Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

la'asar, Kanta a duƙe babu abinda take sai hawaye, don sosai wa'azin matar ya ratsa ko ina na Jijiyoyin jikinta.

Sai wajajen shida da rabi aka gama, nan aka shiga raba takeaway da Surveynias .
Taro yayi taro inda aka hada an kammala Komai Cikin Jin dadi daga Bisani aka hada malama da shatara na arziqi, sai godiya take.

Itakuwa Aeesh tana Dawowa Gida  ta sulale dakin Ammi da babu  Kowa taakulle kanta tafada kan gado Sai kuka..

Sosai jikinta yayi Sanyi Jitake ƙaddara ta fado a fasa Auren.

Gobe ne fah Gobe War haka tana nan A matsayin Matar Saleem innalillahi Wainnailaihirraji'un kadai take maimaitawa Idanunta na Zubda ruwa 😭 ,Sosai Takejin Kewar Aareef dinta ko ina yaje oho?, Yasan Zatayi Aure oho?, Ita dai Tunda Ammi ta fara Rashin lafiya rabon Da taji daga Gareshi Ko Wayarsa Ta kira baya Dagawa ,daga Karshe ma kashe wayar yayi Ko ta kira bata samu.

Ashman kuwa da yamma yaje Gidan Su Bamalli dai dai Address din Mahaifiyar sa Da aka bashi, Cikin Rashin Sa'a Ya taras bata nan, Sun Bar kasar Itada 'danta kuma dawowarsu ba nan Kusa ba, Zuwa wannan Lokacin Kuwa ya Sadakar, ya yanke tsammani Akan ta , Sosai ya shiga Damuwa Har hakan Tayi sanadiyar kwantawanshi Zazzaɓi ,cikin  dare mai zafi ya rufeshi baya iya Motsa Koda dan Yatsar sa ne

Washegari

*RANA BATA QARYA*

Yau ranar Asabar ce Mai dinbin Tarihi a Garesu Su Hudu Wacce bazasu taɓa Mantawa dashi ba, Asabar ce wacce zata zama Fara ga wasu Ta zama baka ga wasu , Asabar ce wacce  zata Raba Masoya Kuma ta Kusanta Zuciyoyin da Sukayi nisa Da juna, Tabbas Asabar ce mai Dinbin Tarihi.

Kowa ya hallara a Masallaci Waliyyai da wakilai Duk sun Hallara, Ashman Ne kadai Ake jira ya iso A fara abinda ya hadasu Shine Wakilin Amarya Saboda Abinda ta Biɗa kenan,wannan Shine Alfarmar da ta bida a gurin Saleem.

Sunfi Awa daya suna Jira har Abba yayi Fushi yace shi zai Bayar da auren dakansa, Shigowar Ashman ne Yasashi Dakatawa Kowa ya ganshi Kuma ya San yanda Suke da Aeesh sai ya bashi Tausayi , Ya rame ya zama kaman bashi ba, Ya zamana Bashida Kuzari ko kaɗan.

Nan take aka fara Gudanar da Abinda Ya kawosu, Auren Ashman Aka fara daurawa Wato SUFYAN NASEER SHETTIMA da Amaryarsa KHADEEJAH UMAR Sannan Kuma SALEEM NASEER SHETTIMA da AMARYARSA AISHA MUHAMMAD GIATH Wato Hassan ko wacce Akan sadaki Dubu Dari.


Daurin Auren da ya samu Halattar Manya manyan Mutane daga Bangarori da dama na kasar nan dama Kasashen Waje, Saboda Abba ba Boyayye bane yayi suna a wurare da dama, Uwa Uba kuma Maragayi Alhaji Hassan Mai jama'a Dole Mutane Su halacci daurin Auren tilon Ɗiyar sa wacce daga ita babu wata.


Dafe kai Ashman yayi yana jin Muryoyin maroka Na dadama Ta ko wane kusurwa Suna jaddada daurin Auren .

Shikenan fa!, Shikenan Aeesh ta zama ta Saleem ,dakansa Ya bada Auren matarsa Ga kaninsa.

A fili yake ambaton Kalmar Innalillahi Wainnailaihirraji'un Hasbunallahu wa Ni'imal wakeel.


Duk Dauriyan shi ,Saida ya karaya ya kasa Jurewa Saida Idanunsa Suka kawo Ruwa, ya kasa Riƙe hawayensa Gabaki daya ya manta Cikin taron Jama'a yake.

Ji yayi an dafe kafadarsa ɗagowa yayi ya dubeshi, Dr Aaryaan ne

"Subhanallah Ango,haba Ango me nake Gani haka"

Sai a lokacin ya lura ashe hawaye yake, Saurin Goge Hawayen yayi yana washe baki da ka ganshi zaka san Yaƙe yake bai kai zuci ba, Girgiza kai Dr Aaryaan yayi Cikeda tausayin dan'uwan nasa yace

"Ya Kamata Ka tashi Mu tafi Bakin Mu sun Iso Suna jiran Mu a waje"

Miƙewa Yayi a Sanyaye yana Gyara zaman Hularsa, Abba dake Tsaye chan Gefensa ya Gizgiza Kai Cikeda Tausayin Sa, a yau duk rashin imaninsa sai da yaji babu daɗi *TABBAS ABBA YASAN DA AUREN AEESH AKAN AASH A GABANSA AKA DAURA AUREN YANA KUMA DA HUJJAR DA IDAN YA NUNA DOLE A YARDA, DOMIN KUWA AKWAI CCTV DAKE KEWAYE DA GIDAN, YA SIYE SECURITIES DIN GIDAN YA KARBO MEMORY DIN FOOTAGE DIN GIDAN, A HALIN YANZU FOOTAGE DIN NA HANNUNSA* .


Fitowa Sukayi Jiri na diban sa ya dubi Dr Aaryaan da Rinannun Idanunshi da Suka Kankance sbd zafin Zazzaɓi yace

"Kira Min Mahfouz Ghost Ku rakani Gidan Su Ihty"

Gyada masa Kai Yayi ya shige ciki don Nemo Mahfouz Ghost (Jarumin littafin Maƙaryaci 👻)

Jingina yayi da Motarsa Ya lumshe Idanu Jiri na dibansa Yanajin zuciyarsa na masa Wani Irin Suya.

Jin alamun Tsayuwar mutum a gabanshi yasashi ware idanunsa, Ya diresu akansa.

Saleem Ne ,Fuskar nan A washe kaman Gonar auduga Sanye yake Cikin Manyan kaya Farare tasss Anci Babbar Riga ya karyo hulan Nan ta hagu Sai zuba ƙamshi yakeyi.

Kallon kallo ake tsakanin juna kowanne najin zafin Dan uwansa , Ashman Ji yayi kaman Ya maƙuroshi Yayinda Ran Saleem Take fess Kaman Wanda akayiwa albishir da Gidan Aljanna.

Kankance Idanu Ashman yayi saboda Reflecting Dinda Rana Yayi masa,hasken Farar shaddar Saleem da na rana Sun Gauraye waje guda Suna kokarin kashe masa Ido ,Ga idon Ba lafiya ta cika ba tun Bayan Accident din da ya samu A kwanakin baya.

Kallon shi takeyi a kaikaice

"Saleem Kayi Nasara"

yafada cikin low but dangerous voice.

Gyara zaman Hularshi saleem yana cigaba da taunar Dabinon Bakinshi

"I know"

Shima ya furta cikin Sigar Raɗa Murmushin Mugunta Fall a Fuskar sa.

"But This is not the End Of the Story! Saleem"

Ashman ya fada cikin dakewa .

Kwayar dabino Dake hannunshi ya Mikawa Ashman Yana Cigaba da sakin Murmushi

“congratulations Angon Nana Khadijatul Kubrah"

Shima Murmushin Gefen Baki yayi kaman Yanda yaga yanayi yace

"Nagode Angon Nana A'isah Humayrah"

Yar Dariya Saleem yayi

"Karka bata Min Sunan Mata Kaje ka Koyo"Sh" kafin ka Ambaci Sunanta"

Isowar Mahfouz da Aaryaan ne ya Sa ya kasa Bashi Amsa, yashaYi mai gori akan "Sh" dinda bashida Shi amma bai taɓa damuwa ba bai san Me yasa ba, Gorin Yau yayi mai zafi Sosai.

Shiga Motar yayi Ghost yajasu Suka bar harabar masallaci.

Kai tsaye Gidan Su Aeesh suka Nufa.......🤫











GenGenGen 💃

An fa daura yau Akwai shagali 💃💃🤺

Nayi Gabas 🚶🏻‍♀️

Iya yawan comments

Iya yawan Page


🧗

Bintou ✍🏼

20th July🤩
[7/22, 3:24 PM] Bintou: 🫀🗡️ *_WUƘA A ZUCIYA_*🫀🗡️

_(Bleeding Hearts)_

*022*

Wayar Aeesh Dake hannun Reey ce ta hau Ruri

Hannu tasa Zatayi Sliding dau niyyar kasheta amma ganin mai kiran yasata dakatawa

kallon wayar ta cigaba dayi tana kallon Aeesh Da Makeover Keta Faman Kawata Mata fuska,  shawarar ta shigayi ta daga ne koko

ganin zata tsinke yasata saurin dagawa ta kara a kunne.

"Hello...!, Ihty"

Inji Ashman daga dayan Bangaren.

"Assalamu Alaikum, Yaya Ango!, Har an daura ne?"

Inji Reey.

"Wa'alaikisssalam Juwairiyyah ina mutuniyar?"

Dan shiru Reey tayi, ta ɗan Juyo ta kalli Aeesh Da Ake ma Kwalliya saikuma tace

"oh ana Mata Makeup"

"Kai mata wayar"

Da ok Ta Amsa masa Sannan Ta Nufi Inda ake mata kwalliyar Amarya tasha Kyau kaman ba ita ba, saidai kallo ɗaya zaka mata ka fahimci Damuwar da take tattare da ita .

Mika mata wayar tayi tana cewa ga Yaya Aash Zakuyi magana, Ji tayi Gabanta ya fadi ,Shikenan an Daura ta fada a Zuciyarta.

Hannu na Rawa Ta karɓi wayar, Hakan Yasa mai Makeup din Dakatawa,taja baya

"Hello Yayana"

"Amarya ta"

Guntun Dariya ta saki tace

"Amaryar Yaya Saleem dai!"

Ji yayi kaman da Gangar Tayi don yaji haushi, Aikam Yaji,Shuru yayi na wasu Lokuta yana Shaƙar takaici kafin Daga bisani Yace

''Hope Nine na farko da na fara miki Albishir da an daura?!"

Murmushi mai sauti tayi sannan a sanyaye Amsa da Eh

“tho Amaryar Saleem ki fito Ina Kofar Gidan ku”

Zaro Ido tayi

"Yanzu haka kana kofan Gida?"

Shuru yayi hakan yasa tace

"Saura kadan A karasa Min Makeup "

Ok Kawai yace Sannnan Ya Datse wayar,Ana Gama mata Makeup din tayi kyau kamar sabon halitta, kowa ya gani sai yace MashaAllah saboda zallar Haɗuwa.

Gaskiya ne Masu iya magana Sunce duk munin mutum ko kyan shi,Na ranar bikinshi daban ne .

idan kaga Amaryar lokacin idan ba farin sani kayi mata ba bazakayi saurin gane ta ba

Ta chanza tayi wani fresh sai glowing take Sai kuma yar Ƙaramar Rama da yayi

taci kwalliyarta acikin Coffee wedding Mai kyan gaske ,Kanta yasha Ha'dadden daurin Gyale tayi Wani irin Breathtaking kyau.

Suma Close Friend Sunyi Collaborating Cikin Milk Gown Reey Besty Kuwa Golden Color ne nata Komai iri daya Da Aeesh Amma Aeesh tafita kyau nesa ba kusa ba🤩.

Milk gyale Reey ta Yafa Suka Ratsa Mutanen dake Gidan Suka Silale  .

Suna Fita suka ci karo da Yaya SADEEQ yana Shirin Shigowa.

"A'ah Ina zaku?"

Ya tambaye su yana Kare musu kallo.

Kallon Aeesh Reey tayi ,Aeesh Zatayi magana Reey ta amshe

"Bako Mukayi zan Kaita su gaisa"

"Tayi bako Ko Kunyi bako?"

" Dear ai duk daya"

Harara ya Galla mata yace

“aike bakida Farin jinin Ganin Bako,Nine Nan Bakonki ako da Yaushe"

Dariya Duk sukayi

Kallon Zallar Kyau da sukayi yyi ya kasa Haƙura saida ya fada

“kanwata Kinyi kyau Kinfi ReeReey na kyau"

"Na Gode Yayana Kaima Kayi kyau kaman sabon Ango"

tafada tana lumshe ido fuskarta dauke da murmushi.

Taɓe baki Reey tayi

"Ina Kyau Anan, Ya wani Karya Hula sai kace an Sumar da Akuya”

Dariya Sosai Aeesh tayi don Har ga Allah tayi Mugun bata Dariya.

Shima Yar dariya yayi yace

"Eh din ke Kuma matar Sumammen Akuya ba"

Inji SADEEQ cikin sigar tsokana

Dagowa tayi tana kallonshi tareda zabga mashi harara still fuskarta dauke da Murmushi.

Kallonta ya sakeyi yace

"A haka zaku je wurin bakon?, nifa AM Jealous?"

Kallon Juna duk Sukayi Sai Kuma suka Maida Dubansu Gareshi, a tare duk suka daga Mshi kai sai kuma suka kwashe da dariya duk a lokaci Guda.

Narkar da Fuska yayi

"Muje tare Inyi Guardin ku, duk wanda Ya kalleku in Tsokale Masa Idanu"

Waro ido Reeey Tayi tana kamo Hannun Aeesh

"Haba Malam Kayi Haƙuri mana babu wanda zai kallemu yanzunnan Zamu dawo"

Bin bayansu Yayi yana fadin

"Aje dani Ko In fasa Auren Wata"

Burki sukaja Reey ta juyo cikin Pleading Face dinta tace

"Dear Pls Ka Tafi, Tun ɗazu suke jiran Mu, Please kaji, Yanzun Nan Zamu dawo !”

Tana Gama Fadar haka taja hannun Aeesh sukayi gaba,Bin bayansu yayi da Kallo yana Admiring Zallar haduwar da Sukayi.

A Nan gaban Gidan dake facing nasu Suka hango Motar sa a Parke ,Saurin Karasawa Sukayi.

Ashman ya Fito daga back seat har yanzu Idanunsa Basu dawo daidai ba, Sun daɗayin jazir Fuskar Sa har wani Jajajja yayi,Kallo ɗaya zakayi masa ka hango Tsananin raman da yayi,da ka ganshi kaga Mai zazzaɓi.

Kallonta yake yi kaman Yau ya fara Ganinta, Shagala yayi da Kallonta,ya ma manta da Mutane a wurin.

Jin hasken idanunshi na Neman narkar daita yasata saurin dagowa tana gyara Tsayuwarta

Daidai lokacin da Reey tayi Gyaran Murya Ganin Kaman Bai ma san yana kallon ta ba

Shima sai a sannan ya janye idanunshi ya maidasu ya lumshe cikin takaicin kamashi da Reey tayi yana kallonta.

"Reey Kije Mun Ari Amaryar ku Yanzunnan Zamu Dawo"

Ya fada yana Buɗe wa Aeesh Kofar baya , tsayawa tayi ta kasa Shiga tana Kallon Reey Gabanta na Faduwa.

Murmushi Reey tayi mata, hakan Yasa ta Shiga a hankali Ashman Na gyara mata Gown dinta dake jan Kasa.

Tsayawa Reey Tayi Tana Kallonsu tana Jin wani iri Cikin Ranta.

Bata san Inda zai kai ta ba,Amma Tasan Yayan tane kuma mai Sonta Bazai Iya cutar da ita Ba, Tanada Tabbacin zasu dawo nan bada Jimawa kamar yanda yace.

Shiru motar ta dauka babu mai magana sai can Ghost dake Mazaunin Driver yayi Gyaran Murya

"Amarya In ba Hello Akwai Hi”

Murmushin Ƙarfin Hali Ashman yayi Yace

"Ina Ruwan ka da Ita?"

Guntun Murmushi Aaryaan Dake zaune kusa da Ghost yayi

“Babu Ruwan Mu da ita kuwa ,Kayi Ka Sallami Matar Mutane Mu tafi kasan Baƙi na jiran Mu ko?”

Dariya Ashmanyayi yana shafa gemunshi

"Ghost Ja motar Mu tafi"

"Inje ina?, ina zaka kai Amaryar Mutane?"

Inji ghost yana dan Juyowa

"Gara da kace Amaryar Mutane ba mutum Daya ba Abege Ja Mota muje"

"Muje ina?"

"Mu fara zuwa Gidan ka mu taho da Morh da Marwan "

Murmushin Gefen Baki Mahfouz (Ghost) yayi , ya Tada motar sannan yabata wuta suka fita daga unguwar.

Tafiya sukeyi Mahfouz da Aaryaan na Hira a tsakanin su, amma tsakanin Aashman da Aeesh babu mai cewa uffan kuma babu mai niyyar maganar, kowanne da tunanin daya addabi Rayuwarsa, A yauce Ranar da ya kamata ta kasance ta FarinCiki a Garesu Sai gashi yana neman Zama na bakin ciki a Garesu .

Ahaka suka isa gidan su Ghost din, ko gama daidaita parking din biyiba,Ashman Ya fara addabansu Da suyi Sauri , Babu Shiri Mahfouz ya 6alle murfin motar yafita, Aaryaan ya mara masa Baya.

Binsu da kallo Ashman yayi har suka Ida shigewa , Sannan ya bude Kofar Ya dawo mazaunin Driver, da ƙarfi ya Figi motar ya fice daga harabar Gidan.

Driving yake tunannuka kala kala na yawo akanshi.

Haryanzu yakasa yarda cewa an Daura Auren Saleem akan Nasa.

Dubanshi Aeesh tayi a mamakince tace

"Yaya Ina zamu je?"

Shiru yayi na wasu Seconds kafin Yace

"Siyar dake zanyi"

Ya fada In His low Voice, Murmushi tayi ta maida Dubanta kan hanya gabanta na cigaba Da faduwa.

Kai tsaye ya bar unguwar dasu bai Tsaya ko ina ba sai a malali, sabon Gidan da ya Gina ,Babu wanda yasan da Gidan, Gidane Babban Gaske Ga Kyau da Tsari kaman Ba a Nigeria ba.

Horn yayi Mai gadi ya buɗe bude ya shiga da motar.

Tun cikin motar tasaki baki tana kallon gidan.

Tunda take bata ta6a ganin qayattacen Gida irin wannan ba, wai ahakan tana waje bata shiga ba..

A hankali ya fito ya Zagayo ya Buɗe mata ,kafarta zuro A hankali tafito.

"MashAllah!' Tayi exclaiming ganin zallar haduwa da Gidan yayi.

Ga Flowers ta koina, Kayatattun Abubuwa sai Daukan Ido suke.

"MashAllah"

Ta furta a hankali tana Sake Karema Wajen Kallo

Kallonta yyi cikin Murmushi yace

"Gidan Yyi miki Kuwa?"

Gyada masa Kai tayi ta lunshe Ido tana cigaba da shaƙar daddaɗar Ƙamshin flowers Dake tasowa ta koina Na gidan .

_yanayi mai dadi_

Sanye yake cikin wata dakkakiyar farar shadda babbar Riga da dan ciki.

Anyima babbar rigar aiki da zare Coffee Coloy, ya kashe tsadaddar Coffee din hula ,kafarsa sanye yake da takalmi bakar half cover Agogon Hannunshi Silver Sai daukan ido yake.

A hankali ya kamo Soft hand dinta,Hakan yasasu jin wani baqon al'amari ajikinsu wanda hakan yasasu saurin dagowa tare suna kallon juna.

Saurin janye idanunsu sukayi  gabanta na faduwa.

_yanzu fa Ni matar aure ce_

Qoqarin zame hannunta take yaqara matseta

"Mu shiga Ciki"

Ya fada yana takawa ,dole ta biyo shi, Cikeda tsoro.

Ta yarda dashi Tasan Babu Abinda Zaiyi mata Amma tana tsoro idan Salem yaji labari tasan Bazata ji da dadi Ba.

Cikeda karfin Hali yake komai Sosai yakejin jiki, zazzaɓin dake Jikinshi na neman Kwantar dashi, har wani Jiri Jiri yake gani, Jikinshi na rawa.

Jin yanda hannunsa ke rawa yasata ɗago Ta dubeshi daidai lokacin da suka Shigo katon parlorn tace

"Yaya hannunka na rawa bakada Lafiya ne?"

Sake damƙe hannunta yayi Gam, ya rintse Idanunsa Da ƙarfi yasa Dayan hannun ya dafe kansa dake barazanar Rabewa Biyu.

Take Hankalinta yayi mummunan tashi,Da ƙarfi ta fige hannunta ta Rikeshi Ganin yana Shirin Kaiwa kasa Tana Ambaton Sunansa Hankalin ta na Dada kaiwa kololuwa wurin Tashi.

Kasa Rikeshi tayi ,ya faɗi ƙasa, kuka ta saki Tana Girgiza shi Hankalinta a tashe

A hankali ya bude Red eyes dinsa Da Sukayi masa Nauyi Tareda sake kankancewa ya dubeta a raunane, ya buɗe baki Zaiyi magana amma ya kasa Saboda nauyin da bakin nasa yayi masa,Cikin Kankanin Lokaci jiki ya birkice.

Hankalin Aeesh yayi mugun tashi , banda kuka babu Abinda Takeyi Kallon Yanda idanun nasa Sukayi ja tayi cikin Matsanancin kuka tace

"Yaya Idanunka na Ruwa!, ka daina sa magani Gashi bakada Lafiya jikinka da zafi Ka tashi Mu tafi Asibiti”

Girgiza mata kai yayi ya nuna Mata wata Yar box dake Side din Tv, Ta Gane Abinda yake nufi don Ta Riga Tasan  Box din ,Irin shine a gidansa da tasani.

Da gudu ta Nufi Wurin ta buɗe Ta dauko Ampoule Din PCM Biyu Da Syringe, Sannan Ta haɗa Da Diclo Shima Ampoule daya ganin Nature din Zazzaɓin Yasata hada da Gentamycin ta zuƙo 160mg, Plaster da Cannula ta dauko Tayi masa Cannulating Sannan Tayi masa Alluran Ta jijiya.

Cikeda tausaya wa ta ɗago hannunsa Ta sagala a kafadarta ta mikar dashi Izuwa kan Kujera Ganin yana Zufa yasata Kunna masa AC, Cikin Kankanin Lokaci zufar ta fara Komawa ,yana nan Kwance sai kaiwa da kawowa take gaba daya tayi wujiga wujiga ta koma kamar ba Amarya ba, Makeup Dinnan Har ya Fara Gogewa,Daurin Gele kuwa Tuni akayi Gabas dashi, sai Kallonta yake yi yana Sake Godewa Allah da ya Sakko masa Ciwon Nan a daidai Wannan Lokacin,Ba don Ciwon Ba da yanzu ta KKufuce masa kifucewa Ta har Abada, a yau yayi niyyar sanar da ita komai, hakan yasa Yayi Typing Ɗinshi a takarda yayi Mata Parkaging a Wata Rantsassen Envelope, yanaso ya Bata Takardar ne Cikin kyakkyawar Yanayi, ta yanda idan Ta karanta zata Tuna Dashi ta kuma yi  masa Uzurin rashin Gaya mata da yayi Akan lokaci.

A fakaice ya dauko Wayarsa cikin Karfin hali ,ya D'auketa Hoto bata sani ba, Sannan Lalubo Numbern Saleem ya tura masa Tareda Text message kamar haka

*_use this one Hold body Before I make her Mine_*

Yana Gama turawa ya cire Sim card dinsa ,Ya jefar Sannan Ya lumshe Idanunsa a nan take Barci yayi awon Gaba dashi. .......✍🏼

*Saleem*

Message na Shigowa ya buɗe,Ya gani take Jikinshi ya hau rawa Zufa yaita qetomasa ta ko ina Daga inda Yake zaune. Gabansa banda bugun uku uku babu abunda yake.

Sudai duk Abokansa babu wanda ya lura kowa sai Harkar Gabanshi yake masu Tsokanarsa nayi.

Da ƙarfi ya ciji Lower lip dinsa a bayyane yace *_Kayi Son Ranka Nima Zanyi Nawa_*

Gabaki daya Juyowa Abokan sa Sukayi suka zuba masa Ido

"Ango Lafiya?"

Cewar babban AbokinsA Dr Hisham yana kai zangareriyar Cinyar kaza bakinsa.

Murmushi kawai yayi ya gyara zamansa batareda ya ce komai ba, Contact dinsa ya Fara Scrolling har yakai kan Na *Miss Quark* Sunan Da yayi Saving Numbern Maryam.....✍🏼

Koda Reey ta koma yaya SADEEQ na nan Yana jiransu a bakin Gate, Tambayan ta yayi Ina Aeesh Ce masa tayi Angonta ya fita da Ita Yanzun Nan zasu dawo, Fada ya hau yi mata akan Meyasa Zata bari ya tafi da ita itakadai?,Dukda Tace Angonta ne amma Baiji dadin yanda ta bari ya fita da Ita,ita daya Tun ba'a kai masa Ita ba,Bayaso Ƙanwarsa ta Shiga Gidanta yana Mata kallon wani iri, Yaso sai an kai masa Ita sannan Zai ganta, haƙuri Reey tayi ta bashi tunda take dashi bata taɓa Ganinshi cikin Fushi ba sai yau ,Abinka da Fushin mai hakuri,Itama Tun tana bashi Haƙuri har tayi fushin barin shi tayi anan Ta shige Ciki.

Wasa Wasa

Hour daya babu Amarya, Hour Biyu Babu Ita , Har Hour UKU, Zuwa yanzu Kuwa Hankulan Jama'u Sun fara tashi ,Sosai Aka Shiga nemanta.

Suna Cikin nemanta Kiran Saleem Ya shigo wayar Maryam, Batada Numbern shi hakan Yasa bata dauka ba, Saida Ya katse aka Kuma kira sannan ta dauka da sallama a bakinta , Ko amsa Sallamar Baiyi ba yace

"Ina ne hall dinda Amaryar Yaya Suka Kama?”

Kasa Amsa masa tayi saima Mugun mamakin da ta Shiga yi  " _tho ina Saleem ya samu Numbern ta?_

Kafin ta ida Tunani Taji Muryarsa Cikin Yar Tsawa yana faɗin

"Tambayanki nake!"

Guntun tsaki taja
"Shine zaka mn tsawa?,...A multi Purpose Even CENTER Zasuyi"

"Ke wacece da baza'a miki tsawa ba?, Tarkato min All Friend dinku Kuzo Multi purpose din , Muma nan zamuyi namu Event din"

"Ban gane ba, Already Su Deejah sun riga sun kama wajen"

"Sai a musu refunding na 50% of their money, and Please Ina Nan Zuwa Ki fito waje zan baki wani Aiki Pls"

"What....!, did you just say please?"

Kitt ya katse Wayar ,dariya ta Kwashe dashi, Ta ma manta ta gabata gaya Mishi ba'aga Amaryarsa ba.

Yana katse wayar ya lalubo Number Rabeel,take ya lulluɓeshi da dadin baki yace ASHMAN Bashida lafiya gashi yayi Organizing Event dinda ya kamata yaje, Tunda suna Kama yayi masa Alfarma ya zama Ango A madadin Ashman Mana ,Da Farko Yaki amincewa Amma daga Bisani da Saleem ya dameshi sai ya amince.

Cikin Kankanin Lokaci aka baza labarin Za'ayi Event, Daɗi kaman Ya kashe Deejah Dama Bataji dadin Rashin Event dinba, Iyayenta ne suka Shirya yin Event Wanda Za'ayi koda babu Ango, Sai gashi kaman Daga sama taji Labarin Ango yace ya amince.

Sake Kiran Maryam Saleem Yayi bayan ya daidaita komai yace ta fito yana Jiranta a kofar gidansu Aeesh, Saida ta bata masa lokaci kafin Ta fito a yangance.

Zuwa wannan Lokacin kuwa Ya cika yayi Famm kiris yake jira ya fashe.

Yana Tsaye Jikin Motarsa fuskar nan a Tamke tamau kaman An aiko masa Da sakon Mutuwa,Zuwa Tayi ta tsaya a gabansa tana Taunar cewing Gum.

Kallo ɗaya yayi mata ya kauda kai,Ashe uniform Muni yake Sata,a Kayan Gida Mugun Kyau Gareta

Sanye take cikin Wata dakakkiyar Atamfa mai Brown da Milk Colour, Tayi daurin ture kaga Tsiya, Ta Yafa yar ƙaramar Mayafin ta akanta .

daidaita Muryansa yayi Sannan Ya fara magana a hankali Ba kaman Yanda yayi niyya ba, a yanda Ta bashi Haushi yaso da tazo ya rufeta da Masifar da ya tara a ransa, Amma Ganinta da yayi yasa shi Manta Masifar da ya kwaso.

"Ehhm...."

Jin Muryarsa yayi nauyi yasata ɗagowa ta dubeshi, haka yasashi Jan bakinshi yayi shiru, kara daidaita natsuwan sa yayi

"Ehhm Maryam!, Wata Alfarma nake Son Ki mn Please....."

Waro Ido Tayi ta dubeshi a Mamakince tace

"Alfarma kuma?, From Me?, A lowly co-worker ɗinka...."

"Please"

Taji ya kamo hannunta da Sauri

Kallon sa tayi ,ta kuma dubi hannunta dake Cikin nashi, saurin Sakin hannun nata yayi ya dan ja baya kadan

"Mr Saleem what did u want"

"I want you to be my fake Bride at the Reception"

Zaro Ido Tayi

"I don't get u!"

Lumshe Ido Yayi

"Yeah I want you to be my Bride, fake bride"

Taja da baya tana Masa Kallon baka da hankali , a fusace tacs

" me ka daukeni ne?, baiwar ka?, After Overloading me with work at the hospital Nan ma kazo ka Ƙarasani ne?, Shikenan Ni bani da tym din kaina Sai naka?, Excuse Me!"

Juyawa Tayi a Fusace zata bar Gurin, yayi saurin taran gabanta

"I'll Pay"

Tsaki taja ta raba gefensa zata wuce, ya kamo hannunta a karo na biyu.

"500k!"

Chak taja ta tsaya Amma bata juyo ba, and still Bai saki hannunta Ba.

"Tho free my hand"

Sakin hannun nata yayi yana kallon Fuskar ta.

Fuskar ta daure ta juyo ta galla Masa Harara

"And Don't touch me again"

Ta fada a masifance.

Gyada mata kai yayi Alamar yaji, Zuciyarsa Kaman Zatayi bindiga, Ko a haka Ashman ya kyaleshi ya wulaƙantashi Kuma dole sai ya dau fansa akanta, yasan Yayi dauke Aeesh ne don Yaji haushi ya saketa Amma bazai Saketa ba Zaide koya mata hankalin Da bazata taɓa mantawa dashi ba.

"Make it 1M then I'll agree "

"Yeah na Amince"

"Amma da shara'di bazaka Sake taɓani ba, ka tuna fake Bride kace,And niba muharramar ka bace we'll maintain Social distance ka yarda"

Nan ma gyada mata kai yayi zuciyarsa a jagule.

"Pay before service, kana da account number Dina!, In Fara ganin Alert Tukunna!"

Take ya tura mata dubu ɗari bakwai da cewar idan an gama komai zai cika mata

Daga nan ya gaya mata Shirye Shirye da tsare Tsaren da yayi ,Bata takbayeshi ina Aeesh ba Kuma shima bai gaya mata ba, Kasancewar Kowanne na Jida kansa bayaso ya tabo zancen da bai shafeshi ba.

Aeesh ce kadai ta sanar mawa ,ita din ma don ta kasance  Babban Kawar amarya ne, kuma ta kasa Kwantar da Hankalinta.

Har gida ya aiko da Driver yakaita aka Tsarata cikin Rantsassen Ido ta kece raini,Ta fito cikin Dogon Riga Dark Blue.

Cikin kankanin Lokaci aka baza Ko'ina cewa anga amarya dama Angone yasa Akaita Wajen kwalliya, karfe  biyar daidai aka fara Tafiya dasu Cikin Jigajigan motoci.

Motar Saleem Kuwa kai tsaye Gidan Da aka kai Maryam Ya nufa, Tunda ta fito yake Kallonta Har Driver ya bude mata kofa ta zauna kusadashi.

Wani irin Ni'imtaccn ƙamshi ne ya ziyarceshi, Hakan ya sashi Lumshe ido yana ambaton Sunan Allah, a fakaice yake Kallonta Dukda fuskarta rufe yake cikin Wata hula hakan bai sashi gane Yanayinta ba, kamar dai kullum Fuskar ta a murtuƙe take.

So yake yaga fuskar Amma baya son jama kansa Raini.

A haka suka isa wurin Reception, inda Ashraff ya maye Gurbin Ashman A matsayin Angon Khadijah, ita kuma Maryam Ta maye Gurbin Aeesh.

Har aka fara Gudanar da Bikin bata buɗe fuskarta ba ,Haka shima bai matsa akan haka ba, kaman yanda ta buƙata tun farko baiyi Yunkurin Taɓata ba hasalima Sun bada tazara a wajen zama, kamar yanda take a bangaren Su Rabeel sai Akayi Tunanin May be tasu tsarin Kenan, Ita kanta Deejah bata gane ba Angon ta bane, saidai tana Mamakin yanda yake acting so Strange Duk Yabi ya kosa a gama ya tafi, Ƙarara yake nuna mata takurawa

Please Login or Register in order to submit comment