Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Tareda Ashman.

Hankalin a matuƙar tashe ya shiga Motarsa yaja ya Fice da mugun gudu harga Allah sonta yake da gaskiya ba yaudaraba, Allah ne ya jarabcesa da sonta batare daya shiryama hakanba, yanda take ,itace mace ta farko da ya fara so a rayuwarsa Bazai iya rabuwa da ita ba, Zai iya batawa da kowa ta sanadinta , akanta zai Iya aikata komai.

Tsabar tashin Hankalin da yake ciki sai zufa yake kwararwa dukda ac dake aiki a motar, jikinsa wata irin muguwar rawa yake da ɗaukar azababben zafi lokaci ɗaya, Kansa ya Dauki wani Irin zafi sosai, Tsoronsa hukuncin Da Ashman Zai yanke akansu yasan Izuwa yanzu Labari ya iskeshi Kuma tabbas Matakin Da zai Dauka bazaiyi kyau ba, duk addu'ar da tazomasa a baki yi yake da taimakon ubangiji ya Isa Gidan Su Reey Ga mamakin sa Sai Mai gadi yace basu dawo ba, Duk inda Yake Tunanin zai gansu cikin Daren Yaje Amma bai gansu ba, hakan ya sa hankalinsa Ya dada tashi.

Bashi ya dawo gida ba sai Shabiyu da rabi na dare .

Koda ya dawo yaga Motar Ashman, Amma tsoro da kunyar Abinda ya aikata ya Hanashi Tunkarar sa, karo na farko a rayuwarsa Da yaji tsoro da Shakkar wani,Wanin Ma Ashman da ya raina..

*Aeesh*

Tunda Ya fita ya barta a dakin ta Zabga Uban tagumi,Sai yanzu hawayen da ta kasayi Tun ɗazu ya zo mata .

Kwankwasa Kofan da akayi ne yasata yi saurin share hawayenta, Da sallama Ashman ya bude kofar fuskar sa Manne da wani Sihirtaccen Murmushin da shi kansa Baisan Yana yiba.

Kauda kai tayi

_yayana dole kayi Murmushi ,Ka riga ka samu farin cikin Ranka ka auri wacce kake so_

yana sanye da black straight trouser , sai Farar Men Vest da ya bayyana Faffadar kirjinsa, dakin sai wani irin kamshin mayen turare mai dadi yake.

"Ihkty Kuka kikeyi?"

Ya fada yana zama Kusa Da ita Tareda kamo hanayenta.

Lumshe Idanunta tayi ta girgiza masa Kai hawaye na cigaba da Gangarowa

"Eh mana Kuka Kikeyi?, ba nace ki kwantar da hankalinki ba"

Sake Tamke Idanunta Tayi sosai Hawaye Na Hawaye na zarya a Idanunta.

"A'a ba kuka nakeyi ba"

Ta fada muryanta na cracking

Jikinsa ne yayi wani irin mugun sanyi, Tausayinta ya lulluɓeshi ,hannu yasa Yana share mata hawaye

"Ki daina Kuka kinji, Allah yana sane Dake In Allah ya yarda Hakan Shine mafi Alheri a gareki, Ki Daina Kuka Kinji"

Buɗe Idanunta tayi Hawaye suka sake Zubowa ta cije Lips dinta tana shessheƙa

"Ba kuka nakeyi Ba Ahky, Ba kuka nakeyi ba''

Ta ƙarashe Maganar cikin Shessheƙa sosai, Ta fada Jikinsa Tana cigaba da rera Kukan mai ban tausayi.

Wani irin Ajiyan zuciya ya sauke ,hannunsa yasa yana tapping bayanta k'ad'an-k'ad'an, Kuka Sosai Takeyi bakinsa ya d'ora saitin Kunnenta yace

"Don Saleem ya sakeki bashi ne Karshen rayuwar ba, I know things falls arround but Don't give up...!, You're Folding in!, you are caving in!, I know u are cold, You Are weak and You feel like this is the End, You have the choice to Either Give up or create your own happiness "

Shuru ya danyi Yana Sauraron Shessheƙar ta dake cigaba da taɓa zuciyarsa .

"Give Up or Get UP!, Don't Give up!,stay in it ,stay focused Don't betray ur happiness Manta da wanda bai damu dake ba, Manta da wanda Baisan Darajar ki ba, kar ki Zubar da Hawayen ki akan Wanda Baisan Darajar su ba, ya Sakeki Try another man Again and again!, You just take one step at a time!, Nasan Ba Abu ne mai sauƙi ba!, it's hard but It's worth fighting!, It's worth believing!, It's worth fighting Ur own Dignity!, Baby na Never Give up"

Shafo bayanta yayi a hankali, Ta sake Cusa kanta a Ƙirjinsa Shessheƙanta na raguwa, Cije Lips dinsa Yayi Ya cigaba da cewa

"Ina Son Rana ,Amma Abubuwa Basua Rayuwa saboda Rana dole muna Buƙatar Ruwa 😭, and you Gotta stop looking at Rain In ur life as Something bad!, Abubuwa masu Kyau basu Zuwa from greatest memories, Abubuwa Masu Kyau Sukan zo ne from Defeat memories, Babu Wanda rayuwa bata garawa, Ya kamata Ki manta Da komai but he need to know that He Broke u!, He think he Got u twisted ,You are not a phenomenally skilled but a Phenomenally Willed you'll Not Give up , You I'll not surrender Kar Kiyi Kuka stop crying, stay Encourage, Keep ur head up ,Stick ur chest out , Continue work with pride Kowa da nasa Jarabawar,Damuwa kesa a fahimci Damuwar ki "

Shuru yayi ,ya Furzar da Numfashi daga bakinsa yana Jin Saukar Numfashinta a hankali hakan ne ya tabbatar masa Da cewa tabbas Zantukansa Na matuƙar tasiri a zuciyarsa.

"I know it's Not Gonna be Easy , But nasan U have what it takes ,a rayuwa akwai bakin Ciki, Amma Bakinciki baya zuwa domin Ya zauna, bakin Ciki na zuwa ne domin Ya wuce,Karki dauka Sakin ki da yayi Shine zai zama Sanadiyyar Bakin ciki a rayuwar ki, Ki dauka Sakin ne zai sadaki da Farin Cikin Rayuwar ki !, Kar ki manta dare Duhu ne Amma Dare shine new beginning of another day , Don Saleem Ya sake ki A Daren Aurenki bashi zai hanaki Samun Miji na gari iri na ba"

ya k'are maganar da sumbatar cikin kunnenta

Babu shiri ta k'ank'amesa dan har cikin kwalwar kanta taji sumbatar Ga Sanyin da Jikinta yayi sanadiyyar Tasirin Da Kalamansa Sukayi a Zuciyarta.

Kaɗan ya buga bayanta sannan ya raba ta da jikinsa yana Duban face dinta Idanunta Sunyi jazir kaman Garwashin Wuta, hannu yasa yaja kumatunta

"Good news ,Ki Tambaye Ni Menene?"

Murmushi tayi

yace

"Ammie ta farka,But right now suna Chan Waterloo Canada!"

Zaro Ido Tayi

"Yaushe suka tafi?,ita Dawa?, Meyasa Ban sani ba?"

"Tun da safe suka tafi su da SADEEQ , HABEEB ma ya bisu su Inna Yathai da Goggo ma duk sun tafi , Zuwa Next week Su Goggo Zasu dawo"

Hawaye ne tajiYa taru a Idanunta

"Meyasa Yaya SADEEQ zai min haka?, Meyasa Zasu tafi Batareda na sani ba?, me yasa ?"

Ta fada Tana Kokarin Haɗiye Hawayen ta dake ƙoƙarin Zubowa.

A hankali ya hure Fuskar ta da iskan Bakinshi

"Maida Hawayen nan!, this is not Time for crying"

Ya fada yana kai maida kansa Daidai wuyanta,Yana cigaba da shaƙar Daddaɗar Ƙamshin Turaren dake Tashi Jikinta

“hasbinallahu wani'imal wakil”

Ta fada a fili, ta k'ank'ame Shi tana rintse idanu da cije lips a kasalance tace .

"Please Stop...bazanyi Kuka ba"

Ɗago kansa Yayi yana Duban Yanayin ta, Wani irin Munafukin Murmushi ya kufce masa, ya fara nasarar sanya mata Feeling Dinsa a Cikin Jikinta, His next plan Will Make her his ❤️ for ever.

''so ko na fita karkiyi Kuka kinji"

Kasa Motsawa tayi,Tunda ya fara magana Take kallon Wet Full bounced Lips ɗinsa ,Sosai Tsikar jikinta ke tashi.

Ƙoƙarin Miƙewa yake yi,Ji yayi ta jawo shi tayi Locking din Lips dinsu waje daya .

Zaro Manyan Idanunsa Yayi yana Receiving The Shock of his life

Jikinsa ya mutu nan take, hannu daya yasa ya tarbota ta baya yasake mannata da Jikinshi yana kissing dinta kamar a mafarki Jikinshi har rawa rawa yake.

Lumshe Idanu Aeesh tayi domin kuwa bata iya misalta yanayin datake ciki, batama cikin hayyacinta ne.

Ashman wani irin yanayi ya tsinci kanshi mara Misaltuwa.

Kissing dinta yake Cikin Wani irin salo a hankali,Shi kanshi yafara fita ahayyacinshi.

Sun dau 5mins a haka Daga shi har Ita jin kansu Sukayi a sama.

Ahankali ya fara cire bakinshi daga nata yana kallon Idanunta dake a Lumshe.

A hankali ta fara ware Idanunta har ta ida Waresu akansa.

Kallon juna suke suna sauke numfashi ahankali tare .

Dukansu sun kasa yarda da abinda yafaru yanzu.

Kallon juna suka cigaba dayi kowa na qoqarin daidaita natsuwan shi.

Abinda Ya faru yanzu ne ya Gifta cikin brain din Aeesh takasa yarda da abinda yafaru yanzu Yanzun Nan

Ja da baya tayi Tana Tamke idanun ta, she can't believe She just kissed him.

Miƙewa Ashman Yayi yana Ƙoƙarin Daidaita natsuwan sa Ya fice a dakin, yana tafe a hankali kaman mai Koyon tafiya, gani yake Kaman a mafarki Uhtyn sa ce tayi kissing Dinsa da kanta , She gave him an Emotional Kiss

Koda ya koma dakin Deejah Har tayi Barci ,Bathroom ya fada Ya sakar ma kansa Ruwan zafi     

Murmushi Ya saki yana tuna kissing moment Dinsu
Haryanzu qirjinshi bai bar Racing ba , Abu ne ya toshe mashi maqoshi .

"Any way You're My wife"
Ya furta a fili.

Ya dade a haka kafin daga Bisani Yayi wanka ya fito ,ya Gudanar Da Sallah Yana mika godiyan sa Godiya ga Allah da ya haramta ma Saleem Auren Aeesh .

Ya dade yana Gudanar da Salloli Har karfe biyu.

Sannan ya kwanta can Kuryar gado,Jefi Jefi yana sakin Wani sanyayyen Murmushi jin kansa yake kaman Wani sabon Ango .....


Bintou.... ✍🏼



*Ya rabbi ka kawo mana ƙarshen waɗanan tashin hankali, ya Allah ka ruɓanya rahamarka da rangwame a garemu, ya Rabbi ka yafe mana kurakuranmu, ya Rabbi kaimana maganin abinda bazamu iyaba harma da wanda zamu iya ɗin, ya rabbi ka taimaki bayinka dake cikin gararin rayuwa da hali na buƙatar agaji, ya rabbi ka kawoma muhallansu zaman lafiya, kasaka kwanciyar hankali a zukatansu suma su sami cigaba da rayuwa a yankunansu kamar kowa, ya rabbi ka kawoma ƙasarmu zaman lafiya baki ɗaya da dukkanin duniyar musulunci, ya rabbi ka bamu ikon cinye jarabawa kasa ta zama rahama a garemu duniya da lahira, Ya Allah ka Shiryi Shuwagabannin Mu, ka jiƙan Mu ka zaba mana Shuwagabanni na Gari* _Pray For Kaduna to Abuja Victim_🙏🙏🙏



Nayi Gabas 🚶🏻‍♀️

26th July
[7/31, 12:03 AM] Bintou: _🫀🗡️ *WUƘA A ZUCIYA*🗡️🫀_
[B l e e d i n g_h e a r r]




*024*


Sosai Takejin Haushin kanta ,Ta guji Wannan Ranar gashi Sai bibiyan ta yake, Saida tasha kukanta sannan tayi wankan tsarki, tarasa me ke sakata biyema Ashman?, da zarar ya Taɓa ta sai taji ta rasa Natsuwarta.

Tasha Kuka sosai Da kyar Ta samu Barci barawo yayi Awon Gaba da ita.

Aranar babu wanda yayi barcin kirki cikinsu, musanmman Aeesh data kusan kwana tana kuka.

Da asuba a kasalance ta tashi ta tsarkake Jikinta Dama Bata sallah, Sai ta kuma komawa bacci sakamakon rashin isashen barci datayi jiya.

Da safe Ya shigo Ya tada ta, Sai Kau da kai Takeyi kunyar sa takeji sosai, baice da ita uffanba  ,Baki ya ta6e yana wani ɗage gira d'aya tamkar Baisan Tanayi ba, ya fice.

Wanka Ta shiga, Bayan yan mintuna tafito ,Tana Dudduba Drawers din dake ɗakin, Cikin Sa'a Kuwa taga akwai kayan Sakawa, Kama daga Atamfofi zuwa Shadda Da Ready made Gowns,

Batareda tayi Dogon Nazari ba, Ta dau Atamfa ta saka,Zama tayi Saman Dressing Mirror tana duban kanta..

har yanzu takasa yarda da abinda yafaru jiya, Har yanzu ta kasa Yarda Da Anyi Auren Har ta fito?, ta kasa yarda Da abinda ta aikata ma Ashman, Yanzu da wane Ido zata dubeshi?.

Duban Mirror take a kasalance jiki a sanyaye,ga Mace iya mace, Ga kyau MashAllah Amma babu kwanciyan hankali tunowa tayi da yanzu Kallon Da za'a Farayi mata a matsayin Bazawara, Tasan Ko ba'a faɗa ba Zuwa iyanzu Labarin Sakinta ya karaɗe Ko'ina.

Wasu zafafan Hawaye ne suka zubo mata

_You I'll not surrender Kar Kiyi Kuka stop crying, stay Encourage, Keep ur head up ,Stick ur chest out , Continue work with pride Kowa da nasa jarabawar,Damuwa kesa a fahimci Damuwar ki_

Kalaman Ashman Suka dawo mata, a hankali tasa hannu ta goge Hawayen ta tana Sakin Murmushin Yaƙe.

Turo ƙofan da akayi ne yasa ta Saurin Ƙarashe Goge Hawayen.

Turo kofar d akayi ne yasa ta Saurin  Daidaita Tsayuwarta.

Ashman shigo, Ƙarasowa Yayi Ya tsaya a bayanta, Tana hangenshi ta Mudubi

Suna hade ido tayi alsaurin Sunkuyar da kai ,Murmushin Gefen baki ya saki, yana karema Face dinta kallo ta Mudubi

Kallo daya yayi mata yagane kukan datayi jiya ba kadan bane saboda yanda idanun suka dan kumbura gashi basu ida washewaba.

Tunda suka hada idanu ta kauda kai a kasalance tace

"Ina Kwana Yaya"

Ta fada a kunyace.

"Lafiya,You Look better now, Ko kefa!"

Shuru tayi masa idontana Cigaba da Kallon ƙasa

"Kinyi Kyau sosai, Amma Amma Rigar Tafi kyau Kasancewar ta Na mata ta"

Saurin daga Kai tayi ta dubeshi Cikin mamaki Dama Kayan Deejah ne?, Suna haɗa ido Ta kauda Kai tana Yatsine Fuska.

"Ke Amarya ce, You Deserve to Look Good, Kamata yayi Adonki ta zarce Ta ko wace irin Mace a yau dinnan"

Yayi maganar yana Dafe kafadunta Biyu da Tafukan Hannayensa.

Sanye Take Cikin Dakakkiyar Atamfa wacce tasha Dinkin Manya,Babu Wani Style a jikin atamfar Amma Launinsa nada Kyau ,Blue and Ash ce atanfar anyi mata Fitted Ɗinkin da ya karbi Jikinta sosai,ɗaya daga Cikin kayan da yasa a Dinko mata ne suci Biki dashi ita da Ƙanwarsa Kawwama iri daya Sai Allah ya nufa bazai bata ba saidai yaga Tasa.

Ajiyan Zuciya ta saki sannan Tasa hannu ta cire nasa Hannun dake Dafe da kafaɗar ta a kasalance ,Kokarin Maida Hannunsa Yayi, ta sake Riƙe shi tana Marairaice Fuska.

Murmushi yayi, ya Zagayo Gabanta, ta bishi da Kallo Gabanta na fa'duwa ,Chain Box ya fiddo cikin Drawer ya ciro sarƙar Sannan Ya Zagayo ta bayanta.

Ɗago kanta tayi tana Dubansa Ta mudubi, a hankali Ya Saka Mata Sarƙar.

"I bought This For my wife, But Since You were here You Deserves it”

Sossai taji Haushin Maganar da Yayi ,Dama tunda ya fara Ambaton Matan sa taji Ya fara bata haushi, gani take kaman Da gangan yayi don ya bata mata don Yaga Batada Miji yanzu.

Yana Kallon Ta ta Mudubi Sai Murmushi yake saki, Sosai Sarƙar tayi mata kyau Ya zauna A Jikinta kaman don Ita akayi.

Hannunta Ya kamo ya miƙar da ita yana cewa

"Muje Muyi Breakfast"

Tare suka Fito, hankali take takawa a stairs din hannunta daya da waya danyen kuma riƙe da nasa.

Dinning Suka Nufa , Inda Komai Yake nan Jere Yayi Ready,Shi Dakansa ya shiga Kitchen ya haɗo Komai ,Domin Kuwa Deejah na chan tana Baccin gajiya .

Dakansa yayi Serving Dinsu a mazubi Daya Kaman Yanda Suka saba ci ada.

Hakan Yasa ta tuno da rayuwarsu ta baya, Shuru tayi tana kallon Abincin ta kasa ci, Shikou ko ajikinsa sai Ci yake, Tana kallon Abincin har ya kusa Gama cinyewa.

Sai a lokacin ta ɗago ta dubeshi

"Yaya Ina matarka?"

Murmushi yayi mata batareda ya bata Amsa ba, ya ida Karkare Potato 🥔 Din da ya rage.

Binshi da kallo tayi Ganin ya Sake Zuba Potato da soyayyen ƙwai ninkin Wanda Ya zuba musu da farko, Ya kuma hada wani sabon Tea Cikin Kofi.

Tana Kallon shi har ya gama haɗawa, Ahankali ya matso Gab da Ita ,hakan Yasa Gabanta faduwa ,tunowa tayi da Abinda Ya faru Jiya da tayi Masa Musu.

Waro idanu tayi cikin Tsoro tace

"Zanci Da kaina"

Dariya ta bashi, Amma sai Ya sake hade girar sama da ta ƙasa

Hannunta har rawa Yakeyi Ta jawo Plate din Zata fara ci , ya Damƙe Hannunta, Tsoro ya kuma Cikata Ko Kallonta Baiyi Ba ya sa Fork ya dauko Soyayyen Irish Ya Kai bakinta, Bata da Option Dole ta buɗe baki ya saka mata.

Murmushi yayi ya sake Dauko wani ya kai bakinta yana faɗin

"Munyi waya da su Ammi ɗazu , ki cinye na kira Miki su"

Janta da Hira ya farayi yana bata a baki, Tun tana Biye masa a kunyace har ta ware ta biye masa, yana tsokanar ya tana dariya,cikin Kankanin lokaci sukayi Kaca kaca da Dining Din, idan Ka ganta bazaka ce itace wacce aka saka Jiya ba Sam bazaka hango damuwa ko kadan Dangane da ita ba , Auren d dama ba so takeyi ba, bata san dalili ba , Amma Aduk Lokacin da Take tare da Ashman duk girman Damuwanta shine ke yaye Mata.

Deejah ce ta fito sanye da Kayan Bacci tana Miƙa , Waya ce riƙe a hannun ta tana kallo Labarin Sakin Da Saleem Yayima Aeesh ne ta kafanta a platform dinsu Cikin Muryar barci take Kwala masa kira

"Baby....!, baby kana Ina?”

Jin Muryar Deejah Yasata Saurin Gyara Nutsuwanta Tana nuna Mshi ita da Ido.

Ko a jikinsa, Tissue ya yago Ya goge Mata gefen Bakinta Da ya Ɓaci da maiƙon msi yana Faɗin

"Baby Ji yanda Kika ɓata Bakin ki"

Hannunsa ta riƙe ta ɗan Harareshi, Daidai alokacin Idon Deejah ya hasko mata su

"What!"


Tafada tana kashe Hasken Phone dinta, jikinta har rawa rawa yake saboda tashin hankali.

A dan Tsorace Aeesh taja Gefe tana kokarin raba jikin ta da nashi, Jawota yayi ya sake manna ta da Jikinsa.

Aikam Deejah bata san Ya akayi ba ,Sai ganinta tayi A gabansu

"Look are you ok? What Are You guys doing? Me kuke yi haka ne? ,Dama Kinsa Naki Angon Ya sake ki ne don Ki dawo ma nawa Mijin? No way!, Aisha Ni nafi karfin Bazawara irin Ki!"

Tafada cikin qaraji, tashin hankali qarara a fuska.

Kalmar Bazawara data ambata ba qaramin dukanshi tayi ba, ada Baiyi niyyar tanka ta ba, Yaso ta Ya barta tayi tayi, in ta gaji tayi shiru da kanta, amma bazai iya zuba ido ana Cin Mutuncin matarsa Yana gani ba, hakan yasa ya dago idanunshi dasuka fara chanza launi shima ya zubamata

"Ni Kuma ban Fi ƙarfin Bazawara Ba, Bazawara Ta fiye min ke sau dubu, And As from Today Naji Kin sake Kiranta Bazawara Ranki  Zaiyi Mugun ɓaci !,  Akanta Banƙi in Rabu dake ba,Dama albarkacin Ta kike ci"

Yafada cikin 6acin rai

Kallo tabishi dashi na yan daqiqu sannan tasaki wata bushashiyar dariya Wanda daga ji iyakarta fatar bakin

"Are You serious!, da gaske kake yi?, nifa matar ka ce!"

Guntun Tsaki yaja Ya maida Dubansa Ga Aeesh da Hawaye ya gama Wanke mata fuska, Dama Ta sani ,Tasan Labarin Sakin ta bazai Ɓoyu ba, Tasan Ashman Bazai taba gaya ma Deejah ba, Dole a Social media ta gani Ko kuma Kawayene suka Kirata Suka sanar da ita.

Tissue Ya yago ya share mata Hawayen ,saitin Kunnen ta Ya rada Mata

"Ki daina Kukan nan bana so, ko so Kike in Rama Abinda Kika mn Jiya?"

Saurin Girgiza masa Kai tayi a tsorace .

"Ok Tashi ki koma Room ɗinki”

Yayi maganar yana Manna mata kiss a Goshi .

Deejah ji Tayi Zuciyarta na barazanar Fashewa, Kishi da Haushin Aeesh na sake turnike ta


Miƙewa Aeesh tayi a sanyaye ta Koma Dakin da ta kwana Jiya, Deejah tabita da Kallo, Dole ta sace Zuciyar mijinta Her everything is natural.

Dubanta Ta maida Kan Ashman Dake Tattara Plates dinda suka Ɓata Hankalin sa a Kwance

"Baby  you don't Respect me as Ur wife!, ....like I don't Understand, You don't even Respect the fact that Am ur new Bride it's Too early For this..!and  We're Married!"

Ta ƙarashe Zancen da murya mai ban tausayi .

Dube Dube Ya farayi Kaman Me neman Abu kana Ya maida Dubansa Gareta Baki a sake

Cigaba tayi da fadin

"I can't Even imagine He bought his Brother's Widow into My House.."

Tarar Numfashinta yayi cikin yanayi na rashin Fahimta yace

"Hold on Babe..!, we're married or you are Married?"

Yayi maganar yana auna mata kallon rainin hankali.

Dif taji Komai nata ya tsaya , Kallonshi take a razane

Cigaba yayi da faɗin

"U Are ....!,abinda Ban gane ba Shine, You wanted this marriage , I gave it to you , So be the house wife that U wanna be and let me Enjoy my Life"

Kallonshi take a tsorace Hawaye na Diga Daga Idanunta

"Hey listen Listen...!, there's no Two ways about It!, I like u now and Forever ,but see nida Habeebty We have been Like this All over our life before u came into our life and u can't come yesterday and Expecting everything to change...!, And Kina Kiranta Da bazawara Gara ita nata zawarcin ango bai riga Ya shiga Daki ba, a yau idan Naga dama ,Zan Rabaki da Pride ɗinki in Kuma Sakeki, Just To change Ur name to Real Bazawara”

Ƙasa Cewa komai tayi tatsaya tana kallonsa cikin Firgici  zuciyarta na bleeding, duk Kalmar ta daya furta jinshi take kamar sukar wuqa a zuciyarta, Bata san haka ya tsaneta ba, Da Tasan alfarmar Aeesh ce yasashi Kulata da Ta haƙura dashi,Da bata Soshi ba tun farko.

Kuka sosai Ta fashe dashi Sosai tausayin kanta ya kamata

Taɓe baki Yayi yabi bayan Aeesh.

*Aeesh*

Tana Shiga ɗaki wayar hannunta ya hau ruri

Dubawa Tayi ,Sunan da ta gani ne yasata Fiddo Idanu Waje a mugun Mammakince

*Endocardiac* ta gani Sunan da Tayi ma Aareef Saving, Rabonda taji daga Gareshi har ta manta, Ko ta kirashi Baya dagawa Daga karshe ma daina samunshi tayi

Hannu na rawa Tayi Sliding Gabanta na Bugawa da karfi Ta Kara a kunne, Zazzaƙar Muryarsa ce ta doki Dodon Kunnenta cikin sanyi Yayi mata sallama
Amsawa tayi Cikin arawar murya da

"Wa'alaykumussalamu warahmatullah"

"A'isha Meyasa Kika Min Haka?"

Raunanniyar Muryar sa Ta doki Kunnnenta a karo na biyu.

Shuru Tayi Tana sauraron  Bugun zuciyarta Jikinta har  Rawa Yakeyi, Ji tayi Ƙafarta na neman Gaza Daukarta, a kasalance Tadafe Yar Ƙaramar  Stool din dake gabanta Ta zauna

"nayi Tunanin mu masoya ne na har Abada"

Muryarsa Ta sake Dokan Dodon Kunnenta Cikin wani irin rauni mai shiga zuciya

Gajeren numfashi yaja sannan Ya cigaba da faɗin

" Ban taba tunanin zan Wayi gari inji Anyi daurin Auren ki ba, A'ISHA a iya tunanina Soyayyata a Gareki tamkar Ruwan Teku ne ma'abocin Zubowa mara adadi, Amma ashe a iya ƙwaƙwalwarki nake ba'a zuciyarki ba"

Ya fada Emotionally A iya Muryarsa Kadai zaka iya fahimtar Tsantsar Raunin Da yakeji a zuciyarsa.

Qara tamke idanunta tayi trying so hard wajen controlling emotion dinta, Sosai kalaman Aareef ke neman sata kuka.

"Shin kin manta da Alƙawarin da mukayiwa juna tsakanin mu na cewan bazamu rabu ba duk rintsi Duk wuya?, shin Ko Kinsan Soyayyarki a cikin Zuciyata Tamkar Numfashina ne dake fita daga kirjina, wanda tsayawar sa daidai yake da mutuwa na?, shin Ko Kinsan cewa zan iya sadaukar da duk wani abu da na mallaka domin samar da farinCikin ki?, Shin Kinsan Cewa Rabuwa dake zai iya samar da gagarumin matsala a gareni?, Da ace Kinsan Wadannan abubuwa da Bazaki yanke shawarar zakiiya rabuwa sani ba domin yin wata sabuwar rayuwar ba"

Shuru yayi na Some seconds Yana Jan Numfashi ko ba'a Gaya mata ba Tasan Kuka yake yi,

Runtse idanunta tayi gam tanajin wasu irin emotions na building a zuciyarta Murya na rawa ta buɗe baki a karo na farko tace

"Sadauki Ka saurareni....., it's not my fault"

Katseta Yayi in his cracking Voice

"Aeesh Tabbas Ba laifinki bane, haƙika na Zargi Ƙaddara da Laifin Hada Mutane guda Biyu guri ɗaya bayan Sun san Bazasu Taɓa Kasance Abu daya ba, A'isha Meyasa Tun farko kika bari na shigo Rayuwarki bayan Kinsan ba da gaske kike yi ba Meyasa kika dandana mn Soyayyarki bayan Kinsan zaki iya rabuwa dani?, Meyasa kika koyar damu soyayyar da Bazamu Mora ba?,Meyasa kikasa Na aminta da cewa ke Masoyiyata ce ta Gaskiya?"

Shuru tayi, Ganin idan tace zatayi magana zata iya sakin kuka yasata hadiye wa Dakyar tana kokarin controlling emotion dinta amma her Emotion is so unbearable

"Lallai Na kwadaitu da kasantuwa Tareda Ke har tsawon Rayuwata, Amma saidai Ke wata Mace ce wacce ta rasa Gaskiya a cikin Rayuwarta, Kiyi Haƙuri wannan Itace fahimta ta a Gareki "

Wannan Karon Kasa Riƙe Kukanta tayi Sosai kalamansa ke Sukan zuciyar ta.

Shima Kukan Yakeyi Sosai Numfashinsa Har yana Fita daƙyar, Amma dukda Haka bai dakata ba Cigaba yayi da faɗin

"Nayi Miki takaicin Rasa Gurbin da kikayi a cikin Zuciya ta *A yanzu zan iya cewa mun rasa Juna kenan na har abada* "

"No Aareef Please ka saurareni....!"

"Me Zaki fada Min?, Na halacci daurin Auren Ki fa....!,Cikin Sabuwar Rayuwar da kika Shiga, ina fatan Ki zama mai gaskiya sannan Kuma ki zama Mai Bawa Soyayyar mijinki muhimmanci Akan Abin duniya , A matsayi na Na wanda Yasan Kimar so da soyayya nake Cewa mu kasance masu yiwa Juna fatan Alheri  Ina miki Fatan Alheri Tareda tayaki murnar Shiga sabuwar Rayuwa Nagode "

Duban Screen din wayar tayi  ,Hawaye na Gangarowa saman Kumatunta

"He ended the call...!"

Ta fada a bayyane Idanunta na cigaba da digar Ruwa

"Why Arrow Meyasa Zaka rabu dani?,Meyasa Zaka Yi Tunanin nice na kyale ka?, A tunanina nayi maka dukkan gatan da ya kamata Inyi maka ,Na baka komai da Kake bukata na zama Miji a gareni...!,and Meyasa Zaka yanke shawarar Rabuwa Dani?”

Ita kadai Take maganar tana latsa Numbern sa ,Amma in Kiran Ya shigo sai Yayi Rejecting daga ƙarshe ma kashe wayar yayi Gabaki daya .

Faɗawa Kan gado tayi ta saki Marayar kuka mai ban Tausayi

_Tunda ta fara Soyayya Take fuskantar ƙalu bale na Rayuwa Kala kala,tsakanin jiya zuwa yau taci karo da Tashin Hankalin da inda ace Batada Karfin zuciya da tuni Zuciyarta ta buga ta mutu ko kuma ta jawa kanta Wata gagarumin matsala, bata ga Laifin masu cewa soyayya

Please Login or Register in order to submit comment