Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

daraja"

Wasu hawaye masu zafi suka wanke mata fuska

"Kowane Abu mai daraja yana nan a killace ko kuma a rufe ,kudade Nada daraja Duk Wanda ya sameasu baya wulakanta su ,suna banki a killace, idan kou basua cikin bank suna aljihu a boye kuma ba kowa ke iya tabasu ba sai mai su, zinare suna cikin akwati a kulle Mai shi kadai keda ikon tabasu , motoci suna cikin gareji a kulle idan kou basua gareji suna nan an fakasu a inda babu mai tabasu sai mamallakinta ,credentials suna nan a killace maishi kadai keda ikon sarrafata, sai jikina ne zai zamana a bu'de ga Wanda ba muharramina ba? ,Ni matar aure CE mai daraja wacce darajarta ta kere na Dukiya kudi ,zinare ko mota ,na fi karfin na zama mallakinka har abada ,nayi maka Nisan da ko ka hau tsauni bazaka taddani ba......."

Dafe kuncin sa yayi, Hawaye na sauka a saman fuskarsa

"Aisha....ni Kika Mara"

"Zan kara in hda da mangari Idan tsautsayi yasa Ka sake Kai hannu kan Tufafina"

Cikeda mamaki yake Kallon ta, gabaki 'daya ta chanza sai Huci take,idanunta sun Rine ta koma kaman Zakanya, sai da ya rumtse ido sannan ya sake murza hannunsa a kuncinsa Don Ba ƙarya marin ya shigeshi, Tako ina jikinshi sai rawa Yake don har cikin ƙwaƙwalwarasa yaji Marin.

"Kinsan Koni waye...?'

Taja tsaki
"Muzzammiil Jikan Ahmad bamalli, Ahmadu Bamalli Sarkin Zazzau na yanzu!, Kanada Wani Sunan ne bayan Wannan ?"

Kasa Cewa Komai yayi sai Huci yake
Fuska ta sake tsukewa matuƙa, ta harareshi ta gefen ido tana son maida hawayen dake ƙoƙarin zubo mata.

"Kai Mutum ne Kaman kowa, iya Sarautarance da anyi magana dashi kuke Takama,Sarautar Banza Sarautar Hofi? , Bafa ubanka ne Sarkin ba, kanin Kakanka ke Mulki A masarautar fa Ba Ubanka ba..!, Kuma kowa ya sani Ubanka Bashida Gadon Komai A masarautar Don Duniya kowa yasan ta Yanda aka Samoshi"

Saurin ɗagowa yayi Yana kallonta jin ya kamo hanyar tona masa Asiri, A tunanin da Wannan Sirri ne da Babu Wanda yasani daga Sai mahaifinshi da Kakanshi ko mahaifiyar shi bata Sani ba, ya wani sake ƙanƙance idanu cike da firgici.

Dage masa Gira daya tayi,Ganin yanda ya Rude sosai har Wani rawa Rawa jikinsa keyi

"Eh shi uban naka mana, ka dauka Kai Kadai ka iya Binciken Rayuwar Mutane?, Nima na iya, Tun Randa ka dauko family dinka ka sato ni kaso a daura Mana Aure, tun a ranar na fara bibiyar Rayuwarka, Don Haka ka ɓace min Da Gani , Ko ranka ya ɓaci"

Ta faɗi hakan Fuskarta normal but karkaso ka Tona Xuciyarta a lokacin, It was like Hell, ita kanta bata San Komai akan Bamalli ba, Amma tunda ya bukaci yasan Koshi waye daga bakin Ta, sai ta hada Masa Bomb tace Ubansa shege ne, Not knowing Ashe da gaske ne, Don reaction dinshi Kadai ya Isa ya sanar Dakai gaskiya ne Abinda take faɗi.

Tsoro ne fall a Xuciyarta, Amma bata Bari ya gane ba, ta buɗe mota ta Shiga, ajiyan xuciya ta sauke bayan ta sa ma motar key, tana leƙoshi ta Cikin motar ,lallai Bamally yayi sanyi da dane ai da tuni ya Rufe ta da Duka, ko Kuma yasa yaransa Su kaita ɗakin Horo 🙊.

Ya Dade a tsaye dafe dan kunci Yana jinjina karfin wua'ƙancin da Aeesh ta Masa, waishi wata mace ta mara?, Macen ma Aisha ?, sokuwar Nan?, Wacce duk Duniya Babu Wanda ya Raina kamar ita?, Banda Wannan Ma har bincike tayi akan Rayuwar sa?, Lallai yariyar nan ta Gama dashi.

Yana nan Tsaye Ashman Ya Dawo, Ko kallonshi baiyi ba, Amma ganinshi dafe da kunci ya Bashi Mamakin,Ashman da alama kuma ya ganeshi tsabar miskilanci ne ya hanashi tankawa, ya bude mota ya shige yajasu suka wuce ,har Suka kai gida babu Wanda yace ma dan uwanshi kala, kishi Yake ya ganta da bamalli akan me zata tsya da Wani ƙato bayan tasan babu kyau yin Hakan ,ita Kou Ko a jikinta, yarta ta dauko ta saita bakinta a kirji tana shayar da ita , ta Kuma Ma'kala Airpod ta kunna Waƙa tana karkada Kai Kaman wata ƙadangaruwa.

Ashman ji yayi Kaman ya mangareta, wato bata Ma san yanayi ba, abindake Gabanta Shi takeyi hankalinta a kwance...!.

Da isarsu Gida suka tarar tayi baƙuwa Sureey ce, Saleema Ta rakota , ta zage sai Surutu suke zubawa itada Goggo sai kace sun san Juna tun da jimawa dama Surrey bata iya baƙonta ba, nan Aeesh tasa baki sai tambayan ta Rayuwarta na UK take,ita Kuma ta dage sai Zuba take ,sai Chan dare ta koma Gida da cewar zatazo washe Gari .

WasheGari suna, ranar da tayi daidai da ranar Engagement din Reeey da Sadeeq yayan Aeesh ,rankatakaf Jaruman bintou Sun hallara, Munayfer (Jarumar Littafin Hawan jinjina), da Squad dinta, Janaan da Hafsah ,sai Ma'esherh matar Ghost (Jarumar Littafin Maƙaryaci) da Squad Dinta Aisha (Matar Slugg) Da Kuma Khayri kanwar Ghost, dukkansu mazajen su ne suka kawosu ,besty ma ba'a barta a baya ba, tayi tattaki ta garzayo tun Daga ƙasarsu ,Don halar Wannan gaggarumin Bikin Sunan Da Kuma baikon Bestyn Aeesh, Wanda za'ayi tareda Shagalin Bikin Su Aeesh da Aash , Wai tunda ba'ayi Ba'ayi wani Shagali ba,, An haihu ya kamata ayi.

Nikou Bintou nace sai Kace Dole?🤔😂

Jaruman Bintou Munayferh da Ma'esherh ne suka Shirya Hakan ,don Ashman Baima san da Batun ba .

Aeesh uwar baby na zaune Bedroom ko motsawa batayi, ta dora kafa daya kan d'aya tana cin apple sai murmushi take zabgawa idanunta akan baby dake faman sharar bacci, baby tayi ɓulɓul har kumatunta ya fito sai kace ba bakwaini ba, Aeesh ta kasa ya tsare idonta akan duk wani mai shige da fice aɗakin, _yanzu duniyan Babu tabbas Ban yarda da kowa ba, Bazan Yi sakacin da Ammie tayi aka ɗauke mata Diya a ranar suna ba_.

"Ihty...."

Taji an kirata, Sury ce

"Haba Yar Uwa, Don kinji Ahky ya kirani da ihty sai aka ce Miki suna na kenan?, Aisha sunana, Zaki iya kirana dan Aeesh idan Kuma kin nace sai kinyi larabci kisa "u" a farko, *Uhty* Ahky bashida *"sh"* shiyasa baya kiran Sunana,baya Son ya bata min suna"

Surrey ta harareta

"Ke kika Sani, ni na tafi Zan dawo Anjima, Baby na kirana"

Aeesh ta buɗe Baki

"Ke yanzu Baby kike Kiran zeeyk Gansameme dashi Kuma Yana amsawa?🤔"

Surry ta harareta

"Me zai hana?,sai kace mugun Abu?"

“Just Imagine in gwada kiran Ahky da Baby..!, Taɓ ai ranar Inaga saidai wata baniba 😂😂, koda yike Ahky baya duka Allah ya Dawo dashi lafiya Zan gwada inga Reaction ɗinshi"


Dariya duk akayi Aeesh na tsokanar Sureey har ta wuce, Ma'esherh dake sauraronsu tun dazu ta cire wayar dake kunnenta bayan ya datse kiran ta dubi Aeesh tace

"Wai ke Takwara Meyasa daga dawowan Sureey akayi mata Aure?, Sai nake ganin kaman Bai dace ba, at least ta samu bounding da Mumcy...na lura fa tunda ta Dawo bata sake zuwa gidan ba"

Aeesh tace

"Ita Ta zaɓi hakan "

Ta bata Amsa a takaice

"Amma ya kamata ki gaya mata, in ita bata rayu da mahaifiyar ta ba bata san darajar da mahaifiya kedashi ba, ke ai kinyi zama da Uwa Kuma kinsan darajar ta ya kamata ki bata Shawara ta Dawo Ta rungumi mahaifiyar ta, koda bazata iya zuwa Ta gaidata ba, at least ki rinka kokari kina hadasu a waya"

Janaan ta taɓe Baki

"Aeesherh dama Shuru kikayi, don Wannan Aishar bata ɗaukar shawara, Itafa duk Abunda yar uwarta tayi dai dai ne a wajenta "

Aeesh taja Guntun tsaki

"Mtsww Kuma akwai ku da gulman fitina, ina ruwanku da ita?"

Khairi Ta yanki Nama takai bakinta Hadi Da lumshe ido tace

"Na Lura Bintou tafi Son Aeesh Akan mu, duk ta fimu samun Gata a rayuwar Novel"

Ma'esherh ta Taɓe Baki "Sai yanzu Kika gane Hakan?"

Aeesh tace "Wlhy Duk cikinku bintou tafi wahalar Dani ki duba fa, Irin banzan soyayyar da tasa nayiwa Wannan Banzan 😪, sai yanzu na ke ganin wautana ba haɗa hanya danayi dashi "

Reey tayi dariya Sosai

"Aaah Lallai Besty kinyi Lafiya, Allah ya ƙara sauwaƙewa"

Janaan Ta taɓa Munayferh da gaba ɗaya hankalinta ke kan waya tace

"Stop receiving ur selves bintou Tafi son Wannan Shashashar"

Munayferh ta ɗago kanta fuskar Nan a haɗe Kaman hadari.

Janaan Ta cigaba da fadin.

"Neryfee tafi Zuba tsiya, Amma ƙarshenta yayi kyau Babu nadama ko danasani"

Shiru Munayferh tayi taƙi tankawa, sai ma fuska data ɗaure tamau Ranta a ɓace.

Besty taja Guntun tsaki
"Bintou bata so Munayferh ba, illa ma tausayinta da takeji, eh Ai Munayferh abar tausayi ce, Cikin mu itace aka daura Aurenta a tsakiyan Titi, sannnan Aka biya sadakin Ta Dubu uku"

Munayferh ta juyo a fusace ya kama yi mata masifa , Ai gara ita bata baro ƙasarta Don Ta hargitsa Zaman lafiyan wasu ba, Su Khayri suna bata hakuri cewa Da Wasa take , Amma duk Wanda ya karanta Littafin ~Uwar mijina~ _Hawan jinina~ yaasan Munayferh bata barin ya kwana, Kuma bata yafiya, saida Ta Tuno mata tsiyan da ta tafka a Littafin Maƙaryaci Sannan Hankalinta ya kwanta, ta zauna Tana Huci.

_*Hmmm... Jaruman Bintou kenan, duk inda aka haɗu sai an Raba Hali*_

Haka akayi Taro lafiya, Amma Sai Besty Duk tabi ta tsargu, Iya ttonon Asiri Munayferh tayi mata, sai yanzu take nadamar shiga rayuwar Ghost da tayi, gashi Yanzu Taja ma kanta Wulaƙanci a Tsakaninsu.

_*Mustangs*_

Abin Duniya Duk ya ishe Maryam Saleem bai Dawo ba,Bai Kuma kirata ba, daddy sai zazzagar Kidadensa yake, yayi mata Komai kama Daga Furnitures har kayan sawa orden Su yayi Daga Italy, Musamman Yasa aka kawo mai gyaran Jiki tun Daga Maiduguri, tayi wani irin kyau na Musamman, Suman kanta ya kwanta gashinta sai kyalli yake yi, Golden brown skin dinta sai glowing yake kana kallonta zaiyi reflecting ɗinka.

Sosai fa Ake shirye shiryen Bikin,mama Duk ɗaukanta Saleem ya Saki Maryam tunda da bakinta ta faɗa mata.

Jibi ne bikin, bata gayyaci kowa Ba, Haka bata Shirya Event ba, Anyi mata lalla irin Na amare kan nan yasha Gyara, kana ganinta kaga cikakkiyar Amarya.

Ta ɗayan bangaren Kuma Saleem ya Dage sai gyaran sabon Gidansa yake, Ƙaton gidane sosai, shi Kadai Yasan Abinda ya Shirya.

Tana zaune a parlo ta rungome hannunta a ƙirji tayi shiru yanzu Haka Saleem zai Bari a ɗaura mata Aure da Wanda bata so? Kuma Yana sane da Aurensa dake kanta?,wasu Hawaye taji sun Wanke mata fuska, bata san Soyayyar Saleem yayima Xuciyarta illa ba sai yanzu da Ta Fara hango rabuwarta dashi anan kusa, kanta ta ɗaga ta dubi fuskar wayarta, Hortonsu ne a wallpaper ita dashi,Ranar Graduation dinta a school, Kowannen su Fuska a ɗaure Amma Sunyi kyau sosai.

yana sanye cikin wata farar Armless da wando dark blue iya gwiwa, hannunsu ɗaya cikin aljihunsa ɗaya kuma Wayarsa ce, sai ƙamshi yake ƙafarsa cikin flat rubber shoe, zama yayi kan 3seater Yana Shaƙar daddaɗar Iskan Sabon Gidansa , Wayarsa dake hannunsa ya fara ringing ganin sunan *Quack* 🐤 yasa ya miƙe a hankali yake tafiya cike da kuzari da kuma tarin haiba, ya shige Bed Room ɗinsa Fuskar da fall da murmushi.

Dagawa yyi Amma Sai yayi shuru ,Itama shuru tayi takasa magana don jitayi Duk qarfin gwiwarta data dake dashi ya arce.

Haka tayi shuru tana jiran ya farayin sallama tunda shine babba amma shiru.

Shima 6angaren Saleem hakan take don tunda ta Kira ya tabbata Ta ɓangaren Maryam yayi Nasara.

Shiru ne ya d'an ratsa Tsakaninsu ,jin Shurun yayi yawa Yasa Ta fara motsa bakinta a hankali.

"Hy...uhmm...,"

Sai Kuma tayi Shuru tana gyara muryarta

"Ehhen..uhn...Assalamualaikum "


"Wa'alaikumussalam..."

Ya amsa a takaice

"Ehmm.mm...Uhnmm.. Saleem...!"

"Na'am wifey!"

Ya Amsa cikin danne dariyarsa, Don ba karamin dariya ta bashi ba.

"Ina Sauraronki"

Ya katse Shurun

"Kazo ka Karbi yaronka"

Ta fada Don bata san me zatace ba,tayi missing ɗinshi sosai

"Okay,...!"

Ya Fada a takaice

"Okay..?"

Ta maimaita a mamakince, kitt ya datse wayar, bin Wayan tayi da kallo wasu Hawaye suka Wanke mata Fuska ,meyasa ta kirashi?😪 Gashi Ta Ɓatama kanta rai a banza.

Misalin 10:23 Abba na zaune a Main parlour dashi da Inna saude kamar daga sama suka ga Ashraf ya fado dakin ransa bace, A fusace Inna ta dube Shi zatayi magana abba ya Girgiza mata Kai , hakan yasa tayi Shuru tana kumfar Baki

"Haka kawai don Rashin tarbiyyah yaro zai fado daki babu sallama fisabilillahi?"

Hakuri abba Yake bata,Yana tsaka dan bata hakuri , Ashman ya shigo da sallama cikinsu babu Wanda ya amsa,. Shima bai damu ba ya samu Wuri ya zauna Yana gaida Abba , abba Ya hade Rai yana cewa

"Kaji an Sako Matarka Deejah ko?"

Tamkar saukar aradu haka Ashman yaji saukar zancen Abba a kansa. Ya ɗago da sauri yana duban mahaifin nasa tamkar a razane Harara Abba ya zuba masa.

“Lafiya ka tsareni da idanu halan?”.
Ƙasa ya risinar da idanunsa batare da yace komai ba, Sai dai fuskar ta sake rinewa tamkar an aiko masa da saƙon mutuwa.

“Abba ni dai na gaji, Bazan iya cigaba da Zama da ita ba"

Inna Saude da itama ta haɗe fuska tana hararsa ƙasa-ƙasa tace

"Sannu Sara har Kanada Wani zaɓi ne akan Zabin mahaifinka?"

“Ubana Yafi karfin Komai a wajena, ban taɓa bijirewa Umurninsa ba Duk Abinda ya zaɓa min daidai ne,Duk Muninsa a gareni, bana so Lokaci ya Kure nazo Ina Dana Sani, Babu Wanda Yasan Darajar Mahaifi Kamar Mutumin Daya Rasa Mahaifinsa, bana so na kasance Cikin masu Cizon Yatsa Anan gaba,dukda nasan ba kowa ke Cizon Yatsa ba, Idan Ya rasa abu mai mahimmanci a rayuwarsa "

Inna Saude tasani Sarai Magana ya Yaɓa mata a dunkule wato tunda mahaifinta ya taɓa zuwa neman taimakonta ta Wulakantashi a gabansu Har ya rasu Bai sake Takowa Gidan ba, shine yke auna mata maganganu a fakaice.

Abba Kam Wani irin dadi yaji tabbas Ashman Bai Taba kin Umurninsa ba, Hakan yasa ya Sauko masa da Bukatarsa Kai tsaye, Inna Saude kam Gumm tayi tana Huci

"Yawwwa Son , Ina so ka maida Matarka Nan da sati uku, lokacin ta sake warrr warewa, tunda ba Sakinta kayi ba"

Shuru Ashman yayi kansa a ƙasa ,Dr Naseer ya girgiza kansa idonsa akan Aash, ya tabbata yakai ƙololuwar gajiyawa da magana, danma shine, amma da wanine datuni ya shareshi yabar bada amsa ko Don kutsen da Inna Saude tayi masa a magana, Yasan kaf halayyarsa Ashman ya ɗaukko, amma rashin son maganarsa yayi yawa ,ga Zurfin cikin da ya gado wajen mahaifiyarsa, da Shegen miskilancin da Ya rasa a Ina ya debo shi.

A Hankali ya motsa bakinsa Yace
"Dad in ta Shirya ta dawo..."

Daga nan ya mike ba tareda ya jira cewar sa b, ya fice ransa a ɓace ya shigo babu wanda ya kula ya shige part ɗinsa, kai tsaye bathroom ya nufa bayan ya zame kayan sa,ya sakar wa kansa shower sanyi na ratsa masa tsakiyar kansa, sai numfashi yake fitarwa

Da Abba yasan Yanda ya tsani Deejah da baiyi gangancin Bashi umurnin ya Dawo da ita ba, Wannan Wace irin Kiyayya Abba keyi masa?,Sam bayaƙaunar wani abun dan zai Sashi farin Ciki a kulllun burinsa yaganshi cikin bacin rai ,Ko kadan Abba baya masa Adalci baya kyautawa,yanzu Duk Munin abinda Deejah ta aikata a haka yake tunanin zai iya rayuwa da ita?, Bayan Da ita aka haɗe Baki aka Saka Ihtyn sa Cikin ƙunci.

Saida ya gaji dob kansa ya kashe shower ɗin ya naɗe jikinsa a cikin wata bathrub mai ɗan kauri, idanunsa na rufewa sbd azababban ciwon kai a haka ya kwanta saman gado ya daɗe kafin barci ya ɗauke shi, Aeesh sai Kirashi take a waya yana ringing Amma yaƙi dagawa hankalinta Duk yabi ya tashi Kuka tasa tana adduan Allah yasa lafiya.


Goggo taɗan girgiza kanta tana jan guntun Tsaki, tana ganin Abinda yafi Ƙarfinta, Aisha Mai abin mamaki, ubangiji mai hikimane daya halicci bayinsa iri-iri mabanbanta halayya, da a labari akace mata akwai mata masu irin kalar halin Aeesh na rashin Kunya saita ƙaryata, saboda bata taɓa ganin mutum mara Wacce bata kunyar idon jama'a kamanta ba, ko Ashman da Yake namiji ake ganin Bashi da kunya Aeesh ta takashi ya shanye, a gaban kowa take tarairayan Mijinta da 'yarta babu ruwan ta da idon kowa Duk Wanda ya kalla yaga Abinda yafi karfinshi Shi ya jiwo , Bata la'akari da jegon da takeyi tunda babu mai haanta, gaji Wani irin shakuwa da ta sake dawowa a tsakaninsu, shakuwar har ta zarce nada Don yanzu babu Aikin da Yake zuwa, Already Abba ya koreshi a aiki,ya kwace asibitin shi ya ba Salem, Sannan Kuma meenal (P.A ɗinsa) tana Kula da Komai na Companynsa ,Idan kunga ya fita tho masallaci yaje,Yana Nan tare da Yarshi.


Ranar Muke Jira yau gashi tazo ayau dubban Mutane suka halarta a masallacin ƙofar Gidan Mai martaba Sarkin Zazzau Don Daurin Auren jikokin Sarki, Maryam Sa'ed Bamalli da Muzzammil Abkr Bamalli.

Manyan mutane daga Ko ina sun halarta, manya manyan sarakunan gargajiya suma ba'a barsu a baya ba.

Ana tsaka da dauren Aure Yan Sanda SUKA Diro, Sukayi Arresting daddyn Maryam for attempted Murder, Nan take Masarauta ta birkice, yan Sanda SUKA tafi dashi Yana Cewa "sharrin mahassada ne, kada a fasa Auren Zaije Kuma zai fito"

karfe 2:00 dot aka daura Auren,dai dai lokacin da motocin Saleem SUKA Diro .

Nan da nan Takawa ya fara neman yadda za'a samu alkalin da aka kaiwa karar a kashe maganar ba tare da Maganar ta fita ba.

Nan take ya bada umurnin a cigaba da Ɗaurin aure, gate din masallacin a bude yake Kuma a cike yake, yayi packing ya fito direct ya nufi gate din yana shiga fadawa suka taso suka tare shi, securityn gidan kattin gaske ne , amma naushi daya Saleem yay ma babbansu yayi masa sai ga saura akan gwuiwoyinsu suna kokarin nemo numfashinsu da ya ɓatar musu dashi, nan take sauran securities din sukayi kansa.

Hayaniyar da suke yi ne ya jawo hankalin Mutanen dake Shurn ɗaurin aure, Mai martaba ne ya fito Maƙarrabansa ba taka masa baya, zuwa lokacin kou already Saleem ya zubar da mutane a kasa, yana ganin sarki fito ya gane shi dan Shi ɗin ba boyayyen Mutum bane ya karaso gabansa da sauri, yana zuwa ya zube akan gwuiwarsa, yana huce yace

"Ranka ya daɗe ni ne Saleem Mijin Maryam ,Maryam matata ce, Mahaifinta Da kansa ya bani aurenta, inada shaidun da zasu tabbatar da hakan"

Takawa Yace "Babu banida masaniya akan wannnan Auren Don Haka ya zama Dole ka saketa"


Wani Irin Mikewa Saleem Yayi, ya kakkaɓe jikinsa , ya ɗaga murya Yace

"Ku fito"

Nan take Yan jarida suka fito daga Cikin motor Saleem , Suka saita Cameras dinsu in live, Kai tsaye Wajen abban Bamalli suka nufa

"Ranka Shi daɗe Munji labarin kana Shirin Aurawa ɗanka Matar aure ya gaskiyan zanxen tke?"

Wani Irin Zufa ne ya tsattsafo a Fuskar abban Bamalli, Cikin in Ina Yace

"Ehen....uhm..Nnn..Ni fa Ban San da Auren ba"

Dan jarida Yace

"Tho munji labarin Ka taɓa Aurawa Ɗanka Aure da wata, a sirrince"

Nan ma abban Bamalli Ji yayi kaman Ya tsula fitsari a wando duk ilahirin jikinsa Rawa yake

"A'a Wannan Ba gaskiya bane"

Ya bada amsa batareda Yasan Abinda ya faɗa ba.

Mai martaba na tsaye tsabar Takaici ya kasa yin komai, dogarawa kam sun Cika sunyi fam, pimm suke jira Su farr ma Saleem.

Ɗan jarida ya kalli Carmera man Yace

"Masu Kallo da sauraron mu har yanzu dai,Muna gudanar maku da Wannan Shirin na Gani ya Kori jine Wanda Muke haska muku Kai tsaye daga Nan masallacin Mai martaba, a halin yanzu zamu gudanar muku da Faifen Video wanda zai tabbatar muku da Wannan cewa bawan Allahn nan ya ɗaurawa ɗansa aure da wata, bama Auren Kadai ba, ya kashe maɗaurin Auren akan Yaƙi yarda yabada Yarinyar Sannan Kuma ya kashe jami'an ƴan sanda wadanda suka kasance Shaidan gadi da ido a wajen, Nan take aka haska videon abinda ya faru ranar ɗaurin auren Aashman da Aeesh,Ammma Sunyi editing Sunyi dismissing Fuskar Aash, Sannan Kuma suka nuna video a inda Yake waya yna bada umurnin a kashe baffa da Ƴan sandan da suka Shaida Auren.


Kafin ku Sani Labari ya baje duniya, video ya zagaye ko Ina, Mai martaba ji yyi bazai iya Juren cin Mutuncin nan ba, da ido yayiwa Fadawan sa Alama Nan take suka tarwatsa su.

Cikeda farinCiki Saleem ya baro Zaria hankalinsa a kwance, ƙarfe 4:00 ya Isa kD Kai tsaye masallaci ya nufa ya gudanar da sallahr la'asar Sannan Ya Dira a gidan su Maryam.

A bakin gate ya tsaya ya kira wayarta Yana Ringing Bata dauka ba, Haka ya jera mata 3miss calls bata dauka ba, Abinda bai taɓayi ba, Ko Kai waye ya kiraka sau daya baka daga ba ya ƙyaleka kenan.

Kai tsaye ya Danna Kai Cikin Gidan, Yana shiga idanunsa suka hasko masa ita, tana sanye cikin wata tsadaddiyar' blue lace Tayi kyau sosai ,Da ka ganta kaga Cikakkiyar Amarya, ta rako wata Ƙawarta, Ganin ta nufo gate yasashi komawa da baya.

Ta jima tsaye a bakin gate kafin ta suyi Sallama, tana Shirin komawa ciki taji an wani riƙota Ta baya, ƙara Ta Saki, Yasa hannu ya toshe bakinta, zaro ido tayi duk ilahirin jikinta rawa Yake, Nan take ta birkice.

A Hankali ta sauke sanyayyen Ajiyan Numfashi ta sauke tana jin yadda daddaɗan ƙamshin turaren Saleem na Arabian oud ke ratsa mata zuciya, bazata taɓa Manta Wannan ƙamshi mai daɗin nan ba Tasha jin Irin ƙamshin a jikin Mutane da dama, Amma a jikinsa kaɗai take jinshi da irin Wannan Salon mai narkar da Zuciya, ɗago da kanta ta yi a hankali ta kallesji suka haɗa ido, Murmushi yayi mata yana ƙarewa fuskarta kallo har lokacin hannunsa na dafe da bakinta, Murmushi tayi tana jin wani abu na ratsa Zuciyarta, Hannunta tasa ta cire hannunsa dake bakinta tana Turo Baki.

Yace
"Sake Dan Allah"

Zaro ido tayi.
"Me FA?"

Ya turo baki
"Haka"

Dariya tayi Wanda ya ƙara Ƙawata Fuskar nan nata,fararen haƙoranta suka bayyana tace

"Baka ganka ba, Kaman mace"


Murmushi yayi Yana shafa gemunsa ya ɗanja da baya yana ƙare mata kallo frm head to toe gani Yake Kaman an chanza Masa Ita,Ta cinye kajin kiwo tayi Ɓulɓul

"Kinyi kyau sosai Wifey"

Ya faɗa emotionally, lumshe ido kawai tayi tana Sakin murmushi.

"Yau Zaki tare a gidana f..."


Tau....Bha...Grrrh...tahh...


Harbin bindigan da Yaji har sau huɗu a tare ya hanashi ƙarasawa, maryam tayi baya ya faɗi jini na bin jikinta, da Karfi ya tarota Yana kiran sunanta da ƙarfi Cikin tsananin ruɗewa.

"Maryam....Maryam no Maryam Wake up z Buɗe idanunki, karki lumshe su...."


Ya rude ya furgice Sai Sumbatu yakeyi Hawaye na bin Fuskarsa,Wani Irin zabura maryam keyi tana kallonsa nunfashin ta na Sama, a Hankali idanunta suka Fara lumshe wa

"No.... maryam karki lumshe su nooooo"

Dai dai Lokacin da idanun suka Ida Rufewa








RIP MARYAM 🐤

Nayi GABAS🚶🚶🚶


BINTOU
*WUƘA A ZUCIYA*
_(BLEEDING HEARTS)_



*062*




Ya rude ya furgice Sai Sumbatu yakeyi Hawaye na bin Fuskarsa,Wani Irin zabura maryam keyi tana kallonsa nunfashin ta na Sama, a Hankali idanunta suka Fara lumshe wa

"No.... maryam karki lumshe su nooooo"

Dai dai Lokacin da idanun suka Ida Rufewa,a Lokacin da Ambulance ya faka a tsakiyan Gidan, Aka ɗauketa aka garzaya Da Ita Asibiti.

Kafin akai asibiti Ta zubar da jini sosai, tunkai sukai Asibitin aka cire mata Bullets din Sukayi dressing Wajen Sannan Suka maida hankali Wajen Samo Numfashinta, suna isa Asibiti aka ɗaukota a Emergency stretcher aka kaita mini theater Ana ƙoƙarin Cheto rayuwar ta Saleem na Biye dasu hankalinsa a tashe, yau ma jininsa ya bada aka sa mata, Amma wannan karon Saida aka Bashi gado don Yna gama bada jinin ya fadi a sume sbd tashin Hankali.

Kwakaki Uku Ta ɗauka bata San inda take ba, zuwa Wannan Lokacin kuwa tuni an Kama wadanda Sukayi harbin, mahaifin Bamalli Shi ya aikosu su kashe Saleem Sai kaddara ta faɗa mata, tuni aka garzaya Da Masu laifi gidan gyaran Hali,Daddyn maryam na Nan har ya fara girban abinda ya shuka.


A Rana ta huɗu ta farka duk ilahirin Jikinta yayi Tsami, harbi huɗu akayi,Amma Biyu ne suka sameta a hannu da Kuma gefen bayanta shiyasa take ji Kaman an Dora mata Duniya a wajen, Sai Rintse idanu take , Sai Sannu yake ta faman jerowa, ya ɗagota yayi mata matashi Da pillow Kallon sa take tana ganin yanda yake NanNan da ita

Dama saleem ya iya kula da mace?, A iya saninta kula da kanshi ma sai ya kama dole yakeyi.


kama hannunta yayi yana gyara zama kana yasa hannu daya ya miƙar ƙafafuwan Ta sosai, a Hankali ya jawo Table Ɗin gabansa ya ɗauko Soyayyen Irish ya nufi

Please Login or Register in order to submit comment