Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kofa kuma suna shiga aka rufo kofar wanda Hakan yasa su Aeesh jan Burki

Dafe kai Aeesh tayi cikin Kuka Mai Cikeda Tashin Hankali, rarrashinta Reey ta shigayi Itama hankalinta a Mugun tashe

Acan kuwa a wani daki aka shigar daita akayi ,aka fara bata taimakon Gaggawa.

Likitoci Sunfi biyar akanta wasu na Ƙoƙarin Nemo Numfashinta Wasu  na Ƙoƙarin gano Matsalar ta .


Wayar Aeesh Dake hannun Habeeb ne ya hau ruri, Duban Fuskar wayan Yayi yaga new Number ne ,A Hankali ya tako Inda Take ,Ya miƙa mata batareda yayi magana ba.

Reey Ce ta karba ta yi Sliding tasa a kunne

"Hello...!"

"Ba Mai Wayar Wayarta"

Babu musu ta miƙa ma Aeesh Wayar.

"Check your WhatsApp"

Mutumin Ya faɗa yana Datse Kiran.

Mamaki ne ya kama Aeesh ,hannu na rawa ta kunna data Ta hau WhatsApp.

Wasu Hotuna ne Suka fara Shigowa daga Sabuwar Number, Tun kafin hotunan Su ida buɗewa taji gaban ta yayi Mummunar yankewa.

Hannu na rawa ta buɗe hotunan ,
Wara idanu tayi kawai d tana kallon Hotunan, Zufa na keto Mata ta koina, miƙewa ta tashi Daga Inda Reey take gudun kada ta gane Abinda Ke faruwa.


Wayar tace ta sake ruri A karo na biyu.


Hannu na rawa ta daga tana jin zuciyarta kamar zata faso qirji

"Who... are You!"

Ta fada In her cracking Voice

"Saleem Ne "

Ya fada A takaice.

Jitayi gabanta yayi mummunan Faduwa ,Wannan karon ji tayi Ƙafarta na neman gaza Daukarta,Luuuu tayi zata fadi tayi azamar Dafe Bango da hannu daya.

"Meet me in my Office Right Now"

Saleem ya Fada Cikin Gadara da isa.


*Bamalli*

Fitowa yayi yana Gyara zaman Rigar sa, Fuskar nan Cikeda Annaashwa yau dai Allah Ya Nufa ya fito daga hannun Yan sanda bayan Yayi wanka ya kira abokan sa ,har wata yar Karamar parry Aka hada Aka tashe ,taron party na watsewa Ya shiga ya sauya kaya Cikin wasu arnan Ƙananun kaya Ya fito Boys dinsa na take Masa baya.


A ladabce wani daga cikin shi ya buɗe masa kofa ya shiga Suka bar Unguwar cikin hayanayinyar Music, Ayau Kam ko wane mahaluki dake zaune a unguwar yasan an sako Bamalli.

Kai tsaye Gidan su Aeesh suka Barka ,mai gadi ne ya tabbatar masu da ai Suna Asibiti Ummanta babu Lafiya....


*Hospital*

"Yaya Saleem don Allah ka rufa Min Asiri ka Goge hotunan nan Wlhy idn Ammi ta gani Tsine min Zatayi "

Taɓe baki saleem yayi

"Ina ruwa na!, wannan ke ya shafa ,Zan Goge wadannan Hotunan amma bisa Sharaɗi Guda Ɗaya takkk!, In Kuma ba haka ba Zan Turawa Mayaifiyarki sannan ya yaɗa a Social media"

Baki na rawa tafara motsashi zatayi magana saiya katseta da cewa

"Note..!, your Mum is Unconscious Nuna mata hotunan nan bazai Haifar da 'da mai ido ba"

Saurin girgiza kai tayi a ruɗe

"Yeah...!, Eh na Amince kome kace inyi zanyi Indai bai saɓa wa Addinin Musulunci Ba, Na dau maka Alƙawari Wlhy zanyi"


Shiru yadanyi yana kallonta kamar mai son tunano wani abu, Sosai yakejin Kukanta Har cikin ƙokon zuciyasa,Amma yajin ba zai iya Rabuwa da itaba har sai Ya cika muradinsa na Samunta a matsayin Mata, can kuma saiya daga cikkaken girarshi daya yace

"Will You marry Me...?"

Ja da baya tayi Cikin Ruɗani.


"Speak Up you are wasting my time"

Wasu hawayen suka sake zubomata, tunda take bata ta6a ganin tashin Hankali ƙarara ba sai yau, jitake kamar ta sume musanmman idan ta tuna da Halin Da ta baro Umma a ciki.

"Hey..! "

Ya daka mata tsawa.

A firgice ta dawo da dubanta gareshi idanun ta na cigaba da kawo ruwa Bakinta har rawa Yake cikin Kuka sosai ta fara magana hankalin ta a matuƙar tashe

"Yaya Saleem bakada Imani,don Allah ka dubi halin Da Mahaifiyata take ciki Ka Goge Hotunan Kuma ka Barni In tafi Nayi mak..."

"Shut Up, Ni na Miki Kama da Mai Imani?, Kar ki manta a gabanki Ashman Yaci mutunci na Ya Alaƙanta Ni da Kisan mahaifiyarsa,So Kashe Mahaiyarki ba Komai bane a waje na, ba yau na fara kisa ba ,Bazan gama Akan Mahaifiyar ki ba, dole ki yarda ki Aureni in ba haka ba zan Nunawa Mahaifiyar ki wacce take Kan Gadon Jinya dama Saura Kadan Zuciyar ta ta buga ,Jininta yayi mugun Hawa ga paralysis Dinda ta samu Kinga na hutasheku da kashe kuɗin Jinya...."

Ya ƙarashe maganar Cikin isa Yana mata Kallon Sama da Ƙasa.

Matsawa baya Aeesh tayi tana kallonshi jikinta na rawa.


"Menene Ribar ka don Ka Kuntatawa Rayuwata?, me zaka samu idan Ka Aureni "

"Babu Abinda zan samu, Son Ki nake ,Zan nuna miki Kulawa Zan Maidaki sarauniya idan Kin Aureni karkiga Ina Miki barazana Ki ɗauka idan na Aurenki zan Wulaƙantaki ,No Wlhy Ko Kusa Bazan Miki abinda zai Sakiyi kunci ba, Idan Kin amince Zansa a hada auren mu da bikin Aashman Ayi a rana ɗaya"

Runtse idanunta tayi gam tanajin zuciyarta na wani irin zafi kamar ana gasamata ita a Rushi.

Wasu zafaffan hawaye suka silalo ta qasan ruffafun idanunta , Tunowa tayi da Tsananin Soyayyar da sukewa Juna ita da Aareef da kuma Halin da Ammi ke ciki, Babu alamar imani tattare da Saleem Sarai zai iya aikata abinda ya fada Batareda ya damu ba,Ko kaɗan bata shirya Rasa Mahaifiyar ta ba, Itace komai nata,Ita kadai ta rage mata a duniya

"Are you crying? my words are Emotional abi!, ki adana Kukanki ki bari sai na tura ma Tsohuwar ki sannan"

yafada yana watsamata wani mugun kallo.


Bude idanunta tayi akanshi dasukayi jajur sannan ahankali cikin qunar rai tace

"yes, na Amince, Na amince Zan Aureka...!, Zan Aureka don Ceton Rayuwar Ammina,Na amince Zan Aureka Domin na kare Mutuncina na Amince yaya Saleem Na Amince ka Goge komai, na Amince"

Ta ƙarashe magana cikin Muryar kuka mai tsanani

Daga cikakkiyar girarshi daya yayi cikin yimata wani Irin Kallo shi a dole nan Kallon Soyayya yake mata......










Ƙaƙaƙara ƙaƙa

Yau ake yinta.


Ga dai Bamalli ya fito.

Ga Ashman Har yanzu bai bayyana Sirri ba.

Ga kuma Saleem Yana so ya aureta dan Dole , Wai shin Kuna ganin Zaiyi nasara kuwa?🤔

To malam Aareef Shima Fa ba'a barsa a baya ba, Ya dawo daga Strike dinda ya tafi..



Share
And
Comment ☺️

♡ ㅤ   ❍ㅤ     ⎙      ⌲
ˡᶦᵏᵉ  ᶜᵒᵐᵐᵉⁿᵗ   ˢᵃᵛᵉ   ˢʰᵃʳᵉ

Nayi Gabas 🚶🏻‍♀️

Bintou ✍🏼

6th july
[7/18, 9:30 PM] chubby number: 🗡️🫀 *_Wuƙa a zuciya_*🗡️🫀
_(Bleeding Hearts)_


*017*

Daga cikakkiyar girarshi daya yayi cikin yimata wani Irin Kallo shi a dole nan Kallon Soyayya yake mata.
Yace

"Daga Yau Sunana Ba yaya Saleem ba , Habeeby , Understand!"

Izuwa lokacin zuciyar Aeesh ta Raunana matuqa, Ji take kamar ta haɗiye zuciyarta Ta mutu ko zata Huta da Wannan masifar da take Gani.

"Now Call My name"

Ya fada yana jindadin moment din don yasan ba ƙaramin tsorata ta yayi ba.

Yasan babu yadda za'ayi tayi rejecting dinshi,Dole Ayi auren su nan da sati biyu masu zuwa don umma Saude tana bayanshi, Harta Abba Yanzu ya sauko  , yanada masaniya akan Yanda Akayi Umma saude tayi Forcing din Abba har ya Amince da auren.

Lumshe idanu Aeesh tayi tana qoqarin haɗiye abinda ya tsaya mata a maƙoshi.

"Please Yaya Saleem Ka ƙyale Ni najida Abinda Ke Damu na , Please let me Go"

tafada muryarta nadan cracking

Tashi tsaye yayi ya tako ya zagayo gabanta cikin takun isa da qasaita.

"Really? Dama Akwai Abinda Ke damun Ki?, faɗa Min Meke damun ki?, Tell me , it's my responsibility to take care Of all that worries u"

Hadiye wani Abu daya toshemata maqoshi hawaye na Sake Silalowa a fuskarta, Babu Abinda Take hangowa sai Ummanta dake kwance rai a hannun Allah,Jitake kamar tamutu don takaici.

Murmushin gefen baki yayi na mugunta ganin tana Kuka Sosai , Dukda kukan nata na taɓa shi, amma ya dauki alwashin gama Komai Yau ɗin nan Sai ya dasa Mata Tsoron da bazata Taɓa mantawa dashi ba.

"Kina Ɓata Min lokaci!"

Lumshe idanu tayi tana qara bama hawayenta damar gangara.

Shiru tayi atsaye still idanunta lumshe.

"Then Get Out Of my Office" yafada Cikin Yar Tsawa, yana kallon yadda take hawaye.

Jan numfashi tayi ta baki ,saboda kukan da yaci Karfinta ya toshe Mata hanyar numfashi,  sannan ta goge fuskarta da hanki.

"Habe...by free me please..." tafada tana sake lumshe idanunta .

Wani dadi Saleem yaji jin Ta kirashi Habeeby,Amma saiya wani dago yana kallonta,Kaman Baiji ba.

"Ban jiba Speak Loud"

Kuka takeyi Sosai Amma Ko kadan Bai dameshi ba.

"Habeeby Ka bani Izini na tafi"

Murmushi yasaki na gefen baki sannan ya taso yasake zagayowa wajen ta ya sunkuyo saitin Kunnen ta Ya raɗa Mata

"Count Down 10 days Remaining,kin Kusa Shigowa hannuna”

Yafada yana kafeta da idanu fuskarshi fall murmushin mugunta.

Wasu sabbin hawaye suka sake gangaro mata.

Furzar da iska yayi yana lumshe idanu cikin jindadi sannan ya budesu akanta.

Kauda kanta tayi gefe hawaye na diga zuciyarta na wani irin zafi , a lokacin Ji take ƙila da za'a Auna BP dinta zai kai akalla 250/71mmhg saboda Tsabar Firgici .

"Yanzu Ni waye a wajen ki"
Ya tambaye ta

"My Husband to be"

"Your What ....?"

"My Habeeby"

"Now Muje mu na duba Mara Lafiya....Habeebty"

Ya fada Cikin Murmushin nugunta, Yyi gaba ta bi bayanshi.

Duk abinnan Dake Faruwa Ashman Baisan Komai ba, Yana Chan OPD(out patients Department) Yana Consulting Marasa Lafiya, yana Fitowa ya Haɗu da Dr Khaleed Nan yake gaya masa Yaga an shigo da Ammin Aeesh Anyi Emergency da ita.

Sosai Ashman yayi mamakin dalilin da zaisa Akawo mahaifiyar Aeesh Asibitin sa batareda ta sanar dashi ba, ya Lura Cikin kwanakin nan Aeesh ta fara Juya masa Baya, Tun randa tayi Dare a gidansa ta fara Nisanta kanta dashi yayi tunanin Kila Ammi Tayi mata faɗa ne shiyasa take Haka don Tahuce Takaici , Amma yanzu ya fahimci ba haka bane akwai Lauje cikin naɗi.

Fitowar Shi yayi dai dai Da Fitowar Deejah Daga Maleria Unit inda take Aiki, ta Kwala masa Kira Juyowa yayi yana Auna mata kallon Uku saura kobo.

"Baby Emergency Zaka?"

Gyaɗa mata kai yayi batareda Yace komai ba.

"Naji Ance An kwantar da Mumcyn Aeesh,Muje In raka ka, Nima a tsanmin Ladar"

Baice komai ba Yayi gaba Tabishi suka Jero, Sai Faman Zuba masa Surutai takeyi amma Ko Um bai Ce ba bare ya Amsa Mata.

Lokacin da suka Isa har An samo Numfashinta da daɗewa tana Hutawa kafin a gama gwajewajen.

Tun daga nesa ya hango Aeesh zaune akan kujerar dake kofar ward din

Ranshi ne yaqara 6aci sosai, Hakan yasa ya qara tamke fuskar kamar hadari Deejah kuwa harda Chanza Taku tayi adole tana jerawa da Ashman.

Dagowa Aeesh tayi da idanunta dasukayi jajur wanda da alama ba karamin kuka tayi ba, ta kalli Aash daya qaraso wajen, Wani katon abu taji ya tokare mata Ƙirji Tayi saurin Kauda kai tana Ambaton sunan Allah, Ganin shi Tareda Deejah ba ƙaramin tada Mata hankali yayi ba, ta kuma kasa Gane dalilin hakan.

Kasa yimata masifar dayayi niyyar yimata yayi sai kawai ya cigaba da binta da mugun kallo mai cike da haushi da takaici.

Sauke kanta tayi qasa tana share hawayen dasuka sake gangaromata,Sosai Tausayinta ya kamashi.

Juyawa yayi kawai ya shige Ciki yana jin 6acin rai har lokacin ,Sosai Deejah taji daɗin Sharetan da yayi itama bin Bayanshi Take tana Takun Isa.

Har suka shige tana zaune kanta a qasa batace Komai ba ,Haka bata daina jin nauyin Abinda Ya tsaya Mata a ƙahon zuciya ba,yanzu Bama tasu Take ba Amincewa da Salem kadai ya isheta tashin Hankali.

"Babe Muje ki ganta ko hankalin ki zai Kwanta"

Muryar Saleem taji a Tsakar kanta,Da kaman Ta Musa Masa Amma da ta tuna waye saleem sai Ta miƙe tana share Kwalla.

A bakin Gadon Suka Iske ashman tsaye Yana Checking File dinta, Deejah na Gefen shi tana Danna waya.

Ajiye File din Yayi bayan Yayi wasu Yan rubuce Rubucen sa Akai,Sannan ya ɗago ya dubi Deejah Dake ta faman Danna Waya yace

"Ki Gayawa Nurse She should Prepare the Patient Zamu Maidata Amenity...."

"No need Basai An maidata ba ,Zamu chanza Mata asibiti ne"

Muryar Aesh ta dakatar dashi, Ko kadan bai san Sun Shigo ba, Kallonsu ya Shiga yi daga ita har saleem din .

Tsayawa yyi yana dubanta Duba na mamaki.

Takowa Gabansa Saleem yayi ya karɓe File din hannunshi yana Dan duddubawa

"Wane Doctor ne ya Dubanta?"

Ya tambaya Yana Kallon Aeesh da Tasha Mur ,ko kallon inda Ashman yake batayi ba.

"Dr Saif da Dr Aaryaan ne"

"Cikinsu wa yayi Consulting?"

"Doctor Aaryaan "

Ta bashi amsa Muryarta na dan cracking.

Mika mata File din Yayi

"Tho ki Kai mishi, Ki bashi Ya rubuta Refferal Note"

Hannu ta miƙa zata Karba,Taji Aashman ya Rike hannunta, Kwace hannunta tayi Ta karɓe File din ta juya, Saurin Shan gabanta Yayi ,ya mika hannu.

"Ban File Dinnan!"

Rabawa gefenshi tayi zata Wuce ,Ya kara Shan Gabanta, Bai jira wata wata ba ya fizge File din ,Itama kafin ya sauke Hannunsa ta kwace.

Saurin Riƙe Hannunta yayi zuwa Wannan lokacin kam ya Fusata sosai ya buɗe baki a masifance Zaiyi magana ta dakatar dashi

"Karka Sake taɓani!, niba muharramar ka bace"

"Ke MATA TA ce dole In Taɓaki aduk san da naga dama"

"Niba Matarka Bace ka daina Alaƙanta Ni da wannan matsayin...don Allah🙏 ka ceci Rayuwata karkasa Na sake Shiga wata Ukubar ,bayan Wanda Ka riga ta tsunduma Ni a ciki"

Tana gama fadar Haka ta kwace hannunta da Karfi tabi gefensa Ta wuce.

Binta yayi da Kallo har ta fice not believing what he's hearing.

"Kadan Ka gani dude,More Heart breaks Are Coming"

Inji Saleem Yana zura hannayensa Duka Cikin Aljihu sannan Yabi bayanta.

Itadai Deejah kasa cewa komai tayi sai kallonsu kawai datakeyi itama abin yayi mugun Bata mamaki

Ya zama dole na dakatar dasu,Bazan yarda su chanza Mata asibiti ba!

Inji Ashman yana Latsa Wayarsa ,Numbern dr Aaryaan Ya kira, Bugu ɗaya ya daga Ko sallamar sa bai Amsa ba ya shigayi Masa Kashedin Kada ya sake Ya yarda yyi ma Mum din Aeesh Refer Idan Kou yayi gangancin Rubutawa Tho a bakin Aikinshi, Murmushi kawai Dr Aaryaan Yayi yace ai baya Asibitin ma yanzu Ya Riga yayi signOut For today.

Hamdala Ashman Yayi wa Allah sannan Ya umurci Nurses su chanza ma Umma ward,Su kaita Amenity babu Bata lokaci aka Kaita chan.

Duk yanda Aeesh taso ta chanzawa Umma asibiti hakan ya gagara ,Aash ya tsaya kan Komai ya tsare ya kasa bai yarda Koda wasa Tasamu privilege Dinnan ba.

Saleem Kuma Tunda ya lura ta tsorata dashi Sosai , sai ya kuduri  Aniyyar cim ma burinsa Da wannan.

Bayan Wasu Yan gwaje Gwajen da likitoci Suka gudanar akan Umma Sun Gano Jininta ne yayi mugun Hawa wanda hakan Yasata Samu shanyewar ɓarin Jiki haka Kidney dinta Yaso Ya taɓa, odarta Ta dama Ta fara samun Rauni wato(Acute Renal failure).

Sosai Hankalin Aeesh Ya tashi,ta kasa ci ta kasa Sha sai Kuka ,Tun Habeeb na Rarrashinta har Ya koma shima yana Kukan Cikinsu aka rasa mai rarrashin wani .

Reey ce mai kwarin Gwiwan basu baki, a halin yanzu babu abinda take buƙata face ta kasancewa ita kadai Shiyasa ma ta baro ward ɗin ta fito harabar Asibitin tana rike kanta dake sara mata,Dai dai Entrance Door ta tsaya Sakamakon Wani Sarawan Da kanta yayi mata a lokaci guda.

Zamewa tayi wajen ta tsugunna ta rungumo qaffafunta sannan ta cusa kanta a tsakankanin cinyoyinta tana kuka marar sauti.

Tun ɗazu su Bamalli suka Shigo Asibitin suna neman ta Amma basu Ganta ba  Kasancewar Asibitin nada girma sosai,Sun Zagaye Ƙananun Wards inda Ake kwantar da Manya Amma basu ga koda mai kaman ta ba, Fitowar su kenan Daga PNC har sunyi hanyar fita, ɗaya daga cikin tawagar shi ya hango mutum a zaune ta kife kanta Tana kuka,Tabo Bamalli yayi Yana Nuna masa Ita.

"Bahdo Mu duba wancan Chick din Mana Ƙila mu Dace "

Tsaki Bamalli yaja A gajiye Sannan yace

"Tunda nake Ban taɓayin Tafiya mai wahalarwa irin tayau ba, saboda mace ina neman Maida kaina Dan dako na Dole ,.. idan na samo yarinyar Nan mai rabani da ita sai Allah"

Umurni ya basu Su duba yafrinyar in Itace.

Ji tayi an taɓo kafaɗar ta ,Hakan Yasa Ta ɗago a ɗan Tsorace.

"Babaa Wlhy itace "

Inji wanda Ta dafata cikin Dan Daga Murya.

Ɗagowa tayi,take Idanunta sukasarke da na Aareef hakan yasata miƙewa zumbur a wani irin razane.

Dariya suka kwashe da ita tamkar wasu mahaukata Daga shi har Tawagar tasa, da wannan mahaukaciyar dariyar suka tako har Gabanta.

    
Numfashi ta sauke cikin gajiyawa, kusan A tare duk suka Gimtse dariyarsu cikiin tsareta da kallo Bamalli yace

"Rana Bata karya ,Yau gani na fito, Akanki na kwana gidan maza ,Akanki Mahaifina ya gujeni, ya gudu wata Ƙasar ya Barni a kurkuku abinda ban Taɓa zato ba , All that Aside"

Yayi maganar yana Tsareta da sharp eyes dinsa

"Hope Kin fara Shirye Shiryen Auren Mu, As u Promised"

Waro Idanunta tayi, dama already tana Cikeda tsoron Ganinshi A gananta.

"Daurin Auren mu bazai wuce nan da Gobe ba so Get ready"

"What...!"

Ta fada Awkwardly tana Dan Ja da baya, Gyara Tsayuwarsa Yayi ,ya zura hannayensa Cikin Aljihu Tareda Kauda Kai Gefe yana cizan Lips dinsa.

"Bazan Aureka ba"

Yaji Muryarta Cikin Tsakar kansa, Kasa motsawa yayi don mamaki.

"Kuma baka isa ka Aureni ba..!"

Cikin Fushi Bamalli ya daka mata tsawa

"Shut Up....! ,Rufe min bak...''

"How dare You..."

Ta dakatar dashi

"How dare You raise your Fucking voice on me...!"

Ta fada With Courage but deep down she's dying.

"Baka Isa ka sani abinda banyi Niyya ba ,Nice na kawo batun Aure ..!,And nice nace na fasa Idan Da abinda kaga ya dace kayi Kayi "

Ta fada cikin Matsanancin Fushi .

"A'isha Na Rantse sai na Aurenki"

"Wai kai wane irin halitta ne wanda ka shigo cikin Rayuwata ka Takura Min?, dole ne?"

Saurin Runtse idanu tayi ganin ya daga hannu zai kawo mata mari

Shiru taji Hakan yasa ta  bude idanunta ahankali har ta budesu tarr a kanta.

Bamalli ne tsaye Hannunshi maqale a iske wanda ya daga da niyyar kashe Aeesh da mari

Kallon wacce ta riqe hannun a iska tayi wanda shima bamallin yake kallo idanunshi na chanza launi.

Idanunsa Basu ida sauka akanta ba yaji saukar mari bisa Kuncinsa,baiyi aune ba  ya sakejin wani, kafin ya dawo dai-dai an kuma saukemasa wani, tun yana fahimtar adadin marukan har ruɗani ya sashi gaza fahimta.

Gabaki daya Tawagarsa Ja da baya Sukayi Sun a mugun mamakince Gabaki dayansu Sun kasa kawo masa Dauki.

Da iya karfinta take zabga masa mari ta ko ina,Saida Ta tabbata Fuskarsa Ta kumbura ta bar masa Tabonda bazai Manta da ita ba sannan Ta sauke hannunta tana Huci .

"kasan wake daga hannu akan mace da niyyar duka? ,Bunsuru ,Bunsuru shine yake bin Mace ako wane lokaci Batareda ya damu da Yanayin da take Ciki ba, Shidai buƙatarsa saƙonsa sa ya isa inda yake son isarwa, inada masaniya Akan Duk abinda kake aikatawa , mahaifiyarka itace take Goya maka baya akan Komai Shiyasa Baka dauki mace Wani abu ba,ita kanta mahaifiyar taka bata cika mace ba Shiyasa bata san darajar mace ba,Ahto macen Da bata san Mutuncin yar uwanta mace ba, bata damu da Halin da Zata shiga idan Aka ɓata Rayuwar yar uwanta ba,Ita dai burinta danta ya samu Farinciki,bata damu idan wani ya rasa Rayuwansa ta sanadiyyar Samun FarinCikin Danta ba,Irin Wa'ennan Matayen ba Mata bane su ɗin Uwaye ne don Sun haifa ,amma haihuwar Bai Amfanar dasu da Komai ba sai Taɓewa ,wasu Kuma haihuwar shike kaisu jahannama,Wlhy bambali karka ga na mareka Kayi Tunanin Iya nan karfina ya tsaya, Idan ka sake Tunkarar inda Take ko ka sake hanya ta sake haɗa ku Saina Kakkarya Ƙasussuwan ka , Saina yi maka Raunin Da har ka mutu bazaka manta dani Ba,ku Kuma na dawo gareku"

Tayi magana tana kallon zugar sa

"Ku dauke shi ku bar harabar Asibitin nan dashi ,In ba haka ba sai Ranku yayi mummunar faɗi, ku ko kunya bakwaji Gaku katta ƙatta ga lafiya ga komai amma Bushewar zuciya yasa kuna takawa Dan karamin Yaro baya, ire-iren ku da Allah ya horema lafiya kamata yayi a ganku wurin Dako Ko aikin Ƙarfi ,Aikinda zai Rikeka ya rike iyayen ka da ma Kanne baki daya, Amm kun tsaya dan karamin yaro yana baku na kashewa saboda Mutuwar zuciya yana aikenku kaman wani tsarar ku kun biye mai sai Shirme kukeyi a Titi kuna bata mana Yaran Mutane a banza a hofi, Wlhy idan Allah ya tashi Kamashi Duk haɗaku Zaiyi Yaci Ubanku dama ba wani ya Tayashi Kawoku duniyar ba, Now Leave Our Hospital ko in Kira muku Securities”,

Ɗago jajayen Idanunsa da suka kada kamar wuta yayi ya zubasu akan Reey dake ta faman Masifa, Da ƙarfi ya ciji Lips ɗinsa yanajinwani Abu har Cikin Ransa Da zai Aiwatar da abinda zuciyar sa ke raya masa ne da Ayau Dinnan  ta Ziyarci lahira,Tunda   yake mace bata taɓa masa Tsawa ba saigashi yau harda marinshi plus Kashedi Mai Zafi lallai Reey tajawo ma kanta Bala'in da yafi Karfin ta, Kuma tajawa Aeesh dinma tunda ta sanadinta mace ta mareshi.

Huci mai zafi ya Furzar Sannan ya tasa Zugarsa Gaba suka Nufi Parking lot Suka ja motarsu suka fice, har suka fita daga Asitin Bamalli bai daina kallon Reey ba.

Ashman dake tsaye A bayansu Tun farkon wasan Yayi Murmushi kana Ya ƙaraso Gare su

"Ke Bakya tsoron abin magana ko”

Ya fada yana Kallon Reey.

"Nayi hakan Ne don Gujema Abin magana"

Murmushi yayi sosai ya maida Dubansa ga Aeesh da ko kallonsa batayi ba, amma da Alama A tsorace take,kallo ɗaya zakayi mata ka fahimci hakan daga Gareta.

"Waye shi...?"

“sunanshi muzzammil,Amma Ana kiransa Da Bamalli Dan mallawa ne, Shine tantirin nan da Muke baka labarin Saura kadan Yayi mana Fyaɗe ran nan,inba don kiyayewar Uban Giji ba da yanzu muna nan an Lalata mana Rayuwa,Allah ya tsare Mu daga Sharrinsa Amma ban san dalilin da yasa ya dawo ba"

Shiru Ashman Yayi yana Maimaita sunan Bamalli Tabbas Lokacin Da Duniya zasu san yayi Aure yayi, Mahaifinsa Da kaninsa Suna Manyan shaidan Gani da ido Wa'enda zai Iya tunawa dasu Dole ya nemo Bamalli Don Kare mutuncin Aurensa.

"Kinsan gidansu?"

"Eh Gidansu ba Boyayye bane , billionaire City yake, Amma fa basu kwana A gida daga shi har Uwansa ,SUN fi ganewa Kwana a hotels mahaifinsa kuwa baya zaman ƙasar, Shiyasa ya maida Gidan Nasu tamkar Club Ko bariki wajen baje hajar mata sam Bashida Daraja Ko kadan"

Gyaɗa Kai Yayi yana sake duban Aeesh da ta kauda Kai gefe fuskar ta a hade.

"Ihty , What's Wrong k..."

"Please Ka gyale Ni, ka bari inji Da Abinda ke damuna Pls"

Kafeta yayi da Idanu yana reading mood dinta, Tabbas Tana cikin matsanancin Damuwa ,Amma da alama Dmauwar ba ta rashin lafiyar umma kadai bane akwai Wani Wanda Bata sanar dashi ba.

"Meke Damunki"

Lumshe Idanunta Tayi tanajin daci daci Cikin Ranta

"Nace Ka ƙyaleni"

Tsaki Reey taja Cikin Kufula tace

"Kin ma Samu An damu dake?"

"Don Allah duk Ku tashi Ku bar Min nan, I want To be alone"

Aeesh ta katseta Cikin Muryarta mai rauni.

Takowa Ashman Yayi ya zauna Kusa da ita, Saurin Ja da baya Tayi tana Dan Rarraba Idanu

"Yaya Aash kar ka matso Inda nake don Allah ”

”Ihty ki Nutsu ki kwantar da hankalinki ki gaya mn waya Ɓata miki Rai Inyi maganinsa"

"Kaine, Ya Aash kaine ka dami Rayuwata a dalilin ka rayuwata take Neman Kifewa, Da ban sanka ba da Babu Abinda zai dameni a halin Yanzu"

Zubamata ido sukayi Cikin kaduwa dajin kalaman da take faɗa akan Ashman

Cigaba tayi da cewa

"Saninka a rayuwa ta shine babbar Matsala a rayuwa ta, Da nasan Hakan ce zata faru dani Da ban Saki Jiki dakai ba, Da nasan kaine zaka Soka Min WUƘA A ZUCIYA TA da ban Kaunaceka ba tun farko , Gaskiyar Ammi ne da Ta ce duk duniya Babu Mai Iya Kaunar ka Kauna wacce bazata Jawo matsala ba sai Mahaifiya da Yan Uwanka na jini,don Allah Ashman Idan Kanada Zuciya Ka fita a rayuwata ka Barni Inyi Rayuwata Ni kadai Cikin salama don Allah"

Tayi ƙarashe maganar da haɗe hannayenta wuri guda Alamar Roko.

Ji yayi kaman An zare masa Lakka, ba shi ba hatta Reey Sun kadu dajin Kalamanta Bilhakki maganar daga Cikin Zuciyarta yake fitowa duba da yanayin maganarta..

Kamo hannunta Yayi,Lokaci Guda Ya koma abin tausayi

"Please Ihty tell Me me nayi Miki ,Zan karɓi Laifina, Zan Baki haƙuri In ya kama har Dukawa zanyi in roƙe ki gafara,Don Allah ki daina Kuka ki gaya Min me nayi miki?"

"Babu Abinda ka min ,So nake ka bar rayuwata ,kasancewar ka a rayuwa ta shine babban Kalubalen da nake fuskanta...!, ka gane mana Kaine nake Son Ka rabu Dani, Ka rabu dani mana"

Tafada cikin muryarta dabata fita sosai.

"Please... stop Ihty"

Yafada dakyar saboda yadda bugun zuciyarshi ke karuwa  kamar zai fito daga Maɓoyarta.

Qanqameta yayi cikin Fitar hayyaci yana sauke wani wahallalen numfashi.

"Yaya Ammie, nashiga uku...Wayyo Ammi na"

tafada tana sake fashewa da kuka jikinta na rawa sosai

Qanqameta yaqara yi yana sauke wani wahallalen numfashi yana qara cusa kanshi

Please Login or Register in order to submit comment