Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

na Son Kashe Aeesh su tafi da Noor.

Hankalin Ashman a tashe ya hankadeshi zai wuce, Ashraf ya riƙo shi yana Sakin Murmushi yace Aeesh is safe

" Idonshi ya rina yayi Ja, wannan Family is the First over everything, Kun shigo Rayuwar mu, Kun chanza abubuwa kun cutar da Innocent souls , alot of people suffered because of you Sabo You and Faisal, a dalilin ku ake ganin ihty kaman Bata san abinda takeyi ba, a dalilin ku ta fita hayyacinta, a dalilinku kuka maishe su marayu a dalilin Ku kawunan dangi suka rabu, You killed my Uncle, u killed our emotions""

Daidai lokacin yan sanda suka iso, ko wannensu da bindiga a hannu sun nufosu, ya sake shake Wuyan Sabo sosai wanda da zasu kasance a haka na tsawon Minti goma sha biyar tho babu shakka Dr Sabo zai ziyarci lahira Saboda ba karamin Riƙo yayi masa ba.


"Dont come any closer, stay where You are, dukkan ku kar wanda ya matso kusa dani, Dakaina Zan hukunta shi, Zan Hukunta, stay away, duk ku ja baya"

yanda Ashman yake magana kaɗai ya isa ya Tsorata ka, ya koma kamar zautace, idonshi da fuskar shi sunyi Ja jijiyoyin Wuyansa duk sun mimmike, idanunsa a rufe suke sai Sake shaƙar wuyan Dr Sabo yake wanda tuni azaba yasa ya suma, amma baya ganin kowa burinshi ya ga ya kashe shi, da ƙarfi ya sake lankwasa wuyan sabo a karo na biyu ji kake ƙas, jikinsa ya saki ya cillar dAshi gefe ya zame ƙasa hawaye na cigaba da kwaranya a Idonsa,yan sanda suka Nufi Sabo da gudu Suna tattaba shi bai Mutu ba don Haka Babu bata lokaci suka Dauke shi don Su bashi taimakon gaggawa


sai ya fashe da kuka kaman ƙaramin yaro da ya tuna irin Wahalar da Aeesh tasha A soyayyar Aareef, da irin kallon da ake mata na ta zauce.

Naseer ya karaso a sanyaye ya rungume brother ɗinshi, Haka Ashraff Shima.

Saleem da Noor ta daɗe da yin Barci a jikinsa ya Lumshe idonsa a hankali ya furta,

"Allah have mercy on me"

Sannan tako a hankali ya Rungume su Gabaki ɗaya a jikinshi, Naseer ai kuka yake harda majina

*Aeesh*

A tsorace ta buɗe baki zata saki ihu wani daga cikinsu yayi azamar datse bakin Da wani farar handkerchief, sai zare ido takeyi, Jikinta babu inda baya rawa Yau tashin hankali take gani ƙarara a idanunta

Ɗaya daga cikinsu mai ɗauke da baƙaƙen kaya wanda ya rufe daga face dinshi Zuwa chick ɗinshi ya Zaro wata wuƙa wanda sai walƙiya take yayi azamar saita cikinta.

Aeesh ta Zaro ido da yunkurin yin ihu, mutumin Ya sake danna Hankyn a hancinta, dai dai Lokacin da taji saukan ƙarfe a Gefen cikin ta, innalillahi Wainnailayhirraji'un, ta ambata lokacin da azaba ya ratsa ta jini ya fara bin Duk ilahirin Jikinta

yayinda mutumin Ya sake ɗaga wuƙar cikeda rashin Imani Da niyyar sake coka Mata, aka riƙo wukar ta baya, Sadeeq ne, kokawa ta kaure a tsakanin su, kafin Wani lokaci ya illata Yan banza, Nan Ma yan sandan Ne suka biyoshi suka tafi dasu, ita kuma Aeesh aka garzaya da ita asibiti don A bata taimakon Gaggawa.

Cikin Kankanin lokaci akayi mata Dressing aka mata allurai wanda yasa ta samu baçci gabaki dayansu A asibitin Suka kwana hankulansu a tashe,gashi an hana kowa shiga ya ganta ,suna tareda ita har safe.

Sai a lokacin Saleem Ya samu ƙwarin gwiwan komawa Gida,bayan ya idarda sallar Subh

Tana Kitchen tana Fere dankali Sanye take cikin kayan baccinta mai laushi iya gwiwa, Dankwalin kanta ya zame yayo baya hakan yasa Gashinta ya bayyana,

ya tako Cikin Kitchen din Bata San ya shigo ba sai ji tayi ya zagaye hannayenshi a ƙugunta da daura kansa a wuyanta yana sauke numfashi a hankali, shuru tayi tana sauraron yanda yake fitarda numfashi a hankali.

A hankali cikin nutsuwa mai haɗe da kewar ta ya manna jikinsa a bayansa, hannunsa ya zura ta ƙasan wuyanta tare da manne fuskokin su waje guda, wani irin ajjiyar zuciya mai kama da fitar numfashi Saleem ya sauke.

A hankali kuma ya buɗe idanunsa da suke cike da zallar ƙaunar ta, wanda yake haɗe da matsanancin kewanta, dukkan nutsuwarsa ya tattara gaba ɗaya zuwa gare ta, yadda idanunta suka cike da ƙwalla da yadda Jikinta yayi zafi sai ya tabbatar masa Da jiya ta kwana da zazzaɓi ne, ƙarfin hali kawai takeyi karr-karr haka jikinta ke ɗaukan rawa, cikin wani sanyin jiki da kuma wani kalan tausayin ta daya ratsa Zuciyarsa ya manna bakinsa a saman kunnanta, yana sauke mata wani kalar zazzafan numafashi wanda hucin Numfashinsa ya sanya taji jikinta ya mace sosai, gaba ɗaya ya kashe mata gaɓoɓin da suke sarrafa kuzarin jikinta da idanunta kawai take kallonsa tana sauke ajjiyar zuciya, ta turo baki a shagwaɓe.

Ya hura mata iska mai sanyi da kwantar da ita a ƙirjinsa, slowly kuma yake yawo da hannunsa a saman allon bayanta, ta saki hawaye

"Sorry Wifey Jikin ne ko?"

A kasalance ta zame fuskarta, ta shimfida a kafaɗarsa, muryarta a raunane tace.

"Ina ka kwana ?"

Saida yaja ta baya kaɗan ya gyara mata Daurin Ɗankwalinta don Baya Son Gashi a harkar abinci Sannan Yace

"Good Morning, How is my baby"
Ya faɗa yanaShafa Cikinta.

Hawayen dake zuba a idanunta suka sake sauka a shinfidar fuskar ta tace

“sai wahalar dani yake"

Ya Lumshe Lumsassun idanunsa masu kamada na maijin bacci yace

"AM sorry babe....."


"Saleem jiri nakeji"
ta faɗa tana sake cusa kanta a ƙirjinsa sosai

Yasa hannu ya zagayota gaba ɗaya jikinsa ya Rungume

"Haba Wifey hakan bai daceba,kinsan am a kid u're Scaring me please ki daina kuka"

Mintsili maryam tayi masa mai kyau wanda saida ya gantsere tare da sakinta da sauri yana cewa

"daga fad'an gaskiya zaki illatani?, in kin illata mijinki wa zai taimaka miki in Zaki haihu? "

Sai yayi Shuru yana kallon Yanda ta wani narke babu wani karfi a Jikinta

"Hmmm Allah yasa baza kiyi raki yayin labour ba don naga alama baki da juriya ace daga d'an laulayi amma duk kinbi kin langabe kamar wata lagwani"

Harara ta watsama kyeyarsa kamar idonta zai fad'o, shi kam ko sanin tanayi baiyiba sai Tsokanar ta yakeyi ko kadan baya son ganin Fuskarta a haka sai yaji babu dadi, yafi Son ya ganta cikin walwala kaman da, sai a yanzu yake feeling irin Zafin da mata keyi idan Sunada ciki, sai yanzu ya fahimci yanda mata keji idan ya wulaƙanta su a asibiti.

Laulayi Maryam Keyi sosai, bata Iya komai, ga kasala dake ƙoƙarin durƙusar da ita, hakan yasa bata iya komai sai Kwanciya a ƙasa, In yana nan kuma tayi ta narkewa a jikinsa kaman Mage, Ga aman dake hanata saƙat akoda yaushe, ko ruwa tasha Sai ta dawo dashi, duk ta tsure ta ƙanjame kaman wacce tayi shekaru tana ciwo, tuni Saleem ya Maida Ayyan Gidan Abba, inda suka sanya shi a makaranta a nan Unguwar Dosa Kaduna...

Sometimes haka take tasa shi gaba tayi ta kuka, duk sonda takewa cikin bataƙi aje a zubar ba tsabar Azabar da yake gana mata,Cikin na sati bakwai akayi Admitting ɗinta a General Hospital due to severe hyperemesis, Case ɗin yayi tsananin da har suma takeyi in zatayi amai, gabaki ɗaya Saleem ya fita daga hayyacinsa, ya zama kaman shike Laulayin ,wani ƙarin Abin tashin Hankali shine Ko kadan Maryam bata responding to treatment hakan yasa Babu yanda Suka iya dole sukayi Terminating pregnancy ɗin, Aka zubar da cikin ,sai a lokacin ta dawo cikin Hayyacinta.

Saleem Yayi baƙin cikin wannan Abin saboda yana Son Yara sosai, Amma idan ya duba yaga yanda take walwala lafiyanta ya dawo sai ya godewa Allah ,idan Ciki ne in Allah ya nufa zasu sake samun wani, Inna Yathai da kanta tazo Har Gidan tayi jinyar Maryam bayan An sallamota.


*_A gurguje_*

*Aeesh*

A iya wadannan Watannin da Ta shuɗe bayan Abinda Ya faru, Rayuwarta ta chanza, ta samu Farinciki wacce bata san Dadinta ba sai yanzu , Ashman Ya cike Rayuwarta da Soyayyarsa, ya gamsar da ita soyayya mai cikeda Kulawa wanda takeda tabbacin har abada bazai taba bari ta fadi ba, a duk lokacin da take tareda shi, Zuciyarta da kewayenta nutsewa yake a cikin wani irin Ruwa mai zurfi ,Ya saka Soyayyarsa ya wanke duk wani tsatsa da wuƙar soyayyar Aareef ta soketa a Zuciya, Da kyautatawansa yayi nasarar like Zuciyarsa da nata ya ɓoye tabon Yankan da Aareef yayi mata a Zuciyarta da Soyayyarsa.

Itama a ɓangaren ta haka yake, don bata shakkar nuna masa kalar nata ƙaunar a duk inda take ta zama ƴar gata a wajen Aahky ɗinta.

Bayan komai ya natsa ya siyo mata wata galleliyar waya, amma bai kai kalar nada ba, Kuma alhamdulilah har tabon Yankan da Tasha ya fara warkewa.

yanzu baya zuwa koina kaman Yanda Saleem ma ya daina Zuwa ko ina, sakamakon kwace Asibitin su da gwamnati tayi bayan An kama Baffa da Laifin Employing Gurɓatattun ma'aikata masu cutar jama'a Suna Siyarda odarsu.


Yau daƙyar ya yarda suje gidan Ammie don bai manta wayon Da tayi masa kwanakin Baya ba, bayan Ya kawota gida Tayi zamanta.

Sosai Ammie tayi farincikin ganinsu, cikin kankanin Lokaci aka cika gabansu da kayan Marmari iri iri suna ci suna Hira

Ashman Sai Tsokanar Sureey yake da cewar in ta haifo namiji yayi ma Noor kamu, Ammie tace bata son yaro Noor ta girmi abinda zata haifa , ta faɗi hakan tana Miƙa ma Sureey kunun da ta gama dama Mata, karɓa tayi tana yatsine fuska a hankali.

Sallamar da akayi ne yasa Duk Suka maida dubansu ga mai shigowa ,Mai gadi ne ya sanar dasu Sunyi baƙo, Ammie a cewan ta Manager ɗinta ne wanda sukayi dashi zaizo susan yanda Za'a Yi a dawo da Asibitin Abban Aeesh da Aiki.

Mai gadi na fita babu Jimawa baƙon ya shigo

Zumbur Ammie ta Miƙe bayan idanunta sunyi karo da Halittar dake tsaye gabata, shima Ashman a razane ya Mike tsaye ya sauke idonsa akan Dan Dattijon Dake tsaye yanada Madaidaicin tsawo Da baƙar sajen da ta ziraro har hancinsa , Ga gemu madaidaici kai tsaye da ka ganshi zaka gane Hutu da kwanciyar hankali sun Ratsashi.

Mamaki irin tsoro ne da fargaba mai tsanani ya nuna a fuskar su,iya su biyun da suka iya ganeshi, lokacin da kwakwalwar su ke haska abinda suke gani

DukDa dare da Duhu, da girma da dattako amma duk ba wannan Ba, Koda sun mutu sun dawo ne, sun san tabbas idanunsu Bazasu gaza gane kamannin Ƙanin mijin Ammie ba, Kuma Ƙanin mahaifiyar Ashman ,Ɗan uwa kuma Abokin ammie ada, dukda tazarar Dake tsakanin su na haihuwa Shine play mate ɗinta tun Tana Yarinya.

_Auta Ajmal Heart Surgeon_ (likitan zuciya)

A lokaci guda kwakwalwar ta ta hasko mata lokacin da ya bar gida da matarsa Wacce ta kasance autar su Mardiyyah ,Su din mutane ne da suka daɗe da manta su, Basu kuma san dalilin hakan ba, basu cikin lissafinsu kwata kwata, don Tun bayan da suka tafi Basu taba waiwayan juna ba ko a waya, amma yanzu da yake tsaye a gabansu, sai suke ganin kaman a jiya ne aka wayi gari babu su, kuma yau gashi ya dawo.


"A..jmal". "Uncle"

Duk Suka fada a tare, yayinda Aeesh da Sureey suka zuba musu na mujiya don Basu sanshi ba.

"Noory na..."
Ya amsa yana Kallon Ammie

Duk duniya Bayan Faisal shine mutum na biyu da ke kiran Sunanta Noory na, cikin wannan Sigar , hakan Ya tabbatar mata da shidinne ba mafarki take yi ba.

Sai ta katseshi ta hanyar kallonShi da fararren idanunta ƙal tace

"Ina Mardiyyah...?, Inayaranka"

Ta jero Masa tambayoyin duk a lokaci guda,Zuciyarta na mamakin dalilin da yasa kwakwalwar ta ta mance shi duk tsawon wannan Lokacin

Da mamaki Aeesh da Sureey ke kallon mutumin da ya amsa sunan Ajmal , kamanninsu sak da na Abban su.

Sai yanzu Aeesh ta gane shi, Autan dakin Su Abbbanta ne, Wanda ya auri autarsu Ammie Mardiyyah, likitan zuciya wanda ya samu aiki a Egypt Bata taba ganinshi ba, tana yawan jin Labarinsa a wajen Ashman Amma a lokaci guda Labarin sa ya shafe daga Duniyar mu.

Ikon Allah kenan Cikin ƙanƙanin lokaci labari ya baje family, farin Ciki ya mamaye su ta dalilin dawowan mutumin da suka kwana da mantawa dashi a rayuwar su, bashi kaɗai ya dawo ba, yana tareda da yaransa Ayman da Rihaan, kowa ya shiga mamakin dalilin Da yasa Suka kasa Tuna komai a kansa tun tsawon shekaru, suka mance duk abinda ya dangance shi, a ɗaya bangare kuma cikin Jimami suke jinjina mutuwar yar uwar tasu Mardiyyah (Matar Ajmal) wacce ta rasu 8yrs Back a dalilin hawan jini mai tsanani, tareda mata addu'ar Samun Kyakkyawar Sakamako a wajen Allah.

Tabbas Faisal ya buga game dinsa Kuma yayi nasara, Yana zaune chan wata duniyar ya hargitsa kan dangin nan Gaba ɗaya, burin sa ya cika a Baya ya raba Ammie da Duk wani masoyinta dake tare da ita, yayi masu illa ta ɓangarori mabanbanta ya kashe Mijin Ammie ya dasa Tabo a zuciyar ƴarta wacce take matuƙar so a duniya fiye da kowa, ya rabata da sureey na wasu shekaru, a ɗaya Ɓangaren kuwa ya Birkita kan Ashman sbd ɓata masa duk wani shirinsa da yakeyi , don akowane lokaci na rayuwar Ashman Da Aeesh baya taɓa bari Gari ya waye Rana ta kuma faduwa batayi addu'ar Safe da yamma ba, ga Salloli na nafila da na farilla, da azkar kala kala na neman kariya daga dukkan Wata sharri, da ƙyar Alhaji Faisal yayi nasara akanshi bayan ya tabbatar ya ɗora masa aljanu masu birkitar da mutum , kusancin Ajmal da Ammie yasa yaakayi masa tsuntuwa ya bar danginsa gaba daya ya shige chan wani duniyar da bai san kowa a cikinta ba, Burin sa ya raunana duk wani makusancin Ammie, ya kasance ta koma kaman shi, yanda yake rayuwa da tarin rauni a duniya, kuma Bashida kowa a duniya.

A gidan Abba ,akayi masa masauki, nan take Tsohuwar Soyayyarsa ta motsa tsakanin Shi da Ammie , kullum Yana hanyar gidan ko Kunyar yaransa bayaji haka zai barosu a gidan Abba ya Taho Gidan Ammie Yayita bata Labarin Egypt ,tun Tana kaucewa saboda Idon Su Sureey da habeeb har ta riƙa biye masa , gefe guda kuma Cikin Sureey na daɗa Girma batareda wani Laulayi ba saidai Kwadayi Irin wanda baza'a Rasa Ba, laulayinta kalar na Aeesh😄 ,bikin Su Reey da yaa Sadeeq nata Matsowa Yau saura sati Biyu bikin Haka watannin cikin Bakwai amma Banda faɗin da tayi ta ƙara haske, babu Wani abinda ke damunta, a duk lokacin da ta dafa Cikinta sai ta Lumshe idanunta Ta godewa Allah da ya bata kyauta Mafi daraja da zata rinka gani a matsayin Ƙwan ZEEYK.

Biki ya kankama shirye shirye Akeyi tako wane ɓangare, Su Aeesh Sune ƙirjin Biki da ita ake hada hadan Komai, ran Monday Aka fara event Inda akayi Family get Together, Tuesday kuma Fulani day, Wednesday Bridal Shower, Thursday Kamu, Friday Waleemah, Saturday Aka ɗaura Aure wanda Ya tara ɗumbin jama'a daga Garrurruwa Mabanbanta


Bayan An ɗaura aure Aka fara ɗeban jama'a izuwa Wajen da aka Tanadar don Gudanar da Reception Wanda ya haɗa da Dangi da abokan Arziki ta fanni daban daban,

Bayan Duk sun tafi, Aeesh ta shigo Parlorn Reey inda ake ma Reey Makeup, Sanye take da Golden Bridal gown, da dogo Veil dinshi wanda kejan ƙasa ta baya, Rigar ta hadu iya haduwa, Aeesh ce ke koya ma Reey yanda zatayi taku gun dinner din (🤔🙄), , Ummansu ta shigo da Sallama, Reey tayi saurin Sadda Kai saboda Hawayen da yazo mata, Umma ta isa gunta ta rungumeta tace

"MashaAllah Juwairiyyah kinyi kyau ......"

Nasiha Sosai tayi mata, wanda yasa Jikin Aeesh Yayi sanyi sosai, Reey harda Hawaye, Bayan ta gama, make over ta gyara mata Makeup ɗinta sannan Suka fito zuwa inda Motocin Ango ke jiransu.

Suna isa aka sanar da MC Feenah junayd, nan MC ta buk'aci kowa da ya mik'e tsaye don shigowar Amarya, nan da nan DJ ya sa wak'ar M sharrif na Rayuwata, akasa Amarya da Ango a tsakiya Reey da Sadeeq

Sannan Yan matan Amare a layi daya dogo ,, daya na maza, bibbiyu zaa shiga, Ashman yayi kyau sosai, kayansa shigen na ango Sadeeq ne , haka Saleem, naseer da Ashraf, Abokan Ango Masu jiji da kai, mafi yawan su yan Canada ne, tunda a Chan yafi Spending Rayuwarsa, sai shan k'amshi sukeyi, ko don sun ga suna da kyau sun hadu ne oho, Kawayen Amarya kuwan sun sha kyau sun gaji, Anko suka ji na wani lace mai touches din Golden milk, sun daura Head Golden, chan na Hango su Mum asas a Sahun gaba, da Alama dai tun jiya ta tsare wajen, Ga sister Hadiza da Maryam Delight da tarin Littafan su a jakarta wanda hakan ya tabbatar min da cewa dawowansu kenan daga makaranta suka garzayo don Halartar wannan Gagarumin taron, chan Gefe kuwa Maman Suhaila ce ansha Anko amma da alama Babu mai ɗaurin head a Unguwarsu shiyasa Ta saka Jar kulanta kawai🤣🤣, chan na hango Maman mukarram sai tsaki take bugawa ita ayi ayi a kawo Abin tabawa ta ba cikinta hakkinta, Da na leka waje Kuwa Nanah ƴar Kano na Hango sai hayaniya takeyi da Masu gadi, ta manto gate Pass ɗinta a Kano , Kuma fa tasha Rana sosai 😂😂, don Gabaki ɗaya kwalliyar fuskar ta da tayo daga Kano ,ya zazzago har wuya, sai ƙyalli take tana sheƙi🙄😂.

Cikin Ƙawayen Amarya na hango Aeesh Maibanki,sis Waseelah, pharry, nukhtar Mrs Suraj ansha Anko sai wshe haƙora ake.

Su Harnerh, samrah, Zee, ƴan Yara Yara Kuwa sun Rakuɓe waje ɗaya sai kallon Masu kaiwa da kawowa suke burinsu a fara event su naɗa a wayoyinsu ,suyi updating status nasu.

Maman Mukarram , Mum asas da Maman Maama suna Ɓangaren Iyaye suna hira abinsu gwanin ban sha'awa, inshort masoyan BLEEDING HEARTS masu Ƙaunar Wannnan Hadin sun haɗu ta ko'ina.

Couples suka shigo hall din, aiko sauran suka bisu a baya, Ashman Na tareda Yan uwansa Fuskarsa ba yabo ba fallasa, shidai ba Murmushi yake ba farin Ciki ne fall a Zuciyarsa, shi kuma ba daure fuska yayi ba,

Daddy Ajmal ya zo yayi Welcome Speech sannan aka bukaci Baban Abokin Ango da K'awar Amarya su fito don bada takaicecen tarihin su.

Fairoiz ne babban abokin Sadeeq,amma Da mamakin Ashman sai yaji An ambaci sunansa a matsayin babban Abokin ango suka dubi juna da Aeesh bayan An kira sunanta a matsayin babban Ƙawar Amarya.


A hankali ta kamo hannunshi, suka jera sukayi kan Stage din a tare hannunta a cikin nasa abun sai ya burge Mutane.

Suna Isa kan stage Ashman ya juyo ya kalli Sadeeq Dake ta Faman Murmushi, ya masa Alama da ido _Badai Ni ka zaɓa ba? Kajawa kanka_ sannan a hankali ya fara magana cikin natsuwa.

"Am Sufyaan Khameeth Shettima, and Sadeeq is a younger brother to me, we've been together for the 19yrs of Our childhood before he flew to Canada ....."

Iya abinda Aash ya iya faɗa kenan Don Magana mugun Wahala yake mashi,Sadeeq sai hararar sa Yakeyi yayinda hall ya kaure da tafi.

Aeesh ta fara bada bayani kan Reey, ta fadi kyawawan halaiyarta a tsakiyan zancenta ta dubeta da idanunta da suka fara tara ƙwalla tace

"You have been The second Mum to me, you're more than a best friend, Ina miki fatan Alheri Fatanki na gari a gareni ya Biki"

ta kare da mata fatan Alheri"

Reey ta taso ta rungume ta suna kuka, gaba ɗaya hall aka tafa musu, MC tace kafin su tafi sai sun taka rawa.

Aash ya Dube Aeesh ya kuma duban Dunbin jama'ar dake gabansa kawai sai ya saki Murmushi, ya ɗaga hannu ya nuna Naseer dake zaune kusa da Saleemah wacce ta rako Maryam , sannan a takaice yace

"Su fanshe mu"

Yana Gama fadar haka yaja hannun Aeesh suka bar stage din zuwa mazauninsu. yayinda Naseer da Saleemah suka maye gurbin su

Photographers sai kashe musu hotuna ya ke don Babu ƙarya Couples din Sunja Girma.

Aaash da Aeeesh , Saleem da Maryam, Naseer da Saleemah duk Wanda ya waigo ya kallesu sai ya sake kallonsu a ƙaro na babu adadi.

Biki yayi Biki an kai Amarya dakinta, saidai Mu tayasu da addu'ar samun Zaman Lafiya mai ɗaurewa.

Aareef na gida yana kallon Komai a Bintou Abdool TV Zuciyarsa sai bugawa takeyi, a lokacin da aka hasko Aeesh da Ash gwanin ban sha'awa, kwanciyar hankali ya zauna a taredasu, a lokacin da idanunsa Sukayi Arba da Reey Kuwa saura ƙiris ya zauce tsabar rudewa, yasha kuka yayi dana sanin Da bai taba tunanin zaiyi kamarshi ba, yayi Allah wadar da halinsa na Kwadayi da sonkai gashi yanzu sunjashi yayi two zero.

Ashraff baije bikin ba, yana Gidan Ammie ya na Taya Ammie aiki, wanda a zahiri Kowa yasan Wajen Sureey yazo, Bayan Biki da watanni biyu Sureey ta haifi Tsatalatsantalan Ƴaranta Biyu ta mace da Namiji, Rabeeel da ya rakosu Asibiti ya ɗaga Ɗaya Sama Murmushi manne a fuskar sa

A hankali ya furta

"Welcome to the world Zaid Zaid Sa'id Upcoming ZEEYK InshaAllah"

Sureey Ta Lumshe Ido tana jin Wani daɗi na ratsa zuciyarta ƙwalla suka taru a Idanunta.

A Zuciyar ta ta Furta Allah Ya jikanka baby Be happy in ur home

Sannan Ta dube macen dake gefenta a hankali labbanta ya furta

"Allah Ya raya min ke Mum ɗin Baby, Fateemah Bintou Zaid Sa'eed"

Ashraff ya Amsa da ameen murmushi dauke a fuskar sa.

Ya daura da cewa

"Allah ya bani Ikon Riƙe ku duka cikin Amana"

Ta ɗago ta Galla Mai harara Ya wani marairaicemin kamar k'aramin yaro, yana k'ank'ance idanunsa da suka sauya kala. Yace

“daga yau Nine babansu, Ke kuma mata tah to be InshaAllah”.

Yanda yay maganar cikin sanyi da kasala yanda yake magana sak Aashman, ta Kawar da kai idanunta na kawo ruwa, sai takeji kaman Yanzu Rasuwar ZEEYK ta afku.


“mine...! ina k'aunarki da yawa, zan tabbatar miki hakan randa kika dawo gareni, randa aka ɗaura mana aure, jinake duk duniya nafi sauran maza morewa da samun nutsatstsiyar mace mai tarin baiwa da tarbiyya irinki, Har abada zan mallaka miki Ashraf Khameeth da komai nashi, ki yi yanda kikeso dani, burina ki amince mu zama daya”.

Kwallan da bata san na menene ba ya cika mata ido. Tace,

"Da ace baby na Raye, da yana nan zaune kusa dani yana Rero min Makamancin kalaman nan masu daɗin sauraro, da na masa tukwiycin wannan k'yauta da ilahirin rayuwata na ƙara mai da abu mafi tsada a rayuwata na ninka da abu mafi soyuwa a gareni mai girman darajane, kuma zan mik'ashine gareshi shi ɗaya mai daraja, wanda dolene yakasance a waje mai daraja, baby ya riga yayi ma sauran maza zarra da ya fara samuna a farko, saidai a wannan lokacin nima nayiwa sauran matan zarra, ni Surayya ninaima sauran mata fintinkau wajen yin dace da samunka a matsayin miji, kuma uba ga ƴaƴan Baby...."

Sai ta fashe da kuka,yaji kanshi wani irin farin ciki da bai taba tsintar kanshi a ciki ba , a take anan ya duƙa ƙasa yayi sujjada yayiwa Allah godiya, bai taɓa tunanin samun Sureey cikin sauki haka ba , ji yayi kaman Ya Rungumeta tsabar murna, godiya yayita sharara mata Tana Rarrashinta...


Ranar suna Yara sukaci Sunan ZEEYK da Bintou, daɗi wajen Maryam kam ba'a magana, gani take kaman Sureey ta gama mata Komai Tunda ta haifa mata takwarar Mahaifiyar ta da yayanta wanda yafi kowa sonta a duniya, tayi bajinta wajen bude Bakin Aljihunta ga maman baby yara kam Sun ga gata ta ko ina, Saleem ma ba'a barsa a baya ba, ganin Irin Ɗokin Da Maryam Keyi yasa shima ya bada nasa Gudummuwarsa Sosai ya faranta mata rai kuma hakan yayi masa daɗi sosai, Shikou Duk abinda zaiyi wanda zai sakata Farinciki shi yake yi, Aeesh Kam Sune Uwar Baby Sune gaba Gaba a taron, lokacin Noor na da 9months ta fara zuwa ko ina da kafarta, Ayyan kam an girma, har yanzu yana wajen su Abba, Salem bai daukoshi ba a Ganinshi zai takura masa ne.

Bayan Arba'in Aka daura auren Sureey da Rabeel (Ashraf) akan Sadaki Dubu hamsin Lakadan ba ajlan ba, a ranar da ta kasance rana mafi Farinciki a Rayuwar

Please Login or Register in order to submit comment