Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

idan Kajisu shuru to babu Nafeesah Da Zee a gidan.

Har dare Aeesh taƙi ci taƙi sha sai Kuka, tayi Ta Gwada kiran Ashman Amma baya dauka daga Karshe sai ya koma Rejecting, Da ta dameshi ma Dauka yayi ya hauta Masifa tare da cewa idan Ta sake kiranshi Sai Ranta Yayi mummunan Ɓaci sai Yayi mata Abinda Bazata taɓa mantawa dashi ba.

Tsoro ,mamaki da Fargaba Duk Suka shigeta tunda take Ashman bai taɓa yi mata Magana cikin Irin wannan Yanayin ba, a iya Kalaman sa ta Fahimci zai iya aikata Alwashin sa akanta idan bata Kiyayeshi ba, Zata iya cewa wannnan Ranar Shine Rana Mafi Muni a rayuwar ta ,bazata Taɓa manta wannan Ranar ba sai a yanzu ta gaskata Ammi Da tace Batada Kowa A duniyan nan Sai ita Da habeeb su kadai Suka rage mata a rayuwa,da Ace Wani ne ya gaya mata Ashman Zai iya cewa ya rabu da ita kenan Na har abada da nan take za Ta ƙaryata shi.

Shima Ashman A ranar Baccin Bakin Ciki yayi Cikeda tarin Tausayi da Tsanar AEESH, Domin Kuwa Abba ya taɓo masa Tabon da ya jima da sakayawa dukda bai Warke Ba ,Abba ya tuna masa Da mummunar Tabon Da yayi wa Aeesh a idanunsa Wanda bazai taɓa mantawa ba,Wannan Karon sosai yakejin ya tsaneta dama Duk wanda Yayi kokarin Tunkararsa a wannan Lokacin!.


Saleem Ma Tattara kayanshi yayi ya bar masa Gida Ya koma babban Gida domin Kuwa Haduwan su a wannan Ranar saida Ya kusa Saɓa masa kamanni, haka kawai daga dawowansa masallaci sukaci karo ya Kamashi da duka Duk inda ya samu kai hannu yake ,Cikin kankanin Lokaci ya haɗa masa Targaɗe Ta ko ina da kyar Securities suka kwaceshi a hannunsa.

Koda ya koma ciki kulle kansa yayi a ciki a lokacin kiran Aeesh yayita Shigowa, cikin wannan Yanayin ya Sauke mata Nata buhun Masifar Tareda kwakkwarar Kashedi akan ta fita daga Rayuwarsa Kamar yanda Shima ya fita a nata Rayuwar kenan Har Abada✍️


Yana nan a dakin Har dare Bai buɗe Kofa Ba,Duk Bugun da Deejah tayi tayi Bai buɗe ba, hakan yasa Hankalinta ya tashi matuƙa ta Fita ta aika mai gadi Ya kira masu Ɓalla kofa, nan Take aka kirasu aka ɓalla Kofar.


Ga mamakinsu ya jiƙe sharkaf da zufa dukda sanyin AC dake aiki a ɗakin, gashi idanunsa sun kaɗa sunyi jazur har ana iya hango yanda jijiyoyin kansa sukai ruɗu-ruɗu, Ko ina Na dakin Yayi kaca kaca Da Alama shine ya Tarwatsa su.

Cikeda tsoro ta zo gareshi ta na Rirriƙeshi da faɗin

"Baby me ke damun ka? ,zaka Illata kank....."

Bata ida Fadar abinda ke bakinta ba taji saukar Wani Gigitaccen Mari Wanda yasata ja baya babu Shiri,Idanunta saida suka juya saboda gigicewa

Kafin ta dawo Hayyacinta ya nufota da faɗin

"Me tayi maka ka Kashe ta?, Me Umma na Tayi maka Kasa Aka kashe ta?”

Jada Baya ta Farayi a matuƙar Tsorace,Binta yakeyi Yana Maimaita "Meyasa Ka Kashe ta?"


Sosai Zuciya ya fara rawa,ya jiƙe sharkaf da zufa, gashi idanunsa sun kaɗa sunyi jazur kamar Wuta har ana iya hango yanda jijiyoyin kansa sukai ruɗu-ruɗu, hannayensa Da Jijiyoyi ke a mimmike ya Dunƙule.

      
"baby mike damunka?”
Deejah ta faɗa da tsagwaron Tashin Hankali cikin karfin hali, tana Rufe baki taji saukan naushi a Kumatunta wanda Yayi sanadiyyar Zubowar biyu daga Cikin Haƙoranta na gefe.


"Saina Aikaka inda Ka aikasu, kasheka zanyi, Sai ka bisu....”

wani mugun tsalle Deejah ta yi ,ta kauce masa, amma dukda haka saida ya Sake kai mata wani Naushin a fuska, ihu ta fasa ta fara neman hanyar Fita don Tsira da Rayuwarta.



Deejah Bata san hawaba bata san saukaba kawai ya hauta da duka, tun tana ƙoƙarin kare kanta hatna gaza dan Ba karamin Ƙarfi ya Tara mata ba, gashi kuma bayan Security dinda Ya Buɗe Kofar babu mai karɓarta, shima anan Ya samu nasa Rabon Aka Targaɗe Masa hannu.

       
Tun Deejah na fahimtar abinda ke faruwa harta sume, amma Ashman Baya Cikin Hayyacinsa idanunsa ya rufe bare ya fahimci bata numfashi.


Wani irin Gurnani yake yana iƙirarin kashe Saleem,A cewarsa Deejah ce SALEEM har Shima ya yanke jiki ya faɗi ƙasa babu numfashi


Nan fa hankalin security dinda ya ɓalla Kofar ya tashi, ya dau Keypad din Ashman Da y Gani yashe a ƙasa ,yayi dialing Numbern Abba ,Bugu ɗaya ya daga a tsorace yake sanar dashi Halin da Ake ciki, babu Bata lokaci Abba Ya aika a Kira Psychiatrists Dama Yasan Za'a Rina Tunda Yaga yana Zubo zance a meeting, Ya Kuma yi ma Saleem Duka yasan Abin Ya Motsa.

Tun Rasuwar Mahaifiyar Abin Yaso ya taɓashi Idan makamancin abinda ya faru a Lokacin Rasuwar Mahaifiyar tasa Ta kasance, Sai ya Firgice ya fara abu Kaman Mahaukaci, idan kuma akayi Sa'a da Mutum a kusa dashi sai ya kusa Hallakashi Sannan zai Kyaleshi, Babu mai iya shawo kanshi sai ya suma ..

Da gangar Abba ya tara Ahali ya Kuma kawo maganar Da tayi daidai Da komawan Aeesh wajenshi,Sai Kuma akayi Sa'a Saleem ya dawo a daidai lokacin hadari ke taruwa wanda hakan Ya sake Birkita Lissafi..

Sosai Likitoci suka Hau bashi taimakon gaggawa, kwanakin sa Biyu a kwance ko motsawa bayayi, a rana ta Uku Ya farka kaman Bashi Ba.


Daga wannan Ranar Ya fara Kiyaye duk wata Kaddarar Da zata Hadasa da Gidan Su Abba domin Kuwa hakan Shine mafi alheri a gareshi, Lissafin Abba yazo masa Daidai domin Kuwa haka ya tsara.

A Cikin kwanaki Biyun da yayi a kwance Aeesh tasha Satan hanya da Niyyar Zuwa dubashi Ana kamata,Sun hanata Fita ko ina Sun hanata mu'amala da kowa, So biyu Reey na zuwa Gidan Ana hanata Ganinta A cewar su tana Idda Kuma haramun ne Zantawa da Kowa indan Ana Idda...✍🏼



Tun bayan Wayan da Sukayi da Ammi a ranar da zasu taho Gidan Su Abba ,bata sakejin Komai daga Garesu ba, Dama babu wanda ya damu Da halin Da Ammie ke ciki sai Ashman, Shi kadai ya damu da ya kira yaji Lafiya Gashi Yanzu an Rabata dashi .

Rayuwarta A gidan Su Abba Kaman Rayuwa Cikin Wuta , bata Da Yancin Taɓa Komai na gidan saida Izinin Umma Saude Sun Maidata Bazawarar Dole kullum Kulle take a daki Batada yancin Fitowa waje tasha Iska duk a cewar su Idda Takeyi.


Mazan Gidan Har mantawa Sukayi da Akwai Wata A'isha dake zaune a gidan Inba labari akeyi aka sakota a ciki ba.


Saleem Kuwa saida yayi Jinyar sati Biyu sannnan Ya fara fita, a A ranar da ya fara Fita kuwa Duk inda Yabi sai an Nunashi ance ga Angon Da ya saki Matarsa a daren Farko Tun kan Ya shiga daki.


Bayan Biki da sati Uku Ya koma Asibiti, har a lokacin Ashman bai koma ba, yana dai Zuwa Office dinsa, Kuma ya hana Deejah Aiki a asibitin Sa Yace zai dinga biyanta Albashi Kwatankwacin yanda Yake biyanta a da ,ba haka Taso ba Amma dole ta Amince don yanzu ya fara Sakin Mata fuska dukda ba sosai ba, har abincinta yanaci, Badon komai ba sai don Tausayin Dukan da yayi mata a madadin Saleem ,Da ya dawo Hayyacinsa Aka sanar dashi✍🏼.



Rashin Zuwan Ashman wajen Aiki shi ya sake ba Saleem Daman gwada Rashin Mutuncinsa Akan ma'aikata Yanda Yaga Dama, Wulaƙanci Kuwa Sai abinda Ya ƙaru, baya ganin Kowa da gashi Da zarar kayi masa Laifi zaisa a sallameka in Kayi Sa'a Kuma ya Wulaƙanta ka gashi Yasa A Ninka ma Ma'aikata Albashi ta yanda Zaiyi Tsiyarsa Yanda Yaga Dama , Dukda Saida Akayi ta zama Kafin A yarda da karin Albashin Amma Abba shi ya tsaya Mai kan Komai.



*Maryam*

Yau Da Baƙin Ciki ta tashi Tsakanin Jiya zuwa yau Kajin Ta Sun kai ashirin Wa'enda Suka mutu ga marasa Lafiya Sunfi Goma.


Shiryawa takeyi a Sanyaye Fuskar ta Duk ta Kumbura Alamar tasha Kuka.

Sneakers dinta ta sa, Bayan tasaka uniform dinta, ta rataya jakarta sannan ta Fito cikin Sanyin jiki.


Mamace zaune tana Kasa Wainar safiya, Siddika na Zaune Gabanta sai Zuba surutu take

A wuce ta tayi tana cewa

"Mama sai na dawo"

"A'a Tsaya ki karya mana"

Kamar xata yi kuka tace

"Na koshi"

Mama ta bude ido sosai tace

"A'a toh ke kuma baki da tsoron Allah, kika koshi a Ina? Uban me kika ci?,Jiya ma Ina Kallonki Kika ba Auta Yar Awarar da Nayi dadaddare, oho Ni babu Ruwa na kije can ke Likita ce kinfini sanin Illar ulcer a cikin jikin Mutum Inaji ana cewa Ulcer tsittsinka Hanji yakeyi, Ohow Ina ruwa Na Kika kashe kanki banida Asara Inada Siddika da Salima Me Zai dameni?, ga mijina Lafiyayye Zai iya samar min da wasu Bayan Siddi"

Turo baki Maryam Tayi ta cigaba da takawa, Saleema Ce ta shigo Tana Cewa

"Mama Kaji Uku Cikin Manyan nan sun kara ware wa"


"Innalillahi waina ilaihi rajiun" Maryam tafada ahankali tana lumshe idanu ga mammakin kowa hawaye suka ga ya silalo daga idanunta.

A mammakince mama tace

"A'a mero Meye haka?, kuka kikeyi akan Kaji?"


Aikuwa kaman jira take saita fashe da kuka mai sauti, harda shesheka kamar wanda akayima tsinannan duka.

Sakin baki mama tayi tana kallonta.

Siddiqa Karamar Ƙanwarta ma ganin Antynsu na Kuka yasata Fashewa Kuka mai sauti.

Saleema Dake tsaye tana Kallon ikon Allah dariya ta Kwashe dashi harda tafawa don ita Bataga Abin Kuka ba Don kaji sun Mutu, a cewar ta Lokacin su ne yayi.


"Tabdi yau naga Ikon Allah, Akan Kajin banza kinzo zaki tada Ma Mutane hankali?,Kinga Idan Kuka Zakiyi ga bokiti chan Ki Tara In ya cika, ki tara wani ShashaSha''


Bayan Hannu tasa Ta Share Hawayen ta, Ta dubi Siddika Daketa Faman Rera kuka cikin Turo baki tace

"Auta...!, dauko Min bokiti 😭, Kila sai na cika mata shi zata gane zafin da Nakeji a Zuciyata"

Murfin Coolarn wainan dake gabanta Ta jefe ta dashi

"Kinci gidan Ku dake Da Kajin!, Kika bani haushi kafin ki dawo zan sa Sama'ila Ya yanka Min Dukka ingani ya Zakiyi sakaryar banza"


Fita maryam tayi Tana Cewa

" Wlh aka taɓa min Kajina za'a ga tashin Hankali"





ALHAMDULILLAH

END OF PART ONE


WACECE MARYAM?

MENENE ALAKAR DAKE TSAKANIN SALEEM DA MUTUWAR MAHAIFIYAR ASHMAN?


SHIN ABBA ZAIYI NASARAR SAMUN AEESH KAMAN YANDA YAKE TUNANIN YAYI NASARAR RABATA DA ASHMAN?.


SHIN SALEEM ZAI MAIDA MATARSHI ?, KO KUMA YA HAKURA DA ITA NE?

AREEF

KO

ASHMAN

KO

BAMALLI,

ABBA

SALEEM!.


MEYE DALILIN DA YASA AEESH TA HARAMTA GA ASHMAN???


INA SUREEY? (TWIN SIS DIN AEESH)?


SU WA SUKA KASHE BAFFA?


FIND OUT IN PART 2



BINTOU ✍🏼


NAYI GABAS 🚶🏻‍♀️

1st August

Don't forget to drop ur comment fa!


[10/19, 9:09 PM] Bintou abdool: 🫀🗡️ _*WUƘA A ZUCIYA*_🫀🗡️

_(Bleeding Hearts)_


*PART2*

*026*


Sabuwar Motar da ta siya da Kudin Saleem ta dannawa Key

Qarasowa tayi ahankali zata zagaya

"Me Kaji!"

Muryar Shuraym ya dakatar daita

"Wlh zan Ci maka Mutunci"

"Sorry Anty Nurse, Tun Ɗazu nake ta Kwala Miki Kira Ai,Nasan Kina jina Amsani Ne kawai Baki ga dama ba Shiyasa na miki Yaren Da zaki fi ganewa"

Harara ta galla masa

"I said Am sorry"

Shuraym Ya Fada yana Haɗe hannayensa Biyu waje ɗaya Dramatically

"take" ta cillomashi makullan motar.

Cafkewa yayi yana kallonta da alamun tambaya

"Drive us Hannuna Ciwo yakeyi"

"A'a yau kuma?, To where?"

"To my work place please"

Mere baki yayi

"Ni dai na shiga Uku Da Gatana kin maida Ni Drivern Dole"

Saida ya Buɗe mata sannan
Yadawo ya bude mazaunin driver yashiga ya kunna motar sannan yajasu cikin driving dinsa mai Burgewa, Suna Hira Yana Tsokanarta da Yau dai yaga Hawayen ta (Shuraym Abokin Tsokanan ta ne, Neighbor dinsu ne Amma kusan Rayuwanshi gaba ɗaya a gidan su Yake yinshi Sometimes Shike rakata Delivery Din Kajin dare).

Driving yake tana gwada mashi hanya har suka iso Asibitin, Masu Gadi Suka Buɗe masa Ya Shiga.

Danno kai qossashiyar motar saleem tayi cikin harabar Asibitin.

Tun shigowar motarsa tsirarun Ma'aikan dake wajen suka karkatar da hankalinsu garesa wasu Na Komawa Position din Aikinsu.

Ahankali Shuraym ya qarasa inda ake parka sauran mottocin ya samu wuri Shima ya parka

Cikin Kwarewa Shuraym yayi Parking a Inda Aka tanadarma ma'aikata Batare da yasan Space din Saleem ne ba, yana Kokarin daidaita Parking dinsa Sukaji An daki bayan motarsu da karfin Tsiya.

A Firgice ta ɗago tana Ambaton Sunan Allah, kafin su Ankara an Sake Bugo Bayan Motar da Karfi , wannan Karon Saida Sukaji Ƙarar Fashewar Abu.

Fitowa sukayi kusan tare A mugun Fusace, Shuraym ya fara zazzage Buhun Bala'i ganin Motar Da ta bugi tasu har sau biyu ta baya ,Da alama Kuma da gangar Yayi..

Hankali tashe Maryam ke bin Fasashen Fitila bayan Motarta da Kallo Zuciyarta na Ingiza ta, tsayawa tayi tana kallon Bayan motar kaman Zatayi Kuka , ɗagowa tayi ta dubi motar saleem Babu Abinda ya sameta, Sai yanzu Ta tunada nan ne wajen Parking ɗinsa Babu Mai tunkarar wajen Shida Ashman Wajen Parking dinsu na musamman ne.

Bubbuga Glass din Motar Saleem Shuraym yayi a fusace

"Hey !"

Dakatar dashi Ta yi, tana rike hannunshi

"Kai Shuraym Meye haka?"

"Kyaleni na Koya ma ɗan banza Hankali, yayi mana Barna ji He can't Even Come out and say a word"

"Kasan Koshi waye?"

"I don't Fucking care ko shine mai Asibitin yau sai naga uban da ya tsaya masa "

Duk Abinda Sukeyi Saleem Na nan Zaune a motarsa Yana Jinsu, Amma Ko motsawa baiyi ba.

Da sauri Ɗaya Daga Cikin Securities na Parking Lot ya Rugo ya bude masa murfin kofar

Zaune yake ya dora Hannu daya Bisa Stirring Din Motar

Dayan Hannun Riƙeda waya yana daddanawa cikin Nutsuwa As if Baisan Yayi Barna ba.

Sanye Yake Cikin Bakaken Suits All black hatta Eye Glasses Ɗinsa Black ne ,Da Alama Yau Rashin Mutuncin ne ya Motsa.

Jin an bude kofar yasashi tsayar da abinda yake ta kalli Security dake tsaye still riqeda murfin ayatsine sannan ta watsar

Saida ya shaƙi iska sannan ya kashe Screen Din Wayar, yafara yunkurin fitowa

Ganin hakan yasa securityn qara ja baya sosai cikin girmamawa.

ziro kafa daya yayi saida yaja lokaci sannan ya ida tafitowa cikin salon qasaita fuskar Sa a murtuƙe.

Hakan Da yayi ba karamin Tunzura Shuraym yayi ba.

Saurin Jada baya maryam Tayi ganin Fuskar sa Babu Rahama tana Ambaton sunan Allah don last haduwar su bana Arziki bane Kuma tana Kyaukyata zaton zai rama rashin Arzikin da tayi masa Komin daren Dadewa.

Daga Kai yayi, ya dubi Shuraym Daketa Faman Huci

Yayi Locking Motarsa da Key din Hannunsa Dan yatsine fuska yayi yana daga girarsa daya mai dauke da cikakken shaped lashes Kaman Mace sannan Ya juya ya dubi securityn da ya buɗe masa Kofa , Ya mika masa car key Ɗinsa

"Adjust My car"

ya fadayana juyawa zai wuce Shuraym Ya cakumoshi ta baya a fusace.

"Hey Man....! , wat are You Up to?, ka bige mana Mota and U acted as if U don't know you can't even say a word"

"Shuraym Kyaleshi, I'll handle It"

Maryam ta Fada tana Kokarin daidaita Mood ɗinta, SakinShi Shuraym yayi yana Huci

"Mero Kina Da Hankali?,ji yanda Ya fasa Maki Mota ,sabuwar Motarki ce fa"

"Na sani"

Juyawa tayi Ta dubi saleem Dake tsaye Yana auna Musu kallon Uku saura Kobo

"Sir nayi Maka Uzuri don da Alama Bakar Glasses Dinda Kasa Sunyi Affecting Lens ɗinka Amma Ka sani bazan Bar nan Ba sai an gyara min Mota ta"

Sai a sannan Saleem ya dauke idanunshi daga kanta ya kuma Kalli Shuraym yadanyi wannan dan iskan murmushin na sa sannan Ya tako gabansa Hannunsa Zube a Aljihu

"Shuraym Abbas Mai Dawa at the same time Shuraym Tukur Dan Achaɓa"

Zare Tabarau dinsa yayi Kadan yayi masa kallon sama da kasa

"Dan TITI You even Have the got to nag with me?,Ni da nake tsarkakakke jinin Halal, WOW Ina ka samo Karfin Gwiwa?"

Buɗe Ido Shuraym yayi da mamaki Zaiyi magana Saleem Ya Rigashi

"Ubanka Tukur Ƙanin Uwata Saude ne"

Ya fada yana Maida baƙar tabarau dinsa,Daidai lokacin da Security ya tada Motar Saleem Yayi Reverse.

Cikin Takun Sa Mai Cikeda Isa da izza ya bar Wajen ,security yaja motar da Mugun karfi yayo gaba da niyyar taka Motar Maryam , Da sauri Maryam Ta fizge key dinta a hannun Shuraym da yayi Suman tsaye ya kasa Motsawa kalaman Saleem ba Karamin tayar masa DaHankali yayi ba, a duniyan Nan Baiyi Zaton Akwaiwani Mahaluki da yasan Sirrinsa Banda Mahaifiyarsa Da Mahaifinsa dabai sani ba har yanzu, Ga kuma Sabon Fuskar da bai taɓa gani ba Yana Gwada masa son Gaya Masa koshi waye

Cikin Sauri Maryam Ta Shige motar ta kunna masa key tayo gefe da hanzari har Motar na Kujewa, shi Kuma ya Shigar da Ta saleem Mazauninshi, , da Batayi saurin Kauda nata ba ,Babu abinda Zai hana shi taka Motar don kadan daga Cikin Rashin Mutuncin Saleem Kenan.

Fitowa tayi a fusace ta bi bayan saleem, a Office dinsa Ta Iske shi yana Kokarin saka Labcoat dinsa

Banko Kofar tayi Da Karfi tana Huci

Tsawa ya daka mata

"Hey "
Itama katseshi tayi da tsawa ilahirin jikinta duk cira yake

"Don't you dare *hey* me you Punk...!"

Tafada hawaye na taruwa a idanunta

Jada Baya yayi a Mugun Tsorace ganin Yanda Yanayinta Ya koma abin tsoro lokaci guda.

"WHO did you think u are?, what did u think you are doing?"

Tafada muryarta na cracking.

Wani kallo ya watsamata sannan yaja dogon tsaki yana cewa

"Keh Are You Out Of ur mind?, Fitar min a Office?.

Ya fada yana kokarin Ɓoye mamakinsa.

"Yeah Am completely Out Of my mind,Na haukace!"

Saurin dagowa yayi yana kallonta a mammakince.

Kallon Tsana ta watsa masa

" I'm not putting up with u anymore!, Am not ! Na Gaji, This is so not fair...!,You though I was a fool for not talking back haven't you?, ko ba haka ba?,did you think I left that slide because I was scared Of you?, Kadauka Tsoronka Nakeji?, Ba Tsoronka Nakeji ba, Ina binka ne don inga iya gudun Ruwanka Ka sani Durkusawa Wada ba gajiyawa bane...!"

Saurin dagowa yayi yana kallonta a mammakince

"Kina Da Hankali?"

Nunashi da yatsa tayi dake rawa don Duk ilahirin jikinta rawa yake abinka da mai zuciyay, Ga hawayen kasa Rikewa

"Ina Gargadinka..."

Hannunta yabi da Kallo Cikin mugun Mamaki.

Karkada yar Yatsar tayi

"Na baka nan Da Awa Biyu!,kasa a gyara Min Mota ta ,in ba haka ba Zan baka mamaki"

SALEEM dayayi mutuwar tsaye baya ko motsi yakasa cewa komai don he never Expect this from Her, He knows she's Rude Amma A Kullum tana kokarin Shanye Wulaƙancin Da yake mata Amma bata taɓa nuna masa damuwarsa Akan hakan ba,Sosai take basa Girmansa fiyeda yanda take tunani

Dakyar yabude baki yana nuna kanshi da yatsa

"Maryam Are You saying All these to me...?"

"Kai a wa?, WHO did u think u are!"

"Your senior Colleague"

Ya Bata Amsa Kai tsaye

"Senior Colleague My Foot!,Go to hell! To hell with you and Senior colleague, adane Kake Senior Colleague Dina But now na Bar Aikin nan, idan Asibitin ku Shine last place I could work on Earth na haƙura dashi"

Ta ida atsawace hawaye na gudu afuskarta sosai kamar Wanda akace Uwarta tarasu.

Bai ankaraba yaji saukar takarda a fuskar sa, razana yayi yabi Takardar da kallo inda yafadi, Envelope ne anyi Sealing Ɗinshi

" kana takama da Asibitin yayanka kana amfani da wannan Daman kana Wulaƙanta mutane kasa ido ka Gani kafin nan Da 24hrs saina sa Anyi seizing Licence Dinka I have Alot Evidence to take you Down"

Jifan shi tayi da car key dinta

"Take This !, You have not less than 2hours Ka gyara Min Mota ta or else I'll Surprise you"

Tsayuwar ta ta Gyara sannan ta watsa mishi wani kallon tsana da rinnanun idanunta dake Zubda kwalla tabuga tsaki tareda fadin

"Bloody bastard"

Fuu tafice daga Office ɗin ta bugo kofar da karfi.

Har cikin Yatsun kafarshi yaji tsakinta da gargaɗinta , bugawar kofar da tayi daidai da Bugawar zuciyarsa.

Bin bayanta yayi da kallo gabansa babu abinda take banda Bugawa ga wani abu da ya tokare masa maƙoshi ya kasa haɗiyewa.

Fitowa tayi da Gudu tana share hawaye, Tsirarun Ma'aikatan Dake kai kawo tsayawa sukayi Suna Kallonta Wasu na faɗin Albarkacin Bakinsu,da Alama Yau Ƙanin Oga Ya buga Mata Hauka.

A harabar Asibitin ta iske Shuraym yana Tsaye Kaman Gunki baiko motsa Daga inda Yake ba, Tunanin Zantukan saleem Sun Tsaya Masa Arai, ya kasa Gaba ya kasa baya.

Ta gefensa ta wuce da Gudu ,hakan Yasashi Ɗagowa Ganin itace Yasashi saurin binta yana Kwala mata kira Amma ina harta fice daga asibin, Binta yayi Amma kafin Ya fito har ta tare Napep ta haye, Shima Tare Napep Yayi ya Bi bayanta.

Me Napep na Sauketa ta sallameshi Ta shige ciki da Gudu tana share Hawaye, Shima Shuraym daidai Lokacin Nasa Napep din Ya parka ya Sallameshi sannan yabi bayanta yana Kwala mata Kira.

Wuce su Mama tayi a Parlor Kai tsaye ɗakinta ta shige tasa Key ta fada kan gado Ta cigaba Da Rizgar Kuka.

Koda Shuraym yaga ta shige tana kuka , sai yaji jikinsa Yyi mugun sanyi ,yaune rana Ta farko da ya fara Ganin Kukan ta hakan ba karamin Tayar masa da hankali yayi ba, Hakan yasa Shuraym zargin Duk yadda akayi Saleem Ya gaya mata Mugun Abu akansa,

Lallai yau anta ɓo Maryam don Bata iya zuciya ba, idan ranta ya ɓaci Dole ran kowa ya ɓaci, inba bacci tayi ba Sai abin ya shafi kowa.

Kuka sosai taci ta kuma dau Alwashin bazata sake zuwa Asibitin Su Saleem Ba in Allah ya yarda ,anan Bacci barawo Yayi awon gaba da ita

Awanni Uku tsakani yaro ya shigo wai ana neman Maryam,Mama ce ta aiki Saleema Ta kirata,Bubbuga kofar tayi tayi kaman zata ballata.

Kaman a mafarki Maryam Taji ana Dukan kofar, Miƙewa Tayi Jiki babu kwari ta bude Kofar, Sakon yaro.

Fitowa Tayi tana Tutturo baki, har yanzu ranta a ɓace yake

Mama na xaune parlon tana Baza dakakken garin kuli a Gurasa

Maryam ta shigo ta zube nan kan kujerar kusa da ita ta fashe da matsanancin kuka harda Shessheka.

Hankalin Mama yayi matuƙar tashi Sosai ta tura roban gabanta tace

"Subhanallahi, me ya sameki Mero?"

Cikin kuka sosai Maryam tace

" ba dan iskan Likitan nan bane ya Bibbige min Mota ta harda fasa Min Fitillun bayan mota?"

Mikewa zaune mama tayi ta rufe roban Gurasar ta na Gyara daurin zanin ta

"Wai Wannan Likitan waye Shi?, Waye Ubanshi?, wa ya tsya masa a ƙasar nan?, Yasan Ko ke waye KUWA?, Yasan yanda Akayi aka samoki Kuwa?, Da Alama Sai na je na sanar dashi Dakaina"

Maryam dai kuka takeyi harga Allah har da shessheka

“nidai Gidan Mu zan Koma ,Bazan Iya zaman garin Nan ba na gaji, Na gaji Umma na Gaji mama ni Gidan mu zan koma 😭😭"

Sosai Hankalin Mama ya tashi, Ta shiga Rarrashinta da cewar Zata je har gidan Shi ta ci masa Mutunci

Da kyar Umma Ta samu maryam tayi shiru ta goge idonta.

Mama da kanta Ta zuba Mata Gurasar ta yayyanka Mata Shi kanana, ta kuma yayyanka mata Cocumba kanana ta zuba mata.

Tana hada mata sai Zazzagar Bala'i takeyi, Hankalinta ba karamin tashi Yayi ba da taji Maryam ta fara Batun komawa Gida, Shekarar ta ɗaya Tak a tare da Ita Amma shaƙuwar da Sukayi ya zarce Misali,Ta sanadiyyar ta Rayuwarsu ya sauya daga kunci zuwa haske ,Maryam Alheri ce a Garesu barin ta ba karamin nakasu zai kawo masu ba,

mama na huci tace

"Kuma inshaAllahu sai Mahaukaciyar mota ta Kaɗe banzan ya Mutu"

Da sauri Maryam ta katse ta da cewa

"subhanallahi Mama abin Ai duk bai kaiga haka ba, Dama Cewa Kikayi Allah ya sauko msu da annoba, yar arzikin Da suke takama dashi Ya ƙare ya dawo yana bara a wajen mu"

Jinjina kai mama tayi tana Murmushi

"Anty Maryam ana Jiranki a waje fa"

Muryar Saleema Ta katsesu.
Sai yanzu Ta tuna an aiko a kirata, Tsaki taja a kufule tace

"Kije ki duba min waje"

Fita Saleema tayi tana yi Mata dariya ƙasa Ƙasa.

Babu Jimawa ta dawo riƙe da car key

"Aunty Wai Inji Dr saleem Yace in Baki Makullin Motar ki"

Da Mamaki Maryam tace

"Dr Saleem dakansa?"

"Eh Ba wani dogo Sosai ba?"

"Eh dogo ne"

"Yanada Hushirya giant ne, Murdadde mai Kamada Boxxers Ko?"

"Eh Shine, Mummuna dashi Fuskar sa a murtuƙe baya dariya Ko?"

"Kai Anty wallahi Kyakkyawa ne Ga Murmushinsa Gwanin Burgewa''

"Dalla chan Ina kyau Anan?, kanshi a mulmule Kaman Kwallon Giginya?, Ya akayi Yasan Gidan Mu?"

Da mamaki Mama tace

"Shi wannan Din waye shi?, Me yakai Makullin ki wajenshi?"

"Mamansu Wlhy wannnan Dan iskan Doctor ne, ya kawo min Mota ta"

"Au Mara Kunyan kawo kansa Yayi?, bari inje Inci Mutuncinsa"

Mama Ta fada tana Miƙewa ,ta yafa gyalenta Tayi hanyar Fita, Maryam ji Tayi kaman ta dakatar da Ita, Amma da ta tuna Irin Wulaƙancin da Yayita mata sai ta kyale ta dashi ko yar ashariyan nan Ta buga mashi yaji haushi Zaiyi Jinyar sati bai Warke ba, a yanda yakejin kansa shi shege ne babu mai fada Masa

Please Login or Register in order to submit comment