshi Don Ya tunasar da ita Bautan da ta dade tanayi akansa yana Shiga Office yasa ta kawo masa Breakfast irin wanda ya saba ci a can, wato Sandwich and coffee Bai gaya mata Ƙa'idar ba, itama bata nuna tasan Wata Ƙa'idar sa na rashin Son Albasa da yaji ba, ana hado mata ta kawo masa with full of Onions and pepper A ranar tasha wulaƙancin da har ta manta Rabonta da ayi mata kalar wannan wulaƙancin da saleem yayi mata.

Tun daga Ranar da saleem Ya fara aiki a asibitin Ashman bata sake samun Wata kwanciyar hankali ba, Saida ta gama abinda ya kawota ta bar Mishi Aikin Har zuwa lokacin Bata taɓa Nuna ta taɓa rayuwa dashi a chan baya ba, Shima yana Ganin Haka ya banzatar da ita a cewar sa lokaci na zuwa, Lokacin da Zai tunasar da ita Rayuwar Su ta baya, Lokacin da zai Kawo karshen Girman kai da jijjida kanta ,shine yanzu kuma Nata ya sake hadasu a inuwa ɗaya.

A yanzu ne lokacin yayi, Shine yasa aka kawo mata ɗanta a yanda babu yanda ta iya Dole ta rungume shi, in ba haka ba Dakansa zaije har Gidan Iyayen ta, ya nuna musu yaron yace Sun sameshi ne ta hanyar da bai dace ba, Yace zina sukayi Suka sameshi , ya kuma Nuna masu Hujjar sa ta video clip na Ranar graduation Dinsu .

Gani yake yanzu lokaci ne da zasuyi zaman Mata da miji su kore duk wata Gaba, idan kuma tace zatayi Girman kai zai nuna mata ya fita.

Kwanansu Butty biyu Suka tafi suka barsu Daga ita sai Shi da ɗansu Ayyan Wanda har yanzu bata san Cewa sunan Mahaifinta aka sa masa ba.

*Canada*

A hankali ta tura ƙofar shiga cikin Dakin ƙirjinta na bugawa, tsoro da fargabar Halin da mahaifar ta ba.

A tare suka Zura kafa ciki da Sallama dauke a bakunansu, gently ta ɗaga kanta zuwa direction ɗin da take ganin gado, Ammie Na kwance flat idanunta a rufe, sai nasal Cannula Ne manne a Hancinta wacce aka maƙala masa a hanta domin samun daidaitowar numfashin ta, sanye take cikin Hospital Gown Light blue.

Yatsunta Manne da SPO2 machine Yana reading Pulse dinta, fuskarta tayi wani irin fari ta kumbura ba sosai ba, haka ma tafin ƙafarta da hannayen ta duk sun kumbura.

Dakin Yayi tsit sosai Yanayin dakin Mai ban tsoro, ga Sanyin A.C ta ko ina mai ratsa Jiki har ɓargo.

ɗit ɗit sautin SPO2 ke bada sauti a hankali,Ɗago kanta tayi Ta dubi Pulse reading ɗinta Yana Tafiya ne in a normal Range, Ga kuma Ammie a kwance Kaman Matacciya.

sharrr hawaye ya silalo mata, kasa ƙara sawa wajan tayi ta zube a inda take tare da sakin kuka, Slowly Ashman ya duƙa ya tadata , Miƙewa tayi tana kuka jikinta duk rawa yake ta nufi wajenta da gudu Ta rungume ta tana Kuka.

Ashman ji yayi zuciyarsa ta tsinke, Shi kansa a yanda yaga Condition din AMMI Sai da Yaji kaman Yayi Hawayen She's a second Mother To him Tun mahaifiyarsa nada rai, idanunsa ya buɗe da ƙyar wanda sukai ja ya sauke akansu.

A hankali ya taka Wajen gadon , ya ɗago ta, Cikin Kuka ta Rungume shi tana Shesseƙa.

Sake mannata a jikinsa yayi ga rungume ta sosai

"Ba kuka ya kamata Kiyi ba Ihty, Godiya ya kamata Muyi wa Allah da Ya bar mana ita zuwa wannan Lokacin"

Ɗago kanta tayi idanunta Shareshare da hawaye

"Ahky how...?, Taya bazan yi kuka ba?, look at her...!, Look at her a Haka kuma likitoci cewa suke babu Abinda ke damunta"

Lumshe ido yayi, yanajin Zafi a zuciyarsa

"Look at her feet ,her Arms she has Edema ,A Asibitinka ka dubata You said She has an acute renal failure....Shine ya zama chronic ko...?, Shi yasa ake ɓoye min ko"

Kuka Takeyi sosai ,ya riko hannayenta cikin Sanyi yace

"Ihty trust me da kaina nayi Comfirming An kauda wannan Matsalar a halin yanzu babu abinda ke damunta"

"So why....!, Why Why Is she not responding ?, Why"

Ta fada cikin kuka sosai, ta zube ƙasa tana Cigaba da raira Kukan mai ban tausayi.

Duƙawa yayi yashima ya kamo hannunta,ya riƙe gam cikin nasa.

"Listen ihty,Sickness is not the show for sadness...."

Buɗe ƙofar da akayi ne yasa shi maida dubansa Ga mai shigowa.

Sadeeq ne..........






Ok bye

Nayi Gabas🚶

Comment
And
Share

Bintou ✍🏽
[10/28, 10:30 PM] Bintou abdool: *WUƘA A ZUCIYA*

_BLEEDING HEARTS_

*045*

"So why....!, Why Why Is she not responding ?, Why"

Ta fada cikin kuka sosai, ta zube ƙasa tana Cigaba da raira Kukan mai ban tausayi.

Duƙawa yayi yashima ya kamo hannunta,ya riƙe gam cikin nasa.

"Listen

Please Login or Register in order to submit comment