Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

shiyasa nake datse duk hanyar da zaku bi kuyi nasara".

Wani abu taji ya tokare mata maqoshi

"Zaka iya misalta Yanda nake ji a zuciyata? Mahaifiyata ce fa?"

Tafada tana kafeshi da jajjayen idanunta dake zuban ruwa

Shiru yayi yana kallo yanda take kukan sosai kaman ranta zai fita.

"I have no idea on mother's love,i hate the word mahaifiya....!, Nothing Special About it,mahaifiyarku ta Riga ta rasu Wanda ya kasheta tuni ya manta da yayi wani kisa, ku bar wahalar da kanku ta riga ta lmutu bazata dawoba ,I can't even imagine both of u keda yayanki risked ur lives to find out who was the killer! Huhh.... Mother's killer"

Ya fada slowly Tana Jan tsaki.


Girgiza kanta helplessly

"And kana So Na...?"

Shima lumshe ido yayi batareda yace komai ba,wasu sabbin hawaye suka 6allemata.

"Saleem .I hate you! I hate you so very much! Ban ta6a tsanar wani mahalukiba yadda na tsaneka kuma banajin zan ta6a tsanar wani kamar haka... i hate you more than the killer, if hate you!!!, Na tsaneka!"

Taqarashe cikin kuka sosai ta juya da gudu zata tafi yasha gabanta da sauri ya kamo hannunta ganin tana shirin sake tserewa, wani wawan kallo ta watsa masa mai nuna tsantsan tsanar da take masa, Lumshe idanunshi yayi ahankali yana kokarin maida hawayen dake kokarin zubo masa.

"Cikani..."

"Am sorry , zan baki documents din Ki..."

"Bana so..! ,cikani nace"

Ta fada cikin tsawa tana watsa masa mugun Kallo.

Sakin hannunta yayi ahankali jikinshi na rawa sosai ,kunnensa na sauraron sautin kukanta , Jikinsa duk yayi sanyi kallonta yake yana ganin yadda take fidda kwalla tashin hankalin fuskarta rubuce da CAPITAL LETTERS , Wannan wace irin soyayya take nunawa mahaifiyarta?, dama da gaske akwai soyayya tsakanin Uwa da 'da?, a gidansu kam babu, babu Dangantaka tsakanin uwansa da ya'yanta.

Tureshi tayi ganin yaki matsawa ya tsaya gabanta ya tare mata hanya, amma ko gezau baiyi ba, kukan ta sake saki sosai lokacin kam har muryarta ta fara dishewa tsabar kuka

"Leave....Go...!,leave me alone banason sake ganinka! Please leave!!"

Ta fada tana sake tureshi da iya kafinta, yayi baya , gabaki daya ta gama janye karfin dake jikinsa.


Hakan yasa ta wuce da gudu tana kuka, lumshe ido yayi yana ambaton sunan Allah acikin zuciyarshi don jiyake kamar zata tarwatse..

Kamar zararriya haka ta qaraso wajen motarta ta bude tashiga jikinta na raw ta ba mota key tawani figeta a guje tabar harabar Asibitin da wani irin speed.

Ma'aikatan wurin nurses da Attendants kam abin nema ya samu, kan kace me asibiti ya dauka , dama Ashe Maryam ba son Saleem takeyi ba Shike Neman Favor akan ta shigo rayuwarsa.


Tuki take amma har wani blur blur take gani tsabar tashin hankali.

Maryam Na fita Zeeyk ya dubi Surrey cikin murmushin da yayi matukar kawata fuskar nan tasa ya kira sunanta

"Babby..."

"Hayaty"

Ta fada tana goge kwallar dake gefen idonta

Yace

"Nidake zamuyi aure"

Ta gyada masa kai tana murmushi
"Ashman shine madaurin auren yar uwanki...zamuyi aure amma Sai..Na hada ganinki da Na mahaifiyarki"

Hawaye ne suka zubo mata

"Mahaifiya ta ita taja min rabuwa da yan uwana😭😭..."

Shuru yayi, yana Sauke numfashi , daga nan bata sake cewa komai ba , ta Dora kanta a gefen fuskarsa, Wani irin bacci mai nauyi yayi awon gaba da ita.


Baccin Na dauketa Maryam ta dawo, har wani Rama tayi tsakanin fitanta zuwa dawowanta, har ta dawo kukan takeyi.

Ganinsu duk a kwance yasa ta Nufi inda yake kwance tana tabashi da fadin

"Yaya, Saleem baya tausayin mu, baya goyon bayan mu .."

shiru taji bai motsa ba, tattaba fuskarsa tayi da hannayenta nan ma bai motsa ba, bubuga kafadar sa nan ma bata motsa ba, ta sa kanta akirjinsa taji babu motsi.

" innalilahi wainna ilaihi rajiun"

Sureey ta farka, a gigice ,daidai lokacin mama ta fado dakin

"Mama ya. mutu, Surrey nemo ruwa"

arude ta debo ruwa tazo ta yayyafa masa,suna salati a gigice amma Zeeyk bai motsa ba.

"Surayya Kira likita ,Maryam dubashi bai mutu ba"

Cikin matsanancin tashin hankali ta sa kana a kirjinsa taji shiru, hannunta awuyansa nanma shiru, idonta sa na lumshe amma a kafe


i just dont want to believe it amma nasan Zeeyk ya rigamu gidan gaskiya, da karfi Maryam ke danna kirjinsa Tana kuka

"Yaya ka tashi! wallahi na dainayin jayayya dakai, wayyo Yaya ka tashi...ka tashi Don Allah ka tashi ka dauki fansar Jinin Mahaifiyarka...."







Nayi Gabas🚶

Bintou👻


DEC 2022
[12/19, 2:08 AM] Bintou: _(BLEEDING HEARTS)_



_*Ina Bleeding hearts group members?*_

_🔥🔥_
_keep it flowing⏫, Nima zan Cigaba da Gingering dinku yanda ya kamata_ 😘😘😘

Wannan Page din kacokan naku ne Group members.

WADANDA SUKA HALACCI JANA'IZAR MARAGAYI ZEEYK ALLAH YA BASU LADA😍, muma in tamu tazo Yasa mu cika da kyau da imani.






*059*




i just dont want to believe it amma nasan Zeeyk ya rigamu gidan gaskiya, da karfi Maryam ke danna kirjinsa Tana kuka

"Yaya ka tashi! wallahi na dainayin jayayya dakai, wayyo Yaya ka tashi...ka tashi Don Allah ka tashi ka dauki fansar Jinin Mahaifiyarmu..."

Kuka takeyi Sosai haka mama duk ta tsure,Sureey ta dawo likita Na biye da ita, duk suka fita nan take doctor ya fara Duddubashi , after 20 mins ya fito a sanyaye suna Goge zufa......🚶🚶🚶



Ashman ya kasa gane kan Aeesh Batada lokacin shi ko kadan, bata Kulashi wani irin tsoransa takeji, dukda cewa ba a hayyacinsa ya saketa ba,but she keep denying Itafa yanzu ba matarsa bace,wani Abu dake Bashi tsoro akanta yawan Baccin da yake ganin ta nayi, yasan its Abnormal in pregnancy.

Ta koma wata shuru Shuru ,bata Magana daga Sallah sai bacci sai kuma In taji yunwa taci abinci, ta koma wani iri Sai kace ba Aisha Mai Surutu da yawan sa mutane dariya ba.

Yau yayi deciding zata fara zuwa ante Natal, Don haka yana idarda Sallar Asubahi ya yo gidansu, har zuwa wannan Lokacin baccinta takeyi, tashinta yayi, da kyar ya samu tayi Sallah Sannan Ya taimaka mata Tayi wanka ta shirya Saboda yau Gabaki daya bata jin dadin Jikinta.




Kallonta yake cikeda tsananin Tausayawa ,Ta rame tayi fari ta koma kaman Tsinke ga Cikin da ya fara Fitowa yayo gaba da yayi wani Tsini kaman Ba Dan mutum ne a Ciki ba, Yana Zaune ta shirya idanunsa akanta, yana kallon Duk wani motsinta cikeda tausayawa.

Har ta gama yana kallonta ko ƙyaftawa babu sannan yayi magana yana Kallon Shigar da tayi, Doguwar tana Sanye cikin Gown Royal blue, Tayi Mayafi da bakar mayafi, sannan ta Saka Takalmi mai Tsini

"Takalmin nan kuma ta meye?”.

Baki ta taɓe tana ƙara tsuke fuska. Batare da tace komai ba ta nufoshi Harta ƙaraso idonsa na kanta ,Ya ɗan karya kansa kaman mai Ciwon Sankarau yana binta da kallo

Ɗagowa tayi suka haɗa ido, tayi saurin janyewa da raɓashi zata fice ya dawo da ita,

" ki chanza takalmin naan"

Yanda Yayi maganar babu Wargi, Hakan Yasa ta Turo baki, bata so ba, ta Chanza tana Kunkuni.


Asibitin Saleem ya Kaita, basu bi layi ba, Suna zuwa aka fara dubata, yana Zaune yana Kallon duk abinda ake mata, koda akazo Yin Immunization Na TT, mamaki ne ya kamashi da yaga ta fara kokarin bada hannu a mata alllurar batareda Tayi gardama ba, Murmushi yayi a ransa yace "Hmm yau wace rana Ihty an daina tsoron Allura"

Ganin Yanda take kiciniyar bude hannun ne yasashi Mikewa ya tayata, zaro ido yayi tareda Ambaton Innalilllahi Wainna ilayhirraji'un lokacin da idanunsa Sukayi tozali da Ramin allurar dake cinyar hannunta ,wurin har wani ruwa ruwa yake fitarwa.

"Ihkty.... Menene wannan Na hannunki?,innalillahiaainnailayhirrajiun ihty don't tell me it's what am thinking"

Ya faɗa a zahiri da ƙoƙarin kauda mummunan zaton dake kawoma zuciyarsa farmaki.

Wasu zafafan hawaye suka sauko a idon shi da wani irin karfi ya damko hannunta yayi waje da ita, Suka fito, tashin hankali Wanda ba'a sa mata rana, wani irin Kuka Aeesh keyi ganin Hawaye a idanun Ahky yayi matukar Tsoratata, tunda take Allura bata taba nadama ba irin yau, kuka takeyi Sosai tana Sosa Jikinta da ke mata kaikayi ji take idan batayi allurar a yanzu ba zata iya rasa rayuwarta.


Ma'aikatan Asibiti kam abin nema ya samu, Ashman Na fita aka kira Reeey aka fesa mata, kawarta fa Ashe yar shaye shaye ce, gashi tana Kokarin Hallaka kanta, Hannunta yayi rami Yana Fitarda smelly discharge.
.
Salati Reeey keta bugawa hankalinta a tashe, ta kira layin Aeesh don tabbatarda abinda aka gaya mata, amma batayi picking ba.

kasa Mgn yayi sai buɗewa bayan mota ya wulla ta a ciki,ya shiga da gudu ya fara driving.

Ta madubi yake kallon yadda Aeesh ke Sosa Jikinta a sanyaye

Take furta

"Ahky please...Sorry please"

Kai tsaye gidan Su ya nufa, ya parka motarsa, Ya fito yana huci, rikeshi tayi tana Rokonsa don Allah ya Rufa mata asiri kada ya gayawa Ammie.


Tun Kafin ta ida rufe bakinta ya sauke mata wasu maruka guda biyu zafafa, tashin hankali yasa Aeesh kusan sumewa bakinta na rawa kuka na kwace mata

tace "I'm sorry Ahky, dan Allah...ka rufa min Asiri"

kafin ta Ƙarasa mgn Ashman ta ƙara sauke mata wani marin zai ƙarasa sauke mata wani Sadeeq ya riƙe hannunsa, fuskar Ashman tayi masifar jaaa haka ma idanunsa.

Kuka Aeesh keyi Sosai da iya karfinta

"Kayi hakuri Yaya ka kyaleshi ya hukunta ni, ni nayi masa laifi"

Duban Ashman Sadeeq Yayi

"Maan me Gimbiyar taka tayi maka da tayi deserving those slaps?"

Wani mugun Kallo ya watsa masa Wanda ya tilasta masa kame bakinsa Yayi shuru.

Tsawa ya daka ma Aeesh da ta cika masa kunne da koke kokenta

"Ba zaki min shiru ba sai nayi ƙasa ƙasa dake?,"

Cigaba da kukan tayi, ya wani damko hannunta kaman zai karya ,kuka takeyi cikin tashin hankali a parlor yaja ya tsaya Ganin Ammie da Reey tsaye suna huci, Nufota Ammie tayi , da Gudu ta buya a bayan Ashman Tana Kuka.

Nufota Reey Tayi Cikin matsanancin tashin hankali

"Besty Why...?, why?, bakida hankali ne?, ina Hankalinki yaje?,akan me kike Neman ki halaka kanki?, Akan Me kike Neman Ruguza rayuwarki?, kin bata Kuruciyar ki, kin cutarda Dan Dake cikinki kin sa Zukatan mutane Cikin rauni, Allah ya iya tsakanin mu dakai Aareef, ka lalata baiwar Allah da batajiba bata gani ba, kasa ta ruguza rayuwanta saboda kai, alaka da mai Dan maye koya Yake akwai illa ,nasha Gaya mki amma meyasa kikayi Kunnen kashi Kikayi son ranki?"

yaa sadeeq cikin mamaki da bata barshi ba, mamakin jin Aeesh Na Shaye shaye

Yace

"Ban Fahince ki ba ReeyReey me yake faruwa?"

Cikin Kuka Reey ta zayyane masa komai tun daga haduwansu da Aareff da kuma kokarin da tayitayi wajen ganin ta rabasu, ba don komai ba sai Don Shayeshayen da taga yanayi, da wulakancin da yake mata, motar da ta bashi da Sadakinta wanda Sai daga Baya Suka gano Abindake cikin box din da Ashman ya bata, da Kuma Kisan da ya Laka mata Dukda Sunsan Wasu cikin labarin da Take badawa amma hakan Bai hanasu Firgita ba ,Mamaki da Gigicewa jin Aeesh na Allurar maye ya Ki barinsu.

Zamewa kasa Ammie tayi tana kuka, Ganin Ammien su Na kuka sai hankalin Sadeeq ya tashi yayo kanta zai daka, Ashman Ya boye ta.

"Maaan Ka kyaleni Na babballa yarinyar nan, ka kyaleni Na kasheta, kafin bakin cikin ta ya kashe mana Mahaifiya"

Riketa Ashman yaayi fuskarta a hade

"Ka nutsu Sadeeq ,Karkayi abinda zakazo Kayi Dana Sani"

Kuka sosai Aeesh keyi tana Knkme Ashman, Habeeb ma tsabar tashin Hankali ya kasa hada ido da ita, Ammie ma kukan takeyi, wayanta Sai faman Ringing yake amma Tashin Hankali ya hana ta daga, Reey dake zaune kusada ita tana rarrashinta tayi picking Ganin Private number ne,

"Hello...."

"Ina mai wayar "

"Gata"

"Mika mata"

Cikin Sanyi Reey ta mikawa Ammie wayar , ta karba tana Share hawayenta cikin muryar kuka Tayi sallama

"Nooory....."

Zumbur ta mike Wanda hakan Ya sa duk suka maida hankalinta a kanta.

Bakinta Na bari tace

"F...aisal...!"

Dariya Alhj Faisal yayi daga dayan bangaren

"Am glad baki manta ni ba kaman Yanda bani manta tabon da kikayiwa zuciyata har duniya ta na'de"

Mikewa Ammie tayi ta bar wajen tana Share kwalla ilahirin Jikinta rawa yake

"Kayi Hakuri Faisal ,ba laifina bane, ka kashe min Miji don Allah ka kyale ni haka karka nakasa Rayuwata"

"Noory kenan ai Na Riga Na rantse sai Na Daidaitar da zuri'arki gaba 'daya, Sai Na dandanawa Ahalinki kwatankwacin Raunin da Kika sa naji a lokacin nan, kece silar Arzikina ,kuma saina karar da Dukiyata gaba dayanta wajen Daukar fansa, Ga Yarki Surrey Na Dawo miki da ita, dama aronta nayi, amma nayiwa dayan Raunin da Har abada bazata Taba warkewa ba"

Dittt.... Ya datse wayan, Maganganunsa sai yawo Sukeyi a kwakwalwarta, ta kasa fassara su da yare mafi dacewa. Kalmar ga yarki Sureey Na dawo miki da ita Sai yawo yake mata ,kenan Shi ya sace yarta Sury?, komawa tayi.


Ta iske baki, Maryam ,mama Da kuma Mai kamada Aeesh sak wacce ko Rantsuwa zatayi bazatayi kaffara ba Wannan itace diyarta da tabata Shekaru 21 da suka gabata, ga kuma Zeeyk da aka Turo a Wheel chair.

Kallonsu take jikinsu sai Rawa yake, Idanunta Na tsiyayar hawaye, Shikenan Faisal ya gama da rayuwarta, kenan shine sanadiyyar Lalacewar Aeesh?, kuma shi ya dauke Sureey Tun Ranar Sunan su.?, muryarta Na rawa tace

"Surrey..!"

Sai kuma ta Fashe da Kuka, "

"dama ni nasan 'yata bata mutu ba ,Allah ya Amshi Addu'ata, Allah Na gode maka"

Ta Fada cikin kuka sosai

Ware ido dukkansu sukayi suna Dubanta da mamaki, musanman Aessh da saida taji wani irin yanayi da bata tsammani ba, hawayen Suka zubo mata ,jikinta yayi mutuwan da bazata iya misaltawa ba,kafafuwanta sunyi sanyi, kallon Sureey take tana hawaye itama Sureey kallonta take Idanunta na tara hawaye.


Maryam Tace

"So it true, Surey ga Ummanki, ga twin sis dinki ga kuma yayanki ga kaninki Habeeb shine auta"

Ammie tace

"Baiwan Allah ina kika ganta?, taya kika gane 'yatace?"

"a lokacin Da yayana nuna min Hoton ta a matsayin wacce zai aura a ranar Nayi zargin yar uwan Aeesh ce, don Ko ba'a fada ba kamanninsu ya baci, Kuma ta taba gaya masa su Yan biyu ne, ta karanta dairyn daddynta, satota yayi ..."

A takaice ta basu Labarin Alakar Sureey da Zeeyk da kuma irin zaman da tayi a Chan,shuru Ammie Tayi tana Tuna wasu Abubuwa da suka Shu'de a rayuwarta, tabbas idan ya tabbata Faisal ya cika tantiri zai iya aikata Abinda yafi haka a gareta domin ya dauki fansan Abinda tayi masa.

Kallon Aeesh take da Idanunta da Suka Tara Ruwa, tausayinta ya kamata a ranta tace _kiyi hakuri 'yata, Ni naja miki_

Kallon Surrey sukeyi cikeda mamaki, Allah mai iko, Ita kou sai kauda dubanta take daga Na ammie tana Yatsine fuska da Alama batayi murnar Ganin Mahaifiyar NATA ba

Kallon Aessh Mama tayi tace

"Allah mai Iko aiko kaman An tsaga kara, Ke surayya bakiyi murnar ganin Danginki bane?"

Turo baki sureey Tayi

"Nidai a daura Mana aure da Hayaty....!"

Gyadaa kaai Sadeeq yayi

"Wannaann Shine ikon Allah, ubangiji mai yanda yaso, Sannnu yar nan Ashe inada Yar uwa mace bayan Shashashan nan, Allah sarki Allah Na gode maka, Ranar da muke kallonta a matsayin ta bakin ciki da tonon Asiri A wani fannin ta zame mana Na farin Ciki, Allah ya Shirya Aisha ,taje mun yafeta a familyn mu, ke kuma Taho ki maye mana Gurbinta"

Ganin Duk Jikinsu yayi sanyi yasa Sureey ta dube Aeesh sai Faman Soshe soshe takeyi.

"Yar uwa ?, meyasa Zaku Yafeta a family?, me Tayi Muku?"

"Sanin me Tayi mana Bashine mai muhinmaci a yanzu ba, wanene wannan?"

Inji Ammie

Turo baki Sureey tayi, ta Sake mannewa a Jikin Zeeyk dake zaune a wheelchair kaman mutum mutumi...

Tana Taba gefen Fuskar sa ta dubesu

"Wannan shi nazo Ku aura min Na kma gabana, Shine dangina Shine rayuwata ,Na yadda Zan zauna dashi ko babu Sadaki, bana so ya sake mutuwa a gauro ina sonshi kaman Raina"

.gabaki daya dayansu Dubanta Sukeyi Suna jinjina Karfin hali irin Na Sureey Tunda tazo take naci akan Sai an aura mata shi

Ashman da takaicin Duniyan nan ya gama Rufeshi ya gyara zama sai yanzu yayi magana

"Tunda tace tana So me zai hana a daura mata auren?, ko So kuke itama ta Saka kanta Cikin irin halinda Ihty tasa kanta ne?, nasan Zeeyk Bashida matsala, kuma a irin Halin da yake ciki yana bukatar Ta kusa dashi Sosai kaman Dai matan Sunna haka"

Nan take kowa yayi na'am da zancen

Mikewa yayi yana Binsu da Kallo Suma Duk shi suke Kallo, Duban Aeesh yayi

"Ihty taso muje"

Cikin sauri ta mike tana susan jikinta da karfi kaman zata chanza fatar jikinta.

Duban Ammie yayi
"Ammie...Na tafi da ita, kada Ku neme mu ".

Daga nan ya kamo hannu ta Suka fice,
Har yanzu yana cikin gigita nacewa Aeesh tana shaye shaye kuma shima sanadin Aareef, yana Son Aeesh irin sonda bayawa kansa, amma duk irin Sonda yake mata bazai juri ganin rayywarta ya lalace ba zai iya rabuwa da ita, idan auren Aareef shi zai Zama Silar Daina Shayeshayenta y Yadda zai hakura da ita idan hakan shi zai zame mata mafi Alheri.


Cikeda Murna Maryam ta kira daddyn ta ta sanar dashi Dangin Surrey sun Amince a daura auren, bai damu ba yace a daura Allah ya sanya Alheri.

A Ranar aka daura auren Zeeyk da Sureey wayyo murna kaman Ya kasheta , Sai Tsalle tsalle take murnarta ya Gaza biyuwa, Su mama na shirin tafiya tace Itafa Bazata zauna a gidan Ammie ba, binsu zatayi ,bazata kwana Ko ina ba sai a tareda mijinta.

Tausayin kanta ya kama Ammie, wai ace yarta ta bata Shekaru 21 kenan , ta dawo gareta amma bata nuna Zumudin Ganinta ba?,bata nuna farin Cikin Ganin dangi da Ahalinta ba?, kuka sosai Ammie keyi tana Tausayin 'ya'yanta , duk Ita taja musu, cikin Jimami tayita Sa musu Albarka tareda Neman Yafiya wajen Allah.
.

*Saleem*

A natse yake saukowa daga stairs hannayenshi zube cikin Aljihun wandon dakkakiyar shaddarshi Blue, simple dinki ne Wanda yayi matukar yi masa kyau,Kanshi babu hula sai sumar kanshi da tad'an taru sai shining yake don gyaran da yasha, saleem baya son Sa hulla saboda takura Masan da yake yi,Hannunshi na dama na sanyeda agogo rolex kafafunsa babu takami, Hannunsa Rikeda wata file

Kallonshi Inna saude take, tana ganin Yanda yake saukowa cikin Isa, fuskar nan tasa a murtuke, ta lura cikin kakanakin nan ya rage Saka kananun kaya ya koma sa manya.

Kallonshi take har ya Sauko ya zauna Saman kujera yana Lumshe idanunsa ,hafsah ce ta shigo Ayyan na biyeda ita, Shima cikin irin shigan baban Nasa Amma ya Saka Hulla, Hafsah Na janye da Trolley din kayan Ayyan,shi kuma ayyan hannunsa rikeda Takalman Saleem, Dubansu yayi wani irin kewar inna Yathai yaji ya saukar masa a lokaci daya, Allah sarki Da tana nan da ita dakaanta zata Shirya Ayyan, ta hado masa coffee mai zafi, tunda ta tafi bai Sake shan Coffee mai dadi makamancin Wanda take masa ba.

Duban Inna saude yaayi ya kauda kai, Idanunsa ya maida ya Lumshe
"Sannu ko...!"

Ya fada batareda ya kalleta ba, Inna Saude ta gane da ita yake, amma ganin Yanayin gaisuwan Nasa Na rainin hankali yasa ta waske kaman Bata San yanayi ba.

Bai damu ba, ya fito hafsah ta Saka masa trolley Ayyan a booth tana mamakin Inda zasu ,yasata kwaso Dukka kayan Ayyan.

Driving yake yana tuna Kalaman Maryam

_*Zaka iya misalta Yanda nake ji a zuciyata? Mahaifiyata ce fa!*_

A fili ya furta, _"Yau zaki misalta min Yanda Kikeji a cikin Zuciyarki, idan Akwai wata soyayya a tsakanin uwa da 'da ya zama Dole ki rike Ayyan"_


Kai tsaye Asibitin da aka Kwantar da Zeeyk ya nufa, an sallamesu, Fitowa yayi yana Jan tsaki, kai tsaye gidan su ya nufa.

Mama ya iske a parlor ta tareshi cikin murna, Bari in kirawota, nan take ta shige ciki baabu jimawa ta dawo tace gata nan zuwa.

Kallon Hotunan Zeeyk yake Yana Ayyana Abubuwa da Dama a ransa, ya ji Labarin Yayi Aure kuma Yar Uwar Aeesh ya Aura, kuma Ya Samu Stroke ta sanadiyyan Tashin Hankali da damuwan da Sukayi masa yawa kwanakin baya har akayi tunanin ko ya mutu ne.

Sallama tayi bakin kofar falon,Saida taji an amsa sannan ta Shigo.

Haka kawai taji gabanta yafadi batareda wani daliliba,Kallo daya tayimusu ta kauda kai

"Mummy hy..."

Jin muryar Ayyan yasa gabanta sake faduwa, ya dago kai ta dubessu ,trollyn kayanshi ta gani a gefe, me yazoyi da trolley a gidan ?.

Cikin nutsuwa ta isa kujerar dake facing dinsu ta zauna sai a sannan ta dago ,wani kallo ta watsamasa wanda yasashi saurin dauke idanu ya maidasu kan Ayyan daketa washe baki

"Malam Saleem me ya kawo ka Gidan mu?".

"Babu Sannu babu ina wuni haka ake tarbar miji?"

Yafada Yana Tsareta da Kallo

"Da Alama Bakada aiki, I get a lot to do kaji"

Ta mike tana Shirin barin wajen

"Monstang wait please..."

Tana jinshi tayi kamar bataji shi ba.

Saleemah tashigo da tray dake dauke da Drinks da Snacks a hannunta, sallama dauke a bakinta.

Amsawa sukayi suna kallonta, Qarasowa tayi ta ajiye saman centre table din sannan ta gaidashi a ladabce , ya amsa Yana Sakin Murmushi, Duban Maryam Saleemah tayi

"Aunty ,matar Yaya Tace ta ari wayarki..."

Kyada mata kaai tayi, Saleemah ta fice tana Dariya ,

Shiru ne yadan ratsa falon na dan wani lokaci, kaman An kamar da ita, ta kasa fita



Itadai Maryam haryanzu. tana Tsaye ta kasa gaba ta kasa baya, kuma bata kalleshi ba Sai tambayar kanta dalilin zuwanshi gidansu take ta kasa samo kwararriyar Amsar da zata Fahintar da Ita.


Tsaki taja a zuciyarta, ta wuce ta dube shi kaman Zatayi magana sai tayi shuru ,dama barazana tamai Tace zata tafi sai kuma taga bai hanata ba, hakan Ya sa ta tsaya a tsaye kaman an dasata.

Shiru dakin ya dauka babu mai niyyar magana ita kanta kasa tana wasa da zoben hannunta, sai hadiyar bakin ciki takeyi, shima hankalinshi nakan TVn dake aiki a parlor Yana Kallo amma hankalinsa kacokan Yana kanta, Ayyan Kuma sai ciye ciye yake , Yana Cin mutuncin Snacks dinda ke Jere akan table.


Sun dade ahakan Amma babu wanda keda niyyar motsawa, dukda kowa ta gaji da tsayuwan Amma pride ya hanata zama ya kuma hanata Tafiay

A cewarta, ai nan Gidan su ne, inta tafi ta bashi dama kenan yazo gidansu tabar parlor saboda shi?, nan gidansu ne, in yaso su kwana haka,kuma bazata zauna ba Saboda Ta Riga ta tashi Tace zata tafi.

Shima Saleem dagangar yaki magana Ganin tana Neman tafiya ya kirata tayi banza dashi, jira yake ta tafi Yabi bayanta, ko dakin wa ta Shiga Sai ya bita.

Haka sukaita zama kowa da abinda yake sakawa, sun kusa hour daya a haka ,tana Tsaye har ta gaji Tayi folding hannayenta a kirjinta , itama kallon takeyi, bata kulashi ba, Yadda kasan kurame , ayyyan kam Ko a Jikin shi, tuni ya shanye juice yake Neman Gamawa da Snacks.

Ta qasan idanu ya dubeta, Ranta a bace sai yace

"Kin fasa tafiyar ne?"

Harara ta watsa masa

"Menene..?"

Ya mika mata documents din hannunsa

"Gasu...make sure baki dau doka a hannunki ba,.".

Kallon banza ta Watsa masa a kufule

" meye wannan..?"

"Documents dinda kika bida"

"Bana so...ka tafi da abinka"

Ta Fada tana Hadiye kukan da yazo mata
"Bakyaso fa kikace..."

"Eh nace bana so, ka tafi dashi"

Ta Fada kukan da take boyewa ya fito fili.

Gyada kai yayi. "Okay it's fine"

Sureey ce ta Shigo, Ganinsu Yasa taja ta tsaya daga Nesa Tana Kallonsu da mamaki.

"Aunty Maryam Menene password din wayarki, ya sake Shiga lock"

Bayan Hannu tasa ta share hawayen fuskarta, murya a dishe tace

"Kawo in bude miki"

"A'a nide ki gaya min"

Maryam taja Karamar tsaki, ta maida duban ta kan saleem da ya kafesu da ido

"Auty don Allah...."

Ɗan jimm tayi kaman mai tunani idonta akan saleem ɗin har yanzu,duban File din hannunsa tayi

"Tho Malam In Abinda ya kawo ka kenan zaka iya tafiya"

Ta faɗa cikin takaici kamar zatayi kuka. .

"Aunty...please"

Surrey ta Fada kaman zatayi kuka.

Kaiii yarinyar nan akwai naci.

" *Milas* backward shine password din"

" *Salim?*

Surrey ta Fada Tana Shigarda password din,

"Ah dunno"

Maryam Ta Fada a hankali batareda ta dube shi ba ta gifta zata fice ya damƙota, ƙoƙarin ture hanunsa ta shigayi tana wani ciccijewa .


A karon farko ya saki murmushi, saitin Kunnenta ya rada mata

"Da gaske Sunana kika Saka a matsayin Password dinki?, dama Kina sona?"


"Cikani, bana So....bana Sonka ka kyaleni"

"Bazan Cikaki ba sai kin Fada min gaskiya kina Sona?"

Yaayi maganar Yana rungumota gabaki daya a jikinsa, ji yake kaman ya hadiye ta tsabar farinciki.

ta ɗago a matuƙar firgice tana kallonsa. Ido ɗaya ya kashe mata da cije gefen lips ɗinsa, dole ta kauda kanta tana tureshi saboda yanda takeji tsigar jikinsa ta na tashi. Matsota yayi

Please Login or Register in order to submit comment