Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

bakinta yace

"Buɗe bakinki"

yadda ya tsareta da Idanu yasa ta kasa buɗe bakinta Ta kauda Kai tana murmushi, hannu Yasa ya juyo da fuskarta,ta Lumshe ido tana Kauda Kai, Don Taji kunyarsa sosai

Bai masan tanayi ba, ya sa hannu ya ɗago Fuskar ta.

"Mustang Kunyata kike ji....?"

Girgiza kanta tayi, "Then Haa"

A kunyace ta buɗe bakin ya zura mata irish din a hankali ta shiga taunawa, a nutse yake bata abincin tana ci cikeda basarwa, kaɗan taci ta ɗauke kanta , Kallonta yayi

"Me kenan?"
Ta yamutsa Fuska
"Na ƙoshi"
Baice komai ba, juyawa yyi ya ɗauki wata yankakkiyar Water Melon ya Kai bakinta, tasa hannu ya Amshe

"Allah da gaske na Koshi, ko Ka manta am on fluid...?

ta fada tana Kai water melon din bakinsa d

Nan Take ya wangale Baki ta sa Mai,ya tauna Yana murmushi, Haka tayi ta bashi yana amsa, mamaki ya kamasa da ta duba plate ttaga tass ya shanye fruits ɗin gabaki ɗaya, ya ɗauke plates ɗin ya maidasu kan drawer, tashi yayi daga kan Kujerar dake fuskantar Ta, ya zauna a gefen lallausar katifan da take kwance.

Shuru Wajen ya dauka for some minutes kamin ya katse Shurun da faɗin

"Please Wifey ku hakura kubar wahalar da kanku, daukan fansa Ba naku bane kiniji?"

Banza tayi Masa Ta kauda Kai fuska a haɗe

"Bakisan Justice Hamza ba, shiyasa Kike tunanin Zaki iya nasara akansa, ya wuce duk yanda kike Tunani, kinyi tunanin lalata masa kidney da kikayi shi zai tsorata Shi?, Tho inaa a ranar da kika lalata Mai kidney washe Gari aka Chanza masa Wani Kuma Har yanzu baisan kinyi ba, ya daiga Rubutunki a kirjinsa, "

Fuska ta sake tsukewa matuƙa, taƙi kuma cewa komai sai harar gefen ido data ballama masa ya wani tsareta da idanu ina ruwanshi da Fansar da take Shirin ɗauka?

“Ina saurarenki ..,.,Ya kamata kuyi wa kanku karatun Ta Natsu ku Sani A wannan Ƙasar tamu in an cuceka babu Abinda zaka iya ”.
Nan ma ƙin cewa komai tai,ta ɗago sosai ta kalleshi har suka haɗa ido. Saurin kauda nata tayi da zamewa ta kwanta tana son maida hawayen dake ƙoƙarin zubo mata.

Saleem Ya girgiza Kai watou Maryam Akwai Taurin Kai,amma zaiyi duk iya ƙoƙarinsa Wajen Ganin ta bar Tunanin Nan Na daukan fansa,Don rayuwar su tana Cikin haatsari.


*SUREEY*
Aeesh tayi ƙoƙari matuƙa Wajen shawo hankalin Yar Uwar ta ,ta fara Kiran Ammie a waya suna gaisawa har yanzu Bata Wani saki jiki Da Ita ba, in tana waya da Ammie sai ta rinka Jin Ranta yina ɓaco, yanzun ma dawowan Ta kenan daga gidan, Ranta a ɓace

Fitar mama kenan taje duba Maryam a asibiti, baba Kuma ya Tafi aiki su saleemah sun Tafi makaranta.

Ta iske zeeyk Zaune a Garden shi Kadai Newspaper ne a hannunsa yanaa duddubawa, Zama tayi Tana Kirkiro Murmushi a saman Fuskar Ta

"Baby na duba ciki Ban ganka ba, Ashe kana Nan?, wa ya Fito Da kak?"

Rufe jaridar yayi Yana Kallon Surrey, ƙuri tayi masa da Manyan idanunta da suka kumbura, hakan ya tabbatar masa Da tasha kuka Sosai ada kafin ta dawo Nigeria a kulllun burinta shine tazo Nigeria ta ga mahaifiyar ta, Har hotonta ta taɓa sa ya ɗauko mata a ɓoye, Amma ya rasa dalilin Da Yasa daga dawowan ta ta tsane mahaifiyar ta, bata So ayi maganarta, idan Taji muryarta kuwa ranar wuni zatayi tana kuka, hannunsa ya miƙa ya shafi fuskarta tare da jan hancinta, ba tare da yace komai ba , rau rau tayi dan idanunta tana ƙoƙarin maida hawayenta, muryarta na rawa sosai tace

"UK zani...I miss my dad"
shiru yyi mata yana kallon bakinta dake motsawa ganin yyi shiru yasa ta ƙara cewa

"Zamu Tafi tareda Kai mu bar masu boring country ɗinsu ko"

Ta sake faɗi tana Kallonsa da jiƙaƙƙun idanunta, Magana takeyi tsakaninta da Allah Hawaye na taruwa a idanunta, hannunsa na hagu Yasa ya jawota,ta faɗo jikinsa ya manna mata lightly kiss a forehead nata yana tallafo haɓatar da hannunsa ɗaya Don ɗayan Sam bata aiki, fuskarsa manne a nata yace

"Ya hanya"

ya faɗa clamly Cikin muryarsa da bata fita sosai, yana lashe hawayen dake bin fuskarta, kwaɓe fuska tayi tare da sakar masa kuka sossi, kanta ya kwantar da ƙirjinsa yana patting bayanta yana jin yanda take rera masa kukan, murya can ƙasa yace

"Hayateey Mene?"
Muryarta har rawa yake tace

"Ni Bana Son ƙasar nan, ni ka mayar dani bana son su Ka maidani"

gira ya ɗaga mata kafin ya langwaɓar da kansa yana shafa fuskarta da laɓɓanta , Cikin sigar rarrrashi yace

"Ok then, stop crying.."

da sauri ta Sa hannu ta goge hawayenta tace

"To ka tashi muje"

Idanunsa ya lumshe kaɗan kafin ya buɗe a kanta yace

"Wat in mutu a hanya?, Mu jira Yan Gidan su dawo.." .

Waro ido tayi, sai Kuma takai mishi naushi a ƙirji

"Ni dai Ka daina zancen Mutuwa Bazaka mutu ba"

Lumshe idanunsa yayi Yana jin yanda take dukan ƙirjinsa da iya ƙarfinta.

"Surayyyah...."

Ya kira sunanta Cikin Wani muryar da bata taɓa jinsa dashi ba, Tunda take bata taɓa jin ya kira sunanta Kai tsaye ba Sai yanzu.

Chak hawayen dake bin fuskarta suka kafe Ta dubeshi da jajayen idanunta, ya janye nashi idon Yana Maidasu kan Furannin da iska ke tsalle dasu, a Hankali ya sa hannu ya maidota jikinsh, ya manna kanta a kirjinsa Yana Sauke gajeren Ajiyan Zuciya.

"Baby Ina so in Gaya Miki Wani abu...Ko bayan Raina Ki Sashi a zuciyarki Kuma kiyi amfani dashi"

Shuru tayi hakan ya bashi damar cigabawa

"Rayuwa Da Wanda kake so Bashi ne ƙurewar farin Ciki ba, kkalaman Soyayya daga Bakin masoyi baya taɓa zama ƙurewar farin Ciki, Ƙurewar farinciki shi ne, Annabi Muhammad (SAW) Ya kalleka Ya ce; wane ɗan gidan wane (Ya ambaceka da sunan mahaifinka). *Kai kuma ka ce; Ya Rasulallah! Ta ya ya ka san sunana?* Sai Ma'aiki Ya ce; *sanadiyyar Salatin da kake yi mini* Baby...inaso Ko bayan Raina Ki yawaita salatin Annabi (S.A.W) aduk Lokacin da kikaji kewana"

Zuwa wannan Lokacin kuwa gaban Rigansa gabaki ɗaya ya jiƙesharkaf da hawayenta, Cikin Kuka sosai har muryarta na dishewa tace

"Nide Ka daina bana so, Bazaka mutu ba, tare zmu mutu"

Ɗago Fuskar Ta yayi, ya kalli Cikin idanunta da Sukayi sharkaf da Hawaye

"Ki daina kuka Matata, Itafa mutuwan nan Dole ce, ni dake da Bintou Mai rubutu Da Masu karatu duk Basu da masaniya akan Ranar Da zamu mutu, Wani yanzunnan aka haifeshi Kuma Yanzun nan zai mutu, Wani yayi Shekara ɗari amma bai mutu ba, ni kaina da nake miki wannan bayanin ban Sani ba, Ko kece Zaki rigani Mutuwa"

Sosai Kukanta ya ƙaru, maganganunsa na Shiga Har Cikin jinin jikinta, tsikar jikinta sai tashi take gabanta na faɗuwa, Wani iri iri takeji sosai ,kaman Mutuwa zatayi.

Murmushi ya sakar mata Fuskar nan tasa ya kara wani haske da annuri na Musamman Sai ya ƙara kyau sosai Calmly yace ta maidsshi Ciki, Jikinta na rawa ta Tura keken Ta kaishi bedroom ɗinsu, ta taimaka Masa ya rage rigar dake jikinsa Sannan Ta taimaka Masa ya kwanta ,Ta haye Gadon ta kwantar da kanta a ƙirjinsa Tana Sauke numfashi a Hankali.

Shafa kanta yyi,ganin duk a tsorace take

"Baby bacci zakiyi?"

Kai ta gyada Masa, ya gyara kwanciyan Ta a saman ƙirjinsa, Cikin sanyi Yace


"Baby kafin bacci ya daukeki... Ina so na sake tunasar dake Mai bacci ba ya sanin ya yi mafarki sai ya farka, hakazalika wanda ya shagala da duniya ba ya sanin ya yi asara sai ya mutu"

Kuka ta fashe dashi

"Ni dai Ka daina"

Murmushi yyi

"Baby Kuka kikeyi...?, Nima zakisa nayi Kuka"

"Nidai Ka daina ya isa Haka"

Girgiza kansa yayi yace

"Ko kaɗan bakida da masaniya a kan rigar da kike sanye da ita a halin yanzu, shin kece zaki cireta ko kuwa masu wankan gawa ne zasu cire maki? Kinga Dole Muna sa Mutuwa a lissafin mu"

Sai yayi shuru, Hawaye suka Sauko masa

"Ko kaɗan ita rayuwa ba ta da tabbas, mutuwa tana iya zuwa mana a koda yaushe; ka shirya ko baka shirya b...,"

Maganar ta Maƙale sakamakon Saukar lips dinta da yaji a saman nasa, daga nan ta birkita shi da wasanni ,Cikin ƙankanin lokaci Hankulan su ya Gushe suka zarce duniyan Ma'aurata, sun jima sosai kafin Su tsahirta ba don waninsu ya gaji ba, sai Don zazzaɓin da ya Rufe Surrey a Lokaci ɗaya, bata taɓa jin daɗin mijinta Irin na yau ba, jinshi tayi kaman mai Cikakkiyar lafiya don saida Hankalin Ta ya Dawo Ta gane Ashe he's paralyzed Da taimakonta ta kaishi Bathroom, Ta taimaka Masa ya Shiga bahon wanka, da kansa yayi wankan saboda sosai zazzaɓi ke neman kwantar da ita, Cikin ƙarfin Hali take yin komai,ta dawo dashi ɗaki ,tayi Masa Clipping oximeter a Yatsar sa, Musamman Maryam tasa aka kawo mata don Ya rinƙa alarming ɗinta akan Pulse rate dinsa, so tari haka zai kwanta, Chan dare saidai suji nunfashin sa na Sama.

Kanta ta aza a ƙirjinsa bayan ta kunna na'urar, Nan take bacci yayi awon gaba da ita.

3:37 Taji Kaman Yana tashinta yana Cewa " _baby tashi kiyi sallah, Lokacin sallah yayi,"_ a Hankali ta ware idanunta akansa Yana Kwance bacci yakeyi Kuma Babu alamar ya tashi yayi mata Magana, Hakan Yasa Ta maida kanta ta kifashi a saman ƙirjinsa.

Difff taji,babu bugun Zuciya, ƙirjinsa bata sama da ƙasa alamar babu Nunfashi, idanunta ta ɗaga ta dube na'uar da ta jona Masa, taga layin ya miƙe sambal kaman Titin zaria zuwa kano.

Ta kasa gasgata Abinda zuciyarta ke ƙoƙarin raya mata
" Baby Ka Tasheni..meyasa Ka koma?, Ka tashi"

shiru taji bai motsa ba
Jijjigashi tayi, bai motsa ba sai ma Wani nauyin da ya ƙara, ta sa kanta akirjinta taji baya motsi,

" innalilahi wainna ilaihi rajiun"

jan Shi tayi da karfi ta rungume Shi Tana

"Baby wake up....wake up please Ka tashi"

Jagwab yyi baya ,hannayen sa suka saki,arude ta tashi ta debo ruwa tazo ta yayyafa masa tana salati a gigice amma zeeyk bai motsa ba.

Dukan shi ta farayi a ƙirji tana kuka

"Baby Stop it Bana Son Irin wasan nan"

Ta sa kanta a kirjinshi taji shiru, still bata yarda ba, tasa hannunta awuyansa nanma shiru, idonshi da ta bude ya kafe.

Dai dai Lokacin baba ya Dawo, Yana Shirin Parka motarsa ya ganta ta fito a gigice tana Kuka


"Baba Kazo,....kazo Ka gani....kazo....b..b..."

Kasa Magana tayi, Hankalin Baba a tashe y bi bayan ta, Kallo ɗaya yayi Masa ya gane Zeeyk ya rigamu Gidan Gaskiya.


A gigice ya dauke shiya fito ya saka shi a mota basu nufi ko ina ba sai hospital mafi kusa atare dasu, suka shigar da sai dai ko minti biyar basuyi ba suka fito.

likitan yafito yana basu hakuri,damko shi sureey tayi da karfi idonta jajur ta ce

" me ya sameshi? Kar kace min ya rasu"

ya girgiza kai a kasalance ya dube Baba yace

" kunsan asali yana da cancerous brain tumor , he has the history of brain surgery And its fortunate yanzu ya rasu of malignant brain tumor, irin condition ɗinshi masu shi basua tsawon Rai, Allah Kadai Yasan Abinda ya gani Yasa ya rayu zuwa yau, Rayuwar su a kirge take, now he's gone "

a hankali ta sulale jikinta tayi kasa ta rasa me zatayi kuka zatayi Ko Hawaye , tunda take bata taba ganin tashin hankali tsantsa irin na yau ba, Maryam ce tashigo da gudu mama na biye abayanta dama baba ya kirasu, Kuma a asibitin Aka kwantar da maryam, ganin yadda Surrey take suka gigice, Yasa suka rude idon maryam yayi jajur ya kafe tun kan a Gaya mata zuciyarta ta riga ta sanar da ita, kanta ya daina aiki balle tayi tunanin wani abu, haka ta shiga Rarraba idanu tasa hannu ta ja sureey tayi gefe, ta Shiga dakin tana zare ido daidai lokacin da nurses suka rufe masa Fuska da farar kyalle.

kasa motsi tayi daga wurin sai ga Saleem ya faɗo dakin, wani Irin bugawa zuciyarta keyi duhu ya mamaye ganinta, nan take ta faɗi kasa a sume, tashin Hankali wanda ba'a SA masa rana ,tarota Saleem yayi Amma kafin ya Isa gareta har ta Kai ƙasa, ta faɗi kanta ya bugu da tiles sai jini, hankalinsa a tashe ya Kira likita aka maidata kan gadonta.

Mika musu gawar akayi suka koma gida ,gidan yacika makil harda su Sadeeq dasu Ashman, Ashraf, Abba, Naseer, Goggo ,makota da dai sauran mutane kowa ya hallaru an taru Aeesh ce bata zo ba, tsoro takeji, Gidan rasuwa tsoro yake Bata,

Chan Sai ga baba ya shigo ya tsuguna agaban gawan shi baiyi magana ba shi bai tashiba Kuka yakeyi sosai kaman karamin yaro Abin yaba Mutane mamaki ,amininshi Alhaji Sabo ya taɓa Shi Da mamaki Yake cewa

"Alhaji ina dauriyanka? ko da matarka ta rasu bakayi kuka ba don Allah kayi hakuri, kaga idon mutane akanka yake"

yana sheshekan kuka sosai yace

"Allah bai Nufeni da haihuwar da namiji ba, sai gashi Rana tsaka ya Aiko min, Zaid Cikin rayuwata ,tun daga ranar na daina kukan rashin haihuwan'da namiji ,Amma yau gashi a gabana baya motsi"

Jikin kowa yayi sanyi barin ma ni dana dawo abun kallo, jikin kowa yayi sanyi idon baba kaman zai fadi don yaji tsabar hawaye,

Cikin takaitaccen lokaci akayi masa wanka Sureey sai kuka take a kaita tayi Masa addu'a, a kaita suyi bankwana, har zuwa Lokacin Maryam bata san inda kanta yk ba.

ahankali sureey ta zauna Gawan tana kallonshi yayi fari sai ya kara kyau sosai, fuskan nan har alamun murmushi yakeyi, jikinta na bari kirjina yana bugawa,sai Hawaye Bakin ta na rawa Ta kasa yin addu'a, Da kyar aka ɗauketa daga Wajen , Aka kaishi gidansa na Gaskiya .




_Kullu nafsin za iqatul maut_
*Kullu Nafsin Za'ikatul Maut💔😭*
*_In ka tuna da mutuwa,_*

yanda za'ayima wanka, a sallace ka, a kaika makwancinka na gaskiya, a barka daga kai sai ayyukan bima kyakkawa ko akasinta!
sai kaji duk wani isarka,takamarka,jiji da kanka ka nemesu ka rasa!!!

*Allah ka sa muyi kyakkawan karshe, ka jiqan magabatanmu, mu kuma in tamu tazo kasa mu cika da kalmar shahadaa!, Kuma Aljanna ta Zama makoman mu*

Allah ya jikan ZEEYK dama sauran Musulman gabaki ɗaya wadanda suka rigamu Gidan gaskiya.


Ameen

Bintou.....😢

Nayi gabas😢🐔🐤🐤
*WUƘA A ZUCIYA*
_(BLEEDING HEARTS)_



*063*




Har dare Amma maryam bata farka ba sai addu'a ake mata, dare nayi kowa ya kama gabansa, na nesa ne kawai suka zauna ,Tuni Labarin Rasuwar Zeeyk y karade ko Ina, Bloggers dama suna kan Yaɗa wancan ne,sai ga wani, Tuni duniya ta dauka Babban Ɗan *_S.S Bamalli_* ya rasu bayan an Kama Mahaifin shi da laifin kisan mahaifiyar Sa adaidai Lokacin da ake tsaka da ɗaurin Auren kanwarsa, Tuni Yan media Aka sauya salon Labari duk inda Kika gifta a media Hotunan ZEEYK photographer ne ke yawo _Dama Media ta gaji Hakan a Lokacin da kake Raye Babu Wanda Yasan Ka, babu wnda ya damu da Rayuwarka, wasu ma Ko sun sanka Basu damu da Rayuwarka ba koda Abin alheri ne ya faru dakai babu mai tayaka yadawa, Amma Idan Ka Mutu sukaga An fara posting Hotunan Ka, Sai Suma su daura ba don mutuwan Ka ya tabasu ba, sai Kawai don Su Shiga sahun Trends su Samu likers and reposters_ *Allah Yasa mu dace Ameeeen*

Kwanan ta daya a asibiti ta farka amma Har yanzu jiki yaki sauki sai addua ,mama ce da saleemah zaune da ita a Amenity inda aka Kwantar da ita, Ayyan yana tareda Baaba, Dr Sabo ya buɗe ƙofar ya shigo da sallama a bakinshi , karasowa yayi yana Duban Maryam dake kokarin bude nauyayyun idanunta

"Sannnu sister....ya jikin?"

"Da Sauki dai zamuce, Amma Ta farka dazu sai ta sake Suma, Amma ta sake farkawa da Kuka nayita Rarrashinta har ta Koma Bacci"

A sanyaye yake Duban Maryam dake motsawa a Hankali Yace

"Sannu, Allah ya ƙara Lafiya"
prescription sheet ya dauko ya rubuta mata magani ,yabama mama takardar Sannan Ya fice

Ahankali taɗan buɗe idanunta wanda suka ƙanƙance saboda tsabar kuka, da wani irin firgici haɗi da tsananin tsoro ta tashi tana kame jikinta, ɗan lumshe idanunta tayi, take mafarkin da tayi yanzun yadawo cikin tunaninta, Mafarkin yayanta tayi as usual.

A Hankali tasake buɗe idanunta ta sauke su akan mama hawaye suka silalo mata, brain dinta ya fara recalling Abinda take kokarin Karyatawa

_yanzu shikenan Zeeyk ya Tafi?, Batada kowa a duniyar nan Sai shi, Yanzu shi kenan Batada kowa a duniyar Nan?, Jininta gabaki ɗaya Babu Su?, Ita Kadai ta rage a duniyar ta!_

Kuka takeyi sosai harda shessheka, Mama ta Zuba mata ido batace komai ba, atleast atimes it's okay to cry

Miƙewa tsaye mama tayi tare da share hawayen dake kan fuskarta, ta kamo hannunta, tare da miƙar da ita, ta zauna itama gaba ɗaya zuciyarta ta gama karyewa.
Cikin halin tausayawa tace.

"Kuka bashida amfani, sannan kuma baya magance damuwa, ki riƙa maimaita kalmar Innalillahi wa'inna ilaihirraju'un, insha Allah zakiji sauƙi acikin zuciyarki, Allah ya jiƙan Zaid."

Cikin sheshsheƙan kuka ta jinjina kanta, ahankali ta soma motsa laɓɓanta wanda sukayi mata nauyi, so take ta furta kalman Innalillahi winnailayhirrajiun, amma harshenta rawa yake, kamar yanda duka ilahirin jikinta ke rawa.

Ganin haka ne yasa Mama ta soma faɗin kalman abakinta, take kuwa ta amsa, ta jingina kanta da cinyar mama tana amsawa da

'Innalillahi wa'inna ilaihirraju'un."

tana magananne cikin matsanancin kuka da rawan murya.
sai kuma ta fashe da kuka ,mamá ta girgiza Kai Itama ji take Kaman Ta Dora hannu aka tayi ta kukan.

Turo kofar akayi, Saleem ya shigo hannunsa ɗauke da ledoji, zama yayi saman Kujera yana kallon Su, da kyar ya iya buɗe baki yace

"Sannu mama"

Saboda bai saba ba, gaisuwa wahala yake mashi, itama amsawa tayi da sannu.

Saleem yyi ƙasa da murya yace

"Ta sake Suman ne?"

ya faɗi hakan yana kallon maryam dake faman Zubarda Hawaye.

Mama ta Girgiza Kai
"Yanzu ta farka"

"Sannu kinji"

Ya faɗa yana dubanta kaman an Tilasta Masa, Bata ma san yanayi Ba, Hankalinta gabaki ɗaya baya jikinta.


Taɓe baki Saleem yana jan numfashi ya jima a haka kafin ya ɗago kansa ya kalli maryam, a Hankali ya miƙe tsaye har zuwa inda Maryam take kwance, ya zauna a gefen gadon, ya dube cikin idanunta dake tsiyayar hawaye, murya a sanyaye yace.

"Mutuwa kake ma Kuka Wifey?,"

Kamo hannunta yayi yana kallon yanda take kukan a hankali amma duk ilahirin jikinta rawa na yake Cikin sanyi ya ambaci sunanta
"Maryam..."
Ta dago rinannun idanunta ta Zuba Masa
"You need To pick up a piece and move on with ur life, stop feeling sorry for ur self, Zeeyk ya riga ya rasu, Kuka bazai dawo dashi ba, if I tell you my own personal Story, Zaki godewa Allah akan kaddarar da ya faru dake"

Yayi humming Sannan ya cigaba

"The world of vanity , nida kike gani banida Kowa a rayuwata sai Mahaifi na, Relationship Dina da brothers duna kman wutar lartarki ne, yau Naji dadinsu Gobe sujani kaman Shocking,naga jarabawa iri iri,naga Rayuwa , Mutuwa ce Kawai bangani da idanuna ba,but who am I to question God?, Waye ubana?,duk da haka I still Pray for 5× every day, with nafilah and istigfar saboda nasan Allah ba mugun bawansa bane, mune mugayen kanmu, ki godewa Allah kina Raye kinada Lokacin da zakiyi serving for ur Destiny"


Shuru yayi Yana Sauraron Shesshekanta har tsakiyan Kansa, a Hankali ya kira sunanta

"Mustang..."
Bata Amsa ba, sai Ma Cusa kanta da ta sakeyi a cinyar Mama, murza hannayenta tayi yariqe sannan cikin sigar rarrashi yace

"Maryam....death is not the greatest Loss in life, pick up the pieces and move on with ur life, Go back to the Old You, the life is short utilize urs and Serve till the end"
Cikin sanyi yace
" kiyi hqr, Allah baya dorawa bawa abinda baya iyawa, ki kasance mai Neman juriya da godiya a wajen Allah kuma ki kasance mai hqr, idan kinadashi ada ki Dora akai,duniyar nan ba wajen zama bace Ni dake da kowa ma Muna shirin barinta, ki daina Kuka kinji"

Maryam ta gyada masa kai, kanta duke tana hawaye.
"Ya isa haka Mero, kiyi hqr kinji? Kowa haka in lokacinshi yayi zai tafi, kiyi hqr"
Mama Tafada tana kokarin miqar daita tsaye,
Saleem ya dubi Saleemah ,Yace ta dauko ledar da ya shigo dashi, tashi tayi ta dauko Itama jikinta duk yayi sanyi, ya Mika wa mama Ledojin.

"Mama Ga Abinci na siyo maku, naga tun jiya babu Abinda Kuka ci"

mama ta ɗan ɗago marym ,cikin kulawa tace.
"Ki Tashi Ki sa abu a cikinki kinji, kada yunwa ta illata ki"
Cikin kuka ta girgiza kanta, don batajin akwai wani abu aduniya da take buƙata, batajin cewa zata iya sanya wani abu abakinta yayi mata daɗi, ji take Ina ma mutuwan Nan ta dawo ta dauke ta itama, ta Tafi ta huta da Wannan rayuwar, Yanzu shikenan Batada kowa mahaifiyar ta tarasu, mahaifinta na gidan yari, kannenta sun Rasu yayanta ma ya bisu, Dangin mahaifinta sun gujeta
Cikin muryarta dake rawa haɗi da sarƙewa tace.
" bazan iya shaba, banason komai, bana sha'awar komai"
Hawayene suka kuma cika idanun Mama, yanda Maryam tayi maganar gabaki ɗaya ya tafi da dauriyan ta,kukan da Takeji ya taso, amma saita shanye su, sam bata bari sun fito kowa ya gani ba, sake tallafo Maryam tayi, cikin sanyi, da lalllami tace.

" kiyi haƙuri kisha ko kaɗanne, kinga shima zai taimaka sosai wajen ɗan baki ƙarfin jiki, buɗe baki kisha ko kurɓi biyune, yafi ace bakici komai ba."
Mama ta ƙare maganar cikin kulawa, murya na rawa kaman zatayi kuka ,kallonta Saleem Yakeyi jikinsa yayi Sanyi sosai.

Haƙiƙa mama nada matuƙar daraja da ƙima a idanunta, saboda haka batajin akowani yanayi take ciki zata iya yi mata musu, cikin rashin kwarin jiki ta buɗe balin ganin ta buɗe baki ne yasa mama da kanta ta shiga bata tea ɗin abaki, kurɓan farko da tayi haka taji tea ɗin kaman ta kirbi ruwan shuwaka, sam babu wani ɗanɗano acikinsa, wanda kuma ta tabbatar cewa rashin ɗanɗanon daga bakinta ne, bawai daga tea ɗin ba, ga Saleem ya Wani kafeta da idanunsa kaman zai hadiye ta, hakan yasa Ta takure sosai, cikin rashin kwarin jiki ta galla masa harara ta gefen ido ,ya Kauda kai Yana Murmushin Yaƙe, kurɓa biyu kadai tayiwa shayin ta kauda kanta gefe tana Ture kofin, cikin sanyin murya hawaye na zuba tace
"Mama na ƙoshi".
Gyada mata kai Mama tayi, ita kuma zamewa tayi ta kwanta akan gadon tare da jawo blanket ta rufu har Fuska, cikin sanyin murya take maimaita kalaman
"Innalillahi wa'inna Ilaihirraju'un."
Cikin sheshsheƙan kuka, hawayen da Maama ke kokarin boyewa ne suka zubo,wani wahalallen bacci ya sake ɗauketa , wanda dagani kasan na dole ne, don ko acikin bacci'n sheshsheƙan kuka kawai take saki.

Jigum haka mama da Saleem suka zauna, tare da sakata gaba suna kallo, sosai sukejin tausayinta barin ma Saleem da yakeji kaman Yayi mata kuka, lokaci ɗaya gaba ɗaya ta rame ta fita hayyacinta, idanunta sun kumbura kamar wanda ta shekara guda tana kuka, bacci take yi, amma hawaye ne kebin gefen fuskarta, sai faman sakin sheshsheƙa take.

Duban mama yayi

"Ina takardar da Dr ya rubuta?"

Miƙa masa Tayi ya fice Yna addu'ar Allah ya sauwake.
Kai tsaye Saleem gida ya nufa kasancewar dare yayi, tare motarsa da motoci Baffa da Abdul sukai parking a parking lot na gidan, Zama Saleem yyi cikin motarsa yana mai cire Rigar suit din jikinsa, Abdul ne ya fara buɗe motarsa ya fito hannunsa riƙe da briefcase, yana sanye da suit ɗinsa baƙaƙe, black chocolate skin ɗinsa na haske, Baffa shima ya buɗe motarsa ya fito kallo ɗaya zakai masa kasan cewa he's serious sick Hankalinsa a tashe yake babu kwanciyar hankali a tattare dashi, kallon juna sukai Baffa da dansa barr Abdul, Baffa yace
"Abdul wancan kaman Saleem"
Kafin Abdul yyi magana Saleem ya fito daga motarsa cikin cikin bakaken suits ɗinsa, a gajiye Yna tafe kaman an tilasta sa, yana gyara zaman Rigar Suit dinsa a kafadarsa , batareda ya kallesu ba yyi gaba abinsa, Abdool yaja tsaki yayi gaba Abinsa
Baffa yabi bayansa yana kiran
"Saleem" saleem dai

Please Login or Register in order to submit comment