Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

mata Surutu bayan Sunyi sallama da Aeesh taje duba Aareef.

Reey ta gaya mai taje duba Aareef,yasan Gidan Aareef don Babu nisa da asibitin shi, Babu ɓata lokaci ya nufi gidan, amma sai ya tsinci kansa da kasa shiga, ya tsaya chan gefe, ya dade a nan kafin daga bisani ya hango fitowan ta tana kuka.

Yana ganin Sanda ta tare napep ta shige tana sharar hawaye, yabi bayan su, mai napep na sauke ta ya sauka, amma ganin Zeeyk ya sha gaban ta sai ya dakata, ya kasa karasawa.

Jin Kalamanta yayi kaman Sukan wuka a zuciya, da auren ta akansa take ma wani ƙato irin wannan so haka?, Kenan bata damu dashi ba, akan Areef take zubar da ƙwalla?.

Yana nan tsaye Reeey ta dawo daga lectures ya tareta yace don Allah ta kirawo masa ita, tace Saƙo aka Kawo Mata daga Canada ,Ammin ta ce ta Aiko a bata.

Maganar yake mata kaman zaiyi kuka, duk yabi ya koma kalar tausayi, Jikinta a sanyaye ta gyada masa kai tace

"Ya Aash baka da Lafiya ne?"

Yay Murmushin yaƙe yace

"Me kika gani?"

"Naga ka koma wani iri, kalar tausayi"

Murmushi ya kumayi cikin basar da zancen yace

"Please kiyi sauri don Allah"

Gyada masa kai tayi maimakon ta shige sai ta kuma cewa

"Kunyi fada da ita ne?, Meyasa bazata fito ba sai an mata ƙaryata?"

Wani irin Kallo ya watsa mata ya haɗe rai, ba shiri taja kafarta ta shige ciki.

Tana isa ta isketa a kwance, ta tadata tace

"Ke banza kije waje AMMIE ,Ta aiko miki da saƙo"

Kallonta tayi a raunane cikin Fuskar bacci, take kalaman Aareef ya faɗo mata.

_she's the one I love_

_Ina Drugs buh saboda ita na fara Injectables, Nayi iya kokarina wajen Cireta a zuciyata, ki maye gurbin ta a zuciyata, amma Abin ya faskara ji nake idan ban same ta ba zan iya rasa rayuwata, ki taimaka Min kisa ta soni.._

Kuka mai karfi ya kwace mata, tsayawa Reey tayi tana kallon Ikon Allah baki sake tace

"Ke lafiya....?"

Cikin hawaye take girgiza mata kai tace

"Ba komai, ba komai"

Sai wani kuka mai karfi ya kwace mata, zama Reey tayi kusa da ita cikin tsantsan kulawa , ta dafa kafadar ta cikin sanyi tace

"Besty... something is wrong with you, ki gaya min me ke damun ki?"

Hannu tasa ta share hawayen ta

"Nace ba komai, babu Abinda ke damu na, kawai condition din Ammie na tuna"

Sai ta dau hijab dinta dake ninke ta saka, ta mike tana share ƙwalla

"Bari in karɓo saƙon Ammie"

Daga nan sai tayi gaba tabar Reey cikin nazari,har takai bakin ƙofa sai ta juyo tace

"Meyasa bai baki Saƙon ba?"

Reey ta kauda kai tace

"Anturo saƙon ne da hoto, Kinga dole sai an ganki"

Fita tayi , Reey tabita da kallon tausayi ,,don dukda bata san dalilin kukanta ba, tanada tabbacin Aareef nada Alaƙa da zubar hawayen ta.

Shuru tayi tana nazarin yanayin tafiyar ta, da alama akwai abinda ya faru da ƙafar .

Tana fita daga chan nesa kadan ta hango Wani na daga mata hannu, yana sanye cikin baƙaƙen kaya, da wani Jibgegen cardigan Da hular sanyi, fuskar sa manne cikin baƙar face mask.

Gabanta taji ya fadi Saboda ƙamshin turaren Ashman da taji ya baje ko ina.

Ciki a sanyaye Ta ƙarasa wajenshi.

Yana ganin Fitowanshi Shima yaji gabansa ya fadi sai yaga ta kara Kyau, sai dai she looks unhappy, ya zama dole yasan meke faruwa don ya takama Areef burki y daina shiga rayuwar ta.

gaishe shi tayi kan ta a ƙasa, ya ciro wata yar box ya miƙa mata batareda ya amsa Gaisawanta ba.

Ta daga hannu zata karɓa jikinta na rawa, yasa dayan hannunsa yayi saurin kama hannunsa.

Saurin dagowa tayi a gigice daidai lokacin da yasa dayan hannun ya yaye facemask din Fuskar sa.

*Saleem*

Safa da marwa yake tayi a tsakar falon, hannuwanshi goye a bayanshi, sai cijen lips yake yana huci

Kallo daya zaka yimashi kasan yana cikin tsananin ɓacin rai.

Tsaki yasake ja a karo na ba adadi.

"Kai impossible wlh!" Yafada cikin qaraji.

"Da Aure na a kanta ta fita da wani ƙato a gabana?, Wlhy bazai yiwu ba saina koyawa yarinyar nan hankali"

Ya kai zancen yana fidda huci kaman Wanda ya hadiyi taɓarya.

Ƙara kai dubanshi yayi ga agogon dake manne a hannun shi, 10:17.

Tsaki yaja cikin talauci ya dau wayarsa , ya danna ma Zeeyk kira, bugu daya ya daga cikin masifa yace

"Ina matata?"

"Bata dawo bane?"

"Kai ya kamata nay ma wannan tambayar"

"Ikon Allah bari na gwada Layin su mama inji ko lafiya?"

"Good for you , listen na Baku nan Da 20mins inaso Inga matata a gidana, if not dukkanku Sai ranku ya ɓaci cikin daren nan, kuma idan haka ake Zuwa gaida uba kun kashe kasuwar gobe"

Daga nan Ya datse wayar cikin huci, Aikam yana dire wayar ko ida sata a aljihu baiyi ba saigata ta shigo fuska a kumbure ,Yawo sukaje itada bamalli, basu dawo ba sai gabda magrib, lokacin daddy ya tafi, Sai kuma ga Shuraym Nan fa suka sha hirarsu, sai bayan Isha'i ya tafi.

Aikou tace tafaga gidan zama babu inda zata koma, da ƙyar mama ta lallaɓata ta Koma don Bata so Yaron nan yazo ya buga mata hauka.

Gyara tsayuwar sa yayi yace

"Ke daga ina kike?"

Banza tayi masa ,ta zauna kan cussion tana ƙoƙarin cire takalman ta, ya daka mata tsawa

"Nace daga ina kike?"

Nan ma ko Motsa wa batayi ba ,ballantana tanuna tasan yanayi.

Ransa ya sosu sosai, ya damƙi wuyar rigarta da Ƙarfi yana huci idanunsa Tuni Sun Kaɗa sun Koma kamar wuta.

“nace daga ina kike?, Don't allow me to repeat my question Again"

A tsiwace tace

"Cikani"

"Don't Allow me to repeat my question! Again daga ina kike"

Ya fada yana huci kaman mayunwacin zaki.

"Repeat your question ban jika ba"

ta fada hankali kwance.

"Dan u**nki Ina kikaje?"

yafada yana sake shaƙota da iya karfinshi.

"To ai ka maimata tambayar ka mallam, Wai ya haka? Ka sakarmin wuya mana"

Sake hado wuyar rigar ta yayi da wuyan ta ya shaƙota ,ido rufe cikin tsananin Kishi da Ɗacin rai.

"Uban wa ya baki umurnin Fita yawo da wani ƙato?, Bayan kinsan kina da aure?"
Injishi yana huci

Tsayawa tayi tana kallon Karfin Hali, aurenshi har wani abin azo a gani ne? Da zaibi ya tada hankalinsa don ta fita da wani?.

"Ina Ruwanka da Rayuwa ta?" Maryam ta fada tana matse idanu sbd shaqarar da Saleem yayimata.

"Dan u**anki daga yau na soke fita a gidan nan, ko mutuwa ubanki zaiyi in an kaishi saidai ki ga kabarin shi a waya don Ko taaziyya Bazaki ba, Winch Yar talaka"

"To sakeni mana in tafi"

Sakinta yayi yana galla mata Harara.

"Ki shiga kitchen ki hada min dinner"

Ya fada cikin tsare gida.

Gyara wuyar rigar ta tayi, ta rama hararar da yay Mata, ta kwashe takalman ta a hannu Tayi hanyar dakin ta tana fadin

"A hungry man is Always an angry man, find your Winch Yar talakawa Tazo ta maka girki Ni ba Baiwarka bace"

Ta fada Cikin Daga murya.

Biyota yayi da gudu, tayi saurin shigewa tasa sakata ta ciki.

Ta shafa wuyarta da tasha Shaƙa Taji wurin yayi tauri don azaba

"Allah Ya Isa mugu kawai"







Nayi gabas🚶🏻‍♀️

I Heard that you All miss me 😍

Nima I missed u more than u do😍😍😍😍😍😍😍😍

Na dawo kenan inshallah no going back.

Inaso kuyi Surprising Dina da Awesome comments of yours😍😍😍

17th October


Bintou ✍️
[10/27, 10:11 PM] Bintou abdool: *WUƘA A ZUCIYA*

(BLEEDING HEARTS)


*041*





Ta daga hannu zata karɓa jikinta na rawa, yasa dayan hannunsa yayi saurin kama hannunta.

Saurin dagowa tayi a gigice daidai lokacin da yasa dayan hannun ya yaye facemask din Fuskar sa.

Zaro ido tayi cikin ƙoƙarin ƙwace riƙon da yayi mata, yasa dayan hannun ya riko duka hannayen ta sosai.

Cak ta tsaya jin ya riqomata hannun duka.

Tsayawa tayi batareda tayi yunƙurin kwace wa ba gabanta na faduwa.

"I miss you" yafada ahankali

Shiru tayi kanta a ƙasa.

"I know I wrong you but, Please find a place in your heart to forgive me , i'll be grateful no matter how smaller the space is"

yafada emotionally.

Shiru tayi bugun zuciyarta na qaruwa sosai, she's feeling somehow, tanajin wani iri sosai, ba ta san Dalili ba,Aduk lokacin da yayi mata ba daidai ba duk girman Laifin da yayi mata bata iya riƙe shi na tsawon lokaci ,da tayi ido hudu dashi take rasa nutsuwanta.

"Please give me a chance to Crown my self on your Throne"

yasake fada still riqeda soft hannunta yana ɗan murzawa a hankali .

Sake duƙar dakanta tayi tana jan karamar tsaki

"Idan ka gama, Free my hand I have Alot to do"

tafada muryarta nadan Shaking.

Shiru yayi yana kallonta na wasu seconds sannan ahankali ya sake matsa hannayen ta cikin nasa, wannan karon har tsakar kanta taji wani abu ya Ratsa ta.

A tare suka sauke wani ɓoyayyen ajiyar zuciya, duban Idanun ta dake kallon ƙasa yayi yace

"Fushi kikeyi dani ko?"

Shuru tayi masa kanta a sinne, ya gyara tsayuwar sa

“By the way ,Daga yau ,bana so na sake ganin kin kula guy dinnan *Aareef* , kinji."

"If I may ask why?" ta dakatar dashi lokaci daya ta dago Rinannun idanunta da suka fara tara ruwa batare da ta yadda sun hada ido dashi ba, ta kuma cewa

"If not what will happen?"

Ta fada a tsiwace, tana kallon cikin gefen sa amma a dan tsorace

Cikin mamaki ya dinga kallon ta,Binta yayi da kallo saikuma ya kalli hannunta dake riƙe cikin nashi.

"Let's end this" yafada ahankali.

"A yau dinnan zan kawo karshen komai" yafada yana kallonta.

Shiru tayi tana kallonshi batareda ta iya cewa komaiba don bata Fahimci inda zantukansa suka dosa ba.

"Ki nemi letter da na baki Ranar daurin Auren ki da Saleem Ki karanta"

Yafada tana dan janye hannunsa kadan

"Ni mijinki ne, It might sound crazy but Baffa da kansa ya daura mana Aure kafin ya ras...."

"Hey...malam dakata mana"
Ta dakatar dashi ta kwace hannunta da ƙarfi.

"Kada kayi masa Sharri...!,baffa ya rasu!, "

Ta fada slowly Hawaye na taruwa a idonta ta girgiza kanta sadly.

"Ka karbe budurcina, Wannan baiyi maka ba yanzu kuma so kake ka alaƙanta Ni da matar ka?, so kake in baka hadin kai mu rinƙa Aikata badaidai ba da sunan aure??"

Lumshe idanunta tayi, ta Bama hawayen ta damar saukowa.

"Don Kaga Baffa ya rasu shiyasa kake neman ka kafa hujja dashi ko?"

Tsareshi da ido tayi tana kallon yanda mood dinsa ke chanzawa cikin hawaye tace

"Kada kayi tunanin Rabani da budurcina da kayi kaci bulus Ka jirayi sammaci daga Kotu ,Sai na kai ƙarar ka an yanke maka hukunci mafi dacewa dakai"

tafada tana dan janye ido ganin yadda ya kafeta da idanu.

"Did you hate me?" Ya tambaya cikin wani yanayi.

Kallonshi tasakeyi sannan ta kauda kai tasa bayan hannu ta share hawayen ta.

"Tell me, kin tsaneni ko? Kinaji kamar ki kasheni ko?"

Ya tambaya yanajin Heart din shi na pumping abnormally.

Tasa bayan hannu ta share hawayen ta, Ta daidaita tsayuwar ta, ta dubeshi cikin ido batare da shakka ba ta bashi Amsa.

"Yeah I hate you"

Saukar dakansa yayi ya ciji lips dinsa da ƙarfi, ba haka yaso Ta kasance ba, baiso abin ya juye masa ba, shuru yayi yana kallonta for some seconds

"Ihty Ni zaki kai kotu?"

Ta turo baki hawaye na bin fuskar ta , a hankali tace

"Eh din "

"Okay you can go, idan haka kika fi so"

Sake turo baki tayi, ta sake share hawayen ta, sannan ta dago jajayen idanunta ta dubeshi

"Ashman Tell me ,me kake so?"

"I want you Back as my wife "

"Ta ya ake sauya Haram zuwa haram?"

Ya girgiza mata kai

"Baya Sauyuwa"

"Kaman yanda na kasance haramtacciya a gareka"

Rintse ido yayi da ƙarfi , baya Son Tuna wannan kalmar Tana sashi jin Wani iri kaman bashi ba, sauya maganar yayi cikeda tausayi ta

"Ihty your Relationship was unhealthy to you, cutar dake yake"

Ta Dakatar dashi tareda tsareshi da mayattun idanunta

"But am not complaining ...!, Let me be wai meyasa kake Son takura wa rayuwata ne?"

"Because I love you"

Ya fada Emotionally ,ji tayi kalmar ta shige vein dinta direct, ya rarrabu ruwa Arteries dinta take kalmar ta rarrabu cikin jinin jikinta ya fara yawo ta ko'ina.

Qwalalo watery eyes dinta tayi ta dubeshi unbelievably

Dagowa tayi tana kallonshi in shock.

"You love me?"

"Yeah, starting from your first breath, and I will continue loving you till your last breath!"

"Really? How? When?, Why?, Saboda kasan privacy dina?"

Tafada cikin mamakin da ya kasa barinta

"No kafin Abin ya faru,I don't know how why and when ba .. all i know is Ina sonki, I gave you all I have because of love ,I Care for you because I love you"

Kasa cewa komai tayi, ta saki baki tana kallon sa cike da mamaki, zuciyar ta kou kaman ana tsare, Tuni hawayen Idanunta suka kafe

Ya miƙa mata box din da ya kawo mata

“take this box ,it Explains everything''

Harara ta Galla masa gabaki daya jikinta babu inda baya kyarma, kalaman sa sun Sacar Mata da Gaɓɓanta .

"You know what?Am done here ok?"
Ta fada in her Cracking voice.

Ya dakatar da itada cewa
"So you're walking Out on me?"

Saida tayi taku biyu sannan ta tsaya batareda ta juyo ba tace

"You're not ready to be submissive, I can't continue listening to ur trash any More"

Daga nan tayi wucewan ta tana hawaye.

Ta barshi nan tsaye kaman wanda aka dasa Duƙar da kansa yayi a zuciyar sa yace _Idan nayi wasa Ƙadangare yana gabda min Kafa, bazan iya cigaba da Ɓoye aurena da ihty ba dole na sanar da Abba , asan yanda za'a yi a maida min matata_

Shiga motarsa yayi, ya figeta da ƙarfi, ya bar makarantar Kai tsaye office din ABBA ya nufa.

Yauce rana ta farko da ya taba taka ƙafarsa cikin asibitin Abba, tun bayan Shekaru Ashirin kenan da Wallafuwar ta.

Yanda ake bashi labarin Asibitin, sai yaganshi a zahiri ya zarce hakan , tangamemen Asibiti ne kaman a ƙasar Turai ,tsarin su ma ba irin namu bane.

Ko ina zagaye da jami'an tsaro sai kace gidan Yari , ga na'urai masu Matakan tsaro ciki harda wadanda bai taba gani ba.

Saida akay masa Screening wajen Biyar kamin daga Bisani a barshi ya shiga Office din.

Yana Zaune a inner office dinsa yana duba patient dinsa dake main office.

Kai tsaye ciki ya shige

"Sannu Dad"

Dagowa ABBA yayi daga computer da yake Dannawa a hankali yasa hannu ya zare farar Glass dinsa ya dubeshi a kaikaice

"Son yau kaine dakanka a asibiti na?"

"Eh Abba dama wani abu nazo na sanar dakai"

Yayi maganar yana Gyara tsayuwarsa

"Bismillah ga wuri ,bari nasa A kawo maka Mocktail your fav"

Ya fada yana nuna masa Kujera tareda daga telephone da niyyar kira a kawo masa

"I don't need it"
Ya fada yana ƙara matsowa gabda teburin gabansa.

Sake nuna masa seat ABBA yayi

"Then Sit down"

"Ba zama nazoyi ba"

"What happened"

Ya furzar da numfashi ya dubeshi kai tsaye yace

"Dad Aeesh Mata ta ce"

"I know , Yaya Imaam shi ya daura Auren"

Baki sake Ashman ya dinga duban Abba

"How comes....?"

Taɓe baki Abba yayi Yana maida hankalinsa kan system dinsa.

"I have evidence and everything"

"But Dad why did you Keep it with you Allowing me suffering?"

Batareda Abba ya dago ba ya bashi Amsa

"Because you didn't deserve her, Aeesh tawace Idan Ban same ta ba saidai duk mu rasa, wani ya aureta ba kaiba”

Kallon mamaki yabishi dashi cikin rudani

"Are you still on your point?"

Dagowa ABBA yayi ya Gyada masa kai, yana sake balancing a katafaren Kujerar sa.

"Yeah, na gommace Saleem ya dawo da Matarsa akan na bari ta zauna dakai"

"What...!"
Ashman yayi Exclaiming cikeda tarin takaici.

Daga masa kafada Abba yayi hankalinsa kwance yace

"Yeah very soon xansa ya maida matarsa"

"Dad why did you hate me that much?"

Murmushin manya Abba yayi

"I don't hate you ..son da nake maka ne yasa naji bazan iya sharing choice da kaiba"

Cikin Kankanin lokacin gabaki daya Ashman ya gama fita cikin Hayyacinsa,jin kalaman Abba yake kaman sukar mashi a zuciyar sa, ashe dama duk zaman da yayi yana riƙon Abin a ransa Abba nada masaniya?, Tho meye ribarsa don Ya Raba sunan, bayan kowa ya shida babu Aure a tsakanin shi da ita!.

Cikin Rudewa dakyar bakinshi ya iya haɗo iya kalmar

"Dad what did u mean"

Cikeda izza dad yace
"I mean nothing but an everlasting Happiness for you ”

Ashman ya girgiza kai cikeda yanayin tausayi yace

"But you took away my happiness , Dad so kake zuciyata ta buga na daina numfashi?”

Kai tsaye Abba yace

“da hakan Zata kasance da Nafi kowa murnar Haka, ASHMAN a halin yanzu rayuwar ka bata da wata Amfani A gareni"

Innalilahi Wainnailayhirraji'un Wannan wace irin Masifa ce?, Wane laifi ya taba ma Abba da zaisa yayi deserving mutuwar sa akan Rayuwarsa?, Meye Amfanin rayuwar sa idan Mahaifinsa na Masa fatan Rasa Rayuwar sa?

Duƙawa yayi har ƙasa ya rarrafo on his knees Ya kamo ƙafarsa Cikin tarin tashin Hankali ,cikeda juria yake rokonsa

"Don Allah dad idan wani laifi nayi maka ka yafe min,bazan iya juran jin irin wadannan Kalaman daga bakin ka ba"

Cikeda izza da isa Abba yace

"Then ka rubuto mata takardar ta,in ba so kake Nima zuciyata ta buga ba"

Dago jajayen idanunsa yayi, ya diresu Akan Abba duk ya koma kalar tausayi

"Dad is that what u want?"
ABBA ya Gyada kai
"Yeah..."

Shuru yayi yana share gumin da suka cika masa fuska.

''But she's My Life koda na saketa bazan iya rabuwa da ita ba"

Tunda yafara yake kallonshi babu kyaftawa yanajin zuciyarsa na melting don ganin zallar shauqi dake tattare dashi.

Kallon pleading face dinshi yayi data koma abin tausayi Sai ya nuna masa hanyar fita

"You can Go”

Jiki ba ƙwari haka ya miƙe jiri na kwasan sa ya fice daga Office din

Binshi da kallo yayi tayi zuciyarshi na bugawa da qarfin gaske, tabbas idan ya raba Ashman da Aeesh Da gaske Ashman zai iya rasa rayuwar sa akanta, ba ƙaramin Abu zaisa Ashman ya fiddo sirrin da ya adana a zuciyar sa ba ,a iya sanin shi da Ashman Bai taba sa abu a zuciya ya fitar ba, duba da baƙar Zurfin Cikin da yake fama dashi.

Sai gashi yau shi da kansa ya fiddo abinda ya dade a ɓoye a zuciyar sa, bayan nan har da bayyana Masa yanda Yake ƙaunar Aeesh, wanda kou ada Ko wuƙa za'a sa a makoshin shi ace ya Fadi yanda yake jinya a ransa cewa zaiyi baya sonta, kallon Yar uwa yake mata...

*Aeesh*

Reeey na kwace tana chat sai faman Murmushi take da Alama tanajin dadin chat din sosai.

Da sallama ta shigo ta zauna gefen Rug tana share hawayen ta

ta gefen ido Reey ta kalleta kaman ta shareta, sai ta kasa ,ta ajiye wayar tace

"Besty ya tafi ne?"

Gyada mata kai tayi, Hawaye na bin kuncinta.

Cikin sanyi Reey ta sake ambaton sunan da ta saba kiranta

"Besty"

"Na'am"

Ta amsa A sanyaye

"What's wrong?"

Ta girgiza mata kai

"Nothing!"

"Yaushe kika fara ɓoye min Abinda ke damunki?"

Shuru tayi

"Me yaa Aash din yay miki?"

Shiru tayi nan ma yaona jin zuciyarta na wani iri , gyara zaman ta tayi, tadubi Reey sannan a hankali tace

"Besty in tambaye ki?"

"Ina jinki"

Ta amsa tana kafeta da idanu

Ajiyar zuciya ta sauke tace

"Please zuciyar Mutum Zai iya kamuwa da Soyayyar mutane biyu a lokaci Ɗaya?"

Shuru Reey tayi tana kwallon ta, sannan cikin rashin fahimta tace

"As in...?"
Sake maimata tambayar tayi

"Shin As in Mutum daya zai iya Son Mutane biyu at the same time ,kuma Real love irin wanda nake ma Aareef?"

Shiru tayi tana tunani saikuma tace

"Uhhmm....Gaskiya A'a Amma kafin nace wani abu meyasa kikace haka?"

Lumshe idanunta tayi ,tana jin zuciyarta wani iri cikin sigar raɗa tace

"I feel Lonely without him, he wrong me but my heart need Him back😭"

Kallon mamaki Reey tayi mata
"Wa kenan?"

"Ahky"
tafada tana kallonshi tanajin hawaye na neman taruwa a idanunta

Kama hannunta Reey tayi cikin nata tace

"What did you mean?"

" I love him..."

tayi maganar kusan cikin rada

Dago fuskarta Reey tayi ds tafukan hannunta ta kalleta da Surprising idanunta.

Aeesh Ta Gyada mata kai

"more than Everything, akoda yaushe da tunaninshi nake kwana nake tashi, and at the same time zuciyata na bugawa ne aduk sanda na tuna Aareef Am confused I don't know who I love "

Wani Murmushi mai haɗe da dariya Reey ta saki

"Are You serious?"

Wasu zafafan hawaye ne suka gangaro suka wanke mata fuska,Cikeda tausayin kanta take share hawaye Tana shesseƙa, Reey itama ji tayi kamar itama tayi hawayen, idanunta itama sun Kada

Dagowa tayi ta kalleta taga itama ita take kallo, sai kuma Wasu sabbin hawayen suka balle mata, she's Confused Tana neman Mafita in ba haka ba Zuciyar ta gab take da Bugawa

Murmushi Reey tayi mata daidai saukar wani hawayen saikuma tayi saurin sharewa da bayan hannu.

Murya a dishe Aeesh ta cigaba da cewa

"And he confessed that he love me too bayan a gaban Jama'a yayi rejecting Dina Yace Ni haramun ce a gareshi ”

Ajiyar zuciya Reey ta sauke jiki a sanyaye, lamarin Aeesh yanzu ya daina bata Haushi ta koma tana bata tausayi , Soyayya na wahalar da ita, ta daina ganin laifin ta, laifin zuciyar ta ce ,zuciya wacce ba'a iya sarrafa ta.

Cikeda karfin hali tace

"Hmmm Gaskiya besty Babu Abin rudarwa anan abu ne da yake a bayyane, Ashman shi yafi dacewa dake , Zuciyar ki zata iya kamuwa da Son Mutane fin dubu a lokaci daya, Amma soyayya kala-kala ce mai yiwuwa kowanne da Irin Son da kika masa, da farko dai babu wanda zai ganki yaga Dr yace babu Komai a tsakanin ku!, Akwai strong bound a tsakanin ku, soyayyar ku cike take da shauƙi Wanda abinda kika rasa kenan a soyayyar wannan Shasahsahan Arifu"

"Dama kin san ina son Ya Ash ne?"

Harararta tayi
" Ko makaho ya ganku ya san ku masoya ne, Munafukan masoya Zura Muku Ido nayi naga iya gudun ruwanku, manafukai”

"Amma zuciyata tafi ƙaunar Aareef"

"Ke wlhy idan baki daina ambaton sunan wannan shasahsahan ba saina zabga Miki Mari, Ana nuna miki gaskiya kina taketa ke a dole sai kin kama gaibu, Soyayyar ki da AAREEF ba mai Amfani bace, Akwai cutarwa babu shauki ko kadan a cikinta, nifa gani nake kaman Shasahsahan ba sonki yakeyi ba, Akwai Manufar sa na Ɓata lokacinki, kiso Yaa Aash kiji dadin rayuwa bani zan sanar dake Irin Kulawar da zaki samu daga Gareshi ba,tun tasowar ki kika taso da saninshi ya baki kula iri iri in different ways , Bakida Uba Bakida Uwa ya maye miki gurbin su a lokaci ɗaya, a bayyane yake soyayyarsa akwai shauƙi a cikinta idan kikayi kuskure kika gujeshi zaki zama marainiya"

Harara ta Galla Mata da jan tsaki
"Mtswww, tun yaushe kuma?, dama ai Ni marainiya ce bani da uba ba uwa, Ni ai tunda ya furta baya sona a gaban dukka family na fara Ƙoƙarin cireshi a raina, ko yanzu da Yace yana sona nasan ba son tsakani da ALLAH Bane, akwai abinda ya dandana Yaji shi da garɗin da bazai iya rabuwa dashi ba shi yasa Ya dawo min domin ya cigaba da kwasar Banza"

Hannayen ta dukka biyun tasa ta Shafo Hawayen da suka ɓata mata fuska, taja numfashi tace

"A halin yanzu Areef dina ya fiye min shi sau dubu, zan iya jurar rashin shi ,i wanna move on with my Life"

Da idanu Reey ta bita ,tana kallon Zallar rashin hankali, cikeda takaici ta budi baki zatayi magana

"M...."

Ta dakatar da ita ta hanyar daga mata hannu

"Please don't interfere, it's my life"

Babu yanda Reey ta iya dole ta kyale ta, ta cigaba da sabgar gabanta.

Da ƙarfi sarah ta Danno ƙofa tana haki kaman an biyo ta tana zabga sallama,Amsawa duk sukayi hankalinsu na komawa kanta

"Sister Juwee, Aeesh guess what?"

Zura mata ido duk sukayi batareda sun ce komai ba, kowanne cikeda da takaicin banko ƙofar da tayi

"Your exams Time table is out, senior year BNSC (Nursing) you're starting by next week"

"What How comes iwk Reading break?"

Inji Reey

"There's no break it is written lectures will continue "

Inji sarah

Reey ta dage kai cikin damuwa

"Ya Salam Why ,Meyasa duk wata mugunta a Nursing department ya ƙare ne?,Meyasa Sauran Dept din ba'a masu haka sai mu?"

Qumshe Dariya sarah tayi tana rufe bakinta da tafin hannunta

"Sis ba Mugunta bane, It's concerned with your Professional Ethics..."

Wani kallo ta watsamata tace

"Ethics my foot...!, Akanmu aka fara nursing ne?"

"Kaman yanda ba'a kanku suka fara haka ba”
Inji Sarah

Harara Aeesh ta Galla Mata

"bar nan"

Da sauri tabar dakin tana cigaba da qumshe dariyarta

Kwafa tayi sannan ta gyara kwanciyar ta cikeda takaici.

Kalaman Ashman na Cigaba da ratsa ko ina na cikin Jinin jikinta

Da zarar ta Lumshe idonta,sai ta hango labbansa sanda Suke furta Mata kalmar YANA SONTA.

Ko kadan maganar Exams Bai dameta ba ,tunaninta gaba daya ya rajaa kan soyayya.

*United kingdom*

Home Library

Ko'ina zagaye yake da littafai kala kala ta kowane fanni, Ga Uban computers dake Jere a kowane kusurwa na dakin, Kallo daya zakai ma dakin ka fahimci cewa Mai Amfani da dakin Kwararriya ce wajen bincike da karatun Litattafai.

Zaune take sai faman danne danne take a system dinta ,Alhaji Faisal na zaune kusa da

Please Login or Register in order to submit comment