Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

wuto, inda mamake tsaye ya tsaya yana Sosa kai , ta taɓe baki

"Mene na sosa kai?,nasan abinda zaka ce, ka tai da kayan mun baka kyauta, naka da ka ɓata da Giya kuma Kaje Zaidu Zai wanko maka"

Wai yau shi ake Bama kyautar kaya, abinda Bai taba tunani ba ko a mafarki.

So yake yayi Magana As in Yayi mata godiya amma ya kasa,amma bai ma san Daga ina zai fara ba.

Fita yayi yabi bayanta, har ta shige Motarta tana shirin tada Motar.

Fuskar nan a tamke, kana ganinta kasan ranta a ɓace yake kuma bazata bar kota kwana ba.

Tsayawa yayi yana kallonta don tunda yasanta be taɓa ganin Ranta a ɓace haka ba she's always expressionless, irin face dinta da ya dade yana Burin Gani Kenan,gashi yau ya gani at the wrong moment.

Qarasowa Yayi daidai Sanda take tada Motar, ta zuge Glass Ɗin motar ta dubeshi kallo daya Ta masa Ta kauda kai gefe

"Open The Gate please "

Ta fada tana Kafeshi da ido.

Kutt.. Yafada yana Waro idanu

"Mr Man Please Be fast"

Tayi Maganar tana kauda dubanta daga Gareshi, still Fuskar nan kaman hadari.

Jiki a saɓule ya Nufi Gate harda ɗan waigowa ko zaiji tace ya dawo badashi take ba, Amma sai shirin Tada motar take, Haka nan ya buɗe Gate din

Taja Motar ,tayi Gaba Kaɗan, ta tsaya Daidai inda yake tsaye ,yana Jira yaji tace ya shigo yaji Shuru, ta buɗe Handbag dinta ta fiddo naira ɗari sannan Ta zuge Glass Ɗin Motarta yayi ƙasa sosai ta jefa mishi

"Gashi Ka hau Napep nasan Zai kaika gida "

Motarta ta kunna tayi reverse, wani uban horn ya danna kamar ana yaƙi sannan ta fice a tsiyace .

Tsayawa yayi yana kallon kudin cikin rashin sanin abinyi, wai wane tsautsayima ya kawoshi gidan ma tun farko?, wannan shi ake kira rabon ayi, ya haɗu da wacce ya daɗe yana Nema ga Kuma Tarbar da tayi masa

(Ni kou nace ga qoshi ga kwanan yunwa🤣)

Ya dade sosai tsaye a bakin Gate din kamar mai jiran tasake dawowa har saida yaji kaffafunshi sunfara sanyi sannan yajuya afusace ya fice, ya kullo gate din ta waje feeling so sad, mad in anger, jiyake kamar yadora hannu aka yaita ihu, haushin Kansa ya kamashi

Tafe yake yana huci ga idanunshi dasukayi jajir, jiyake kamar yaita kuka don takaici, kai amma ko a haka Maryam Ta kyale shi tagama dashi .

Wai shi zata kalla ta Bama Naira dari ya hau adaidaita, kaman Mabaraci?, Bayan tasa ya buɗe mata Gate a tunaninshi Taji fadar Mama zata Koma Gida tare dashi.

Kwafa yayi yana tare mai Napep ya dau drop ya kaishi har Gida

Ko parking din kirki bai bari yayi ba ya sauko daga napep din sannan Ya wuce, already kafin ya iso yayima Mai gadi text yana nan zaune a kofar gida yana Jiran Isowarsa, ya Shige gida ,sannan Mai Gadi ya sallami mai Napep.

Saleem Jiyake kamar ya hadiyi zuciya kawai, he can't believe yau duk zumudin da ya tashi da shi na Son Sake Ganin Maryam Irin Abinda zaibiyo baya kenan.

Direct part dinshi yashige yana wani ƙwala ma inna Yathai kira da qarfi.

Allah Sarki baiwar Allah yadda kasan ita tamashi laifin 😏

Kayan Jikinsa ya cire, ya watsa kan Sofa ya rage dagashi sai boxer.

Tsaki yaja yafara safa da marwa dakin cikin tsananin 6acin rai, jiyake kamar yaita ihu Ko Za'a taru a ji yanda Yake ji a zuciyarta _Yana Mutuwar Sonta tana Wulaƙantashi ji yake kaman yayi hauka_ .

Inna Yathai ya sake Ƙwala ma kira yana huci.

Shigowa tayi da sallama Hannunta janye da na Ayyan , yana Ganinshi Ya ruga ya Rungumeshi Da Murnar shi,Amma ko kallon shi bai yi ba, ya dubi inna Yathai Yana Huci yayi mata nuni da Kayan da ya cire

"Kwashi kayan nan Ki trash Bin"

Inna Yathai ta dubi kayan, ta dubeshi yanda taga Fuskar tasa ne yasa tayi Shuru ta kwashi kayan Takaima Ado Driver.

Tsaki yaja yana shigewa ɗakinsa, Ayyan ya biyo bayansa yana Tambayanshi ina ya kwana Jiya?, Jiya Shida Granny(sunn da yake kiran Inna Yathai) su kadai suka kwana, baice masa komai ba sai Faman huci yake.

Ataqaice ranar saleem kasa runtsawa yayi don baqinciki, Ayau duk wanda ya raɓeshi saida Yaji a jikinsa.

Har dare bai daina takaicin Abinda Maryam ta masa ba, Gani yake kaman a mafarki the whole Saleem Shi aka Bama Naira ɗari ya hau Mota, bayan Ya buɗe Gate Idan ya tuna Sai yaji kaman yayta ihu, dama da nasa Ra'ayin ne ya bude mata cikin Soyayya irin soyayyar da zata Gani Ta kuma gane me take nufi bazai damu ba, Amma he serve as a Gate man, and she payed him ₦100

Yanda yaga rana haka yaga dare azaune ya kwana don bakinciki.






Yau duk wanda yaga Deejah zai san tana cikin Farin Ciki mara misaltawa, Abbanta ma haka ma'aikatan Gidan ma sun shaida hakan, tun shekaran Jiya ake ta faman Shiryawa sai kace wacce in taje Bazata dawo ba.

sai wajajen 12:30am, yazo ya dauketa Bayan Abbanta Ya gama masa Tijara baidamu ba don yasan zai rama akan yarsa.


Gidan Su ya Kaita, saida sukayi bankwana dasu Abba Sannan Ya nufi wajen Goggo nasiha tayi masa kaman yanda ta saba a koda yaushe ,shiyasa Ya fiso in yazo gidan yaje sashenta Itada inna Yathai Su kadai Ke iya karantar Sa, sosai da inna Yathai tayimusu addu'o'in tsari sannan suka baro gidan cikin motar da Abba yasa Driver yajasu.

Sai a ranar Salem yasan Ashman Ya dawo, kuma Tafiya yayi tare da Aeesh, Bai damu ba don a halin yanzu ba tasu yake ba.

lokacin dasuka isa airport din saura mintuna Ashirin jirginsu yatashi

nan suka shiga yin duk wani tantancewar daya kamata suyi kafin lokacin tashin jirgin.


cikin takaitaccen lokaci suka gama jirgin Su ya ɗaga, Jirgin su na ɗagawa wayar Aeesh ya Shigo.


Murmushi yayi ya ɗauka, yana dauka ta fashe masa da kuka cikin rarrashi yake cewa

"Haba Ihty wa ya saki Kuka?"

Cikin kuka tace

"Ba kai bane?"

Ya zaro ido

"Ni...?, Me nayi?"


"Inada ciki"


Wani irin ajiyan zuciya ya saki, ya dubi Deejah, yaga hankalin ta nakan waya, amma da alama Kunnenta gaba daya suna Suna kan wayan da yakeyi, sai yasa Handsfree cikin salon ƙunsa mata yace

"Banjiki ba Me kikace?"

Cikin Kuka tace

"Ahky AM pregnant...."

Dumm.. gaban Deejah yafadi jin muryar Aeesh daabindaTa fada ta waya wanda hakan yasata dago idanunta.

Caraff suka hada idanu dashi wanda dama tunda yasa wayar a Handsfree ya kafeta da ido .

Saurin janye idanunta tayi gabanta beating sosai don ba qaramin kashemata idanu idanunshi yayi ba.

Ashman ya gyara zama yace

"har yanzu nakasa fahimtar inda zancenki ya dosa Kina nufin kicemun ke Ihty ke dauke da ciki! Cikin ma Kuma na haihuwa to ta Yaya hakan zata kasance?, Who's Responsible?"

Yayi maganar cikin barkwanci, yana Danne dariyar sa.

Take kukan Aeesh ya tsananta Muryarta na rawa sosai tace

"Kaji Tsoron Allah Ahky, wallahi wallahi Wallahi Kai kaɗai na sani ,kaine Uban Cikin nan, Don Allah karka juya min baya kar ka ƙaryata Ni ,ban taɓa aikata wani abu da wani namiji ba bayan kai wlhy kaine Uban Cikin dake jikina"

Jin yanda take kuka Da iya Ƙarfin ta yasa ta bashi tausayi, Ya saussauta murya speaking clamly yace

"I am sorry wify mun kusa zama Parents ko"

Ya faɗa yana sakin Murmushi mai sauti, yana Satan kallon Deejah.

Kuka Aeesh ta saki

"Ni wlhy Bazan yadda ba, kawai a ganni da ciki ba Aure!, Tho ince wa ya min?"

Murmushi yayi, yana kallon yanda jirginsu ke ɗagawa a hankali Izuwa sararin samaniya sannan ya sauke ajiyan Zuciya a hankali ya ambaci sunanta

"Ihty....!"

"Na'am"

Ta amsa cikin shesseƙa

"Ki daina kallon Cikin nan a matsayin Shege Kinji ko?"

"Taya Bazan Kalleshi a Shege ba?, Ba da aure aka sameshi ba fa, kallon Shege za'a ma ɗan"

Yayi Murmushi

"Tho Meyasa Baki so a Alaƙanta shi da Shege?"

"Saboda Shege bashida Uba"

Ya ciji lower lips dinshi, Murya ƙasa ƙasa yace

"Tho kada kiji kunya duk wanda ya Tambaye Ki Cikin waye ko kinyi Aurene kice Eh, Nine Mijin Kuma Nine Uban cikin Kinji ko"

Shuru tayi tana Share Hawaye, chan ta ambaci Sunansa cikin raunin Murya

"Ahky...."


"Na'am Ihty...."

Cikin rawar murya tace

"Bazaka guje Ni Ba?"


"Nayi miki Alƙawari"

Ya fada murya bata fita sosai

Tayi shuru tana sauke ajiyan zuciya,a hankali yakejin Shessheƙan Kukanta a kunnensa,Hawayen daya cika masa Idanu ya sakko a hankali yayi saurin kaudashi da bayan hannun shi.


" Aeesha,If you were not in my life, I would have seriously missed an opportunity of falling in love with an angel, ihty I'll always love you Until my heart stops beating"
Ya fada Emotionally

Izuwa yanzu saura kadan Deejah tayi bindiga.

hawaye taji mai zafi yana tahowa daga kirjita amma naki ta barshi ya karaso idona saboda karya gani ya fahimci Raunin ta Sai ta Kife kai da gwiwa tayi mai isarta Yana kallon window yana satar Kallonta baice komai ba tasha kukanta ta gaji dakanta don ta kwanta.



Aeesh

Ta ƙi yarda suje ayi gwajin Ciki,, Dukda Reey Na zargin Akwai Cikin Haka ta barta aka Cigaba da zama.

Sai ta rage Ciye ciye gabanta ganin Ta sa mata ido...

Amma yanzu wani sabon Abinda ke damunta jin Soyayyar Areef take yi kaman numfashi wanda idan Babu shi bazata iya Rayuwa ba.

Dakanta Takaima Aareef Tsarabar da ta siyo masa daga CANADA haɗida takalman da ta siyo a Boutique dinda suka hadu da Maryam , Murnar da ya nuna yasa ta fahimci Kyauta nada Muhimmanci a soyayyarsu, Sai ya zamana a halin yanzu bata kakkautawa wajenyi masa Kyauta, a duk sanda tayi masa kyauta Kuwa soyayyarw Ranar Ta musamman ce.


Sai yanzu ya samu damar tuƙa Motar da ta bashi, don Koda Suka tafi bata Bashi asalin Motar ba Mukullin da takardun kawai ta bashi.


Soyayyar da take nuna Masa a yanzu ta zarce nada, tafiyar Ashman Yasa ta samu Sake Idan tana free sai ya dauketa a motarsu suyita zagaya gari.


Wannan Soyayyar da zumuɗin duk basu wuce Na sati ɗaya ba ,ya Daina duk wani rawar kafa a kanta, Ya zamana a koda yaushe itake kiranshi idan Bata kirashi ba batajin daɗi.

Yau tun safe take ta kiranshi yaki dauka har gida tabishi ta kwankwasa, abokansa na ganin Itace suka shirya masa Rashin Lafiyar ƙarya ya lulluɓa a bargo Da ta shigo Sukace ya daɗe a kwance Wani abu ne ya tsiro masa a ciki Ake Son Ayi masa aiki wanda akalla kuɗin aikin zaikai 100k yanda yayi Acting Kaman Da gaske, tayi kuka sosai kaman Ranta zai fita tausayinsa takeji sosai Yanada uba Amma kaman bashidashi, Yana da uwa amma shike kula da ita, wannan Itace main Abinda yasa take tausaya masa matuƙa, takejin zata iya sadaukar da komai da ta mallaka akansa.


Yanzu haka tunani take idan ta tafi ta barshi a wannan Halin wa zai biya Hospital Bill ɗinsa?, Wa zai biya kudin aikin da za'a masa? ,Bata taɓa Tambayan Abba Kudi ba, Amma saboda lafiyan Aareef ta roƙi ya bata Kudi zatayi Shirye Shiryen grad dinda Suke Shirin yi, dubu ɗari biyu ya tura Mata, ta basu dubu dari da Hamsin, ta rike hamsin cikin Hawaye tace idan Wani buƙata ya taso su kirata. _Awwn Rich kid_ 😂


Tana Fita ya ware, A washeGarin Ranar suka Shirya anyi masa aikin ta kuma yarda, After each minute sai ta kira taji ya Jikinshi? bata je asibitin Ba don shirye shiryen final Exams Dinsu ya kawo kai.


Nan Ma FarinCikin sati guda ciff akayi, ya koma ɗaukan wayanta Wannan Karon Abokinsa Bashh ta kira yace Ai an sace Wayar Aareef nan ma Latest Samsung Ɗin ta da Ahky ya siya mata Ita ta damƙa masa, All she want is happiness Gani take kaman Daga gare shi ne kawai take samun Farin Ciki and she can do anything To make him happy If he can share with her.

Yanzu ya kasance every week take biyansa Kuɗin Farinciki and ko kwana Uku ba'a yi kudin yake Expire ,Da zarar ya karar da kudaden zai fara Nuna mata Shariya,idan ta nuna Masa Bata ji dadi ba sai yace shi ya riga yace baya Sonta, itace ta nace mai ,Shi ko yanzu Tace a rabu A shirye yake, cikin dake Jikinta yasa ta zama kaman zautacciya akan Son Areef.

Tun abin naba Reey haushi tana mata Mata fada har ta fara bata tausayi take bata Shawara , Har yanzu Aeesh taƙi yarda Taƙi abincewa Reey tasan Ciki ne da ita, dukda ita a ranta Tasan ciki ne, Amma it's about Time Ciki ai ba'a Ɓoye shi ko an ɓoyeshi da kansa zai fito.


Jiya Aeesh tayi Sub din farinciki a tsakanin ta da Areef, Amma tuni Ya gama da Kudin tun da safe hankalinta yake a tashe sai kiran Layinshi take, shi kuma yaƙi ɗauka gabaki ɗaya Ta koma wani kalar tausayi.


Reey na Zaune kan Gadonta tana Karatu don Next week suke shirin Fara zana jarabawar su ta ƙarshe ,Aeesh na zaune Gadon sarah dake Reey da sarah ne a Down bunk, Aeesh da Jessica kuma a Sama.

Sai Faman Kira take Amma No Reply chan Saiga Message ya Shigo, duban Reey tayi ta gefen Ido sannan Ta maida Hankalinta kan wayarta

Reey tace

"Besty ki dauko Littafi Muyi karatu"

Batareda Aeesh ta kalleta ba tace

"Karatun me zanyi?, Bade gashi kinayi ba?"

Jin Muryarta a chunkushe yasa Reey ta dubeta na wani lokaci Sannan tayi Murmushi tace

"Ya naga kaman Ranki a ɓace?, Ko nayi miki wani laifi ne?"

Sai yanzu Aeesh ta ɗago ta dubeta Ranta a ɓace tace

"Meyasa Zaki tambaye Ni bayan Kinsan Abinda Kikayi?"

Reey ta ajiye Littafin hannunta, ta gyara Zama Tace

"Me ya faru"
Aeesh tace

"Meyasa zaki gayawa Sadauki Zan iya rabuwa dashi?, Yanzu gashi Kin Jawo min matsalar da bansan yanda zan maganceshi ba"

Reey tayi Murmushi tace


"Me hakan ya jawo?"


Aeesh tace "meyasa kike tambaya bayan ba iya maganceshi zakiyi ba ma"

Ta fada tana sake haɗe rai.

"Besty....." Reey ta Kirata da Wata murya a sanyaye.

Aeesh ta ɗago Batareda Ta yi magana ba.

"Kinsan idan matsala ta taso nidake ne muke Taruwa mu maganance matsalar , don Allah ki fada min wace matsala ce ta taso, Mu hadu mu maganance ta dukda Kin daura damuwan yin hakan akaina..."

Aeesh ta Katseta da fadin

"A'a ke kika daurawa kanki bani na sa miki ba, kinje kin fada mashi zan iya rabuwa dashi gashi duk kinsa ya tada Hankalinsa"

Reey tayi Murmushi mai sauti Cikeda tausayin Aeesh _Wai kinje kinsa ya Tada hankslinsa_

"Yanzu wannan shine matsalar"


"Ai kinsan Hakan me zai haifar, yanzu kinja ya fara Tunanin Ko Wani ne yake neman Ƙwace masa Ni"


Reeey ta sakeyin Murmushi a karo na ba adadi Lallai Da gaske Aeesh batada hankali da gaske Take son ta haukace Akan soyayyar namiji, dubanta tayi tace

"Da gangar na Gayama Areef haka, Saboda ya damu"

Aeesh t tace

"Meyasa kike son ya damu?"

Reey tace

"Saboda ya soki ya kuma mutunta ki"

Aeesh tace

"Waye ya gaya miki, Sadauki baya sona?, Wa ya gaya miki baya Ganin Mutuncina ko ke idanuwanki basu ganin So ne?"

Reey tayi Smirking da Gaskiyan Masu Masu addu'a da suke cewa _Ya Allah marasa lafiya na gida da na Asibiti Allah ka basu lafiya_ don Da gaske ga mara lafiyan Gida wanda nata rashin Lafiyan ya zarce na wasu yan asibitin.


"Ni ba cewa nayi Areef baya sonki ba, So nake ya dinga ganinki da daraja, Besty abinda nake so shine ki ringa ɓoyewa Areef abinda Kikeji a zuciyarki Dangane dashi, saboda ya rinƙa takatsantsan dake Ya kula dake kaman Ƙwai"

Aeesh ta gyara Zama fuskar ta abar tausayi tace

"Waye ya gaya Miki Areef baya takatsantsan dani?, Waye ya gaya miki baya Kuladani kaman Ƙwai?"

"Idan da Areef yana takatsantsan dake da bazai Bari kina hawaye a kansa ba, idan Areef na takatsantsan dake bazai rinƙa Kawo rabuwa a tsakanin ku ba, duk namijin da kikaji yana cewa Ko yanzu kika shirya barina Ni a shirye nake bai daukeki a bakin komai ba, don Allah Besty ki iya soyayya"

"Tho Reey Koya min Soyayya, yanda zan so Areef"

Reey ta Taɓe baki

"Ni kaina ban iya soyayya ba, Amma zan baki shawara, kiso Areef dari bisa dari kinyi daidai, Amma ki ɓoye hamsin Saboda Areef ya gane cewa Kofa baya tare dake zaki iya rayuwa da wani, ba dole sai dashi ba, hanyar da zaki bi ki nuna masa hakan Kuwa shine ki sama masa Kishiya, Kishiyan kuwa shine cikin dake Jikin ki da kuma Mahaifinshi"

Dummm aeesh Taji gabanta ya fadi, ta ɗago ta dubeta cikeda mamaki, Amma sai ta kauda kai ta cigaba da fadin

"Domin Idan Areef ya gane kina da ciki Kuma ubansa na raye, dukda bana sunna bane zaigane Kinada wani zaɓin bashi ba Don Allah Besty ki dauki shawara ta koda sau daya ne"

Aeesh ta Turo baki
"Besty Nifa bani da Wani da wani ciki"















Muma munsan bakida komai Reey zata mana sharri😒😒😒



Nayi Gabas 🚶

9th nov
Bintou ✍🏽
[11/10, 11:43 AM] Bintou abdool: *WUƘA A ZUCIYA*
_(BLEEDING HEARTS)_



*_A Gaskiya bazan boye muku ba inajin dadin comments 😘da goyon bayan da kuke bani ALLAH ya barmu tare_*



WANNAN PAGE DIN MALLAKIN KU NE GABAKI ƊAYA MEMBERS NA BLEEDING HEARTS GROUP

INA SONKU SOSAI😘😘😘




*050*

"Besty Nifa bani da Wani da wani ciki"

Reey tayi Murmushi

"Nasan Bakida ciki, But Am just Imagining, nide Dan Allah let me Beg You For The last Time, Please Ki ɗauki shawara ta"

Aeesh ta taɓe baki

"Wannan Shawarar taki Gurguwa ce, idan na bita zan iya Rasa Sadaukina"

Kasa cewa Komai Reey tayi for some seconds cikeda Jin haushin Kalamanta jitayi kamar ta zubamata rankwashi akai don takaici , amma ta danne takaicinta tace

"Idan kin yarda Aareef yana sonki Sosai tho Bazaki Rasashi ba, Idan Kuma sonda yake miki bai taka kara ya karya ba zaki iya Rasashi takan Abinda bai kai wannan ba ma, don Allah Besty ki dauki shawara ta, ba gurguwar shawara nake baki ba"

Ta karshe maganar cikin Rage murya

Juyar dakai tayi ,Ita bata masan inda Kalaman Reey Suka nufa ba ,bare ta fahimci me take nufi, ta taɓe baki tace

"Mu ajiye shawarar ki a gefe, Ki kawo min Mafita a cikin wannan Bala'in da kika sani a ciki"..

Reey tace

"Zan Kawo miki Mafita Daga yanzu zuwa kafin magriba"

Aeesh ta zaro ido

"How...?"

"Ba kince Yana Zuwa Ƙwallon Yamma a filin Kargi ba?"

"Eh zakije ki same Shi ne?"

"Eh..."

Cikin Zumuɗi Aeesh tace

"Don Allah ko zamuje tare ne?"

Reey ta harareta

"Bakida hankali"

Kamar yadda Reey Ta dau Alƙawari, Yamma nayi Ta nufi filin Kwallon sun fito Kenan da zugar su, sai gardama Sukayi da Alama dai Team Dinsu Aareef akaci don Yanda taga idanunshi sunyi jawur kaman Ya hadiyi garwashi.

Batareda wani shakka ba tasha Gabansu, Areef da Abokan sa suka bita da kallo

"Areef Kake ko wa?"

Dagowa yayi ya kalleta itama shi take kallo ranta a ɓace

"Haka ake soyayya?, Ka dauka yiwa Mace barazana shine So?, don na gaya maka zata iya rabuwa dakai Shine kaƙi daukan Wayanta a ganinka wannan Shine hanyar da zaka huce takaicinka a kanta?, this's Not how men Do...!, Idan kai namiji ƙaramin Abu Bazai sa soyayyarka ta samu tangarda Ba,hakan Ya nuna min kai ba namiji bane, kuma baka kai matsayin da za'a Kiraki mace ba, saboda mace tayi maka gata ta kawo ka duniya, Amma ka kasayiwa mace Gata ta baka Zuciyarta Ka Raunanata"

A fusace Abokinshi baSh ne ya katse ta

"waitt...!Waiku Mata meyasa bakuda aji ne, ayita koranku Amma kuyita naci, ke yanzu bakiji kunyaba? Kin wani wanko kafa kinzo gun namiji har filin Kwallo?? Da anyi magana kuce self defense Ina defense din anan, wai anan Ƙwarki kikazo nemawa Fada, yace baya Sonta Ta nace Sai shi ,duk wulaƙancin da take gani Ita ta siya da kudin ta Kema Da alama Ragowan wulaƙancin Kika zo ki kwasa, Assistant Girlfriend mtswww"

Yaja Tsaki

Tunda ya fara Magana take Binshi da kallo, yana magana Yana Wani tutturo baki kaman Mace, taji zafin kalamanshi sosai amma sai ta danne tace

"Mr Man ya kamata koda sau ɗaya ne ka duba Madubi a rayuwar ka, ko zakagane Alfarmar da Allah yayi maka ya rufa maka Asiri kake neman Tona wa kanka"

Hadiye wani Abu daya toshemata maƙoshi tayi ,ta dubi Aareef da yayi nisa gurin kallonta ,Batareda ta lura da irin kallon da Yake mata ba Tace

"Ba rokonka nazoyi ba Akan Aeesh, nazo ne nayi maka kashedi ,idan ka fasa rabuwa da ita kai ba dan halal bane,Don Allah wannan karon Karka fasa Raba Rayuwar ka da ta Aeesh, ka raba Rayuwar Ta da duniyar ne gabaki daya anan ne zan gane ka cika tantiri, ShashaSha Kawai, Ni wlhy Banga abin so a wannann abin ba, Me akeyi da namiji mara aikin yi fisabililllah, Don Girman Allah idan ka cika mai zuciya wannan karon Karka ƙi Ɗaukan wayarta, Ka rabu da ita ne Gaba ɗaya"

Aareef dayayi mutuwar tsaye beko motsi yakasa cewa komai don he never Know she was this Stubborn , Bash yaja hannunshi yace su tafi don Kunnuwansa bazai iya juran Jin irin wadannan Munanan Kalaman daga bakinta ba.

Cigaba tayi da kumfar baki ita kaɗai har ta Koma Hostel,tun bayan tafiyar ta Aeesh ta zauna Ta zabga uban Tagumi tana jiran Dawowanta, Shigowanta a fusace yasata ɗago ta dubeta.

"Besty ya Kukayi dashi"

Reey na huci ta faɗa Gadonta tana haki, ganin yanda Reey ta shigo yasa Hankalin Aeesh ya Tashi tasan ba lafiya ba, ita kanta Tsoron Fusatar Reey take ta tabbata basu kwashe Lafiya da Aareef ba, Hankalinta a tashi ta dau wayarta, ta danna Layin Aareef Bugu ɗaya ya Dauka, tasa a Handsfree

"Hello..."

Daga chan ɓangaren Aareef cikin Fushi yake cewa

"Me Zaki Gaya Min?, Ba kin Turo kawarki ta ci Min Mutunci ba? tana Min barazana akan Cewa zaki iya rabuwa dani?,tho ki rabu dani mana?, Idan kin rabu dani sai me?, Kin daukeni mara zuciya wanda baisan Ciwon kaina bane?, Ko daukanki kowa irin ki ne?, Kada ki sake kiran Wayata kinji....."

Reey ta Karɓe wayar

"Kai din Banza, Kai har ka Isa ka haɗa kanka da ita da har kake cewa ko ta dauka kowa ma irinta ne?, idan Kaine autan maza a duniyan Nan yau Aeesh ta rabu dakai ka gani idan Bazata rayu ba,ka ɗauka kai ne Rayuwarta shiyasa kake Juyata yanda kaga dama!, Walhy koda kai ko babu kai Aeesh zata cigaba da Rayuwa cikin kwanciyar hankali, kaine asararre da kayi Asara har Aeesh ta suɓuce Maka, har ka mutu bazaka Taba samun Macen da zatayi maka kwatankwacin soyayyar da ta nuna maka ba, kuma insh...."

Aeesh bazata iya juren Irin wannan cin mutuncin da Reey take ma Aareef ba, da sauri ta karɓe wayar ta kashe Ranta ɓace tace

"Juwairiyyah, dama Da kikace zaki gyara daɗa ɓatawa kikayi?, Meyasa zaki rinƙa haka ne?, Wannan wane irin abu ne da zaki rinƙa min zagon ƙasa?, Laifin me Aareef yayi miki da kike son Raba Alaƙar mu?, Meyasa kullum bakya komai sai ƙoƙarin Rabani da Sadauki na?, Kullum fafutukan Rabamu kike,gashi yanzu kinyi Nasara Kinsa ya furta kalmar da kike so Yace yarabu dani"

Itama Reey ranta ɓace tace

"Ba fafutukan Rabaku nake ba"

Katseta Reey tayi

"Karya kike, ƙarya ne , inba burinki kenan ba meyasa zaki min haka?, Okay so kike Ki raba Ni dashi ke ki zaga Kije ya soki ko mene?"

Reeey Ta waro ido in shock

"Wannan Wane irin magana Kikeyi Aisha?"

"Dalla Malama Rufe min baki, ƙarya kike Munafuka Yar zagon Ƙasa, Tho Burinki Bazai cika Ba sai naje da kaina na gyaro Alaƙar dake tsakanin Mu, Aareef bazai taba sonki ba"

Sai ta Sungumi Hijabi ta dau wayarta ta fice tana Surutai kaman taɓabbiya.

Kai tsaye school Mosque ta nufa, a daidai lokacin da ake Kiraye kirayen Sallar Magrib ta shiga tayi sallah, sannan Tayi Nafila tasha Kukanta sosai Kaman Ranta zai fita, ji take Dama Reey bata Kasance cikin Rayuwar ta ba, ji take da ana Goge mutum a rayuwa, da ta goge Reey a Rayuwarta gaba ɗaya.

Tayi ta trying Number Shi Yana Ringing Amma Yaƙi dauka, nan take ta yanke shawarar Zuwa gidansa Don ji take idan har bai Yafe mata ba a yau din nan Zata iya rasa Rayuwar ta, Ji take yafiyan sa a gareta shine Rayuwarta, damuwan ta Yanda Reey ta gasa masa magana karya kwana da ɓacin rai

Tana Idarwa ta kama hanyar Gidansa, bisa shawarar Zuciyar ta, ta iske babu kowa a gidan hakan yasa tayi tazauna a Waje har Lokacin da aka fara kiraye kirayen sallah Isha'i ,Dan kwalin ta ta shimfida tayi sallah sannan ta zauna tana tazbihi, tana zaune ta hango tahowansu shida baSh tayi saurin miƙewa idanunta cikeda

Please Login or Register in order to submit comment