Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ƙofa Taja ta tsaya ta kasa ƙarasawa ciki, wani irin fisgar numfashi tayi ta sanya hannayenta ta rungume ƙirjin shi, tana manna fuskarta a ƙirjinshi ta saki kuka gabaki ɗaya ta gama cukuikuya shi.

Kusan a tare su Ammie suka ɗago suka dubesu, da sauri Ammie ta kauda kai itada Inna Yathai, Matar Baffa kam Murmushi tayi tana taɓe baki .

Dumin jikinta yaji yana shiga jikinsa daga shi shiru sukai suna sauraran bugun zuciyoyin juna, hankalinshi yayi Masifar tashi ji yayi kaman ya Maido Ciwon dake Jikinta ya maida Jikinsa, ko kusa basu kula da Su Ammie dake zaune a ɗakin ba.

Ahankali hawaye suka gangaro daga ruffafun idanun AMMIE Tanajin tausayin Ɗiyar ta.

Inna Yathai Kou Sunkuyar dakai tayi,tama kasa kallonsu itama da alama jikinta yayi sanyi.

Matar Baffa dake zaune ƙasan rug kusada Ammie itama kallo daya zakamata kasan itama jikinta a mace yake don sai kallonsu take da expression din tausayi a Fuskarta.

"Ashman Me ke damunta?"

Muryar Ummy (Matar Baffa) ta dakatar da su.

Daƙyar ya iya daga kai ya dubesu,Shiru yayi yana kallon mutanen falon wanda sukayi tsitt banda kallonshi babu abinda suke, Ammie idanunta sunyi jajur don hawayen dake fita a idonta, sosai jikinsu yayi sanyi don kallo daya zaka masu kagane hakan.

Jin muryan Ummy yasa tayi ƙarfin hali ta ɗago kai wani Azababben ciwon da taji yasa ta ƙwala ƙara mai sauti ta sake ƙankameshi Shi tana shesseƙa.

Muryar Ashman na rawa yace

"Ummy Kizo ki taimaka mata bazata iya tafiya ba"

Tasowa Matar Baffa da Inna Yathai Sukayi suka taimaka janye ta daga Jikinshi , kuka take sosai tana Rike ciki.


Kallo ɗaya Ammie tayi mata ta fahimci Abinda ke damunta, ta dauko takarda ta rubuta mata magunguna tace ya siyo Magungunan, zai fita Sukaci karo da Abba zai shigo.


Kallon Kallo aka shiga tsakanin Ashman da Abba gabansa na Faɗuwa.

Washe baki Ashman yayi irin yanda Ashraff yakeyi in Sun Haɗu da Abba yace

"Daddy tun ɗazu naga kayi Parking Sai yanzu ka shigo?"


Wani gauron ajiyar Zuciya Abba ya saki yana fesar da iska daga Bakinshi, yace

"Rabeel kira min Sufyan nayi trying line Nashi but i couldn't reach him"

"Abba Ban zo da waya na ba"

Yay maganar yana tattaba Aljihun sa like serious, Gyada kai ya kawai Abba yayi ya shige ciki, Ashman kuma ya karasa Ficewa hannunsa rike da takardar maganin da Ammie ta rubuta masa.

Ammie da kanta ta ɗaga Aeesh ta shigar da ita Ɗaki, Cikin Magungunan ta ta dauko wata Allura tayi mata, cikin ƙankanin lokaci Bacci ya ɗauke ta .


Ta dawo , a Parlor ta iske su Abba da inna Yathai zaune suna fuskantar juna,Kallon Kallo sukeyi da Alama magana Sukeyi mai mahimmanci Ganinta ne yasa Suyin shuru, Matar Baffa kam har ta tafi.

Ajiyar Zuciya Abba yayi ya saki fuskarsa dauke da murmushi, ita kuma inna Yathai ta kafeshi da ido tana kallon yadda fuskarsa ke fitarda annuri .

"Noorr Ya jikin?" Yafada softly Yana duban Ammie

Gyada kai kawai tayi tana Kallonsu da Mamaki, ba tun yau ba ta lura da akwai Wani ɓoyayyen Alaƙar dake Tsakanin Abba da Inna Yathai , Yau ma ta sake tabbatar da Abinda take zargi Don a gaban Kowa Abba nunawa yake kaman Rayuwar Inna Bai dameshi ba, Amma da zarar sun kebe sai kaga Mood din kowannensu ya sauya.

Kafeshi tayi da Ido cikin Tuhuma, ya shafa kanshi yana dan murmushi

"Allah ya qara sauqi kinji?, Bari na tafi Inada Meeting By 2:00"

Daga nan ya tashi yanufi waje, Ammie tabishi da kallo harya fice.

Ajiyar zuciya ya sauke yanajin kamar anyi lifting wani qaton dutse daga saman qirjinshi, yau da Ammie ta fahimci Abinda Suke zantawa da ya shiga uku.


Yau Sunday, tunda ta dawo Daga zaria bata yarda Zaman 2mins ya hadasu da mama ba, bata so tayi mata Batun komawa gidan Saleem don wannan Karon Cewa tayi Tazo tayi mata kwana biyu ne.


Fitowanta kenan daga bathroom qirjinta daure da Milk towel iya gwiwa kanta sanye da net cap.


Gaban mirror ta nufa tana gyara daurin towel din qirjinta, Dark Skin dinta sai glowing yake,Gashin jikin ta duk sun kwanta sunyi luff sanadiyyar ruwan daya jiƙasu.


Tsayawa tayi tana kallon kanta a mirror ganin yadda skin dinta ya chanza sai glowing yake.

Murmushi tadanyi sannan ta dauki man shafanta tana shafawa, Wayarta dake kan Mirror ne ya hau ruri ta ɗauka, Shuraym ne .

Murmushi tayi tayi sliding,ta Kara a kunne, suka hau hira.

Mamace ta shigo, ta samu Guri ta zauna tana kallon yanda take Wayar tana dariya Sosai rabon da Taga farinciki a fuskar Maryam haka Har ta manta.

Ganin mama ta zuba mata ido yasata dan dagowa ta dubeta sannan ta katse wayar tana murmushi mai haɗe dadariya qasa qasa sbd Last maganar Shuraym da ya bata Dariya.


Shiru Mama tayi tana kallon Maryam cikin takaici kamar ta kifeta da mari, da aurenta take waya da wani ƙato?

"Da Auren ki kike waya da Wannan yaron?!" Inji Mama tana binta da harara

Bata Fuska Maryam tayi, ta Turo baki

Itafa Sai yanzu ta tuna tanada wani Miji Ashe.

"Haba Mama, haba mama? Dan allah ki tausayamin mana, nifa bani da Aure ke ma Kinsan Shuraym Shi nake so"

Wani kallon banza mama tayi mata tace

"Don Iskanci ma,kina tsirrara kike waya da wani ƙato da Auren wani a kanki"

Duban kanta Maryam tayi, sai yanzu ta tuna Ashe Ɗaurin ƙirji ne a Jikinta, kai mama ma akwai Rigima to meye a ciki don tayi Waya da Shuraym Ɗaurin ƙirji? Sai kace video call sukeyi?🤔

Mama ta cigaba da cewa

"Ki shirya Kayanki Gobe Gobennan ni da kaina zan rakaki har Gidan ki Ni kam bazan iya ba,haka kawai mu taru Ni dake muyita daukan Alhakin Bawan Allah"

Kallonta Maryam take kamar zatayi kuka, ahankali tace

"Mama yanzu dake za'a Haɗa baki a kassara min Rayuwa da Ƙuruciya ta?

"Ohon miki, Ko kasheki zaiyi nide wlh na gaji, in Abu yake miki wanda bakiso Kiyi hakuri Rayuwar zaman Aure ta gaji hakan, saida hakuri ake cin riba"

tana kaiwanan tajuya ta fice a dakin tareda bugo kofar da ƙarfi.

Bin bayanta Maryam tayi da kallo, ita kenan Haka Rayuwarta zata ƙare cikin baƙin ciki?, Da wannan kalmar kiyo hakuri Rayuwar Mahaifiyarta ta salwanta, ta auri mahaifinsu babu Soyayya a tsakanin su, yana muzguna mata ,kowa ta gaya mawa cewa ake tayi hakuri, Batareda tayi masa wani Laifi ba ya saketa da yara huɗu, a lokacin da ya tabbata batada Kowa a duniyar nan ya barta cikin gararin rayuwa daga bisani hakan ya kaita inda ta Riski Ajalinta.

Ta tabbata idan ta koma zama da Saleem hakan ce zata kasance, Rayuwarta zata Lalace a wahalce daga bisani Rayuwar ƴaƴanta ya ƙare a Fafutukan Daukan Fansa da Tsanar mahaifinsu kaman yanda nasu rayuwar ta kasance , gaskiya ko me za'a yi saidai ayi bazata koma gidan Saleem bah, Bata shirya ma rayuwar Kunci ba, tana so tayi rayuwa cikin farinciki koda so daya ne a rayuwarta, Kuma inshaAllah ta dau alwashin Aduk sanda ta sake haduwa dashi Saita sa ya rubuta mata takardar ta a kawo ƙarshen Komai.




Abba na fita, Ashman ya dawo bayan Ya siyo magungunan baiyi Mamakin ganin yanda Ammie tayi saurin gano Aeesh na dauke da Ciki ba don Magungunan da ta rubuta mata Duk na masu ciki ne, Saboda Ammie Itama Gynecologist ce.


Bai Sake cika da Mamaki ba saida yaga ta karbi maganin Cikin sakin Fuska tana Murmushi wanda hakan ke nuna masa cewa inna Yathai ta Riga ta sanar da ita komai ,ta fahimtar da ita Aeesh matarsa ce , Amma gnin batayi Masa maganar ba yasa ya baro Gidan a sanyaye

8:37p ta farka, wanka tashiga Bayan yan mintuna tafito sannan tayi sallah jikinta a kasalance, har yanzu jinta take kaman ba Ita ba.

Tana zaune bisa sallaya bayan ta idar da Sallah, a hankali ta shafo cikin ta tana Lumshe ido ,wani irin farin Ciki takeji Especially da ta taɓa cikinta tajishi da ɗan Ƙarfi, Murna Takeyi ta kusa zama Uwa ta kusa haihuwan ɗanta na kanta itada Ahky.


Tunawa tayi da marin da ya zabga mata ɗazu, tayi saurin dafe kuncinta tana zazzare ido kaman yanzu Akayi Hakan.


Tunowa tayi kaman Ɗazu taga Amminta, kodai Mafarki ne?.

Turo ƙofar da Akayi ne yasata maida dubanta kan Ƙofar, Wani mugun tsalle Aeesh tayi ta koma kan gado jawo bargo ta Lulluɓe kanta tana zazzare ido gudun kada Ammie ta ga cikin dake Jikinta.


Dubanta Ammie tayi tana karasa Shigowa hannunta riƙeda tray mai dauke da simple meal da Ledar magani.


Shigowa Ammie tayi ta Dire Tray din bayan ta karanci yanayin ta tace

"Sauko Mamana, Zo kici Abinci kisha magani Kinji"

Kallon Magungunan da Ammie ta kawo tayi, ta Sake jawo blanket take hawaye suka fara bin kuncinta. _Shikenan Ammie taga Cikin tasan komai_

"Mamana kukan Me kike yi?,jikin ne?"

Inji Ammie cikin kulawa tana Taɓa Fuskarta .

Wasu sabbin hawaye suka sake gangaro mata ta sunkuyar dakai.

"Ehrm....Kiyi ...Kiyi haƙuri AMMIE" t

Aeesh ta Fada murya na rawa

"Ehh what happened?" Tafada tana kafeta da idanu fuskarta dauke murmushi.

"Ammie Kiyi Hakuri na kasa Riƙe mutunci na, Na kasa controlling kaina akansa!"

Ammie ta Kafeta da Ido

"Shi wa?"

Aeesh ta sake sunkuyar dakai Hawaye suka biyo kuncinta Muryarta na rawa tace


"A...hky"

Furzar da iska Ammie tayi tana lumshe idanu ta budesu akanta.

Kanta na ƙasa hawaye na diga , Hannu Ammie tasa ta ɗago Fuskar ta da yayi jagajaga da hawaye

"Look into My Eyes Mamana"

Kasa dubanta tayi Sai Sunkuyar dakai da tayi.

"Bai gaya Miki shi Mijin ki bane?"

Aeesh tayi saurin Ɗagowa in shock

"Kamar yaya kenan Ammie?"

Lumshe Ido Ammie Tayi

"Kwarai Kuwa , Yathai ta gaya Min duk abinda Ya faru tsakanin ki dashi, kuma Ummy ta bani Tabbacin Kawun ku Shi dakanshi ya daura Auren A ranar da zai Rasu bayan Wani yayi niyyar Aurenki ta hanyar da bai dace ba......ta Samu Labarin Hakan ne a Wasiƙar da Ya rubuta kafin Ya rasu...."

Nan take Ammie ta haɗa bayanan Inna Yathai da na Matar Baffa ta gaya mata a dunkule

Tun kafin ta kai aya taji Jikinta ya mutu nan take kamar Wanda aka zarewa lakka, tausayin Ashman ya kamata ashe Duk haukan da Takeyi da igiyoyin Auren sa akanta Kuma ya zura mata ido take abinda yaga dama?.

Kuka sosai Aeesh keyi wanda ita kadai tasan Abubuwan da kukan nata ya ƙunsa, wani irin Farinciki takeji irin wanda bata taɓa ji ba tunda tasan kanta, bata taɓa Burin Auren Ashman ba saboda a kullum gani take kaman yafi Ƙarfin ta, Ba komai yasata kuka ba Kuwa sai da ta tuna Auren nan Shi zai zame mata katanga tsakaninta da Sadauki.....😩.


Kuka Takeyi sosai, Ammie na rarrashinta ,saida tayi mai isar ta sannan tayi shuru ,Ammie dakanta ta Abincin a baki sannan tasa tasha magani.

Yau gidan Su Abba a rikice yake, Baffa ya farka da wani irin matsanancin Ciwon Kirji da ciwon Ciki, cikin kankanin lokaci ya fita a Hayyacinsa .

Kai tsaye Asibitin Ashman aka kaishi, Gwajin farko da akayi masa aka gano ya kamu da renal failure Yana buƙatar Urgent kidney transplant kasancewar anfi yin aikin Emergency a babban Asibitin Abba yasa akayi referring dinshi Zuwa chan.

Hankula fa sun tashi kai ya dau zafi, cikin ƙanƙanin lokaci Aka kaishi dayan asibitin.

Duk Rashin sa damuwan Mutum a rai irin Ta saleem sai da ya shiga tashin hankali, don Tun tasowan shi bai taba ganin Kawun sa a yayi Makamancin irin Wannan ba, Bai taɓa Ciwon Mai tsoratarwa ba kuma lokaci Guda ba Sai wannan.


Duk inda suka wuce sai mutanen dake kai kawo wajen sun tsaya suna kallonsu don ganin yadda ake gurguro gadon Baffa manyan doctors na Binshi da gudu, hakan ya isa ya nuna cewa Baffa ba karamin Mutum bane kuma sananne ne a asibitin


Emergency room suka nufa, tun kafin su qaraso aka bude masu kofa kuma suna shiga aka rufo kofar wanda.

Abdul, Naseer, ASHMAN da saleem su suka rakoshi kowannensu Tashin Hankali kwance a fuskar shi.

Dafe kanshi saleem yayi ya yashiga yin safa da marwa cikin mugun tashin hankali.


Shima Ashman tashin hankaline rubuce koina a fuskarshi.

Abdul da Naseer ma haka

Nan take likitocin guda biyu suka rufa akanshi suka fara bashi taimakon Gaggawa kafin Su kaishi Renal Unit.


Saleem Shine jagorar Tafiyar, saboda daga asibitin shi aka kawoshi nan, don haka dashi akaje Renal Unit aka baro su Ashman a Emergency.


Cikin Ƙankanin Lokaci aka fara aikin babu kama hannun yaro da iya basirar su suke Son saving life dinshi don ahalin yanzu yana cikin very critical condition Wanda idan ba Kidney transplant Akayi masa ba Zai iya rasa rayuwar sa.


Dukda Kasancewar Saleem shine jagorar Aikin,amma kasa tsayawa wuri guda yayi ya kuma kasa Shiga ciki, safa da marwa kawai yakeyi a harabar wajen cikin tsananin tashin hankali, idan ya kalli kofar da aka shiga da kawu sai yaji kamar yaje ya ɓallata yashiga yaga wane hali take ciki, Amma sam Zuciyarsa na fargaban ganin Halin da zai iya iskanshi a ciki.


Babban tsoronshi shine kar a Rasashi a yayin da ake aikin , domin Kuwa Kowa ya sani Cikin Kashi ɗari daga Cikin wadanda Ake shiga Dasu Renal Unit, Kashi 35-40 ne suke fitowa da rai, he's scared, haka nan kawai bai san meyasa y damu ba.

Yana Tsaye ya hango giftawan ta cikin Scrub irin Ɗinkin Uniform na ma'aikatan Renal Unit.

"No gizo take min"

Ya Fada a bayyane yana Lumshe idonsa.

Sake ware idanunsa yayi, daga chan ya sake hangota tana shirin Shiga ɗakin da ake ma Baffa Aiki, wannan Karon ba gizo bane ita dince, a hanzarce ya dakatar da ita.


"Stop Right there"

Cakk ta tsaya bugun zuciyarta na tsananta.

"So? Are what are you doing here?... Nasan Baki da Alaƙa da Asibitin nan...!"

Jitayi jinin jikinta na kafewa yayinda wani daci daci ke ziyartar maƙoshinta fanta kada Saleem ya dakatar da ita daga abinda take shirin aikatawa.


"What Bought you here?, Ko kema turokin akayi?"

Yafada yana takowa inda take tsaye bata juyoba


"Am here for work"...

Ta faɗa daidai lokacin da yazo Gaban ta.

"Ƙarya kike Maryam...!, Ban yarda dake ba"

Murmushin da batayi niyya ba ta saki tana duban Agogo.


"Am here for my dad...."

Ta Fada tana juyawa a hanzarce zata tafi, bata ankara ba taji ya damƙi hannunta ya fizgota gaba ɗaya ta faɗa jikinsa ya ƙanƙame ta sosai a ƙirjinsa ya haɗata da bango yana sauke numfashi, ƙoƙarin turesa take da iya ƙarfinta ta kasa gaba ɗaya tsoro ya Kamata kada wani yazo wucewa ya gansu gashi Lokaci sai tafiya yake, an kusa gama aikin, nan da 10mins zasu fito, idan kuma ta bari damar nan ta suɓuce mata zuwanta baiyi Amfani ba kenan.


Wani sihirtaccen murmushi yasaki ya kalleta babu abinda Yake iya hangowa a Idanunta Sai Tsabar Ruɗewa da fargaba , Hadi da Tsoro da Rashin Gaskiya. Bai san Maryam nada Tsoro ba sai Yau ,duk da Rigimanta da nuna ba'a Isa ba'a Isa ba, bata yarda Ta nuna tsoron ta akan abinda yafi ƙarfin ta ba.

Hakan ya tabbatar masa da cewan Lallai akwai Rashin Gaskiya a lamarin ta, Kuma ya dau alwashin hanata aikata manufar ta koma meye shi

"Mey haka Saleem ,Free Me Please....let me Go"

ta faɗa cikin Ƙarfin hali kaman mai shirin sakin kuka tana ƙoƙarin tureshi.


ajjiyar zuciya ya saki ya sake haɗata da bangon,yana ƙura mata idanunsa yana ƙarewa face dinta kallo, sosai baƙar fatarta dake always glowing yake burgeshi sosai, Saikuma ya matso fuskar sa dab da nata har suna shaqar numfashin juna, idanunshi cikin nata.

Murya ƙasa ƙasa yace

"Nasan Turo ki akayi so tell me waye shi?"


Dukda yadda takeji na yanayin kusancinsu ta danne ,Amma sam Tsoron da takeji ya gaza ɓoyuwa a fuskar ta jin Kanta take cikin wani irin yanayi ,Sosai kusancin su yasata cikin wani yanayi a yanayin Tsayuwar su Tana jin yanda zuciyar sa ke Bugawa, itama ta tabbata yana jin nata bugun zuciyar.

"Tell me..."

Ta Tsinkayi muryarsa Kaman daga Sama, Idanunta suka kawo ruwa, hannu tasa ta sake ƙoƙarin ture shi da iya ƙarfin ta Amma ko gezau baiyi Ba.


Murmushin gefen baki yayi yana kallonta, itama samun kanta tayi da d'an rausayar da kanta gefe hawaye suka zubo mata, ganin lokacin da ya rage bai wuce 5mins ba

duk yadda taso kwace kanta ya gagara ,ba ƙaramin riƙo yayi mata ba.

"Ka taimaka min Saleem"

Ta faɗa Idanunta cikeda hawaye, ta kasa yarda yau itake roƙon Saleem.


idanunsa da suka fara sauyawa ya ware sosai yana jin wani kalar abu na jansa tare da fizgar nutsuwasa ,shi kansa Kalaman _ka taimaka min_ ya bashi mamaki, Amma mamakin Yazo da wani shauƙi da ya dauke Nutsuwansa gaba ki ɗaya.


Gabaki daya Salem ya gama tafiya da ƙarfin ta,Sakin Jikinta tayi tana hawaye, zuba mata ido yayi yana kallonta yanda hawayen ta ke jiƙa gaban Rigar sa, yana taɓa zuciyarshi.

Jitake inama zai iya fahimtar halin da take ciki a yanzu?, Domin ta samu Wannan damar ta daukan Fansa tasa Rayuwar ta cikin hatsari, ta dalilin haka ta aure shi, ji tayi zata iya yin komai don ganin damar nan bata Kufce mata ba.

A hankali ta ɗago wet eyes ɗinta, ta zuba mishi ,Shima Kallon ta yake yi .

Ganin bashida niyyar Sakinta yasa ta saka hannunta ta zagaya bayan shi, Ya sake matsota Jikinsa sosai, a hankali ta ƙarawa ƙafarta tsayi Kasancewar yafita tsayi, ta haɗe Lips ɗinsu waje ɗaya, slowly ta shiga bashi scary Kiss a Tsorace Jikinta na rawa.....✍🏼











Nayi Gabas 🚶🚶🚶🚶

Bintou ✍🏼

Nov 17th
[12/7, 8:23 PM] { Queen_Hernah }: *WUƘA A ZUCIYA*
_(BLEEDING HEARTS)_


*053*



hankali ta ɗago wet eyes ɗinta, ta zuba mishi ,Shima Kallon ta yake yi .

Ganin bashida niyyar Sakinta yasa ta saka hannunta ta zagaya bayan shi, Ya sake matsota Jikinsa sosai, a hankali ta ƙarawa ƙafarta tsayi Kasancewar yafita tsayi, ta haɗe Lips ɗinsu waje ɗaya, slowly ta shiga bashi scary Kiss a Tsorace Jikinta na rawa.....

Lumshe ido yayi a hankali ya sauke Ajiyan Zuciya, Ji yayi komai ya tsaya chak

Itama Lumshe ido tayi,tana sauke ajjiyar zuciya one after the other, She feel her senses slipping away from her.

Hannun saleem daya ya zagaye kugunta dashi ya matseta a jikinsa daya hannun kuma ya dafe bangoz haka yasa jakar hannunta ya suɓuce ya faɗi.

Allah ne kadai yasan adadin time din da suka dauka a haka ,Kaman an tadata daga bacci, tayi firgigit ta dawo Hayyacinta.

Ware idon ta tayi in shock This was not what she planned.

A firgice ta dan sake shi , ta zame taja baya kadan tana Rintse Ido da Ƙarfi,amma ko inchi biyu bata matsa ba ya jawo ta da karfi ya mayar da bakin su ya hade,ji tayi kaman ta kwarma ihu, tun daga rikon da yayi mata tasan saleem ba'a Hayyacinsa yake ba, Burin ta kenan So take ta birkitashi ta yanda zai Sarara Mata tayi abinda ya kawota.

A hankali ta ɗora hannunta kan Hannunsa dake Waist ɗinta, cikin dabara ta cire hannun ta Juyashi ta maida shi jikin Bangon.

A hankali ta janye Bakinta tana Kallon face dinsa,Ajiyar zuciya saleem yake yi Jikinsa na vibrating.

Kallon juna suke suna sauke numfashi ahankali tare kamar wadanda suke yaƙi.

Saleem ya zuba mata dukkan emotions din da ke a idonsa emotions With full Of Love.

Daga ita har shi karkarwa suke yi tamkar wadanda ake karkadawa.

Lumshe ido tayi tana Ƙoƙarin Saita kanta, da ƙyar ta samo kanta, ta dube shi har yanzu Jikinta rawa yake.

Shima kallonta yake Amma har yanzu ya kasa Tattaro Nutsuwarsa, ji yake kaman ya jawo ta ya sake.....,Amma a yanda yaga fuskar ta ,zata iya wankeshi da mari a lokacin da ya kwatanta hakan.

Murya ƙasa ƙasa cikin sigar da bata sanadashi ba tace

"Za...n iya tafiya?"

Kaman an dasashi Haka ya tsaya ko Motsawa bayayi, a hanzarce ta maida ta dau jakarta da ta faɗi, tayi gaba.

Yabita da kallo har ta Shige Batareda ya iya dakatar da ita ba, a lokacin da zaka tambaye shi ya sunansa bazai iya baka amsa ba.

She took away his Sense,a sudden Kiss, unexpectedly, from Unexpected Person At unexpected moment , passionately with Full Of love and revenge, dole saleem ya rasa Nutsuwarsa,tarko ta ɗana masa kuma ya kamashi , ita kanta ba'a cikin Hayyacinta take ba.

Tana shiga ta iske har an gama aikin, ɗinki ake masa, gabaki ɗayan su zuba mata ido sukayi .

Hannu tasa ta gyara zaman facemask dinta sannan ta tako Ciki,Wata scrub Nurse ce ta ɗago zatayi magana Maryam ta shaƙa mata Wani abu wanda ta fito dashi daga cikin Aljihun Uniform din ta, nan take ta fadi ta suma, sauran ma suka taso mata kaman zasu Daketa duk ta shaƙa masu suka faɗi sumammu.

Dr ɗaya ya rage, shima sanye yake cikin facemask, a hankali ya sauke facemask ɗin yana sakin Murmushi, itama murmushin tayi amma da ka ganta kasan bai kai har zuci ba, saboda gabaki ɗayanta a firgice take, da ƙyar ta iya ɗaga Harshen ta tace

"Nagode Dr Aash"

Murmushi Ashman yayi Batareda yace komai ba, ya miƙa mata Sterile surgical Globe da Kidney Dish Mai dauke da sabuwar Surgical blade har yanzu Jikinta rawa yakeyi, ta dau Surgical blade cikin Kidney dish.

A hankali Ashman yasa hannu ya yaye yar ƙyallen da aka rufe Baffa dashi.

Gently ta tako Gaban Gadon da Baffa ke kwance kaman matacce jikinshi manne da na'ura ta ko'ina.

Kallon Fuskar sa tayi, wanda yayi fayau yayi haske, nan take Hoton Video sa da yayi ma ummyn ta a lokacin da yake mata fyaɗe ya faɗo mata.

Ta rintse idanu da ƙarfi hawaye Masu zafi suka sauko mata, ta daga Hannunta dake riƙe da Surgical blade Cikeda Tsanar sa,ta Saita saitin ƙirjin baffa dake buɗe, hannunta na Rawa.

Take kuma abinda ya faru tsakanin ta da saleem ya faɗo mata,Ta rintse ido ganin Hankalinta na neman ya rabu kashi dubu,Qoqarin tattaro sauran nutsuwarta takeyi ,Amma ta kasa hannun ta sai rawa yake, Blade din hannunta ya suɓuce ya fadi ƙasa.

Ganin kamar taki nutsuwa yasa Ashman cewa

"Maryam Are You okay...?"

Rintse idonta Tayi da ƙarfi Image ɗin Saleem sai yawo yakeyi a kwanyanta batacikin Hayyacinta gaba ɗaya.

Jikinta na rawa ta duƙa ta sake daukan Blade ɗin, ta rintse ido take hawaye suka sake wanke mata ido.

Duban Baffan ta sakeyi wani tsanarsa ya dirar mata, ta ciji Lips dinta da ƙarfi Hannunta na rawa ta soka ƙarfen Blade ɗin ta saitin zuciyar sa , Hannun ta na rawa ta jashi ƙasa ta rubuta FZ20.

Nan take jini ya fara fita a gurin, Blade ɗin ya suɓuce a hannun ta ya fadi ta fice da gudu tana Share hawaye.

Da ƙyar saleem ya iya jan ƙafarsa da tayi Masa nauyi ya nufi Office ɗin Abba, da ƙyar masu tsaron ƙofar suka barshi ya shiga Dukda Kasancewar shi Nagaban Goshin mai office ɗin.


Turesu yayi cikin zafin nama yana watsa masu jajjayen idanunshi dasuka koma kamar gauta.

Hanyar toilet yanufa cikin sassarfa yabude yashige sannan ya turo kofar da karfi, ya sakarwa kansa shower mai ɗan zafi Batareda ya Cire kayan jikinsa ba, numfashi saleem yake saukewa a hankali,More emotions na taso masa.

Ya kusa 30mins a haka sannan ya cire kayan, ya barsu a yashe a ƙasa,farin towel ya ɗaura jikinsa sannan Ya saka bathrube fara ya fito fuskar nan a turɓune kaman mai shirin yin kuka.

Zaune ya iske Abba,Yana signing wasu document Wani mutum na tsaye da Alama jira yake a miƙa masa Takardun,amma na gamawa ya miƙa masa Takardun.

Duban shi Abba yayi ganin shi da Bathrube Gashinsa na ɗigan Ruwa.

Zama Saleem Yayi kan kujera yayi yana Sauke Numfashi dubanshi Abba yayi cikin kulawa yace

"Son....are you okay..?"

Shuru Saleem yayi,Ganin bai motsa ba yasa Abba miqewa ya zauna kusa dashi haɗi da dafashi, ganin yanda take fidda Numfashi Ya Tsorata.

"Me ya faru?, Kodai wani abu ya Sami baffan naku ne?”

Abba ya faɗa yana shafa suman kansa dake digar ruwa, Hannu saleem yasa ya dafe hannun Abba dake yawo akansa yana jin zuciyar sa kaman zata fito.

A hankali yasa ɗayan hannun ya kwance Bathrube ɗin dake Jikinsa, Numfashi yake fiddawa kaman mai shirin suma.

Ƙirjinsa dake dauke da Kwantacciyan gashin dake sheƙi ya bayyana.

A firgice Abba ke kallonsa, saleem ya Rintse ido, yakai hannun Abba daidai saitin Zuciyar sa, cikin fizgar Numfashi yace

"Dad.....is it Normal...?"

Abba ya Sake zura hannunsa a saitin Zuciyar Saleem , Jin bugun zuciyarsa yaji beyond normal

"What's happening ?"

Lumshe idanu Yayi Hawaye suka sauko masa

"Am dying..."

"Bazaka Mutu ba, what's wrong?"

"My Wife......Please I need her back....."

Shuru Abba Yayi yana kallon yanda hawaye ke gudu a idanun saleem, Jikinsa yaji yayi sanyi, a sanyaye yace

"ur wife...?, Wacce

Please Login or Register in order to submit comment